Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 41
Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 41: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 41. maryama na tsaye har kusan mintuna shabiyar ATA bai gama…
3,152 words
maryama na tsaye har kusan mintuna shabiyar ATA bai gama wayar da yake ba haka zalika bai bud'e kwayar idanunshi ya bata umarnin zama ba haka ma segun na tsaye bai zauna ba adaidai lokacin da qarfe d'aya na rana ta buga wanda a daidai lokacin wasu masallatan sun tada sallarsu dan haka ranta ya soma 'baci ta soma tunanin an janyota ne kawai dan a sake wulakantata a karo na biyu ji tayi kamar ta juya ta wuce shi da segun ta kama gabanta ,ta kalli inda segun yake tsaye shima ya kalleta haka nan ya tsinci kansa da shafa mata qirjinsa alamun tayi hakuri "segun !yes sir ya fad’a cike da girmamawa ya mika masa farar takardar dake rike a hannunsa batare daya bud'e idanunshi ba "ina bukatar copy's dinsu "okay sir ya amsa ya fita da sauri ."ko bayan fitar segun ata bai bud'e idanunshi ba bare yayi mata magana sai kuma taga bai kamata ace tana jiran sai shi ne zai fara mata magana ba dole dai sai itace zata fara masa magana kafin ya saurareta ,dan haka ta qara taku d'aya ta tsaya daidai saitin kunnensa cikin muryar dake nuna alamun gajiya "ta gaishesa bai amsa ba sai ma ya matsa baya ransa a 'bace yayinda zuciyarsa na tafasa dan ya tsani yazo jira duk abinda zaayi masa dole shi zaa jira karo na farko kenan daya zauna jira jiran ma akan itace zata qaru dashi .”
wulakanci da yayi mata yayi mata ciwo, dan ta tsani disgi da wulakanci kamar taja masa tsaki ta fice daga office din sai kuma tayi wani tunani su manyan nan haka halinsu yake kafin kayi nasara akansu dole sai ka kwantar da kai dan haka ta sanyawa zuciyarta hakuri tayi kasa da muryarta da kanta tana wasa da yatsun hannunta "ranka shi dade lokaci na tafiya yana da kyau abani aikin daya kawoni nayi ga kuma lokacin sallah yayi ina buqatar nayi sallah "sake jin sautin zazzakar muryarta ya sanyashi bude idanunshi ahankali tamkar mai tsoron ganin wani abun agabansa ,ya zuba mata tsumammun idanunshi masu mugun rikitarwa yana kallon cikin qwayar idanunta dake d'auke da zara zaran gashi ido itama shi take kallo tana jira daga garesa ". shiru yayi yana cigaba da kallon cikin kwayar idanunta gabansa na wani irin luguden bugu da karfin gaske,kallon da yake wa kwayar idanunta kallon né na sani "jiki a sanyaye ya nuna mata wata kofa dake manne da office din "ki shiga kiyi alwala "yana gama fad'ar haka ya juya mata baya .”
shiru tayi kafin ahankali cikin sanyin jiki ta juya ta shige toilet ta d'auro alwala ta fito ta tada sallah a natse yana zaune yana kallonta yana waya ,ganin har ta idar da sallah bai tashi ba bare shima yayi tunanin ya tashi yayi sallar yasa tayi zaton ko ya manta daita acikin office din ne hakan yasa ahankali ta matso kusa dashi ta motsa labbanta"sir abani aikin da zanyi bani da ishashen lokaci da gefen idanunsa ya kalleta a d'age sannan muryarsa ta biyo baya a dake "kece kika zana ni? muryarta a sanyaye tace "eh nice sir !kinsan ko ni waye ?"shiru tayi har kusan mintuna goma tana nazarin maganarsa sannan cike da girmamawa tace "eh sir ! "Waye ni ?ya sake tmbyrta a dake tamkar bashi yayi maganar ba "kai ne shararren dan kasuwan nan da kasar nan dama duniya gabad'aya take ji dashi "tana gama fad'ar ya juyo a matuqar fusace ya fuskaanceta yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "shine dan iskanci kamfanina ya buqaci yin aiki dake amman kikayi rejecting?ya qarasa maganar a matukar tsawace yana zare mata idanunshi .”
nan da nan hankalinta yayi matseefar tashi tayi saurin matsawa baya jikinta na kyarma "aikin banza kawai yanzu haka ke din ba diyar kowa bace amman kin d'auki girman kan tsiya kin d'aura wa kanki nonsense" yana gama fad'ar haka ya mike ya barta tsaye sake da baki "nice nonsense? ta tambayi kanta cike da mamaki jin abinda ya fad'a mata “nonsense!ta sake maimaitawa a fili tana mai jin d’acin kalmar domin tunda take ba’a ta’ba dangantata da kalmar ba .tana kallonsa ya nufi wani d'aki tana mai jin wani irin tuttukin bakinciki tare da damuwa mai tarin yawa har ya tura kofar zai shiga sai kuma yaja ya tsaya yana jan tsaki "give me ten minutes " yana gama fad'ar haka ya qarasa shigewa .” runtse idanunta tayi "wannan kuma wani irin sabon salon wulakanci da 'bata lokaci né ? ya kuwa san me ake kira da zane ?"abu ne da yake bukatar isashen lokaci "ita bama kanta take ji ba kamar yaya sadam mutumin daya sadaukar da farincikinsa ya biyota cike da zafin zuciya ta juya zata fita daga office din sai ga mr segun , ya tsaidaita yana cewa "ina zuwa kuma ?zan wuce ne dan bana tunanin aikin nan zai yuwu "calm down madam ki samu natsuwa kiyi abinda ya kawoki baqaramin sa'a kika taka ba da mai gida ya bukaci yin aiki dake "yana 'bata min lokaci gashi tare da mijina muke "nasani yanzu me yace ko tunda na fita bai yi magana dake ba ?"Yayi a qarshe wai na bashi ten minutes ."tayi mgnr kamar zatayi kuka "ok kiyi hakuri ki bashi lokacin dayace kin 'bata sama da awa acikin office din nan sai mintuna goma né kawai zai gagara watakilla ma bazaki yi aikin a yau ba ,zai baki ne kije gida kiyi idan kin gama sai ki kawo cike da jan hankali ya dinga karfafa mata zuciyarta dan haka ta cigaba da tsayuwar jiran ATA ."
kusan mintuna goma sha ya d'auka sai gashi ya fito tare da furta "kika ce kice kika zana ni? Kamar tace masa a'a dan taga abun nasa akwai rainin hankali ciki .amman sai ta tsinci kanta da jin tsoro dan haka ta maida kwayar idanunta ta lumshe masa tana wasa da agogon tsarka hannunta wanda ya qara wa zanen lallenta kyau ,lallen yabi da wani shu'umin kallo tun da yake bai ta'ba ganin zanen lallen da yayi masa kyau har ya d'auki hankalinsa ba sai nata yaji kamar ya kamo yatsun hannunta ,ya d'ago idanunshi a natse ya kalli fuskarta nan da nan idanunsu ya tsarke cikin juna wannan karon sauri cire kwayar idanunta cikin nashi tayi tana mai kawar da fuskarta gefe tare da danne bugun zuciyarta "shi kuwa wani yanayi ya tsinci kanshi ciki mai sarkakkiya da wuyar misaltuwa sakamakon idanunsu da suka sake tsarkewa cikin juna abinda ya lura atattare daita itama tana da jin kai da miskilanci"a natse ya sake bin zanen lallenta da kallo wani irin kallo ta watsa masa gabanta na fad'uwa wanda ta rasa dalilin jin haka ."
Ahankali ya samu waje akan kujerun kushin dake office din ya zauna batare daya bata umarnin zama ba "bata zauna ba sai ma idanunta data tsura masa tana kallonsa tana sauke numfashi dan itama taci alwashin bazata yi mgn ba har sai yagaji dan kansa yayi . abinda batasani ba shi ko ajikin ATA da zasu kwana a haka ma bazai damu ba abinda yasani ne ba zai barta taje koina ba har sai tayi masa abinda yake buqata daga gareta ."ya lumshe tsumammun idanunshi yana jijiga kafarsa d'aya yana jira daga gareta ."a qalla sun kusan minti talatin yana zaune ita da segun suna tsaye ta kalli agogon dake d'aure a hannunta a karo na kusan biyar a kasan ranta taja qaramin tsaki bata san me ya janyota zuwa wannan aiki ba nan take kwakwaluwarta ta shiga aikin neman mata mafuta ."kafin ahankali ta samo zance zuci"maryama dole ki ajiye komai ki qarasa gabansa Kiyi masa magana idan aikin nan zai yuwu ayi idan bazai yuwu ba ya sallameki ki kama gabanki tun kafin hakurin mijinki ya qare"da sanyi jiki take qarasowa zuwa inda yake ahankali ahankali har ta iso ta zauna a kujerar dake facing dinsa "wani irin zane zanyi "? tayi tmbyr cike da sanyi murya "ahankali ya motsa lip's dinsa "ina kayan aikinki ?da hanzari ta bud'e jakar kayan aikinta ta fito da kayan aikinta tare da janyo kujerar gabanta zata ajiye ta jiyo sautin muryarsa "ba'a nan zakiyi ba” ya fad'a tare da mikewa tsaye "biyoni ! "
fitowa sukai daga office din yana gaba tana biye dashi haka ma segun yayinda gbdy hankalinta ya rabu gida biyu wani yana gurin mijinta wani yana gurin ATA ."wani office ya shiga daita kai tsaye gaban wani farin baod yaja ya tsaya tare da jingina jikinsa da bango segun yayi saurin janyo kujeru guda biyu daya a gaban baod din dazaayi zane d'aya kuma a inda ATA zai zauna "sir ka zauna ! ya zauna tare da daura kafarsa d'aya akan d'aya jiki a sanyaye maryama ta zauna tana jiransa sai daya gama shan kamshinsa sannna ya sallami segu ya fara mata bayani tana jin ya fara magana ta d'aura hannunta akan boad ta fara fidda kyakkyawar shep din jikin zanen da yake buqata , yana mata bayani tana zanawa lokacin data zana karan hancinta taji wani mummunar tsoro ya shigeta cak ta tsaya ta kasa cigaba da zanen da take ta tsurawa baod din gabanta ido kwaayr idanunta ta zana da hancinta har ma da yanayin jikinta babu abinda yazo zuciyarta kamar zanenta data gani a office din m . malik “ nan da nan gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta.shi kuwa gyara zamansa yayi sosai yana kallon zanen lallen hannunta da yadda take tafiyar da aikinta bai san ya'akayi ba yaji saukar hannunsa akan hannunta yana shafawa ."
Cikin gigita gangan jikinta ya kama rawa wanda yasa ATA ya dawo haiyacinsa sai dai ya kasa d'auke hannunsa ajikinta da kwayar idanunshi wani irin tsoro da matsanancin firgici ATA yaga ya bayyana afuskar maryama ,yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da karfi numfashinta ya soma barazanar d'aukewa, cikin sanyin jiki ta sabule hannunta cikin bacin rai tace "meye haka ?"dan allah aiki nazo yi banason irin wannan wasan iskanci mai barazana ga rayuwata wannan ya zamo karo na farko da qarshe karka sake kuskuren sake kai hannunka jikinta "ta fad’a tana jan tsaki" ajiyar zuciya ya sauke tare da kafa mata tsumammun idanunsa cikin sayin murya yace "look at me “ta kallesa Kmr yadda ya buqata babu wasa acikin kwayar idanunshi "Kinga nayi miki kama da dan iska ?sosai kuwa dan gashi naga alama daga zuwa aiki sai ka bige da kai hannunka jikina batare da kayi laakari da ni din matar aure bace ko kuwa budurwa bace ".hakan nan yaji ya tsinci kanshi da adduar allah yasa single ce ba matar aure ba ya sake kai hannunsa tsintsiyar hannunta tayi saurin zare hannunta har agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta ya zame cikin nashi “wai meye haka dan allah nifa matar aure ce kuma tare da mijina nazo aikin nan “ta fad'a hankalinta a matukar tashe shiru yayi yana qare mata kallo qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin karfi wanda baya jin haka akan kowace mace sai akan mafarkinsa.”
ahankali ya motsa labbansa "ko zan iya ganin fuskarki ?"ya tmbyeta yana qara gyara zamansa "no !ta bashi amsa a matukar tsorace ya sauke numfashi tare da mikewa tsaye ta sake ja baya tana cewa "karka matso kusa dani domin bazan ta'ba kasancewa cikin wawayen mata masu cin amanar mazajensu ba ganin tana nema ta fice daga hayyacinta ya sanyashi kamota hadi da zaunar da ita "lokacin daya kamota wani irin socking ne ya ziyarci zuciya dama gangar jikinsa nan take bugawar da zuciyarsa take ta qaru fiyye da kaida sai dai ya kasa magana a fili sai a zuci "ki natsu wallahi babu abinda zan miki ni kaina bansan meke damuna ba yau , tun da kika kasance tare dani naji komai nawa ya sauya .” Yayi shiru tare da tsura mata ido ita kuwa banda bugawa babu abinda zuciyarta keyi, neman hanyar guduwa take daga garesa ."yayinda wasu irin hawayene masu azabar zafi suka taru a kurmin idanunta "wallahi ka cuceni tun da nake babu wani nmj daya ta'ba kai hannunsa jikina tun ina matsayin budurwa sai yau dana kasance mallakin wani tana gama fad’ar haka ta fashe da wani irin kuka "okay ki zauna ki qarasa min aikina na sallameki and ki yafe min bisa kuskurena kafin ya gama mgnrsa har ta soma tattara kayan aikinta ta zuba cikin jaka ta fice da sauri ."da sauri ya fito ya biyota yana kiranta "ke!!!
"ita kuwa da sauri sauri gudu gudu ta shiga lift ta danna grand segun ne ya fito da sauri sakamakon jin sautin muryar mai gidansa , cikin gigita segun yace sir meke faruwa ne ?"karka bari yarinyar nan ta wuce ka tsayar min daita !ka tsayarda ita segun amman ina cikin kankani lokaci maryama ta sauka kasa tana goge hawayen fuskarta cike da tashin hankali ta nufi inda motar yaya sadam yake a pake jikinta na wani irin kyarma ta bud'e ta shiga ta zauna kallo d'aya yayi mata ya fahimci tana tattare da damuwa nan da nan ya rud'e ya shiga jera mata tambayoyi "ka taimakeni yaya sadam ka bar garin nan dani akwai matsala "wacce irin matsala ?zan maka bayanin komai idan mun isa gida daga haka bai sake cewa komai ba yaja motarsa a guje suka fara qoqarin ficewa koda segun ya fito har motarsu ta fice daga ma'aikatan ."
Wani irin gudu yaya sadam ke falfalawa akan titi yana cikin gudu ya hango wasu motoci gudu uku abayansu suna biye dashi idan ya rage gudu suma sai su rage gudu haka idan ya qara gudun motar zasu qara "maryama kamar ana binmu ki fad’a min meke faruwa ? ta kasa magana kawai ta fashe masa da kuka dan bazata iya fad'a masa abinda mai kamfanin creation yayi mata ba ,ya zama abun kunya gareta ace ta fad'a masa wani kato ya ta'ba mata jiki ya zai dauketa ina yarda da yayi mata ?"kuka ta cigaba da yi shi kuma yana falfala gudu akan titi shi kansa kana kallonsa kasan a matukar tsorace yake sun yi tafiya mai dan nesa sannan suka nemi motocin uku dake biye dasu suka rasa sai daf daa zasu fita daga ogun state kawai sai ga motocin guda uku sun sha gabansu."cak yaya sadam yaja burki ya tsaya cikin tsananin fargaba wasu tika tikan murd'ad'd'un mutane suka shiga firfitowa daga cikin motar d'aya bayan d'aya har suka fito gaba d'ayansu sanye da kaki wanda ke nuna alamun sojojin nigeria ne wani irin matsanancin tsoro da firgici ne ya kama marayam tayi saurin riko hannun yaya sadam gam cikin nata jikinta na kyarma shima ya riketa gam bai yi tunanin ko yan fashi da makami bane sakamakon kakin dake sanye ajikinsu zuciyarsa tafi bashi wani abu dabam ,mutun uku daga cikin sojojin suka qaraso da sauri suka bugi kofar motar da karfi batare da 'bata lokaci ba kofar ta bude basu tsaya wata wata ba suka fito da yaya sadam tare da buga masa bakin bindiga nan take ya zube kasa .”
maryama ta saki qara mai sauti ta fito ta durkushe gabansa cike da matsanancin tsoro yaya sadam ya janyota zuwa jikinsa ai kuwa ta kamkamesa dan gabad'aya a tsorace take hawaye né ya soma bin kuncin maryama cikin sheshekar kuka maryama ta soma magana "bayin Allah laifin me mukayi maku ?dan Allah karku cutar da ni da mijina ,dan allah ku barmu mu wuce tunda nasan bamuyi maku laifin komai ba "ke ce bakiyi mana laifin komai ba amman shi wannan bakin munafikin yasan abinda yayi mana "inji cewar daya daga cikinsu da sauri maryama ta tsurawa yaya sadam idanunta tana kallonsa "wai kai dan rainin wayo ko ?mu zaka rainawa hankali ?".a d'an rud'e yaya sadam yace "Nifa duk ban fahimceku ba hasalima ban san laifin da nayi maku ba ,su waye ku ?meye hadina daku ?laifin me nayi maku ?ya jera masu tambayoyin yana sake riko maryama jikinsa "kai karka nemi ka rainawa kanka hankali dan ubanka kayi tunani laifin daka aikata acikin satin nan wanda kai kanka kasan dole zaa iya bibiyarka?".
yaya sadam yayi shiru yana nazarin maganr shi dai asaninsa bai aikatawa kowa laifin komai ba baya ga auren maryama da yayi "har kusan minti biyar yaya sadam bai ce uffan ba yasa suka cigaba da magana "me taurin kan tsiya kawai amman tunda baka tuna ba idan kaje lahira zaa maka bayani dalla dalla akan taurin kan da kayi ,kai jojo ku daukosa mu aikasa lahira yadda yayi taurin kai dan son more duniya bazai zauna a duniyar ba "nan da nan suka rufe masa ido da bak'in kyalle ,suka d'aure masa hannayensa duka abayansa kafafunsa ma a d'aure ,suka rufe masa baki suka ciccibosa suka watsa shi acikin mota "itama yarinyar kuyi mata kamar yadda kuka masa ku sata acikin mota ku had'a daita batare da 'bata lokaci ba aka rufe fuskarta aka tasa keyarta cikin mota tunda tashiga motar take rutsa kuka mai ta'ba zuciya tare da kiran sunan Allah yayinda yaya sadam yasa hannuwansa duka ya dafe goshinsa yana zurfafa tunaninsa alokacin da motocin suka karya kwana cikin wani kungurmin daji mai cike da duhu da ban tsoro suna sharara gudu."
tunanin duniya yaya sadam yayi amamn iya tunaninsa bai ga wanda zai iya masa haka ba idan safiya ce yasan baa akansa zata huce ba sai dai akan maryama tunda tasha fad'a masa muddin taganta sai ta aikata lahira ."nadiya kuwa yasan kwata kwata bazata masa haka ba shi kuwa wa yayiwa laifi ?"idan ma laifi ne to sai dai akan auren maryama da yayi ne to waye wanda zai masa hk ?bai samu amsar tambayarsa ba yaji motocin sun ja wani irin burki sun tsaya a daidai karshen dajin tare da bubbud'e kofofin motocinsu a zuciye, na karshen ne ya fito rike da kwalar rigar yaya sadam wanda babu halin yin kwakwaran motsi ballantana yasamu damar yin ihun ceton ransa da'ake barazanar raba shi dashi, ahankali suka shiga jansa a k'asa suna tafiya dashi cike da tsansar rashin imani , wanda kallo daya zaka masa kasan a rikice yake d'aya daga cikinsu ya rike hannun maryama ."
Basu tsaya akoina ba sai a bakin wani katon rami suna huci "ku binnesa da ransa jin haka yasa maryama ta rikice ta gigice tashiga wage wage tana kiran sunan yaya sadam "dan girman allah karku kashesa karku binnesa da ransa gara ku kasheni wallahi banason na rasashi yana da matukar mahimanci arayuwata na bada rayuwata fansa, gara ku dauki raina ku barshi dan Allah karku kashesa duk wani abu da zaku masa kuyi min ni daman nafi bukatar mutuwa da rayuwata dan bana jin dadin rayuwar nan na rasa komai karku bari na rasa mijina tausayinta ya kamasu "d'aya daga cikinsu ya jawosu gefe yace "me kuka ga zaa yi ?"ya tambayesu "kar mu batawa kanmu lokaci wajen tausayi mu cika aikin daaka ba mu "shikenan a wuce gurin .”