Kenza eBookz

Mar'adams book 3 - Chapter 20

Mar'adams book 3 - Chapter 20

Mar'adams book 3 Chapter 20: Mar'adams book 3 Chapter 20. Ahankali ya samu waje ya zauna yana sauke numfashi tare da dafe goshinsa yana jan tsaki inda…

3,335 words

Ahankali ya samu waje ya zauna yana sauke numfashi tare da dafe goshinsa yana jan tsaki inda zuciyar maryama ta cika da tsananin mamakinsa wannan shine karo na biyu da yake nuna damuwarsa akan mijinta to me haka yake nufi ?”ta tambayi kanta ganin ta kasa gano dalilinsa kuma kamar matsawa kanta da son gano dalili tamkar bawa kanta wahala ta tarkata komai ta watsar ta mike ta fito ta koma office dinsu .mr ata ya jima zaune ahaka yana saka da warwara ahmed yaronsa na Z&A ya shigo cike da girmamawa ya gaishesa sannan yaja kujerar dake fuskantarsa ya zauna ya ajiye masa file a gabansa "sir ana bukatar saka hannunka anan da anan ya fad'a tare da zaro biro a gaban rigarsa ya mika masa ya karbi biron yayi sign sannan suka fara tautaunawa akan kasuwanci sun d'auki sama da awa d'aya sannan yayi masa sallama ya wuce yana fita James ya shigo ya ajiye masa cup din coffee wanda ya za me masa jiki sannan ya ya juya fice .”

ahankali ya d'auki cup din ya kai bakinsa kamar ance ya kalli office dinsu maryama wani maaikaci mai suna ema ya hango duke a gabanta suna magana fuskarsu d'auke da annashuwa duk da bai san maganar me suke yi ba amman fuskokinsu ya nuna alamar maganar tana masu dadi sosai .”anatse ya ajiye cup din hannunsa ya zagayo hannuwansa duka cikin aljihunsa yana taku zuciyarsa na tsinkewa yana shiga office din bai ce masu uffan ba sai ji ema yayi mr ata ya zagaye wuyansa da hannunsa yayi hanyar waje dashi a gigice yake kallonsa yana biye dashi ,haka ma maryama a gigice tabi bayansu da kallo ahankali ta maida kanta ga aikin da take kafin ya gama dashi ya dawo kanta "kai tsaye office dinsa ya nufa dashi tare da hankad'a keyarsa ."fuskarsa a hade tamkar kumurci macijin dake neman abinci yace " zance me kuke yi ?"yayi masa tambayar yana juya masa baya ".

“kayi hakuri sir muna magana ne akan wannan sabon aikin dakayi mana bayani akanshi d'azu na banjana company shi muke sake tautaunawa akai domin yana bukatar nazari sosai "bayan shi kuma?” ”amm sai kuma dan naga sabuwar zuwa ce ita shine nake son na koya mata wasu abubuwa "mr ata ya juyo a natse fuskashi babu annuri yace "waye yace maka bata iya abubuwa ba ?ema yayi shiru sai dai à matukar firgice yake da irin kallon da mr ata yake jifansa dashi ".wannan da kake gani tafika fikira sannan tafika kwarewa akan komai zai fi kyau ka tsaya iya inda aka ajiyeka aiki ba yawon shiga cikin rayuwar wasu ba "wannan gsky ne sir dan yadda take magana ma kawai ya isa yasa mutun ya manta tarin ayyukan dake gabansa dan tana magana ne cike da shauki "what .?"mr ata ya furta acikin ransa qirjinsa na wani irin luguden bugawa sannan yana aikawa da ema da kallo mai hargitsa tunanin mutun da saka mutun shiga uku ."

Ya tsaita kallonsa sosai ga ema sannan ya cigaba da magana "yadda take magana da kai haka take magana da karnuka da kuma aladu da jakuna dan kasan ba wai matsayinka ne yasa take magana da kai haka ba ,ka tattara ka koma office din qasa kwata kwata "ema ya zaro idanu waje da sauri yana dubansa a marairaice "kana ‘ batawa kanka lokaci maza kaje ka tattara ka koma inda nace "ayi hakuri sir ban san cewar matsayinta ya .."leave my office kafin nasa a dakatar da kai gabad'aya ai da wani mugun sauri ya juya har ya kusan kai bakin kofa ya jiyo sautin mr ata cak yaja ya tsaya da girmamawa “bance ka fad'awa kowa dalili ba muddin kuma naji wani to kasan ka kori kanka da kanka aiki da sauri ya qarasa ficewa ya shiga office na tsakiya wanda ya kasance anan yake aiki ya dauki bakar jakarsa ya saba a kafad'ansa sannan ya d'auki laptop dinsa ya rungume yana kallon sauran abokan aikinsa yusura tace "ema ina zuwa haka "?an maidani office na qasa gabad'aya "what ?"ta mike tsaye hankalinta a matukar tashe alokacin da shi tuni ya fito.”

ta biyosa tana tambayarsa dalili amman bakinciki ya hanashi yi mata bayani haka ta juyo jikinta a sanyaye ta koma office cike da kewarsa dan gskiya ema yasan kan aikinsa gashi da sauki kai ,dan duk lokacin da ya gama aikinsa zai kar’bi nasu yayi.." Yau Kamar abun had'in baki kusan hankalin mazan dake aiki tare da maryama duk yayi kanta bini bini zasuje inda take ita kuma cike da sakin fuska take sauransu suyi abinda zasu yi su koma mazauninsa wanda hakan keta faman baqanta ran mr ata hatta masu shiga da fite dan duk wanda ya shigo sai dai idan bai daura kwayar idanunshi akanta ba amman sai hankalinsa ya tsayu akanta wannan alamari fa ya daga hankalin mr ata matuqa sosai yasanya ido akanta ".Mr ata na zaune tare da wasu abokon business dinsa mutun uku alhj deeni ,alhj farooq alhj bb ya tsinkayo muryar maryama tana neman izinin shigowa.”

muryarsa a tsarke ya bata izini a natse ta shigo tunda ta shigo wad’an nan mutun nan suka tattara hankalinsu gareta,cike da girmamawa ta gaisheku Sannan ahankali ta qaraso gaban mr ata ta ajiye masa file din da zanen datai ." ya tsurawa zanen ido na second goma kafin ahankali ya motsa labbansa yace "you can go back to your work ."har tayi taku biyu yace "ke.."ta juya a natse idanunshi na kanta kamar yadda idanun bakinsa ke kallonta kamar zai cinyeta wanda hakan ya haddasa mata jin wani mummunar faduwar gaba "shiru yayi kafin yace d'auki cup din can ki samu some ta nuna miki yadda ake had'a min coffe "okay sir “. ta furta cikin sanyayyar muryarta yayinda jikinta ke rawa rawa ya d’auke kanshi ya maida kan bakinsa daya lura sunata kallonta amman sai ya share .”

Ta qarasa inda cup din yake ta dauka ta soma tafiya kamar wace aka hankada aiko qafafunta suka hard'e tayo kansu mr ata bai san sanda ya mike tsaye ya shiga tsakaninsu ba ta fad'a saman faffad'an qirjinsa tayi masauki atare suka dinga sauke ajiyar zuciya "ki dinga bi ahankali kada ki jima kanki ciwo kija ma kanki asara.” ya furta cikin wani salo da sautin murya mai sanyi yayinda hucin bakinsa dana numfashinsa na dukan wuyanta da fuskarta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa yrrrrr". "Kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta dinga furtawa ahankali ahankali sakamakon yanayin data tsinci kanta .”ya riko tafin hannunta ya zaunar daita akan kujera qirjinta na bugawa fat fat kamar zata fasa qirjinta tayo waje . ta had’e yatsun hannunta waje daya tana murzawa shi kuma ya janyo wata kujera ya ajiye adaidai saitin bayanta ya zauna yana kallon inda su alhj deeni ,alhj farooq ,alhj suke zaune sun zubawa ma iyalinsa idanunsu kowa da abinda yake sakawa a ransa,a hankali mr ata ya lumshe idanunsa tare da sanya hannunsa a saitin kirjinsa yana murza dai-dai indai zucyarsa take beating vry fast,su kuwa cigaba da kallonsa suke suna kallon sarautar Allah "dan babu tan tama mai kamfanin AGC ya kamu da mummunar qaunar yarinyar nan qauna kuma mai girma qauna ce da ma basu ta'ba ganin irinsa ba ".

tsumammun danunsa ya ware sosai akansu yana cewa "mintuna goma kacal sun isa ku tattara duk wasu kalamanku masu mahimanci." sarai sun fahimci inda ya dosa dan haka suka taikaita maganarsu kamar yadda ya bugata suka kama gabansa tun kafin yace ya fasa halqallar kasuwanci dasu ."bayan tafiyar bakinsa ya mike tsam ya janyo kujera zuwa gabanta ya zauna tare da ware qafafunsa ,sunyi mugun yin daf da juna ta dan ja kujerar baya kad’an amman hakan bazai hana idan ya sauke numfashinsa taji ba. ganin yadda idanunshi ke yawo ajikinta yasa tayi saurin sunkuyar da kanta qasa natse alokacin daya soma magana a tsanake amamn idan mutun ya natsu sosai zai fahimci cikin tsananin fushi yake "anya kuwa kwakwaluwarki tana da cikakkiyar lafiya kuwa ?" ta d'ago kanta a gigice tana kallonsa "yes !dole na tambayeki dan kin wani tsareni da idanu "ya qarasa maganar yana lumshe mata ido .”

“Ko me ya gani atattare daita yasa zai had’a da wannan mummunar ciwo ?” tabi jikinta da kallo na second goma sannan ta d’ago ta zuba masa idanunta “me yasa zaki fad'a kan mutane ?" Muryarta na rawa tace “wallahi ban sani bane ni ma haka kawai naji jikina ya kama rawa.” taso ta fad'a masa idanunsu ne yayi mata yawa amman sai ta tsinci kanta da kasa fad'ar haka dan batasan me hakan zai haifar ba tunda ta rigada tasan halinsa abu kad’an ke hassalashi "idanun maza yayi miki yawa kina gani bai kamata kiyi aure anan kusa ki huta ba "?tayi shiru tana cigaba da kallonsa yayinda qararrawar zuciyarta na kad'awa da sauri sauri sakamakon kusancin da suka samu na haifar mata da shiga cikin wani yanayi "ya dai kamata kiyi tunani ko sanin cewar ke matar aure ce zai saukaka miki wasu abubuwan ."numafshi ta janyo ta sauke da kyar tana sake sunkuyar da kanta gabdaya ta sake neman natsuwarta ta rasa rawar da jikinta keyi ta qaru ".

“Maryama ki tsaida miji kiyi aure zai fiye miki kina aure kina aikinki , dan bai dace ki dinga kula kowani kare alade da jaki ba "idan dai kema din ba irin hallitarsu gareki ba ."ya qarasa mgnr yana jan tsaki tabi shi da wani irin kallo zuciyarta na tsinkewa idan ta fahimcesa da kyau" idan halittartata ba irin ta jaki kare da alade bace ta daina kula kowa kallonsa take fuskarta da bayananen mamaki “to shi da yake kulata take kulasa fa ?”kenan shima ya kasance d’aya daga cikin abinda ya lissafa kare da alade da jaki ne ?”tayi maganar a can kasan makoshinta ta yadda ko shi da yake zaune a gabanta bazai iya fahimtar komai .ya juya ya d'auki kwalin sigari ya bud’e ya zari d’aya ya kai bakinsa ya kai hannu ya dauki abun kunnawa tana ganin haka ta zabura ta mike ranta a matukar bace ta nufi kofar fita tana jan tsaki da kallo yabi bayanta yana ta'be fuska "abinda zaki qarasa tsawon rayuwarki daita itace abar gudu ai gara ki fara sabawa daita sannna ya lumshe idanunshi lokacin guda kuma ya budesu yana cewa "ke dawo ki zauna ."!

Maryama taki tsayawa bare ta dawo kamar yadda ya bukata "idan kika kuskura kika bar office din nan ki tabbatarwa kanki kin tafi kenan har abada bazaki sake da aiki a AGC ba ".cak taja qafafuwanta ta tsaya tana sauke wani wahalallen numfashi daga inda yake zaune yana kallon yadda kafad’unta suke d’agawa sama alamun tana kokuwa da numfashinta Ahankali ta juyo tare da sunkuyar da kanta kasa dan bazata iya cigaba da kallonsa a yanayin da yake ba saboda yayi mugun tsareta da ido yana kallonta tana takowa ahankali har sanda ta qaraso ta tsaya "set "! ya fad'a yana kunna sigarinsa muryarta sanyaye tace "sir kayi hakuri ka kashe wannan abar bana son warinta "daga yau ki koyi son warinta set !ya sake maimaitawa" inna ilaihi ita kam ta shiga ukunta da wannan mutumin ta sake yin kasa da muryarta sosai kmr zatayi kuka "sir kada kamin haka dan Allah "me nayi miki ?"ya tambayeta yana dage mata girarsa d’aya “sigari ce fa kawai ?meye illarta?" set and don't let me repeat my seif again ".

babu yadda maryama ta iya da rayuwarta haka tayi shiru ta toshe hancinta da hannunta d'aya dayan hannun kuma taja kujerar baya kad'an domin rage kusancinsu ta zauna sai dai duk a rud'e take . tunda ta zauna bata d'ago kanta ba yayinda shi kuma kwayar idanunshi ke kanta yana zugar sigari yana zance zuci "ta d'ara duk matan duniya a idanunsa ita kadai zuciyarsa take so ,kuma bazai ta'ba son wata bayanta ba ,sai dai duk runtsi bazai d'auki raini daga gareta ba farar takadar ya janyo ya ajiye mata sannan ya janyo wata roba da kayan zane yake ciki shima ya ajiye mata "ki zanani ahaka . "what ?" ! ta furta à matukar razane tare da d'ago fuskarta ta tsura masa yana rike da sigari yana zuga muryarta a raunane tace "sir kayi hakuri bazan iya zanaka kana shan sigari ba ka canza min da wani aikin na yarda "okay ! zana min mata da miji rungume da junansu suna kissing din juna a bakin kofa "oh my goodness god ya rabbi ka taimakeni akan wannan mutunin ta furta a can qasan makoshinta sannna ta sake tsura masa idanunta gbdy ta rasa natsuwarta ji take kamar zuciyarta zata buga haka ne ma yasa ta cigaba da kallonsa ko dai a buge yake ne ?sai dai tsaf yake abunsa idan ma baa a gabanka yake shan sigari ba bazaka ta'ba cewar shi din dan sigari bane dan babu abinda ya nuna ko ya sauya ajikinsa "Kina 'batawa kanki lokaci domin kuwa babu inda zaki har sai kinyi abinda nake bukata."

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 19

Zuciyar maryama cunkushe da haushi had’e da takaicin mr ata ta zari pencil din zane ta soma aikin daya sakata wanda tai masa laqabi da aikin mugunta tana zane bakincikinsa na sake ninkuwa a kasan ranta, yayinda zuciyarta ke wani irin zafi da suya . ina ma zata iya murje idanunta tare da cire d’an burbushin tsoronsa dake ranta ai wallahi data zage kunjinta ta zabga masa rashin mutunci fiyye da wanda ya iya .amman ina bazata iya ba ,bazata iya karawa da mr ata ba ,dan ko a yanzu ya gano wani abu daga cikin rauninta domin kuwa ya fahimci aikinta yana da matukar mahimanci arayuwarta. cikin kankanin lokaci ta zana namiji sanye da kaya wondo da riga tare da jacket sannan ta zana mace tana rungume da namiji sanye da dogon riga kanta lullu’be da mayafi,ta gama amman tsabar ‘bacin ran sigarin da yaketa faman bankawa cikinsa yana busa mata hayaki ya hanata d’agowa ta kallesa bare ta sheida masa ta gama.”shi kuwa mr ata zuba mata ido yayi ganin yadda ta gama amman tana jin wani abu aranta yasa ya sake ware qafafuwansa ya kunna wani sigari a ransa yayi murmushi ,shi ko kwana zasuyi a hk daidai ne.”

“ ganin muddin bata yi managa ba zasu kwana a haka ba damuwarsa bane dan ta tabbrwa kanta miskilancisa da jin kansa bazai barshi yayi magana ba , dan haka cike da tsinkewar zuciya da kyarma jiki ta d’ago fuskarta inda yake karaf idanunsu ya tsarke cikin juna ,ganin haka yasa maryama sake had’e ranta tamau dan bata son ya kawo mata wani sabon rainin hankali ko rainin wayo tare da d’aga masa farar takardar hannunta tana nuna masa alamun ta gama .” kina son ki zamo matsalata?” yayi mata tambayar yana tsareta da tsumammun idanunshi ahankali ta girgiza masa kai tana cewa “bazan ta’ba son na zamo matsalar kowa ba ,abinda kasani kenan sir , kuma wannan shine iya abinda zan iya yi . shiru yayi kawai yana ajiye qarshen bakin sigari acikin wani dan qaramin kwanon tangaran .”sannan ya cigaba da dubanta tare da cewa “tsarin yanayi rungumar bai min ba kasancewar babu remotic .“ ta kalleshi da tarin mamaki akan fuskarta lip’s dinta take matsawa alamun magana take son tayi masa sai dai ta kasa furta komai dan zuwa yanzu gaba d’aya a firgice take dashi .”

Yanayin zamansa ,yanayin kallonsa ,yanayin maganarsa duk sun canza dan hatta kwayar idanunshi sun canza kala yayinda shirunta ya bashi damar kallonta son ranshi dan ko son kifta ido ba yayi ,ga wani kalar murmushi da yake wanda shi karon kanshi bai san yana yi ba sosai itama ta shagala da kallonsa amman ita kallo ne dake tattare da tashin hankali da tsoro ,ahankali ya matso kusa daita ya hura mata iskar bakinsa da sauri tayi kasa da kanta tana jin wata irin fargaba yayinda gabad’aya ilahirin jikinta rawa yake .zuciyarta ta cika fal da matsanancin tsoronsa ,jigun sukayi daga shi har ita barin maryama wacce komai ya tsaya mata cak ,yadda bai sake yin mgn ba itama bata ko motsa ba daga inda take zaune sai dai kowannen su da abinda zuciyarsa ke saqawa acikin zuciyarsa .” zurfa goshinta ta share tana kallon mr ata tace “sir ko zan iya wucewa “?numfashi ya sauke da kyar yana soka yatsan hannunsa a gefen bakinsa.”

“ kamar yace mata “a’a sai kuma yayi mata alama da hannunsa dan ya tabbatar muddin yace zai yi taurin kai zata maimata masa abinda tasaba ,dan yana ji kuma yana gani zata wuce abunta ta barshi zaune ” ahankali ta mike ta biyo ta raba gefensa zata wuce har jikinta na zozon jikinsa saurin d’auke numfashi yayi yana jin kamar ta jona masa wutar lantarki ne ta juya a natse ta soma daga qafafuwanta da kyar gyara zama yayi tare da ware qafafuwansa yana bin every step of her tafiyarta kad’ai aka bar mutun dashi wani abu ne mai tsayawa arai bare akai ga samunta gabad’aya .”ahankali ya dinga bin kugunta da wani mayataccen kallo cikin salon magana yace “wannnan kugun zai sha wuya a hannuna domin kuwa bazan ta’ba saurara masa ba haka zalika wannna bakin rashin kunyar zai sha kissing har sai yayi kukan neman sausauci.”sai bayan la’asar maryama ta soma shirin tafiya gida taso kwarai ta sake yi masa magana akan sabon aikinsu amman sai taga gara kawai ta rabu dashi idan ranar ta kusa zata sake nemansa da maganar wata killa zuwa lokacin ya amince suyi .” wucewa tayi abunta tana tunani hali irin na mr ata “tsarin yanayi rungumar bai min ba kasancewar babu remotic girgiza kai tayi tana murmushi.”

******

Da daddadre da misalin karfe takwai yana zaune atsakiyar gadonsa hannusa rike da remut ya canza channel zuwa breaking news yana kallo sai dai hankalinsa baya wajen kallon labarai yana gurin tunanin yadda zai mallaki maryama ne cikin sauki har sanda mami ta shigo hannunta rike da cup din coffee'nsa bai sani ba ta tsaya shiru tana kallonsa tana nazarinsa kafin ahankali ta kira sunansa "adamcy "! yayi firgigib ya dawo haiyacinsa yana kallonta "kar’bi !" ta mika masa cup tana cewa "wai meye matsalarka madadin naga lapto agabanka kana Kan aiki amamn kayi busy kallo kana tunani ". "na gaji ne sweetheart !"ba maganar ka gaji bane what's wrong with you?" ta tmbyesa tana kallonsa " me kake tunani yanzu koda yaushe cikin tunani kake , meye matslarka"? babu !"ya fad'a atakaice yana kai cup bakinsa "akwai gskyar ko damuwar da zaka iya boye min duk yadda mami tayi dashi yaki fad'a mata damuwarsa abinda bai saba mata ba Kenan ya ajiye cup din hannunsa ya koma Kan kujera ya zauna ya dafe goshinsa."

ta dawo kusa dashi ta zauna" abinda kake min wani lokaci yana damuna "ya d’ago ya kalleta kawai kuma zai iya kashe ne tun kwanakina basu kai ba .”ta fad'a tana dubansa shi fa duk saboda wannna yarinyar maryam ne yasa baya jin zai iya fad'a mata damuwarsa domin dai ya fad'a yaga mafarkinsa a yanzu zai iya janyo masa damuwa bugu da qari shi karon kansa bai san takamaiman makomarsa ba ta yaya zai fito da damuwarsa yana cikin zance zuci ya cigaba da jin maganarta "idan ka kamu da soyayyar yarinyar nan dake aiki a qarqashinka fine let me know?" ya sake d'agowa ya kalleta atsanake amman still bai ce mata komai ba dan ba maganar kamuwa bane magana ce tsananin qauna kuma jin zai iya hakura daita duk runtsi duk wuya sai ya mallaketa kuma acikin wannan lokaci zai organizing wasu mutane dabam su nema masa aurenta ."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull