Labarina complete - Chapter 5
Labarina complete Chapter 5: Labarina complete Chapter 5. Bude idon ta tai a hankali kamata yai ya zaunar da ita sannan ya samata pillow a bayan ta sannan…
1,010 words
Bude idon ta tai a hankali kamata yai ya zaunar da ita sannan ya samata pillow a bayan ta sannan ya hada mata shayi yana bata a baki har sai da ta koshi ya miko mata magunguna ya bata ta sha tun da ta tashi yake mata sannu yayi ta yafi a kirga,ina so nayi sallah ta fada temaka mata yai ta tashi ya kai ta toilet da kan sa yai mata alwala sannan ya kamota ya sa mata hijab sallar ma a zaune tai tun dg azzahar har isha'i sannan tayi shafa'i da wutiri tana idarwa ana fara karaye shima alwalar yai yazo yana jera nafilfili haka har akai asbah sannan yai tai makata ta kwanta shi,sai da gari yai haske sannan likita yazo ya kuma duba ta,sannan ya fita yai ma wata nursa magana yace ta kula da ita kan ya dawo Ok badamuwa sai ka dawo shigowa tai ta zauna suna dan taba hira har bacci ya gaba da ita, shi kuma yaje office yai complain daga nan yaje gida yai wanka ya debo mata kayan da zata sa, Sai da ya fito Palo sannan ya kula da inda kwalbar ta fadi ta fashe durkusawa yai yana kallon wajen har yayi baki alaman acid ne ya zube lallai Angelina bayan dukan da kikai mata har kinso ki illata ta,Kwafa yai sannan ya gyara wajen cikin hanzari,yai sauri ya gama ya koma asibiti,
Ya dawo yai ma nurse godiya ga wannan ya miki mata kudi aa ka barshi ae aikina ne eh na sani kawai kyautace na baki ta karba nagode sannan ta fita,
Sai da tai Kwana biyu a asibitin sannan aka basu sallama,
Koda suka dawo wata irin kulawa yake bata sabida doctor yace ta daina wayan aiki da zai sa ta gaji, Komai shi yake mata har tausayi yake bata,
Yau Sati daya da sallamo ta suna zaune a Kasan carpet yana mata tausa a kafafunta dear sannu da kokari ya dago ya kalleta da akai me fa da irin abinda kake min mana,ja mata hanci yai yace in ban miki ba wa zan ma, Dazu kana wanka mukai waya da umma tana gaishe ka na ma kira hajiya tace Kwana biyi baka kirata ba lapiya,me kika ce mata cewa nai aiki ne yai ma yawa a office yawwa dan bana son kowa yasan baki Ji dadi ba sabida kat hankalin su ya tashi, turo kofa akai aka shigo tunda ta shigo nake kallon ta sai a sannan shima ya juyawa Ke me kika zo yi min a gida,
Durkusa wa tai tana bashi haquri,shutoff yace mata cikin tsawa bata re kuka zo gidan ba tare muka zo ta fada muryarta na rawa,ban san abinda zata yi ba Ke nan nadai haka tace nazo muje muga matar ka,kuma ni na hanata zuba mata acid din da zata yi,
Naji ya fada yana tsareta da ido yanxu tana ina tunda abin ya faru ban kuma zuwa gidan ta ba,amma nasa in take tana ina ya fada da sauri nan take ta fada masa.cikin azama ya tashi zai fita na kira swthrt ina zaka zanje naji dalilin da yasa tazo har gida taimika haka kayi haquri ka dawo ka kyaleta ko gama fadan banyi ba ya fita sai na dawo,har ya fita ya dawo ya dau jakar ta ya fita da sauri
Ya bar mu nida Mary sannu madam ta matso daf dani ta rike hannu na tana bani haquri komai ya huce,Karki damu suka cigaba da hira sama sama can ta tashi ta tafi,tace zata dinga xuwar min in bata da skul nai mata godiya ta fita,
Shi kuwa yana zuwa kofar gidan ya danna door bell zai kuma dannan wa aka bude, Halfbest da wani mini skirt a jinka ta, tana ganin sa gaban ta ya fadi zata rufe Ke nan ya hankadata ya shiga ciki sannan ya rufe kofar je fa mata Jakarta yai sannan yace me yasa kika je min gida har kika taba min mata,zata yi magana ya Dakar mata bakin ta to yau ko ubanki wane a garin sai jikin ki ya gaya miki ta juya zata shiga daki a guje cikin zafun nama ya zanyo gashin ta da karfi ta saki kara,kafa yasa ya hankada faduwa tai kan ta ya bugi center table,ball ya kuma yi da ita taje ta bugi kofa sabida a zaba kasa kuka tayi, betl din jikin sa ya jaro ya fara dukan ta da wajen kan tun tana kokarin guduwa har takasa shi kuwa beda na dukan ta ba sai da ya gaji sannan yace kya kuma karambanin zuwa gida na sai na miki wanda ya fi wannan,karuwar banza ya fita ya barta ya kuma targaden da yai mata,
Sai da tai wajen awa a haka kamin wata kawarta ta zo ta kwashe ta tai asibiti da ita,
Cikin ta yakai wata bakwai zai shiga na takwas su zaune a Palo suna hira,albishirin ki tace goro yace next month zan gama aikin da nazo yi,da sauri tace haba yace eh mana amma baza mu koma ba sai kin haihu tab ae kuwa koda baka gama ba a gida zan haihu a nan wazai kula dani, Nuna kan san yai gaba ni ba dariyata tace da anyi danyen jego,
Tun dg wannan lokacin kullum sai sun fita tayi exercise daga nan suje suyi siyayya,tun tana zabar kaya ita da baby har ta daina dan siyayyar daya ke yi tayi yawa, Sai da cikin ya shiga wata na tara sannan zasu dawo rananr da zasu tashi farin cikin ta ya kasa boyuwa,
Haka Mary da abokan sa suka rako su airport suka shiga jirgi dgan nan sai Nigeria, jirgin na sauka ta tashi da dasauri ya riko ta haba starshine Ke ko Nayi jikin ki bakya kawai so nake naje naga umma a haka suka fito yana rike da ita har inda mutane suke suka kara sa wajen Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Arewa hausa novels Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO: +2347039625239