Kenza eBookz

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 42

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 42

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 42: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 42. aiko suka dauki yaya sadam suka jefa cikin rami suna shirin…

3,306 words

aiko suka dauki yaya sadam suka jefa cikin rami suna shirin jefa maryama mutun daya acikinsu wanda shine yafi jin tausayin maryama yace mu barta tunda daman shi kadai aka bamu aiki "okay! suka amsa. a matukar gigice take batasan ya’akayi ba ta zare kyalen da suka rufe mata ido dashi tana gama bude idanunta yaya sadam dinta ta gani acikin rami suna zuba masa kasa zuciyarta ce ta tsaya cak ta daina aiki a lokaci har suka rufesa da ransa ." Bayan sun gama suka hau jijigata a gigice ta dawo haiyacinta idanunta na zubar da hawaye wani razananniyar qara ta saki da karfi tana kiran "ina mijina yake ?idan har kun kashesa ku had'a dani ku kashe dan allah karku barni a raye dan bazan iya rayuwa babu shi ba haka ma mahaifiyarsa ." numfashi suka sauke atare "aikin gama ya gama yarinya tuni mijinki mai taurin kai yana cikin nan suka nuna mata inda suka binnesa, an gama da labarinsa sai dai uwarsa ta haifi wani idan an sake haifosa a duniya bazai sake kinjin magana ba "ai tana gama jin maganarsu numfashinta ya soma barazanar d’aukewa "me yasa ?me yasa zaku masa irin wannan hukuncin inna lillahi wa inna ilaihi rajiun me yasa zaku kashesa tayi taku biyu zata isa inda suka binne mata miji kafafuwanta suka gagara daukarta ga wani irin nauyi da kanta yayi idanunta suka fara rufewa jiri take gani nan take ta zube kasa sumammiya ."

Mmn Sudais

💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 26

Ran ATA a matukar 'bace yake zaune acikin jirginsa yana tunanin maryama ,wani irin ciwo yake ji a zuciyarsa dan bazai iya misalta yanayin bugun zuciyarsa ba ,ga wani sara da kanshi ke masa har baya iya bud'e idanunshi sosai yayinda kowani second 'bacin ransa na sake nunkuwa wanda baya raba d'ayan biyu damuwar maryama ce bai san dalilinsa na kai hannunsa jikinta ba ."mai yasa yaji sauyi ajikinsa adalilin sake d'aura kwayar idanunshi akanta ?"mai yasa yaji yana buqatar ganin fuskarta a zahiri ? yana jin wani irin sauyi akanta lallai yana buqatar ganin halittarta a zahiri zuciyarsa ta amsa masa kuwan haka ." da wannan tunanin ya isa gida alokacin da magariba ta kawo kai .jirginsa mai saukar ungulu na gama tsayawa a haraban gidansu rai a 'bace yake tattaka matattakala yana qoqarin saukowa , kai tsaye ya shiga bangaren mami sosai yake jin damuwa acikin zuciyarsa qoqarin danne damuwarsa yayi dan kar hankalin mami ya tashi sai dai kallo d'aya tayi masa ta fahimci akwai damuwa atattare dashi ."

"muryarsa a kasalance ya gaishe da mami ."kamar ko yaushe ta amsa masa tana mai tsura masa kwayar idanunta kamar wacce taga wani sabon halitta ,cike da kulawa tace "sannu da zuwa adamcy ya hanya ka dawo lafiya ?da sauri ya amsa mata da "lafiya !"yana qoqarin hayewa samansa hannunsa d'aya soke acikin aljihun wandonsa .bayansa tabi da kallo "shigowarsa cikin wannan yanayin yasa duk mami ta d'an rikice kasa samun kwanciyar hankali tayi ,cike da tashin hankali ta mike tsaye tabi bayansa . ahankali ta tura kofar parlour'nsa ta shiga duhu falon dan haka ta kunna wuta nan da nan haske ya haskaka koina a parlour'n sai dai bata gansa ba dan haka ta nufi hanyar bedroom dinsa ta shiga nan ta iskeshi tsaye ya jingina jikinsa da bango d'akin yayi sama da kanshi hawaye ne kwance acikin idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa ya rasa meke masa dadi arayuwarsa bai san ta ina zai fara ba ,komai ya rigada ya tsaya masa gabad'aya baya jin dadin rayuwarsa ,ya kasa fahimtar kansa ko kuma yace yau tazo masa da abubuwa da yawa wanda duk tarin damuwa ne akan wanda yake ciki ya dinga jin kamar ya kashe kansa ya huta da rayuwar da yake ."

lumshe tsumammun idanunshi yayi sai ga hawaye sharrr na bin kuncinsa "adamcy nah ! ".mami ta kira sunansa cikin tsananin tashin hankali har jikinta na rawa . amatukar firgice ya tsaida kwayar idanunshi dake cike da ruwan hawaye akanta qirjinsa na wani irin dokawa da sauri dan bai ji motsin shigowarta ba sai sautin muryarta wani irin zazzafan numfashi ya sauke yana sake maida kanshi sama tare da ciro hanky ya shiga d'auke hawayensa"lafiyarka kake zubar da hawaye adamcy ?ta tambayesa cikin tsananin tashin hankali dan duk abinda zai sashi zubar da hawaye baqaramin abu bane da muninsa ya wuce misali. shiru yayi ya kasa magana dan bai san me zai fad'a mata ba "kayi min magana mana adamcy dan kasa har zuciyata ta fara tsinkewa." da yatsan hannunsa ya nuna mata daidai saitin zuciyarsa dake bugawa fiyye da kaida ."sake matsoshi tayi sosai tana cewa "meke damunka "?"zuciyata sweet.." yana kai wa nan yayi shiru ya kasa cigaba da maganar idanunshi na sake cikowa da ruwan hawaye"me ya samu zuciyarka ?" ta sake tambayarsa hankalinta na qara tashi "I don't know what's wrong with me sweetheart amman dai nasan zuciyata kullum ciwo take min"."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun " allahumma rahmataka arjun fala takilni ila nafsiy d'arfata'ai wa aslihli shahni kullahu la ila a illa anta "abinda mami ta shiga furtawa kenan tana sake maimaitawa " i know something is wrong with my heart wallahi sweetheart akwai ciwo mai zafi acikin zuciyata wanda zai iya kasheni nan kusa .."

nan da nan fuskar mami ta qara sauyawa hankalinta a matukar tashe tace "ka dinga sausautawa kanka adamcy da yawon tunani ,ka dinga addua akan duk abinda ya dameka addua tana canzawa bawa qaddararsa kuma tana saka natsuwa acikin zuciyar bawa "numfashi ya sauke da karfi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ,magana yake son yi amman zafin da zuciyarsa keyi ya hana shi cewa uffan "kasamu natsuwa adamcy ka dinga furta wannan adduar zaka samu natsuwa da sausauci a wajen Allah zai yaye maka dukkanin damuwarka "allahumma rahmataka arjun fala takilni ila nafsiy d'arfata'ai wa aslihli shahni kullahu la ila a illa anta ahankali ya sauke idanuwanshi ya tsura ma mami kawai yana kallonta cikin yanayi na tsanani damuwa "ka sani idan wani abu ya sameka nice farkon wacce zata fara shiga damuwa ga kuma d'an cikin jikin maryam wanda bamu san abinda zata haifa ba karka bari muyi maraicinka. adamcy kasan yadda nake sonka idan na rasaka zan shiga damuwa a kullum adduata na mutu na barka a duniya ba ka mutu ka barni ba tunda ta fara magana bai ce mata uffan ba sai ma ciro wayarsa da yayi ya soma neman layin likitansa muryarsa ce ta katse mami daga maganar da take masa ahankali yake magana tamkar mara lafiya "doctor kazo ka dubani please ".daga haka bai sake cewa komai ba ya katse kiran d'akin yayi tsit tamkar babu mutane acikinsa ."

Ahankali ya soma d'aga kafafunsa zuwa Kan gado ya fad'a ya kwanta flat ransa duk babu dadi yayinda idanunshi na kallon saman d'akin babu abinda yake gani sai kwayar idanun maryama da yatsun hannun ta da sautin zazzakar muryarta mami tazo ta zauna kusa dashi tana daura hannunta saman kansa tana masa sannu "bayan mintuna shabiyar sai ga doctor ya shigo tare da sallama tashi yayi ya zauna ya jingina bayansa da abun gado yana sauke numfashi da kyar tare da yiwa doctor bayanin yadda yake ji batare da 'bata lokaci ba doctor ya fara masa gwaje gwaje bayan doctor ya gama yayi masa allura sannan yace "ranka ya dade jininka ne ya hau kad'an yana da kyau ka dinga saukakawa kanka wasu abubuwa dan zuciyarka na bukatar hud'u yanzu dai nayi maka allurar bacci in sha allahu kana tashi zakaji daidai Allah ya baka lafiya ya ajiye masa magunguna yace zai wuce ."mami tayi masa godiya adaidai lokacin da doctor ke had'a kayansa yayi mata sallama ya wuce ."

"Ka tashi kayi sallah magriba kafin bacci ya d'aukeka sannan me za'a kawo maka coffe ko tea "any one sweetheart." ya furta tare da mikewa da kyar ya shiga bathroom ita kuma mami ta fita kawo masa coffe dan tasan shi yafi bukata wanka ya fara sannan yayi alwala ya fito ya cire kayan jikinsa ya canza zuwa jallabiya brown colour mai ratsin baki ya isa inda abun sallarsa yake ya gabatar da sallah bayan ya idar ya koma Kan gado ya kwanta lamo tare da janyo bargo ya rufe jikinsa koda mami ta dawo d'akin ATA na bacci ta zauna gefensa tare da zuba masa idanunta tana jin wani irin qaunar d'anta na ratsata bata iya dogon fushi dashi hakazalika bata son ta rasa shi. hawaye ne ya fara bin kuncinta ji take a duniya data rasashi gara ta rasa komai dan idan ta rasashi ta ina zata cigaba da rayuwa?" ina bazata iya ba bazata iya jurar rasashi ba gara ita ta bar duniyar tun kafin taga mutuwarsa ahankali ta mike tana goge hawayen idanunta ta qarasa ta rage masa karfin ac sannan ta canza masa wutar d'akin zuwa mara haske ta duka daidai fuskarsa tayi masa addua sannan ta fita daga d'akin ."

Washgari tun da yayi sallah ya koma bacci har karfe goma bai tashi ba yana kwnace yana sharar bacci shigowar mami yafi sau uku dubashi yana bacci sai dai ta kalli fuskarsa ta fita sai wajen shadaya da wasu mintuna ya tashi hanyar bathroom ya nufa ya fad'a yayi wanka ya fito yana goge sansar jikinsa ya sanya kananan kaya masu matukar kyau he look very attractive kullum ka kallesa qara kyau yake ya d'auki kwalbar turare yana feshe jikinsa yana fesa turare kwakwaluwarsa na tunanin maryama da sauri ya ajiye kwalban turaren hannunsa ya qarasa inda ya ajiye kayansa na jiya daya cire ya dauki dogon wondonsa ya shiga laluba wondon cikin kankanin lokaci ya ciro agogon sarkarta .yayi shiru yana kallon agogon yana ganin tsinysiyar hannunta aciki "mai yasa zuciyata ta damu akanki ? zuciyarsa tace "kasani ko ubangiji ne ya turo maka ita cikin rayuwarka da wata manufa a boye kayi duk yadda zakayi tayi aiki akarkashinka sosai ya dinga jin damuwa akan abinda yayi mata abu ne da bai tabayi ba .wai ya kai hanunsa jikin wata mace da sunan ta burgeshi ya dauki kusan mintuna goma yana kallon agogon tsarkar sannan ya bud'e durowarsa ya jefa ciki ya fito yana taku . "

cike da isa yake taka step, tun daga kan step yake jiyo sautin muryar baba qarami yana tafiya da kyar har ya sauko kasa ya tarar da mami zaune a inda ta saba zaman a parlour'n gabanta kuma baba qarami ne zaune yana magana cikin tsananin fushi tunda yayi masa kallo d'aya ya dauke kanshi bai sake kallon inda suke ba ya wuce dining ya dibi abinci da kanshi ya a zauna akan kujerar dake kallon step bayansa kawai zasu iya hangowa haka zalika duk abinda suke fad'a yana jinsu bayan ya gama cin abinci ya d'aga kanshi yana kallon agogon dake manne a parlour'n dake walwalin haske karfe 12:00 na safe ne yanzu mikewa yayi ya qarasa gurin mami yace "sweetheart ni zan fita mami tace "kai da baka da lafiya ina kuma zaka ka dinga hutawa dan Allah ?" numfashi kawai ya sauke batare da yace komai ba "ka zauna akwai maganar da babanka yazo dashi shiru yayi yaki zama "banason musu kayi abinda nace "a natse ya samu waje ta zauna still bai kalli inda baba qarami yake ba bare ya gaishesa "magana ce yazo daita akan hindu me kasani akai ?zuciyar ata a dake ya fad'a mata komai game da abinda ta aikata ."

baba qarami ya kalli ata yana jin haushi irin haushin da mutun zai iya kashe mutun "na dauka ko wani ka ga yayiwa hindu haka sai inda karfinka ya qare kuma zaka taimaki rayuwarta amman wulakanci ka bar min 'ya a tsare har tsawon watani sannan aka wuce daita gidan yari bancin na tashi tsaye da haka rayuwarta zata qare . tsakanina da kai adamu allah Ya isa ban yafe maka ba duniya da lahira "kayi hakuri baba qarami duk abun bai kai haka ba zai sa a sakota in sha allahu "wani irin kallo ata yayiwa mami ta juyo ta kallesa a tsanake tace "me yasa kayi haka adamcy ?dokarki nabi kikace a dauki mataki akan duk wanda yayi yunkurin kashe miki maryam ko ba haka ba ?mami tayi shiru tana dubansa sam bashi da tsoro akan komai "naji amman kasa a sakota bana jin ma itace zata aikata haka "kiyi hakuri sweetheart babu ta yadda zaayi na saka baki saboda abinda ta aikata mummunar laifi ne kuma ta amsa da bakinta ta aikata "a gidan ubanka ta amsa haka ?" "mugun kawai mai mugun hali ni nasan hindu bazata aikata hakan ba sai dai idan azabtar daita akayi yasa ta amsa laifin da ba nata ba gefen bakinsa ya ciza da karfi "nifa duk abinda zaa fad'a akaina ba damuwata bace idan kuna da hujjar da zata wanke kanta tayi ,ku kuma ku sake shigar da qara kotu amman ni Adam bazan saka baki a fito da tantiriya yar tasha irinta ba." tayi laifi kuma ta amsa laifinta dole hukuma ta hukuntata ni na gama magana sweetheart ko zan iya tashi ?"daga baba qarami har mami suka zuba masa ido suna kallonsa ranshi fess ya mike yayiwa mami sallama ya wuce yana fita ya iske masu tsaronsa a inda suka saba tsayawa suna ganinsa suka qaraso da sauri cike da girmamawa suna gaishesa atakaice ya dinga amsa masu batare da bata lokaci ba aka bude masa bayan mota ya shiga suka bar gidan a can parlour'n mami kuwa hakuri kawai take bawa baba qarami tana tabbatar masa lallai hindu zata fito ya bar komai a hannunta da kyar ta samu ya wuce sai dai kallo daya zaka masa kasan ransa a bace yake kuma zai iya aikata komai akan adam ."

*****

Bangaren maryama kuwa har karfe goma na dare babu su babu labarinsu, aunty da umma da habib da sauran yanuwan ummah wadan da suka zo biki da dangin mahaifinsu da basu wuce gida ba duk suka damu sukai ta neman layinsu amman shiru ga dai wayoyinsu yana ringin amman ba d'agawa nan fa hankalinsu ya tashi matuka zuciyarsu ta fará tsinkewa gabad'aya suka taru acikin parlour'n umma cikin jimami da tashin hankali ."Allah sarki umma duk yadda take jin mummunar faduwar gaba da tsinkewar zuciya amman sai ta dake ta kasa nunawa kowa damuwarta da yanayin da take ji sai ma ta dinga kwantar masu da hankali tana cewa "babu komai wata killa yanayin aikin ne ko kuma ababen hawa né sukai yawa a hanya "haka suka kwana zaune cikin tashin hankali da zullumi ." washegari kuwa tun da asuba fari habib da a bokinsa faisal suka d'auki hanyar ogun state kasamcewar duk inda maryama zata aiki tana tura masa address gabad'aya habib baya cikin natsuwarsa ji yake kamar zuciyarsa zata buga hakan ne ma yasa sam baya ganin gudun da motar tasu take akan titi har ma yaji kamar su fita su canza wata motar kamar bazasu kai ba sai gashi sun karaso jikinsa na tsuma kamar wanda ake zubawa ruwan zafi suka dauki hanyar ma'aikatan isarsu ke da wuya aka sheida masu sunzo amamn tun a yammacin jiya suka wuce cikin tsananin tashin hankali habib ya shiga kiran number aunty kira d'aya ta dauka tana kiran sunansa nan dai habib ya sheida mata komai tunda aunty ta kira sunan habib idanun ummah ke kanta tana jiran ta gama wayar taji mai zata fad'a ganin yadda ta fashe da kuka tana salati yasa ummah ta dawo kusa daita jikinta na wani irin rawa "balkisu meke faruwa mutuwa sukai ko me ?

"Cikin muryar kuka aunty tace "ummah wai tun da yammacin jiya suka baro kamfanin salati ta saka tana addua tare da karfafa zuciyarta data aunty "karki damu balkisu babu abinda zai samesu koma menene in sha allahu Allah zai kawo masu mafuta ta fad'a tana share hawaye "gsky ummah ina ji ajikina akwai wani abu dake faruwa dasu." numfashi ummah ta sauke cikin karfafa ma aunty zuciya "haba bilkisu ki daina wannan tunani kisa aranki babu abinda zai samesu "Allah yasa amman tun jiya da yammaci suka baro kamfani amman har zuwa wannan lokacin babu su babu alamunsu "ke dai kiyi masu addua kawai ta fad'a cike da tausayawa kanta dan ita kanta tana ji ajikinta akwai wani abu dake faruwa dasu sai dai tana fatan ya zama alkhairi arayuwarsu gabad'aya."ta mike ta shiga dakinta ta zauna cikin tsananin tashin hankali hawaye ne ya dinga zuba daga idanunta ahankali idanunta ya sauka akan frem din hoton sadam dake ajiye akan qaramar durowarta yana sanye da kananan kaya ya daura rigar sanyi akan kayan idanunshi manne da bakin glass ,tayi shiru kawai tana kallonsa kallonsa take saboda shi kadai ne ya rage mata a duniya bata da uwa bata da uba bata da miji yanzu idan wani abu ya samesa dole zata shiga damuwa ta qarasa zancen zuci tana fashewa da kuka mai ban tausayi "in sha allahu bazan rasaku ba sadam da maryama ina maku fatan alkhairi a duk inda kuke Allah ya dawo mun daku cikin koshin lafiya ."

suna nan zaune cikin tsananin jimami da tashin hankali har yamma sai ga habib da abokinsa ajigace suka karaso gida sakamakon yanayin damuwar da suke ciki cikin tashin hankali aka kira baba gali da sauran yan'uwan dangin mahaifinsu cikin kankani lokacin suka hallara dan daman suna bangaren aunty hassana .bayan sun gama jin komai suka fara zuba ruwan maseefa hajiya fatima tace "ai duk abinda ya faru laifin umman sadam ne dan itace ta basu gudunmuwa tafiya , inda take shiga batan take fita ba nan da nan sauran yan'uwa suka kama ita dai ummah shiru tayi kawai tana karanto duk adduar datazo bakinta ita yanzu batasu take ba yadda ya'yanta zasu dawo gareta take ."yadda suka wuni jiya cikin tashin hankali haka suka wuni yau din ma dan har karfe 12:00 na dare ba labarinsu ummah tace kowa yaje ya kwanta aga zuwa gobe ."washgari baba gali da habib da sauran yanuwa maza suka bazama nemansu har ogun state din aka sake komawa sai dai babu wani labari duk hankulansu a tashe yake aunty kuka kawai take ummah kam tayi dauriya habib ma kuka yake yana kiran sunan maryama da yaya sadam abun gwanin ban tausayi ."

bangaren aunty salma kam abun yayi mata dadi fiyye da tunanin mai karatu ,dan adduar mutuwa ma ta dinga masu ,allah yasa mummunar hatsari suka samu a hanya "burinta daman maryama ta bar duniya ko kuma tayi rayuwar kaskanci ko zama babu aure. sai gashi burinta ya cika batare da ta 'bata kudinta ba ,tana zaune baba gali ya shigo ya tsaya akanta "salma ina fatan dai babu hannunki cikin rasa sadam da maryama ?wani irin kallo ta watsa masa "idan da hannuna me zai faru ?Aa to gsky ni dai babu ruwana kuma muddin da hannunki Kiyi maza kisa a dawo dasu "gsky a wasu lokutan sai naga kamar kana bin bayana amman kuma wani lokacin sai naga kana nuna min wariyar launi ,kai yanzu meye damuwarka dan an nemesu an rasa kai daya kamata kaji dadi kayi farinciki an nemesu an rasa maryama bazata yi rayuwar jin dadi a gidan ba zata bar ya'yanmu suyi rayuwarsu cikin jin dadi ko da yake shi kanshi yusif din yanzu mun rasa gane kanshi ko shekaranjiya da suka zo daurin aure da abbansa bai leko inda muke ba da alamun aikin daakayi masa ya fara barin jikinsa sai an sabanta wani sabo ".

Readers Also Read