Mar'adams book 3 - Chapter 27
Mar'adams book 3 Chapter 27: Mar'adams book 3 Chapter 27. Tsaye mr ata yayi a wajen gidansu maryama tamkar wanda aka dasa tsabar mamakin kansa da yake duk…
3,285 words
Tsaye mr ata yayi a wajen gidansu maryama tamkar wanda aka dasa tsabar mamakin kansa da yake duk yadda yake son ya boye tarin soyayyarta da qaunarta acikin zuciyarsa abun ya cutura har yau gashi tsananin kishinta da son kare lafiyarta da mutuncinta ya kawo shi kofar gidansu a karo na biyu har sai daya ga shigarta cikin gidansu sannan ya samu natsuwa da kwanciyar ahankali ,yana tsananin qaunarta ita kuma tana tsnanin qaunar waninsa . " "wasu hawaye masu zafi da ciwo ne sukayi nasarar biyo fuskarsa a lokacin daya tuna tun sanda ya fara ganinta a mafarkinsa wanda shine asalin lokacin daya fara jin zazzafar soyayyarta acikin zuciyarsa haka rayuwar take cike da tarin abin mamaki da fari ya d'auka komai da sauki ake samusa ashe abun ba haka yake ba ,abun ba kamar yadda ya taso bane da duk abinda yace yana so ya zama dole ayi masa, idan kuma babu dole sai an nemoshi a duk inda yake an bashi."
Ahankali mr ata ya d'auke kwayar idanunshi akan kwara'babben get din gidan su maryama ,ya juya cike da sanyin jiki, ya soma tafiya zuciyarsa na sake nitso cikin tafkin shaukin qauna da tunani da kyar yake iya d'aga qafafuwansa tamkar wanda bashi da laka haka yake ji a sansar jikinsa inda zuciyarsa ke wani irin bugawa da karfin gaske "wai shine yau acikin irin wannan kwarababbiyar unguwar a karo na biyu ?" a tun tasowarsa idan aka fad'a masa cewar a irin wannan unguwar zuciyarsa zata mace zai karyata wata killa ma sai anyi mugun rigima dashi." sannan duk tsawon shekaru da yayi yana nemanta bai d'auka daga irin wannan family zata fito ba ,ya d'auka daga gidan mulki ko gidan wani shararren attijira ko d'an siyasa da duniya tasan da zamansa sai gashi zuciyarsa ta tsallake tarin mata bilaadadin masu tarin arziki mulki tattare da boko soyayya tayi wuji wuji dashi ta wullosa cikin wani ahli da ba kowa bane ,bama kowa ne ya sansu ba a iyakar agage ma yayi imani ba kowa ne yasan da zamansu ba ."
a natse ya cigaba da taku yana cigaba da zance zuci still yana jin dinga hawayensa akan kuncinsa shi ba gudun ahlinta yake ko kyamar ahlinta yake ba a'a tsantsar mamaki ne kawai cunkushe a zuciyarsa da tarin iliminsa da tarin dukiyarsa da tarin nasabarsa da tarin nuna isarsa amman Allah ya nuna masa shi din ba kowa bane face bawansa kuma wanda yake qarqashin ikonsa ,ya nuna masa wannan itace irin kalar qaddarar da zai d'aura masa kuma bai isa ya canzata ko ya gudarwa qaddarar dake biye dashi ba ko akan maryam ya kamata ace ya fahimta duk yadda ya kai ga kin yarinyar yadda ya dinga gudun aurenta babu irin qiyayyar da bai nunawa yarinyar ba amman a qarshe sai da allah ya nuna masa shi din bakowa bane ya aura masa ita ya kuma zauna daita a qarshe ga ciki "ya rabbi " ya furta a fili alokacin daya tsoma qafarsa d'aya cikin ca'balbali ai bai tsaya dubawa ba dan yasan zuciyarsa bazata d'auki kallon inda ya sanya qafarsa ba gara ya cigaba da tafiya zai fiyye masa alkhairi da kwanciyar hankali ."
" ya d'auki tsawon shekara shatakwas yana tsnanin sonta shi kad'ai yasan irin wahalar da zuciyarsa ta sha akanta ,babu dare babu rana kullum muradinsa da rokonsa ya ga ko mai kama daita ne a zahiri sai gashi allah ya amsa rokonsa ya had'asu a gaske ai duk yadda maryama take ya amsa koda kuwa zata kasance bata da kowa ,bata da komai bata da galihu kai koda kuwa acikin tsatson bayi ta fito zai 'yantata da ko nawa akace ya maidaita mallakina take wani bangarensa na zuciyarsa yace "tabbas adam kai din masoyi ne tunda kana sonta a duk yadda take "wallahi ina matukar son maryama ya bawa zuciyarsa amsa da haka .bayan mahaifiyata itace abinda nafi só a kaf duniya yana tafiya yana ciza lip's dinsa yana ganin hanya da kyar kasancewar unguwr nada mugun dubu. naunayen ajiyar zuciya ya sauke yayinda soyayyar maryama ke cigaba da kutime meniya da zuciyarsa da gangar jikinsa qaunar maryama ya dinga bin dukkanin sansar jikinsa ji yake kamar ya zarta duk mazan duniya saa da allah ya kwatota a hannun wani ya dawo masa da farinciki rayuwarsa."
" hakika Allah yana son shi domin daya had'u daita da aurenta da lallai zaayi gagarumin tashin hankali dan ko ta kashe auren ta dawo garesa ko kuma ta kasance mai maza biyu amman bazai ta'ba yarda ya barwa wani ita ba ,amamn dake Allah yana son shi da rahma kuma had'uwarsu tana cikin qaddararsa sai ya kashe masa tsohon mijinta saboda shi ya sameta ."Allah kenan yadda yaso haka zai yi inda yayi parking din motarsa ya qaraso da kyar yana kakkabe qafarsa data fad'a cikin cabalbali ". Mr ata ya iske tarin samarin unguwar dake zaman banza a bakin titi kamar safiya haka yaga wajen kasancewar zuwa wannan lokacin an kunna street light suna ganinsa duk suka matso suna sara masa a hakan ma basu san ko waye shi ba kawai dai kyawun motar daya zo daita ne yasa sukai masa kyakkyawan zato, bud'e motar yayi ya shiga ya zauna sai daya saka seat belt sannna ya d'auko bandir din yan dubu d'aya d'aya guda uku yayi warning glass din motar kad'an ya miko masu yace su raba . nan take ihunsu ya karad'e unguwa wad'an da ya bawa kudin suka shiga bashi hanya suna korar mutane a guje ya figi motar ya hau babban titi yana tunani"yana son dauke maryama daga wannan unguwar amman yana tunanin soyayyarsa ."
"Zai so ya fito mata da zahirinsa amamn kuma jin tsoron tace bata son shi "kai kuwa adam akwai macen da zatace bata sonka ?" Wani bangaren ba zuciyarta ya tambayesa .zata iya cewa bata sona mana tunda zuciyarta da hankalinta yana kan matacce tunda gashi tna mata maganar aure amamn ita ba wannan maganar bane arainta “akwai tarin abubuwa dayawa agabana wanda aure ne zai zamo last .”kwakwaluwarsa ta tariyo masa maganrta tsaki yaja yana sake ganin aurenta a boye shine kawai mafuta agaresa idan yaso ahankali zai koyar daita yadda zata shi fiyye da wancan mataccen ."qarfe shadaya na dare da mintuna ashirin ya tako cikin babban parlour'n mami wanda babu motsin komai da kowa acikinsa sai nã makeken tv bango da ac nan dake aiki ,kai tsaye samansa ya nufa yana furzar da hucin iska daga bakinsa yana shiga ya fad'a bedroom dinsa ya fad'a kan makeken gadonsa yana sauke wani wahalallen numfashi."
Yana kwance mami ta shigo har cikin bedroom dinsa ta tsaya akanshi tana qare masa kallo tsab dottin data gani tun daga step har parlour'n kenan a takalminsa ya kwaso ?” to ina yaje ma har ya kai by this time ?shi da matukar yana gari duk tsanani takwas a gida take masa "adamcy !"mami ta kira sunansa ahankali ata ya juyo yana kallonta kafin ya dauke tsumammun idanushin daga cikin idanun maminsa ya yunkura ya tashi ya zauan yana dafe goshinsa da hannunsa daya kusan minti goma mami ta dauka tana kallonsa batare da tayi yunkurin cewa komai ba sai dai yanayinsa take karanta yanayinsa yau tamkar wani mara lafiya tana kallonsa ya gyara zamansa tare da numfasawa ya zare takalmin qafarsa da duk dottin unguwar maryama ne yayi shiru kawai yana kallonsu gabansa na fad’uwa .” tsawon lokaci mami ta dauka tana dubansa yayinda cikin zafin rai ya kamo lips dinsa na kasa ya soma cizawa da karfi sakamakon hawayen da yaji yana kokarin son zubo masa." wani irin nauyin zuciyarsa tayi "yana ji yadda qirjinsa ke masa zafi da ciwo tamkar an daura masa dutse mai shege nauyi a sama kirjinsa yanayinsa yasa hankalin mami yayi matukar tashi duk abinda kaga ya maida adamcy haka baqaramin abu bane ."
guri mami tasamu nan kusa dashi ta zauna tare da kamo tafin hannushi cikin nata tana mai cigaba da nazarin yanayin daya yake ciki ,ka natsu ka kwantar min da hankalinka adamcy ka daina sakawa zuciyarka damuwa too much idan ba haka ba zaka Sakani a tashin hankali. fad'a min wani abu ya faru ne a AGC ?tayi masa tambayr cike da kulawa irin ta uwa hannusa ya kai goshinsa yana sauke numfashi "zuwa Ibrahim uku bai sameka ba ko akwai wata matsala ne data taso ?dago tsumammun idanushi yayi yana kallon mami dasu "ni a wajena babu wata matsala sai dai ko daga garesa "to allah yasa shima haka .ka kai dare a waje a ina ka tsaya haka”?shiru yayi gabansa na cigaba da luguden bugu “ko kuma nace ina kaje daka kwaso dotti mai muni haka .” Takalmansa yabi da kallo yana mai runtse idanunshi “duk takalminka ya 'bata step da parlour'n ka ?shiru yayi kawai yana soso gefen kanshi "ko wajen wannan sabuwar maaikaciyar kaje ?sake kallonta yayi a d’an rikice "adamcy kana son yarinyar nan? "take yaji wani abu ya tsigar masa a gabad’aya ilahirin jikinsa yana yawo cikin ’ bargo da tsoka tsayawa yayi yana kallonta ya kasa kwakwarar motse ballanantana yace mata wani abu .”
ahankali 'mani ta numfasa sannan ta cigaba magana “wannan shine karo ba biyu dana tambayeka , irin wannan soyayyar zaka boyewa sweetheart dinka "?zan so naga yarinyar nan naga abinda tafi maryam dina dashi, nasani baza tafi maryam dina da komai ba, maryam dina yar asali ce yar dangi ce ,yar gata ce, kuma mai galihu ce ace mutun yana da dangina kamata ai abun ayi alfahari dashi ne “shiru yayi yana duban mami yana nazarin inda maganrta ta dosa "kenan dai hasashensa ya tabbata idan ya kawo maryama matsayin matar da zai aura ahlinsa bazasu amince ba, idan kuma sun amince zabasu sota ba zasu kyamaceta ?yayi wa kanshi tamabayr "ina son naganta adamcy da kyar ata ya samu ya had'iye abinda yaji ya tsaya matsa a makoshinsa sannan 'ahankali ya iya motsa lip's dinsa tare da kiran sunan mami " sweetheart ki bar maganr nan zamuyi later mami ta katse shi ta hanyar daga masa hannuta, nasan halinka adamcy bazaa qara maganar ba "ki kwantar da hankalinki yarinyar zata zo a gidan nan zaayi presentations kinga dole zaki ganta amamn fa babu komai a tsakanina daita bayan shaani na aiki ."ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa."
"yanzu kai haka zaka qare rayuwarka ?we will talk about it later “yana gama fadar haka ya shige bathroom."shiru mami tayi tare da bin kofar daya rufo da ido ."tarasa gane abinda ke damun tunanin d'anta shine zurfin ciki shine miskilanci shine jin kai shine rashin son magan shine rashin kunya ya rabbi ka taimakeni ni idan son yarinyar ma yake ya kawo min ita amatsayin wacce zai aura zan fi samun natsuwa dan gara yayi aure da zaman da yake haka tana bukatar ganin ya'yansa masu tarin yawa gashi ance maryam mace zata haifa tana son duk abinda ke cikinta amamn taso ace d'a namiji zata haifa masa domin kuwa haihuwar da namiji yana bawa uwa kariya daga duk abinda zai taso gaba na tashin hankali ,domin ita karon kanta misali ce tayi imani da babu adamcy acikin rayuwar ita da ya'yanta mata da tana ji kuma tana gani zata kaskanta acikin dangin ubansa amman tun yana yaro yake takawa duk wanda ya nemi ya kawo mata rainin hankali burki ."
Bangaren maryama har qarfe d'aya na dare idanuta sun kasa runtsawa ta yunkura ta tashi ta zauna sosai a tsakiyar katifarta ta janyo pillow ta rungume tsam a qirjinta tana going over maganganun mr ata tana son ta gano wata gaskiya da yake qoqarin boye mata ,wani bangaren na zuciyarta sai taji tana so ta yarda a cikin yanayinsa akwai alamun soyayya amma kuma acikin maganganunsa kwata kwata babu wata alama ,acikin kwayar idanunshi ma zaa iya tabbatar da akwai wani abu acikin zuciyarsa .”shiru tana tana tariyo irin kallon da yake mata domin son gano wani abu .”girgiza kai tayi tace “wad'an mugayen idanuwan nashi babu komai acikinsu sai tarin firgici "Idan kin san baki tashi aure ba a yanzu kar na qara ganin kin kula sultan magana ma ta fatar baki kar ya qara shiga tsakaninku dashi maganarsa kusan ta qarshe kenan to me yake nufi da hakan shi bai ce yana sonta ba sannan kuma zai ce karta kula wanda ya nuna yana sonta ."
Kwakwalwa maryama ta bude sosai duk abinda mr ata ya fada sun samu kyakkwan mazauni acikin zuciyarta ta rufe shayayyun idanunta ta jingina bayanta da jikin gado ta sake rungume pillown dake makale a qirjinta tana jujjuya maganganunsa tana kuma yin filla filla da su tana so ta fito da komai daga rami daya shige ya fake a ciki, ta sake tariyo hirarsu da sultan a kanta ta kuma hada da maganar sa, ta so ta fahimci abubuwa da dama a kansa amma wani abu guda daya yafi komai girma, he is smart duk abinda yake yana yinsa da gogewa idan ba mugun karantarshi kayi ba bazaka ta'ba gane inda ya dosa ba , maganar sultan kuma wannan ba wani abun damuwa bane a wajenta saboda a yanzu ba soyayya bace a gabanta kamar yadda ta sheidawa mr ata bare tayi tunanin aure a nan kusa , abu daya yake tsaye a cikin zuciyarta wanda yasa kwakwalwata ya kasa samun kwanciya shine yaya sadam dinta da take jin har yau cewar yana raye ."
Washegari maryama bata samu zuwa office da wuri ba sai wajajen karfe goma da wasu mintuna dan tuni duk wani maaikacin dake aiki a qarshin AGC yana cikin kuma yana kan aiki jiki a sanyaye ta shigo office dinsu bakinta d'auke da sallama ta gaishesu ta cire jakarta sannan ta samu waje ta zauna tare da yin shiru tana kallon sauran abokan aikinta da suka dukufa suna kan aiki madam some ta shigo tace "sai yanzu maryama ?me yasa baki d'aukar aikinki da mahimanci ai shikenan daman idan kana jin mugunta bakayi wa kanka ba ai baka cika mugu ba. "maryama ta kalleta a kaikaice sannan tace "madam please me haka yake nufi ?"ina nufin duk ranar da sir ya gaji da halinki ya dakatar dake kinga ai kanki kika cuta ,"maryama ta numfasa sannan tace "duk abinda Allah ya hukunto akaina daidai ne "ai shi kenan kuma daman muslim’s din nan haka kuke da taurin kai ,ga aikinki gobe zaa kar'ba idan kuma kingama shi a yau mrs ata zai ji dadi maryama tasa hannu ta kar'ba tana cewa me zaa zana? ahankali madam some ta soma mata bayani tana gama mata bayani ta fita ."
Maryama ta mike ta dauki jakarta ta fice daga office din ta koma qasa office din da'aka maida ema. yayi matukar mamakin ganinta amman dake bai san zuciyar mr ata bace kawai ya sakar mata murmushi yana murnar ganinta wunin ranar tana tare da ema inda mr ata bai sanyata acikin kwayar idanunshi ba amman dai ance masa tazo kuma har an bata aiki sai dai bai nemeta ba duk da kwayar idanunshi ita suke son gani amman ya danne saboda kar ya bada kofar da wasu zasu fahimci halin da yake ciki ." karfe shida daidai maryama ta hawo sama ta ajiye aikinta a gaban madam some dake zaune tayi mata sallama tace zata wuce gida tana gama fadar hk ta juya bayanta ya hango daga inda take zaune tana rausaya kmr ba daga wacan jagwal gwalaliyar unguwar take fitowa ba komai mata tsab tsab kuma a natse . ya hard'e qafafuwansa waje d'aya yana cigaba da kallon yadda take juya sansar jikinta anya kuwa bazata koma saka asalin kamilalliyar suturarta ba ? dan irin wannan tafiyar ai sai wani yayi masa ganganci ,haka ma the next day a kasa tayi aikinta tare da ema duk yadda mr ata yaso ya ganta taki yarda su had'u aranta tace "aiki take masa ba jikinta ta kawo masa ya dinga ta'bawa ba yana yin yadda yaga dama ita ba ."
Tsawon kwanaki biyu kenan bai sanyata acikin idanunshi ba sai dai ya hangeta daga nesa ta shigo ko ta sauka hankalinta ma gabad'aya baya Kanshi tsabgar gabanta kawai take, yana zaune akan kujera sanye da riga da wondo blue sai yar cikinta light blue yayinda nick tied dinsa ya kasance brown colou hannunsa rike da wani nicktie din brown yana nadewa ahankali har ya gama ya soka cikin aljihun gaban rigarsa yana kallonta ta shigo office din some . gata ga office dinsa amman ko d'aga ido tayi ta kalli office dinsa batayi ba haka yana kallonta ta juya yaga ta nufi qasa wani zazzafan numfashi ya sauke sannan ya yunkura ya mike ya fito ya biyo bayanta tana zaune tare da ema da wasu ma'aikatan takalmansa ya shigo office din ,kamshin sanyayyen turarensa daya ziyarci hancinta da kuma bugun da zuciyata yayi ne ya tabbatar mata da shine ya shigo "good morning sir "!!! duk ma'aikatan dake cikin office din sai daya gaishesa illa ita qoqarin juyowa take ta gaishesa taji sautin muryarsa a zafafe "ke me kike yi anan ? cikin tsananin firgita, da tsinkewar zuciya da tsoro, tare da kyarman jiki, ta qarasa juyowa ta fuskanci inda yake tsaye sanye da suit yayi matukar kyau kamar wani matashi dan shekara talatin” just one second na baki ki tattara ki koma inda aka ajiyeki. tamkar gilmawar walkiya yaga ta zabura ta mike ta rungume jakarta da kayan aikinta gam-gam cikin tsuma da karkarwa ta bace .
wani irin masifeffen dariya ne ya taso masa tun daga kasan zuciyarshi har zuwa kan lips dinshi amman dole ya taune lip din shi na kasa kana ya gimtse ya murtuke fuska cikin tsare gida yace.ema "! yes sir ya fad’a cike da girmamawa “da alamun kagaji da aiki damu ko ?"no sir wallahi babu ruwana sir bance .." “enough! ya d’aga masa hannu “to be your last warning. iya abinda ya fad’a kenan ya juya ya koma office dinsa sai lokacin hankalinsa ya dawo gangar jikinsa duk lalacewa ko wani abu bazai had'asu ba gara tana sama yana kallon duk abinda take ."ranar kusan tare ma sukai aiki akan presentation dinsu dake motsawa ,yadda bata sakar masa fuska ba haka shima wanda daman shi kusan fuskarsa a daure take .”aiko ta gane bata da wayo dan ya lafta mata aiki kamar me dan haka a matukar gajiya ta qarasa gida tayi wanka tayi magriba da isha’i saboda tsananin gajiya ma bata ci abinci ba ta kwanta.”
******
Yau ne ya kama zaa gabatar da presentation zaune mr ata yake tare da client dinsa mutun uku a gidan mami tun daga sama yasa akayi decoration har zuwa kasa surayya ce ta fara fitowa sanye cikin riga da siket na suit tayi juyi kamar yadda yan fashions desings keyi sannan ta koma gefe ta tsaya sannan yusura ma ta fito tayi Kmr yadda surayya tayi mutun na uku some ce sai wasu maikata guda biyu sai maryama wacce ta sauko cikin doguwar riga ta rike gefen rigar kad'an tana rausaya tamkr wata fure wani murmushin ne mai daukar hankali kwance akan fuskarta wanda ya bayyana wushiriyarta da dimples dinta ,tayi matukar kyau sosai mr ata ya gyara zama yana kallonta tun daga samanta har qaraso saukowa kwayar idanunshi na kanta .” Mutane da suka zo ganin new design dinsu suaki tafi yayinda mutun daya acikinsu yace "wooo gsky naji dadin ganin representation dinku yayi min kyau sosai thank you so much mr ATA "wannan desings din ya bambamta da sauran desing daka saba kazo da wani salo dabam daman kuma ina da yakinin AGC company ne kawai zatayi min abinda zai kwanta min arai akan kowani kamfani dan haka akan wannan suprisse din zanyi double din order kaya."