Mar'adams book 4 - Chapter 14
Mar'adams book 4 Chapter 14: Mar'adams book 4 Chapter 14. "Sweetheart ina son ki fahimci wani abu shi so wani yanayi ne na halitta da'ake jin shi acikin…
3,292 words
"Sweetheart ina son ki fahimci wani abu shi so wani yanayi ne na halitta da'ake jin shi acikin zuciya wanda yake sa tsawon rayuwa sannan yake sa mutun cikin nishad'i da farinciki wallahi sweetheart Ina matukar son maryama da dukkan nin zuciyata da raina,ina son tafiyar da rayuwata da maryama ne kawai mu rayu tare daita har abada saboda Ina matukar sonta irin son da bazan iya rabashi da kowacce irin mace ba a duniya ,shiyasa ma tun farko kika ga na kasa gabatar miki da kowace mace amatsayin matar aurena. da kin barni tun farko to da yanzu zukatanku suna cikin natsuwa da kwanciyar hankali domin da ba'ayi auren danasani ba dan wallahi da ban had'u da maryama ba to kuwa zan karar da rayuwata ne ni kad'ai batare da kowace mace ba saboda Itace farincikina itace halittar da zuciya da ruhina da gangar jikina suke marukar so."
runtse idanu mami tayi k'irjinta yana wani irin bugawa saboda d'acin maganarsa dan jin maganar tayi tamkar fad'ar mutuwar wani daga cikin ahlinta,sai dai tai shiru tana saurronsa har kusan minti goma ta kasa furta masa komai dan bakinciki da kalamansa suka jefata ciki zata iya cewa tunda take ba'a ta'ba fad'a mata magana mai d'acin wannan ba ,cikin yanayi na kuka mami take kallonsa ".bil hakki abinda yake fad'a mata a yanzu haka maganar take dan yanayinsa kad'ai ya tabbatar mata maganar daga k'asan zuciyarsa ta fito. kenan idan yafi son yarinyar akan kowace mace a duniya kenan har daita kenan tunda har zai iya kallonta ya fad'a mata cewar yana sonta da zuciya da ranshi. "inna lillahi!" hakan yasa mami ta cigaba da kukan bakinciki da take ita kam wannan son bai mata rana ba .gabad'aya sai taji abun ya had'e mata ga matsalar maryam ga kuma wannan zazzafar son da yake wa wannan maryama ."
muryarta cike da matsanancin tashin hankali tace"adamcy har zaka iya bud'e baki ka fad'a min cewar kana sonta da zuciya da ranka ?"kenan ma kafi sonta dani mahaifiyrka ?"tun da har ka iya bud'e baki ka fad'a min haka nasan da gaske ne". ta fad'a tana janye jikinta daga garesa byn ta d'auke hawayen idanunta ."runtse idanunshi yayi yana mai sake kamo hannuwanta cikin nashi yana jin rashin dad'in jin maganar mami ta yaya ma zata had'a kanta da maryama !"ai ita bata cikin misalinsa dan soyayyarta dabam ce." ahankali sautin muryarsa ta fito tamkar mai koyon magana "dan girman Allah sweetheart karki min haka ta yaya ma kike irin wannan tunanin ,kina ganin akwai macen da zan so sama dake ne ?"kefa mahaifiya ce Ina magana ne akan wata mace dabam "naji amman ita din wacece da har ta cancaci irin wannan son daga gareka ?"
Shiru yayi tare da bud'e idanun shi akanta bai san yaushe ne sweetheart dinsa ta dawo haka ba ita din macece da bata fiyye shiga abinda babu ruwanta ba koda kuwa akan ya'yanta ne bata matsa masu akan ra'ayinsu most especially shi amman me yasa a yanzu take son canzawa asalin halinta zuwa wani hali dabam?"kuma ma idan zata canza sai da abu yazo kanshi !"shi fa sai dai tayi hakuri idan dai akan maryama ne ba zai ki bin umarninta ba sannan bazai ki son farincikin sa ba, ko yanzu tace a maida aurensa da wancan yarinyar a shirye yake da ya sake cika mata burinta amman fa batun na son ne babu zai yarda yayi rayuwa daita amatsayin matar kaddara." "ai ni kam nasan bakincikika ne zai yi sanadin mutuwata adamcy dan gabad'aya ka haukace akan soyayya,ka canza daga d'abiarka kamar wanda aka yiwa wani abu".tayi maganar tana dubansa sai dai wannan karon cike da tausayawa ne."
numfashi ya sauke yana dubanta zuciyarsa na wani irin bugawa da karfi shi ba abinda yayi tsamanin kenan daga gareta ba, abinda yayi tsam mani dabam abinda ya iske dabam har yanzu ko fatan alkhairi bata masa ba a auren nan da yayi abinda ya kamata shine farkon abinda yayi expecting daga gareta dasu shahida da khadija amman gabad'ayansu babu wanda yayi masa fatan alkhairi sai ma saka shi damuwa da take son yi ."tun sanda ya fara magana har zuwa sanda yayi shiru yana kallonta kuka mami take yayi duk yadda zai yi ya tsaida kukan abun ya fassaka dan bai son kukanta jin kukan yake har tsakiyar kanshi ."cikin tausasa muryar da sigar rarrashi yace "sweetheart kiyi shiru haka wannan kukan da kike yana ta'ba min zuciyata Ina jin kamar nima nayi kuka ne." hannu tasa ta goge hawayenta "kiyi hakuri sweetheart ban san yaya zanyi da soyayyar maryama bane amamn wallahi kinsan Ina sonki fiyye da son da nake mata ."
a sanyaye tace "baka sona adamcy tunda ka kasa son farincikina ".murmushi takaici yayi kafin yace "wannan rana ta yau din nan ta kasance ranar farinciki ce agareni bayan tsawon lokacin dana d'auka Ina gurzuwa da tarin damuwa iri iri murna tare da taya farinciki ya kamata kowa ya tayani acikinku ,nayi expecting komai ya wuce a zuciyarki tunda mun rigada mun gama da mgnr wannan yarinyar, sweetheart ya dace ki sauke wannan nauyin akanki a yanzu tayani murna da wannan auren ya kamata kiyi ,mami ta kwa'be baki tana kawar da fuskarta ."a wasu lukutan bana gane miki sweetheart ni ne bakya so ko kuwa farincikina na ne bakya so ?".
Shiru tayi tana sauraronsa "karki manta akan mafarkin yarinyar nan babu kalar damuwar da ban shiga ba, babu irin wahalar da ban shiga ba sam ban d'auka bayyanarta har zuwa mallakarta zai zama damuwa a zuciyarki ba amman babu komai, na gode sosai ba dai kuna son maidani marayan karfi da yaji ba?" gabad'aya duk kun juya min baya akan yarinyar nan maryam ?" "Idan bazaku tayani murna ba ni zan taya kaina zan kuma godewa Allah daya nuna min wannan ranar mai cike da tarin farinciki mara misaltuwa congratulations to me."ya k'arasa maganar cike da rauni yana k'ok'arin kikewa tsaye ."ai nan take mami taji ilahirin jikinta yayi sanyi taji tausayin d'anta ya mamayeta, taji hukuncin data d'auka akanshi yayi tsauri sai dai bata jin zata sausauta masa yayi rayuwar cikin farinciki yayinda d'iyar d'anuwanta take rayuwar kunci ."
tayi biris dashi taki cewa komai har sanda ya mike tsaye ya nufi kofar fita tana zaune tana kallon bayansa cike matsanancin tausayawa tasan bancin abinda yake tsakaninsa da maryam da babu shakka zata nunawa wannan auren gata babu wanda zai kaita murna da farinciki dashi duk da tasan har abada ba zata ta'ba dawo da burbishin soyayyar maryama data fara samun kar'buwa acikin zuciyarta ba sakamakon tozarcin da yayi mata a gaban d'anuwanta ."Jiki a sanyaye adamcy ya fito zuwa parlour'n idanunshi ya sauka akan yan'uwansa suna kallonsa kowace fuskarta a had'e banda zabiba wacce alamunta ya muna tana son masa magana sai dai yanayinta ya nuna masa tana jin tsoro.kallonsu ya cigaba da yi gabad'aya ya kasa samun taya murna daga garesu atakaice dai sun had'e masa kai lallai kuwa zai yi dasu ."
"yadda suka nuna masa shima haka zai masu zai ciresu acikin rayuwarsa zai yi rayuwarsa babu su zai yi rayuwarsa daga sweetheart dinsa sai mrym da ya'yan da zata haifa masa daman ba tun yau ya saba da rayuwar rashin d'an uwa namiji ba domin yasan da ace yana da yaya ko kani namiji da bazai ta'ba juya masa baya akan wannan matsalar ba ." shi a yanzu har gara su sultan akan su, domin duk tswon lokacin da'aka d'auka suna nuna masa kiyayya da rashin jituwar dake tsakaninsa da baba karamin yau dasu aka d'aura masa aure ."inda hajiya zulf'au ta kallesa tsanake sannan tace "Adam har ka fito ?"kan shi kawai ya gyad'a mata alamun "eh!" tare da kai hannu yayi baya da hular kanshi ya shafa goshinsa hajiya zulfa'u ta kalli su aunty shahida taga duk sun yi masa dip sunyi wani iri kuma tasan duk wanan shirun bai wuce na auren yayi bane tunda mahai fiyarsu bata so dole suma bazasu so auren ba amman duk da haka bai dace su zare kansu cikin lamarin auren ba ."
magana take son tayi dasu gabad'ayansu sai dai taga yanayin adamcy din kamar yana cikin tsananin damuwa tana kallonsa ya fara taku a natse ya nufi kofar fita ta yunkura ta biyosa tare da kiran sunansa ,adaidai bakin kofa yaja ya tsaya batare daya juyo ba yana jin zallar damuwa acikin ranshi ta tsaya a kusa dashi tana cewa "ka natsu ka kwnatar da hankalinka komai mai wuce wa ne ,"bana son ka tsani 'yanuwnaka duk da sunyi maka ba daidai ba, lamarin mahaifiyarka zaka duba su ya'ya mata ne wad'an da a kasani da Taya iyayensu kishi amman da sannu komai zai wuce barin ma idan yarinyar tana da kwantar da kai ".numfashi kawai ya sauke batare da yace uffan ba duk da maganar yake son yi sai dai ya tsinci kanshi da kasa yi ."
"zuwa karfe nawa ne zaaje d'auko surukartawa dan ina son na d'an kwanta kad'an kafin lokacin "my aunty ki kwanta abunki ki huta sai zuwa karfe uku saboda minti talatin zuwa awa d'aya zata kai ku "okay shikenan bari naje na d'an kwanta kafin azahar na tashi in sha allahu."tana gama fad'ar haka ta juya shi kuma ya k'arasa fice wa ya koma cikin abokinsa aka cigaba nishadin kowa ka gani fuskarsa cike take da matsanancin farinciki taya adamcy murna ,sai dai shi adamcy karara fuskrsa ta nuna yanayi na damuwa duk da daman kusan yanayin fuskarsa kenan amman kuma duk da haka akwai masu iya ganewa dan kallo d'aya amar yayi masa ya fahimta dan yana hankalce dashi da idanunshi ,ya d'an matso kusa dashi tare da yin kasa da murya ta yadda babu mai jin abinda zai fad'a yace ya kamata ka kawar da duk wata damuwa da kake ciki ka bayyana farincikinka " da kyar ya janyo numfashi ya sauke yana mai runtse idanunshi da karfi alokcin da yake jin tsokar zuciyarsa tana tattarewa waje d'aya ,acikin ranshi yake hango gagarumim bala'i da za'ayi dashi idan wani acikin yan'uwnasa yayi kokarin taka masa mata ko ci mata mutunci."
Bayan kamar awa bbiyu ya mike yace yana zuwa ya sake komawa bangaren mami kai tsaye ya haye samansa tare da cire hullar kanshi sannan ya rage kayan jikinsa ya zauna yana neman layin maryama domin yaji lafiyarta ,ya kira layin ya Kai sau uku sai dai ga dukkanin alamun wayar akarshe take dan switch off ake masa ya zauna shiru tare da kamo lip's dinsa yana cizawa ahankali ahankali yana tunanin ko ya kira umma ita dai ya samu kiran ya shiga sai dai bata d'aga ba zame wa yayi yana tunani ,a yau din ya kamata ace yana cikin farinciki sai dai gabad'aya ya rasa meke masa dadi ko dan yanayin da weetheart dinsa ta nuna masa ne bai sani ba duk yadad kiran amar yake shigo wayarsa bai d'aga ba dan yana bukatar zama shiru na wani lokaci ko zai samu kanshi ."
Sai bayan azahar ya samu kansa yayi wanka yayi sallah ya shirya kansa cikin wata hadaddiyar shadda milk colour ya d'aura hulla dark blue ya d'aura agaogo a tsintsiyar hannunsa tare da fesa turare ya d'auki wayarsa d'aya,yana k'ok'arin fitowa daga parlour'nsa yaji alamun za'a shigo Dan haka ya d'an ja baya kad'an yana jiran yaga Wanda zai shigo gabad'aya yanuwansa ya gani d'aya bayan d'aya suna shigo da mamaki yake kallonsu ransa a matukar 'bace yace "lafiya me kukeyi anan ?"yayi masu tamabayar yana hura hanci "kayi hakuri da yan'uwnaka adam karka ga laifinsu idan akwai mai lafiya to aunty ce "hajiya zulfa'u ta fad'a tana k'arasa shigowa d'akin ta tsaya a kusa dashi tana dubansa ."
"My aunty wad'an nan ba yan'uwana bane suyi rayuwarsu nayi tawa ni tuni na ciresu acikin jerin yan'uwana "ya fad'a yana watsa masu harara tace "aa adam karka ce haka kai dai kayi hakuri kawai komai ya wuce mu dinga yiwa kanmu uzuri duniyar nan ma meye acikinta "?babu komai fa ,dole kowa sai yayiwa d'anuwansa uzuri sannna a zauna lafiya"yaya dan Allah kayi hakuri ka yafe mana munyi kuskuren kuma muna nadamar abinda mukayi kuma muna tayaka murna wannan auren Allah ya sanya alkhairi ya kuma baku zaman lafiya "inji cewar zabiba numfashi ya sauke yana kallonsu d'aya bayan d'aya acikinsu ita kad'ai ce yanayinta ya nuna nadama amamn sauran kana kallonsu kasan dole akayi masu "duk da khadija da shahida su girme maka amman kasancewarsu mata ne dole su kasance a kasanka kayi hakuri komai ya wuce ."
Numfashi ya sauke ya so ya fad'a mata duk abinda suka shirya akanshi da maryama amman ya danne domin yana son ganin gudun ruwansu sai da hajiya zulfa'u ta ta'ba aunty khadija sannan tace "Allah yasanya alkhairi ".ta fad'a atakaice taja bakinta ta tsuke ,haka ma aunty shahida sannan nana hauwa'u wacce yake ganin kusan tafi kowa d'aukar zafi a zuwan k'awarta ce maryam yaji kamar ya gaura mata mari sannan yaji baasin kunbure kunburen da take masa "gashin nan gabad'ayansu sun baka hakuri ka yafe masu "shiru yayi yaki cewa uffan dan bai ji zai hakura, kuma Allah yasani bai so zuwansu a yanzu ba domin yana son ya samu damar keta masu rashin mutunci ne dan duk rashin mutuncin da suke ji yafi su iyata "kayi shiru adam suci darajata aunty khadija tayi masa wani irin mummunar kallo tana ayyana irin haukan da zai yi idan maganar rabuwarsa da wacan tsinan niyar yarinyar yazo ."
shima nan take ya maida mata da irin kallon da tai masa yana furzar da iska "suci daraajata adamcy muryar hajiya zulfa'u ya sake shiga cikin kunnuwansa "shikenan ya wuce!" to na gode Allah yayi maka albarka Allah kuma ya sanya albarka a aurenka yace "ameen !"adaidai lokacin da aunty khadija ta fice daga parlour'n tana cika tana batsewa tana fita aunty Shahida ta biyo bayanta tare da nana hauwa'u d'akin ya saura daga hajiya zulfa'u sai zabiba da adamcy tsaye parlour'n yayi shiru baka Jin motsin komai sai na ac dake aikin acikinsa ya kalli zabiba dake tsaye yaga duk a tsorace take sai dai bai ce mata komai ba "lokaci na sake karatowa saura awa d'aya bari naje na k'arasa shirina zabiba tace "my aunty zan biku d'auko amarya "to shikenan zabiba hakan ma zai sake goge maku laifinku a wajen adam tayi maganar tana murmushi shi dai bai ce uhm ba bare uhm uhm har suka bar parlour'n."
Kai tsaye ya fito ya samu su amar suna zauen ga plate din abinci nan a gabansu kusa da amar ya zauna yana kiran sunan Allah, hannu yasa ya dafe kanshi dashi yana fadin."bahaushe ya ce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi"amar yayi murmushi kawai yana kallonsa "wallahi a gajiye nake sosai gashi bana samun bacci isasshe spoon din da ke cike da abinci mb ya kai bakinsa yana taunawa ya furta." Ka kusan sauke gajiyarka dan aikin ne agaban wannan yarinyar sai tayi juriya dan akwai tarin kalubale wanda ba kowa ne zai gane ba sai wanda ya san yadda al'amarin yake ko da yake ai tasan komai bazata baka wahala ba "duk da haka ni dai ina tausaya maryama wallahi dan wannna namjin gaske ne zaki ne akanta idan ya cafketa sai Allah da malaman gari "inji cewar amar aiko suka sa dariya "tsaki adamcy yaja yayi kamar bai san abinda suke nufi ba ."
Da misalin karfe uku saura mintuna talatin ya kira layin umma inda yayi sa'ar ta d'aga yake sheida mata wad'an da zasu zo d'aukar maryama zasu taso yanzu sai dai cikin tashin hankali take fad'a masa "jikin maryama ya sake rikicewa sosai yanzu na isketa kwance tana fidda numfashi sama sama amman nasa akira doctor dan babu abinda jikinta yake fitarwa sai hucin zafi ". cikin wata irin wahalalliya murya wanda ke fallasa sirrin zuciya da gangar jiki ya furta" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun..!"al'amarin daya janyo hankalinsu amar da mb har ma da sauran abokansa da suke tare dashi kenan suka tsura masa idanu gabad'ayansu suna kallonsa suna jiran suji abinda zai fad'a bayan wannan kalmar sai dai gani sukai ya d'auke kanshi akan su dan baya son suyi masa tamabayar da yake hangowa acikin kwayar idanunsu ."
ganin haka yasa suka cigaba da abinda suke shi kuwa acan kasan zuciyarsa babu abinda yake maimaitawa sai "ya Allah ka taimakeni akan yarinyar nan da abinda ke shirin faruwa mikewa tsaye yayi kunnensa manne da wayar ya kasa cirewa yayinda k'irjinsa yayi masa bala'in nauyi yana tsananta bugawa a natse ya cire wayar yana juya ta a tafin hannunsa yana k'okarin nemawa kanshi mafuta akarshe dai ya yanke shawarar zuwa gidan batare da sanin kowa ba ya shiga motarsa baka wacce take da bakin glas ya fita ta kofar baya."
Acan gidansu maryama kuwa a rude umma ta mike ta nufi part din aunty ta sanar mata halin da maryama take ciki tare suka dawo gurinta da wasu kawayen aunty guda biyu wanda zuwa yanzu jikin maryama ya tsananta zafi fiyye dana safiya tare da karkarwa , ban da salati bbu abinda umma da aunty keyi da sauri suka karasa kusa da maryama suka sakata a tsakiyar su tare da riko hannuta" mai zan gani haka ni biliksu "?maryama kina son ki kashe kanki ne Ko yaya ?aunty ta fad'a hawaye na wanke mata fuska " kinsa fa ke kad'ai garemu maryama a duk duniyan nan, km ke kad'ai ke debe ma mahaifiyr ki kewar yar'uwanata , ba ita kad'ai ba ko ni bazan iya jurar rashinki ba maryama dan Allah ki tausayi mana yau fa ranar farinciki ne a garemu karki bari ya zamo ranar bakincikin mu ?"tana gama magana sai hawaye shar shar daga idanun umma ,"
sosai aunty da umma ke zubda kwallar tausayin kansu dana diyarsu ganin yadda duk ta fita haiyacinta cikin lokaci d'aya umma tace"bilkisu kama min ita dan Allah su aunty suka kama maryama suka fito zuwa parlour daita "kai tsaye umma tace subai'a ta sake zuwa ta kira doctor sannan ta sake kira adamcy yace mata gashin nan zuwa yana kan hanya sannan tace ayi d'akin sadam da maryama saboda hayaniyar yan'uwa tafiyar minti talatin ce ta kawosa unguwarsu adaidai lokacin da'aka zo da doctor yana zuwa ya soma duddubata tare da bata taimakon gaggawa umma ta dubi doctor hankalinta a tashe tace " doctor me ke damunta ne ?doctor yace " gasky damuwace tayi mata yawa idan bata bi ahankali ba hawan jini zai iya jamata dan zuciyarta na bugawa very fast a yanzu "amman inshallahu idan ta kwantar da hankalinta ta cire damuwa zata dawo daidai ."
Agaugauce adamcy ya shigo yana shigowa d'akin mutane suka d'an ragu har aunty ,sanyayyen kamshin turarensa ta soma juyowa mai matukar sanyi da kwantar da ahankali ta d'an lumshe idanunta duk da doctor na tsaye akanta amman tasan shine ya shigo ,aranta tace "sarkin naci sai daya zo "ita wallahi gidansu ne bata son zuwa bare taga fuskar mahaifiyarsa, ita da za'a fasa kaita gidansu Allah da zata samu natsuwa d'aga balain da take hangowa kanta ."ahankali ya karaso kusa da umma idanunshi na kan fuskar maryama dake kwance ya tsaya yana tamabayar umma yana yin jikin nata taja numfashi sannan tace da sauki zamu ce dan baka ji yadda jikinta ya dau zafi ba kamar garwashin wuta ."idanunshi ya sake tsura mata tana kwance akan bed din sadam an lullubeta da bargo wanda yaji aransa bangon rufarsa ne .shr yayi tare da zuba mata tsumammun idanun shi yana jin wani zallar kishi na taso masa tun daga tsakitar kanshi har zuwa yatsun kafafunsa "kenna da yace ta bar d'akin ki tayi "shi dai ya shiga uku Allah ya had'a shi da gamonsa yarinya bata jin maganarsa haka ."