Kenza eBookz

Mar'adams book 3 - Chapter 3

Mar'adams book 3 - Chapter 3

Mar'adams book 3 Chapter 3: Mar'adams book 3 Chapter 3. Ya janye farar takardar yana girgiza mata kanshi tare da lumshe mata idanuwanshi na second biyu…

3,218 words

Ya janye farar takardar yana girgiza mata kanshi tare da lumshe mata idanuwanshi na second biyu sannan ya bud'esu fés akanta "ki zauna ga guri nan sannan ga kayan aiki nan duk anan kiyi abinda nasakaki ta tsaya cike da matsanancin tsoro da firgici tana dubansa tare da mamakinsa "wannan mutumin fa katon mugun d'an duniya ne wato dai sai yaga karshenta ?ta fad'a haka acikin ranta ." Ganin ta kasa kwakkwaran motsi tana tsaye tamkar an dasata yasa zuciyarsa ta soma tafarfasa a matukar tsawace yace "zauna mana Kiyi aikinki ai nasan zaki iya tunda kina da tabbacin zanenki ne cike da tsoro tace "yes sir !ya girgiza kai ya zagayo gurin sectry dinsa ya cigaba da yi mata bayanin abubuwan da yake buakta tayi masa yayinda har lokacin sultana na tsaye cikin tsananin tsoro da tashin hankali "wani irin mugun kallo ya d'auketa dashi yana zabga mata harara,da mugun sauri ta samu waje ta zauna akan d'aya daga cikin kujerun dake fuskartasa ta d'auki pencil ta rike tana tunanin ta ina zata fara ?nan da nan ta qara shiga tashin hankali mai tsanani fiyye da wanda take ciki ahankali zufa ya shiga tsatsafo mata a fuska da sansar jikinta kallo d'aya zaka mata ka fahimce a matukar tsorace take ."na shiga uku nah na dibo ruwan dafa kaina “ta ina zan fara ?tayiwa kanta tamabyar hantar cikinta na wani irin kad’awa .”

Sectary dinsa ta d'auko file green ta mika masa ya kar'ba yana cewa sultana "are you done ? batare daya kalli inda take ba" muryarta da jikinta rawa suke gurin cewa "no sir ! ya gyad'a kai "yau zaki gane baki da wayo muddin bakiyi abinda nace ba ya fad’a a kasan ranshi ,wayarsa tayi ringing some ta d'auka da sauri ta mika masa ya amsa yana manna wayar a kunnensa yana cigaba da duba file din hannunsa at the same time yana magana a waya ."Sosai ya fahimci yanayin tashin hankalin da sultana ta shiga ya sauke numfashi ya ajiye wayar ya maida hankalinsa gurin sectary dinsa suka cigaba da tautaunawa har tsawon mintuna talatin sultana na zaune cikin tsananin tashin hankali batare da tayi abinda ya sata ba ."

ya sake yunkurawa ya mike tsaye rike da zanen maryama a hannunsa ya zagayo ya isa inda take zaune jin hucinsa numfashinsa daya sauka a gefen wuyanta yasa ta waigo a gigice jikinta na wani irin kyarma "ai daman nasan bake kikayi zanen nan ba , sam sam wannna ba zanenki bane ko har yanzu kina kan kece kikayi ?ya tambayeta yana ja da baya yayi taku biyu ya tsaya yana jira yaji karyar da zata sake girba masa ya samu damar cin ubanta son ransa." cike da tsoro da in ina tace" eh gaskiya ba nice nayi ba amman kayi hakuri."tayi mgnr duk a rud'e jikinta na rawa tamakr an jona mata wutar lantarki."ai daman ko baki fad'a ba nasani wannan bazai ta'ba zama zanenki ba ya fad'a yana mai sake tsurawa zanen maryama tsumammun idanunshi kafin ahankali ya soma tafiya yana cigaba da kallon zanen yana lumshe idanuwanshi har ya qaraso ya tsaya bayan sultuna nan take ta sake shiga firgici "”mai yasa kika min karya ?tayi shiru ta kasa bashi amsa gabad’aya ilahirin jikinta na sake d’aukar rawa “why did you lie to me ?yayi maganar a tsawace dan girman Allah kayi hakuri “enough !a ina kika samu wannan zanen ko kuma waye ya zana miki shi ?” “No sir babu wanda ya zana min.”

“Where did you get this desing?” uhmm ammm daman sabuwar staff din da'aka dakatar d'azu mai suna maryama hussein ce ta zana ta barshi akan table a office dinmu."nan take gabansa ya cigaba bugawar da yake fiyye da kaida yana kallon zanen yana jin wani irin shauki a gabad'aya sansar jikinsa da jijiyoyin jikinsa wanda bai ta'ba jin irinsa akan kowace halitta ba sai akanta lumshe tsumammun idanunshi yayi sannan ya motsa lip's dinsa ahankali "daman mutane dakikai irinki ya zasu iya zane kamar haka ? Ke..! ya kirata da haka muryarsa a kausashe ta natsu sosai agabansa ya d'an rage girman idanunshi "ki daina shiga lamarina " ki tsaya amatsayin da kike dashi a wurina wanda ni ban ma d'aukesa da mahimmaci ba kin fahimci abinda nake nufi da hakan ? tai saurin gyad'a masa kai ya d'auke akanta "kenan zumunci dake tsakaninmu "ta sake gyad'a masa kai jikinta na sake d'aukar rawa dan yanayinsa gabdaya ya gama tsoratata" gud oya leave my office .."ai da mugun sauri ta juya ta nufi kofar fita ."

Komawa yayi ya zauna akan kujera qirjinsa na wani irin bugawa da karfin gaske a natse ya dinga kallon zanen ya kasa hakura da kallon zanen wani irin sonta ne Ke taso masa yana sake bin jinin jikinsa "soyayyata qaunata farinciki rayuwata kece komai nawa ya fad'a a fili tare da mikewa ya koma Kan doguwar kujera tare da zanen a hannunsa ya zauna ganin zanen yake tamkar itace a tafin hannunsa kwakkywan fuskarta yake ganin acikin kwayar idanunshi tana masa yawo can Jim kad'an ya mike tsaye yana lumshe idanuwanshi, abun mamaki ji yayi daidai saitin inda zuciyarsa ke makale a qirjinsa yana bugawa da karfi, ya kai hannunsa daidai saitin gurin yana runtse idanunshi "Tabbas yasan lallai idan bai yi wani abu akan lamarinsa da yarinyar nan ba yana daf da kamuwa da mummunar ciwon zuciya ,"amman me zai yi tunda yarinyar nan matar wani ce ?Ahankali ya dinga daga qafafunsa yana tunanin nemawa kansa mafuta "Adam !zuciyarsa ta kira sunansa da karfi "kayi qoqari ka mallaki yarinyar nan ta kowani hali kasa karfinka ka kwaceta kamar yadda ammar ya fad'a maka "kanshi ya girgiza yana cewa ai matar aure ce ,tô shikenan ka dawo daita kusa da kai ganinta kusa da kai zai d'an samar da natsuwa arayuwarka "na koreta da kaina kuma na sake dawo daita da kaina ?ya tambayi kansa "Kai ba zan iya wannan kasadar ba sosai yayi zurfi cikin tunani ya koma mazauninsa yay rewarning d'aukar safe yana kallon tun daga shigowarta har zuwa fitarsu har inda ta mari salim ya tsaya daidai inda suka tsaya acikin office dinsa yana kallo har sanda ta fito zuwa koridoor ta juyo tana kallon office dinsa fuskata kwance da ruwan hawaye ."naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi lokacin daya kawo inda salim ya sake shan wani marin a hannunta "wani sanyayyen murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa ya kai hannu yana shafa sajen fuskarsa yana cigaba da murmushi " daman nasan dole zakiyi rigima princess."

Cike da sanyin jiki ya janyo wayarsa ya kira mataimakiyarsa ringin daya ta d'auko "kizo! ya fad'a ataikaice yana hura hanci ya d'auke idanunshi akan kallon da yake qaramin tv sakamakon knowking din da akai ,umarnin shigowa ya bayar yana sake daukar zanen maryama sectary dinsa ta shigo ta qaraso ta tsaya cike da girmamawa "sir gani ! " wannan zanen maryama né ba ? "Nata ne sir lokacin da kace naje na sallameta na isketa tana zana wannan zanen ina ganin saboda tashin hankali data tsinci kanta ciki yasa ta manta dashi amamn tabbas nata né "lallai wannan yarinyar tana da baiwa tana da kwarewa akan irin ra'ayina amman kuma zuciyata ta koreta "sir ko zamu kirata ne ?ya wani d'ago da sauri ya kalleta a d'age "wai sir saboda cigaban kasuwancinka domin zata baka duk abinda kake so kuma zama daita riba biyu ne garemu ga iya zane ga sanin Kan kasuwanci ."

Shiru kawai yayi yaki kulata duk da abinda ta fada din abinda zuciyarsa da gangar jikinsa suke bukata né amman ya rasa dalilin daya kasa bata umarni." ta kusan mintuna talatin tsaye a gabansa bai ce mata uhm ba bare umm umm ganin qafafuwanta sun fara sagewa yasa ta bud'e baki cike da tsaro tace "sir ko zan iya wucewa ."?da hannu ya bata dama . wunin ranar cikin tsananin tunani yayisa duk inda ya motsa yana jinta ajikinsa da zuciyarsa ganinta yau ya qara wutar soyayyarta a cikin zuciyarsa .”kiran d’aya daga cikin yaransa yayi yace akawo masa sigari dan a halin damuwar da yake ciki ita kawai yake bukatar sha cikin kankani lokaci akayi knowking tare da neman izini ya bada izinin shigowa James ya ajiye masa a saman makeken table dinsa sannan ya juya da sauri ya fice .”yadda ATA yake cikin tsananin damuwar abinda yasa akayi ma maryama haka itama maryama ta kasance cikin damuwar maseefar dake bibiyar rayuwata kuka ta yini shiyasa kafin shida na yamman ranar jikinta yayi zafi tamkar garwashin wuta .

umma ce tsaye akanta tana shafe jikinta da jikakken towel byn ta bata magani tasha ta zauna kusa daita ta riko tafin hannunta cike da tausayawa , bata son rasata kamar yadda ta rasa sadam dinta saboda qaunar da take mata yasa idan ta ganta cikin tashin hankali itama take shiga cikin damuwa .”“ta rasa gane meke sa abubuwa suke juya mata baya haka ?dame zataji ?da kiyayyar mutanen gidansu ko kuwa da wannan jarabawan dake bibiyar rayuwarta ? ahankali maryama ta bude kwayar idanunta ta tsurawa umma “sannu kinji maryama allah ya baki lafiya”Ameen “ karki damu komai mai wucewa ne kuma duk abinda Ke faruwa dake da sanin allah,ki qara rike addua duk wanda yace allah to allah zai isar masa in sha allahu bazaki sake fita zuwa koina da sunan neman aiki ko wani abu makamancinsa ba sai dai ya biyoki har gida da azinin allah “Allah ya nuna min wannan lokacin.”tayi maganar muryarta na rawa” sannu kinji maryama zakiyi farinciki arayuwarki “shi kuma mr ata yaje can ya qarata ya rike aikinsa ai da can ba da aikishi kika rayu ba muna nan aiki zai biyoki” naunayen numfashi da ajiyar zuciya maryama ta sauke tana mai runtsa idanunta dan idan akwai abinda ta tsana a halin yanzu shine mai kamfanin creation .”

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 3

Kira ne ya shigo wayar umma dan haka ahankali ta mike tsaye ta qarasa inda wayarta take ajiye akan qaramin table din dake d’auke da hoton sadam wanda hakan yasa maryama sake bajewa akan katifa tare da sakin wani marayan kuka mai ban tausayi tana toshe bakinta da hannuwanta dan kar umma ta jiyo sautin kukanta “hakika Mr ata bai kyauta mata ba ,bai mata adalci ba meye laifinta data cancanci wulakanci ?idanuwanta ne suka shiga hasko mata kyakkyawar fuskarsa da kwayar idanunshi wanda ita acikin idanunta muninsa take gani da masa kallon mugu azzalumi mara imani da tausayi ,kuka take sosai zuciyarta na mata zafi da quna tana mai sake toshe bakinta dan bata son umma tajiyo sautin kukanta amman ina abinda batasani ba tunin sheshekar kukanta ya kaiwa kunne umma ziyara. Allah Allah take taji wake kiranta dan hankalinta kacokan ya koma ga maryama dan haka sai faman kiran “hello !take amman bata jin sautin komai sai na saukar numfashin mutun “hello !”wai wake magana ne ?tayi maganr a hassale cike da jin haushin wanda ya kirata sannan yayi mata shiru still dai shiru ne ya biyo baya dan haka cike da jin haushi ta katse kiran dif tana mita “sai a kira number mutun kuma ayi shiru aki yin magana “ta fad’a tana mai jan tsaki da dangwarar da wayar akan table ta qaraso inda maryama take ta zauna kusa da tace “wai ke bazaki saurarawa kanki da wannna kukan ba sai wani ciwo ya kamaki kisa mu shiga uku .?”

hawayen tausayin kanta ya sake gangaro mata tace “ummah Kiyi hakuri ta hanyar haka ne kawai zan raqe tarin damuwar dake tattare acikin zuciyata ta fad’a tana cigaba da sheshekar kukanta tare da dafe goshinta lokacin da zuciyarta ta hasko mata irin kallon da mr ata ya kafeta dashi wanda ko alamar kyafta idanunshi ba yayi haka ma mutumin daya kawota garesa mai tsananin kama dashi wanda yake ta qoqrin dakatar daita “duk da haka kukan ya isa haka kusan fiyye da awa biyar kenan kina abu d’aya kalli idanuwanki duk sun kunbura fuskarki tayi jajur maryama ta sunkuyar da kanta qasa tana sauke ajiyar zuciya akai akai .”“sun jima ahaka umma tana rarrashinta kafin ahankali umma ta kai hannu ta d’ago ha’barta tana kallon kyakkyawar fuskarta da ta ‘bata da ruwan hawaye, ta sakar mata murmushi mai ciwo tare da tsura mata ido “hakika duk nmj daya mallketa amatsayin mata shi ya morewa rayuwar duniya ,hakika mijinta zai yi saar samu mata kyakkyawa mai kyakkyawar zuciya da d’abia mai kyau ko waye wannan mai saar ?umam tayiwa kanta tmby tare da sakar mata murmushi kamar wacce ta tuna wani abu maryama ta mike zumbur ta nufi wajen kayanta dake d’akin umma ta zaro babban littafi wanda take rubuta abubuwan da suka shafi rayuwarta na bakinciki da farinciki ta dawo ta zauna kusa da umma “me kuma zaki rubuta “zan rubuta irin kalar wulakanci da’aka min yau a tun tsawon rayuwata wannna shine abinda aka min wanda yafi komai yi min ciwo “har da irin musgunawar da kawunki da matarsa suke miki “?a wajena bai kai wanda mr ata yayi min ba yasa an wulakantani an tozartani kuma ya ganni a gabansa amman hakan bai sa yaji cewar abinda yayi min zalinci bane he didn't even bother akan yayi ba daidai ba umma tsakanina da wannan mutumin allah ya isa nah ta fad'a a fili cikin zafin zuciya sannna ta fara rubuta kwanan wata kana ta soma rubutu tana jin zuciyarta tana mata zafi kamar zata fashe sakamakon fuskarsa da ta dinga mata gizo acikin kwayar idaninta.”

ta runtse kwayar idanunta gam tana jin ranta na sake 'baci zuciyarta na tafarfasa ita dai umma idanu ta tsura mata kawai tana kallon ikon allah tsaki taja tare da yage takarda ta dukunkune ta jefar daita ta koma ta kwanta tana sauke numfashi "kin fasa rubutawa ne ?"shiru tayi ta kasa bawa umma amsa dan bazata iya fada mata abinda idanuwanta suke gane mata "bazan gaji da fada miki kalmar kyi hakuri ki manta da abinda ya faru domin komai mai wucewa ne bahaushe yace wata rana sai labari ga gabe can tana d’ago miki hannu jikina na bani aiki nan har gida zai biyoki “kanta ta d’aura akan cinyar umma tare da runtse idanunta tana jin maganar umma na bin jinin jikinta suna sanyayya mata zuciya .”hakika bata da kamar umma acikin zuciyarta ita din cikakkiyar uwa ce gareta ta maye mata gurbin komai arayuwarta “daga yau bana son ganinki cikin damuwar nan matsawar ba so kike damuwarki ta juye zuwa jikina ba ayi uwa kwance ‘ya kwance ba shiru sukai umma ta kai hannunta saman gashin maryama tana cewa “a duk sanda na ganki cikin danuwa zuciyata tafasa take bana samun kwanciyar hankali har sai na ganki cikin walwala Kmr sauran mutane “love you mumy “!umma tayi murmushi tare da d’aga kanta ta kamo hannuwanta “ki manta komai kiji maryama ta gyad’a mata kai “in sha allahu mumy komai ya wuce zan cigaba da rayuwata kamar yadda nakeyi “yauwa diyar Allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi.”

daddare da misalin karfe takwas da rabi na dare ma’aikatan dake kula da bangaren kitchen ne suke ta faman kai kawo daga kitchen zuwa dining area kowannensu sanye da uniform kamar koda yaushe yayinda babbar yarinyar hjy zulai ke zaune tana kula da duk abinda suke abinci kusan kala shida ne akan dinning had’e da lemuka da ruwa sha marasa sanyi sosai ahankali ATA yake saukowa daga samansa jikinsa sanye da riga ash colour da wondo baki ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa wandonsa yayinda qafafuwansa ke sanye da wani hadadden silifas baki mai shegen kyau idanunshi sanye da glass ga wani kamshi na musamma mai natsar da zuciya na tashi ajikinsa .”ahankali yake saukowa tamkar wanda bashi da jini a jikinsa a d’age ya dinga kallon ma’aikatan dake jera kulolin abinci akan dining yana qare masu kallo domin qara tabbatar da ingancin aikinsu ,suna ganinsa duk suka shiga hankalinsu tare da qarawa jikinsu natsuwar aiwatar da aiki dan sun san halinsa muddin akai kuskuren ya gani zai ce ya dakatar da mutun aiki ,shiyasa komai cikin takatsantsan da kulawa suke yinsa .”cike da tsoro da fargaba suka cigaba da komai yayinda shi kuma ya cigaba da taku yana kallonsu duk ma sai suka sha jinin jikinsu dan wasu ma daga cikinsu sun fara tunanin wani acikinsu zai bar aiki gobe.”

A natse cikin isa da takama ya tsaya akan step na qarshe shi bai sauko ba shi bai koma ba yana ciza gefen lip’sdinsa na qasa yana sauke numfashi ahankali,byn kmr minti biyar ya sauko still hannuwan sa duk na cikin aljihunsa bai tsaya akoina ba sai inda mahaifiyarsa Take zaune akan kujera tana duba jarida punch wacce ke d’auke da hotonsa .”ya cire hannunsa d’aya ya d’aura akan hannun kujerar da take yana mai juya mata baya .” ta waigo a natse ta kalli bayansa kawai dan tun shigowarsa ta fahimci yana tattare da damuwa bari tayi sai ya huta ta tuntu’besa abinda ke damunsa “ya’akayi Adamcy meke damunka duk na ganka wani iri ?bai juyo ya kalleta ba haka zalika bai zauna ba “ka zauna mana Adamcy “bai zauna ba ya soma mgn cikin sanyin murya kamar zaiyi kuka “sweet heart ko zan iya tambayarki wani abu ?”.da sauri tace “sosai ma kuwa ka tambayeni duk abinda kake so a shirye nake dana baka amsar kowace irin tambaya “.ta fad’i hk cikin d’an damuwa dan duk lokacin data ganshi cikin damuwa tana finshi shiga damuwa ya juyo gabad’aya ya tsura mata tsumammun idanunshi “alal misali mutun ne ya zamanto yana da fikira sannan kuma shi mai wannan baiwar yana da katuwar matsala bayan haka kuma kana jinsa acikin rayuwarka sannan bazaka iya tafiyar da ayukanka batare dashi ba ko mutun zai iya janyo shi wannan mutun kusa dashi ya zama mallakinsa gabadaya ?”.

numfashi ta sauke da karfi sannan ta numfasa ta riko hannunsa ta zaunar dashi a gefenta kana ta fara magana cikin salon hikima irin nasu na manya “kowani bawa dake rayuwa acikin duniyar nan yana da matsala ,mutane mabam bamta amman akwai wasu matsalarsu bata kai ta wasu ba dole duk wanda zakayi muamula dashi sai kayi hakurin zama dashi saboda duk dan Adam yana tattare da matsala kawai na wani ne yafi na wani ,dan haka shi mai wannan fikira idan kaji har acikin zuciyarka ya samu matsuguni karka damu da matsalarsa dan matsala bata qarewa arayuwar d’an adam hakuri zakayi ka janyosa ajiki ka bashi kulawa idan akayi sa’a sakamakon hkn sai kaga matsalarsa ta ragu sannan km ka amfana da fikirarsa kaga anan ma ka samu riba biyu ka sanyashi ya samu natsuwa sannan ka amfana dashi na baka amsar tmbyrka ko nima zan iya tambayarka ?”tsura mata tsumammun idanunshi yayi yana kallonta haka nan yaji zuciyarsa ta gargadesa da kar ya yarda tai masa nata tmbyr dan haka ya girgiza mata kai alamun a’a “ok mr ATA muje kaci abinci ammi ta kwalla ma tabawa kira har sau biyu .”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull