Kenza eBookz

Mar'adams book 3 - Chapter 26

Mar'adams book 3 - Chapter 26

Mar'adams book 3 Chapter 26: Mar'adams book 3 Chapter 26. daidai kugunta mr ata ya rike yayinda ita kuma hannuwanta duka suka sauka akan kafad'ansa saurin…

3,271 words

daidai kugunta mr ata ya rike yayinda ita kuma hannuwanta duka suka sauka akan kafad'ansa saurin d'auke numfashi tayi cike da tashin hankali ta tsura masa shayayyun idanunta tana kallon cikin kwayar idanunsa, azababen kamshin turarensa ne mai sanyin dadi da bugar da zuciyar duk wanda ya shaka ya ziyarci hancinta, nan take zuciyarta da kwakwaluwarta suka soma amsar wani babban sako na musam man ,ajiyar zuciya kawai maryama ta dinga saukewa da sauri da sauri yayinda kwayar idanunta ke cikin nashi cike da matsanancin tsoro."shi din ma kallonta yake sai dai shi hankalinsa a kwance yake kallonta babu wata alamar tsoro ko firgice a tattare dashi, a inda tsoro da matsanancin firgicin ya bayyana akan fuskar maryama ,zuciyarta kuwa banda bugawa da karfi babu abinda take a sakamakon yanayin data tsinci kanta ciki mai wuyar misaltuwa, dan zuwa yanzu numfashinta ya soma barazanar d'aukewa sakamakon kamshin turarensa dake kai kawo a hancinta ."sun d'auki kusan minti goma suna tsaye suna kallon juna cike da jin wani yanayi na dabam a gabad'aya sansar jikinsu mai kama da shocking wanda shi daman ba sabon abu bane agurinsa itace dai ya zamewa sabon al'amari dan ba sai an fad'a maka ba ,kana kallonta kasan sabuwar shiga ce shiyasa azahiri yake iya hango tashin hankalinta ."

"Nana hauwa'u da mami ne tsaye suna kallon abun mamaki fitowarsu kenan daga parlour'n mami nã biyu domin kallon presentation wanda ita mami din da biyu ta fito tana son ganin sabuwar maaikaciyar adamcy'nta a natse ta cigaba da kallon adamcy'nta cikin wani irin yanayi wanda kwata kwata bata ta'ba ganinsa ciki ba sai yau ,sosai ta tsura masu matsakai tan idanunta ,yadda mami da nana hauwa'u ke kallonsu haka sauran ma'aikatan dake tsaye a parlour'n ke kallonsu cike da fargaba da tashin hankalin abinda zai biyo baya ,da'akace a office ne bazasu damu ba saboda norma normal suna ganin hakan na faruwa a tsakaninsu. yawon kallonsa gareta amman irin haka ma basu ta'ba gani ba wannna shine karo na farko da suka gani kuma ko haka zai faru sai a gidansu qarin tashin hankalinsu ma ganin yadda mami da nana ke kallonsu a firgice". ahankali nana hauwa'u ta gyara tsayuwarta tana sake dafe bayan ashraf dake rungume a kafad'anta ta waiga inda mami ke tsaye jikinta na d'an kirma tace "mami ko kinga abinda na gani kuwa ?"ta tambayeta tana sake maida kwayar idanunta kansu mr ata qirjinta na bugawa ."

mami ma kallon diyarta tayi tace "auta na gani "wacece wannan yarinyar?"meye matsayinta a wajen yaya ?"nayi imani duk duniya babu macen da yaya zai yiwa haka cike da kulawa mami lallai akwai wani abu a kasa". numfasawa mami tayi tana sake maida kallonta garesu adaidai lokacin da suka had'a ido da maryama dake fuskarta na kallon kofar shigowa ne shi kuma fuskarsa na kallon step ne ". da sauri maryama ta dawo haiyacinta tare da cire hannuwanta duka ajikinsa ta tsya tana wasa da yatsunta ."duk da batasan ko su waye tsaye ba amman zuciyarta ta gigita da ganinsu."sanyayyen numfashi ya sauke muryarsa a kasalance yace be careful I wil not always be there for you".ya fad'a yana lumshe mata lumtsatsun idanunshi ."shiru ne ya biyo baya kafin ahan kali ta gyad'a masa kai alamun taji sannan ta sake juyawa ta cigaba da tafiya cike da sanye jiki ,shi kuma ya juyo da niyyar ya dawo wajen client dinsa kawai yaga mami tsaye a bayansa tana kallonsa ."

Ahankali mami ta soma tahowa zuwa inda yake tsaye suna kallon juna inda sauran ma’aikatan suka bi bayan maryama zuwa sauya kayan jikinsu muryar mami a raunane ta soma magana "halan wannna yarinyar itace maryama ?"yayi shiru yana dubanta batare da yace komai ba dan bai san me zai fad'a mata ba ".adamcy ban ta'ba ganinka cikin irin wannan yanayi ba sau yau ,yayi taku d’aya yana gyara tsayuwarsa tare da tura hannuwansa duka cikin aljihun suit dinsa yana cewa “itace amman abinda ke tunani ba haka bane yana gama fad’ar haka ya soma taku cikin isa da kasaita don barin wajen kafin ta sake wata tambayar sai dai cikin sanyi murya mami ta kira sunanshi “adamcy …” ya tsaya cak tare da juyowa suna fuskarta juna da maminsa idanunta ta zuba mishi kawai tana kallonsa tare nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sake sauyawa cikin d’an kankanin lokaci .

Suna tsaye mami bata bata kai ga sake magana ba su maryama suka sauko d’aya bayan d’aya suna gama saukowa kawai sai shigowarsu baba qarami suka gani mr ATA bai lura da shigowarsu ba madam some ce ta hankaltar dashi ya juyo a hankali yana dubansu tare da sultan ."a natse client din ya qarasa ya samu baba qarami "barka da dare mr Edris!” ya mika masa hannu fuskar baba qarami a hade ya mika masa hannu "yanzu nake maganarka araina gsky naji dadin yadda akayi representation din yau.” gaban baba qarami yayi mummunar faduwar “inda cliet dinsu ya cigaba da magana “ shiyasa ma zanyi order kaya masu yawa a hannun mr ATA gsky wannan yaron naka yasan Kan kasuwanci "baba ni ..."baba qarami yayi saurin daga ma sultan hannu inda client ya cigaba da magana "gsky wannan yaron shine hasken kamfaninku duk ranar da'aka babu shi gsky kamfaninku zai samu matsala .”

Nan take zuciyayoyinsu ya dinga bugawa "he has figueira and effort , bealiant “. ya sake fad'a yana kallon mr ATA daya fuskanci baba qarami fuskarsa a had’e tamkar wani zaki kafin ahankali ya motsa lip’s dinsa "banason mutune na shigowa inda nake batare da neman izinina ba ,baba qarami ya sake kallonsa cikin matsanancin ‘bacin rai zuciyarsa kamar ta buga tsabar bakinciki “mr lawyer's I will like to show you my design “inji cewar sultan mr lawyers ya girgiza masa kai yana cewa "no time for now til next time saboda yanzu gbdy mun gama zabar wanda yayi mana a gurin dan’uwanka dan haka mu yanzu ma zamu wuce ya fad’a yana kallon mr ATA “dan allah ka tabbatar zuwa sabon wata komai yayi ready ,bazan samu damar zuwa ba kawai ka tura a sauke min kaya "an gama” na gode sosai mr ATA ya fad'a yana mika masa hannu sukai sallama sannan ya juyo yana kallon yammata d’aya bayan d’aya tare da cewa su biyosa a lokacin maryam na amsa kiran umma ".

Muryarta can kasan makoshinta take magana dan idan ba kusa kayi daita sosai ba bazakaji muryarta ba ta ra’ba ta gefen mami inda mami ta d’auketa da wani kallo tun daga samanta har qasa tare da yi mata kallon sani bata kai ga qare mata kallo ba maryama ta wuceta tana cewa “umma kinga yadda aikinmu ya samu kar’buwa wallahi nayi mamaki ban d’auka new design dinmu zai samu nasara haka ba kinga yadda mai order kayan ya dinga murna yana jin dadi "na godewa allah da sanyi idaniyana ta samu nasara a aikinta kinsa ina kallon fuskarki d’auke da murmushi, Kiyi maza ki dawo gida da wuri kinga banana banason kina dadewa a waje “in sha allahu amman umma dan allah ki dawo gida gobe mana dan gidan baya min dadi idan bakya nan .”“karki damu bari da zarar na gama abinda nake zan dawo ina miki fatan alkhairi da samun nasara arayuwarki, farincikinki shine farincikina maryama allah ya dangwamar dake cikin farinciki “Ameen umma na gode ina jin dadin yadda kike bani kulawa sannan kike supporting dina akan komai nawa shiyasa matsayinki ya zarta na kowa acikin zuciyata ,"ni dai ki kasance cikin farinciki sannan ki rike mutuncin kanki da aikinki da kyau domin ki samu nasarar da tafi wannan "in sha Allahu umma amman kinsa wannan nasara har da mr ATA aciki domin shima ya bada gudunmuwa sosai “ kingani ba shiyasa nake yawon cewa ki kwantar da hankalinki Kiyi hakuri da halinsa da sannu zaku saba ki fara jin dadin aiki dashi “see you umma sai kin dawo “take care of yourself my maryama ."

Shiru mr ata yayi yana kallonta har sanda tai sallama da umma ganin yadda take cikin farinciki shima sai ya tsinci kanshi cikin farinciki ya dinga kallonta yana jin kamar kar ya bari ta wuce gida ,a yanzu tunanin wannan uguwar tasu yake, runtse idanunshi yayi yana mai tsananin tausaya mata, ko yace ya bata kyautar mato a yanzu ba lallai ta amsa ba amman zai had’asu gabad’aya yayi masu kyautar mota bisa qoqarinsu yasan bazata fahimci komai ba dan bazai juri ganinta cikin tirmitsitsin mutane a motar haya ba .idan ka bata mota a ina zata ajiyeta ?”kwakwa luwarsa tai masa tambayar ya kai hannu ya shafa goshinsa zuwa karan hancinsa “abinda yafi kawai ka hanzarta aureta shine mafuta agareka gabadayansu mr ata yasa aka d’aukesu acikin hadaddun motocin sa tare da bada umarnin a sauke kowaccce a gidansu, sannna ahankali ya dawo zuwa parlour’n mami .”

Inda zuwa wannan lokacin parlour’n ya cika da mutane tsaye mami , yaya Ibrahim ,aunty abida uncle jay da dai sauran yan’uwansa yana gama shigowa uncle jay ya hausa da fad’a "me yasa kayi abinda kayi adamcy ?kafin uncle jay ya cigaba da magana baba qarami yayi tsigil yace “me ka d’auki kanka? ka fad'a min ina jinka ,mr ata yayi shiru kawai yana kallonsa “ka bani amsa ina sauraranka ka bani amsa”. baba qarami ya sake mgn a matukar fusace uncle jay ya matso kusa dashi ya dafa shi yana cewa “yaya kayi hakuri abinda zai faru ya rigada ya faru amman bai kyauta ba .”muryar baba qarami ta cigaba da fitowa a zafafe “kowa yasan wannan zalinci ne dan bama kasuwancinmu haka kuma bazan ta'ba yarda da hakan ba Adam ya had’u da client privet bayan nayi masa gargadi mai qarfi har uwarsa tana bani kwarin gwiwa bazai yi ba kawai sai naga ya aikata kenan duk abinda zanyi nayi ?kuma nasan yayi haka ne da had’in bakin uwarsa .”

Mr ata zai yi magana mami tai masa gargadi da idanunta tana qarasowa zuwa inda yake dan haka ya furzar da hucin numfashi yana kamo lip’s dinsa na kasa parlour'n ya dauki shiru har mr ATA bai ce komai ba sakamakon qafarsa da mami ta take tana masa gargadin kada ya furta komai "dan allah kayi hakuri tabbas yayi kuskure kuma ina tabbatar maka bazai sake ba ka ga dare yayi yanzu kaje ka kwanta gobe sai ayi magana "bazan ji wani hakuri ba ko naje na kwanta har zuwa wani gobe yanzu nake bukatar amsa daga bakinsa”. mr ATA ya kallesa idanunshi cike da’ bacin rai "baba ai Adam bazai iya cewa komai akan tambayar daka masa saboda shi kansa ba ra’ayin kansa bane wannan fa duk ba plan dinsa ba plan din wata maryama ce ."da sauri mr ATA ya maida idanunshi kan aunty abida yana mata wani mugun kallo mai razanarwa .”

"Maryam !? “Wacece maryama” menene had’inta da kamfanin mu?wannan shegiyar yarinyar data fita yanzu tana waya tana wulwulaga idanuwa kamar mayya itace maryama kuma itace yarinyar da yake wulakata yar uwarsa sultana akanta "wannan ai wulakanci ne akwai dokoki akan kamfanin dan me yasa wata staff can zata canza mana tsarinmu ?”to na rantse da Allah kayi na farko kayi na karshe da zaka sake had’uwa da client private karka manta wannan ba kamfanunka bane kai kadai kamar yadda kasani hadin gwiwa ne ,bazai yiwu ka dinga yin mana abinda kaga dama ba, idan iko da takama kake son yi ka tattara ka koma compines dinka kaje can kayi abinda kaga dama, amman anan baka isa kayi abinda kaga dama ba “.

“wallahi baba duk ya canza tsarin komai shi da yar iskar yarinyar nan "bazan duba wata dangantaka ba idan kika sake kiranta da yar iska sai na wulakantaki ya fad’a yana nuna aunty abida da yatsan hannunsa sannan ya kalli yaya Ibrahim “warn your wife kana ya sauke zazzafan numfashi ya cigaba da magana “wannan ba plan din maryama bane tsarina ne ni ne naga dama yi kuma nayi abinda raina yake so ya fad'a tare da juya masu baya” wannan new desings din yanzu aka fara kuma zaa cigaba da gabatar dashi a duk lokacin dana so kuma babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa ko acikin kamfanin ko kuma a wajen kamfani "amman kasan wannan cin amana ne , ya kake son muyi damu kasuwanci ?abinda baka son a fad'a ne kuma sai an fad'a wannan maryama itace ta tsara komai kuma wallahi bazamu ta'ba d’aukar hakan ba cewar baba qarami zan tabbatar dana dauki mataki akan wannan tsarin naka idan ba haka ba komai zai iya faruwa .”

“Enough please!” kada wanda ya sake sako sunna maryama cikin matsalar nan dan bata da hannu ciki mami ta sauke numfashi kawai tana dubansa wato har laifinta baya so lallai akwai wata a qasan zuciyarsa ? "babu ruwanta amman me yasa kake side din yarinyar ?cewar baba qarami sabod nasan bata da hannu ciki idan zakuga laifin kowa kuga laifina domin nine na shirya komai kuma nine na kawosu gidan nan sannaan akan kamfani naji komai zaku ce amman anemi a wulakanta maryama wannnan ne kuma bazan dauka ba”gabad’ayansu idanun suka zuma masa sultan yafi kowa shiga tashin hankali domin qarara yake hangon soyayyarta atattare dashi "babu ruwan maryama aciki wannnan plan din ni nan na tsara komai ku fita harkar ta kar wanda yayi qoqarin shiga rayuwarta “yana gama fadar hk ta wuce ya barsu Adam !!! Har sau uku baba qarami ya kirasa amman bai tsaya ba ya haye samansa da sauri .”

Mmn Sudais Mmn sudais💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 24

"Saurin 'bata fuska maryama tayi "dan me zai dinga dangatata da kalmar hauka alhalin ita ba mahauka ciya ba ?"kuma ta lura daga lokacin daya ganta da sultan ne ya sake shigo da wani sabon salon wula kanci ,mr ata yayi bala'in tsareta da ido duk da suna cikin duhu ne amman idanunshi suna iya karantar halin da take ciki sakamakon maganar da yayi mata a yanzu ,cike da tsananin tsoro tace"please sir ka daina dangantani da kalmar haukan nan ina jin kamar na munzanta dayawa " bai ce daita uhm ba bare uhm uhm kawai sai ji tayi ya riko tsintsiyar hannunta da qarfin ya soma tafiya daita, nan take ta turje amman yaki sakar mata hannu dole tasa tace "ka sakar min hannu nayi tafiya da kaina ."yana jinta yayi mata banza tamkar ba dashi take magana ba ." "acikin unguwarmu muke idan wani ya ganmu haka wata fassara daban za'a mana "ta fad'a tana 'dora hanunta a saman shi a qoqarinta nason zare hannunta, shareta yayi batare da yace mata kala ba sai ma sake damke tsintsiyar hannunta yayi ya cigaba da tafiya "shi ina ruwansa da wasu , ita din tashi ce kuma kome zaa ce akanta zuciyarsa bazata d'auka ba ."

"jin yaki sakar mata hannu yasa jikinta ya fara rawa dan tasan tunda ta bari ya tunzura sai abinda yaga dama zai yi." alhankali muryarta ta fito "please sir kayi hakuri wallahi bazan sake jayayya da kai ba ka sakar min hannu"dogon tsaki yaja yace "wannan kuma problem dinki ne ".bai tsaya daita akoina ba sai daf da bakin get din gidansu sai dai yaki sakar mata hannu ,inda zuciyarta ta shiga tashin hankali mai tsanani da jin tsoron abinda zai biyo baya, dan bazata so wani acikin 'yan unguwa ya fito ya gansu haka, bare wani daga cikin 'yan gidan su. shi kuwa tsura mata ido yayi acikin duhun yana kallonta yana jin kamar ya janyota jikinsa ya rungume tsam tsam!! maryama bata gama tunaninta ba sai ga fitowar husna diyar aunty hassana daga cikin gida tana waya tana waige waige da alamun wani ta fito nema jin sautin muryarta yasa maryama ta d'an juyo cike da tsoro ,ganin husna yasa wani bakinciki ya tokare mata kahon zuciya wanda yasa hawaye zuba daga idanunta ,da sauri ta dawo da kallonta garesa muryarta can kasa cike da shagwa'ba tace "ka gani ko ."

Shima muryarsa a kasalance yace "me nã gani ? "cousing dina ce ta fito yanzu "so what ina ruwana da fitowarta ?ko gani tayi ina miki wani abu ? "ba zaka gane abinda nake jin tsoro ba, abinda zai je yazo nake gudu ".tayi maganar muryarta cike da matsanancin tsoro "ki ganar dani zan gane "ya fad'a cike da kulawa yana sake motsata so take taja baya saboda bata són kusancinta dashi amman tana gudun husna ta gane itace tsaye a wajen "menene damuwarki a gidan ?yayi maganar cikin wani irin salo "da sauri ta girgiza masa kai tana cewa "no karka damu kawai sakar min hannuna na wuce "ke matsalarki kenan kinsan bana son taurin kai da jayayya bare kafiya amman a dole sai kinyi min "ya qarasa maganar yana hura mata hucin bakinsa a fuskarta da wuyanta sakamakon kusancin da suka samu saurin lumshe idanunta tayi zuciyarta na wani irin tsinkewa ."yayinda husna tayi shiru tana duban inda suke tsaye sun yi mugun yin kusa da juna wanda bai fi taku d'aya zasu qara jikinsu ya had'e ba . "a fili tace "wacece wannan kamar maryama ?"

"aiko jin haka yasa hankalin maryama yayi matukar tashi tun da take arayuwarta baa ta'ba ganin tasamu kusanci irin haka da wani d'a namiji ba ."ganin husna na qoqarin tahowa inda suke tayi saurin jan hijab dinta ta rufe rabin fuskarta iya bakinta da rabin hancinta ne kawai a waje tun kafin ta qaraso ta ganta taje ta bazawa aunty hasana ita kuma tasamu abun zaginta dashi ."husna na gama qarasowa kusa dasu ta tsaya tana cewa "maryama !" ko ba maryama bace ?" maryama na jinta amman tayi mata banza a zuwan ba ita bace ,shi kam mr ata kallon d'aya yayi mata ya d'auke kanshi ya cigaba da kallon princess dinsa ." ganin da husna tayi ba'a kulata ba gashi wanda take waya dashi yana sheida mata inda zata zo ta samesa yasa ta juya tana taku tana cigaba da wayarta sai dai zuciyarta cike take da wasi wasi akan maryama ce ko kuma wata ce daban tsaye a kofar gidansu amman wani bangaren na zuciyarta yafi amince mata da maryama ce."

sai sanda mr ata yaga dama sannan ya sakar ma maryama hannu tana jinta free ta juya ta nufi cikin gidansu da sauri batare data waiwayo ba ,tana shiga bangaren umma ta nufa tana haki bata iske umma ba da alamun tana ciki tana sallah ta zauna akan kujera ta kifa kanta akan hannun kujera kawai sai hawaye ya soma gangaro mata kukan da bataso tayi akan shi shine ya kufuce mata ba dan taso ba dan hakan ne kawai zai iya sanyaya zuciyarta akan wulakancin da yake mata "yana son ya maida mata jiki banza, babu wani shamaki kawai daya so zai riketa, ita kam sam bazata d'auki wannan wulakanci ba gara tun wuri ta takawa abun burki bazata sake yarda ya dinga ta'bata anyhow ba ,jikinta mai daraja ne ,jiki ne data d'auki tsawon shekaru tana killace abunta bazai yuwu lokaci d'aya yazo ya dinga wasa dashi son ransa ba ,ya hanata saka hijab da nikaf ta yarda amman jikinta kam tana da rowarsa bana ta'bawa bane nã aure ne, tana kuka tana zancen zuci sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru ta shige d'akinta tun kafin umma ta fito ."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull