Kenza eBookz

Mar'adams book 3 - Chapter 4

Mar'adams book 3 - Chapter 4

Mar'adams book 3 Chapter 4: Mar'adams book 3 Chapter 4. cikin kankanin lokaci ta bayyana sanye cikin doguwar riga tace “mami gani !“muje kiyi serving din…

3,360 words

cikin kankanin lokaci ta bayyana sanye cikin doguwar riga tace “mami gani !“muje kiyi serving din Adamcy abinci cewar mami kai kuma muje ko ? “no sweetheart barni kawai anan “shikenan bari akawo maka abincin nan bai yi mgn ba ya runtse idanunshi shi kad’ai yasan me yake ji a gangar jikinsa damuwarsa ta ninku fiyye da can baya “mami ta janyo qaramin table gabansa “adaidai lokacin da mai aiki ta qarasa da d’an hanzarin gudun karta tafi da sauri ta sha zagi a gurinsa mami ta mike tabi bayanta .”a natse take komai duk bai motsa ba ta wuce taje ta tsaya kusa da mami “mami !naam !”wani abinci zan zuba masa ? Kinsan shi yafi son shimkafa ki zuba masa kiyi masa plet din salad dabam ta amsa da to ta yi Kmr yadda mami tace ta d’auka ta kai Kan table din gabansa ta ajiye har ta juya tayi taku biyu taji sautin muryarsa a dake “Ke!ta tsaya cak hantar cikinta na wani irin kad’awa yayinda jikinta ma ya d’auki rawa ta fara sauke numfashi da karfi tana addua allah yasa ba wani laifi tayi masa ba “ba dake nake mgn ba ?ta juyo da wani irin sauri ta tsura masa ido abun mamaki idanunshi a runtse suke cikin hanzari mami ta qaraso wajen tana cewa “Lafiya Adamcy ? numfashi ya sauke yana bud’e idanunshi akan mami “kiyi tafiyar ki sweetheart tace “to ! ta kama gabanta sai dai duk hankalinta na kansa ya kalli mai aiki cikin isa da kamewa “ meye aciki ?muryarta cike da tsoronsa tace “rice and stew “.daukesu bana bukata?” shiru tayi can tayi karfin hali ta kwantar da murya tace “yalla’bai to me zakaci ai sai a dafa maka komai ka kake so ?ware idanunshi yayi sosai “waye zai ci jagwalgwalonku I think you’re cray.”

tace “to yau kuma abun ya motsa ta koma da baya ta kame tana cigaba da addau acikin ranta allah yasa maganarta bata hassalasa ba yaje ya koreta ta shiga ukunta bai qara magana ba ya tashi ya canza wurin zama ta kwashe komai ta maida kitchen tana yiwa mami bayani “barni dashi bari naje na samesa dan da alamun yau rigima yake ji “Adamcy nah ya’akayi kuma kace baza ci abincin ba ?yatsina face dinsa yayi “am not feeling eating any…”haba Adam ka dinga qoqarin bawa cikinka hakinsa ko na dafa maka kusku ne ?kamar yace “a’a !sai kawai yaji tausayin mahaifiyarsa ya kamashi tana matukar kula dashi da rayuwarsa dan haka ya gyad’a mata kanshi kawai tamark wani qaramin yaro.” ta juya ta koma kitchen da sauri tana kiran tabawa tazo ta tsaya kusa daita “ dauko min abubuwan da zamu had’a joluf din kuskus zan masa a natse mami take yin komai cikin kankanin lokacin ta dafa masa joluf din kusku wacce ta wadatu da korrot,green beans da kayan kamshi hanta da koda a madadin nama nan da nan kamshi curry da tyme ya soma tashi kusku din yayi kyau sosai sannan tace maza tabawa d’auko ki biyoni dashi “.

Turus mami tayi tsaye sakamakon rashin ganin ata a inda ta barshi “ina kuma yayi ?tayiwa kanta tambayar “kardai fita yayi ?Aa bazai fita adaidai wannan lokacin ba sai dai idan dakinsa ya koma kai tsaye hanyar step ta nufa inda mai aiki tace “mami na biyoki da abincin ne ?”eh tabawa biyo dashi da hanzari mami ta tura kofar parlour’nsa tare da sallama taga baya nan wani yawu tayi qoqrin hadiyewa sannna ta dakatar da tabawa da cewa ajiye tray kiyi tafiyarki ta nufi d’akinsa nan ma baya nan ta sake fitowa da sauri ta shiga d’ayan bedroom dinsa tsaye ta gansa ya rungume hannuwansa duka a saman faffad’an qirjinsa ya tsurawa zanen hoton maryama ido a tsorace take kallon bayansa inda shi kuwa yayi zurfin cikin tsananin tunaninta “bazai iya hakura daita ba tabbas soyayyarta tana da matukar tasiri a rayuwarsa ,ji yayi kamar da ba sonta yayi ba a yanzu ne ma ya fara sonta yayi shiru tare da runtse idanuwansa sosai yana kiran sunan Allah zuciyarsa na sake nitso acikin tafkin qaunarta ” a hankali ya bud'e idanuwanashi wanda suka kad'a sukayi ja saboda wannan qaddarar tafi komai yi masa ciwo acikin rayuwarsa a fili kuma cewa yayi "adam ka hakura daita karka kuskura ka shiga hurumin Allah ballantana ka bayyana mata soyayyarka bare ma kasan yarinyar nan bazata soka ba sakamakon abinda kayi mata. bugu da qari kuma matar wani ce Ya qarasa maganar wasu hawaye masu zafi suna saukan masa akan kumatunshi “wace yarinyar ce matar wani ?yaji saukar muryar mami ?daga sama cikin sauri ya share hawayensa dan kar mami ta gane halin da yake ciki a dan tsorace yace “amm ..” sai kuma sai yayi shiru yana tunanin abinda zai fad’a mata dan bai iya karya ba duk abinda zai fito daga bakinsa to gsky ne “.

mami ta tsura masa ido jikinta ya kama rawa numfashinsa ta hango yana fita da karfi saboda zubar hawayensa “kayi min bayani wai meke damunka ne kake zubar da hawaye?ko dai har yanzu matsalar yarinyar nan ce ?shiru yayi ya kasa cewa komai dan bazai iya mata karya ba kuma bazai iya fad’a mata cewar ya ganta amatsayin matar wani ba .”mami batayi mamakin shurin da yayi mata ba domin tasan halinsa a duk lokacin da yayi shiru haka baya son fad’ar gsky abinda ke cikin ransa ne tana kallonsa ya nufi kofar fita jiki a sanyaye ta biyo bayansa alokacin da ya samu waje ya zauna akan kujera ya d’aura kafarsa d’aya akan d’aya yana kallon saman parlour’n yana cizan lips dinsa dan shi ne kawai abinda yake ganin zai iya yi a halin damuwar da yake ciki dan zuciyarsa tafarfasa take ta sake nitso acikin tafikin qaunar maryama .”ahankali ta zauna a gefensa “adamcy ga abincin kaci kar yayi sanyi lumshe tsumammun idanunshi yayi ,shi dai baya jin zai iya sakawa cikinsa komai bashi da wannan kuzarin ,bashi da wannna natsuwar ,bashi da wannna ‘yancin tun da ya rasata yasan ya rasa komai nashi bazai sake morewa ba ko kuma yace rayuwarsa tazo qarshe dan idan babu ita cikin rayuwarsa shima babu shi .”

sunkuyar da kanshi yayi kasa yana kallon zara zaran yatsun qafafunsa masu kyau da haske “shikenan wahalar bazan nayi adamcy bazakaci komai ba ?shiru yayi batare da yace mata qala ba “sanin halin yanayinsa tamkar mai nasaba da jinin sarauta yasa ta matso da table din da tabawa ta daura tray abinci akai gabansa tana cewa “yau dai da alamun miskilanci ya motsa?” ta fad’a tana bude masa kula abinci tana zolayarsa sannna ta mike ta qarasa inda fridge dinsa yake ta bude ta dauko ruwa mara sanyi sosai tazo ta ajiye masa kallonta yayi cike da tausayawa yana wahalar da mahaifiyarsa over “kiyi hakuri sweet heart .” dakayi me adamcy ?ina wahalar dake dayawa “babu komai Allah yayi maka albarka ni dai fatana da adduata Allah ya yaye maka tunanin yarinyar nan dan idan akwai abinda ke cin raina bai wuce naga ka zauna kana bata lokacinka akan tunaninta ba .”numfashi ya sauke kawai batare da yace komai ba “nifa banga abun so a wajen wannna aljanar yarinyar ba bai san ya akayi ba murmushin ya bayyana akan fuskarsa yana cewa aljana kuma sweetheart?sosai ma kuwa aljana ce mana shiyasa kullum nake nemar maka tsari daita domin tana cikin ta bada gudunmuwar rabuwarka da matarka da har yanzu baka waiwayi inda take ba, ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe ina ganin ma kusan tare zasu haihu da auta “rayuwar maryam na matukar bani tausayi adamcy domin nasan duk abinda tayi ba da son ranta bane tursasata akayi bugu da qari soyayyarka ..”

Lumshe idanunshi yayi na second biyu sannan ya bud’e yana kallonta a tsanake dan shifa sam ya manta da wani labarin wata maryam arayuwarsa dauke da ciki sai yanzu da tayi maganarta “sweetheart !ya kira sunanta “na’am adamcy ka tausayawa maryam tana bukatar tausayawarka “dan Allah sweetheart ki bar maganr wannna yarinyar ta rigada ta zama tarihi arayuwata ita kuma aljanar da kike magna akanta itama an bar tunaninta kai na ma cireta arayuwata sai yanzu na fahimci cutar da nayiwa kaina akanta na ‘bata tsawon shekaru akan abinda ba samu zanyi ba yayi maganar cike da raunin zuciya “alhamdulillah Allah na gode maka kai gsky ka wanke min zuciyata yau “yanzu dai ka fara cin abinci!babu mutsu ya fara cin abinci a natse ficewa Mami tayi daga dakin ta sauko zuciyarta cike da farinciki shi kuwa bayan fitarta kasa cigaba da cin abinci yayi ya kai tafin hannunsa ya shafa sumar kanshi zuwa fuskarsa ya had’a tagumi yana tunani .” duk inda ya motsa yarinyar yake ji acikin ransa ji yake tmkr ransa zai bar gangar jikinsa ranar dai kwana ata yayi yana juyi da tunanin maryama sai yayi kamar ya saita tunaninsa yayi amfani da karfinsa sai ya sake shawara saboda jin tsoron allah duk yadda ya kai ga sonta bazai iya taka dokar Allah ba .”

Washegari bai tashi da wuri ba sakamakon rashin baccin da bai samu ba adaren jiya ,sai bayan sallah asuba bacci mai nauyi ya daukesa ,shigowar mami biyu dubasa bai tashi ba ,da misalin karfe d’aya ya sauko nan ya iske mami tare da zabiba da yaranta biyu suna ganinsa suka zo gurinsa da gudu suna kiran sunansa d’aukar ammi yayi mai sunan mami ya cillata sama yna mata wasa sannna ya riko hannun siyam yana cewa “yaushe kuka zo gidan “? zabiba tayi murmushin jin dadi tace “bamu jima da zuwa ba ina yini yaya ?shareta yayi tmkr ba dashi take ba yace “good morning sweetheart?morning or afternoon adamcy ka kalli lokaci ka gani bai kalli agogo ba yace “ai dan bamu had’u bane da safen shiyasa sai yanzu .”murmushi ta saki tare da dafa hannunsa dake kan nata kai dai wallahi bahagon mutun ne” numfashi kawai ya sauke yana jan yatsun hannun ammi “mami ta kallesa a tsanake “yaakayi kanwarka tana gaisheka amman kayi mata banza ?ka dinga yiwa yanuwanka uzuri ka yafe masu wannan matslar fa ba wata matsla bace da zaka riketa gam a ranka yanzu ko bayan raina haka zaka dinga hukuntasu idan sunyi maka laifi ?” to a ina kake son su saka ransu idan wata matsla ta kunno kai cikin rayuwarsu ?.”uncle see aunty girl ta hanamu mu fita muje wajen yesmen kuma mu muna son zuwa siyam tayi maganr tana nuna masa mami da yatsanta .”

“murmushi yayi jin suna da take kirata dashi “karki damu aunty girl zata bari kuje kuga yesmin no kace ta barmu muje yanzu saboda yesmin mukazo inji cewar siyam “siyam take your sister and meet tabawa idan zamu wuce zan kaiku ku ganta shikenan tashi sukai suka wuce rike da hannun juna yayinda ata ya bisu da kallo yana lumshe ido yana jin ina ma yaransa ne .”ahankali ya bude idonsa yana motsa lips dinsa “shikenan sweetheart komai ya wuce amman gsky ban so na sauko hk da wuri ba har sai bayan shekaru masu yawa “Au yanzu nan ka sauko da wuri kenan wajen wata biyar ?ya lumshe mata tsumammun idanunshi kawai kallonsa zabiba tayi cike da tausayawa tace “allah dai ya huci zuciyar babban yaya in sha allahu bazamu sake ba “kuma sake ya fad’a tare da mikewa ya nufi kofar fita yana cewa “sweet heart sai nã dawo “bazaka karya bane ?bana jin cin komai sai dai na dawo kawai “to a dawo lafiya Allah ya tsare “Ameen !” ya amsa ya nufi kofar fita .”

kai tsaye hanyar kamaninsa aka nufa dashi yana zaune hannunwansa rike da jaridar daily trust yana karantawa yana son wani abu ya d’auki hankalinsa na son kawar da tunanin maryama acikin ransa amman aikin banza yayi domin duk shafin da zai bud’e sai fuskarta sai ta bayyana aciki wani dogon tsaki yaja ya ajiye jaridar hannunsa ko da yake shima yasan dole abun zai damesa kuma zai hana rayuwarsa sukuni har suka qarasa office dinsa tunaninta ne fal acikin zuciyarsa bai dade da zama ba sai ga some ta shigo bayan ta nemi izinin shigowa wasu file ta ajiye agabansa cike da girmamawa tace "sir ana bukatar saka hannunka anan” bai ce mata komai ba ,ya kar’bi biron data miko masa batare da bata lokaci ba duk ya sign ta kwashe file din ta fice tana satar kallonsa dan da alamun yana cikin damuwa duk da dai ko yaushe fuskar nan tashi a hade take amman na wannan karon ya zarta na sauran lukuta har tayi taku biyu sai kuma ta juyo ahankali ta dawo inda yake zaune ya d’an d’aga kwayar idanun shi ya kalleta sannan ya d’auke idanunshi “sir ko zan iya cewa wani abu ?shiru ya biyo bayan mgnrta na second biyar sannan yace “zaki iya “sir yau yanayinka yayi wani iri Kmr akwai wani abu dake damunka “yes akwai abinda ke damuna wanda nake jin kamar na kashe kaina .”

”what ?ta fad’a tana zaro ido kafin ta sake mgn yace “you can leave shiru tayi tana dubansa rike da file ganin haka yasa ya janyo wasu file gabansa ya shiga dubawa duk a qoqarinsa nason ya manta da komai alokacin amman ya kasa duk shafin daya bud'e still dai hoton fuskarta yake gani tana hawaye cikin mummunar tashin hankalin data bar office dinsa jiya ."tsaki yaja yana dukan table din gabansa da karfi “what’s all nonsense ya fad’a yana mai rike goshinsa da hannunwansa duka yana jin wani irin zugi from no where”ke kuma tsayuwar me kike yi ?yayi mgnr a tsawace da sauri ta nufi kofar fita cikin zafin zuciya ya zabura ya mike tsaye ya fara zariya acikin office kafin ahankali ya tsaya cak a tsakiyar office yana dogon nazari kusan minti goma yana tsaye yana qoqarin nemawa kansa mafuta domin dole ya nemowa kanshi mafutar da zai rabu da tunaninta gabad’aya ya huta saurin waiwayowa yayi sakamakon jin sautin muryar ammar a bayansa .” Bai ce masa uffan ba yaja wani dogon tsaki yana mai d’auke kwayar idanunshi akansa cike da jin haushinsa domin a yanzu ya gane shine ma damuwarsa ,shine mutumin daya bari ya rasa duk wani farincikinsa duk yadda yasan halin da yake ciki amman yana ji yana kallo yarinyar nan ta zama mallakin wani bashi ba .”

ahankali ata ya kasa dauke tsumammun idanunshi daga kan ammar yana jifansa da wani mugun kallo mai d’auke da fassara dabam dabam ahankali ammar ya dawo gaban ata ya tsaya yana kallonsa kamar yayi dariya amman sai ya share saboda ganin fuskar ata din har lokacin tana cikin yanayi na damuwa da tashin hankali wanda kuma yasan na rasa maryama ne shima ata kallonsa yake amman kallon tsana ammar ya saki fuska yana murmushi wanda bashi da maraba dana mugunta “mamaki murmushin ammar ata yake wato ya cucesa kuma yazo ya tasa shi gaba da murmushin mugunta ?sai da ammar ya bashi wasu mintun sannna ya fara magana “haba friend kar dai maryama ce ta gigita rayuwarka haka ?bai kulashi ba sai ma sake had’e fuska da yayi sannna ya juya ya bar wajen “cikin daga murya ammar yace “daman nasan sai tayi wuji wuji da rayuwarka tasa ka fad’i kasa warwasss cak ata ya tsaya yana cizan lip’s dinsa kamar yayi masa mgn sai km ya cigaba da taku ya nufi d’akin dake cikin office wata dariya ta subucewa ammar alokacin da ata yake qoqarin shigewa d’akin bai san sanda ya juyo a fusace yace “kai me kake nufi ne wai dani ?”

“Oho abinda kake nufi nima shi nake nufi yana daga inda yake ya girgiza kai had’e da cewa “ka shiga hankalinka ammar da wannan dariyar da kake “na shiga hankalina ko dai ka shiga hankalinka ina ta faman kiranka a waya tun jiya kaki dauka yanzu kuma nazo ina ta mgn ka min shiru sai faman cika kake kana batsewa “idan dan abinda ya faru ne kake fushi kayi hakuri amman dai yanzu abar duk wannna maganr nazo maka da wata magana ne mai mahimanci .”a wulakance ata yake kallonsa tare da cewa “bana bukatar komai daga gareka coz I hate you !I hate you ammar ganinka da maganarka babu abinda yake qara min ayanzu illa jin bakinciki da tarin tsanarka acikin zuciyata.” da sauri ammar ya matso kusa dashi yana qoqarin riko hannunsa yay saurin ja baya “don’t try me ammar! ya fad’a a matukar fusace ammar bai damu ba dan yasan halinsa ya matso sosai yana dubansa “wallahi ammar ka cuceni ,ka cuci rayuwata bazan ta’ba yafe maka abinda ka min ba sakamakon kasan duk wata damuwa dake tattare da shafukan rayuwata akan yarinyar nan amman dan mugunta irintaka ka cutar da zuciyata, yarinyar da zaka d’aukota musamman ka kawo min ita nayi tozali daita ba wai ka tsaya yi min wasa da hankali ba wallahi ka cutar dani ammar gashi har wani yayi galaba aureta “.

ka tsaya kaji mai zance maka yanzu “bana son jin komai ammar macuci mugu kawai mai bakar fuska ya fad’a yana hadashi da wani kyawawan mari. duk wannan maganar a zuciye yake yi yana cewa “get out from my office I don’t want to see your face again tare da point dinsa da hannusa kana ya cigaba da magana kamar zai zubar da hawaye” dan iska kawai da kai mai zaka fad’a ?bayan ka gama lalata min rayuwa sannna kazo kana cika ni da surutu banza da wofi “Adam ni ka mara ?an mareka wallahi idan ka cika da surutu zan qara maka kuma babu abinda ka isa kayi banza mara mutunci maci amanar abota wallahi ka gama cutata “enough ata bafa tsoronka nake ji ba na cuceka ko ka cuci kanka ?”ya fad’a tare da jan tsaki “.“Oh haka ma zakace kenan “?kenan har yanzu kana da karfin halin cigaba da bata min rai ?wai tsaya ma na tambayeka kai masoyina ko makiyina?”duk matsayin daka bani na kar’ba “okay na baka matsayin makiyina domin duk duniya kaine makiyina na farko kuma na tsaneka fiyye da tsanar da nayi maka daga yau ammar babu ni babu kai ka cire ni acikin duk wata danganta amman kafin nan zan shiga ciki dan girman allah ka cigaba da tsayuwa har na fito kaga yadda zanyi da kai yana gama fad’ar haka ya juya yana sauke numfashi sama sama .”jiki a sanyaye ammar yake kallon kofar daya shiga kamar ya shiga amman yasa shigarsa bazai haifar masu da mai ido ba kuma bazai sauraresa yaji abinda ya kawo sa ba cike da zafin zuciya ya fice .”

*******

Da sauri maryama ta shigo dakinta dake bangaren mahaifiyarta kunneta manne da waya ta qarasa inda kayan aikinta yake ta dauki biro da joter adaidai lokacin da mahaifiyarta ta shigo tana daukar kayansu dana habib zata hada cikin kayan wanki da sauri ta zagayo cike da farinciki ta daura joter akan gadon bayan mahaifiyarta ta soma rubutu tana cigaba da amsa kira “okay!!Ina jinka okay na fahimta shikenan zan tura muku da irin nawa kugani thank thank so much “.aunty ta mike rike kayan tana dubanta itama maryama dubanta take fuskata kunshe da dariya “Kinsan wani abu ?aunty ta girgiza mata kai itama fuskarta cike da farinciki “na samu aiki a alico insurance ta fad’a tana rungumeta ajikinta nan da kwana hudu zan fara aiki dasu “kin gani ba ai daman na fad’a zaki samu wani da yarda allah kofar allah ai tana da yawa in sha allahu daga wannan nasara kin dinga samu nasara kenan arayuwarki domin adduata tana tare daku akoda yaushe na gode sosai mumcy tana sake makale wa ajikinta tmkr yarinya.” karki damu princess maza kije ki fadawa ummanki nasan zataji dadi “okay bari naje wallahi zataji dadi sosai ta dauki qaramin hijab dinta ta saka ta fice .”

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 4

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull