Mar'adams book 4 - Chapter 3
Mar'adams book 4 Chapter 3: Mar'adams book 4 Chapter 3. "Baki isa ba nace ga abinda zaayi kice aa "yana gama fad'ar haka yaja mota kai tsaye gidansa ya…
3,271 words
"Baki isa ba nace ga abinda zaayi kice aa "yana gama fad'ar haka yaja mota kai tsaye gidansa ya nufa daita suna isa ya zare mata hijab din jikinta "cire ki huta !"tana masa magana ko kallonta bai yi ba shigewa yayi ya barta tsaye a babban parlour'nsa kam kema da jikinta tana kallon komai dake ajiye a parlour'n har da kwalin sigarin da yake sha kusan minti goma sha biyar sai ga shi ya fito da doguwar rigar hutawa ta maza hannunsa rike da cup wanda ke d'auke da lemu ya karaso ya zauna kusa daita yana cewa "kinyi kyau fa ta dan yi musmushin dole bata ce masa komai ba ta gefen idonsa ya kalleta "bani wayarki."me zakayi da wayata "banason tamabya cikin tamabaya kuma nasan kinsan da haka Allah ya huci zuciyarka "bani waayrki kafin komai ya biyo baya .ya fad'a yana mika mata tafin hannunsa "kyawawan yatsun hannunsa tabi da kallo k'irjinta na bugawa da matsanancin k'arfin gaske ."
Mmn Sudais
💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗
BOOK 4
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 2
"Ajiye cup din hannunsa yayi a gefensa ya matso da fuskarsa daf da nata har suna iya shakar numfashin juna ,wani irin tsalle zukatansu yayi ."lokacin d'aya zuciyar kowannensu ya fara lugud'en bugu ,ahankali ya lumshe mata tsuma mmun idanunshi yana cewa "bani mana wani abu zan duba" ya k'arasa maganar tare da bud'e idanunshi fes akanta ."shiru maryama tayi tana kallonsa cikin wani irin yanayi yayinda k'irjinta ke cigaba da bugawar da take "give me the phone.! ya sake bata umarni,bata san lokacin data hararashi tana mai kawar da fuskarta gefe acikin ranata tace "wannan mutumin ya cika damuwa banda neman magana me zai yi da wayata ." ya kai hannunsa ya juyo da fuskarta suka sake fuskantar juna"tsorona kike ji da bazaki maganar a fili ba ?"wata harara tai masa tare da tsuke bakinta matsota yayi sosai "irin wannan baiwar da Allah yayi miki kina saurin nuna min ita a arha kamata yayi sai na dinga biya kafin a nuna min ita saboda wannan irin kallo haka mai k'arawa mai kallonki ganin kyaun fuskarki, har ma yaji sonki ya kara shiga zuciyar wanda ya kamu da ciwon sonki ."Idan kuwa daman neman shiga yake idan kika yi masa irin wannan kallon lallai sai yayi tsammanin ya samu kar'buwa ne acikin zuciyarki ."
Shiru tayi kamar yadda shima ayi shiru yana dubanta yana shafa sajen fuskarsa had'e da ciza lip's dinsa na k'asa yana jiran ta miko masa wayar ,baya son ya takura mata ne yasa ya bata dama ta bashi da kanta if not da tuni ya fara lalubarta, dan ko da bai ga wayar a hannunta ba yasan tana soke a jikinta" maryama ya kamata ace a yadda kike haka babu abinda Allah ya rageki dashi kamata yayi a samu hikima da wayo da iya jan hankali tare da tattali da biyayya ta hanyar aikata abu aloakcin da'aka umarceki batare da 'bata lokaci ko jayayya ba amman kashi da alamun banyi sa'a ba ta wannan bangaren ." "ina ganin ya kamata ki koma makarantar da'ake koyar da wad'an nan gaba saboda ni namiji ne mai son mace mai irin wad'an nan halayen kinga idan kina son ki juya ni na zamo sakarai a gareki dole sai kin zamo mai irin wad'an nan halayen dana lissafa." yana gama magana ta sake kawar da fuskarta dan ta fara shiga wani yanayi sakamakon numfashinsa da take shaka ."
"Maryama!" Ya sake kiran sunanta a karo na biyu sai data ji duk wani gashi dake kwance a jikinta sun mike tsaye saboda sanyayyiyar muryar da yayi amfani daita sai dai batayi gangancin kallon inda yake ba dan tasan abinda zataji sai ya nikan wanda take a yanzu ."maryama ni namiji ne mai tsananin son ayi min biyayya sannan mai son idan ya bada umarni abi umarninsa, sannan a kula dashi kamar k'aramin yaron goye dan nifa shagwa babbe ne na bugawa ajarida sai kin gaji dani wajen son jiki koda yake zuwa yanzu kinsan wasu abubuwana ".ta d'an waigo ta kallesa ." "yes dole ne na fad'a miki dan kiyi biyayya dan kin samu dami akala ne dan samuna ba abu ne mai sauki ba"zaune kawai maryama take a wajen tana dubansa tana tunanin abinda ya d'auke ta?. "sakariya ya d'auketa ko me "?"eh mana ita ya d'auke ki "zuciyarta ta bata amsa da haka,bata san abinda ya kamata tayi ba dan tunda ya bukaci wayarta ta shiga cikin mummunar tashin hankali."
Sake miko mata hannunsa yayi yana mata wannan d'an iskan kallon nasa mai matukar firgitarwa da jefe mutun cikin tsananin fargaba da tashin hankali,batare da 'bata lokaci ba ta ciro wayar dake soke a gefen siket dinta ta mika masa tana fesar da iska , ya amsa yana shan iska tare da ciza lip's dinsa na k'asa ."shiru tayi tana kallonsa tare da jin matsanancin tashin hankali da tsoron kar sakon yan'uwansa ya shigo adaidai lokacin gani tayi yana kokarin d'aura kanshi a saman cinyarta kamar ta janye k'afafunta sai dai tunawa da tayi a gidansa take da kuma sanin halinsa da tayi yasa ta hakura tayi zamanta a yadda take kar ta jawa kanta wata matsalar sai dai bakinta da zuciyarta basu yi shiru akan furta kalmar "la ila a illa anta subuhanaka inni kuntu minal zalimi ba ."tana kallonsa kai tsaye what's app dinta ya shiga ya fara duba sakonnin mutane cike da fargaba ta cigaba da kallonsa dan dai ta san anan bazai ga komai ba haka ma message bazai ga komai ba dan bata barin sako a wayarta da zarar sako ya shigo ta karanta take gogewa tashin hankalinta a yanzu shine kar sakon 'yanuwasa ya shigo ."
bata san lokacin daya d'auka yana duba wayarta ba sai dai taji yana girgizata sannan tayi saurin dawowa haiyacinta cikin tsoro taga yadda yake kallonta yace "maryama me kike tunani haka ?." Nan fa ta soma in ina jikinta har karkarwa yayi wajen cewa "babu komai ."sake matsota yayi sosai fuskarsa a d'aure sosai sai dai ita tunin ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta duk da tasan babu abinda ya gani a wayarta amman zuciyarta cike take fal da fargaban abinda zai biyo baya,har tsawon minti goma yana kallon face dinta sannan ya sake kira sunanta "maryama d'ago ki kalleni ido cikin ido saboda maganar da zan miki babu wasa acikinta "jin abinda ya fad'a yasa ta d'ago kanta ahankali ta tsura masa shayayyun idanunta kamar zatayi kuka dan sosai zuciyarta ke bugawa da matsanancin sauri "a'a ya naga kamar kina son kiyi kuka ?"ta sake narke fuska "karki sake kiyi min kuka anan "ya k'arasa maganar cike da gargadi ,take ta soma kokarin maida hawayen dake kwance acikin kwarnin idanunta ".
"Maryama waye ni agareki "?kai mai gidana ne a wajen aiki "ta bashi amsa tana sake jin fad'a uwar gaba mai tsananin ".ban dashi fa ?kai mai sona ne ."da kyau da kika gane haka ya kamo hannu wanta duka cikin nashi "ki saurareni sosai zanyi magana dake, ba zance wasa ko raha ko kuma tsorotaki zanyi ba amman ina son ki yarda a zuciyarki komai ya fito daga bakina to gasky ne ."ya d'an yi shiru kad'an yana kallonta ita kuma ta kawar da fuskarta gefe dan kallonsa ba k'aramin haddasa mata jin mummunar fad'uwar gaba yake ba "amatsayina na wanda zan aureki da zuciyata d'aya ba zan ta'ba yarda na cutar dake ba saboda haka kema banason ki aureni dan cutar dani sannan karki d'auki maganata a matsayin cutar wa ko takurawa domin magana ce ta amfanin ni dake amman fa idan kina sona dan Allah ".
Tai shiru zuciyarta na wani irin bugawa da sauri sauri "kina son ki aureni dan kiyi rayuwar aure dani ta har abada ne ko kuma kina son ki aureni ne dan cima wani buri naki ?"yayi mata tambayr da batayi tsamaninta ba ,kwayar idanunshi na kanta kyam ko kiftasu bayayi yana nazarinta muryarta a sanyaye tace "bangane abinda kake nufi da maga ..."yayi mata wani kallon da yasa tayi shiru dan dole ba dan ta shirya yin hakan ba "idan har aurena zakiyi dan Allah to ina da sharid'd'ina guda uku da zan fad'a miki aciki zaki zabi biyu wanda yayi miki "ya sake had'e fuska "ina son idan kina da wani muradi ne aurena ki janye haka ki aure ni dan Allah ko kuma ki fasa aurena gabad'aya ."zance na fasa aurenka ma bai taso ba haka ma zance janye muradin aurenka bai taso ba ."tayi maganar acikin ranta ."
"Na baki minti talatin kiyi tunani kafin na fad'a miki sauran duk maganar da yake fuskarsa a d'aure take "ni dai dan Allah ka cigaba da magana kawai dan hankalina ya fara tashi tayi maganar tana jin wani sabon tashin hankali na shigart "dole hankalinki ya tashi yayi maganar a cikin ranshi amman a zahiri cewa yayi "tunda na rigada na fad'a sai bayan minti talatin zan cigaba da magana sai kiyi hakuri har lokacin yayi ni yanzu yunwa nake ji abinci zanci ."ya mike tsaye ya barta nan zaune cikin jimami da zullumi mai tattare da tashin hankali da haushi da takaici duk sun taru sun rufeta alokci d'aya taji kamar ta shakesa ko ta rufesa da duka haka kawai tana zaman zamanta zai sake jefata cikin wani tashin hankali ."su kam wasu irin family's ne haka masu mugun hali ?"to kodai an halicci zuriarsu ne dan su jefa mutun cikin damuwa ?"daga shi har 'yan'uwansa da mahaifiyarsa duk halinsu d'aya mugaye ne masu muguwar zuciya."
har ya zauna akan tebirin cin abinci ya juyo ya kalleta bayan ya zauna "Kayan abincin da kika sa a bayan mota nawa ne ko kuwa ?"ta d'auke kanta gefe batare data bashi amsa ba ai yasan nashi ne sarai da zai mata wata irin tambaya ,sosai kwalla ta cika idanunta" ita kam gara duk su taru su kasheta ta huta da wannan duniyar dan sam ba Jin dadin zama acikin duniyr take ba bata an kara ba sai dai kawai ta ganshi a gabanta lokacin har kwallar idanunta sun zubo "yanzu me ye abun kuka "?shiru tayi kawai tana shesheka ya kai hannunsa zai share mata hawaye ta kawar da fuskarta gefe alamun bata so "ki fahimceni ban kawo ki gidan nan dan na sakaki kuka ba ". "Amman me ya kawo wad'an nan maganganun?" "ai kasan dole maganar tasani kuka , ban San dalili da yasa baka son ganina cikin farinciki ". "ni din ?!ta gyad'a masa kai alamun "eh!"tana harararsa "okay zamuyi mgana amamn kiyi min lamani inci abinci tun asuba dana yi training na sha ruwan zafi ban ci komai ba har yanzu kiyi min hakuri in samu na saka wani abu acikina sai mu cigaba da magana."
Bata ce masa komai ba illa ta juyo ta kalli agaogon bangon parlour'n karfe tara saura minti shadaya "karki damu zamu gama komai zuwa karfe goma kilama ba zamu Kai ba,still dai shiru tayi masa dan ita tsoronsa ma take ji "me yasa zai bincika mata wayarta?" sannan me ya kawo batun idan tasan dan wani muradi ne zata auresa ta janye, ta aure sa dan Allah ko kuma ta fasa aurensa gabad'aya duk me ya kawo wad'an nan maganganun ?"idan dai abincin da kika dafo min ne a mota in sa a kawo min inci ?"ni kaje kaci abinci kuma ai kasan naka ne tunda Kai ne kace a dafa maka ?"k'aramin bakinta yabi da kallon yadda take motsa shi ahankali kamar bata so ,ko da yake da gani maganar ma a dole take yinta ."wani farin abu ya danna bayan kamar minti biyar akayi knocking ya tashi yaje ya bud'e kofa ,wani yaronsa ne tsaye cike da girmamawa " "umar kaje bayan motar dana shigo dashi yanzu ka d'auko min jakar abinci" da sauri umar ya juya ya barshi tsaye a bakin kofa tsayuwar jiran dawowarsa bai jima ba ya sake dawowa cike da girmamawa ya mika masa ya amshi jakar abinci ya maida kofar ya rufe ya dawo ya zauna akan kujera ya d'aura jakar akan dining table yana dubanta ."
"dan Allah kayi sauri kaci muyi maganar da zamu yi dan dare ya fara bana son Ina yin dare a waje "baki yi min yadda zanji dadin cin abinci bane ". ya fad'a tare da mikewa ya karaso inda take zaune ya kamo hannunta tayi hanzarin zata fizge hannunta yace "stop maryama kinsan banason kina hanani ta'ba abinda ya kusan zama halal dina "ai sai ka jira har lokacin yayi tukun bawai ka maidani kamar wata sakariya ba "karki damu lokaci yayi "a ranta tace "idan wannan uwartaka ta bari ba ."wallahi na matsu naji na d'aura miki marata kiji..."ai tun kafin ya k'arasa maganar ta fixge hannunta tana hararrasa ya mike tsaye yana murmushin gefen baki "matsoraciya kawai ." Wata hararar ta buga masa "ki san ban ta'ba biyanki komai ba amman akan kallon nan naki mai sa ki kara min kyau karki sa a yanzu nace zan biya "wata hararar ta sake masa ".okay in zo na biya kenan ?ya fad'a yana tahowa ai ko ta canza fuska zatai masa kukan shagwaba bai san sanda ya sake murmusawa ba "I really like all you maryama ya fad'a yana kashe mata idonsa d'aya sannan ya koma ya zauna kamar yadda yayi d'azu ."
A daidai wannan lokacin da mr ata yake zaune yake cin lafiyayyen kuskus din da maryama ta dafa mashi mami na can tare da yaranta suna tautaunawa akan waya "inda aunty khadija tace "mami ki barshi yayi auren sai ki kafa masa duk sharudd'anki idan kina dasu "haka ne khadija maganarki tayi amman ni zan so mami tasa shi ya maida maryam ya had'esu duka "inji cewar aunty shahida "anya shahida kina ganin hakan zai yuwu kuwa ?"mami ta fad'a cike da zullumi "zai yi mana a yadda ya matsu da yarinyar nan ai kina fad'a masa zai amince "to kina ganin ita maryam zata yarda ta koma masa ne dan kwata kwata banga alamun zata koma ba ?"idan dai zan bar shi kawai zan barsa yayi aurensa shikenan yayi galaba akaina "mami ta k'arasa maganar cike da rauni "ai mami halin adamcy ne sai shi inda kika san ba mutun ba "ki bar shi din yayi auren amman karki d'aga masa kafa idan ma da hali yarinyar ta tare agidanki duk abinda zaayi kina gani "kuna ganin haka yayi ace ta tare a cikin gidan nan alhalin akwai tarin gijaje muna dasu ?".
"aunty khadija da aunty shahida har ma da auta suka ce "haka ne kawai zai sa ki san halin da suke ciki akan zamansu dan kinsan yaran talakawan da shegen shige shige kar aje a mallake miki d'a abinda ya kamata ko auren zai yi yaje ya nemi yar gidan manyan mutane amman yaje zai kwaso mana jaraba."sarai zabiba ta fahimcesu suna bawa mami shawarar ne dan su samu damar aiwatar da nufinsu akan yarinyar mutane ." mami tace "to shikenan yanzu idan mun gama wayar nan zan kira maryam naji raayinta akan komawar ta "mami da dai kin dakata da kiranta tukun har kuyi magana da shi yaya adamcy kuji me zai ce ,dan a so samuna ne a hakura da auren nan ,kowa yaje yayi rayuwarsa kamar hakan zai fi mana kwanciyar hankali kar a sake komawa gidan jiya "haka ne zabiba kema kinzo da shawara mai kyau zan jirasa har sanda zai sake nemana da maganar dan bazan nemesa ba .""wannan yayi daidai mami karki nemesa ki barshi idan ya gaji zai kawo kansa ne "inji cewar zabiba daga nan ta masu sallama ta sauka ta barsu akan layi itama mami sallama tayi masu ta soma neman layin maryam dan taji lafiyar khaira kira d'aya tai mata ta d'aga tana gaisheta .""maryam ya kuke ya khaira da fatan duk kuna lafiya ?"muna nan lafiya mami ga khaira nan yau ma akayi mata allurar immunization sai rigima take "
"Dole tayi rigima yana masu zafi idan anyi masu naga kin d'aura ta a status jiya ta kara girma "wallahi mami nima girman khaira har mamaki yake bani sai kace yar four months haka ma dazu uncle mb da ya kira mu vedio call yace wai ta kara girma "mami tai murmushi cike da jin dadi tace "ayya muhd bello Ai kuwa ya kyauta may be daga nonnki ne dan wani lokacin idan nonon uwa yana da kyau zaki ga kafin wani lokaci ya kar'bi yaro sai kiga yaro yayi saurin girma"to ai mami kamar ma kar mu dawo abuja shikenan khaira ta daina karba nono Madara take sha batason shan nono wallahi,ikon Allah aiko bata biyo babanta ba ,adamcy ya shan nono sosai kuma yayi kulafucin nono dan har na yayesa baya bacci batare da hannunsa yana kan nono ba ,maryam tai shiru batare da tace komai ba "Allah dai ya raya mana ita in sha allahu nima zan shigo abuja nazo na ganku "to mami sai kinzo munyi kewarki sosai "mami tai murmushi tace "baku kai ni ba maryam tafiyarku tamkar kun tafi da komai nawa ne bana jin dadin zaman gidan nan in sha allahu zaku ganni nan kusa suka cigaba da hirarsu."
bayan mr ata ya gama cin kuskus zama yayi kusa da maryama kamar d'azu sai dai yanzu lemun gwangwani ne a hannunsa wanda itama tunin ya kawo mata nata gabanta sai dai ita kam ta kasa sha "shawarar me kika yanke ?"ni bani da wata shawara data wuce aurenka zanyi dan..."sai kuma tayi shiru ta kasa k'arasa maganarta" kalleni sosai "ta d'aga kanta fuskarsa a d'aure kamar bashi ya gama murmushi ba ta kallesa kwarjinsa ya mamayeta sosai haka ma kyawunsa ya karu alokcin d'aya wanda yasa taji son shi ya sake dirar mata a zuciyarta tayi saurin kawar da kanta gefe tare da runtse idanunwanta tana sauke numfashi ahankali "me kake son nayi maka adam....."? "ban ta'ba jin wanda ya kira ainihin sunana naji sanyi araina ba sai ke maryama ki d'aure ki aureni saboda da Allah ta bud'e idanuwanta" ai daman saboda Allah zan aureka ta bashi amsa cikin sanyi murya" yayi gyaran murya tare da kawar da idanuwansa daga kallonta idan har na zayyano sharuddana ya zama dole ki zaba biyu aciki Ina tabbatar miki babu fashi ko tausayawa akan kowani sharadi da zaki zaba dole zaki amince tunda na fuskanci bazaki fad'a min gaskiyar da zuciyata take bukata ba "
Gabad'aya kasa magana tayi ta bishi da kallon mamaki"sharadina na farko "ki janye muradin aurena dan wata manufa ,sharadi na biyu idan na aureki ya zama dole a ranar zan kusanceki .""ki zaba d'aya idan kuma bazaki zaba ba in fad'a miki d'ayan wanda ya zama dole shi ki zabeshi ." "Wai duk me ya kawo wannan maganar ki zaba idan kinsan babu komai acikin zuciyarki "daman ance maka zan aureka ne dan wata manufa ko me yasa duk kake irin wad'an nan maganganun?"amsa nake bukata kafin lokacin da sharadi na uku zai zo"zan aureka ne dan Allah sai dai batun kusanta wannan ne gaskiya ..."is okay na rigada na gane dan wata manufa kike son aurena "ka shiga zuciyata kasan menene aciki ?"tayi maganar jikinta na rawa "muje sharadin na qarshe,sharadi na karshe tunda baki zabi biyu acikin sharadina ba zan kashe mu nida ke acikin gidan nan ."