Kenza eBookz

Mar'adams book 4 - Chapter 2

Mar'adams book 4 - Chapter 2

Mar'adams book 4 Chapter 2: Mar'adams book 4 Chapter 2. jikinta na karkarwa"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" ta shiga furtawa"yau kwanaki biyar kenan…

3,353 words

jikinta na karkarwa"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" ta shiga furtawa"yau kwanaki biyar kenan ban saka shi acikin kwayar idanuna ba sannan bai kirani ba abinda bai ta'ba faruwa ba kenan duk yadda zai yi fushi tabbass zai nemi inda nake ,ki sani duk wannan abun ya faru ne saboda ke km ya bar gida ne saboda ke dan haka kiyi duk abinda zakiyi d'ana ya dawo gida kuma a yau din nan ."cikin qarfin hali maryama tace "to mumy in sha allahu kiyi hakuri numbobinsa basa zuwa nima nayi kwana biyar bamu yi waya ba dashi sai d'azu ya kirani " ta fad'a cikin tsananin firgici da sake shiga tashin hankalin "dan Allah kiyi hakuri mumy ?"nace kin min laifi ne ?!" maryama ta girgiza mata Kai da sauri kamar tana gabanta tace "Im sorry ma!" "d'ana ya dawo gida kuma a yau din nan shine abinda nake da bukata nan take maryama ta d'aura hannunwanta duka bisa kanta tare da juyowa bayanta cak ta tsaya cikin wani irin sabuwar gigita sakamakon ganin mr ata tsaye datayi a bayanta rungume da hannunwansa duka a k'irji yana kallonta hannunta ta kai da sauri ta murza idanuwanta tana son ta sharewa kanta tamtamar shi ne tsye agabanta ko kuwa gizo ne?" sai dai koda ta cire hannuwanta a idanuwanta shi din ne tsaye idanunshi kyam a kanta yana kallonta from head to toe ."

tsurawa juna idanu sukayi yana tsaye har lokacin rungume da hannuwansa a k'irji yayi kyau sosai cikin kanana kaya riga da wondo duk bakeke rigar mai gajeren hannu ce idanunshi na manne da farin glass dinsa na kaida sai dai ya d'an rame wanda ke nuna alamun yana cikin damuwa bata san tayi kewarsa na tsawon kwanakin ba sai da ta ganshi tsaye a gabanta ,gabad'aya ma mantawa tayi da halin damuwar da mami ta sakata ciki taji Ina ma zata iya data k'arasa ta rungumeshi abinda ke cikin ranta shine acikin aranshi dan shi tuni ya ware mata hannunwa nsa alamun tazo garesa,ahankali ta soma girgiza masa kai alamun bazata iya aikata hakan ba dan da zata iya wallahi da babu abinda zai hana bata isa garesa ta rungume sa tayi kuka a kirjinsa ba dan ahalin da take ciki yanzu hawaye ne cike a idanunta ." ahankali ya karaso inda take tsaye tamkar an dasata ya fixgota zuwa jikinsa ya rungumeta tsam a faffadan k'irjinsa yana sauke wani bayanannen ajiyar zuciya "ga abinda ya kamata kiyi nan ba kuka ba" ya fad'a yana sake matseta gam ajikinsa ta d'an saki kara mara sauti "washhh!"karka 'ballani mana,kema kin san bazan ta'ba ballaki ba ,idan na ballaki wa zan runguma?" .

mami ta runtse idanunta da sauri zufa na karyo mata ta koina ajikinta dan da furucin adamcy da na maryama babu bambamci dan hakan ya nuna mata alamun suna rungume da juna ne ."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yaushe adamcy ya dawo haka ?" daman adamcy zai iya rayuwa ko babu ita ?"a she zai iya fifita mace akanta? a she zai iya d'aukar kwanaki bai ganta ba ya zauna lafiya alhalin ba wata kasar yaje ba "? gashi ita ta rasa kwanciyarta hankali akanshi amman shi babu abinda ya damesa rayuwarsa ma yake da abinda tace bata so, kenan idan ma mutuwa zatayi sai dai ta mutu bazai bi umarninta ba ?" mami na can cikin matsanancin tashin hankali yayinda adamcy'nta ya kamo face din maryama yana kallo "I miss you badly!" tare da kai mata kiss sannna ya d'an zareta ajikinsa yana kallonta sanye da rigar jikinta wacce ta nuna tsayuwar brest dinta dan har kan nipples dinta yana gani ." da sauri ta kai damtsen hannunta ta kare inda yake kallo ,yana kokarin sake maidata jikinsa tace "dan malam sakar min jiki haka babu damar kaga mutun shikenan "me kike son nayi ?da zarar na ganki nake mance komai ban ta'ba jin Ina Allah Allah na mallaki wani abu ba kamar yadda nake son na mallakeki laifi ne dan na kalleki?".

"Dan Allah mu ajiye wannan maganar ba girmanka bane yanzu dai ka fad'a min ina kaje "?me ma yasa zaka bar gida kai ba yaro ba ?"tayi masa tambayr tana harararsa tare da kai hannu zata d'auki mayafin umma dake ajiye a kasa ta rufe jikinta dan ta lura da yadda ya tsurawa qirjinta idanu kamar wani tsohon maye yayi saurin riko hannunta cikin nashi yana cewa "no !"I don't understand no sir ?"dan Allah ka bari na rufe jikina mana "no !! maryama karki rufe ki bar shi haka babu abinda zan masu "I'm not comfortable "an so cinyeki zanyi !ya fad'a yana canza face "bance zaka cinyeni ba amman muddin kana son na cigaba da tsayuwa anan sai na rufe jikina".tana gama fad'ar haka ya miko mata mayafin tare da yi mata kallon nan nashi na gefen ido mai rikita mata lissafi yana cewa "banga abun wani boye wa ba."taji abinda yace sarai amman ta share ta cigaba da magana cikin sanyayyiyar muryarta"me yasa zaka bar gida "?bai yi mamaki jin tambayarta ba dan yaga sakon ammar shine ma dalilin zuwansa dan yasa lallai sweetheart zata nemeta "sweetheart dinka ta kira ni yanzu, dan Allah ka koma gida ko dan kwanci yar hankalin mahaifiyrka ".

saurin matsota yayi sosai yana kokarin kamo hannunta taja baya da sauri tana cewa "no sir karka ta'bani , na rasa me yasa ka kasa gane banason kana ta'bani "karya ne maryama kina so mana "ya fad'a yana lasar lip's dinsa na kasa "Allah banaso tayi maganar cike da shagwaba kamar zatayi kuka .mami dake rike da waya tace"yau ga karuwanci anya kuwa yarinyar nan ta bar adamcy haka ?""muga wayar ya fad'a yana miko mata tafin hannunsa ta mike masa wayar tana sake ja baya dan tasan halinsa bakaramin aikinsa bane ya sake fixgota ya rungumeta "kallon screen din wayar yayi sannnan ya d'ago a natse ya kalleta sakamakon ganin har lokacin mami tana kan layi wanda alamun ya nuna tana sauraronsu ne yasa ta bar wayar batare data katse ba,ya nuna ma maryama fuskar wayar ai ko da sauri ta zaro idanu waje tana d'aura hannuwanta duka a saman kanta . "ya kashe wayar yana cewa "matsalarki kenan maryama saurin rikicewa ,ganina da kikayi ne yasa kika mance tana kan layi ?"ta gyad'a masa kai da sauri tana cewa "na shiga uku nah ni maryama shikenan taji maganga nunmu ,da me zanji daga wannan tashin hankalin sai wannan ".tayi maganar cikin siririyar muryarta tana k'ok'arin durkushewa kasa yayi saurin rikota zuwa jikinsa ."

kuka ta fashe dashi ji tayi kunyar duk duniya ta kamata wani irin fassara mahaifiyarsa zata mata .?" gabad'aya ta rasa natsuwarta ji take kamar zaciyarta zata buga kokarin zare jikinta take ajikinsa ya sake matseta yana cewa "ki natsu mana bai zama lallai taji abinda muka fad'a ba ?"ya fad'a domin ya kwantar mata da hankali dan ji kam yasan sweetheart taji wasu daga cikin maganarsu.hawaye take zubar sosai "da wahala bataji ba shikenan ka sake ja min wata tsana a wajen mahaifiyrka daman bata son ka aureni yanzu ga hujjar da zata sake tsanar auren " Ya d'an lashi lip's dinsa na kasa kad'an yace "ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru sannna babu abinda zai hana aurenmu muddin Ina raye baki da wani miji bayan ni ." wani sassanyan numfashi ta sauke ta gyara tsayuwarta ajikinsa dan k'afafuwanta sun fara gaza d'aukarta,shima numfashi ya sauke tare da kai tafin hannunsa ya share mata hawaye ya sake maida kacokan hankalinsa gareta, ita kam ta shiga uku taga ta kanta yanzu haka rayuwa zatai ta zuwa mata da kalu bali ?"bata fita acikin wani kalu balin ba ta sake shiga wani ."

"wai meye haka ne ?"yayi mgnr cikin muryarsa mai tsananin kashe sansar jiki ,shiru tayi taki yin magana sai kwalla take zubarwa a natse ya cigaba da magana cikin kasalalliyar murya "idan baki daina kukan nan ba zan tafi na barki kuma bazaki sake ganina acikin sauki ba "wai ya kake son nayi da rayuwata ?".dole fa na damu tayi maganar wasu hawaye na zubo mata "okay shikenan ki cigaba da kukan idan zai miki maganin matsalarki ni zan wuce ".yana gama fad'ar haka taga ya zareta ajikinsa ya zaro wasu document abayan aljihunsa ya kamo hannunta ya damkasu ciki "takardun gidansu umma ne zan so su tare acikinsa kafin qarshen satin nan amamn bazan masu dole ba duk lokacin da suka shirya ki min magana zan turo a d'aukesu ya k'arasa maganar tare da juyawa yana taku cikin isa da nuna rashin damuwa da abinda ya faru ."bayansa tabi da kallo tana jin kamar tace masa ya dawo kar ya tafi dan tasan halinsa tunda ya furta idan ya wuce bazata sake ganinsa cikin sauki ba tasan haka ne zai faru ,mutumin daya kauracewa mahaifiyarsa ai kowa ma zai iya kauracewa ba damuwa zai yi ba ,tana tsaye cikin tsananin damuwa da fad'uwar gaba har sai data daina ganinsa ".

bata iya cigaba da aikinta ba ta dafe goshinta da document din daya damk'amata tana adduar Allah yasa mahaifiyarsa bataji hirarsu ba domin ita shine damuwarta ba kauracewarsa ba ."ahankali ta koma ta jigina jikinta da bango wajen tana rike da kugunta da hannu d'aya still rike da takardar yayinda d'ayan hannun ta jefa shi acikin bakinta tana ciza wa alamun tunani ,a nan umma tazo ta sameta duk ta firgice "Ina adamun yake ko ya wuce ne"?da sauri maryama ta dawo haiyacinta tana d'auke hawayenta tare da d'an tsotsa kanta tace"eh umma ya wuce amman yace zai dawo zuwa anjima ."ta tsinci kanta da girbawa umma karya "kai Alhamdulillah wallahi ba kiji irin farinciki da naji ba dana gansa, Allah ya sani bana son mu rasa shi Ina son kema kiyi aurenki ki zauna a gidan mijinki lafiya kamar kowace mace da dadi da babu dadi kiyi hakuri bare khairan in sha allahu adamcy na matukar sonki ."

"maryama ta kalli umma bata san yadda umma zataji ba a ranar da zataji cewar auren contract tayi dashi dan dole dai sai tasani idan lokacin mutuwar auren yazo "maza ki karasa aikinki kafin ya dawo ko kuma ki barshi na karasa "a'a umma bari na karasa ai nama kusan gamawa yazo, maryama ta mikawa umma takardun hannunta "takardun gidan daya baku ne yace "duk lokacin da kuka shirya tarewa ayi masa magana zai turo azo a d'auke ku umma ta kar'ba tana washe baki ita kuma maryama ta duka domin cigaba da aikinta umma tace "kai masha Allah Allah mun gode maka da wannna niimar da kayi mana umma tayita kallon takardun tana santin gidan da bata gani ba kafin daga baya ta ajiye a gefe tasa hannu cikin d'ayan bucket din tana d'auraye kaya tana shanya tana wa mryama hirar adamcy abinda ta lura dashi tun da batun auren nan ya taso umma bada da wata hira sai tashi bini bini tace adamcy kaza ko ranar auren kaza zatayi atare suka k'arasa aikin maryama ta d'auraye bucket din da tai amafani dasu suka shige ciki sai dai ita kam duk arikice take bata da wani kuzuri ."

Maryama tana zaune cikin zullumi sai ga subai'a ta kawo mata ziyara "cike da murna ta tarbeta suka rungume juna maryama tace "subai'a kinga yadda kika dawo kuwa ?ya na dawo "kin yi kiba kinyi kyau ,ke baki ga yadda kikayi fresh ba ?"maryama ta harareta tana nuna mata wajen zama "ana kai ina ke ta kaya Allah dai ya rufa asiri kawai "inji cewar maryama ,ki zauna bari naje na kawo miki ruwa subai'a ta samu waje ta zauna tana tambayr maryama umma daga inda take tsaye gaban fridge tace "tana cikin d'akinta tana lazimi ,ta dawo hannunta rike da ruwa da lemu ta ajiye mata kana ta zauna suka fara hira k'awata kisan abinda ya kawoni?"maryama ta girgiza mata Kai "tun bayan da'aka ganki nayita son nazo muyi magana akan batun aurenki da alhji mansor sai dai ban samu time ba saboda yanayin aikinmu to jiya na d'auki hutu saboda Ina son zan biya kudin zuwa umara cikin wannnn sati "tun kafin ta gama magana maryama ta fad'a da fuskarta da murmushin farinciki tana riko hannun subai'a cikin nata "Kai masa Allah subai'a na tayaki murna Allah yasa ayi ibada kar'babbiya tace ameen k'awata na gode shine nace nazo naji ya'ake ciki idan har zan iya zuwa naje na dawo na sani duk dai sati biyu ne kawai zanyi ".

"kiyi tafiyar ki subai'a dan tuni an fasa wannan auren subai'a ta zaro ido waje tana cewa "me yasa aka fasa kuma matsalar daga Ina ce ?to wannan Karon dai matsalar daga wajena ce Allah dai ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi arayuwarmu ."Ikon Allah amamn mai yasa zaki fasa aurensa maryama a inda yanzu maza suke wuyar samu ko dan kinga kina da saurin samu ne yasa kika fasa ?"Sam ba haka bane subai'a wata matsala ce ta taso "wace matsala ce ki fad'a min ko akwai shawarar da zan baki?wannnan matsalar bazata fad'u ba subai'a domin fad'ar sa kamar sake jefa kaina cikin damuwa ne ni dai idan kinje umara kiyi min addua sosai dan Ina bukace da addua wallahi "ai shikenan daman sai da nayi tunanin bazaki fada min ba kina nan dai da wannna zurfin cikin naki addua kuma in sha allahu zan miki " maryama tai murmushi "tace na gode ."

"K'awata nima fa Ina da damuwa kusan ma abinda yasa zanje umara kenan akwai wanda na kamu da son shi a wajen aiki sai dai wallahi bazan iya fad'a masa cewar Ina son shi ba amman wallahi ina mutuwar son shi zanje na roki Allah idan har alkhairi ne agareni Allah ya bani shi cikin sauki idan babu alkhairi Allah ya musanyamun da wanda yafi shi ." "kai subai'a mutun bai ce yana sonki ba kawai sai ki kamu da son shi ?"wallahi maryama jarabawar data same ni kenan mutumin ya had'u sosai sai dai ayi min nisa da yawa dan ko gaisuwata ma da kyar yake amsawa "fad'a min waye shi a wajen aikin ?"bazan fad'a miki ba domin nasan muddin kikasani zaki shigar da kanki wajen nemo min abinda nake mutuwar so dan nasan muddin kika shiga ciki lallai zan iya samunsa sai dai ina gudun wulakacin da cin mutunci domin matuqar ba namiji ne yace yana son auren mace ba bata ta'ba samun kwanciyar hankali daga garesa ."

Maryama tai shiru k'wak'waluwarta na budewa domin son gano wanda k'awarta take mutuwar so haka a wajen aikinta to waye wanda take da yakinin muddin ta shiga ciki lallai zata iya samunsa ?"me yasa subai'a bazaki fad'a min ko waye ba tunda kina ganin zaki iya samunsa ta hannuna?" aa k'awata bari dai naje nayi addua na dawo muga mai Allah zaiyi sun samu tsawon lokaci suna tautauna kafin daga bisa umma ta fito suka gaisa inda maryama ta sheida mata tafiyar subai'a umma tayi farinciki tai mata addua sannna tace tai mika gaisuwarta ga maiaiki maryama sukai sallama da subai'a har bakin sabon titi rakota sannan ta dawo ." umma tayita zuba idanun dawowar mr ata amamn taji shiru har karfe goma na dare ta kasa hakuri tace "maryama ba kince adamu zai dawo ba ?"maryama tai tsam da ranta kafin tace "haka yace min amman Ina ganin ya canza raayi ne umma ta d'an numfasa "nifa wallahi banason kuna nisa da juna ,daya zo bai ce miki ga ranar da wakilansa zasu zo bane ?"maryama ta girgiza mata Kai alamun bai ce ba "ni kam ayi ayi auren nan ko zan samu natsuwa dan wallahi bani da wata cikikiyar natsuwa, umma dan girman Allah ki kwantar da hankalinki duk abinda kikaga bai zo hannun mutun ba to wallahi Allah ba rabonsa bane "haka ne Allah yasa muji alkhairi ."

Tunda mr ata ya barta bai sake nemanta ko a waya ba haka itama bata nemesa ba har sukai sati d'aya sai dai sakonin tunin da wannan yar uwarsa tasa take mata kullum shine abinda ke jefata cikin zullumi da rashin kwanciyar hankali sai dai kullum sukai chart da subai'a tana maimaita mata tai mata addua ita kuma kullum tana cikin addua" tana zaune shiru tana tunani kwanakin da suka rage mata acikin lokacin da suka bata, sosai tayi zurfi cikin tunanin har k'arfe shida yamamcin ranar ta buga ahankali wayarta ta soma ringing ko data duba mr ata ne ta gani ai bata tsaya bata lokaci ba ta d'aga had'e da sallam "ya amsa mata yana cewa "princess yunwa nake"ta lumshe idanunta sakamakon wani sanyi daya ziyara ilahirin jikinta "kina jina ?" tace "Ina ji me zaka ci "?"Ki dafa min wani abu mai sauki tun safe banci komai ba "me yasa zaka dinga barin kanka da yunwa ?"bani da cikakkiyar natsuwa ne zuwa 7 :30 zan zo "okay sir !"ta fad'a tana jiran ya katse kiran bayan ya katse jollof din kuskus tayi tunanin tayi masa dan shine abinci mafi saukin dafawa dan lokacin ya tafi bare tayi tunanin dafa masa wani Abu dabam ."

ta shiga kitchen ta fara d'auko abubuwan da zatayi amafani dasu cikin kankanin lokaci ta dafa masa kuskus wacce taji koren tattassai da kwakwamba albasa da hanta ta sauke ta zuba masa acikin wata yar madaidaiciyar kula sannan ta rufe sauran wanda umma zata ci dan ita kam murna son ganinsa ma yasa bata Jin zata iya cin komai ta fito ta duba fridge taga akwai sauran nah'nahr da umma tayi ta maida fridge din ta rufe ta shiga d'akin umma ta fad'a mata zuwansa ai ko umma tayi farinciki yayinda maryama ta fito ta shiga wanka tare da dauro alwala ta fito ." Bayan ta fito ta goge jikinta turare kawai ta fesa a ilahirin jikinta ta shirya kanta da wata atamfa light blue mai zanen fulawa blue black kayan sun zauna ajikinta most especially Siket din dan ya fito mata da hips dinta ta gama shiri adaidai lokacin da'aka kira sallah ta d'auki hijab ta zira ta tada sallah bayan ta idar tai addua ta mike ta saka takalmi flat ta d'auko mayafi blue black zata d'aura sai kuma ta fasa dan bata son tana bayyana jikinta ta d'auki hijab Wanda yabi kayanta ta saka ."

Karfe bakwai da rabi saura ta fito parlour'n ta zauna tana tunanin mr ata dake manne acikin zuciyarta bata wani jima da zama ba sai ga kiransa ta daga a natse tana gaishesa "ya amsa yana shafa sumar kanshi tare da yin shiru "zaka iya shigowa ina parlour'n ."Ina kan titin unguwarku "na fito ne ?amman ahankali dan nasan kinyi missing dina sosai "ta harare ta cikin waya tana cewa "inji wa yace maka nayi missing sonka "na gode da harara akayi min Ina jiranki ." numfashi ta sauke sannan ta mike ta shiga d'akin umma ta sanar mata da zuwansa amamn yana bakin titi "ki gaishesa !tace to ta juya ta d'auki jakar data had'a masa abinci ta fito tana tafiya kamar mai tausayin kasa."natse ta karaso bakin titi inda ta hangosa tsaye a jikin motarsa sai kwayar idanunshi na kan hanyar fitowa daga lungunsu ahankali ta cigaba d'aga kafafunta ta karaso ta tsaya a gabansa tana cewa "yallabai bai dace ka tsaya anan ba "inji wa ?"ya fad'a yana bud'e gaban mota ya zauna a mazaunin direba yace bissimillah shigo ."

Take ta fahimci abinda yake nufi maimakon hakan daya bukata sai ta bud'e bayan mota ta ajiye jakar hannunta sannna ta zagaya ta shiga ta zauna ta rufe kofar tana cewa" Ina yini !"madadin ya amasa mata da lafiya sai kawai taji ya kamo hannunta ya sumbata "ina son muyi wata magana dake mai mahimmanci "bissimillah Ina sauraron ka ta fad'a tana kokarin zare hannunta maganar tana bukatar natsuwa wanda ya nuna bai dace ayita anan ba idan baayita anan ba mu karasa gida sai muyi acan ko "gidanku ne kawai ya dacewa ayi magana mai mahimmanci ta lumshe masa idanunta alamun ce "gidana zamu !"bangene gidanka zamu ba yallabai gasky ni dai a'a idan har maganr ta wuce ayita anan ko a gidanmu sai dai a hakura daita ."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull