Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 50
Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 50: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 50. Babban hall ne aka tanadar masu ,suna zaune gefenta yusura…
3,228 words
Babban hall ne aka tanadar masu ,suna zaune gefenta yusura ce itama sanye cikin shiga ta kamala kowanne ka gani acikin hall din rike yake da takardunsa na makaranta wasu acikin jaka, wasu rungume dashi ,tun daga Kan matakin diploma har zuwa kan digree na biyu .bayan wani lokaci aka fara kiran suna daya bayan daya har aka kawo Kan maryama da addua ta shiga inda zaa mata interview tana shiga ta yaye nikaf din fuskarta kasancewar taga mace ce ,sectary ta sakar mata murmushin dan ita tun ranar data soma ganinta taji ta kwanta mata arai yarinyar tana da natsuwa gashi tana shiga ta mutunci ko yanzu duk masu neman aiki babu wanda yayi shigar mutunci kamarta “ga guri ki zauna “na gode” maryama ta fad’a a natse tare da zama tana ma kanta addaur samun nasara .” bayan awa daya aka gama daita tare da daukarta aiki “maryama hussein idan allah ya kaimu gobe zaki fara zuwa aiki amman wannna abun da kike rufe fuskarki dashi ba lalla sir ATA ya yarda dashi ba .”
shiru maryama tayi tana jin da kamar wuya ta iya fita babu shi a fuskarta domin ta rigada ta saba tsawon shekaru haka ta taso idan ma bata saka shi ba bata jin dadi” muryarta can kasa tace “zan dai gwada zuwa dashi idan ya bukaci na daina zuwa dashi zan kiyaye na gode sosai.” ta fad’a tana mikewa ta bar office din a wajen ma’akatan ta jira yusira itama cikin ikon allah ta samu suka nufo gida cike da murna yanayinta ya tabbatar ma yan gidansu ta samu aiki ta rungume umma cike da farinciki.” “alhamdulillah umma mun dace “kai masha allah masoyiya gsky naji dadi sosai da kyakkyawan albishiri da kika min ,zuwanki aiki zai rage miki damuwa sosai allah yasa ki fara a saa” maryama ta qarasa ta rungume granny” na gode matuka da adduarku da bani kwarin gwiwa ta shafa kanta “babu komai maryama gabadaya parlour’n umma ya cika da murna aunty da habib ma murna fal anan yusura ta wuni currr suna murna sai yamma tayi masu sallama ta koma gida da zumar sai sun had’u gobe .”
Washegari da misalin karfe bakwai daidai a AGC company tayi masu babu ‘bata lokaci aka nuna kowace office din da zata dinga aiki tare da basu file file da zasu fara aiki akansa basu kasance guri daya da yusura ba ,tare da sultana suka kasance a office daya sosai maryama ta dukufa aka aikinta tana Kan aiki sectary ta shigo ta mika ma maryama wasu file “please ki cike yanzu ki kawo min office dina “okay ma”! ta fad’a tare da amsa ta ajiye aikin da take ta fara wanda aka bata .”sultana kam ko ta Kan aiki batabi ba wayarta ma take opereting can ta soma magana da alamun vioce note take yi “kinsan wani abu qawata gani zaune babu abinda nake takardun banza daakawo gasu agabana haka zasu karaci yininsu bazan cike komai ba kuma bazan zana komai ba dan ba abinda ya kawoni kenan ba.” ta tura tai shiru tana murmushi can sautinta ya sake karade office din “wa wannan mutumin ai bai yi ba wani office aka kaini dabam ba idan yake ba amman duk bata ‘baci ba komai zai tafinmin yadda nake so ai bari Ke dai qawa mutumin nan ya hadu fiyye da tunaninki sai ma kin gansa a zahiri sai kin kusan sumewa .”ta qarasa mgnr tana kam kamkame jikinta .”alamun tana jin shauki akansa .”
Maryama na ciki aiki sai ga subai ta shigo office din hannunta rike da wasu file yayinda wuyata ke makale da ID card mai dauke da cikakken sunanta da tambarin Z&A da sauri ta qaraso gurinta tana dafa kafadanta“wa nike gani haka kamar maryama ?maryama ta dago a natse tana dubanta “a’a subaia wallahi nice ya kike ya kwana biyu ? lafiya kar dai kina cikin sababbin ma’aikatan daaka diba?maryama tai murmushi tana gyada mata kai alamun “eh !”kai gaskiya naji dadi dana ganki a matsayin maaikaciya anan .” Maryama ta maida hankalinta ta cigaba da abinda take ai nasan daman allah bazai barki haka ba kullum ina sakaki cikin adduarta na gode sosai da taimakonki gareni “kai karki damu ai yiwa kai ne fatan alkhairi “thank you dear .”har subaia ta juya maryam ta mike tana kiran sunanta ta tsaya “Yauwa subai’a ina ne office din madam some?muje na nuna miki suka fita tare tana sauke nikaf dinta suna qarasa fitowa ta nuna mata da dan yatsanta”gashi can sai mu sake haduwa nima wani aiki ne ya kawoni sukai sallama ta karya kwana “. ita kuma maryama tayi kokari shiga office din data nuna mata ta tura kofar glass sannan ta sanya jikinta ciki adaidai lokacin da idanun ATA ke Kan cctv “wacece wannan data shigo yanzu “?ya tmby yana dauke idanunshi ya maida kan fara takardar dake gabansa ya juyo mata compute daake ganin shiga da fitar mutane .”
Some ta sauke idanunta akan computer maryama ta gani muryar some na rawa tace “maryama hussein!” “wace ce haka ?”sabuwar maakaciya ce “baki fada mata baa zuwa mana da irin wannna shigar bane ? “na fada mata sir “!yayi shiru yana maimaita sunan acikin zuciyarsa maryama hussein sannan yana sake kallon cctv tabbas itace yarinyar “ wannna ba yarinyar da muka bukaci zanenta bane watanin baya ba ?“muryarta na rawa tace “ita itace sir .” what ! ya fad’a tsawace “nan take jikin sectary ya dauki rawa “dan allah kayi hakuri sir “ itace yarinyar da akayi interview akan kasuwanci daita , yarinyar da take da kwarewa sosai akan zane itace yarinyar da kace anemo ta watanin baya “ kenan the same person ce “? ya fad’a yana ciza lips dinsa da karfi “yes sir duk mutun daya ce itace take zane but sir yarinyar tasan kan aikinta duk a rud’e take masa wannan bayanin.” shiru yayi yana jin wani irin mummunar faduwar gaba from no where sai dai bai dago ba ya cigaba da typing din da yake cikin zafin rai .”kana kallon yadda yake daddana keyboard din system din kasan baya cikin natsuwarsa “bana ce kar a Kuskura a dauketa aiki ba ?kuma kikayi son ranki har ma kina min dogon bayani akan yadda ta wulakantamu”sir !sir !!kayi hakuri nayi ta kokarin na fada maka saboda gudun faruwar haka amman kaki bani dama “.
“me kke nufi ni ban fad’a miki ba karta samu aiki har karshen rayuwarta ba bama a wannan company din ba har other companies?Ke ma kinsani bana bawa kowani irin mutun second chance dan haka kije ki sallameta bana son ganinta acikin company din nan “oya go out ! ya nuna mata hanyar fita jikinta na rawa ta fito .”tana fita ya zabura ya mike tsaye ya daura hannunsa daya akan hannun kujerar daya tashi gabansa na wani irin mummunar faduwa zuciyarsa na tuttukin zafin kamar ya dakatar da some amman bakinsa ya kasa furta komai . ya bar wajen ya koma jikin window yana kallon haraban maakatan yaso kwarai ya samu nasara sake ganawa daita amman ina bazai iya daukar iskancinta ba har kamar shi ya sauke girmansa ya kirata amman taki daukar wayarsa har ma da kashe masa waya ga mummunar sako data fadawa james bayan haka ya nemi ganawa daita a ogun shima batayi masa abinda ya bukata ba sai ma qara masa damuwa datayi jin abun yayi kamar alokacin ya faru babu wani sausauci da zai mata wanda ya wuce ya koreta daga karkashinsa .”
da sauri sectary ta fito zuwa office dinsu tana shiga ta isketa zaune da farar takadar agabanta tana zana mutun sanye da suit da wondo har ma da takalmi acikin mintuna da basu wuce ashirin ba ta tsaya tana sauke numfashi, ganin ita kadai ce a office ta qaraso sosai ta tsaya akanta tana tunanin yadda zatai mata magana dan sam babu dadi ka samu aiki ranar da ka fara zuwa ace an koreka tsayuwarta batasa maryama ta dago ba dan bata ma ji alamun shigowarta ba kokari take ta kammala aikin da ta fara dashi amatsayin aikin farko .”muryar some a sanyaye ta kira sunanta “maryam hussein ! maryama ta dago da sauri tana cewa “yes ma ,akwai wani aikin da zan miki “?”No you’re fared cak numfashin maryama ya nemi ya dauke sakamakon jin mummunar labarin datayi nan take dakin ya dinga jujjuya mata wani irin tashi hankali tashig mara misali kafin a hankali ta janyo numfashinta dake kokarin barinta ta dawo dashi gangar jikinta ta fuskanci sectary sosai hankalinta na qara tashi “wannan hukuncin MR ATA né “.
“Hukuncin Mr ATA”. ?ta furta da karfi tô kaifin me nayi masa nida yau na fara aiki anan ?tayi mgnr Kmr zatai kuka cike da tausayawa sectary ta dafata sai dai ta kasa cewa komai “ko zan iya magana dashi dan haka kawai bazaa dakatar da mutun batare da wani laifi ba ?tayi mgnr a fusace .”no no !! ba sai kingansa ba ,dan ni kaina a halin yanzu ina cikin matsala dan allah ki bar nan yanzu kafin ya shigo “ba maganar na bar nan bane ko kina cikin matsala ina son nasan dalilin da zai sa akoreni tunda nasan sai da dalili akewa mutun irin wannan korar lallai sai nasan meye matsalar kafin na bar maakatan nan ,”ki natsu please maryam sir bazai ganki ba a yanzu .” “Kema kiyi hakuri kiyi min iso Ke bari ma naje da kaina .”fuuuuu ta nufi kofar fita da sauri some ta biyo bayanta tana kiran sunanta “maryama ki tsaya karki sake yin wani kuskure ta riko hannunta cikin zafin rai “bazai yuwa ma ki shiga inda yake ba wannan ya sabawa doka .”
“Doka wani doka kuma ?wallahi kusani kun tafka babban kuskure na korata ,bari ma kiji bani nayi applied din aiki a kamfaninku ba yi min akayi dan haka yanzu ma ban damu ba kije ki fad’a masa ko bansamu aikin a anan ba zan samu aiki adalilin baiwar da allah yayi min kuma bare ma zan samu aiki da takarduna” dan allah kiyi hakuri nima ba laifina bane .”shiru maryama tayi kafin ahankali tace”madam some ko zansa exactly laifin me kika min da kike bani hakuri ?ai nice yafi dacewa na baku hakuri ku da ake nema a wurinku ,amman ku kuwa wani irin tsarin ne da maakatarku hk ?a dauki mutun aiki rana daya da fara aikinsa a koresa ?kiyi hakuri maryam ki wuce kawai karma kisa rai ko a wani guri ma zaki samu aiki domin sir nada karfin iko a koina “to ni laifin me nayi masa haka ?ki tmbyr min shi laifi me nayi masa haka ?tai mgnr tana kuka “ai ban isa najewa sir da wad’an nan tamvayoyin naki ba “to shikenan amman wallahi kisani bazanje koina ba har sai naji dalilin dayasa ya koreni muddin bai fad’a min laifin da nayi masa ba anan zan qarar da rayuwata ..” ta samu guri ta zauna tana kuka mai matukar cin rai “.
“okay maryam bari na gwada saata ko allah zai sa ya saurareni ta juya da sauri ta fice yayinda maryama take zubar da hawaye masu zafi bata san sanda ta zamo kasa bisa gwiwowinta ba ta hade tafukan hannunta guri daya “ya allah meke shirin faruwa dani kuma ?wani irin tashin hankali ne wannan ?daga zarar na fita cikin wata maseefar sai wata ta bullo ya allah ka taimakeni .”a can gida ma hankalin aunty da umma har da granny duk a tashe yake umma ta qaraso da magani da ruwa a hannunta hajiya yau baki sha maganinki ba ga lokaci na wucewa “ni gbdy na ma manta da wani batun shan magani dan bana da natsuwa ban san halin da maryama take ciki ba wallahi hakan nan nake jin damuwa ya allah ka taimake yarinyar nan kasa karshen wahalarta ne yazo “karki damu in sha allahu alkhairi ne zai biyo ba tunda an dauketa aiki ai sai fatan albashi su fara shigowa to allah yasa alkhairi ne zai biyo baya .”ameen ta karbi magani ta kai bakinta .”
ATA na tsaye har lokacin ya kasa zama sectary dinsa ta shigo “sir na fad’a mata hukuncinka amman tace baza tafi koina ba har sai ta gana da kai “no way !” ya fad’a yana jin wani irin faduwar gaba mai tsanani ”I won’t meet her ki koma ki fad’a mata haka” sir na fad’a mata taki tafiya ne wai sai an fad’a mata laifin da tayi daaka koreta aiki daga farawarta yau “kije ki fad’a mata ta bar kanfanin nan dan bazan ganta ba kema da kika dawo min da banzar maganarta idan kika sake zuwar min da mgnrta zaki samu matsala dan kinfi kowa sanin laifin datai ko ba da kanta taki amsar aikin da muka bata a tun farko ba ?”sannan na bukaci zanenta shima taki yarda ta ganni sau nawa ina kiran wayarta taki daga wa ta saurareni sannan nayi qoqarin tayi min aiki a ogun shima babu wani biyan bukata,yanzu kuma ta kwaso jiki tazo neman aiki kamfanina ?kema kinsan bazai yuwu ba ya fad’a a matukar a tsawace .”
Nan take sectary ta kame jikinta na rawa dan duk lokacin da yake mgn cikin fushi itama fita haiyacinta take ya sauke numfashi kana ya dunkule hannunsa ya naushi iska “aikin har yana arha haka ka kisa alokacin da kaso sannan ka samu alokacin da kaso “idan ma baki fad’a mata laifinta ba ungo nan ya zaro wata farar takarda ya mika mata kije ki bata amman ganina ko magana dani abu ne da zai mata wahala acikin wannan kafanin ke qarshen rayuwarta bazata sake ganina ido da ido ba “okay sir tasa hannu ta karba ta juya ta soma tafiya “idan aka sake halittarta a duniya aka bata aiki bazata ki karba ba nonsense girl kawai ya fad’a yana furzar da iska .” Da sauri sectary ta shiga office din da maryama take tana mai kiran sunanta ta mike da sauri ta qaraso gareta tana cewa”laifin me yace nayi masa.” mika mata takarda tayi tana qara mata da bayani abinda tayi hawaye ne suka zubo mata” wayyo allah wallahi bana ki amsar aikin bane a wancan ranar dan yin kaina wata kawata ce tafi ni bukatar aiki shine na bar mata amman badan banason aikin bane” wanna shine dalilin da yasa mr ATA ya koreki kema abinda kikayi bai kamata ba bayan shi ma akan zane shima haka kika masa wulakanci bayan saboda abinda ya faru aranar da kikazo kawo zanensa yaji babu dadi aransa shine ma yasa James yayita kiranki akarshe shima ya kiraki baki dauka ba ,da kuma kika dauaka me kika ce ?”maryama tayi shiru tana dubanta “kikace bazakiyi ba !” Muryarta a sanyaye tace “am sorry !” Babu wani maganar sorry zaki iya tafiya dan bazaki samu wata dama ba “is okay na gode Kwarai da gaske tunda da farko nice naki amsar aiki sannan nakiyin aiki daku yanzu kuma na dawo kuka kini bani da yadda zanyi tunda ku kuke da kamfaninku tana gama magana ta juya da niyyar barin office din idanunta ya sauka akan kawarta subaia “kin rasa aikinki akaro na biyu maryama akaina ?”
“karki damu subai ba akanki bane haka allah ya qaddaromin Kiyi min fatan alkhairi.““ dan allah kiyi hakuri nasan duk laifina ne “nace karki damu ko na karba da farko haka zasu min dan da gani mai kanfani har wadan da suke aiki karkashinsa duk mahaukata ne na ma gode da ban samu aiki akarkashinsa ba suna cikin wannan halin sai ga yusura ta fito daga office din daakaita ,kusa da maryama taje ta tsaya tana tmbyarta “aikinta ta rasa adalilina aikinta da bar min “wata uwar harara yusura ta maka mata “ai gsky ne adalilinki ta rasa wancan aikin yanzu ma ta rasa wanna kenan ?subai’a ta gyada mata kai “a wani dalili ?”Ke !me ma ya kawoki ma tunda ai baa nan kike aiki ba ?karki manta da mai wannan kamfanin da A&Z duk mutun daya ne wani mahiman aiki ne ya kawoni “karku tsya bata lokaci please zaku iya wucewa kuje kasa ku cigaba da magana inji cewar some“maryama bari na dauko jakata mu tafi tare kawai zaman me zanyi ?no yusura karki damu kiyi zamanki bazan zama sanadin rugujewa farincikinki ba ,ina miki fatan alkhairi all the best to both of you tana gama fadar haka ta juya ta soma taku ,da kyar take iya d’aga wafafuwanta saboda nauyin da suka mata ,wani matashin mutun ta gani tsaye bata bi ta kansa ba ta raba ta gefensa ta wuce shi tana sauke nikaf din fuskarta shi kam kamewa yayi ya kasa kwakkwaran motsi shin mafarki yake ko kuwa zahiri yake gani ?.”
ya kai second goma yana kallon bayanta har ta kusan ‘bacewa ganinsa sannan ya juyo ya dubi some “ kinga wata doguwar yarinyar ta wuce yanzu ? “ yes sir ! da sauri yace “ mutun ce ko fataluwa ce ?mutunce sir sunanta maryam hussein “.maryam hussein !? ya furta a dan razane adaidai lokacin da yusura ta fito ta tabi bayan maryama da sauri tana kiran sunanta hankalin salim a matukar tashe yace “Adam ya ganta kuwa ?No sir aiki tazo nema har an dauketa yace akoreta” da sauri yace “kai bari naje na sake tabbatarwa itace ko kuwa dai kama ce ya bi bayanta da sauri ya sauka har kasan kamfanin yana nemanta bai ganta ba tsaki yaja yana cewa “ amman Adam ya cika hauka me yasa bai tsaya yaga yarinyar nan ba yana tsaye sai gasu ita da yusura maryama tana magana muryata da alamun tayi kuka sosai “karki damu yusura ki tsaya Kiyi aikinki karki yi Kuskure irin wanda nayi ,kin dai ga yadda abun alkhairi ya zame min ko? to ki tsaya kiyi aikinki ina miki fatan alkhairi “ta fad’a tana tsaida yusura tare da rike hannunta cikin nata .”Ahankali salim ya kara taku ya matso kusa dasu “shikenan maryama naji kuma na gode da shawarki allah yasa haka shine mafi alkhairi arayuwarki sai mun hadu a gida dan allah karki saka damuwa aranki komai yana da lokaci kuma in sha allahu zai zama alkhairi .”
numfashi ta sauke sannnan ta saki hannun yusura dake cikin nata ta juya itama ta juya ta soma tafiya da sauri kawai taga mutun agabanta yana sauke numfashi bai tsaya wata wata ba kawai ya daga nikaf din fuskata tare tsura mata ido byn Kmr second biyu ya saki wani irin murmushi wanda bashi da maraba dana farinciki muryarsa cike da in.. ina.. ya soma mgn”itace wallahi tabbas itace wallahi itace wacce danuwana ya dade yana nema yayi maganar yana riko tsintsiyar hannunta “dan Allah kiyi hakuri mu koma ciki akwai wanda zan nuna wa ke .”bai gama rufe bakinsa ba ta fixge hannunta tare da daukeshi da wani gigitaccen mari tana cewa “itace wa ?” “Akan wani dalili zaka kai hannunka jikina ?”ammm but da kin ..”“kar kace min komai bana bukatar jin komai dan baka zo da siffar da zan saurareka ba daga ganin mutun sai ka wani kai hannunka jikinsa kasani koni matar aurece ta fad’a a fusace tana sake juyawa ya sake shan gabanta”wallahi babu inda zaki sai na kai ki gurin ..”“wallahi ka sake kuskure tabani sai na maka wulakanci da har ka matu bazaka manta dani ba ,matsa ka bani hanya na qara gaba da rayuwata “.