Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 12
Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 12: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 12. Ta juya ranta a matukar bace yace “idan kina shiga harkata…
3,277 words
Ta juya ranta a matukar bace yace “idan kina shiga harkata zan iya sallamarki aiki , akwai wata mace ne bayan nuzla acikin zuciyata da zaki zo kina wasu surutan banza ?tsaki yaja ya fara duba file din data ajiye agabansa .”tana fita daga office din hisham office din abdull ta shiga tana kiran sunansa “abdull !! “menene ?ya tmbyeta tare da barin abinda yake ya dago ya zuba mata ido “wai me abokinka ya taka akan wannan banzar yarinyar nuzla ne da zai iya ciwa kowa mutunci akanta wai me tafi sauran mata ne ?kaga irin wulakanci da yayi min yanzu saboda suna yin waya daita “kinsan me ?ta girgiza masa kai alamun tana jinsa “hakuri zakiyi zakiya dan wannan yarinyar itace muradin ransa dan ko matarsa baya sakewa daita akan wannan yarinyar kuma bata son yana muamula da kowace mace “ai kuwa wallahi tayi kadan dan bata isa ta hanashi muamula da kowa ba .”
“Ita din me ? sannan akan me ?to sai dai idan a gidinta zai tare ko kuma ya cicibota ya dawo daita office dinsa inyaso duk abinda yake tana gani ko kuma ta dinga binshi duk inda za shi .”yayi murmushi yace “ko dai kina kishi daita ne naga duk kin damu ?”“kishi ?meye tsakanina da hisham da zanyi kishi akanshi bayan aiki da kuma dangantar dad dinsa da nawa ?”kawai dai wallahi naji ina tausayin matarsa ne yarinyar kirki ce ga hankali ga ladabi shine kawai nake tausaya mata saboda nasan duk lokacin daya auri wannan banzar yarinyar ina tausayawa rayuwar matarsa duk da nasan yarinyar nan bazata yarda ta auresa ba wata manufa gareta .”
“Me yasa kika fada haka ?ince guduwa tayi lokacin da zaayi aurensu dashi sannan yanzu ta dawo masa ai kasan akwai abinda take nufi dashi wallahi , wakilla haushi taji dan ya auri nana hauwa’u kawai ta dawo ta hanashi zaman lafiya da matarsa kuma tasan idan batayi amfani da karfin soyayyar da yake mata ba bazata yi galaba akanshi ba shi kuma dake qaramar kwakwaluwa ce dashi yake wani biye mata yarinyar daya kamata yaci ubanta laada waje “. Abdull ya sake yin murmushi wanda dagani na takaici ne “ kinsa me ? kije kawai Kiyi aikinki zai fiyye miki amman hisham kam bai ji bai gani akan nuzla bancin nasan gidansu nuzla basa biye biye da ni kaina nace anyi masa wani abu ne “.
“gsky kam amman ni matarsa nake ji ka duba kaga ranar d muka je gidansa baka ga yanayinta ba kamar tana jin tsoronsa komai a dar dar take yi shi kuma ko kallon biyayyar da take masa baya yi sai ma wayar da yake da wannan banzar yarinyar ina ma ni ya samu da naci ubansu daga shi har ita “gsky nana hauwa’u bazata iya ba Ke dai zai fi kiyi abinda Ke gabanki sarkin shiga abinda babu ruwanta “kana ji ko abdull “dan allah Zakiya kije na gaji da mgnr hisham nayi masa mgn har na gaji idan zai canza ya canza idan bai zai canza ba tare dani allah zai wa hukunci ba daga haka bai sake cewa kala bata juya ta bar office din cike da takaici .”
Qarfe biyar daidai motocin ata suka shigo gidan yayinda maryam ke zaune a parlour’n kasa cikin tsananin tashin hankali tana waya da nana hauwa’u “wallahi sister duka fa kwanaki biyu ne kawai nayi acikin gidan nan amman ji nake tamkr a makabarta nike zagi kuwa acikin kwanakin nan sai dai kawai nace Alhamdulillah ,shi kawai baya ganin abubuwan da yake min kuskure ne shi kawai kanshi ya sani eh ko jiya ya sha yanzu haka ma cikin matsala nike dan daren jiya na kwashe kwalin sigarin na zubar a shara ashe da saura aciki kuma yace lallai sai na dawo masa da abunsa ,ni yanzu tashin hankalina na aika a siyo masa sigarin baa samo exactly irin wanda yake sha ba ….”
“Shiru tayi sakamakon turo kofar parlour’n da akayi idanunta data zubawa kofar suka sauka akanshi sanda yake qoqarin takuwa ,sosai ya dauki hankalinta koda yaushe fuskarsa tashi a daure take kallo daya yayi mata ya janye idanunshi akanta “sannu da zuwa” ta fad’a a matukar tsorace tana qoqarin mikewa ta bar parlour’n tun kafin ya soma cin ubanta , bai amsa ba yace “me na fad’a miki ?bana ce karki sake na dawo na ga wannan fuskar ba ? ya qara taku biyu taja baya da sauri “dan allah kayi hakuri ta fad’a cikin tsananin tashin hankali“.ina sigarina ?”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 8
A matukar razane maryam take kallonsa jikinta na wani irin rawa idanunta suka canza kala sakamakon hawayen data soma d'an taruwa acikin kwayar idanunta cikin tsananin fad'uwar gaba maryam tace "ga ..gashi can akan table sai dai ba'a samo exactly irin ..."sai kuma tayi shiru ta kasa qarasa maganarta dan tasan me karshen maganar tata zata janyo mata, ta tsura masa ido kawai tana cigaba da kallonsa hawaye na gangaro mata akan kuncinta ."
"exactly irin me ye ba'a samu ba ? yayi maganar a tsawace yana sake had'e fuska "ta runtse idanunta gam hawaye masu zafi suka biyo kuncinta "irin wanda kake sha né ba'a samo ba "me yasa ba'a samu irinsa ba ?"ya tambayeta yana tsareta da tsuma mmun idanunshi masu matukar firgitarwa "tayi shiru tana kallonsa hawaye na faman turereniyar zubo mata "nima ban....ban sani ba ?"ta fad'a a muryarta na rawa tana share hawayenta da hannunta d'aya tare da kai tafin hannunta daidai saitin zuciyarta dake beating very fast ."
Tsumammun idanunshi ya ware sosai akanta yaga yadda ta qara shiga tashin hankali wanda hakan Ke masa dadi, a duk lokacin daya ganta cikin damuwa yana jin sukuni aransa, wani abu ya had'iye mai d'aci a makoshinsa kafin ahankali ya motsa lip's dinsa da kyar "babu ruwana ki nemo min exactly irin sigarina shi nake bukata kuma a yau dan kinsan halina sai dai ki bawa wani labari ,ban ta'ba d'agawa kowa kafa ba kuma bazan fara akanki ba yana gama fad'ar haka ya juya a zafafe ya soma d'aga kafafunsa zai haye sama ."
jiki a sanyaye ta qara taku biyu tana wasa da yatsun hannunta tace "wallahi yaya Adam ban san yadda zanyi a samo maka irinsa ba sai dai kayi hakuri ka aika wanda ya saba zuwa inda yake siyo maka ko kuma kayi amfani da sauran na jiya ."wanda kika zubar a shara kike nufi ?ya juyo a fusace tare da fad'ar haka, taja baya da sauri tana gyad'a masa kai gabanta na dukan uku uku "you are very stupid ,ki nemo min ko kuma inci ubanki acikin gidan nan yau ."
"Ubana kuma !?"yes of course ubanki ko zaki rama ne da kika tsaya kina tambayata ?ta sauke numfashi tana girgiza masa kai "okay ki nemi min abata kuma irin wanda kika wulakanta min “cikin kasa da murya tace "ni dai gsky ban san yadda zanyi ba kai dadin me ma kake ji a shan sigari abinda zai cutar da kai ?” ”ni zaki fad'awa haka ? kanta ta gyad'a masa alamun Eh !to ai gsky ne me zakayi da wani sigari abinda yake saurin kashe mutun "are you out of your sense ?."
"ni kike fad'awa haka "? shiru tayi tana tunani amsar da zata bashi wanda kafin nan idanunta sun sake kawo hawaye tace "yanzu meye illar maganata bayan gsky na fad'a maka "?"Are you mad ?"da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a "okay iskanci ne kenan yasa ina magana kina magana ?"ta sake girgiza masa kai idanunta na kawo ruwan hawaye domin dai gbdy a tsorace take dashi ,maganar ma allah ya sani dauriya ne kawai take yi da kuma son rage tsoronsa dake kunshe a zuciyarta ".
cikin rawar murya tace "am sorry"!da sauri yace "sorry for your self "amman dai kuma kasan shan sigari yana da matuqar illa sosai arayuwar d'an adam "so what? ina ruwanki da rayuwata ?gabanta taji yayi mummunar fad'uwa ta shiga girgiza masa kai hawaye na sake fita daga idanunta ."ahankali taga ya soma takowa zuwa inda take tsaye yana mata wani mugun kallo ."nan da nan jikinta ya fara rawa ganin idan ta tsaya kanta zata cuta yasa ta juya da sauri ta fad'a d'akin dake manne da parlour'n ta murd'a key ."ta jingina bayanta da kofar ta tsaya tana sauke numfashi.”
A zafafe ya qaraso jikin kofar ya tsaya tare da runtse idanushi kafin ya dunkule hannunsa ya kai wa kofar naushi yace "me yasa kika gudu baki tsaya ba kiga yadda zanyi dake shasha duwaf din banza kawai ?” ”wallahi wallahi da kin tsaya da sai na karya miki kafa sai dai uwarki ta haifi wata mai kama dake nonsense "muryarta a sanyaye tace "kayi hakuri dan allah bazan sake ba ."yana jin yadda take kuka take bashi hakuri tana tsaye kusan minti biyar dafe da saitin zuciyarta dake bugawa da sauri sauri , taji alamun tafiyarsa amman ta kasa fitowa har sai da minti biyar ta wuce bata sake jin motsinsa ba hakan ya tabbatar mata ya bar gurin .”
ta bud'e kofar ahankali ta fito tana maida numfashi tare da goge hawayenta ta hau sama, ahankali ta sanya kai cikin d'akinsa ta leka tsaye ta samesa ya bawa kofar baya hannuwansa hard'e a saman faffad'an qirjinsa sai huci yake fesarwa tmkr zakin daya nemi abincinsa ya rasa ,gefe guda kuma duk ilahirin gashin dake kwance a jikinsa sun mike tsabar bala'i ji tayi kamar taje ta rungume shi ta baya ta sake bashi hakuri ya sauko dan bata son ganin yana fushi most especially daita ."
Wani dogon tsaki yaja yana sauke hannuwansa ya rike kugunsa da hannu d'aya acikin ransa yace "wannan wace irin jaraba ce ?yarinya kamar mayya duk abinda zai mata bata damuwa ko ya zagi uwarta ya zagi ubanta duk a banza baya mata ciwo sai dai tayita bashi hakuri "ya fahimci mugun hakuri ne daita ,kuma shine dalilin da yasa mahaifiyarsa tayi masa sha'awar aurenta" tsaki yaja ya soma cire kayan jikinsa ya fad'a bathroom ya sakarwa kanshi ruwa ya fito ."
Bai sauya wasu kaya ba vest da boxcer kawai ya saka ya kwashi wayoyinsa guda biyu ya sauko zuwa parlour'n kasa ya zauna ,ya d'auki remut ya canza channel sannan ya d'auki wayarsa ya soma danne danne yana duba sakwani mutane ringing din waya ne ya karad'e parlour'n ya bar abinda yake yana yatsina fuska alamun qarar na damunsa ko ba’a fad'a masa ba yasan qarar wayarta ne ,can gefen kujera ya hango wayar yashe tsaki yaja , ya d'auke kanshi ya cigaba da abinda yake yayinda aka cigaba da kiran wayar ,qatar wayar ta dameshi sosai gashi kuma shi bazai ta'ba iya bud'e bakinsa ya kirata ba ."
cikin haka ta sauko ta shiga kitchen ta soma fito da abubuwan da zatayi amfani dashi na girki wayarta ce ta sake d'aukar qarar sauti ,ya tsaya cak ya bar abinda yake ransa na qara 'baci ,da d'an saurinta ta fito tana goge hannunta da towel ta soma duba inda wayar take ta d'auka taga sunan mahaifiyarta ce ke yawo a screen din wayar tayi shiru ta kasa d'auka a gabansa ,ta d'an d'ago ta kallesa taga ita yake kallo ta qasan idanunshi "nan take gabanta ya shiga fad'uwa "mummy ce "ta fad'a muryarta na rawa."
" yasan zaa rina dan zata fad'a masa ko wacece ta kira ,tsaki yaja "na tambayeki ne ?ya fad'a yana sake jan wani tsaki "naga kana kallona ne shiyasa nayi tunanin ko kana neman qarin bayani ne "akan me kenan zan bukata ?duk ma wanda zai kiraki ya kiraki mana menene matsalata da hakan ?kai kuwa kake da matsala dani tunda zamanka nake "ta fada tana tsura masa ido taji abinda zai sake fad’a ."bai sake cewa uffan ba yayi tmkr bai ji abinda tace ba ta juya ta koma kitchen ta kira layin mahaifiyarta tana aiki suna waya daita wanda duk hirar akan zaman aurenta ne ."
******
Da misalin karfe shida daidai hisham ya shigo gidan a gajiye a parlour'n gidansa ya zauna yana sauke numfashi nana hauwa'u dake zaune cikin tsananin tashin hankalin abinda zai faru tsakanin maryam da yayanta tai masa sannu da zuwa babu yabo babu fallasa ya amsa yana furta "wash allah ! sannu ka gaji ko ?girarsa ya dage mata alamun “eh ! ko cikakken minti biyu bai yi da zama ba nana hauwa'u ta mike tsaye tana cewa “bari naje na kawo maka ruwa mai sanyi kasha ya juya "tafiyarta yabi da kallo ,yadda take jujjuya jikinta yana ta’basa.”
Daman kuma ba tun wannna lokacin ba yasan tana da kyawun jiki sosai fiyye da maryam dan tana da tsawo sosai , gyara zamansa yayi ya cigaba da kallo every step of her , .”ya runtse idanunshi sannu ga ruwa kasha da alamun ka gaji dayawa yau "ta fad'a tana miko masa cup ahankali ya bud’e idanunshi yana kallonta sannan ya karbi cup din hannunta alokacin da wayarsa ta fara ringing ,ya ajiye cup din ruwan akan table din gabansa ya ciro wayarsa a gaban aljihun rigarsa yana duba screen din wayar ." ganin mai kiransa ya d'auka da sauri yana cewa "hello my dear "
Wani irin bugu qirjin nana hauwa’u yayi da karfi ko baa fad’a mata ba tasan ko wacece ta kirasa ta samu waje kusa dashi ta zauna tare da janyo kafafunsa ta d’aura akan cinyarta ta soma mammatsa masa “ no no!! your time is my time my time is your time am always with you,kowani lokaci naki ne karki damu am always with you my dear ai tunda nace miki zanzo zanzo ne bari na dan watsawa jikina ruwa ,ko banzo yanzu ba zan shigo da daddare "tunda ya cigaba da wayar ta kasa cigaba da massaging din da takewa lafafunsa ta janyo wayarta tana neman layin maryam taji yadda suka qare da yayanta .”
Kira kusan biyar tayi mata bata d’aga ba yayinda hisham ya cigaba da wayarsa da nuzlah yana fad’a mata kalamai masu sanyi da sanya natsuwa wanda hakan yasa nana hauwa’u ta soma jin wani iri aranta zuciyarta ta dinga tafasa tana mata zafi da ciwo ,nan da nan yanayinta ya sauya haka ma kwayar idanunta ta cika da ruwan hawaye sai dai duk yadda taso ta danne amman sai da sheshekar kukanta ya bayyana "ta fara gajiya da wulakanci da yaya hisham yake mata, wallahi gara ya aro nuzla din su zauna tare da su taru su kasheta da bakincikinsu ."
runtse idanunta tayi gam tana zubar da hawaye tana sake zurfafa tunaninta " bata son ta sake masa magana akan nuzla tunda sun rigada sun gama mgn akanta sai dai duk da hakan bai kamata ta dinga d'aukar wulakanci har haka ba "wani bangare na zuciyarta ya fad'a mata haka ,ahankali ta girgiza kai sakamakon wankakkiyar zuciyarta dake bata shawara "kema ya kamata ki sake tuntubar mumy ta amince ya auri nuzla a wuce gurin ,ai kuwa gara ki tursasa mata ta amince da haka akan wannan wulakanci da suke miki, dan kuwa da zarar sunyi aure shikenan wasu abubuwa dole zasu ragu tana kallonsa ya sauke kafafunsa ya mike tsaye ya shige d’ayan parlour’nsu ."
ahankali ta dinga share hawayenta tana rarrashin kanta "meye dan ya wulakantaki ya kaskantar dake a karkashinsa fa kike ai wanda ya isa akewa haka dan allah nana hauwa'u ki sanyawa zuciyarki hakuri ki daina nuna damuwarki daman tare kika gansu dan haka ki kawar da idanunki akansu sosai ta bawa kanta hakuri kafin daga baya ta tashi ta nufi hanyar parlour’n daya shiga ta iskesa zaune yana cigaba da waya ta durkusa a gabansa muryarta a sanyaye ta kira sunansa "yaya hisham !bai amsa ba illa tsura mata ido da yayi yana kallonta "ban san me yasa ba amman ina jin kamar nayita kuka ina baka hakuri akan abinda nasan ba laifi nayi bane ."
" ina matukar tausayawa kaina a yanzu yayinda nake jin nadamar aurenka da nayi arayuwata ". jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta karye da jin abinda ta fad'a sai dai ya nuna mata tamkar bai ji komai ba ya cigaba da wayar da yake ,ta kai hannunta taja dogon sajensa mai maseefar kyau da sheki tattare da d'aukar hankali ,da sauri ya ciza lips dinsa yana fadin "auchhhhh "tare da tsura mata ido sosai yana kallonta yana jin wani sauyi a gabad'aya ilahirin jikinsa ."Itama din tsura masa ido tayi tana masa murmushi wanda yafi kuka ciwo tace "dan allah ka bar wayar nan haka."
Ya cire wayar a kunnesa yana cewa “a kan wani dalili kenan zan bar wayar ? " adalilin na baka dama ka auro nuzla ka had’amu “. wallahi a shirye nike da amsarta a matsayin abokiyar zamana ban hanaku aure ba bare hakan yasa ku zabi ku dinga quntata min ."wallahi wallahi!! da nasan nuzla na sonka da bazanyi wasa da rayuwata ba ,hakika nayi mata laifi mai girma dana cancanci wannan hukunci daga gareta amman tayi hakuri ,na rokkeku ku yafe min ?"
nunfashi yaja ya sauke yana katse wayar gabad’aya ya ajiye a gefe ya rungume hannuwansa a qirji yana kallon kafafunsa dake sanye da safa"ku yafe min kuskuren shiga rayuwarku da nayi "sarai yaji ta amman ya shareta ya d'auki wayar ya soma danne danne ." ta kamo hannunsa d'aya cikin nata tana shafa saman tafin hannunsa ahankali ,dole ya tsaida duk wani abinda yake ya dawo da hankalinsa gareta qirjinta yabi da kallo babu abinda ta rasa kuma babu abinda nuzla tafita hasalima tafi nuzla dirin jiki mai kyau .”
Ya tsura mata ido sosai a kallon da yake mata bai san sanda ya zame hular kanta ba tulin gashinta dake d'aure ya kalla ahankali kuma yasa yatsunsa guda biyu ya zame ribbon din dake rike da gashin nan take gashin suka baje abayanta bai tsaya wata wata ba ya fara shafa yalwataccen gashin kanta ." Naunayen ajiyar zuciya ta sauke tace "ka auro nuzla wallahi zamu zauna lafiya da 'yaruwata idan kuma kana ganin bazaka iya had'ata dani ba ka sakeni ka aurota."sai lokacin ya d'an ja numfashi yace "bazan iya sakinki ba saboda mumy na matukar sonki sosai ba kuma zata yarda ba ".
zan fahimtar daita sannan zan bari ta yarda zan fita arayuwarku gabad’aya , da dai ka dinga wahalar da abinda mumynka take so gara ka raba kanka daita gbdy ka huta dan .." wani qara ta saki mara sauti tare da yin shiru sakamakon yatsunsa biyu da yayi amfani dashi ya buge mata baki, ta kama bakinta dake mata zugi tana shagwabe masa fuska ."Kmr zatai kuka tace " da irin damuwar da kake kunsawa zuciyata gara ka sallameni ka bawa zuciyarka abinda take ..."shiiiii !mum wil kill me idan na sakeki ."
“Shikenan haka ni rayuwata zata qare agidan ka ?haka mumy ta tsara ,itama kuma ta tabbatar da hakan rayuwar zata qare kalamansa yasa ta zare hannunta dake cikin nashi ta mike tsaye da kyar dan kafafunta sun soma rikewa, ta juya da kyar zata bar wajen tana cewa " kayi shawara yaya hisham ni zan so rabuwar da kai ka bawa zuciyarka abinda take so karka ji komai ni zanji da mumy " hannunta ya fixgota da karfi ta juyi luuuu ta fado jikinsa ."Suka tsurawa juna ido suna exchanging din numfashi juna .”