Kenza eBookz

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 43

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 43

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 43: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 43. "ni yanzu ba wannan bane damuwata ki fad'a min gsky da…

3,203 words

"ni yanzu ba wannan bane damuwata ki fad'a min gsky da hannunki a rashin dawowar su gida ko babu hannunki ciki ?"ta sosa idanunta da hannunwanta duka tace "babu hanuna !"to amman ai shekarajiya naji kina waya da malaminki kina cewa ayi duk yadda zaayi a salwantar da .."kaga dakata daka ji ina magana cewa nayi a salwantar dasu duka ko maryama ?to ai ni ko maryama ma bana son ta rasa rayuwarta bare kuma sadam "tsaki taja tana turo masa baki "ai daidai ne ma idan sadam ya mutu idan bakasani ba bari na fahimtar da kai, idan sadam ya mutu kai ne zakaji dadin rayuwarka dan duk wani abu daya mallaka zai zama naka halak malak kai da sauran yanuwanka hassalima naka ne zai fi na kowa yawa tunda bashi da magaji ,mahaifiyarsa ce kawai ita kadai ranta kuma bazata gajesa ba "kinji zaki sake lalata komai ni dai bana son ran kowa ya salwanta a hannuna ".yana gama fad'ar hk ya fice tabi shi da kallon kaskanci tana ta'be baki "ina ganin shima wannan sokon sai nasa an gama min dashi gabad'aya na huta tai murmushi "wallahi ina farinciki da rashin dawowarsu allah yasa ko gawar su kar agani ."

Maryama kam cikin wani jahili gida su jojo suka nufa daita a sume can wajen gari a tsakanin lagos to ile ife , gida ne na sirri wanda ba kowa yasan dashi ba gida ne da mai gidan ya gidana domin taronsa na sirri ko kuma duk sanda zai holewarsa ko kuma wani meeting sannan yana ajiye mahimman abubuwansa agidan ,gida ne mai hawa daya kuma agyare yake babu abinda babu acikinsa najin dadin rayuwa gida ne wanda babu wanda zai san an shigar da mutun sai su da kansu idan sunyi raayin asani ." a babban parlour'n sukai masauki tare da wanda ya basu aiki shima kuma ba gidansa bane gidan abokinsa ne ya amshi key a hannunsa kai tsaye ya nufi bedroom suka biyosa da maryama kan wani makeken bed din dake dakin ya nuna masu suka shimfideta "aikin ku yayi kyau sosai fa .gabad'aya suka kwashe da dariya shikenan an kashe boss kowa ya huta sosai kuwa suka amsa masa atare tsaye yayi yana kallonta yana sauke numfashi yana lashe lip's dinsa "kusan wani abu ?gabadaya suka girgiza masa kai "da alamun yarinyar nan ta shiga comer?nima abinda na fahimta kenan "idan dare yayi ku dawo ku dauketa ku bar nan daita domin bata da wani sauran amfani agareni , ku dauketa ku kaita duk hospital din da kuka ci karo dashi amatsayinku na sojoji bazaayi wani bincike akanku ba, kuce kun tsinceta ne a hanya cikin wannan yanayin ."an gama!" zuwa gobe zakuji alert dina "okay babu matsala ."

Da misalin karfe goma ba daren ranar mutun biyu acikinsu suka fitar da maryama wacce bata san halin da'ake ciki ba suka nufi wani hospital daita yadda akace suyi haka sukai suka ajiyeta da wayarta da jakarta suka qara haba taimakon gaugauwa aka fara bata sai dai har zuwa washegari bata farfado ba har sanda aka kira number number wayarta suka dauka tare da sheidawa wanda ya kira halin da'ake ciki ." Kallo daya zaka yiwa su ummah ka tabbatar da cewa baa cikin nutsuwa walwala da kwanciyar hankali suke ba, tunda suka duro hospital bayan wayar da sukai da ma'aikatan hospital din ,daman kuma tun ranar farko da tafiyarsu sadam din basu sake samun isashen bacci da nutsuwa ba har sai da suka daura kwayar idanunsu akan maryama "me ya sameta haka da har ta fice hayyacinta bata gane kowa?,me ya kawota asibiti "ina sadam da suka ganta ita kadai kwance rai hannun allah? kamar kar su zo ta fara sambatu tana kuka tana kiran sunan yaya sadam tana fad'ar irin abinda akayi masa aunty Kuka ta fashe dashi cikin tsananin tashin hankali tana bubbu qasa tana fad'in "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "dan allah karku kashesa dan Allah ku fito min dashi daga cikin rami ,su waye suka sakaku wannan aikin ku fad'amin wanda ya sakaku zan mika masu rayuwata dan bana son na rasa yaya sadam .wannan mummunar kissar dani yafi dacewa bada bawan Allah kamar shi ba dan Allah ku fito min dashi "tana ihun fad'ar haka sai taji anfasa wani razanannen kuka akanta mai kukan tana fad'ar "lahaula wala kuwwata " me ya samu sadam shikenan kin kaishi an kashe mana shi"inji cewar aunty hassana ummah kam kalmar innalillahi wanna ilaihi raji'un kawai take furtawa "wannan yarinya me yayi miki da zaki sakamasa da wanna muguwar sakayya."?

farkawa maryama tayi ta ganta akan gadon hospital cikin yan'uwanta dana ummah ,ummah ta riko hannunta cikin nata tana mata sannu aunty kam kuka kawai take tana furta adduaoi, cikin haka doctor ya shigo ya sallamesu gabdaya domin duba jikin maryama sai bayan daya fita suka dawo dakin suka cigaba da zage zage har sai da ummah ta dinga taka masu burki , duk wanda zai yi magana sai ummah ta hana tare da cewa yaje waje maryama na bukatar hutu a qarshe dai daya bayan daya suka fice sai daga baya suka dawo har dare babu wanda ya sake cewa komai sai da irin kallon da suke binta dashi babu sausauci ."maryama dake kwance cikin tsananin tashin hankali ta zuba ma ummah dake zaune a gefenta ido tana dubanta ,itama umma ita din take kallo duk ta fita haiyacinta yadda idanunta suka kunbura sukai wani irin girma sun bata tsoro matuka yayinda gabad'aya fuskarta tayi jajur saboda kuka ahankali ummah ke mata nasiha tana tofa mata addua wani irin yanayi maryama ta shiga alokacin da idanunta da kwakwaluwarta suke sake hasko mata komai daya faru ."

a natse ta dinga bin kowa dake gurin da ido sai dai taga wani irin mugun kallo suke mata zuwa can taji aunty hasana na cewa "ji yadda take bin mutane da kallo wannan yarinyar fa muguwar munafuka ce dan allah tashi ki fad'awa mutane inda kika kai mana d'anmu daga rakiya ai wallahi baki isa ba sai kin fito mana dashi dan shi kadai muke kallo a matsayin mahaifinsa ."mikewa maryama tayi jikinta a sanyaye har ga allah tafisu bukatar yaya sadam arayuwarta sannan yadda suke nuna mata baya mata dadi duk da tasan basa qaunarta amman batayi tunanin zasu zargeta ba kanta ta daura akan cinyar ummah tasa kuka tare da jin wani kullin abu ya tsaya mata yaki gaba yaki baya "ummah ce ta dinga rarrashinta tana yiwa aunty Hasana fad'a "wallahi ummah bansan mutane nan ba bazan iya cutar da mijina kuma danuwana ba wallahi ina son yaya sadam ." "nasani maryama bazaki ta'ba iya aikata hk ba cikin jin dadin kalaman ummah maryama tasa kuka tana cewa "ku taimakeni ku nemo min yaya sadam domin ban san inda zan saka rayuwata ba tana kuka ummah na share mata hawaye duk da itama hawayen take sosai hankalin mutane ya tashi kowa kuka yake a wajen ".

"ummah Kiyi hakuri ki yafe min nayi nadamar fita wannan aiki ban san me ya jani na aikata haka ba kuma wallahi na daina farinciki da iya wannan aiki da nayi arayuwata ummah kuzo muje inda aka binne yaya sadam da ransa zaa iya samunsa a raye ina ji ajikina bai mutu ba hawaye umma ta share amman maryama kwanaki biyar kenan da faruwar wannan alamarin kina ganin zai rayu "?numfashi ta furza mai zafi "ummah !"sai kuma tayi shiru tana wani irin kuka tana tuna kalamansa na qarshe gareta "abinda nake so dake maryama ki natsu sosai kiyi abinda ya kawoki ina sonki ina kuma alfahari dake na kuma yarda dake a duk inda zaki kasance nasan zaki kame min kanki da kuma mutuncina wani sabon kuka ta fashe dashi "ummah ta riko hannunta gam cikin nata itama kuka ta fashe mata dashi sosai cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunan allah tana cewa "laifin me d'ana yayi masu wannan hukuncin yayi tsauri ga rayuwar sadam babu wanda zuciyarsa batai rauni ba aunty da wasu daga cikin yanuwa hawaye suke dan tausayawa ga umma d'aya bayan suka dinga barin dakin inda dakin ya saura daga aunty sai ummah da maryama "umma muje inda aka binne yaya sadam a fito dashi jikina na bani yana nan a raye ummah ki tausaya min wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba "ki samu natsuwa maryama in sha allahu zamu je gobe"iya abinda ummah ta iya fad'a kenan bata sake cewa komai ba dan bazata iya magana mai tsawo ba ."

washegari aka kai maganar gurin hukuma aka shigar da qara tare da nuna hoton yaya sadam daga nan aka yiwa maryama tambayoyin daya dace sannan aka saka maryama gaba sai hanyar ogun state tafiya suke tana share hawaye tana addua duk kwanar data gani sai ta rikice tace nan ne . sai an tsaya tace a’a ba nan bane ahaka suka kusan kaiwa cikin ogun state dan daga inda suke suna iya hango sambaod din wel come to ogun state tayi sauri tace “ kamar kafin mu kawo wannna sambaod din ne .”cak direba dake tukasu ya tsaya tare da juya Kan motar suka koma dayan hannun sun sha wahala sosai a qarshe dai ta gane daidai inda sojojin suka sha gabansu saka makon warin takalminta data gani yashe a gefen titi .” jikinta na rawa ta soma kuka tana cewa "ku tsaya nan ne !"batare da bata lokaci ba suka firfito “tabbas anan ne suka sha gabanku “ta fad’a tana kuka .daya daga cikin jami’in tsoro yace a ina aka binnesa nan maryama ta hau zazzare ido “tabbas daga nan suka rufe mana ido amman duk da haka jikina na bani wannan kwayar suka shiga damu basu mutsa mata ba suka shiga mota suka bi hanyar tafiya suke amman jikin maryama rawa yake dan bata son tayi kuskure wajen gano wajen .”

gabad’aya babu inda baa duba ba ko zaa ga alamar tudun kasa amman babu ,jami'an tsoro suka tsaya suna kallonta "kin tabbatar nan ne?tayi shiru tana share hawaye dan gbdy ta rikice ummah Ummah duk ta rude sai zufa take fitarwa ta matso kusa daita tace “maryama ki natsu da kyau a samu a gano inda suka binnesa” tayi mgnr cikin rawar murya maryama ta fashe da kuka tare da zubewa kasa sakamakon ta rasa mafuta.”dan kwakwaluwarta ta cunkushe waje d’aya yadda maryama take kuka haka umma take kuka tana janyota jikinta gabdaya jikknta ya d’auki zafi kamar garwashin wuta yayind jami’an tsaro suka cigaba da dudduba wajen ko zasu ci karo da tudun kasa amman still dai babu wata alama inda aka binnesa ganin suna bata alokacin su ne yasa suka ce su wuce zaa zaa sanar a gidan radio da tv maryama kam duk ta gama rikice masu sai sunan yaya sadam dina kawai take kira “ku nemo min shi dan Allah karku barni haka da kyar aka samu aka saka acikin mota suka kama hanyar gida .”

******

Shabiyu ne na rana yana tsaye acikin office dinsa sanye da t shirt long sleeve light puppy da wondo baki sai tie baki zagaye da wuyansa ya tura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa wani irin kamshi jikinsa ke fitarwa mai sanya natsuwa da kwantar da hankali fuskar nan tashi a murtuke zariya ya soma yi acikin office din yana tunanin maryama wanda bai san dalili ba tunaninta yaki barinsa babu abinda zuciyarsa yake kwadayin sake gani kamarta kafin ahankali yayi burki a daidai mazauninsa turo kofar office din akayi batare da an nemi izinin shigowa ba ya kalli kofar ammar ya gani yanayin yadda yaga fuskarsa ya dan fahimci akwai wani abu yana gama shigowa ya soma magana cikin tsananin fushi "burinka ya cika maryama tayi aure “ “so what idan tayi aure what’s my business with her ?wai menene matsalarka adam ?"da nayi me kenan ?wallahi ban san baka da sa'a arayuwarka ba sai da maryama tayi aure "tô ni menene damuwa ta da aurenta ?kaga dan Allah karka sake min maganar ta karka qara min damuwa akan wanda nake ciki "kai ne kuwa kake da damuwa daita ."hade rai ata yayi sosai yana yiwa amar wani irin mugun kallo mai bugar da zuciya "kasani inada dalilina na son ku hadu daita tun kafin tayi aure.ata yayi taku daya biyu yana mai juya masa baya wallahi da ka daure kaga maryama da zaka fahimci abinda na gani har yasa nake son ku hadu daita."

juyowa ata yayi ya fuskancesa yana hura masa hanci tare da kai hannu yana sunce tie din wuyansa "kai ma tunda kaga na na nace ai ya kamata kayi amfani da sense dinka ,bazaka ta'ba jin dadin wata mace a duniya ba sama daita" look ammar bana son damuwa ,"my friend you have to use your common sense and think akwai dalili mai karfi dayasa naso ku hadu "ata ya sauke hanunsa daga wuyansa ya maida cikin ajihunsa yana nazarin maganar ammar "ba dai ka rasa maryama ba kasani zuciyarka zatayi nadama fiyye da kowani nadama da d'an adam keyi a rayuwarsa "ya d'ago ya tsurawa ammar idanunshi tare da cire hannunsa d'aya cikin aljihunsa ya rike kugunsa," wasu ma suna janyota jikinsu domin su amfana daita bare kai da ..."wai meye haka ammar ?ka dameni ka cika min kunne da surutun banza da wofi dole ne sai na aureta ko dole sai na janyota jikinta ?"kaga enough please ka rabani da maganar wata maryama din banza bana son jin ko sunanta bare na aureta "yayi maganar a tsawace yana furzar da iska mai zafi "ai kuwa ka shiryawa shiga tashin hankali da damuwa domin duk ranar da zaka ganta kuma amatsayin matar aure sai kayi nadamar rashin haduwarku akan lokaci ,kuma lallai bazan daina fad'a maka rashin haduwa daita damuwa ne akan damuwa kuma har qarshen rayuwarka bazaka daina da kasani ba kai in takaice maka zaka iya rasa ranka ". ata ya dafe goshinsa da hannunsa daya "ammar kana rikita min kwakwaluwa zuciyata tana tsinkewa magangunka gabad'aya suna nema tarwatsa min zuciya gabad'aya na kasa fahimtar abinda kake nufi yayi maganar kamar zai yi kuka tare da zama akan kujera yana kallonsu "you are mad adam yanzu abinda ya rage maka ka zauna kayi tunani akan maganganuna " yana gama fad'ar haka ya buga masa table din gabansa ya juya ya fita a fusace ."

ata ya kai hannu goshinsa kafin daga baya ya soma jujjuya jikinsa akan kujera wani irin ihu yayi yana kai hannusa ya ture tarin file din dake Kan table sannan ya mike tsaye zambur Kmr zaki ya dafe kanshi gabad'aya ya rasa meke masa dadi dan wani irin abu yaji yana yawo acikin ilahirin jikinsa mai kama da abinda yake ji akan mafarkinsa yau shine karo na biyu da yaji wani abu wanda ya shafi mafarkinsa akan wata mace "wacece mai zanen creation wacece maryama datai aure coz the same abu yake ji akansu wanda yake da kusanci da abinda yake ji akan mafarkinsa “karka matso kusa dani domin bazan ta'ba kasancewa cikin wawayen mata masu cin amanar mazajensu ba itama matar aure ce “ya rabbi what’s wrong with me ?yana cikin wannan halin james yayi knocking yana neman izinin shiga sai da ata ya dauki lokaci sannan yace "coming !" ya shiga cikin taka tsantsa "mai gida ina son nayi magana da kai ko zan iya magana ?" leave!" mai gida magana ce mai mahimanci "I said leave bana bukatar jin komai yanzu."da sauri ya juya ya fice .cikin company ranar kam kowa ya kama kanshi dan dukkanin alamun sun nuna an tabosa, duk kuma wanda yayi kuskuren shiga track dinsa zai sha bala'i idan ma bai ce ya kori mutun ba har ya dawo gida maganar ammar na damunsa cikin rai sai yayi kamar ya kirasa ya sake masa karin bayani sai muguwar zuciyarsa ta gargadesa "

Bayan sati d’aya wanda yayi daidai da kwanaki shabiyu da daura auren maryama da yaya sadam sultana ta dirá a kasar kuma kai tsaye abdullahi estate aka nufo daita murna wajen aunty abida abun baa magana ,tun daga lokacin da sultana ta shigo estate din aunty abida ta fara aiwatar da shirinta kullum suna bangaren mami sai dai basa samun ganin ata suna samun sa’banin shiyasa yau sukai sakamakon yau .ahankali yake ssukowa daga Kan step cikin shigarsa na kullum sai kamshi yake idanunsa bai sauka akan kowa ba sai akan aunty abida da sultana kallo daya yayi masu ya dauke idanunshi ya cigaba da taku har ya wucesu ta mike ta sha gabansa tana kiran sunansa “adamcy barka da saukowa.” ya tsaya kawai yana kallonta batare da yace mata komai ba “ga sister ta kawo mana ziyara Ya ganta ta hadu ko ?still dai bai tanka mata ba tayi murmushin yake tana cewa “daman nace bari na kawota ku gaisa sultana ga cup din tea dinsa can dauko ki bashi .” jikinta na rawa ta juya ta dauko Orenge cup din dake ajiye wanda daman dan shi aka tanada ta mika masa ,sai dai bai kar’ba ba yace "am okay coz am oready late” zai wuce ta sake tsaidashi Ya tsaya cak yana duba agogon dake daure da tsintsi yar hannunsa kamr yadda kasani sultana kanwarmu ce kuma ta kware a harkar zane dan naji ance kana bukatar kwararun masu zane shiyasa nace tazo dan tasan Kan aikinta sosai idan bazaka damu ba ko zaka bata dama kaga irin nata kwarewar ?shiru yayi bai ce uffan ba “.

“nasan bazaka ta'ba zuba ma yaruwarka kasa a ido ba zaka gwada yaruwarka kaga irin nata baiwar bayan shi ma ina son ka taimaka ka bata aiki a maakatarku Z&A idan ma da hali ka barta a kusa kusa da kai wato P.A dinka dan na yi imani zaka ji dadin aiki daita dan ....”duk naji bayaninki.” ya katseta ta hanyar fad’ar haka kafin ya cigaba tayi saurin cewa “ zata joining compaing kenan ? kai amman na gode sosai sultana bana fada miki ba bashi da matsala gashi da sauki kai ga kirki da son yanuwa gyaran murya yayi yace " ammm karki yi Godiya tukun dan bani zan bata aikin ba kiyiwa mijinki magana I know he can do more that for her “mijina kuma ?tai masa tmbyr tana kallonsa tare da nazarin maganarsa tana kallonsa ya zagayesu ya kama gabansa “nifa Aunty duk ba wannan bane matsalata ni dai kawai kisan yadda zakiyi na kasance a kusa dashi nasan komai zai zo da sauki “amman yanzu a gabanki kikaji ina masa magana zaki ce bakiji abinda yace ba, wai nayiwa Ibrahim mgn Ibrahim din da ba wuri daya suke ba .”

Dan allah ayi min afuwa posting zai koma a sati sau daya sakamakon bana samu lokaci ga hidima da mai gidana ga business ga typing sannan ina bukatar hutu Kunga abun yayi min yawa ina maku fatan alkhairi sai Saturday ko sunday in sha allahu.”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 27

Readers Also Read