Kenza eBookz

Mar'adams book 3 - Chapter 5

Mar'adams book 3 - Chapter 5

Mar'adams book 3 Chapter 5: Mar'adams book 3 Chapter 5. Cike da sauri maryama ta isa bangaren umma inda ta isketa tsaye rike da waya tana mitar masu…

3,277 words

Cike da sauri maryama ta isa bangaren umma inda ta isketa tsaye rike da waya tana mitar masu kiranta da numbobi dabam dabam basa magana ita kam wannan matsalar ta fara isarta maryama ta iso gareta tana fad’in “umma nah!! adduarki dai yau ta kar’bu ta riko hannuwanta duka cikin nata cike da tsananin farinciki “me ya sakaki farinciki haka maryama ?maryama tayi murmushi tana cewa “umma ki cinka mana !”umma ta tsura mata idanu cike da farinciki tana nazarinta kafin a tsanake tace “ina tunanin aiki ne ko ?gabadaya maryama ta rungumeta ajikinta tana murna “wallahi umma nah aiki ne ya biyoni har gida kamar yadda kika min addua maryamarki zatai aiki da aliko insurance kamfanin dake gogyaya da duk wani kamfanin ATA dake cikin qasar nan bama AGC ba.” alhamdulillah mahakurci mawadaci tabbas duk wanda yace Allah hakika allah zai isar masa yanzu dai bari na fita na siyo sweet na rabawa marayun unguwar nan Allah ya kawar mana da mugun ido, karki fad’awa kowa bayanin kin samu aiki bayan ni da ummanki “in sha allahu umma babu mai ji .”sosai maryama take jin dadin yadda umma take mata ,bata nuna mata damuwarta akan rashin sadam kawai nuna mata take itace a gabanta da cikar burinta ko da yake ai daman can umma ta tace koda kuwa babu yaya sadam a tsakaninsu .”Qarfe biyar daidai maryama ta mike tana cewa umma mai zamu daura ne ?mai zamu ci maryama ?itama umma ta tamvayeta cike da kulawa “ko nayi miki kunun gyad’a ni kuma sai na dama kostad na soya Kwai na hada dashi “kai maryama wai mai yasa bakya son cin abinci mai nauyi ne ?shiyasa gaki nan kullum a rame “wallahi umma abinci mai nauyi damuna yake bari na shiga kitchen ta nufi kitchen domin tanadawa ummah abinda zata ci yayinda ita kuma umma ta fita domin siyan sweet ta rabawa yara.”

Qarfe d’aya daidai na rana salim ya shigo cikin office din ammar ya d’ago a natse sukai 4 eye’s da salim numfashi ya sauke sannan ya maida idanunshi akan aikin da yake, salim ya samu waje ya zauna akan kujerar dake fuskantar ammar “salim yaakayi ne kwana biyu ka boye ba’a ganinka ?ya fad’a tare da mika masa hannu suka gaisa “wallahi ina nan ya harkoki ?to gamu nan acikinsa alhamdulillah .”office din ya d’an d’auki shiru na wani lokacin kafin salim ya cigaba da magana “tun shekaranjiya nake son nazo muyi magana da kai akan ATA “uhm ina jinka! ammar ya fad’a yana ture file din gabansa ya had’e hannuwansa waje d’aya ya rike ha’barsa dashi yana kallon salim .” ya kamata ka duba halin da ATA ya fara shiga , gabdaya duk ya fita haiyacinsa tafiya kawai yake yi amman baya cikin natsuwarsa da kwanciyar hankalinsa .”to ni meye nawa aciki yaga zai iya ne sai abarshi da damuwarsa “no no !! ammar bazamu biye masa ba kasan shi kasan halinsa ko nace kusan kowa yasan da wannan ,ka ajiye komai mu fuskanci matsalarsa kar ya sake rasata a karo na biyu mu shiga uku .”

zuba masa ido kawai ammar yayi yana sauraronsa yana jin wani zallar ‘bacin rai na rasashi “”wallahi komai ya cakud’ewa ata baya cikin kwanciyar hankali “kai kasan radadin da yake ji bazai tsaya iya haka ba tun daga kalmamominka na wancan ranar komai ya tsya masa “me zanyi ko me kake son nayi masa naje gurinsa domin na fad’a masa gskyar komai amman ya koroni da rashin mutunci ai Adam ya gama wulakantani marina fa yayi kamar wani yaronsa gsky ni yanzu na yanke shawarar ma bazan fad’a masa matsayin maryama ba dan kwata kwata maryama bazata iya dashi ba, ta ina zata fara irin wannan rayuwar da yake sam bazata iya ba .” sororo salim yayi yana dubansa da mamaki kafin yace “gskyar adam yanzu na sake tabbatar da baka qaunarsa kanka tsaye kake fad’ar wannan maganr ?salim ya furta yana kallonsa a natse kamar yadda ammar yake kallonsa shima “kana kallona ai gsky ne ka fito ka fad’a masa gsky ko ni ka bani dama na fad’a masa yasan ta yadda zai bullowa lamarin yanzu haka na barosa a office dinsa yana shan sagari kai kasan waye shi idan yaji sigari bata kawar masa da damuwarsa wani abun zai koma sha kaga ai mun cutar dashi kuma mun cutar da kanmu domin dai duk abinda ya faru dashi a yanzu duk zamu shiga damuwa kuma kaine silar faruwar komai dan haka tun wuri kasan abunyi ni na gama maganata ya fad’a tare da mikewa tsaye ya nufi kofar fita daga office din.”

Bayansa ammar yabi da kallo kwakwaluwarsa na caji da tunanin maganganunsa “tabbas maganrsa gsky ce duk yadda ammar yaso yaki daukar shawarar salim a qarshe dai sai daya dauka domin bazai so ya rasa lafiyar danuwana kuma abokinsa ba yayi masa ma abinda yafi wannan abaya bare d’an wannan abun da bai taka kara ya karye ba idan da sabo ya dace ace ya saba da halinsa shi haka tashi qaddara take ahankali ya mike tsaye jikinsa a sanyaye ya d’auki wayoyinsa ya nufi kofar fita yana kiran direbansa .”ko daya sauka qasa har direba ya juya Kan mota yana tsaye yana jiran fitowarsa ya bude masa ya shiga .” da hanzari ya bud’e masa bayan mota ya shiga ya zauna ya maida murfin motar ya rufe ya shiga mazauninsa ammar na fad’a masa inda zasu ahankali suka fito suka d’auki hanyar AGC cikin kankanin lokaci suka kawo ahankali direba yayi parking din mota ya kashe ammar ya fito kai tsaye hanyar da zai hau lifte ya nufa qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi dan bai san irin tarbar da zai samu ba kafin ya fad’a abinda ya kawo shi adduarsa kada ya iske kowa bare ya masa rashin mutunci a gaban wani gara idan daga shi sai shine da sauki .”

tun daga nesa ya ammar ya hangosa yana shan sigari ya sauke wani naunayen ajiyar zuciya ganin babu kowa a office din sai shi kadai ya daura qafafuwansa duka akan table sigari ne a hannunsa yana cigaba da busawa, gabad’aya idanunshi na kansa jikinsa a matukar sanyaye ya isa office din ya zauna agabansa batare da yace masa koami ba sai dai kwayar idanunshi na kallon kyakkyawar fuskarsa yayinda idanun ATA Ke runtse yana sauke numfashi yana sake kai sigari bakinsa kusan 20 minutes ammar yana zaune yana kallonsa cikin kwanaki kad’an har ya fara fita haiyacinsa “lallai kam yasan zai iya aikata komai akan maryama dan ya rigada ya gama kamuwa da matsanancin soyayyarta “ahankali ATA ya bud’e idanunshi sai dai ganin ammar ne yasa ATA mikewa ya d’auki wayarsa ya fad’a d’akin dake cikin office din ammar ma ya mike tsaye da sauri ya biyosa yana kiran sunansa “ATA ka tsaya ka saurareni kaji abinda ke tafe dani “garam kawai ammar yaji ya rufo kofar da karfi yana danna mata key .”

“ya rabbi ammar ya fad’a yana dafe goshinsa da hannunsa d’aya “kafin ahankali ya fice yana kiran layin salim bayan ya dauka ya zayyane masa komai har ya koma office waya suke da salim a qarshe sukai sallama “Qarfe takwas na dare ammar ya shigo cikin gidan mami batare da ya bukaci rakiyan salim ko wani ba, ya shigo ya gaishe da mami sannan ya haura sama zuwa kayataccen falonsa dake upstairs, bai iskesa a parlour’n ba ya wucewa direct zuwa bedroom dinsa jin alamun saukan ruwa ya fahimci wanka yake dan haka ya fito ya dawo zuwa parlour zaman jiransa mintuna fiye da ashirin ya dauka zaune sai gashi ya fito sanye cikin jallabiya milk colour mai azabar kyau, dukkanin ilahirin jikinsa na fidda wani azababban gamshinsa da ya gama kama komi nasa.hannunsa rike da wayoyinsa. kawai yaga mutun zaune yana fuskarshi wani dogon tsaki yaja tare da juyawa alamun komawa yaji sautin muryar ammar “heyy Mr ata sarkin nasara, sarkin zuciya sarkin girman kai ,ba komai yasa kaga ina ta faman bibiyarka ba sai dan na fad’a maka cewar maryama ba matar aure bace, sai ka ajiye wannan girman kan naka ka shiga sawun masu neman aurenta “wani irin waiwayowa ata yayi da sauri qirjinsa na wani irin buguwa da matsanancin karfi Ji yayi jikinsa suna barazanar kasa daukarsa lokaci daya zuciyarta ta nemi ta tarwatse ya dinga bin ammar da wani irin kallo kafin ahankali kuma ya fara taku ya tsaya agaban ammar yana kallonsa kawai batare da yace masa uffan ba duk da harshensa magana yake son yi masa .”

ahankali ammar ya sakar masa murmushin “da gaske abokina maryama rabonka ce ko ma nace matarka ce in sha allahu ammar ya furta yana dukan kafad’ansa ata bai yarda ba saboda ganinsa wasa da hankali kawai yake son yi masa ”“Wallahi wallahi !! kaji na rantse maka maryama bazawara ce zaka iya shiga cikin sawun masu sonta duk da ahalin yanzu babu kowa sai kai kad’ai “dan girman allah ammar karka min wasa da hankali zuciyata tana daf da bugawa “ka jifa na rantse maka duk iskancina bazan rantse maka akan karya ba “Allah ya shiryeka ammar Allah kuma ya yaye maka wannan mugun hali naka kai wato komai sai ka batawa mutun rai wata dariya ce ta subucewa ammar yace “ai zama da kai ne boss dole a koyi kalar halinka tsaki ata yaja yana cewa allah ya isa “what ?har yanzu dana fad’a maka gsky allah ya isa kake min ?kai nima Allah ya isa marin daka min Ata ya zabga masa harara “allah ka bani hakuri na yafe maka “wani tsaki yaja ka mutu idan dai sai na baka hakuri ai nine na cancanci ka bawa hakuri ni da ka kusan kaiwa lahira ammar ya kwashe da dariya “gsky dole fa muyi celebrity din wannan farinciki ko me kace ?”numfashi ata ya sauke yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa “ammar bana bukatar kowa yasan da zaman maganar nan bayan ni da kai da salim sai mb da dole na fad’a masa itama yarinyar banason ka fad’a komai “.

“itama iskancin zaka mata ?no ba haka bane a yanzu bazan iya fuskarta ta ba tunda kaga abinda ya faru a tsakaninmu gara na fara da dawo daita karkashin ikona da sannu komai zai tafi daidai fatan nasara abokina amman dan girman allah ka tausaya maryama yarinya ce qarama shiru ata yayi yana jin wani irin sanyi na mussaman na mamaye sansar jikinsa “ammar ina son yarinyarta nan soyayyarta gareni mai tafiyar da ruhi ce wallahi ina jin idan na rasata zan iya rasa komai nawa kuma zan iya sadaukar da komai nawa akanta “maryama tayi saa arayuwarta allah yasa ta gyara min kai ta caza maka kwakwaluwa “murmushin gefe baki yayi “kana ganin bazata iya ba ?”kai yanzu kaga nayi maka kama da irin wadan nan mazan?karka cika min baki ata yanzu fa kace zaka iya komai akanta?”yes of course nace amamn bazan dauki raini ba “iskanci banza yarinyar ma da bakasani ba ko zata amince da soyayyarka .” karta amince da soyayya amman zata amince da aurena “sun jima tare suna hirar farinciki a tsakaninsu wanda yaushe rabon su kasance haka sai da suka ci abinci sannan ammar yayi masa sallama ya wuce gida zumar zasu had’u gobe AGC.”

Washegari

Maryama na zaune akan gadon mahaifiyarta rike da takardan zanenta wayarta ta dauka tana cewa hello daga can bangaren taji ance “some ce daga AGC compaing shiru maryama tayi ta kicewa komai sai dai tana saurararta ATA dake zaune ya sauke naunayen ajiyar zuciya sakamakon jin sautin muryarta ,nan take yayi wa some alama ta saka wayar a hands free take some tabi umarninsa “fatan kin fahimci me magana ?can bangaren maryam tace “Eh naso na dan fahimta fatan dai lafiya kuka kirani ?“eh ! lafiya da..daman muna bukatarki ne domin Ki cigaba da ai.. “ai kar ma ki qarasa wannan mgnr dan har abada bazan qara tako wadan nan kafafuwan nawa acikin wannan banzar kafanin naku ba.” ta katseta ta hanyar fadar haka .”ni yanzu ma na samu aiki mai kyau a wani kamfani dayafi naku komai yanzu haka jibi jibin nan zan fara aiki dasu dan haka ki nemi wata ta soma qoqarin katse kiran “ki tsaya kiji maryam karki yi sau..” na tsaya naji nayi miki me ?me ma kuka daukeni shasha wacce batasan ciwon kanta ba ?“kunsan zaku bukaceni me yasa kuka wulakantani?“Kiyi hakuri dan allah maryama some ta tsinci kanta da furta hakan .”

“sorry for what?, wallahi ko duk duniya zaa bani a wannan kamfanin babu ni babu wannan kafanin har abada ki tsaya ki saurareni “mr ATA da kanshi ya bada umarnin a kiraki “me naji kikace yanzu ?sectary ta sake maimaita abinda tace “oh yanzu na fahimceki wulakanci da mutumin nan yayi min na lura yayi miki dadi ko ba haka ba ?,” a’a karki ce haka wannan ma dai allah ne ya qaddara hakan zata faru da km laifinki “amamn dai baki da hankali ko ?a gabanki aka tozartani byn kun daukeni aiki idan ke aka yiwa abinda aka min zaki iya cigaba da aiki?” “kinga sakariya karki damu kanki akaina “ki tsaya ki girmama wanda yace a kiraki ata ya zabgawa some wata katuwar harara yana hura hanci wanda batasan dalilin hararar ba “waye shi wanda yace a kirani ?some tayi shiru tana dubansa kamar yadda yake kallonta “shi wannan mutumin a wajenki yake wani abu mai mahimanci a wurin maryama kuwa zero ne ku nemi wata please Kmr yadda na fad’a dan ni har abada bazan sake dawowa AGC company ba “. tana gama mgn ta katse kiran maryam !!hello kina kina shiru taji alamun ta kashe ganin haka yasa ta kalli mai gidanta .”

“Sir fatan kaji duk bayaninta wai zata fara aiki da wani kamfani bazatai aiki damu ba gabadaya bata bukatar tayi aiki damu yanzu me zamuyi sir ?nasan me zanyi wannan abu yayi min dadi ina son haka ya fad’a tare da yin shiru yana jin wani iri a gabdaya ilahirin jikinsa “zuciyata da wannan kafanin yana matukar bukatar maryam y fadi sunanta yana lumshe idanunshi ina bukatar gabadaya diters dinta tun daga Kan address dinta kai komai da komai har zuwa Kan kafanin data samu aiki kai gabadaya komai daya shafeta ai idan ba wannan kafanin ba babu wani kafani da zasu dauketa aiki ya fad’a “okay sir .”ta juya ta fita da sauri domin ta nemo james dan shine zai fita hanzarta gudanar da komai .”sai bayan da some ta fita yayi tunanin kiran ammar dan dole zai san komai nata wayarsa ya dauka ya soma neman layinsa kira daya ya dauka nan ya fad’a masa komai ai kuwa ammar yace me zai yi idan ba dariya ba yana cewa “kai gsky maryama ta burgeni haka ake son mace “kai banason isknaci na kiraka ne dan ka fad’a inda take kuma diyar waye ba wai ka tsaya min dariya ba “.dan girma allah ka barni nayi dariya daman nasan bazaka samu maryama cikin sauki batare da kasha wahala ba “inna lillahi wai kai dole sai kagani acikin matsala ne ?”no ba haka bane amman wallahi abun yayi min sikari bari Gobe zan zo na kaika gidansu da kaina daga nan ..””dif ammar yaki ya kashe wayar ya kwashe da dariya yana nemansa a layi sai dai kiran na shiga yaki dauka .”

Tsaki maryama tayita ja babu kaukautawa tana fitowa zuwa parlour’n “ta zauna akan kujera tana furta “iskanci banza da wofi shasha ma suka daukeni kamar wannan né kawai kamfanin mutane zasu rayu dashi ,ina bazan ta’ba daukar wannan wulakanci ba gashi ma Allan yayi min arziki da wani aikin daman kuma haka lamarin allah yake idan ya kulle maka wata kofar sai ya bude maka wata .”washegari babu abinda aka fara gabatar dashi gaban ATA sai batun maryama good morning sir ?mornig ! Kawai ya furta atakaice sir maryam hussein zata fara aiki da alico insurance shiru yayi yana cigaba da abinda yake tamkar babu wata damuwa atare dashi “sai me kuma ? ya tamabayeta “sai danginta ita din family din bagoro ce tana unguwar gwagulori dake cikin agege da zama.” da sauri ata ya dago ya bar abind yake ya tsura mata ido har ya bata tsoro” ya shiga uku yar geto area ? ganin irin kallon da take masa yasa ya dauke idanunshi yana cewa “uhm ina jinki .” “sannan yayan mahaifinta yana da qaramin kafanin bired wanda yanzu ya zama mallakin matarsa sakamakon mutuwar da yayi wannan kafanin yayi karfin da yake supply din biredi ga ciki da wajen agege a halin yanzu kanin mahaifinta mlm gali ne Ke kula da komai na gidansu da kuma gidan biredi “ya zaayi a samu numbresa ?ai gabadaya mukayi komai gashi ta ajiye masa cike da girmamawa “yanzu kuma sai me sir ?zaki iya wucewa “amman sir kayi wani abu da sauri dan gobe ne zata fara aiki da alico insurance,karki damu kota fara aiki dasu zasu koreta ta juya ta fice ta barshi tana jin dadi da kuma jinjinawa karfin ikonsa gbdy mutun ne shi da baya wasa da kasuwancinsa da kuma karfin ikonsa.” 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 65

Numfashi ya sauke ya koma ya samu guri ya zauna a kan kujera yana jujjuya jikinsa gabansa na wani irin bugawa da karfin gaske haka nan yake jin zuciyarsa na matukar jin tsoron abinda zai faru yayinda a hankali maganganunta na jiya da sukai waya da some ya dinga dawo masa daki daki " na tsaya naji nayi miki me ?me ma kuka d'aukeni shasha wacce bata san ciwon kanta ba ?"kunsan zaku bukaceni me yasa kuka wulakan tani?"ya runtse idanunshi gam yana jin matsamanancin tashin hankali "wannan yarinyar fa da gani rigimammeya ce ."ya furta a fili qirjinsa na lugud'en bugu alokacin da maganarta ta sake yi masa kuwa acikin kunnuwansa da zuciyarsa ".sorry for what?, wallahi ko duk duniya za'a bani a wannan kamfanin babu ni babu wannan kamfanin har abada "shi wannan mutumin a wajenki yake da mahimanci amman a wurin maryama zero ne ,dan haka tun wuri ku nemi wata amman ni har abada bazan sake dawowa AGC company ba ".

Wani irin zufa ne ya shiga tsatsafo masa akan hancinsa da ilahirin jikinsa ,ahankali ya kai hannu ya lalubo wayarsa ya soma binciken unguwar da take domin dai yana bukatar yaga yanayin tsarin unguwarsu "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ya furta a fili yana mai sake tsurawa wayarsa do tagumi yayi da hannu d'aya yana tunani irin rayuwar da mutun zai yi a irin wannan bazar unguwar numfashi ya janyo da kyar ya sauke sannan ya soma neman layin mb yana d'agawa yace "kazo yanzu yanzu ina AGC yana gama fad'ar haka yayi discounting din kiran ya kira salim da ammar."yayi baya da kujerar da yake zaune yana ciza lip's dinsa da qarfi babu abinda yake gani acikin kwayar idanunshi sai kyakkyawar fuskarta mai mugun kyaun gaske da yanayin jikinta tana rayuwa acikin unguwarsu imagenation dinta kawai yake tun daga qarancin shekarunta har zuwa sanda ya fara daura kwayar idanunshi akanta ,yanayin tsayinta da dogon hancinta shine yafi komai fito da ainihin sahihin kyawunta da Allah yayi mata ya numfasa yana sake lumshe tsumammun idanunshi "hakika maryama iyayenki sun iya haihuwa tunda suka haifa muradin zuciyar Adam .”yana cikin wannan halin sai gasu ammar sun bayyana a gabansa ."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull