Kenza eBookz

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 13

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 13

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 13: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 13. ya kai hannusa saman sumar kanta data zubo baya batare da…

3,318 words

ya kai hannusa saman sumar kanta data zubo baya batare da yace uffan ba, numfashi ta sauke tana cigaba da kallonsa tayi imani bancin nuzla data dawo rayuwarsa da yanzu ita dashi sun zama abu daya ,bakinta ta kai daidai lip's dinsa ta fara tsotsa yaso ya hanata amman ya kasa hanata dan yana matukar jin dadi “wani numfashi yayita saukewa da sauri sauri ."wani irin kissing take masa tun yana iya daurewa har ya fara mayar mata da martani yayinda koina ajikinsa ya soma rawa tunda yasa mu ya cafke bakinta yaji komai ya sauya masa karo na biyu kenan da yake rasa gane kanshi sakamakon kasancewarsu tare ."

sosai yake juya harahensa abakinta jin yana ta'bo wasu wurare ajikinta yasa tayi qoqarin zare bakinta ya riketa gam aranshi yake cewa "karki min haka please ki cigaba da kasancewa dani sake qoqarin zarewa tayi tare da yunkurin mikewa taji hannunsa abayanta ya rike kugunta gam "zan tashi !"ta fad'a kwayar idanunta cikin nashi ."na rikeki ne ? ya fad’a yana lumshe idanunshi ta kai hannunta saman hannunsa dake rike daita, numfashi ya sauke da karfi sannan ya zare hannunsa yana sake lumshe idanun ta mike tsaye da kyar tare da juyawa zata bar parlour’n ."

Ya gyara zama yana dan bud'e idanunshi sosai yana kallon yadda take juya mazaunanta ,tafiyarta ma kawai abun burgewa ne uwa uba bare akai ga lafiyayyun nonuwa bombom tamkar wanda aka dasa mata su ahankali yake jin kamar yana murzasu anya kuwa bazan hakura da matata na bar nuzla ba ?" yayiwa kanshi tambayar yana kallon yadda gabansa ya mike sambal ,sosai kwakwaluwarsa ta shiga tunani yayi imani ko mumynsa zata bari ya auri nuzla ba yanzu ba to kuma shi haka zai yita zama yana cutar da kanshi abanza , gashi baya neman mata bare yace yana da gurin zuwa ya rage zafi ."

Da misalin Karfe takwas na dare ATA na zaune yana amsa waya mb ,maryam ta qaraso inda yake tana cewa “yaya Adam sannu da hutawa "yayi mata banza ya cigaba da wayarsa "na kawo abincinka nan ne ?" yayi mata banza "bari na zubo maka abinci still banza yayi mata, taje ta zuba masa ta kawo gabansa ta ajiye "ga abinci dan Allah kaci ko kad'an ne "ke dole ne sai naci abincinki ko daman ina cin abincinki ne ?"ta girgiza masa kai"to maza ki tattara ki bar nan dashi bana bukata "haba yaya tun da na tare a gidan nan baka cin komai dana girka ba "meye zanyi da wani mugun abincinki .?"

"Allah kaci kaji zakaji dadinsa ya kwabe fuska Kmr yaga wani mugun abu "maggie zanci naji dadi ?numfashi ta sauke sannan tace "ka ci kaji idan bai maka ba sai ka barshi na sake dafa maka wani .” shiru yayi dan ya soma gajiya da magana "bud'e bakinka na baka to "Oh my god sweetheart me yasa kika had'ani da maseefa ?me yasa kika hadani yarinyar da zata kasheni da damuwa ? Nace bana bukata sai kace dole “ ya fad'a yana dafe goshinsa ."

cikin rawar murya tace "me nayi da zan kasheka da damuwa ?"ni bance zaka kasheni da damuwa ba sai kai ?"wai dan girman allah me nayi maka ne da ka tsani ne haka ka tsani duk wani abu daya dangan ceni ?ya tsaya cak yana kallonta a dage."dan girman allah ka daina tsanata ka barni naji da damuwata domin zuciyata tana cikin tsaka mai wuya ".nan take ransa ya qara 'baci zuciyarsa ta soma tafarfasa sakamakon jin maganganunta wasu marasa Kan gado bai san lokacin daya ya soma mgn cikin zafin zuciya ba "ni zaki fad'awa kina cikin tsaka me wuya ?tayi shiru tana zubar da hawayen bakinciki "

"Dole na fad'a maka domin kai kafi kowa cancatar na fad'awa dan Allah ka bar zuciyata haka nan ta huta , ka kalleni da kyau ya Adam kallo d'aya zaka min ka fahimci bana cikin kwanciyar hankali da walwala tun daga ranar da aka sheida min sakon mami akan aurenmu ban sake samun isashen bacci da natsuwa ba "me yasa haka ?"me yasa na rasa duk wata natsuwata da kwanciyar hankalina ?"

Wani kaskance kallo yayi mata mai firgitarwa wanda yasa tayi shiru ta kasa cigaba da maganar ta qara shiga tashin hankali mai tsanani shiru ne ya ratsa parlour'n bata sake cewa komai ba kamar yadda shima bai sake cewa komai ba har tsawon minti biyar suna zaune kafin daga baya ya motsa labbansa muryarsa a tsarke yace "karki yi kuskuren kamuwa da soyayyata domin muddin kikayi haka hakika kin d'aukarwa zuciyarki wahala “dan kuwa mummunar ciwo ne zai kamaki a karshe ki rasa rayuwarki gabad'aya ,gara ki cigaba da rayuwarki haka batare dani ba domin ni a kowani lokaci zan iya rabuwa dake saboda nayi matukar tsanarki ."na tsaneki ina sake fad'a miki na tsanakeki ".yana gama fad'ar haka ya mike tsaye ya barta ya haye sama cikin sauri sauri yake taka step ."

kuka maryam ta fashewa dashi tana cewa "ya allah idan wani laifi nayi ma yaya adam yasa hankalinsa bai kaina ya allah kasanyaya zuciyarsa ,allah ka sani ina tsananin son mijina ta yadda bazan iya rayuwa idan babu shi ba ,allah ka sanyaya zuciyarsa akaina ,allah ka juyo min da hankalinsa gareni ka bamu zaman lafiya tana kuka wayarta na ringing wanda kuma tasan nana hauwa'u ce amman ta kasa d'auka domin dai kota dauka daga mata hankali zatayi kawai da kyar ta mike ta nufi dakinta ta kwanta lamo tana neman mafuta akan zamansu .”

Sosai zuciyarta da kwalkwaluwarta suka shiga tunani “Ya kamata yaya Adam ya dandani zafin so ko dan yasan martaba da kimar son da take masa,” to me ya kamata nayi “? ta tambayi kanta “dan dole akwai bukatar na tashi tsaye na kwatarwa kaina yanci a wajensa shiru tayi “tana son mijinta bazata iya rabuwa dashi ba ,dan ko da wasa bazata iya furta masa ya saketa ba sannan bazata iya ta’ba bashi damar ya had’ata da kowace mace ba taya kenan zai d’andani zafin so bare yasan darajanta ."?”

Zumbur ta mike zaune “dawa ya kamata nayi wannan shawara “?nan take kwalkwaluwarta ta bata amsa da “sister mana ita kad’ai ce zata baza baki shawarar yadda zaki yi ta mike ta isa inda ta ajiye wayarta ta soma kirata alokacin tana zaune a parlour’n tare da yaya hisham tana shirin mikewa domin ta shiga dakinta ta amsa wayar yaya hisham ya zame ya kwanta akan cinyarta yana d’auka remut dole tasa wayar a silet dan karta damesa ta cusa hannunta cikin sumar kanshi tana jin sanyi aranta dan batayi tunanin zai kwanta a saman cinyarta ba duk tunaninta barin gidan zaayi yaje gurin nuzla .”

Ahankali ta cigaba da shafa sumar kanshi ta d’an kai bakinta daidai kunnensa sai da ta sakar masa murmushinta sannan tace “abinci fa ?wani zazzafan numfashi ya sauke yana qara narkewa akan cinyoyinta masu laushi da kyar ya fixgo magana “zanci sai na gama kallon new’s “yayinda maryam sai faman kira take baa dagawa “oh my goodness wai me yasa sister bata daukar waya ne ?ita kanta nana hauwa’u tana son ta d’auka amman bata son ta damu mijinta kuma bata son yaji abinda zata fad’a sai dai hankalinta ya rabu gida biyu wani yana tare da mijinta wani kuma na wajen maryam bini sai ta kalli screen din wayar taga kira na cigaba da shigowa a karshe dai yaya hisham yace “lafiya ?”

“Me ka gani ?kamar baki da natsuwa wake kiranki ?” ”maryam ce!” ta bashi amsa atakaice ya d’ago idanushi ya tsura mata “ki d’auka mana kika san damuwar da yayanki ya qunsa mata take son tayi magana dake “shiru tayi dan ita kanta tasan haka ne amman dan kawar da maganar tace “kai yanzu tunaninka kenan amman lafiya lau suke zaune “ “taya za’a zauna lafiya da wannan yayan naki mai shegen taurin kai kamar na kafuran farko .”

A firgice nana hauwa ta kallesa “kina kallona karya na fad’a ?tasan gsky ya fad’a amman meye na sake fad’a mata ?ta sake duba wayar zata mayar ta ajiye ya karba ya d’aga tare da sakata a hands free nan take muryar maryam ta bayyana cikin fashewa da kuka “sister ina kika shiga ne tun d’azu nake kiranki ina cikin damuwa “wallahi zuciyata kamar ta fashe ki bani shaawara ya zanyi da yaya Adam wallahi idan aka cigaba ahaka komai zai iya faruwa dani “.

“Sister !”nana hauwa ta kira sunanta “ina jinki sister ina bukatar ki bani shawara sister yaya zanyi da yaya Adam ya zaayi ya dan dani zafi so ?ina son yaji zafi da ciwo kamar yadda nake ji ,sonshi yayi min yawa “ murmushi nana hauwa tayi “wannan kuma ai abinda muka dade dasan ne kece daman kika kasa yarda da hakan “maryam bata san sanda hawaye ya zubo mata ba tace “amman kisan cewa yayi kar na kuskura na kamu da soyayyarsa domin muddin mayi haka na d'aukarwa zuciyata wahala “dan kuwa mummunar ciwo ne zai kamani a karshe na rasa rayuwata gabad'aya ,gara na cigaba da rayuwata haka batare dashi ba domin ni a kowani lokaci zai iya rabuwa dani saboda yayi matukar tsanata ."

Yaya hisham yayi saurin runtse idanunshi yaji zafin kalmar ahankali yaji zuciyarsa na yi masa zafi kamar zata fito waje tausayin maryam ya kamashi Yayinda nana hauwa tace “subhallah gsky yaya Adam bai kyauta ba sam abinda yake baya kyautawa amman ki bari zamuyi waya zuwa gobe yanzu bani kadai bace “tana gama fadar haka ta katse wayar gbdy “kinga irin muguntarsa ba wallahil azim adam mugu ne sam sam zuciyarsa babu imani bare tausayi babu imani acikin zuciyarsa “yana gama fad’ar haka yaja tsaki ya mike tsaye ya shige d’akinsa .”

Nana hauwa tabi bayansa da kallo tasan yayanta bai da kirki amman me zasu iya yi akai ?”yayyunta ma baya jin maganarsu bare ita da ko kusa da inda yake bata isa taje ba matsawar bashi ne ya bukata ba .”tana zaune yaya hisham ya fito da key din motarsa ya nufi kofar fita “ta mike da sauri tana cewa “ina zuwa kuma ?fita zanyi baka ci abinci ba fa?ya juyo ya tsaya tare da tsura mata ido kawai yana qare mata kallo batare da yace mata komai ba kafin daga baya yasa kai ya fice daga parlour’n ya barta tsaye cikin tashin hankali dan tasan wajen nuzla zashi zama tayi tare da zabga tagumi .”

*******

Tashin hankalin da ba'a sa masa rana wayewar gari yau din nan subaia suka tashi da mutuwar mahaifinta sosai suka shiga tashin hankali ita da kannenta wanda baki bazai fad'a ba tabbas rayuwarsu zata sake shiga cikin matsala babba yanzu saura abinda ya rage masu mahaifiyarsu ce itama kuma ba wani isashen lafiya gareta ba lallai suna cikin tsaka mai wuya basu da mataimaki sai allah shiyasa sunyi kuka kamar me maryama taje ta kuma ta tausaya mata matuka dan tana tausayin kanta amman idan ta tuna rayuwar subai'a sai taga gara ita akanta from rich to poor is not easy .”

a bayan can mahaifinsu mai arziki ne sai dai bai yiwa kanshi tanadin komai ba har zuwa lokacin da yayi accident ya samu matsala a bayanshi ."alokacin da yake tsaka da jinya sai yayi tunanin da zaman da yake na rashin sanin ranar warkewarsa mai zai hana bazai hada kwssamominsa da abokansa guda biyu ba tunda shi bazai iya komai ba su kuma daman ba wani samu suke ba kusan a karkashinsa suke samu alhj sani da alhj dan umma ,tofa tun daga wannan lokacin daya hadasu komai ya sauya agareshi domin kuwa babu abinda ya biyo baya sai danasani dan kuwa tunda suka fara samun kudi suka juya masa baya basuyi tunanin su taimaka masa ba.”

tun suna masa naci har yazo ya gagaresu sai rufin asiri allah mahaifinsu na cikin wannan halin mahaifiyarsa ta kamu da hawan jini ga diebites daman tana dashi , shekaru biyar yayi yana jinyar sai yau rai yayi halinsa aunty tazo da ummah zaune su subai da kanneta suke wajan gaisuwa amman da ka kalli fusk'okinsu kasan suna cikin rud'u da tashin hankali ."sai dai fatan samu sausauci daga Allah.”

Ranar asabar da misalin karfe tara na safiya bayan an shirya komai na bangaren umma tsaf yayinda aunty salma tayi duk wani shiri domin janye zuciyar yusif ta hanyar malaminta ya koma kan soyayyar daya daga cikin yayanta , kausar data gama gaisawa da umma ta fito neman maryama tana kwance acikin kalubalin rayuwa da yake zuwan mata lokaci lokaci ita gbdy ma data sanin girmanta take domin gara tana yarinya radadin rashin mahaifi ne kawai Ke damunta da kuma cin zarafin yan gidansu amman bata taba kwana da abinda Ke daga mata hankali har ya hanata runtsawa ba ."

Da gudu kausar ta fado kanta tana cewa masoyiya I miss you a lot duk da halin qunci da take ciki bai hanata nuna mata itama tayi farinciki da zuwanta ba "wallahi gidanmu kullum zanceki muke kowa mamaki yake wai yaya yusif yaga mace Kuma yana sonta har kuma ya kasa samun sukuni saboda ita tayi shiru kawai domin neman take ta daurawa zuciyarta damuwa acikin kahon zuciyarta domin dai ita tuni ta rufe babinsa da komai rayuwarta kawai take "dan Allah masoyiya ki tashi ki shirya yana parlour'n umma nasan ke kadai yake jira ."

Maganarta ta bata mamaki to idan haka ne ina batun baba gali da yace yusif din ya amince da auren shikura abbanau ya yarda da batun da baba yaje masa dashi maryama batayi nauyin baki ba kamar yadda ta saba tace “ai ina ganin Ke akwai abinda bakisani ba kausar ta kalleta cikin rashin fahimta tace "kamar me fa ?bayan tafiyarku baba yace sunyi magana da abbanku an maida wa yusif shukura amatsayina “kausar ta zaro ido tace "saboda ana hauka Ke waya ya fad'a miki wannna" baba !"

Sakina da shikura kuwa duk wani abinda ya Kamata aunty salma tayi masu wanda zasu jewa yusif dashi dan hK suka shirya cikin hadaddiyar kwaliya mai daukar hankali suka dauki abinda aka tanada domin shi suka nufi bangaren umma yana zaune jin tafiya yasashi fad'a da murmushinsa har wani mikewa yayi amman ganin sabanin abinda zuciyrsa Ke mararin gani ya dauke idanunshi daga kallonsu sukai sallama cikin siririyar murya tare da durkusawa suka ajiye mishi farati gabanshi suka zauna "ina kwana ya kuma hanya ?”ya dan kallesu "sannna ya tsaida kallonsa akan sakina yana cewa "kece sakina ?"

"Eh nice tayi mgnr tana sunkuyar da kanta "sannuku da kokari atare suka sakar masa wani kayataccen murmushi "me mukayi na Godiya batare da ya kalleta ba yace “ya cancanta na gode tunda kunyi aikin da baku ya kamata kuyi ba maryama ta baku wahala domin wannan aikinta ne tazo gareni da abinda zan saka abakina idan ma da hali ta ciyar dani” gbdy jikinsu yayi sanyi ta gyara zama "ai ya cancata muyi maka haka ya dan gyara zama sannna ya fuskancesu da wani iyayi da suke masa "akan me kenan ?sukai shiru hankalinsu ya soma tashi "tabbas wannan mutumin mai wuyar shaani ne idan da hali ma suce masa dan wulakanci, akace daya daga cikinmu zata iya maye gurbin maryama a wajenka ko baa fad’a maka bane .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 9

"Yusif ya d'an yi dariya kad'an sannan yace "saboda kuma kawai a garin mahaukata ake sai ku maye gurbinta? " maye gurbin maryama ko mace' yar kasar england ce maryama tafi gabanta awajena ." Jikin a sa'bule suka d'an yi shiru daga bisani shukura tace "amma baka san cewar akwai wanda yake son maryama ba har ma ana shirye shiryen kawo kudin auren ta?"wani mugun harara yusif ya buga mata yana d'aga kafad'unsa alamun ko ajikinshi ."

Ta sake bud'e baki zatai magana a fusace yace,"Ku dan Allah ban son sakarci da iskanci banza ku ta shi kuje ku sanar da maryama dominta kawai na zo gidan nan ba dan wasu 'yan iska ba ,ta yi sauri tazo ta samar da nutsuwa acikin raina ita kad'ai zuciyata Ke muradin son gani baku marasa kamun kai ba"

sakina da shikura sukai shiru suna kallonsa tare da jinjina girman wulakancinsa, yayinda zuciyar shukura ke qara lissafo mata abinda zata sake fad'a masa amman ta kasa domin tsoron amsar da yusif din zai bata "lallai wannan ba wanda zasu zo suyiwa wargi bane, dole sai mahaifiyarsu ta sake shiri akanshi atare suka tashi jikin babu kwari suka fice daga d'akin cike da 'bacin rai ."

Aunty salma na zaune tana tunanin ya yusif zai kar'bi ya'yanta sai gasu sun shigo mata rai 'bace ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mike tsaye da sauri cike da fargaba duk da dai bata da já akan aikin malaminta tsayawa tayi tana kallonsu d'aya bayan d'aya kafin daga baya tace "yana ga kun dawo min jiki a sanyaye .?"

"wallahi mama wannan mutumin mugun d'an wulakanci ne na bugawa a jarida nan shukura ta zayyane wa aunty salma komai daya faru cikin 'bacin rai sakina tace ,"ni dai gsky mama ki hakura ki barwa maryama yusif ta aura tunda ya nuna ita din dai yake so bashi da abinda zai yi damu ita kuma shukura sai ta auri malam yahuza " .bayan aunty salma ta gama jin abinda ya faru tas da abinda sakina ta fad'a tace "bazaa hakura abar mata shi ba wannan auren muddin ina raye sai anyisa da d'aya daga cikinku ."

"to gsky mama ni dai banda ni sai dai ki aura masa shikura taje can su qarata dan bazan iya da wulakancinsa ba "na gode sosai yar'uwa dan dama zuciyata tana cikin d'ard'ar ne kar shirin mama yayi tasiri akanki gashi daman dani yafi dacewa tun dana d'aura kwayar idanuna akanshi na kamu da matsanancin qaunarsa "inji cewar shukura ".

"yauwa shukurata nasan bazaki ta'ba bani kunya ba daman kuma kamaninmu d'aya "haka ne kuma dole halinku yazo d'aya ba" sakina ta fad'a acikin ranta sannan fili tace "yar wahala sai kije kiyita fama amman kisani bazaki ta'ba daraja acikin idanunshi ba karshe ma ki qarasa rayuwarki a wahala "tana gama fadar haka tasa kai ta shige d'akinsu ta barsu tana jin babu dadi aranta duk da ahalin yanzu babu wani shakuwa da soyayya a tsakaninta da maryama amman a wasu lokutan tana jin babu dadin abinda mahaifiyarta take mata ."

"Kece yar wahala daga nace ina son shi sai Kiyi min mummunar fata in sha allahu akanki zai qare "aunty salma taja hannun shukura zuwa cikin d'akinta tana cewa "manta da sakina muyi abinda Ke gabanmu "ta saki hannunta ta qarasa gaban wasu kwanuka ta bud'e d'aya daga ciki ta d'auko tandun kwalli ta mikawa shukura tana cewa "ungo nan shukurata maza ki shafa wannan kwallin à idanunki" shukura ta kar'ba ta soma qoqarin shafawa yayinda aunty salma ta juya da sauri ta sake d'auko wani qaramin gwan gwani wanda Ke d'auke da wani bakin magani ta sake dawowa inda shukura take tsaye ta miko mata hannunta d'aya tana cewa "bani kwalli ki bani tafin hannunki idan yasan wata ai bai san wata ba zai san dani yake ".

Cike da farinciki shukura ta mika mata tandun kwallin sannan ta mika mata tafin hannunta kamar yadda ta buqata cikin sauri ta zuba mata bakin maganin tana cewa "ki fad'i sunansa sau uku sannan ki fad'i duk abinda kike son yayi miki idan kin isa gabansa ina mai tabbatar miki bazai sake miki mutsu akan komai ba sai akan abinda kika fad'a masa zai yi aiki dashi kuma zai bi umarninki ."

Readers Also Read