Kenza eBookz

Mar'adams book 4 - Chapter 4

Mar'adams book 4 - Chapter 4

Mar'adams book 4 Chapter 4: Mar'adams book 4 Chapter 4. "Ban fahimci abinda kake nufi ba baki san mutuwa ba kenan ?"nasan mutuwa mana kashemu fa kake nufin…

3,317 words

"Ban fahimci abinda kake nufi ba baki san mutuwa ba kenan ?"nasan mutuwa mana kashemu fa kake nufin zakayi ?"ashe zafin zuciyar ka har ta kai ka iya kisan kai ni dai gsky ban tashi mutuwa ba Ina son na cigaba da rayuwa tare da mahaifiyata ,kai idan ka gaji da duniyar zaka iya kashe kanka amamn bayan na fita a gidan nan "ya isa ya isa !!"shikenan to ki bani kanki a yanzu na sanki ya mace shikenan zan samu natsuwar cewar ba aurena zakiyi da wata manufa ba "gabanta ya fad'i hantar cikinta ya kad'a nan take taji jiri na dibarta ,da kyar ta samu taja baya ta mike tsaye tana tangadi da baya manufar hakan da tayi shine ta samu ta gudu ."ta dan kalli fuskarsa taga babu wani annuri akanta nan kuma dukkanin alamu sun nuna da gaske yake zai iya aikata abinda ya fad'a,take taji hankalinta ya sake tashi matuka yayinda gumi ya shiga tsatsafo mata ganin har ya cire rigar shan iskar dake sanye ajikinsa ya wurga a saman kujera shine abinda ya sake tsoratata ta juya a guje tana ihu azo aceceta ."

hankalinta bai sake tashi ba sai data karasa bakin kofa ta ta'ba tajita a kulle gam tayi tayi kofar ta bud'e taki bud'e wa tana cikin wannan halin na tashin hankali taji ya karaso gareta yana kokarin ta'bata tai saurin gocewa ta koma jikin window parlour'n amman babu motsin mutane sai data zagaye parlour'n tass yana biye daita amman bata samu hanyar fita ba "ki tsaya mana ki daina 'bata min loakci idan nayi bashi zai sa na fasa aurenki ba zan aureki ,kanta kawai take girgiza masa tana taresa da hannunta dan maganar ma taki fitowa daga bakinta hankalinta gabad'aya ya gama tashi kallo d'aya zaka mata ka fahimci bata cikin haiyacinta sauran kad'an ta bashi dariya dan bakaramin rikicewa tayi ba ,da gudu tabi wata doguwar hanya da tai tunanin zata fitar daita zuwa kofar waje." bashi da tabbacin kofar a rufe take aiko taga ya biyota a guje wata irin fixge yayi mata ya had'ata da bango ,shi yayi daidai da fasa ihu da tayi wanda bai razana shi ba sai ita kanta datayi kayanta ta razana shi kuwa tsumammun idanunshi har sun canza kala ya matseta da bango yana sauke numfashi yana kokarin had'e bakinsu adaidai lokacin tasa iykar karfinta ta turesa sai dai ko gezo bai yi ba ji tayi ma kamar dutse ta ta'ba ,tana jinsa ya sake matseta ajikinsa "kayi ..kayi hakuri dan giraman Allah karka sadu dani babu aure ,wallahi gara ka bari idan ka aureni kayi duk abinda kake so kayi dani "okay yanzu acikin sharadin farko kin zabi d'aya kenan ?"tai saurin gyad'a masa kai tana haki ."

Ya Kai hannunsa yana shafa fuskarta yana kallon face dinta data fara 'batawa da ruwan hawaye "sauran sharadi d'aya ai daman biyu nace zaki zaba." Shiru tayi tana son tuno d'ayan "kar dai har kin manta ?"tai saurin gyad'a masa kai dariya ta bashi amman ya fiske "na baki minti shabiyar ki tuna "inna lillahi "ta shiga furtawa tana maimaitawa yayinda shi kuma ya cigaba da shafa fuskarta can tace "na tuna !"okay ina jinki zan aurena ba da wata manufa fa "are you sure? "tai saurin gyad'a masa kai "kin ta'ba mafarkin mun kasance tare acikin gida d'aya kuma a waje d'aya muna rayuwa kamar haka kafin zuwan wannan lokacin "?kanta ta girgiza masa da sauri "karki min karya mana ."yayi mgnr muryarsa a kasalance yana zagaye pnky lip's dinta da d'an yatsansa "nasan kina mafarkin haka dan a yadda nake kallon wad'an nan shayayyun idanun naki sun dade cikin nitson son adam ".ta sake girgiza masa kai alamun "a'a!numfashi ya fixgo da karfi ya fitar ,kallon fuskarta yake cike da tsananin tausayawa tana da matukar rauni kuma daman yasan sai raunin ta ya jawo anyi mata illa kuma shine dalilin da yasa ya kasa gabatar daita ga yan'uwansa dan a yadda idanunsu ya rufe akan son wacan yarinyar sai sun nuna mata wariya abinda ya guda dai sai da ya faru shi ."

Shida zuciyarsa ke cike da tsananin muradin kasancewa daita shine za'a kafa mata sharad'i akansa ,zai ga uban da ya isa ,zai ga ta yadda wannan sharadin zai yi aiki aiko mami ce tace kar ya kusance wallahi sai dai tayi hakuri bare wasu can "maryama na sha mafarkin mun kasance tare acikin gida d'aya kuma a waje d'aya muna rayuwa kamar haka kafin zuwan wannan lokacin" yayi maganar yana sakè had'e ta da faffadan k'irjinsa tare da sauke mata numfashinsa a wuyanta,jikinta ya sake d'aukar rawa sosai duk maganar da yake mata bata fahimta komai amman ta'ba mata jiki da yake ji take kamar tasa ihu ko ta bashi wani lafiyayyen mari saboda bakinciki,shi kuwa gabad'aya jinta a jikinsa ya sake rikita masa lissafi da kyar ta aro jarumta ta sanyawa jikinta sannan ta soma magana cikin bacin rai "idan ka gama wulakantani ka sakar min jiki ka maidani gida dare nayi !"tayi maganr hawaye na zubo mata." shiru yayi yana shafa lip's dinta yana tunanin wani wulakanci yayi mata? jikinta kawai ya ta'ba kuma daman ya saba ta'bawa kuma bazai daina ta'bawa ba har zuwa sanda zata dawo karkashinsa yanzu ma so yake ya d'an tsotsa bakinta dan yasan zai yi dadin sha ,dan haka ya sake matso da fuskarsa zai kamo lip's dinta "ban san baka da mutunci ba sai yau ... " "cak ya tsaya ya kasa aiwatar da abinda yayi niyya yana mata wani irin kallo ,ji yayi ma kamar maganar ba daga bakinta ta fito ba amman yasan ita tayi maganar yace "ke ki kalleni da kyau waye bashi da mutunci ?"yayi maganar yana janye jikinsa daga nata dan yaji zafin kalmar ".

"waye da wuce Kai wallahi baka da mutunci "ta samu karfin halin fad'a masa haka ne ganin sun samu tazara a tsakaninsu "yanzu ni zaki fad'a wa wannan kalmar ?" ba dole na fad'a maka ba tunda ka nuna min baka da mutu..."ai wani lafiyayyen mari ne ya ratsa mata kwakwalu warta abinda bata saba ji ba arayuwarta jinshi yau kuwa sai ya zame mata wani bakon alamari sai ya zamo duk ta rude ta rasa Ina ma zata saka kumatunta taji sanyi ai ko ta zame kasa ta durkushe , ta dinga shafa kumatunta kamar mai sabon ciwon hakori sai data d'auki minti biyar tana jinyar kumatunta na dama tare da idonta da d'an yatsantsa ya d'an shafa ,ahankali ta iya d'aga kanta sai dai ta hangosa zaune yana fuskantarta sanye da Kaya ajikinsa sa'banin d'azu ,ta girgiza kanta tana son tabbatar wa kanta da gaske abinda ya faru daita kenan ?" ,kumatunta ta cigaba da shafawa dan har yanzu dai tana Jin zafin radadin zafin marin data sha ."to a yaushe ne har yaje ya canza Kaya bata sani ba ?"ina zaki sani kina cikin gigita ."zuciyarta ta bata amsa da haka .

mikewa yayi ya nufi kofar fita jiki a sanyaye ta mike ta isa gaban mirrow dake parlour'n ta duba fuskarta a madubi ta ganta kalau babu abinda ya sameta sai dai gefen idanunta yayi ja sai lokacin taga d'an digon hawaye sun cika mata ido suna kokarin fito wa daga kwayar idanunta ahankali ta maida idanunta ta lumshe domin su karasa gangarowa taji sanyi aranta wata uwar ashar ta zuba masa wanda wallahi ta tafi karfin shekara goma batayi ashar ba dan ba dabiar ba ce sai bayan da tayi ta dawo tana nadama duk da ba agabansa tayi ba hawaye ta cigaba da zubarwa sannnan ta tabi yo bayansa tana gunji kuka tare da nadama me yasa zatai masa rashin kunya ?tamabayr da tayiwa kanta kenan ,sai ma tazo tana ganin laifinta da rashin kyautawarta ,a haraban gidan ta iske shi tsaye ya bud'e mata gaban mota yana jiranta kanta a sunkuye ta shiga ta zauna ya maida kofar ya rufe mata ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna ya fizge motar da gudu uka suka bar gidan ."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 3

Zuciyarsa na matukar zafi yake murza stearing batare daya kalli inda take zaune ba, ahankali ta d'an waigo inda yake zaune ta kallesa a tsanake fuskar nan tashi a had'e tamkar zaki kwata kwata babu alamun annuri akanta numfashi ta janyo ta sauke da kyar zuciyarta cike da matsanancin tashin hankali,tana son ta bashi hakuri amman tana jin matukar tsoron abinda zai biyo baya dan fushinsa ba kyau shiyasa bata son wannan fushin nashi dan zuciyarta bazata iya d'aukar fushinsa ba, kwananki baya da yayi fushi daita ta azbatu matuka."basu zame koina ba sai akan titin unguwarsu yayi parking batare daya kashe motar ba alamun jira yake ta sauka ya k'ara gaba." shiru tayi taki sauka tana kallonsa kamar zatayi kuka har acikin zuciyarta bata ji dadin rashin kunyar da tayi masa ba ,a kalla sun d'auki kusan minti shabiyar suna zaune shiru acikin mota sanyi ac motar na ratsa masu sansar jikinsu yayinda kamshin turarensa wanda ya gauraye da sanyi dake ratsa cikin motar suka dinga bugar mata da zuciya ."

zaune kawai take acikin motar tana ko kuwa da numfashinta da zuciyarta tana tunanin hanyar mafi sauki da zata bi wajen bashi hakuri kafin su rabu amman ta rasa, shi kuwa agogon motar ya duba a karo na kusan biyar tare da jan dogon tsaki bai san zaman me take masa acikin motar ba ,jarumtar ta aro ta sanyawa jikinta tare da kwantar da muryarta cike da girmamawa tace "yalla…."ai tun kafin ta kai k'arshe taji sautin muryarsa cikin tsananin fushi . "Get down !". ya fad'a atakaice zuciyarta cike da rud'ani da tashin hankali ta kai hannunta ta bud'e murfin motar ta fito tana kallonsa shi kuwa ko kallonta bai yi ba gabansa yake kallo yana jiran ta k'arasa sauka yaja motar, tana maida murfin motar ta rufe ya soma kokarin yin revise tare da jan motar wani suuuuu taji motar ta d'auki hanayr fita titi ." Ahankali ta tabi bayan motar da kallo har sai data daina ganinta, two second ta d'auka tsaye tana kallon hanyar da ya bi da tsantsar tashin hankali akan fuskarta,sannan ta soma d'aga kafafunta duk yadda taso ta d'aure karta yi kuka amman sai da hawaye ya zubo mata saboda tasan me zai iya faruwa ,ita kad'ai tasan irin fushin da zai iya yi akan wannan matsalar ."

Jiki a matukar sanyaye ta shigo haraban gidansu idanuwanta akansu baba gali da aunty salma tsaye adaidai kofarsu bata dai san tsayuwar me suke ba, duk da cikin duhu ne amman ta lura idanunsu na kanta ."bangaren umma ta wuce kai tsaye ,ai suna ganin shigarta da sauri suka shiga haska haraban gidan suna duba sawun takalman ta,rigerigen kwasan k'asar takun suke ." maryama ta iske umma a parlour daman tasan anan zata tarar daita zaman jiran shigowarta umma tace "aa maryama kin dawo yanzu nake shirin kiranki ashe kina kan hanya "?ya adam din yake da fatan yana lafiya?" gabanta ne ke fad'u wa har lokacin tace "yana lafiya !"ta fad'a tana cire hijab din dake sanye ajikinta waayrta ta ajiye a hannun kujera tana kallon wata yar qaramar akwati dake gefen umma yayinda idanun umma ke kanta tana kallonta har ta samu waje ta zauna tana kiran "sunan Allah "!sannan tace "umma wannan akwatin fa ?". "d'azu bayan fitarki subai'a ta aiko miki dashi "har ta dawo kenan ba gobe ko jibi ne dawowarta ba ?"gashi nan dai ta dawo" ikon Allah kamar jiya ne fa tayi tafiyar ?".

"Ai kwanakin gudu suke da zarar dare yayi gari ya waye Allah dai yasa mu cika da imani "ameen!maryama ta fad'a tana janyo akwatin tare da budewa tana duba kayan ciki dadduma sallah ta fito dasu guda uku sai Jallabiyiyo guda biyar masu shegn kyau d'aya bayan d'aya ta dinga nunawa umma ."gasky maryama kayan sunyi kyau subai'a tayi kokarin ko da yake ai komai tayi miki bata fad'i ba kin cancanta Allah dai ya barku tare ya nuna mana aurenku ."maryama ta amsa da ameen acikin ranta ".gabad'aya sukai shiru har na tsawon minti goma kafin ahankali umma ta sake kallon maryama ". "Maryama wai me kuke ciki ne da adam ?maryama ta dafe kanta da hannunta d'aya tace "wallahi umma ban San me ake ciki ba "ko dai akwai matsalar da kike boye min ne dan yanzu ma gabad'aya na karanci yanayinki kamar ba lafiya ba ?"karki boye min maryama "tabbas umma akwai matsala nayi ta kokarin na boye miki domin Ina ganin cewar matsalar zata zo karshe sai dai kwata kwata banga alamu hakan ba ."matsala daga adam din ne ?"umma ta tamabayeta cikin fad'uwar gaba duk da bata da tabbas din daga garesa ne ."

"a'a daga mahaifiyarsa ne gaskiya umma mahaifiyarsa bata kar'beni a matsayin surukarta ba a ranar farko da mukaje "ahaf ai nace wallahi sai da nayi wannan tunanin araina."maryama ta dubeta tana sauke numfashi."mman ita kuwa meye illarki data ki karbarki ?"umma tayi tamabayr tana duban maryama "ban da wata illa umma kuma bata da wata hujja da zata bayar akaina data wuce ni bazawara ce bazata yarda d'anta ya auri bazawara ba ". ahankali maryama tayi wa umma bayanin komai d'aya faru aranar da taje gidansu mr ata amamn sai ta boye mata shirin yan'uwansa, umma tayi murmushi tace "gaskiy bata da wata hujja ban da abunta ai addini bai hanamu auren bazawara ba amman wasu mutane har yanzu da sauran su ."

"wallahi umma na gaji da rayuwar nan gabad'aya rayuwata kullum cike take da kalubali "kiyi hakuri maryama naji dadi da naji matslar da'ake ciki sai mu sa rokon Allah shi aure irin haka a karshe alkhairi yake zama ,abinda nake so dake kiyi hakuri kiyi hakuri ki kara hakuri akan wanda kikeyi hakika dukkan wanda ubangiji yake so shi yake wa jarabawa Allah yayi miki jarabawa Allah ya baki ikon cinye jarabawa abinda zakiyi duk runtsi duk wahala ki taya adam yiwa mahaifiya rsa biyayya sannan ki fad'a masa ya kyautata mata domin su rabu lafiya da mahaifiyarsa dan Allah madaukakin sarki yace (wakada rabbuka alla tahbudu illa iyahu abil walidaiya ihsan) iyaye guda biyu a kyautata masu ki tayasa yi mata biyayya kinji maryama ta gyda mata kai kwalla na cika idanunta."

" hakika maryama alamarin ki akwai tashin hankali,ina jin tausayinki fiyye da tsammaninki kice masa shima yayi hakuri yayi juriya sannan ya kyautatawa mahaifiyarsa maryama bata san lokacin data kama kuka ba tana jin kmaar ta fad'awa umma sauran matsalolin da take ciki amamn kukan da take yasa ta kasa magana ."Kiyi hakuri maryama komai mai wucewa ne kuma zamu fad'a wa Allah shi yace idan muna da wata bukata muzo garesa zai amsa mana ." "umma addua nake amamn kamar ba addaur nake ba "ki cigaba maryama kuma karki gaji khairan sha Allahu tashi kije kiyi sallah ki zo kici abinci kinji babu abinda zai faru sai alkhairi ta mike da kyar tana goge hawayenta ta nufi d'akinta umma ta tattara kayan data fito dasu daga cikin akwati ta maidasu ciki ta zuge akwatin ta ajiye tai shiru cike da jimami halin da suka sake tsintar kansu ciki ba maryama da matsalolin ke bibita ba ita kanta ta shiga damuwa matuka."

wani abun bakinciki da haushi tana gama cire kayanta sai ga sakon yan'uwansa suna sake tuna mata kwanakin d'aya saura aiko sai tasa wani sabon kuka tama rasa da me zataji da marin data sha koda ta'ba mata jikin da danuwnasu yake ko kuma da fushin da yayi daita ?"wurgi tayi da wayar ta shige bayi tana kuka ita kam gara su turu su kasheta , shirin nasu ma tana ganin kamar mr ata yasani dan maganganunsa na yau yayi Kama da yasan wani abu ko kuma yana zargin wani abu akanta ,ita dai Allah yasani bata son ta tozartane wallahi data tona asirin komai amamn kima da mutuncinta dana iyayenta yafi komai a wajenta wanka tayi ta dauro alwala ta fito bayan ta kammala da abinda zatayi wondo da riga na bacci ta saka ta hau gado ta kwanta lamo tana sake karanta sakonsu tana tunanin kiran mr ata ta bashi hakuri."

Bangaren mr ata kuwa har yaje gida abinda maryama tayi masa yanata damunsa mamakinta kawai yake ta yadda har ta iya bud'e baki ta kirashi da mara mutunci, ai duk son da yake mata baya jin zai d'auki wannan rainin daga gareta kuma yaji dadin marin da yayi mata dan kwata kwata bai yi nadama ba kuma zai ganar daita kuskuren ta yadda bazata sake maimaita wa ba dan bai irin su ake wa rashin kunya akwana lafiya ba "amman ai kaine ka jawo tai maka rashin kunya dan ba halinta bane "zuciyarsa ta fad'a masa haka tsaki yaja ya d'auki kwalin sigari ya bud'e ya zari kara d'aya ya kai bakinsa ya kunna yana zuka ahankali yana cikin wannan halin sai ga kiran maryaama ya shigo wayarsa ya daga wayar ya manna a kunne yana zukar sigari batare daya duba mai kiran ba sallam muryar maryama yaji a kunnensa bai amsa ba ya katse kiran ya ajiye wayar yana sake jan tsaki ."

bayan second biyu wani kiran ya sake shigo ya daga a fusace "me zaki ce ma mara mutunci?"magiyar yayi hakuri ta dinga masa acikin wayar sake ajiye wayar yayi batare da yace mata komai ba ".maryama ta kasa hakuri ta sake kiransa ai yana d'aga kiran ya hau zuba masa matseefa muryarta a raunane tace "haba mana ka tsaya ka saurareni muyi magana nasan ban kyauta ba amman ni ya kamata na nuna fushina fiyye da yadda kake nuna naka amman ban yi ba ko kana tunanin kai kad'ai kake da zuciya a k'irjinka ."bayan ka wulakantani kuma nazo Ina baka hakuri banda cutar daka so kayi min Allah bai baka sa'a ka mayar dani mai ido d'aya ba shine kuma zaka fini fushi akan laifin da Kai ne kayi ."".okay ko zaki rama marin da nayi miki ne ?"saurin katse kiran tayi ta koma ta kwanta akan gado ta cigaba da kuka "wayar ya bi da kallo yana mamaki "shi zata kashewa waya ?"ya fad'a a fili yana jan tsaki "maryama kukan me zaki zauna kiyi?zuciyarta ta tamabyeta casbaha ta janyo ta fara ja tana karkafa zuciyarta "ya allah karka bari soyyyara bawan nan naka yayi galaba akaina kwata kwata bana son na cigaba da sonshi domin kuwa bazan iya jurar ganina cikin damuwa ta soyayya ba ,ya allah d'an son nan da nake masa ma ka cire min shi gabad'aya na huta ta fad'a ta zubar da hawaye."

bayan wani lokaci bacci ya d'auketa sai dai cike da shaukinsa."shi kuwa yana nan zaune har wani kiran ya shigo wayarsa ya d'aga a zuciye yana cewa "maryama zaki had'u a mummunar bacin raina ,me kuma zaki fad'a min?" yayi maganar a tunaninsa itace sai dai jin muryar amar yasa ya dafe goshinsa yana furzar da iska mai zafi daga amar yayi shiru kafin daga baya suka gaisa yace "ita kuma maryamar me tayi maka haka ?"kaga malam kayi abinda yasa ka kira" numfashi amar ya sauke yace "Ina son mu had'u gobe mu tautauna akan matsalar nan data kunno kai ."okay zaka iya zuwa gobe karfe tara ka sameni a Delphi muyi abinda zamuyi dan zuwa goma akwai taron da zamuyi okay sai gobe zan zo akan lokaci ,sukai sallama yana ajiye waya kiran emran na shigowa kamar bazai d'aga ba dan ya gaji sai kuma ya duba yaga shi ne sai ya d'aga yana cewa "emran ya'akayi?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull