Kenza eBookz

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 5

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 5

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 5: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 5. Shiru ya d'an ratsa d'akin can baba ya d'ago ya dubesa sannan…

3,313 words

Shiru ya d'an ratsa d'akin can baba ya d'ago ya dubesa sannan yace "hisham ya dace ace ka kama hanyar komawa gida ko akwai abinda kake so ne...?" ya jefa masa tambayar domin yaji meye raayisa akan nuzla ." sake shafa keyarsa yayi sannan ya d'ago cikin yanayin jin kunya ya fara magana "ammm baba .."dama...dama"!! sai kuma ya fara in ina, shiru baba babba yayi yana kallonsa duk ya wani rikice ahankali yace "relaxes hisham kwantar da hankalinka kayi min magana ina sauraronka" .

da kyar ya samu nutsuwa sannan ya fara magana "dama baba na shigo ne na qara baka hak'uri akan abinda nuzla tayi wallahi tayi nadama baba baza ta sake kwatanta abinda tayi ba dan Allah kayi hak'uri ka yafe mata ka kuma bata wani dama zata gyara Still shiru baba babba yayi yana kallonsa kawai cike da tausayawa duk mai hankalin da ya kallesa yasan yana cikin shaukin só ,koma yace soyayya na tangalili da rayuwarsa ,lumshe idanunshi yayi kawai dan ba hakurinsa yafi buqata daga garesa ba,a halin yanzu babu abinda yake bukatar ji kamar ya furta masa cewar zai aure nuzla ya had'ata da yar'uwarta".

"kayi hak'uri baba nasan kayi fushi sosai daita yanzu idan ka koreta daga gidan nan ina kake tunanin zata ?".mu godewa allah ma data dawo gida da ba'a nemeta gbdy an rasa ba" still dai shiru baba yayi "baba bana son rayuwarta ta lalace dan Allah kayi hak'uri ka barta ta cigaba da rayuwa acikinmu shine kwanciyar hankalina ;;" yai maganar cikin yanayin tausayi yana zubar da hawaye"..

Hmmm....!!! baba babba ya sauke nannauyen numfashi sannan ya fara magana "hak'ik'a hisham nuzla ta aikata min babban laifi wanda kullum na kan zauna nayi tunanin abinda yasa tayi min haka . "ina tarbiyar dana bata?"wallahi rai na yab'aci sosai akan abinda tayi amma ba komai komai ya wuce ka daina kuka taci darajanka wallahi banci kai da sai dai ta koma inda ta fito ka tashi ka wuce gida dare nayi Allah yayiwa rayuwarka albarka ka gaishe min da matarka tashi kaje"

wani irin sanyin dad'i hisham yaji ya mamayesa bai san sanda ya rungume baba babba ajikinsa kamar wani k'aramin yaro yana fad'ar "thanks my dad i love you so so much am very proud of u my dad" nima ina alfahari da kai hisham Allah yayiwa rayuwarka albarka "ya sakesa ya fita yana murna baba babba kuwa banda murmushi babu abinda yake yana mamakin irin son da yakewa nuzla "....

karfe d'aya daidai hisham ya shigo gidan kuma akan idanun hajiya zulfa'u da nana hauwa'u ya shigo bayan ya shigo ya rufe koina yana qoqarin kwanciya akan kujera mai zaman mutun uku ya ga mumy tsaye akanshi tana masa mazurai da idanunta gabansa né yayi wani irin mummunar fad'uwa muryarta a kausashe ta soma magana "daga ina kake adaidai wannan lokacin?"shiru yayi tare da sunkuyar da kai cikin tsananin tashin hankali dan bai san me zai fad'a mata ba ,gashi shi bai iya karya ba daya girba mata karya ya huta ."

"Ba da kai nake magana ba kana jina kayi min shiru.?"amm daman ..."sai kuma ya sake yin shiru yana shafa sumar kanshi alokacin da nana hauwa'u take taku domin fitowa daga daki "kai nake sauraro ka ji dani bacci nake ji daman me ?".daman mumy nuzla ce ta kirani shine naje na d'aukota na kaita gida ."

"what ?"! "hisham kana da hankali kuwa?"ka tsallake matarka kaje ga wata nuzla din banza " numfashi ya sauke sannan ya motsa lip's dinsa yana mai d'ago kanshi daga sunkuyar wa da yayi "mumy nuzla fa ba banza bace, bai kamata dan tayi d'an wannan Kuskuren ba ki d'auki zafi dayawa akanta ,sannan ko babu komai nuzla diyarki kuma kinga dai irin halin da kowa ya shiga akan rashinta ,"kiyi hakuri dan allah nasan nayi ba daidai ba dana fita adaidai wannan lokacin amman nuzla tana da matukar mahimanci arayuwata domin zuciyata ce bazan.."

saukar mari akan kuncinsa ya katse masa maganarsa ,hatta nana hauwa sai da jiyo saukar marin ajikinta dan tana daf da fitowa parlour'n mumy tayi masa marin ."cak ya tsaya yana kallon fuskar mumy dafe da kuncinsa yayinda nana hauwa'u ta fito jiki a matukar sanyaye ta tsaya abakin kofa tana dubansu cike da tashin hankali idanunta suka cicciko da ruwan hawayen abu biyu rashin son da hisham yake nuna mata da kuma na dawowar nuzla gida." "hakika tayi farinciki da jin wannan labari dan daman kullum zuciyarta cike take da tunanin inda take ."

"wallahi wallahi !! sau nawa kaji na rantse idan ka sake min magana akan nuzla zuciyarka ce sai nayi mummunar sa'ba maka ,idan ban iya tsine maka akanta ba allah yayi min yadda yake so, kai shashan ina ne ?da zata gudu tayi shawara da kai sai da zata dawo gida ne tasan da kai ? kai kuma ga shasha tantabara sarkin alqawari ka girba wa matarka karya an kiraka an contract ka kwashi jiki kaje wajenta ,in da da wani abu ya sameka fa ?"tayi masa Kmr zata zubar da hawaye ."

"yarinyar nan tace bata sonka bata sonka !! dole ne hisham ?ko dole ne soyayya da bazaka hakura daita ba "? hisham ya sauke numfashi yana shafa kuncinsa yace "wallahi mumy sai kin ganta ,tayi nadama sosai "babu ruwana da wata nadamarta tunda bata min alkunya akanka ba nima bazan mata ba ,kai kad'ai fa na mallaka arayuwata ni duk yadda muke da mutun yace bai sonka ai sai inda karfi ya qare akan kiyayyarsa ,kasani nuzla diyar dan'uwana ce amman bana sonta da kai tayi rayuwarta kayi naka allah ya bata wani mijin ."

"Haba mumy take it easy now duk fa abun bai kai haka ba "ka kamin baki anan karka sake min magana akanta bana són ji ta fad'a à hargitse, tsayawa yayi kawai yana duban mahaifiyarsa gbdy ta hargitse ta canza masa Kmr wata mai ciwon iska " wallahi ka sake zuwa inda take sai na ...."saukar hannun abba taji a bakinta yana cewa "haba my dear wai meye haka ne ?hucin numfashi ta fesar na 'bacin rai tana dubansa cike da takaici, bai sake barin tace komai ba yaja hannunata zuwa d'akin baccin su yana rarrashinta."

Ahankali nana hauwa'u ta tako ta tsaya gaban hisham tana kallonsa rasa abun yi tayi saboda ganin yadda fuskar hisham tayi tana cikin yanayi na tsnanin damuwa dan haka ta zuba masa idanunta tana canza fuskarta zuwa yanayi na murmushin farinciki shi kuwa sunkuyar da kanshi kasa yayi zuciyarsa na tafasa"yaya hisham !" ta kira sunansa ahankali bai amsa ba yaji ta cigaba da mgn "ina tayaka murnar ganin nuzla hakika naji dadi sosai."

d'ago kanshi yayi ya zuba mata kwayar idanunshi yana kallonta kamar yadda take kallonsa sai dai nashi kallon mai cike da tsananin mamakin jin abinda ta fad'a ne sai daya d'auki wasu mintuna sannan ya motsa bakinsa ya fara magana "idan har da gaske kinji ddin dawowarta na gode "yaya hisham me kake nufi ?". abinda kike nufi nima shi nake nufi ya fad'a a d'an tsawa ce ."

Ta girgiza masa kai jikknta na rawa tace "walalhi har cikin zuciyata naji dadi sosai kuma allah yafi kowa sani meye acikin zuciyata ,meye riba ta idan naji dadin rashin dawowarta?rashin dawowarta ba zai ta'ba canza zani daga halin da nake ciki ba ta fad'a tare da juyawa ta shiga kitchen bata jima ba ta fito hannunta rike da qaramin cup ta durkusa gabansa ta mika masa tana kallon cikin kwayar idanunshi cike da tashin hankali sakamakon rashin sonta da take hangowa acikinsu ."

Yaki amsa ta kai hannunta ta kamo laulusan tafin hannunsa ta saka cup din ciki ,yaki amsa ya cigaba da kallonta "kayi hakuri kasha zaka ji sauki zugin da zuciyarka take maka "na sani akwai zafi akwai radadi da ciwo sosai abaka wanda baka so ,ka sani ni nana hauwa'u bazan takura maka ba bazan hanaka abinda kake so ba ,idan ma ta kama ka auro nuzla ka had'amu kana da damar yin haka bazan damu ba ."

Idan kuma bazaka iya had'amu ba zaka iya sakina ka zauna daita kad'ai na yarda na amince idan kuma zaka iya cigaba da zama dani shima na yarda na amince koda baza kayi komai na aure dani ba, abu daya kawai nake so daga gareka shine ka bani kwanciyar hankali." tsareta yayi da oly eye's dinsa masu firgitartata a yanzu , hakan yasa tayi saurin kawar da kanta gefe tana danne kukanta."

Bin jikinta da kallo yayi yana mamakin jin abinda ta fad'a ,hakan nan yaji tausayinta ya mamaye jinin jikinsa tana da matukar saukin kai sannan bata da yawon damuwa da fari ta tayi qoqarin tsaida mutuncinsa dana iyayensa har ma dana dangi gabdaya domin auresa, sannnan tayi qoqarin karesa a wajen mahaifiyarsa daya fita yanzu kuma tana tayasa murnar dawowar masoyiyarsa har ma da albishir din ya aurota "kai sakarai ka dawo cikin haiyacinka bata son kaga dole zata fad'a haka ,kai ba haka bane to me yasa taki fad'awa mumy komai bayan taji wayarka da zaka fita .?"

Wani zazzafan numfashi ya sauke yana cewa" idan ni kuma bana raayin aurenta fa? ya fad'a tare da amsar cup din hannunta yana sauke numfashi "bazai ma yuwu kace baka son aurenta ba wannan ma ba abinda hankali zai dauka bane nuzla fa zuciyarka ce ta fad'a tana qoqarin mikewa tsaye zata juya taji ya hard'e mata kafafu nan da nan gbdy ta juyo ta zubo jikinsa a gigice take kallonsa duk da tasan shine ya hard'eta amman hakan nan ta tsinci kanta da bashi hakuri ."

"Ka..Ka... kayi haku... "shiiiii! ya fad'a yana kai cup din hannunsa ya ajiye akan table din dake gefensa ya tsura mata ido suna shakar numfashi juna yayinda ita kam tuni ta runtse idanunta dan bazata iya jurar kallon ba dan duk yadda take jin numfashinsa na saukar a fuska da wuyanta hakan bai sa ta bude idanunta ba ."

laulausan tafin hannunsa ya kai saitin wuyanta sakamakon zafin da yaji ajikinta yayi wani abu yaji ya tsarga masa da sauri itama ta bude idanunta suka tsurawa juna ido muryarsa a rauni yace baki da lafiya ne ."?numfashi ta sauke da karfi sannan ta mike daga jikinsa ta zauan a gefensa tana cewa "lafiyata lau nima haka naji yanayin jikinkina ya sauya."

"Okay yanzu mu ajiye maganar wasa da gaske kin amince na auro nuza ?ta gyada masa kai alamun eh ! ya gyara zamansa yana kai cup din madara bakinsa "nima zan miki abinda kike so amman sai kin shawo min kan mumy ta amince na auri nuzla idan kika min haka zan baki duk wani kwanciyar hankalin da kike bukata daga gareni ".

shiru tayi tana tunanin kafin daga baya tace "dan wannna mai sauki ne zan mata magana kuma in sha allahu nasan mumy zata amince ."shiru Kawa yyi "gsky nana hauwa'u tana da kirki da hakuri dan kwata kwata bai ta'ba tsamanin zata amince ba tunda itama bata sonka ai dole ta amince zuciyarsa ta fda masa haka tsaki yaja domin sai ya sake tsintar kanshi da jin haushi "muje ka kwanta ka huta dare nayi bai ce uffan ba ya mike ya nufi kofar d'akinsu itama tabi bayansa ."

Kai tsaye suna shiga d'akin ya fara zare rigar jikinsa bathroom ya shiga ita kuma ta kakkabe inda zata kwanta ta kwanta tana kokuwa da numfashinta duk da bata son yaya hisham amman bazata so wa kanta kishiya acikin kwanakin da ko goma batayi a gidan miji ba ,hassalima bata tare agidanta ba zuciyarta banda rawa da bugawa babu abinda take wasu siraren hawaye suka gangaro mata ta fara sheshekan kuka tana jin motsin fitowarsa tayi saurin danne kukanta tana share hawayenta ."

Numfashi ta dinga saukewa sama sama ya dawo gabanta ya tsaya daga shi sai 3 qauter dake jikinsa duk wani zati dake jikinsa mai daukar hankali ajikinsa ya bayyana wani tsoro ne qarara ya bayyana akan fuskarta dama zuciyarta gbdy wanda yasata saurin runtse idanunta gam ji tayi ya kwanta jikinta har tana jin saukar numfashinsa ya kai hannuwansa ya d'an matsar daita "ki koma wajen baccinki sannan kukan me Kike yi wa mutane ?"

"Ba kuka nake yi ba " ta fad'a muryarta na rawa "uhm shi wannna kuma ya sunansa?ya fad'a yana kwanciya "qoqari tayita ta danne kuka ya fuskanceta sosai "alokacin da numfashinta Ke sama da kasa ya kai hannu daidai qirjinta inda ya suka sauka akan dukiyar fulaninta wani abu yaji alokaci daya yadda numfashinta Ke sauka da kuma tsarga wa wani abu da yaji mai kama da shoucking "

"Kina jina zuciyarki tayi nauyi sosai da alamun akwai abinda Ke damunta "ta lumshe idanunta tana sauke numfashi kuma har lokacin bai dauke hannusa ba "na rashin son hisham ne ?ta girgiza masa kai alamun a'a "to na meye to?bana komai bane "okay yanzu ki bude baki kiyi kuka mai sauti domin ki rage nauyin da zuciyarki tayi aiko kamar jira take ta bude zatayi kuka dan har sautin muryarta ya soma fitowa taga ya zaro ido tare da bude bakinsa ba zato ba tsanani yaji saukar laulausan lip's dinta akan na nashi .."

"Tsura mata ido yayi batare daya sake cewa komai ba illa kwayar idanunshi daya zuba mata yana jin wani irin sauyi ajikinsa tmkr wanda ake jona masa wutar lantarki cikin lokaci kankani komai ya birkice masa bai san yadda akayi ba ya had'eta da jikinsa still bakinsu na manne cikin juna , sai fidda numfashi nana hauwa'u take cikin jin wata irin kunya sam bada wata manufa tayi hakan ba gudun abinda zai fad'a ne dan yanayin yadda ya zaro ido babu sauki zai iya yin komai ."

Da ba dan period din da nana hauwa'u take ba da babu abinda zai hana hisham saninta ya mace a daidai wannan lokacin wannan shine abinda ya hana komai faruwa amman murza kam ta sha gbdy ya manta wata kiyayya jin dadinsa kawai yake da jikinta ita kuwa babu abinda Ke fitowa daga cikin kwayar idanunta sai ruwan hawaye tare da mugun tsoronsa tana son hanashi abinda yake tare da sheida masa bafa ita bace zabinsa amman tsoronsa ya hanata ."

"Yau ne kawai shima nice na jawo ta fadawa zuciyarta hakan, in sha allahu hakan bazai sake kasancewa ba ,ita dai bata jin wanzuwar tsanarsa ko kiyayyarsa acikin zuciyarta idan ya shirya yin rayuwar aure daita zata bashi dukkanin farinciki idan kuma zai cigaba da nuna tsanarta ne zata janye jikinta sosai hisham yazo hannu gashi babu damar aiwatar da komai lumshe idanunshi yayi tare da komawa gefe ya kwanta yana mayar da numfashi bai san meke damunsa adaidai lokacin ba domin kuwa idan yace yasani yayi karya ."

Bayan ta juya masa tana rufe rabin jikinta ya dan waiga ya kalli bayanta wanda hakan yasa shi jin wani irin ajikinsa gabansa ya dinga tashi tsurawa bayanta ido yayi shape dinta mai matukar kyau da d'aukar hankali,duk da yasan jikinsa na da taushi amman sai yaji nata kamar yafi nashi soft kai everything ko dan bambamci halitta ne jikin ,nuzla ya tuno wanda yasa tunaninsa ya koma kanta itama fa masha allah tana da sura mai kyau da taushi uwa uba kuruciya dan nana hauwa ta girmeta da kusan shekaru hudu zuwa biyar ya dauki kusan mintuna talatin a haka bai motsa daga inda yake ba yana kuma jiyo saukar numfashinta ,numfashi ya sauke ya canza hasken d'akin zuwa mara nauyi sannan ya zame ya kwanta ya d'an janyo gefen bargon data rufa dashi ya rufe jikinsa ."

Washegari hisham ya bude ido bai ga nana hauwa'u ba ya kunna wutan dakin tare da kai idanunshi ya sauke akan agogon dake ajiye akan table it was 9:44tsaki yaja tsaki sannan ya mike ya shiga bathroom ,bathtube ya shiga yayi wanka ya fito black boxcer da black singlet ya saka sannan ya daura kaya akai ya fito fuskarsa a hade ya gaishe da abbansa dake zaune rike da jarida sannan ya shiga dakin mumy domin ya gaisheta ko kallonsa batayi ba bare ta amsa sallamarsa, ahankali ya qaraso har inda take zaune juyar da kanta gefe tayi alamun bata son ganinsa "momy Kiyi hakuri nana hauwa'u ma da kike fushi akanta bata damu ba ."

maganarsa ta sake bata haushi "mumy ina magana "a shake ta juyo ta kalleshi "maganarka bata da wani amfani agareni fitar min a daki kar na qara ganin ka shigo min daki sha sha kawai da bai san ciwon kanshi ba korosa tayi daga dakinta ." ya fito sami abban yana masa complain shima da farko abban bude masa wuta yayi amman ganin yana bashi hak'uri da janyo masa ayoyi akan masu hakuri da yafiya ya hakura shima ya daura da yi masa nasihohi yana janyo masa ayoyi da hadisai akan irin tanadin da Allah yayiwa masu hakuri da biyayya ga iyaye ."

bayan ya gama ya riko hannunsa zuwa dakin da mumy take ya mata nasiha sosai akan hakuri da yaya nan mumy tace "naji na hakura amman ka fad'a masa kar na sake ji ko ganin yaje wajen nuzla idan ba haka ba zaka sha mamakina zaka haddasa gabar da baa san ranar qaresa ba akan nana hauwa'u kuwa zan iya tsine maka "hisham ya dan saci kallon mahaifiyarsa Kmr zai mata kuka "wai momy me yasa yanzu kike yin haka ne ?."abinda bakya yi da

"yanzu ka canza shiyasa nima na canza idan ka só abinda nike son zaka cigaba da ganina a yadda kasani sabanin haka kuwa matsaloli zamuyita samu da kai sha sha mara hankali "Ke dai kiyi hakuri ki bar mgnrsa da nuzla raayinsa ne idan yana sonta ya qara daita tunda allah ya halasta masa ajiye mata sama da daya "a ina ?ba dai wannan yarinyar ba sai dai wata dabam kai watan ma ba dai ina raye ba mu iyayensa mu ishesa misali tunda muka haifesa ya taso mu biyu kawai ya gani ya koyi example daga garemu ".

Abba yayi murmushi yana cewa "wannan raayinmu ne ta yuwu shi kuma bashi da wannan raayin "mumy zatayi mgn abba yayi saurin dakatar daita ta hanyar cewa "abar maganar haka yanzu dai ki sanya masa albarka tare da kyakkywar addu'a da kuma fatan alkhairi acikin rayuwarsa " mumy ta numfasa kana tayi Kmr yadda abba ya umarceta ,hisham sam bai ji dadin kalaman mumy ba ya tashi ya fito ransa a bace ya shiga d'akin baccinsa ."

Nana hauwa'u na gyaran daki taji an shigo ta dan juyo ahankali domin ganin wanda ya shigo , yaya hisham ta gani a tsaye fuskarsa babu alamun fara'a ya sha kunu tamkar bai tab'a dariya ba,tana kallonsa ya qarasa inda durowar mirrow yake yana dube dube ta bar abinda take ta qaraso ina yake ta tsaya gabanta na wani irin bugawa da karfin gaske "me kake nema ?shiru yayi har sai data sake maimaitawa, fuskasa a hade yace "ai Kinsan abinda nake nema ki dauko ki bani "babu musu ta nufi inda ta ajiye wayoyinsa guda biyu da wallet dinsa daman da zata goge saman durowar ne ta canza masu wajen ajiya ta dawo ta mika masa tana cewa "fatan ka tashi lfy?bai amsa ba ya fice daga cikin dakin yana jan tsaki tabi bayansa da kallo ."

lumshe idanunta tayi tana jin damuwa cike da sanyin jiki ta gama abinda take ta fito yana zaune a falo ."Kusa dashi taje ta zauna tana wasa da yatsun hannunta "abinci fa yayi ready ? a qalla ya kusa minti goma sannna yace "bana da raayin ci "tayi shiru ta rasa me zata sake cewa" oh allah ban ta'ba tunanin zan yi irin wannan rayuwar ba ,sai yanzu take ganin gskyr maryam akan yayanta aure ba abu ne da zaka iya sadaukar da rayuwarka akanshi ba domin abune da mutuwa ce kawai take rabawa tashi yayi ya nufi wata kujerar yana dane dane a wayarsa ."

Readers Also Read