Kenza eBookz

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 23

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 23

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 23: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 23. kamo kafad’unsa MB yayi ya zaunar dashi a saman kujera yana…

3,283 words

kamo kafad’unsa MB yayi ya zaunar dashi a saman kujera yana qoqarin calming dinsa “plse ATA try to calm down d’ago idanunshi yayi wad’an da gabad’aya a rikice suke, kau da kai gefe ATA yayi yana sake tariyo abubuwa da ummah ta fad’a masa lokacin guda ya dunkule hannuwansa yana murzasu waje d’aya .”shawul ya qaraso ya kamo hannun ATA yana dubansa cike da tausayawa dan gsky shima bai yi sa’ar samun suruka ba ,sam sam bai yi exepeting haka daga mahaifiyar maryam ba ,yadda yake kallon maryam ya d’auka mahaifiyarta zata fita saukin kai a she abun ba haka bane . ATA huci mai zafi ya furzar sannan ya mike ya isa jikin window ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa cikin rashin sanin abinda zai yi.”

suna tsaye cirko cirko mami ta shigo cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunansa “where’s adamcy ? ”Kasa juyowa yayi sai dai jin muryarta ya soma qoqarin saisaita kanshi ,MB ya numfasa wanda har lokacin yana tsaye ya tsurawa waje d’aya rinannun idanunshi, dafashi yayi yana fad’in “try to calm down ga mami tazo karkayi abinda zai ‘bata mata rai “duk kuna nan zaune aka dinga ciwa mahaifiyata mutunci babu wanda ya taka mata burki ,kodan dan ba mahaifiyarka aka zaga ba ?” MB yayi shiru yana dubansa daman kuma haka yake duk sanda ransa ya ‘baci he can talk nonsense. ya sake dafashi yana qoqarin cigaba da magana “ don’t ever ask me to calm down again .” yayi maganar jijiyoyin goshinsa na sake fitowa sosai gumi na kuma tsatsafo masa kafin ATA ya sake cewa wani abu mami tace “wai meke faruwa ne ?!.

“salim tunda ka kirani jikina ke rawa haka ma zuciyata bugawa take fiyye da kaida ina maryam take tukun ?shiru sukai gabad’ayasu “kunyi min shiru ,ku fad’a min abinda Ke faruwa “mami ki zauna first zan miki bayanin komai “inji cewar salim “ina maryam take ina son nasan halin da take ciki kafin komai ?“maryam tana lafiya babu abinda ya sameta tana sama ya fad’a yana kamota ya zaunar daita akan kujera yayinda MB ya janyo hannun ATA ya zaunar dashi bai d’ago kanshi ba sakamakon zafin da zuciyarsa keyi masa tunda yake babu wanda ya taba ciwa mahaifiyarsa mutunci sai yau .”

“Ku sanar dani abinda Ke faruwa tun kafin zuciyata ta tsaya ta daina aiki gabad’aya “MB ya bud’e baki zai yi magana kenan ATA ya d’ago tare d’aga masa hannu ya janyo wayarsa ya shiga recond dan tunda ya fahimci rashin mutunci ummah zatai ya danna record ya kunna ya tura wayar gaban mami nan take sai ga muryarta ta bayyana ,mami tai shiru tana sauraro tare da runtse idanunta abun ya girgizata matuqa ,kuma yayi mata zafi duk da tasan halin d’anta he can talk rubbish and nonsense idan rashin ya’baci amman ai ita bata cancaci haka a wajen madina ba” mami ta numfasa irin nasu na manya tana dubansu, sannan ta soma magana a natse “duk me ya kawo wannan tashin hankali haka ?”duk sukai shiru “ lallai akwai abinda ya faru bancin haka ina da yakin madina bazata aikata haka ba ?gabad’ayansu suka tsaya suna duban mami suna duban ATA “magana nake daku kuna jina kun yi min shiru kuna dubansa ?MB ne yayi karfin halin fad’a mata komai daya faru “tabbas mami abinci yayi yaji da maggie amman ban so yadda adam yayi react ba.”

“Naso ko zai mata magana ba a gabanmu ba bare har ta kai ga kiran mahaifiyarta ,sannan itama ummah bai dace abinda tayi ba babba dasanin ya kamata akasanshi amman duk ataru ayi hakuri .” mami tayi murmushin takaici tana tsarke hannunta cikin juna lokaci guda ta maida hankalinta ga ATA tana dubansa a tsanake “ I hope you learned lesson now?” you should know there’s no right way to do wrong things, next time sai ka kiyaye bakinka tunda baka son a ta’ba maka mahaifiya .”ATA ya tsura mata idanunshi yana kallonta zuciyarsa na tafasa “dan me zaka kirata ka fad’a mata haka? “yanzu sweetheart tsakani da allah yaushe kika ta’ba girki mai yaji ko maggie yayi yawa?zaginta fa kayi ka kuma had’a da yar cikinta dan ma kayi sa’a maryam diyar kirki ce bata iya rashin kunya ba ?”ai wallahi data gane bata da wayo “ya fad’a a zafafe “kai dai kayi qoqarin ka canza halinka sannan ka dinga control din zuciyarka da fushinka ba kowa zakawa ya kyaleka ba.”

“ yanzu sweetheart baki ji zafin abinda tayi ba ?to ko naji zafi adamcy ya zanyi ?wa yaja min cin mutunci da akayi min ? da bakayi ma madina rashin kunya ba bazatayi min haka ba dan bata isa ba ,nafi karfin ta fad’a min haka .”ta karshen maganar cike da jin zafi dan da zaa bud’e zuciyarta bakinkirin zaa gani tsabar ciwon da taji amman babu yadda zatayi dan kuka shi ke jawowa uwarsa jifa “ATA bai ce uffan ba har ta gama maganganunta sai dubanta da rinannun idanunsa yake “yanzu nasan zakace zaka huce akan maryam “?ta tambayesa tana tsaresa da ido wanda ko motsi mai kyau ya kasa sai ma damke hannunwan sa da yayi ,mami ta gyara zamanta tana karantar d’anta tasan halinsa tasan abinda zai yi da wanda bazai yi ba “tunaninka a yanzu yadda zaka huce akan maryam kakeyi ko?still shiru yayi ya kasa cewa komai dan ya ma rasa mai zai ce amman tabbas tunaninsa kenan ,mami ta dubi MB ta kuma dubi salim da shawul “ku sheida muddin adamcy ya ta’ba lafiyar maryam ban yafe masa ba “ta fad’a tana dubansu d’aya bayan d’aya nan taga yanayin ATA ya sauya tamkar wanda aka cirewa laka ajiki sai dai zuciyarsa tayi bakinkirin jin abinda mami ta fad’a.”

ahankali mami ta yunkura ta mike ta nufi hanyar step bata tsaya akoina ba sai abakin kofar d’akin maryam ta tsaya sai dai hakan nan zuciyarta ta dinga rawa rawa har ta kai hannu zatai knocking sai kuma ta sauke hannunta tana nazarin zuciyarta .”ahankali ta tura kofar d’akin ta shiga maryam na tsaye ta juyawa kofar d’akin baya tana sheshekan kuka “inda acan bangaren ummah take cewa “wallahi maryam wannan miji naki ya zame miki damuwa arayuwarki amman bamu da yadda zamuyi tunda allah ya jarabeki da mutuwar sonshi amman idan muna son muyi nasara akanshi dole sai munyi abinda zamu rabashi da tunaninsa dole ya zama abokin rayuwarki ya shiga jikinki ki shiga nashi ku zama abu d’aya “mai zanyi ummah da zan samu wannan matsayi a zuciyarsa ?”ya kusanceki shine cikar burina a yanzu bayan ya kusanceki ina fatan kuma ya zama “d’a “zan so faruwar hakan “amman ummah ta yaya hakan zai faru a tsananimu ?Kai nifa gsky ummah na gaji na gaji !! da yin amfani da magungunan da kike aiko min dashi dan baya ci komai daga gareni “wallahi kuwa duk wannan bala’i da yayi bana tunani ya had’iye abin…“.

“Maryam !” mami ta kira sunanta a matukar firgice ta juyo ganin mami tsaye tayi saurin sauke wayar a kunnenta tare da kashewa tana dubanta jikinta na kyarma kafin ahankali tace “a’a mami har kin zo ?sannu da zuwa mami ga waje ki zauna ,tayi mgnr a rud’e cikin rawar jiki ,mami tai mata duban natsuwa sannan tace “ban jima da zuwa ba daman kin san zan zo ne ?ta gyad’a mata kai alamun eh !“ai nice ma nace yaya salim ya kiraki ta fad’a tana duban mami mami tayi shiru itama maryam tayi shiru cikin rasa abinda zatace dan hankalinta yayi matukar tashi adduarta d’aya allah yasa bataji maganarta ba. cikin zafin nama mami tace “ya kikayi shiru haka ?ta girgiza mata kai tana cewa “babu komai “dawa kike waya “? muryarta cike da tashin hankali tace “ummah!”okay !”amman ya’akayi maryam kika bari yaji da maggie yayi yawa acikin abinci?naunauyen ajiyar zuciya ta sauke dan ba abinda tayi tsamanin zai fito daga bakinta kenan ba duk tunaninta mami taji maganarta cikin rawar murya tace”wallahi mami bada niyya bane sautsayi ne kawai sai gani nayi ya kira umma yana fad’ar maganganu marasa dadi .”

Mami ta numfasa kana tace “kiyi hakuri maryam nasan adamcy baya kyautawa kuma bai kyautawa ummanki ba kuma naji dadin abinda tayi masa allah yasa ya zame masa darasi kuma nayi masa gargadi mai karfi akanki dan haka ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru kinji diyata mami ta riko hannunta ta zaunar daita a saman kujera tana cewa “kema ki dinga kula most especially akan girki . “ba tun yau nake fad’a miki ba ,ba’a són maggie da yaji na zarcewa abinci ,a wannnan rayuwar da muke ciki idan nmj na tsananin son mace ko bata iya girki ba ya Kan yi hakuri yayi rayuwa daita a yadda take amman Idan tana da matsalar girki ko tsaftacce muhalli da jikinta kuma akayi sa’ar babu so tsakaninsu to shi yafi komai rashin kwanciyar hankali dan kuskure kad’an zatayi zai zame masu damuwa .“ina sonki da adamcy shiyasa nake yawon jan hankalinki ,ki dinga kula daidai girkin da zakiyi daidai maggie da yajin da zakiyi amfani dashi ,karki lura da yanayin girkin da’ake nunawa a social media kice zakiyi amfani dashi a’a suma suna duba yanayin yawon girki ne ,dan haka ki dinga duba yanayin yawon miyarki ko qanqantarsa , ki dinga kula kinji allah ya baku zaman lafiya .”

Zuciyar maryam tayi fari qal farinciki biyu suka hade mata fahimtar mami bataji komai ba da kuma tabbatar mata dole ATA yayi hakuri ya barta batare da yayi mata komai ba ,ta mike tsaye tare da riko hannu maryam suka fito zuwa parlour’n kasa “nayi closing case din nan kuma har abada banason naji an sake ta dashi ATA ya gyara zama yana mai shan mur sosai ,kafin ya soma girgiza kafarsa d’aya cikin tsananin bacin rai yana duban mami “zanyi maka gargadi na karshe adamcy for the last time karka sake kiran madina da magana irin makamanciyar wannan dan ba abokiyar wasanka bace, uwarka ce duk abinda zai faru a tsakaninka da maryam ka barshi a tsakaninku .”tana gama fadar haka tace “ni zan koma gida allah yayi maku albarka gaba d’ayansu har maryam suka fito yiwa mami rakiya amman banda ATA dake zaune cikin tsananin ‘bacin ran bai samu damar cin uban maryam ba “.

Maryam taja mami kusa da motar data kawota tana cewa “mami na gode sosai bancin inada ke da bansan ya rayuwata zata kasance acikin gidan nan ba na gode na gode !! allah ya shirya miki zuriarki Allah kuma ya jikan iyaye “nima na gode maryam allah yayi maku albarka mami ta d’an yi shiru can kuma ta numfasa sannan ta fuskanceta da kyau “maryam kamar koda yaushe ga d’ana adam ,a kullum shi masa albarka nake, duk da abinda nake masa akanki ba wai banason shi bane a’a kema kinsani adamcy raina ne ,ina matukar sonshi fiyye da komai ban had’a shi da komai ba ,duk abinda ya shiga raina ya kan shiga ransa ya zauna daram ,sai dai a waje d’aya muka samu sa’banin ra’ayi shine aurenki dashi wanda yaki ya kar’ba uzurin da nazo masa dashi nasan yadda yake jin radadi zama dake amman nasan da sannu zaki zama jinin jikinsa “ki cigaba da hakuri da adamcy kinji ,ta gyada mata kai tana wasa da yatsun hannunta “ki kular min dashi karki manta adamcy amana ne agareki sai kinyi hakuri dashi kafin kiyi nasara akanshi “cikin rawar murya tace “in sha allahu mami zan kular miki dashi ta qarasa maganar cike da tausayawa mami .”

“Anya kuwa tayiwa mami adalci da take son biyewa mahaifiyarta ?”tayiwa zuciyarta tambaya nan take gur’bataccen zuciyarta tace “adalcin kenan kina tsananin sonshi ita kanta mami tana son faruwar haka kuma zata fi kowa jin dadi idan zamanku ya daidaita dashi “sai na kuma zuwa wanda ina fatan ziyarar da zata kawoni ba sulhu bace alkhairi ce ta fad’a tana shiga mota maryam ta rike murfin motar tana ce mata “bye mami !”bye maryam take care of adamcy ki rike min amana “jiki a sanyaye ta gyada mata kai daga nan sukai sallama har dasu mb wad’an da basu koma ciki ba kowannensu ya kama gabansa.” tamkar mara laka ajiki ta shigo tana dubansa a tsanake yanayinsa gabad’aya ya sauya daga zafi zuwa sanyi ta wucesa hankalinta kwance dan tasan babu abinda zai faru ta haye sama tana jujjuya masa jiki amman shi ko kallo bata ishesa ba dan bai ga abinda zai burgesa ajikinta ba bare ya kalla.”

Tana shiga d’akin ummah ta fara kira “bangaren ummah tmbyrta tayi” wacece tazo “mami ce !”ta bata amsa” yanzu yaake ciki ?komai ya daidaita kinsan halinsa zuma ne sai ancisa da wuta ake zaman lafiya “ai zagewa zakiyi ki dinga cin ubansa ,maryam ta zaro ido waje tana dafe qirjinta tare da cewa “ummah ki rufa min asiri wallahi bazan iya ba “to shikenan daman idan lalla’bawa yaki bud’e wuta shine mafuta ,banda yaya adam bazai d’auka ba idan baso kike ya nakasa miki ni ba” karki damu nan kusa zai gane shi din ba kowa bane, wallahi duk wannan zafin ran da zuciyar zaki nemasa ki rasa akwai maganin da zan aiko miki akarkashin gadon baccinsa zaki saka masa da zarar ya Kwanta sai dai ya tashi da muguwar soyayyarki ,zai manta soyayyar kowa sai taki dan a cewar malamin har uwarsa sai kin tuna masa wacece ita agaresa ,amman malamin yace matukar aka sakashi akarkashin gadonsa yayi kwana uku bai kwanta ba aikinsa ya karye ,ai kina samun damar shiga d’akinsa?wannan ba damuwa bane dan bai fiyye rufe d’akinsa ba yanzu haka d’akinsa a bud’e yake yanzu yaushe za’a turo ?gobe da dafe “nan suka cigaba da tautaunawa.”

Shiru ATA ya cigaba da yi zaune he’s thinking of what his going do to her dan zuwa mami bazai sa na barki haka ba ko ban ta’ba lafiyar jikinki ba tunda anyi min iyaka zan yi punish naki cikin ruwan sanyi I can never leave you at all saboda duk wannan abun da sweetheart take ,so take ta kawar da tsorona acikin zuciyarki and I will never let it happen “what’s your gain in this ? kwakwaluwarsa ta aikawa zuciyarsa tambayar “my gain is that I don’t want her to be happy at all bana son taji dadi wannan shine ribata a zamana daita kullum so nake naganta cikin damuwa a qarshe ta tattara ta bar rayuwata “this is very bad adamcy zuciyarsa ta sake fad’a masa haka ahankali ya girgiza kai yace “a’a it’s not mikewa yayi a natse cike da kwarin gwiwa ya nufi step da sauri sauri yake takawa ya shiga d’akinsa ya sauya kaya ya d’auki duk abinda yake bukata ya sauko ya rufe kitchen ya zare key tare da fitowa zuwa haraban gidan yana bawa masu tsaronsa umarni cire wutar gidan ,sannan ya kulle kofar shiga ciki sannan ya bawa masu tsaron get umarnin kar abar duk wanda yazo ya shiga ,ya shiga mota suka bar gidan .”

Maryam na zaune tana waya taji wuta ta d’auke amman son jiki ya hanata tashi ta cigaba da waya bayan sun gama waya ta shiga social media sannu ahankali idanuwanta suka fara mata yaji alamun bacci ,ta ajiye wayar a gefenta ta kwanta nan da nan bacci ya d’auketa, ba ita ta tashi ba sai karfe shida da kyar ta yunkura ta mike ta shiga bayi ta d’auro alwala tana mamakin daukewar wutar gidan alhalin yana gida tunda tazo wutar gidan na d’aukewa ake kunna dizu .jiki a kasalance ta fito ta gabatar da sallah laasar byn ta idar ta mike ta fito kai tsaye kofar d’akinsa ta nufa ta murd’a tajita a kulle shiru tayi kafin ahankali tayo hanyar step ta sauko qasa bata gansa ba tayi tunanin fita yayi dan haka ta soma tattara kayan abincin da sukai amfani dashi sai dai tana isa bakin kofar kitchen taji gam kofar a rufe handling ta kalla taga babu key ajiki .

Mamaki ya kamata nan take kuma taji tashin hankali mai tsanani yana shigarta kwakwaluwata ta fara hasko masa wasu abubuwa “kar dai yaya adam cire wutan gidan yayi ?babu shakka cire wa yayi tun da gashi ya kulle mata kitchen jiki a sanyaye ta dawo rike da kula ta ajiye akan table ta zauna jagwab akan kujera tana dafe goshinta “what’s all this ?ta furta tana zaune har bakwai tayi lokacin duhu ya shigo sosai ,ta yunkura da kyar ta mike ta nufi kofar fita da niyyar bawa masu tsaron gidan umarnin su kunna mata wutan gidan tana murd’a kofar tajita gam nan wani sabon mamaki da tashin hankali ya ziyarci ilahirin jikinta “mai haka yake nufi ?tayiwa kanta tmbyr “ki koma d’aki ki jira har sanda zai dawo “nan take ta amince ta koma d’akinta ta d’auki waya lokacin sauran kad’an cajinta ya qare a 10 percent yake ,ta ajiye wayar akan sallayya ta sakê shiga bayi ta d’auro alwala tayi sallah magrib byn ta idar ta d’auki wayarta what’s ta shiga tana duba sakonin qawayenta dana yan’uwa.”

Tana nan zaune har takwas tayi ta mike ta gabatar da sallah ishai, byn ta idar ne ta d’auki wayarta taga battery low tayi tunanin kiran nana hauwa’u number na soma ringin wayar ta matu gabad’aya“inna lillahi .”ta furta a fili tare da mikewa ta kullo kofar d’akinta ta dawo jikin window d’akinta bata hango masu tsaron gidan ba kasancewar window d’akinta ta baya yake ,labule ta d’an zuge ta bar net awa d’aya tazo ta wuce shiru bai dawo ba wata awa d’aya tazo ta sake wucewa goma da wasu mintuna amman shiru babu alamunsa sam bata ji tsoron komai ba ta cigaba da zama ita kad’ai yunwa data soma ji ne ta fahimci lokaci ya tafi .ta bud’e kofarta wani mugun duhu tagani ko tafin hannunta bata iya gani ta fito tana shafa bango.”

Ahankali ta dinga tafiya daf da zata sauko daga step ta tuntsura ta fad’i akan goshinta wani azababben zafi ya ziyarceta ta dafe goshinta tana runtse ido tana jin kamar tayi kuka ,rarrafawa ta cigaba dayi har ta samu ta gano inda center table din yake da hannuwanta duka take lalube allah ya taimaketa hannunta ya sauka akan plet din abincin data zuba masu bata tsaya neman na kula ba ta d’auka ta soma ci ,abinci yayi sanyi sosai amman bata da zabin da wuce taci ,tas ta lashe ta koma laluben ruwa da kyar ta gano ruwan roba ta kafa abakinta bata cire ba sai data shanye tasss sannan ta ajiye roban tana sauke numfashi ta soma qoqarin komawa sama wannan karon da kyar ta gano hanyar step dan ta kusan minti shabiyar tana shawagi.hankali ta hau saman katifarta ta kwanta abunta , matsalarta a yanzu wayarta da babu caji dan ita idan tana da caji a waya bata da damuwar komai nan da nan bacci ya dauketa sakamakon babu abin yi.”

Washegari ma haka ta yini babu wuta babu ATA tayi tunanin zai dawo gida da daddare amman kamar jiya har karfe d’aya na dare idanunta biyu acikin duhu bai dawo ba gabad’aya hankalinta ya tashi damuwa ta saukar mata na rashin wuta da kuma rashin miji ita dama kulleta kawai yayi ya bar mata wuta ,ranar ma haka ta kwana cikin duhu dan abinci yunwa tasa taci abincin jiya ruwa ne dai ta koma shan na bayi dan ta shanye wanda yake Kan table ,ahaka tayi kwana biyu wanda zuwa lokaci bata iya cigaba da cin sauran abincin, ruwa kawai take sha tayi kuka har idanunta suka kunbura “da wannan punishment din ai gara dukan mutuwa yayi mata ,tayi datasanin zuwa mami domin kuwa shine ya jefata cikin halin da take ciki yanzu ,dan da yayi mata duka bazai mata punishment ba .”

Readers Also Read