Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 4
Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 4: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 4. wani tsaki ya sake ja tare da kiran "nonsense sau kuyita yi…
3,350 words
wani tsaki ya sake ja tare da kiran "nonsense sau kuyita yi tunda kun zama bayin mata kai ma zaka zama bawan mace ne muje dai zuwa ."a natse ya cigaba da motsa lip's dinsa "wani sako na gani daga m malik to nayita kiran wayarsa baa dauka ba shine naji hankalina bai kwanta ba nake son naje naji me sakon yake nufi, hakan naji sakon ya tsaya min arai ,sakon ma yayi three day's da turowa ."Allah yasa lafiya shiru kowannensu kafin daga baya suka cigaba tautaunawa wanda kusan duk akan rayuwar da ATA ya jefa kanshi ciki ne ."
suna cikin tafiya daya daga cikin wayoyin ata ta fara Ringim ya dauka ya duba sunan aunty khadija ya gani kamar ba zai dauka ba sai kuma ya dauka tare da cewa"kanwa yaaakayi fatan ba da wata matsala kika zo ba ?gsky adam kayi mugun rainani kema Kinsan shishigi kawai kikayi kika rigani zuwa duniya amman duk da haka dai kece akasana "tunda kasan da haka ai shikenan ya karfin jikin naka "daman bani da lafiya ne "baka dashi mana amman yanzu na fahimci ka samu lafiya yanzu daman na kira ne akan abinda kayiwa ummu habiba wacece haka kuma "bangane wacece haka ba ?ummu habiba din ce bakasani ba?"
"kiyi maganarki kai tsaye dan bangane ko wacece ba shi yasa nace haka "to mahaifiyar maryam "tsaki yaja yana sauke numfashi sai lokacin ya tuna mami tace ya kira "Adamcy ya dace ka kira mahaifiyar maryam ka bata hakuri ."akan wani dalili kenan ?" akan abinda kayi mata mana "ni bansan nayi komai ba" idan kayi haka baka kyauta ba dan gsky abinda kayi yayi tsauri dayawa amman zan ari bakinka naci maka Albasa" ni dai ban sakaki ba idan zakiyi Kiyi da sunanki karki yi da sunana yana gama fadar haka ya katse kiran ."mb ya dan waiga ya kallesa "kai mai yasa baka son gsky?" ka bada hakuri shine zai zama wani aiki "amman kai zaka bawa wani labarin halina bazan ta'ba bada hakuri ba ."
"amman ita wannan ai tmkr mahaifiyace adam yadda zaka girmama mami hk zaka girmamata "wannan raayinka kenan . "dole fa ka sauya yanzu bazai yuwu ka dinga bin raayin zuciyarka ba kana aikata ba daidai ba " dan allah malam karka damu rayuwata raayinka dabam nawa dabam hakuri ne bazan bayar ba idan dole sai na bayar wallahi sai na saki yarta inga ta tsiya " a fusace yake maganar yana kaiwa nan yaja tsaki sake girgiza kawai kai mb yayi tare da yin shiru tafiya mai dan nisa sukayi suka qaraso bakin get din gidan securities na ganin motocin ATA sukai saurin bude masa tafkeken get din ."
Ahankali suka shiga sukai parking a haraban gidan kusan atare suka fito cike da girmamawa suka shiga gaishesa inda yake tmbyrsu m malik nan suka sheida masa abinda ya faru babu bata lokaci ya tmbyi hospital din da yake suka fad'a masa suka koma cikin mota suka fice ."ATA ya shiga tashin hankali matuka lokacin da yake iso cikin dakin da m malik Ke kwance yana kallonsa rai hannun Allah.abakin matarsa yake jin qarin bayanin yadda abun ya kasance hawaye na zuba daga idanunta ".
shiru kawai ata yayi zuciyarsa cike da tashin hankali" yanzu mai likitoci suka ce ?"wai sai dai a fita dashi waje ya gyada kai tare da cewa "ku shirya at any time zaku iya wuce yana gama fadar haka ya fito daga cikin dakin zuciyarsa cike da tausayawa ,matarsa ta biyosa tana masa godiya. da tunanin me m malik yake son fad'a masa ya baro hospital sai tunaninsa ya kai ga mafarkinsa sai kuma yaji ba haka bane menene abinda zai fad'a min haka yayita aikawa kwakwaluwarsa tmby karfe takwas suka dawo gida mb ya shiga motarsa ya wuce gida shi kuma sai da yayi magariba da ishai sannan ya nufo gidan mami ."
da kyar ata yake daga kafafunsa a natse ya sanya hannu shi ya turo kofar falon tare da sallama akan lip's dinsa ,mrym na ganinsa ta lumshe idanunta sakamakon kamshin turarensa da ya bugi hancinta dan ta gefensa yabi ya zauna a kusa da mami yana kiran "washiii Allah !" sannu ka gaji ko "wallahi sweetheart ya gida ?daga hk bai sake cewa komai ba yayi shiru "lafiya dai ko naganka wani iri ? "ba lafiya ba sweetheart ya fad'a sanda yake gyara zama .
gbdy mami ta tattara hankalinta garesa " "wallahi sweetheart wani tsautsayi ne ya samu wani babban yarona maganar da nike miki ma sai an fitar da dashi waje anyi masa aiki a kwakwaluwarsa "suballah mami ta furta nan yayi mata bayani komai "ai kuwa mun gani a labarai lallai dole matarsa ta shiga damuwa shi km direbasa Allah ya jikansa ta qarasa mgnr mami tayi wa mrym alamar tayi masa sannu da zuwa "yaya adam !ta kira sunansa ya bude idanunshi dake runtse ya zuba mata" barka da dawowa ta ambata tana kallonsa bai amsa ba kamar yadda bai dauke idanunshi akanta ba "Allah ya qara kiyayewa shi kuma allah ya bashi lafiya "still dai bai amsa ba illa karfin halinta da ya gani ."
" mrym kawo masa ruwa ya sha ta tashi taje ta kawo masa "ga ruwa yayi mata banza dole ta ajiye a kusa dashi tana jin fad'uwar gaba bayani ya cigaba yiwa mami tana jimami bai sha ruwan ba ya sake lumshe tsumammun idanunshi byn Kmr second biyar ya bude idanunshi yaga idanun maryam kyam akanshi tana kallonsa kwayar idanunta cike da qaunarsa wani abu yaji ya tokare masa makoshi mikewa yayi tsaye dan baya son ya sake yin wani abu da zai ta'ba zuciyar sweetheart dinsa "sweetheart sai dai safe "allah ya tashemu Lfy ya nufi step bayansa tabi da kallo har ya bacewa ganinta gbdy ya tafi da rayuwarta bata son abinda zai sa tayi nesa dashi ."
Yana tsaye a dakinsa yana kokarin cire kayansa yaji anyi knocking cike da mamaki ya qarasa yana balle maballin gaban rigarsa ya bude kofar , daya daga cikin masu aikin gidan ne hannunta rike da wani qaramin tire dake dauke da glass cup an rufe sbd sanin halinsa ta rusuna cike da girmamawa sannan ta mika masa yayi shiru yana dubanta tare da mamaki, ganin yadda yake kallonta tai saurin cewa "hajiya ce tace na kawo maka jin tace mahaifiyarsa ce ya kar'ba ya maida kofar ya rufe , madara ne mai sanyi ya kai bakinsa ya fara shan kad'an wani dadi ya ji dan har sai da kunnensa ya motsa dan hk ya sake kai bakinsa ya shanye ya ajiye cup ya soma cire kayansa ."
tabawa mai aiki ta nufi inda maryam take tsaye tana jiranta tana ganinta tasan adduarta ta karbu tai murmushin jin dadi tana dafata tana cewa "bai miki tambayoyi ba "yana shirin yi nace hjy ce ta aiko ni" da kyau na gode sosai tabawa mai aiki ta kama gabanta "ya kwashe kayansa ya zuba a basket ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito ya sanya kayan bacci mai budaden gaba ya qara karfin ac dakin kwanta ya lullube rabin jikinsa ya canza wutar dakin sai dai ya kasa runtsawa m malik ne ya fado masa ya tashi ya zauna ganin tunanin nason hanshi bacci ya yaye bargon daya lulluba dashi ya sauko ya dawo falo ya kunna sigari yana zuga Ahankali tunani sosai yake yana bukatar sanin abinda m malik yaso fad'a masa sakonsa kuwa ya karanta yafi sau goma amman ya kasa fahimtar akan me ye ?dole dai ya jira har zuwa lokacin da zai dawo norma.
****** Yau asabar wanda yayi daidai da kwanaki shida kenan da aurensu ata Wanda ya kama a lissafin hjy zulfa'u Gobe ne nana hauwa'u zata tare a gidanta hisham yana kwance akan kujera mai zaman mutun uku sai ga hjy zulfa'u ta fito daga dakinta ta kai idanunta kan agogon dake manne a parlour'n karfe goma har ta wuce gashi tun da nana hauwa'u take gidan a parlour'n yake kwana baya shiga dakin da take sai dai idan zai dauki wani abunsa mai mahimanci ranta a bace tace " ka tashi ka shiga daki ka kwanta ka wani zo ka kwanta anan ka bar nana hauwa'u ita kad'ai" ." babu mutsu ya mike tsaye dan bai son damuwa har yayi taku uku ta tsaida shi ta soma magana "hisham ka kular min da yarinya kada ka wulakantar min da 'ya idan na lamunce komai banda wulakanci bai tsaya jin kalamanta ba dan idan ya tsaya ya cigaba da ji zuciyarsa zata tarwatse
A natse ya tura kofar d'akin ya shiga tana zaune aka katifa ta jingina bayanta da abun gado ya zagaya dayan bangaren ya samu waje ya kwanta bai jima da kwanciya ba wayarsa ta dauki sautin qara ya d'auka ya duba ganin sunan dake wayo akan screen din wayr ne yasa shi ya zabura ya miki zaune yana daukar wayar tare da kiran sunan da dan karfi "nuzla !" Kina ina ? tun da ya fara wayar ta zuba masa idanunta kawai tana kallonsa yayinda idanunta ya ciko da ruwan hawaye "karki damu nace miki ganin nan zuwa ki tsaya a wajen ya qarasa wayar yana bude kofa ya fito zuwa haraban gidan yana qoqarin shiga motarsa qarar tada motar ya janyo hankalin hjy zulfa'u dake tsaye tana shirin kwanciya ta yaye labulen window taga hisham ne kallon yadda yaja murfin da karfi ya rufe da yadda figi motar zai nuna maka da baya cikin haiyacinsa."
"Ya allah ka shirya min hisham ina kuma zashi adaidai wannna lokacin ta tambayi kanta tana jin faduwar gaba hankalin hajiya zulfa'u yayi matukar tashi dan haka ta kasa kwanciya ta fito daga dakinta ta shiga dakin da nana hauwa'u take ."take taji zuciyarta ta karye dan koda tashiga dakin kuka take sosai tamkar ranta zai fita duk yadda taso daurewa ta kasa ta fad'a jikin mumy da kyar ta iya daure abinda take ji .mumy ta shiga rarrashinta da kyar ta samu nana hauwa'u tayi shiru ."
"Har abada bazaki yi danasanin auren hisham ba muddin ina raye sai kin zama tauraruwa a gidansa ki qara hakuri ,amamn idan har kika ji bazaki iya zama dashi ba ki fad'a min aurenku bazai qara koda second daya ba wannan kalmar dake fita daga bakin mumy yana mata dadi da sanyaya ranta a duk sanda ta furta hakan ma yana sa ta danne duk wani abu da take ji dan tasan ba cuta tasa ta hada auren da danta ba ."wani tausashen murmushi ya subuce mata sosai take jin dadin kalaman mumy tana ganin yadda abun zai zo masu da sauki ta hanyar mumy yanzu ya kike jin zamanki kina ganin zaki cigaba da rayuwa da hisham ?ta gyda mata kai .
"Yauwa diyar albarka allah yayi miki albarka Ameen ta fad'a tana jin qaunar mumy acikin ranta "yanzu fad'a min ina hisham ya tafi ?shiru tayi tana neman abind zata fad'a mata domin ta kareshi a wajen mumy byn Kmr second biyu tace "na dai ji yana magana akan wani contract "contract? mumy ta tambaya nana hauwa'u ta sake gyada mata kai tana sunkuyar da kanta kasa mumy tayi mata sai da safe ta juya idanunta ta zubawa mumy har ta fita daga dakinta ta lumshe idanunta "bata ga abinda nuzla ta fita ba da yaya hisham ya kasa karbata acikin zuciyrsa yanzu dai tasan sai dai tayi zaman aure dashi darajan mumy ."
Yana tuki yana jin wani irin bugun zuciya kuka zuci yake wanda yafi na fili ciwo idan har ya tuna nuzla bata son shi sai yaji radadi sautinta yanzu ma yawo sautinta yake masa acikin kunnensa yana jin kamr ya juya ya koma gida amman sai yaji bazai iya ba ko babu komai zataci darajan baba babba salim da yaya Ibrhim yasan muddin ya maidata gida zasu ji dadi kuma hankalinsu zai kwanta ."yana gama isa inda nuzla ta kwanta masa yayi parking ya fito cikin tsnanin tashin hankali ya rufe murfin motar da karfi nan da nan zuciyar nuzla ta karye ta qara sautin kukanta da take akaro na biyu" allah sarki yaya hisham hakika sai yanzu ta soma jin nadama abinda tayi masa ."
daga inda take ta fito ganin yana waige waige da qoqarin neman layinta "yaya hisham ta kira sunansa da sauri ya juyo ya ganta tsaye abayansa tsayawa yayi yana kallonta tun daga kasa har sama cikin wata atamfa dinki riga da siket kayan sun mata cif cif ajiki ta rame sosai sai dai baqaramin kyau tayi masa ba wani abu yaji ya tsarga masa tun daga tsakiyar kanshi har zuwa yatsun kafafunsa ,bai san sanda ya fixgota jikinsa ya rungumeta tsam kamar zaa kwace masa ita." ahankali ta saki wani kuka mara sauti ya sake kamkameta ajikinsa yana shafa bayanta "tun tana kuka slow slow har ta bari kukan ya fito da sauti tun baa je koina ba tayi nadamar rashin aurensa."
"Me yasa na biyewa son zuciyata ?me yasa banyi hakuri ba ?kuka take sosai wanda kukan nata yana qara daga hankali da dawainiya da hisham gabadaya ya dawo mata wani iri sai daya dauki second talatin rungume daita sannan ya sautata rungumar da yayi mata".bai ce mata komai ba yaja hannunta ya nufi inda motarsa take "ina zaka dani ?yayi mata banza ya bude gaban mota ya sakata ya maida murfi ya rufe ya zagaya ya bude mazaunin direba yaahiga "dan allah karka kaini gida "me yasa bazaki gida ba ?tayi shiru kawai tana wasa da hannunta dan bata san me zata fad'a masa ba ."
"kin gudu akan bakya sona yanzu kuma wannan ya wuce a tsakaninmu, babu wani batu na soyayya sai na yanuwantaka ne a tsakaninmu, ai gara ki koma gida ki cigaba da rayuwarki ."tayi narai narai da idanuwa tana dubansa kallon dake tsuma zuciya da gangar jikin yaya hisham ya numfasa ya cigaba da mgn "yanzu matsayin kanwa kike agareni ki koma gida ki fara sabuwar rayuwa " daga hk bai kara magana ba yaja motar bai tsaya akoina ba sai acikin haraban estate dinsu tsayuwar motarsa ya sake daga mata hankali yayi parking ya fito yana daidaita nutsuwarsa bai mata magana ba yayi mata alamar ta fito yanayin yadda taga fuskarsa babu annuri ko daya sannan kuma babu wasa yasa ta fito tabi bayansa ."
Duk da dare ne idanun mutane na kansu kasancewar akwai hasken fitilu ahankali ya tsaya bakin kofar gidansu alokacin da shadaya da rabi ta buga hannu ya kai yayi knocking sautin muryar mahaifinta taji yana cewa" waye ?baba hisham ne "hisham kuma adaidai wannan lokacin Allah yasa lafiya? ya fad'a yana bude kofar ya koma gefe hisham ya shigo yana gama shigowa nuzla ta shigo tmkr mai jin sanyi da idanu baba babba ya bita dashi kafin yace "ita kuma wannan fa daga ina ?baba kayi hakuri dan allah."
hajiya salema kam tuni ta zabura ta mike ganin nuzla ta qaraso ta rungumeta ajikinta tana kuka "haba nuzla me yasa zaki min haka kin kuwa san halin damuwar dana shiga "hisham ka dauketa ka maida ita inda ka daukota bazata cigaba da zama dani ba." dan girman allah baba karkayi haka kai din fa mai hakuri ne kayi hakuri ka yafe mata nuzla yarinya ce har yanzu idan kaki amsarta ina kake son taje ."?"ta koma inda tayi kwanakinta amman ba a gidana ba." yana gama fadar haka Ya juya ya shige turakarsa jin haka yasa hajiya Salema ta saki nuzla ta bi bayansa tana kuka ."
Cikin fushi nuzla ta nufi kofar fita yaya hisham bai san lokacin daya fizgo hannuta ba ya sanya cikin nashi ya dan matsota kamar zai shige jikinta ganin kallon da take masa yasa shi janyota gabadaya jikinsa "kina hauka ne ina zaki ?bakaji abinda baba ya fad'a ba? shine saboda baki da hanaki zaki fita to me zanyi ? tayi mgnr a shagwabe "bazaki koina ba kin dawo gida kenan karki sake ganganci sake barin gidan nan ya rad'a mata acikin kunneta wani iri taji agabadaya ilahirin jikinta "ya zareta ajikinsa ya nufi dakin hajiya salema daita yana cewa "matukar kika sake barin gida karki sake marmarin kirana a waya dan haduwarmu bazai mana kyau ba ya zaunar daita akan gado yana já mata kunne."
ta kallesa shima cikin kwayar idanunta yake kallo yana jin sonta na bin jinin jikinsa yana son nuzla da dukkanin rayuwarsa rausayar da kwayar idanunta tayi a cikin nashi kamr da gaske zai iya aiwatar da wani abu akanta idan ta sake barin gida " sai da safe ki kula da kanki" ta gyada masa kai tana kallon bayansa numfashi ta sauke "wani irin so yaya hisham yake mata haka ?duk shawarwari da nasihar daaka sha mata akanshi basu ta'ba tasiri ajikinta ba sai acikin kwanki bakwai kacal da yayi aurensa ta soma jin wani iri akanshi ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 3
...... A parlour hisham ya iske hajiya salema zaune ta dafe kanta da duka hannuwanta tana risgar kuka, cike da tashin hankali hisham ya qaraso ya durkusa a gabanta yana bata hakuri "dan girman allah hajiya ki daina haka ." "ban san me Alhaji yake so dani ba hisham, taya zamu haife 'ya acikinmu mu watsata duniya?" kuskure ne kowa yasan nuzla tayi kuskuren amman tunda ta dawo ai sai kowa yayi hakuri tunda qaddara tana kan kowa, kuma qaddarar aurenka da nana hauwa'u ce silar fitar nuzla daga gida."
ta d'an tsaida kukanta sannan ta cigaba da magana "hisham ka taimakeni ka shawo min kan alhaj ya barni da yarinyata mu cigaba da rayuwa idan kuma ba haka ba za'a samu matsala domin muddin nuzla bazata cigaba da rayuwa acikin gidan nan ba wallahi nima zamana acikinsa bashi da wani amfani gara na tattara na bita mu bar masa gidansa kamar yadda ya fad'a."
Cike da tashin hankali nuzla ta fito daga cikin d'akin sakamakon jin sautin kukan mahaifiyarta sai dai jin furucinta yasa ta qara shiga tashin hankali mai tsanani cikin rud'ewa ta shiga fad'in "pls umma babu inda zaki sai dai idan nice zan bar gidan nan amman Ke babu inda zaki." ta qaraso ta zube ajikin hjy salema tana wani irin kuka dan duk ita ce silar jefa mahaifiyarta cikin tashin hankali ."dan allah ummah kiyi zamanki bari na tashi na bar gidan nan tun yanzu" ta mike tsaye cikin rawar jiki zata nufi kofar fita."
wani irin razananniyar tsawa hisham ya buga mata wanda ya firgitata tare da yi mata alama da ido ta koma d'aki " kina hauka ne ko kin fara shaye shaye ne ?ya tambayeta a matukar fusace yana tsare gira." Kallonta yake mai had'e da harara "ki shiga hankalinki sannan ki koma d'akin ko kofar parlour'n nan ban yarda ki taka ba bare ki bar gidan nan ."babu musu ta juya tsimi tsimi ta koma tana kuka ."Yaya hisham bai tsaya sake cewa komai ba ya mike tsaye ya nufi d'akin baba babba ."
bakinsa d'auke da sallama ya'isa cikin d'akin baba babba yana zaune yana shan ruwan tea ya amsa masa sallama ." ahankali hishsm ya k'arasa ya durk'usa har k'asa a gaban baba babba ,cikin d'aure fuska baba babba yace "a,a har yanzu baka wuce gidan ba?" cike da fargaban ganin yanayinsa ya d'an sosa bayan keyarsa yace "eh baba wallahi ban wuce ba saboda na kasa samun natsuwa ."
baba ya sauke numfashi kawai saboda yasan kwanan zance shi kansa yana jin alhinin rasashi da diyarsa tayi amatsayin miji domin samun miji kamar hisham wallahi sai an tona ,kaf mazan daginsu yafi su nagarta da hakuri wanda hakan yana d'aya daga cikin dalilin da shi karon kanshi yake ta bin nuzla akanshi amman taki bin umarninsa dan ko adam bazai nuna masa komai ba sai tarin dukiya ".