Kenza eBookz

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 7

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 7

Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 7: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 7. “A tunanina idan akayi aure shikenan kusancinka da miji kan…

3,315 words

“A tunanina idan akayi aure shikenan kusancinka da miji kan sashi ya canza ashe ba haka ba, sai yanzu nake ganin gskyrki da kike kin auren yaya adam hakika shawo Kan yaya hisham ya gagareni bare ya adam” you're my life sister i love you so much duk duniya yanzu kece kawai wacce zan iya fad’awa damuwata ,ina shakar bakinciki a gidan yaya hisham most especially akan nuxla “ ni ban hanashi aurenta ba bare ma ban isa na hanashi ba, kawai ni abinda nafi buqata daga garesa ya kwantar min da hankalina shine kawai abinda nike so amman yaki kullum cikin d’aga min hankali yake ,ga yawon wayan da suke daita wani lokaci har asuba .”

“abinda ya bani mamaki daman nuzla tana son yaya hishsm ne? “ kamar tana son shi sister “idan tana son shi me yasa ta gudu ta barshi?"allah masani nima haka nagani abun nasu har da gayya amman ni na mika lamarina ga allah kullum shi nake roka ya zaba min abinda yafi zama alkhairi “ajiyar zuciya maryam ta sauke dan tuni farincikinta ya gushe ahankali kuma take jin wani irin tsanar nuzla na shigarta domin duk abinda zai damu sister ya dameta kuma zata iya yin komai akai "bari na fad'a miki irin abubuwan da nakewa yaya hisham da basu yi tasiri ajikinsa ba amman ki gwada yi wata kila yayi tasiri ajikin yaya adam "ki rufa min asiri sister kema kin kasa shawo Kan yaya hisham bare ni? “ zaki iya nima da babu digon soyayyarsa nayi bare ke da na fahimci tsananin son da kikewa yaya."

“Kai sister !kai sister ko gsky "baki bazai iya misalta irin son da kike masa ba you just keep it in your mind naunayen ajiyar zuciya ta sake saukewa tace "haka ne sister ina tsananin son shi kuma bana jin zai daina wannan son har zuwa lokacin da numfashina zai bar jikina shine kad’ai muradin raina zan zauna dashi a kowani hali wannan alqawar ne “ shiru nana hauwa'u tayi tana sauraron bayaninta “uhmm ai nasani gbdy yayana ya tafi da komai naki ya bar min saura ."harara maryam ta sakar mata kamar tana gabanta stil fuskarta dauke da murmushi ta cigaba da magana "sister ko bai sona na kasance dashi hakan zai dangwamar dani cikin farinciki ko bazai soni ba zan rayu dashi ."

“Ina rokon allah idan har dole dayanmu ne zai samu farinciki samun soyayyar gidan aure to ya zamanto kece zanji dadi zanyi farinciki domin kece kike tare da abinda kike so ni kuma daman banyi aure dan soyayya ba ,”ni kuma ina rokon allah dukkaninmu mu dace mu samu soyayyar mazajenmu so na har abada “mrym ta qarasa mgnr tana hawaye yayinda itama nana hauwa'u hawaye take zuciyar kowacce na cike da tunani .”maryam na tunanin halin da zata shiga a gidan aurenta yayinda nana hauwa’u ke tunanin halin da take ciki a gidanta sun jima suna waya nana hauwa'u na fad'a mata abubuwan da zatayi domin janyo hankalin yayanta sannan sukai sallama.”

Maryam ta zauna shiru tana mamakin hakurin nana hauwa’u zata iya hakuri akan komai na gidan miji amman banda hakuri akan wata ko bata dauki mataki akan miji ba lallai zata dauka akan duk wacce zata ra’bi mijinta ,mijinta nata né ita kad’ai dan haka babu wacce zata daukarwa rainin” ta dade zaune tana saka da warwara kafin daga bisani ta mike ta nufi d’akin mami inda su aunty shahida suke,jiki a sanyaye ta tura kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama gbdynsu suka maida hankalinsu gareta cike da girmamawa tace “aunty shahida me zaa daura maku ?.”

Aunty shahida tayi murmushi kana ta dubi sauran yan’uwanta tace “ me zaku ci ? duk abinda zaki ci shi zamu ci “okay mrym kin iya fankaso?mrym tayi shiru na second biyu sannan ta gyada mata kai alamun” eh! “tô kiyi mana fankaso na kwana biyu ban ci ba ,suma kuma nasan zasu ji dadi ahankali tace “tô !ta juya ta bar d’akin zuwa kitchen tana kiran masu aikin gidan cikin kankanin lokaci suka bayyana agabanta nan ta fad’a masu abinda take son su tayata ita kuma ta soma qoqarin kwa’ba fulawa duk abinda mrym tayi ranar cikin sanyin jiki tayisa tare da tunanin halin da nana hauwa’u take ciki .”

Washegari da misalin karfe shida na yamma ATA ya tashi daga bacci wanda ya soma tun karfe biyu dan baccin ne ma ya dawo dashi gida, mika yayi tare da salati sannna ya sauko daga shi sai boxer ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya fito kugunsa d’aure da towel yayinda hannunsa ke rike da wani qaramin towel yana goge sansar jikinsa bayan ya gama ya feshe ilahirin jikinsa da body spray sannan ya qarasa inda kayansa yake ya dauko blak and whit rigar mai hade da wula ya saka yayi kyau sosai tamkr wani matashi d’an shekara talatin a duniya ya gabatar da sallah la’asar ya fito parlour ’nsa ya bud’e fridge ya dauki holladia milk mai sanyi ya sha sannan ya sauko daga samansa ya nufi gurin mami yana qarasowa ta ajiye jaridar hannunta tare da mika masa hannu.”

ya qaraso ya zauna kusa daita kallonsa tayi cike da kulawa "shigowata uku ina duba ka baka tashi ba daman tun da naga irin kwanciyar da kayi nasan ka gaji domin bacci kake mai tattare da stress ." numfashi kawai ya sauke batare da yace komai ba "muje kaci abinci kallonta yayi cike da qauna aransa ,yace "sweetheart na sha hollondia milk bana jin yunwa yanzu may be kafin na kwanta yayi mgnr yana zuba mata kwayar idanunshi ."adamcy nah ! ta kira sunansa yaji wani faduwar gaba dan duk sanda ta kirasa haka yasan akwai damuwa.”

"dan allah mar.."no sweetheart karki ce wani abu yanzu we 'll talk later amman right now karki ce min komai akanta dan allah ki barni na huta da mgnrta haka ,kullum magana daya kmr wata zinariya "yayi mgnr cikin fushi murmushi tayi tana dungure masa kai "bazaka bari nayi maka nasiha ba "wani nasiha kuma sweetheart ?nasihar da acikinta muka tashi idan ma nasihar ce ita ya kamata kiyiwa nasiha dan ni dai kinsan bana son qazanta a gidana , ina buqatar kamshi akoina na shiga bana son shirme da hauka agidana “ya qarasa mgnr tare da yi shiru "sai me kuma ?thats all I need bayan wadan nan bana buqatar komai ."

"shi gyara shim....fi...da.." rawar da muryarta ta fara da in ina saboda kallon daya tsareta dashi yasa da kyar ta samu zancen ya kai qarshe tace “me yasa kake kallona haka kmar zaka cinyeni ?”allah adamcy zaka iya kashe mutun da kallon nan naka ,mutun sai mugun kallo “lumshe tsumammun idanunshi yayi tare da riko hannunta daya cikin nashi yace "sorry sweetheart ban fahimci abinda kike nufi bane shi yasa kika ga ina miki kallo haka "ajiyar zuciya ta sauke tace " ina son jikoki daga wajenka shine maaanar gyara shimfida dan karka ce zaka ki hada shimfida daita ".ta qarasa mgnr tana dubansa .”

"Sweetheart iya jikokin da kike dasu sun isheki haka ba sai kin samu qari daga gareni ba” ya fad'a yana zare hannunsa daga cikin nata yana sake kallon fuskarta ganin yana qoqarin mikewa tayi saurin rikosa za tayi magana ya katseta da cewa "ina son haihuwa amman bana bukatar haihuwa daga gareta d'an haka tun wuri sweetheart ki daina tunanin zaki samu jikoki daga gareta dan bazaki samu ba ." murmushin karfin hali mami tayi cikin tsigar rarrashi tace "ka dai bi ahankali karka zo kana rage wa diyata murya fa ."na gwamaci mutuwa akan nayi haka "come on adamcy nah ka daina cika baki karka zo kana min kuka kana sonta fa ."

zare hannunsa yayi tare da barin gurin ya nufi hanyar fita yana cawa “sai na dawo! bayansa tabi da kallo tana jin wani irin zafi na taso mata duk da ac dake aiki a parlour'n komawa tayi ta jingina jikinta zuciyarta na tsalle saboda sarai tunda ya nuna baya só baya só né kuma zai yi wuya ya só ko yayi wani abu da mrym amman tunda akayi wannan auren babu mai kashesa sai allah, duk yadda zatayi sai tayi ya só mrym ,shiru tayi tana tunanin dan bata son takura wa d’anta har karfe goma bai shigo gidan ba mami ta kasa shiga ta kwanta duk ta kasa sukuni saboda bata son yana dadewa awaje haka ma maryam yadda mami bata runtsa ba itama bata kwanta ba tana kusa daita "

Suna zaune suna duba agaogo ya shigo tamkar wani zaki ganinta cikin wani yanayi yasa ya qaraso ya zauna kusa daita kallonsa tayi tana sauke ajiyar zuwa ganin babu wani sauyi atare dashi "sannu da zuwa yaya "mrym ta fada. yayi mata banza tmkr bai ji ba yana cewa "sweetheart ba kiyi bacci ba ?cike da kulawa tace “taya zan iya bacci byn adamcy nah bai shigo ba “ina kaje.?" naje waya unguwa né amman na dawo since muna tare da mb né “ baka ci komai ba har yanzu”? numfashi ya sauke daman yasan sai ta tambayesa "bana jin cin komai sai da safe naci "kana son barin kanka da yunwa mrym maza tashi zubo masa abinci kafin mrym ta mike ya mike ya nufi samansa ."

Mrym tayi dining ta zubo masa abinci ta dawo mami gashi” yi hakuri mrym ki bar abincin nan bari na hada masa coffee nasan zai sha tunani tayi tasan halinsa tunda yace baya ci bazai ci ba zagayeta tayi ta hada masa coffe tayi samansa tana shiga parlour'n ta taraar dashi zaune idanushi a lumshe "adamcy nah "ta kirasa ahankali tare d zama kusa dashi gyara zamansa yayi ya zuba mata ido bai ce komai ba "ga coffe ka sha babu musu ya karba ya soma sha ahankali tana tare dashi har sai daya shiga wanka sannan ta sauko ta shige dakinta tayi alwala tazo tayi shafai da wutiri ta kwanta ."

1:00 na dare maryam ta shigo dakin ata cikin sand’a , a hankali ta kai hannu tana nenan makunnin wutar d’akin tayi saa ta gani ta kunna wutar ta tsaya akanshi tana qare masa kallo yana kwance ya lullube jikinsa , ahankali ta kai hannunta ta yaye bargon da lulluba dashi daga shi white pant " wani abu taji ya tsarga mata tun daga yatsun kafafunta zuwa kanta duk wani zati na jikinsa gashi nan a bayyane tana kallo har kan jijiyarsa tana gani “ina ma zaka iya bani dama dana bayyana maka irin yadda nake ji akanka, ina sonka yaya adam tun kafin mahaifiyarka tayi nasarar had'a aurenmu ,ina da mahimman sako acikin zuciyata.”

ka bani dama isar maka da sakonin zuciyata you are my life ya adam I love you ni kadai nasan yadda nake jin sonka a zuciyata ,I can't live without you duk duniya kai ne abinda nake tsananin so kuma nake shiga tashin hankali idan naga wata zata kusaceka."dan Allah ka soni ko yaya ne "ajiyar zuciya ta sauke tana kare masa kallon tsab " world can't describe how much I love you ,I love with all my heart shiru tayi jikinta na qara mutuwa akanshi daya daga cikin wayoyinsa ne ta dauki qara da sauri ta durkushe kasa ta kankane jikinta wuri daya tana rawa jiki."wayar tayi ringing har ta katse wani Kira ya cigaba da shigowa .”

ya motsa da kyar ya lulobo wayar ya d’aga batare daya bude idanunshi ba "hello !!! yaji shiru dan haka ya mayar ya ajiye wayar a gefensa ya sauke naunayen ajiyar zuciya tare da komawa ya kwanta dan ya gaji sosai ."ahankali mrym ta mike tana leka fuskarsa bacci ya koma dan hk tasa shi gaba da kallo har da tagumi sai murmushi take tana ganin tayi nasara arayuwarta tunda ta mallakesa a matsayin miji sai ta soma kokarin barin dakin wani kiran ya shigo da wani irin mugun sauri ta hantsila byn kujerar sofa tana rawar jiki wannan karon daukar wayoyin yayi ya kashe gbdy ya janyo pillow har guda biyu ya matse a qirjinsa ahankali ta fito ta bar dakin tun kafin asirinta ya toni ta ballowa kanta ruwa dan tasan muddin ya kamata bazai raga mata ba "..

Karfe shida daidai na yammacin ranar asabar maryam tana zaune cikin girmamawa a gaban mami ,sanye cikin wata haddadiwa madam gezner fara sol wadda aka yiwa aiki da yellow zare da stone ,aunty shahida ta yafa mata mayafi fari wanda ya fito da ainihi shape din fuskarta ta sanya takalmi fari sol tsintsiyar hannunta daure yake da farin agogo na fata mai baqar fuska,qamshi jikinta ke fiddawa mai sanya nutsuwa da kwantar da hankali wannan kuma duk aikin ya’yan mami né ."

Gabadayansu ya’yan mami nasiha suke mata mai ratsa jiki,wadda tabi kowacce gaba ta jikinta,suna sake tunasar daita haqqin daya rataya a wuyanta cike da gamsuwa cikin sanyin jiki ta soma yi masu godiya,a daidai sanda uban tafiyar ya shigo,cikin shigar da yafi yi , wato kanana kaya ,baiyi tsammanin zai gansu a nan ba da bazai shigo ba ,amman babu yadda zai yi kiran sweetheart ne gashi gbdy sun gansa sallama yayi dai dai lokacin da mami take cewa"mrym ki goge hawayen,ai bamu rabu ba muna tare duk sanda kike son ganina ki kirani zan zo idan banzo ba zan sa aka wo min ke ."

Wani haushi ya kamashi dan hk ya kau da kanshi gefe yana maida hankalinsa kan wayarsa ya isa gaban mami nesa da mrym ya duqa yana mata sallama sanda ta yunqura zata tashi don basu wuri aunty shahida ta dakatar da ita ta koma inda ta tashi "Adamcy !"bai amsa ba ka zauna kusa da matarka gefen lip's dinsa ya ciza sannan ya zauna sai dai nesa daita aunty khadija ta kamo hannunsu ta tsarke cikin juna "adam ga amanar mrym “ tsaki yaja tare da zare hannunsa cikin nata yana cigaba da danna wayarsa ita kuwa mrym gabanta ne ke wani irin mugun faduwa wanda bata ta’ba jin irinsa ba sai yau ."

"Yau zata kwana gida daya wata kila ma daki d’aya dashi ya allah ka kawo min dauki ka bani kwarin zuciya ka daurani akanshi "adamcy ga amanar mrym nan na damka maka,kada ka cutar da ita don kana ganin baka sonta ,ko ban gaya maka ba kasan aure amana ce ta mace da ake danqawa namijinta wanda duk kuma yaci amana Allah bazai qyaleshi ba,na tabbata diyata mrym bata da matsala,idan naga wata matsala to daga kaine, ka kuma kuka da kanka don wallahi bazan taba daga maka kafa ko baka uziri ba,ki kiyaye".

Ya dago idanunshi da suka gama canza kala ya zubawa mami "sweetheart bazan boye abinda ke raina ba domin idan nace zan rike amanar nan nayi karya dan bazan rike ba ,kice na aureta kuma na aureta amman batun amana kiyi hakuri am sorry bazan iya rike wata amana ba "ni kake fad'awa haka adamcy ?yayi shiru wai har sai yaushe za kasan ka girma ka wuce wad’an nan abubuwan?sweetheart babu wani batun girma anan auren dole fa kika min .”

“da na maka auren dole wa yaja akayi maka ?yayi shiru “allah ya ganar da kai gsky mrym ki qara hakuri kinji kiyi qoqari ke sauki hakin daya rataya a wuyanki allah yayi miki albarka "Insha Allahu mami zan kiyaye,Allah ya qara girma, Ameen summa ameen,Allah yayi muku albarka gbdy ."mami na yin shiru ata ya mike ya fice ,mami ta mikar da mrym tsaye ta rungumeta tana shafa bayanta ta dauko littafin adduoi ta mika mata "duk wani maganin damuwa yana cikin nan karki yi sakaci da addua in sha allahu komai zai zama tarihi wata rana ta mika hannunta ga Aunty shahida suka fito daita suka sakata a bayan mota inda ata ke tsaye tare da salim da hisham ya rungume hannunwansa a qirji .”

salim ya dubesa "ata ga amarya can zaa kai maka yau fa zaka shige daga ciki nima dai bari nazo na lalubo wacce zamu rufawa juna asiri"za dai ka rufa mata asiri ata yayi mgnr tmkr ba daga bakinsa ta fito ba ." “Za dai mu rufawa juna "idan baka da hankali kayi daga yau kasa acikin kwakwaluwarka cewa duk nmj daya auro mace shi ya rufa mata asiri.” salim yayi murmushi yana cewa "haka né amman dai .."kaga abar mgnr haka hisham ya gyara tsayuwarsa kawai yana kallonsa batare da yace komai ba "salim ya numfasa yace "amman dai Ya kamata kaje ka sauya kaya a wuce da kai "zuwa ina kenan ?ba yau zaku tare ba ?dawa kenan ?ban gane ba kai da mrym mana "Uhm ita kadai dai .”

hisham ya kyallesa kawai ya girgiza kai yana sake gyara tsayuwarsa "su biyu ne zaune a bayan mota sai aunty khadija da driver a mazauninshi ya tada motar suna qoqarin barin gidan ." hawaye ya ziraro mata dan wannan lokacin ta kasa daurewa saboda nasihar aunty shahida ta sunkuyar da kanta tana damqe littafin da mami ta bata sannu ahankali har suka qaraso tampatsetsen gidan ata dake surulere driver yayi parking suka firfito har mrym suka sakata a tsakiyarsu cike da nutsuwa take takawa gabanta na faduwa har suka kawo bakin kofa shiga parlour’n suka ce "mrym shiga da kafar dama allah yasa kin shigo kenan mutuwa ce zata raba ."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 5

...Kusan minti biyar maryam na tsaye a bakin kofar shiga babban parlour'n gidan gabanta na wani irin bugawa da karfi, sai da aunty shahida ta sake maimaita magana sannan ta d'aga kafarta ta dama da kyar bata sauketa a koina ba sai acikin had'ad'den parlour'n ." yadda gabad'aya penting jikin gidan yake fari sol haka zalika cikin gidan yake ,gidan ba wani babban gida bane akan sauran gidajensa domin kuwa duplex ne sama da kasa ,sama d'akuna uku ne sai d'aki d'aya wanda aka waresa domin baki , babu abinda babu acikin wannan d'akin, idan baki suka shiga cikinsa bazasu fito domin yin ibada ba dan anyi masa tsari na musamman tare da kujerar kwaya d'aya a d'akin wanda ake kira da (L)."

yayinda kasan gidan babban parlour ne mai d'auke da d'aki d'aya da bayi , sai makeken kitchen da dining area sai kujera three seter manya manya guda biyu da one one seater guda biyu na alfarma ga makeken tv bango 80 inches ,iya had'uwa wannna gidan ya had'u domin kuwa an zuba duk wani kayan qawa na more rayuwar duniya ,kai tsaye sama suka nufa da maryam rike da hannunta har d'akinta suka zaunar daita a bakin gado sannan aunty shahida ta shiga kallon d'akin komai kamfani ta tsarashi da kyau dan bata samu damar zuwa ba lokacin da zaa kawo kayan maryam "

Numfashi aunty shahida ta sauke kana ta soma magana "maryam yau dai allah yayi ikonsa gashi kin tare a gidan mijinki kuma danuwanki kiyi hakuri da duk wani abinda zaki gani marriage is sweet and sometimes is not sweet , so idan kikaga dadi kiyi farinciki ki gara godewa allah ,idan kika ga sa’banin haka Kiyi hakuri wanda daman hakuri kowacce mace ke yi a gidan aurenta ,matakin nasara a gidan aure ba komai bane sai addua juriya da kuma hakuri dan haka ki qara hakuri akan wanda kike dashi ko ba adamcy kika aura ba dole zakiyi hakuri bare kuma kinga irin mijin da allah ya baki mai matukar wuyar shaani ,amman da sannu idan kina masa abinda yake so zai canza miki daga adamcy da kika sani zuwa sanyin idaniyanki kiyi duk abinda mijinki yace abinda yace baya só ki barshi."

Readers Also Read