Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 49
Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 49: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 49. “sannu muguwa! “Inji cewar Aunty hasana “maryama ta kalleta…
3,321 words
“sannu muguwa! “Inji cewar Aunty hasana “maryama ta kalleta a natse batare da tace mata komai ba “nace sannu muguwa ko karya nayi da kike kallona a wulakance ?”daman babu abinda kika iya sai tsiya da mugunta muniyar banza kawai kin wani kafeni da wasu gwala gwalan idanuwa ko zaki cinyeni? still maryam bata ce mata komai ba idan da sabo ta rigada ta saba da halinta sai dai abinda take mata ita da mahaifiyarta yana matukar damunta koma tace ya fara isarta amman tasan duk runtse duk wuya baza ta’ba iya maida mata magana ba yadda batayi magana ba haka umma da granny basu ce ci kanki ba ,maryama ta cigaba da abinda take tana bawa granny labarai masu dadi da kwantar da hankali granny ta lumshe idanunta tana cewa “yauwa diyar albarka ya isa haka ma na gode sosai Allah yayi miki albarka allah ta jikan mahaifinki Allah ya rabaki da mahaifiyarki lafiya walalhi har naji saukin zugin da yake min allah yayi miki albarka allah yasa ki gama lafiya .”maryama ta amsa da “Ameen”. fuskarta da bayyanan ne murmushin na farinciki dan idan akwai abinda ke sakata jin farinciki da natsuwa bai wuce taji kana mata fatan alkhairi ba .”
ATA tsaye acikin office dinsa sanye da wasu hadaddun suit wondo da riga ash colour haka ma takalman dake sanye a qafafunsa ash colour ne masu kyau da tsada yayinda jikinsa ke fitar da wani sanyayyen kamshi turare mai sanyi da kwantar da hankali .muryarsa a dake ya kira sunan sectary dinsa “Some !da sauri ta amsa masa da “ yes sir!” tana mai dubanshi cike da girmamawa da tsananin tsoro bai ce mata komai ba ya cigaba da aiki a system dinsa . yayinda itama ta cigaba da tsayuwa tana kallonsa da bayyanan ne tsoro a saman fuskarta ,fuskarsa babu walwala ya sauke kwayar idanunshi akanta tare da mika mata system dinsa “gashi ki duba sakonin masu neman aiki ne yau tsawon sati d’aya kenan ban samu dama dubawa ba yanzu haka ina son na d’an huta kad’an . “okay sir angama yanzu zanyi komai na gama ,ya dawo kan kujera ya zauna yana lumshe idanunshi yayinda some ta soma abinda ya sakata tana kallonsa ya mike a kan doguwar kujera da yake zaune ya kwanta tare da yin pillow da duka hannuwansa yana kallon saman office dinsa .”
Bayan kamar mintuna talatin ya mike ya shiga bayi ya d’auro alwala ya shiga d’akin dake cikin office dinsa domin gabatar da sallama bai fito ba sai around 2 :30 yana fitowa ya kirata da wayar office ,ta shigo da sauri still rike da system din dan sauran kad’an ta gama duba wad’an da suka cancata tace ” sir gani ! “ya ake ciki ? ta d’ago da sauri tana dubansa sakamakon ganin sunan maryama cikin jerin masu neman aiki “sir !! na duba duka sakonin amman wannna sakon na qarshe akwai ….” kinga kiyi abinda ya dace kawai hanyar fita yayi daga office din “but sir!” kinga akwai abinda zanyi yayi saurin katseta ta hanyar fad’ar haka ya qarasa ficewa ” D’aya bayan d’aya take bin number masu neman aiki har ta kawo Kan number maryama, ta kira number ya kusan sai uku ba’a daga ba a karo na hud’u ne ta d’auka tare da cewa “hello!daga can bangaren aka amsa mata da” hello ko muna magana da maryam hussein ne ? “Yes of course itace muna kiranki ne daga nan AGC company bisa sakon neman aiki da kika tura mana mun duba takardunki da safur din zanenki duk babu wata matsala yanzu dai sai mun ganki domin yin interview ta qarasa maganar a lokacin da ATA ya dawo office din ya zauna ya janyo system dinsa yana dubawa ”nan take maryama ta rud’e ta shiga kallon umma a rikice “aiki kuma ?”ai ni ban tura wani sakon ai …”umma ta matso kusa daita da sauri ta dafa kafad’anta “ki ce kinji ni na tura masu sako neman aiki .”
maryama tayi shiru tana duban umma tana jin wani irin bugun zuciya” ki natsu kiyi magana dasu da girmamawa” nan take maryama ta ‘bata rai amman babu yadda ta iya dan bazata iyawa umma mutsu akan komai ba ,numfashi ta sauke da karfi tace “shikenan yaushe Zanzo domin interview din ?On 28 march tana gama jin haka ta katse kiran tana duban umma “why umma wani aiki kuma nifa wallahi babu wani tsarin aiki arayuwata tunda yusira tana samo min zan dinga yi a gida “.murmushi umma tayi tana cewa “a’a maryama Kiyi shiru kiyiwa kanki fatan alkhairi karki ja da ikon allah “bazan yi jayayya da ikon allah ba amman ni wallahi umma …” kar ma ki rantse idan kika ga bakiyi aikin nan ba mutuwa nayi amman muddin ina raye sai kin ci amfanin karatunki “maryama ta shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace”zanje ne kawai saboda son da nake miki babu yadda zaayi kice nayi abu nakiyi “nima ina sonki maryama shiyasa ma na tura miki neman aiki domin nasan shine cikar burinki wani dalili ne dabam yasa kika ce bazakiyi aiki ba ta qarasa maganar tana riko hannun maryama cikin nata tana jin wani irin a zuciyarta yayinda idanunta suka cika da ruwan hawaye sadam dinta ta tuna .” ahankali maryama ta zare hannunta cikin na umma ta shige dakinta da umma ta barma ta fad’a kan gado ranta duk babu dadi tunanin rayuwarta ta shig yi sannu ahankali har bacci ‘barawo yayi awon gaba daita .”
“sir ina son nace wani abu shiru yayi bai amsa mata ba sai qarar daddana system dinsa kawai akeji sai data maimaita maganarta sannan yace “okay ina jinki na gama duk abinda kasani na kira wad’an da suka cancata “nasan zasuyi matukar murna dan babu wanda zai samu kiran daga kamfanin AGC bai ji dadi ba “sai wacan banzar yarinyar ba .” ya fad’a aciki ransa amman a zahiri cewa yayi “okay !sectary dai tayi shiru taso ya bata dama tun kafin ta kira number maryama amman yaki ,alamarin mai gidan nasu ne sai hakuri shi kawai zaiyi abinda yake so kuma alokacin da ya ga dama amman wani bai isa ba .”parlour’n mami dauke yake da manyan baki domin kuwa baba qarami ne tare da uncle jay da mami da aunty shahida har ma da aunty abida tare da sultana ,table din gabansu cike yake da kayan motsa baki wanda mami tasa aka kawo masu hira tayi dadi sosai inda aunty abida ta sako batun aikin sultana nan take baba qarami yace “ kai diyata karki damu ta shirya kawai ta fara zuwa aiki bama ita ba idan kina da masu bukatar son aiki akarkashinmu ki kawo muna maraba dasu “.
“wani irin murna tayi tana mai jin dadin maganarsa ita dai mami bata ce uffan ba aka cigaba da hira har sanda ATA ya shigo mami na ganin shigowarsa ta mike zuwa kusa dashi dan tasan baya son azo acika masu gida da hayaniya kuma baqaramin aikinsa bane yayi abinda zai korasu gabadaya “abinda ya bawa mami mamaki bai wuce yadda sultana ta mike tazo ta tsaya gabansa ba tana wani irin rausaya da lumshe masa ido “thank you so much for giving me the job ,gsky naji dadi sosai zanyi aiki a qarqashin AGC company “what ?ya fad’a a matukar tsawace yana kallonta kafin ahankali ya motsa lip’s dinsa “ina ganin kamar kin fara shaye shaye wa ya baki aiki a company “?baba qarami !”tayi mgnr tana duban inda baba qarami yake zaune”ni na bata kuma zatayi aiki alokacin dataso saboda itama uwarta nada ‘yanci acikin AGC “gsky baba qarami kana da matukar kirki amman shi wannan d’an naka ya fiyye jin kai ya manta cewar ni dashi asalin mu d’aya “to ai shi Adam bai da wannan kirki kuma duk cikin zuriarmu babu mara mutunci kamarsa amman wannan karon ko yana so ko bai so yarinya dole kiyi aiki a kamfani kwana nan ma zan dawo na cigaba da kula da kamfani dan nasan kan kamfani fiyye da wannan gatalallen yaron mara kunya idan ma naga dama zan iya dakatar dashi dan dama bai iya tafiyar da kasuwanci ba hauka da shirme kawai yasa a gaba saboda rashin sanin kan kasuwanci komai cikin zafin rai da fushi yake.”
ATA yayi shiru yana dubansa a kaskance har ya soma taku zai isa inda baba qarami yake aunty shahida tayi sauri ta mike tare da rike masa hannunsa gam cikin nata tana masa alamar kar yace komai “amman da kin bari nace wani abu saboda yarinyar sam bata dace da aiki a company dinmu ba dan babu abinda ta iya sai hauka “koma dai menene kayi shiru ka barsu qanin mahaifi ne kuma tmkr mahaifi ne abinda kasan baza kayi wa dad yana raye ba karka yi masa albarkasa albarka dad ne ,dan haka ka tafi d’akinka ka huta” mami tace ko akawo maka coffe “no !ya bata amsa a fusace tamkar itace ta ‘bata masa rai, me zakaci ko sai zuwa anjima ?”bana bukatar cin komai ni kawai ku bani dama nayi magana da wancan mutumin” ina mai baka umarni adamcy karka ce masa komai dan Allah kaje d’akinka kuma a yanzu idan kace masa wani abu ban yafe maka ba .”
shiru yayi kafin daga baya ya nufi hanyar d’akinsa har yayi taku uku yaji sautin muryar abida ta kira sunansa da isa ,da kamar bazai tsaya ba sai yayi wani tunani ya tsaya bata tsaya akoina ba sai a gabansa ido cikin ido take kallonsa tana masa murmushin gefen baki mai nuna alamun sunyi nasara daman da biyu suka shirya zuwa dan su aiwatar da nufinsu uncle jay ne kawai tafiyarsa dabam “ya kaji umarni da baba qarami ya zarta nasan baka ji dadin haka ba ko? amman dai aikin gama ya rigama ya gama ko kana so ko baka so kamar yadda ya fad’a sultana sai tayi aiki kuma a duk inda take so koda kuwa acikin office dinka ne baka isa ka tsaidaita ba, tunda ka kasa bata aiki wanda yake da iko akanka da kuma kamfani ya bata dama yanzu sai kayi duk abinda zaka..”ai bata kai ga qarasa maganarta ba taji saukar wasu lafiyayyun mari ji kake tass tass !! har guda biyu ajere akan kuncinta “enough..!ya fad’a a matukar tsawace gbdy mutanen da ke zaune a parlour’n babu wanda hankalinsa bai tashi ba cikin tsananin tsoro da tashin hankali aunty abida ta tsaya cak dafe da kuncinta tana dubansa fuskarta da bayyanan ne mamaki “Adam ka mareni ? “kad’an kika gani muddin bazaki daina shiga rayuwata ba “ ya fad’a a matukar tsawace .”
Hankalin aunty shahida a tashe ta qaraso inda yake tsaye jikinsa na wani irin tsuma ta dafa kafad’ansa tare da fad’in “kana da hankali kuwa ?”ka kusan wacce ka mara ?matar aure ce kuma matar shakikinka tana magana tana nuna masa aunty abida da hannunta “.iskar bakinsa ya fesar yace “nasan ko wacece kuma nasan matsayinta kuma itama tasan ko waye ni bana cikin irin wadan mutanen da zuciyarsu Ke jurar raini wallahi idan bata daina enter dinta ba wata rana dukan mutuwa zan mata zaro ido aunty shahida tayi jikinta na wani rawa kamar yadda na mami ke rawa kana hauka ne adamcy ?”I don’t know but I fell like na haukace “wai meke damunka ne da kake abubuwa haka ?”dan Allah shahida ki barni kin cika min kunne abinda ya kamata kiyi ki ja mata kunne ta fita hanyata ta daina shiga lamarina that’s all yana gama fad’ar haka ya haye sama da sauri sauri yake taka step .”
gabad’ayansu da kwayar idanu suka bisa dashi har suka daina ganinsa .”aunty shahida ta soma taku zata bisa mami tayi saurin riko mata tana girgiza mata kai”karki bisa shahida kinsan halinsa “an san halinsa mami amman shikenan sai a zuba masa ido ya dinga abinda yaga dama .”?ai daman ita ke daure masa gindin yin iskanci da wulakanci da taka duk wanda yaso dadin abun itama bai barta ba shegen yaro mara tarbiya kawai “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun abinda aunty shahida ta furta kenan alokacin da taji abinda baba qarami ya fad’a tayi data sanin yin maganarta, da kuma tasan kalmar da zai fad’a kenan da wallahi bazatace komai ba jiki a sanyaye mami ta nufi hanyar bangarenta aunty shahida ta juyo ta kalli baba qarami dake qoqarin mikewa tsaye zuciyarta na wani irin tafasa taso kwarai ta furta koda kalma daya ce akan kalmar shegen daya furta ga adamcy amman sai zuciyarta ta gargadeta domin a yanzu ma kuskurenta ne ya janyo ya fad’a abinda ya fad’a bazata so ta sake aikata wani kuskuren ba ranta a ‘bace ta juya tabi bayan mami .”
Zaune ta isketa mami a baki gadonta tayi shiru idanunta na kallon sama d’akinta ta samu waje kusa da qafafunta ta zauna cike da girmamawa ta kira sunanta “mami ! mami ta sauke idanunta tana kallon aunty shahida fuskarta da alamun damuwa aunty shahida tayi kasa da kanta kana ta soma magana cike da biyayya “dan allah mami kiyi hakuri bisa kuskurena sam ban ji dadin abinda baba qarami ya fad’a ba domin idan mutun yace wa d’anka bashi da tarbiya to kai yake son ya zaga ya fake da zagin d’anka “numfashi mami ta sauke tana cewa “karki damu shahida idan da sabo na rigada na saba da halinsa kuma hausawa sukance dan kuka mai jawa uwarsa jifa duk wa ja min koda zagina yayi ?ni dai fatana allah ya canza adamcy allah kuma ya tsaresa daga sharrinsu Allah yasa kafin mutuwa naga canzawarsu aunty shahida ta share hawayen daya zubo mata “menene kuma abun zubar da hawaye ?wallahi mami kalmar tayi min zafi bansan me yasa yanzu baba qarami yake nunawa adamcy kiyayya haka ba ,ji nayi kamar na tanka masa “gara da baki tanka masa ba ai sai ya tabbatar da rashin tarbiyar da yace allah dai ya sawaka kawai zamu ce ahankali suka dinga tautaunawa wanda kusan duk akan adamcy ne .”
*******
On 28 cikin sauri sauri maryama tayi abinda zatayi ta shirya cikin riga da siket blue da ratsin yellow ta dauko after dres ta daura akan kaya tayi rolling din kanta da mayafin after dress din ta rufe koina ajikinta ga kyau ga qarancin shekaru wanda yasa tayi looking very attractive ta fito zuwa parlour’n sai dai duk ranta babu dadi , da granny ta soma cin karo ta durkusa har kasa ta gaisheta “barka da safiya granny “barka maryama fatan kin tashi ?”Lfy ina umma? bata rufe baki ba umma ta fito daga dakinta ta qaraso ta tsaya kusa da maryama ta dafa kafadanta “har kin shirya masoyiya ? maryama tayi murmushin jin dadin sunan da umma ta kirata dashi tace “na shirya umma barka da safiya “kin tashi lafiya ?ta gyada mata kai tana cewa “ alhamdulillah gamu zamu yakin karshe grany ta matso sosai kusa daita “maryama ki bi komai a hankali ki kiyaye banda shiga abinda bai shafeki ba allah ya baki saa a dukkanin abinda kike sa gaba .murmushi maryama tayi tana “cewa Ameen angama kakata ta kaina zan kula da duk abinda kikace, ta juya bangaren umma tana kallonta “sai ku tayani da addua, in sha allahu zakiyi nasara amman kamar kinso kiyi late ?” Aa banyi latti ba zamuyi daidai sai na dawo umma “ai baki karya ba ta fad’a tare da mikewa ta janyo hannuta bata tsaya koina daita ba sai inda ta ajiye mata plet din abincin data zuba mata ta zaunar daita ta soma bata abinci a baki tana ci tana duba mata lokaci har ta koshi ta sha ruwa ta mike tsaye tare da jiran adduarta “fatan alkhairi diyata karki sawa zuciyar karaya ki karfafa zuciyarki kisa aranki matsalarki tazo karshe da yarda allah ki kula da kanki please “in sha allahu ta kalli inda Aunty Hasana take zaune akan kujera wacce ko kallon inda take batayi ba a tun sanda ta fito daga daki sai man karanta wani littafi take .”
jiki a sanyaye kamar kartace mata komai tunda tasan ba fatan alkhairi take mata ba amman dai ta barwa allah komai kuma ko babu komai kanwar mahaifinta ce sai datai adduar samun nasara akanta sannan ta bude bakinta da kyar tace “aunty hasana ni zan tafi interview” fuskatar ta babu yabo babu fallasa ta dago tana cewa “in sha allahu bazaki samu aikin nan ba yadda kika fita da murna in sha allahu da bakinciki zaki dawo gidan nan kinyi sanadin kashe mana d’a amman Ke har kin manta kin fara neman aikinyi jikin maryama yayi sanyi hawaye ya cika kwarnin idanunta “hasana bai kamata ki dingawa diyar danuwanki haka ba “to mama ni meye nayi mata bayan gsky na fad’a aiki ne a gabanta ko zama tayi tunanin abinda Ke damun rayuwarta muddin kina son zaman lafiyarki damu ki kiyaye takurawa yarinyar nan kinji na fad’a miki “ai daman nasan duk kun tsananeni akan wannan yar iskar yarinya irin tsiya irin jaraba kawai masu mugun jini taja tsaki ta dauke kanta akansu .”
Shiru maryama tayi tsaye ta kasa kwakkwaran motsi tana duban Aunty hasana cike da sarewa gbdy sai taji zuwa interview din ma ya fita ranta domin tana ji ajiknta kotaje bazatai nasara ba granny ta janyota zuwa jikinta “maryam ki maida hankali lokaci na tafiya fa karki damu da maganar wannan mayar in sha allahu zaki samu aiki “okay granny na gode sosai “abinda granny ta fada in sha allahu haka ne zai kasance karki manta cewar hasana ba itace takawoki duniya ba dan haka babu abinda bakinta zai miki inji cewar umma idanun maryama suka kawo kwalla muryarta a raunane tace “ni dai ku bata hakuri idan wani laifi nayi mata ta yafe min dan banason tana fadar mummunar kalamai akaina umma idan kin sani bayan babu ran iyayenka addaur yanuwansu tamkar adduar iyayenka ne “. “haka ne amman ita mummunar adduarta bazatai tasiri akanki ba saboda baki mata laifin komai ba ai baza ta’bawa yiwa diyar cikinta mummunar addua ba “Aunty ki daina hada diyar cikina da wannan yarinyar ita din ba diyata bace ya kamata ki fahimta “allah dai ya ganar dake gsky dan ni banga amfani kiyayyar nan ba , idan uwarta tana da laifi dan ta auri danuwanki ai danuwanki ma yana da laifi daya nace sai daya aureta .”inji cewar granny “Ni wallahi umma da nayi zamana dan ina ji ….”bazaki zauna ba kuma babu abinda kike ji sai alkhairi maza kama hanya ki wuce fatan alkhairi allah yayi miki albarka “Ameen ta juya cike da sanyin jiki take daga kafafunta .”
Ganin haka yasa umma ta mike ta biyota tana cewa “ki shiga wajen Auty ku gaisa kafin ki wuce amman kiyi sauri karki yi latti kinji masoyiya maryama tace” to umma na wuce sai na dawo “to sai kin dawo allah ya tsare “fatan alkhairi maryama allah ya bada saa ta fito bangaren mahaifiyarta ta shiga bayan ta gaisheta tayi mata sallama itama fatan alkhairi tayi mata “aunty ina after dad?yana ciki yana bacci “okay ki fad’a masa na tafi interview ku tayani da adduar samun nasara tana qoqarin fita daga part din aunty ta kira sunanta “princess ! ta tsaya cak tare da juyowa ta fuskanci mahaifiyarta tana mai gyara zaman Jakarta a kafadarta“kinyi breakfast kuwa da kike kokarin fita ta qaraso gabanta hannunta rike da cup din tea mai kauri tare da bread bata tsaya jiran mai za tace ba ta kai cup din tea bakinta “bude bakinki ki sha ko kadan ne bana son kina fita batare da kin sakawa cikinki komai ba .”ahankali ta bude bakinta tace “naci abinci daga hannun umma kuma na koshi amman bari naci daga hannunki ta soma kurban tea ba wani mai yawa ta sha ba tace “ya isa haka na gode sosai ta rungumeta tare da yi mata sallama tana fitowa daga part dinsu ta rufe fuskarta da qara min nikaf .”
********