Kenza eBookz

Mar'adams book 4 - Chapter 5

Mar'adams book 4 - Chapter 5

Mar'adams book 4 Chapter 5: Mar'adams book 4 Chapter 5. "Wallahi lafiya daman na kira naji ya kukayi da yarinyar?"da alamun abinda ka fad'a gasky ne sai…

3,220 words

"Wallahi lafiya daman na kira naji ya kukayi da yarinyar?"da alamun abinda ka fad'a gasky ne sai dai na duba gabad'aya wayarta babu wata sheida data nuna haka kuma nayi mata duk dabara dan ta fad'a min taki kasan yarinyar ce akwai tsoro da zurfin ciki amman zan bari ayi min binciken layinta da duk wasu call da message's din dake shiga da fita ta layinta "very good hakan yayi dan Allah yallabai idan an tashi hukunci acire matata dan wallahi bata da natsuwa akan matsalar nan ko baccin kirki batayi saboda tausayin yarinyar ." Mr ata ya sauke numfashi yace "ai tayi kokari ma data fad'a maka kaima ka kyauta thanks ya fad'a tare da katse kiran ya bar emran rike da waya a hnnusa."

Washegari maryama bata farka ba sai shida saura da carbi a hannunta tayi adduar tashi daga bacci ta shige bayi ta fara da watsa ruwa ajikinta domin ta samu jikinta ya warware tayi alwala ta fito bayan tayi sallah tayi azkar ta sake komawa ta kwanta lamo tana tunanin rigimar mr ata bazata iya da wannan rigimar tashi ba ,bama zata sake kiransa ko nemnasa ba ta gaji, ahankali zuciyarta ta soma bata shawara maryama me zai hana duk gabad'aya kiyi blooking dinsu daga shi har yan'uwansa ki huta da balainsu "take kuwa ta amince da wannna shawarar to kuma ai mr ata kawai zata iya rufewa a kira ,ammn su sunfi mata sako akan kira."cike da fad'uwar gaba tayi blooking dinsa a kira da kuma what's app tana kallon sunansa dake rubuce." karfe tara daidai a gidan mr ata tayiwa amar bayan sun gaisa ya fara masa magana akan abinda ya kawosa "ata ka rabu da maryama tunda har mami tace bata sonta". kallonsa kawai adamcy yayi tare da jan dogon ajiyar zuciya ya sauke yace "amar wllh kayi masifar bani mamaki idan har na rabu da maryama na kama wa?.

"yau ace ba da wata manufa sweetheart take son hanani auren marayma ba zan iya cewa zan hakura daita amman wallahi wallahi ko dady ne zai dawo duniya yace kar na aureta sai na aureta."to ka aureta a boye kamar yadda muka tsara tun farko albashi daga baya sai kowa yasani "bazan iya ba ko da din ma saboda maryama ne alokacin bata sona kuma batasan Ina sonta ba , a yanzu kuwa da nasan tana sona Ina sonta me zai sa nayi haka ?""kai matsalata da kai kenan idan ka nace akan abu, kai yanzu don Allah bazaka ƙyale maryama ba sweetheart fa "?amar yayi maganr cike da zolaya."adamcy dake shan coffe me bala'in zafi ya kalli amar cikin ido ya ce, "ai tunda maryama ta zama gaskiya ta bayyana agareni na rantse da ubangijin daya halicceni ya busa min rai bazan barta akan cikar burin wasu ba sai mallaketa sai ta rayu cikin salama dani ,sai na tabbatar da cewa na bata dukkanin kulawa da farinciki ,ba kuma zan yarda a keta alfarmarta ba kai baka masan halin da su khadija suka jefata ba."

"kasan kwanaki baya kana uk anyi kidnapping dinta baka ga wahalar dana sha ba har nayi zargin yarinyar nan sultana ashe Ashe yayan mami ne suka sace yarinyar nan "nan ya zayyowa amar komai aiko ya cika da mamaki yace "Kai ya'akayi kasani "emran ne ya fad'a shekaranjiya shima kuma zabiba ta fad'a masa wai karya fad'awa kowa amar ya girgiza" Kai gasky basu kyauta ba Allah sarki maryama baiwar Allah amman kayi hakuri ka bar maganar yanzu tunda ka nace muje ka bawa mami hakuri da kanka nasan zata hakura mr ata yace "wallahi zasu gane basu da wayo idan na daga masu kafa Allah yayi min abinda ya ga dama ,could you imagine wai har da auta ?"ai akan maryma kowa zai ga back to back zan bawa kowa size dinsa ,amar ya rike ha'barsa yana kallon yadda mr ata yake motsa bakinsa ."

Ahankali amar yay ƙasa da muryarshi cikin sigar rarrashi ya ce,"amma sai nake gani kamar zai fi kyau kayi hakuri tunda Allah yasa kasan komai "gaba ma ta kaini dan ita ma maryama ta shirya min muguntar auren wani mummunar mutun adaidai lokacin suka saceta suka kafa mata sharadin ta aureni na wani laokci ta barni ". "kaga abinda suka yi ma kamar taimakonka suka yi ?"sosai amamn kai kana tsammanin zan bar wani ya aureta ne ?"ai sai dai a mutu ,itama jiya daga na d'an ta'bata ta kirani da mara mutunci aiko na nuna mata inda rashin mutuncina ya kai ." amar ya ware ido yana kallonsa "ba dai wani abu kayi da yarinyar mutanen ?"kai me zanyi daita ai ita din nake so ba jikinta ba lafiyayyen mari nayi mata mai kyau dan tasan ba'a min haka amar ya sake ware ido yana girgiza kai "don Allah adamcy kayi haƙuri ka dinga d'agawa yarinyar nan kafa "kallon rainin hankali mr ata yabi amar dashi yana taɓe baki tare da sake kai cup ɗin dake hannunsa baki ya ce,"ba zanyi hakan ba kai kasan halina bazan ta'ba d'aukar mata raini ba zanyi komai akanta amamn raini bazan d'aga kafa ba ita fa bata saba da irin rayuwarka ba "kafi kowa sanin halina akanta kuma bazan canza ba a haka zata saba i will never tolerate it ."

Shiru amar yayi yana kallonsa cikin wani irin yanayi, haka kawai sai yake jin tausayin maryama yana huɗar ko wani sashi na tsokar zuciyarsa ya rasa wani irin zuciya ce da adacmy itama kenan da yake mutuwar so bai d'aga mata kafa bare wata can Jin shirun yayi yawa ne yasa adamcy ya ɗaga kai ya kalli amar ya ce,"yanzu menen next dan Ina da muradin na mallaki yarinyar nan bayyanarta ta haddasawa jikinta kullum samun fellings, wata irin sha'awa nake fama daita fiyye da lokutan baya na ."tashi zakayi muje mu samu mami ka bata hakuri kai ma bai kamata kayi fushi daita ba "wallahi banyi fushi daita ba tana raina ajiyar zuciya amar ya sauke sannan ya ce gsky kaje ka bata hakuri ka samu ka shawo kanta ta huce ayi auren ." kallonsa mr ata yayi tare da ajiye cup ɗin dake hannunsa ya ce,"naje ko muje ai tare zamu kayi min rakiya murmushi amar yayi tareda miƙewa yana kallon cikin ido mr ata ya ce," shikenan da daddare by 8pm zan kiraka sai muje ." daga haka ya nufi ƙofar fita daga ƙayataccen parlour'n yana jinjinawa baƙar zuciya irinta adamcy ."

mikewa mr ata yayi tare da ya wuce bedroom ɗinshi, yana mai manna wayarsa a kunnensa daga yanda yake magana a wayar zaka fahimci waya ce me mahimmanci daga can ɓangaren jami'an da yake son yaje masa kamfanin mtn yace "yallabai in sha Allah zuwa gobe zan kammala maka komai "okay I will be expecting you ,bayan yay discounting din kiran yaji kamar ya kira maryama sai kuma ya ajiye wayar a gefan gadon ya shiga wanka ."Ya jima yana watsa wa jikinsa ruwa ya fito d'aure da dogon farin towel a ƙugunsa, faffaɗan ƙirjinsa wanda ya wadatu da kwantaccen gashi sunyi luf luf gwanin sha'awa ko ina ajikinsa a murɗe yake saboda tsananin jim din da yake hakan ne ma kullum yake kara zama kamar yaro d'an shekara talati abunka da akwai kudi gashi kuma yana kula da jikinsa idan ba an fad'a maka ba wallahi bazaka ce ya kai 43 ba ruwan dake ɗigowa ta cikin sumar kansa ne ke ratsowa ta dokin wuyansa zuwa kwantaccen gashin ƙirjinsa shiru yayi yana tafiya har ya karaso ya tsaya gaban mirrow ya d'an bud'e towal din dake d'aure ajikinsa yana kallon halittar jikinsa babu wacce tazo ransa kamar maryama Ina ma ace yadda ya fito din nan tana kusa kuma a matsayin matarsa ai babu abinda zai hana bai yi having sex daita ba sai dai yaje ya sake yin wani wanka ."

ahankali ya maida towel din ya d'aura ya goge jikinsa sannan ya shirya cikin wani had'a den yadi dark green mai matukar kyau da taushi a gaban rigar an rubuta "TAT "kasancewarsa fari Kayan ya kar'bi jikinsa sosai ya d'aura hula a kansa hular daya saka ta matukar taimakawa wajen fito da aihinin kyawunsa ya ɗau tsadadden links ya saka a bakin hannun rigar sanyayyen turarensa red me sanyin ƙamshi ya feshe jikinsa dashi ya sanya cover shoe mai shegen kyau sai faman kyalli yake sannan ya kwashi wayoyinsa ya fito, kai tsaye ITG direbansa da masu tsaronsa suka nufa dashi inda zasu gabatar da taro na manyan 'yan kasuwa yana takun nan nasa cikin isa da takama yayinda masu d'aukar hoto da vedio suka shiga daukarsa har ya shiga cikin babban conference hall din da za'a gabatar da taron ,hall din cika yake makil da manyan 'yan kasuwa sai dai mafi yawansu turawa ne kowanne sanye yake da hadadden suit da abun wuya wanda yake d'auke da sunan mutun ."

mutanen da suka sanshi suna ganinsa sai su mike su bashi hannu domin sun gaishesa tare da girmamawa alhj abdulbasi executive director BUA group at the food and energy security yana ganinsa shima ya taso sanyen da manya kaya babbar riga da yar ciki farare sol mr ata ya k'arasa suka mikawa juna hannu tare da rungume juna suka gaisa sannan ya k'arasa waje na mussaman da'aka tanada domin manyan baki ya zauna a kusa da wasu mutun hud'u uku sanye da suit d'aya sanye da manya Kaya .hall din yayi shiru alokcin da alhj abdulbasi ya soma bayani bayan ya gama gabad'aya hall din ya d'auki tafi raf raf raf!!! haka ma wani acikin manyan bakin ya mike ya amsa speaker ya soma magana bayan ya gama ne aka mikowa mr ata speaker daga zaune da yake ya soma magana tare da d'aura kafarsa d'aya akan d'aya yana magana a natse tamkar baya son magana cikin tsadadden turancinsa yana bada misali da hannunsa ."

ya d'auki lokaci yana bayani sannan ya ajiye spker a gefensa na gefensa ya d'auka duk dai tautaunawa ce akan shaanin kasuwanci bayan awa biyu akayi hotuna in group sannan aka bawa yan jarida damar suyi masa tambayo da kyar ya zanta da mutun d'aya ya soma haramar barin wajen alhj abdulbasi ya biyosa yana mika masa hannu tare suka jero hannunsu cikin juna har haraban wajen inda masu tsaronsa ke tsaye aka bud'e masa murfin mota ya shiga ya zauna suka bar wajen cike da jiniya d'aya daga cikin wayoyinsa ya lalubo ya soma neman layin maryama dan duk abinda yake tana makale aransa sai dai numberta bata shiga yayi shiru can ya shiga what's app yayi mata salam kusan minti biyu ya sake dubawa yaga bai yi mark biyu ba kuma babu hoton mahaifinta dake makale a dp hakan yasa ya fahimci tayi blooking dinsa ne ya cika da mamakinta wato itama fushi zatayi dashi alhalin shi ko saukowa bai yi ba take ya bada umarnin a wuce dashi unguwarsu yaji dalilin da yasa tayi blooking dinsa ."

Umma wacce ta tsinci kanta da matsanancin ciwon kai sakamakon matsalar data kunno masu ta Kira maryama wacce itama kanta ke ciwo tun safe dan marin da mr ata yayi mata ba iya idanunta ya ta'ba ba har gefen kanta ya taba ta shigo da kyar umma tace "maryama duba kan table din can ko akwai sauran maganin ciwon kai nan ki miko min na sha kaina ciwo yake "sannu umma nima wallahi kaina ciwo yake"ashsha maryama to duba sai mu sha ta fad'a alokcin da maryama ta k'arasa gaban table din ta tsaya tana duba maganin tace "umma babu amman bari naje ta siyo magani a kemis na dawo "da kyar umma tace "to maryama !"bayan ta fito daga kemis ne taga motocin mr ata a parke a gefen titi an bud'e masa bayan mota yana kokarin fitowa sukai four eyes dashi ido cikin ido suke kallon juna sam batayi tunanin dawowarsa ayau ba da wani mugun sauri ta d'auke idanunta ta nufi hanayr gida bayanta ya biyo."sai dai ya nemeta ya rasa da alamun wata hanyar tabi acikin kananun lungunan dake lugunsu sai dai ya cigaba da takowa a natse har ya k'araso cikin haraban gidansu ya tsaya tare da tura hannunsa d'aya cikin aljihunsa yayinda d'ayan hannunsa ke rike da waya yana neman layin umma ."

Bayan ta bawa umma magani taji karar wayar umma ta d'auki wayar tana dubawa babu suna kuma bata san number ba dan haka ta d'aga tun daga d'aga wayar ta gane mr ata ne cikin sanyayyiyar muryarsa mai cike da girmamawa yayi gaisuwa "umma barka da rana"? a tunaninsa umma ce shiru tayi tana sauke numfashi da karfi yace "okay kece kika d'auki wayar to ki fito Ina cikin gidanku "ni yanzu Ina da abubuwan yi saboda haka ayi min hakuri zuwa wani lokaci fatan ka gane ?"ta fad'a tana kokarin ajiye wayar yace "karki ajiye wayar wallahi idan kika ki saurarata zan shigo kai tsaye goshinta ta dafe ita dai ta had'u da gamonta babu yadda ta iya ta fito zuwa haraban gidansu a tsaye ta iskesa ya d'aga kanshi sama yana kallon sararin samaniya har ta iso ta tsaya kusa dashi bai dawo da kanshi ba duk da sallamar datayi shiru tayi tana kallonsa shigrsa tai mata kyau matuka wato dai shi din gwanin iya ado ne duk Kayan daya saka sai ya kar'bi jikinsa "ahankali ya dawo da kwayar idanunshi kanta ya sauka adaidai inda ya mareta wani iri yaji a gabad'aya ilahirin jikinsa kusan minti goma yana kallon waje sosai yaji babu dadi aransa dan har jini ya d'an kwanta acikin idon "banzo da niyyar baki hakuri ba ammna ganin idanunki haka yasa naji babu dadi acikin raina kiyi hakuri fatan zaki yafe min ?"

"Da kayi me kake bada hakuri ?"ai ka tsaya kawai a raayinka na farko tunda bakayi niyyar bada hakuri ba "tana gama fad'ar haka ta juya ta nufi bangaren umma tana ji yana kiranta amman tai masa banza sai dai tausayi da qaunarsa ya sake mamaye zuciyarta d'akin umma ta koma tai mata sannu "yauwa maryama kin kuwa sha maganin ?"dan nasanki da rashin son shan magani "ban sha ba amman zan sha "ayya maryama ciwo baya warkewa sai da shan magani ki d'aure ki sha kinji "zan sha ne bari naje naci abinci sai nazo na sha". ta fad'a haka ne dan umma ta barta ." ta fito zuwa parlour'n tana gama fitowa kawai ganin mutun tayi zaune sai da gabanta yayi wata irin mummunar fad'uwa amman bata nuna ba balle ya gane taji fad'uwar gaba akanshi "yallabai ya haka zaka shigo babu neman izini ?"ban san abinda hakan yake nufi ba " ya bata amsa da haka yana furzar da iska "kaga yallabai ka tashi ka kama gabanka tunda kaga nayi blooking dinka ta koina ya kamata ka fahimci na yanke duk wata halaka dake tsakaninmu,ni na kawo ka gidan nan nace zan aureka to na fasa "kika kawo ni ko na kawo kaina ?"duk wanda ka kace daidai ne a wajena dan bazan iya wannan auren ba tun kafin ayi an fara da mari Ina ga anyi aure sai dai duka ni maryama bana sonka na fasa auren ".

"shi wancan alkawarin da kika d'aukar masu fa ?"na fasa ?"ta fad'a da karfi sai bayan data fad'a ta fahimci kamar ta tafka kuskure a maganarta "okay that's god da kika fasa ."ya fad'a yana tsareta da tsumammun idanunshi kallonsa tayi a natse tana son tuna abinda ya fad'a da amsar daaya bata ."tana can dogon tunanin kawai taga mutun a gabanta da sauri taja baya zata gudu ya fixgota ya dawo daita gabansa ya tsareta da tsumammun idanunshi babu shiri ta sunkuyar da kanta "d'ago ki kalleni maryama ki fad'a min cewar kin daina son ni adam tariq abdullah ." ta d'ago ahankali suka had'a ido ya lumshe mata tsumammun idanunshi wanda yasa taji duk gashin dake kwance ajikinta sai da suka mike tayi saurin sunkuyar da kanta "idan har da gaske kin daina sona ki tsaya zan miki wani abu wanda zai tabbatar min da lallai da gaske kin daina sona "meye shi ?ta tambaya a gigice "d'ago ki kalleni sai naji dadin yi miki abinda zan tabbatar da gaskiyar maganrki in kuwa har na gane gaskiyar cewar kin daina sona zan barki har abada "go ahead?!"ta fad'a tana mai d'ago da kyakkwar fuskarta me zata ga mr ata zaiyi sai gani tayi ya kamo kumatunta da hannunwasa duka ya had'e bakinsu waje ."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 4

Wani irin kissing yake mata mai tsananin rikitarwa domin kuwa ya had'e lip's dinta da hakoranta waje d'aya yana sarrafawa nan take maryama ta rud'e ta rikice da sauri ta kai hannuwanta duka kan nashi ta tattara iya karfinta ta kwace fuskarta da bakinta"sir kana da hankali kuwa ?"ta fad'a tana wani irin huci tamkar wacce tayi gudun tsere yayinda idanuwa nta suka cika da ruwan hawaye ."what !"?ya furta a d'an rikice fuskarsa d'auke da tsananin mamaki "tare da girmamawa sir gsky baka da mutunci na sake maimaita abinda yasa ka kusan illata min ido ,"acikin gidanmu kuma acikin bangaren umma haka kawai ka biyoni har gida a parlour'n umma fa, kuma ma umma tana ciki babu mamaki ma ta ganmu ,imagine ace ta fito ta ganmu alokcin da kake kissing dina ?". "wai ma ya ka d'aukeni?"koda nake bazawara ance maka ni irin wad'an nan zawaranwan ne masu zubar da mutuncin kansu ?"nasan kaina nasan mutuncin kaina, ba kuma zan biye maka da sunan zaka aureni na zubar da mutuncina ba "sau nawa zan fad'a maka cewar banason hannun ka yana kaiwa jikina ?"aikin bazan kawai mutun sai jaraban son ta'ba jikin mutun."ta k'arasa maganarta zuciyar na wani irin bugawa da k'arfin gaske sakamakon maganganun datai masa amfani dasu ."

ahankali ya rage girman idanunshi yana kallonta cike da tsantsar mamaki "wato dai wasa wasa itama bata jin magana jiya jiya nan yayi mata hukunci akan wannan kalmar amman still gashi ta sake maimaitawa har ma tayi k'ari akan na jiya idan yaso yayi mata duk abinda zai mata gasky yayi saken daya bari maryama ta raina shi dayawa ji yayi kamar ya sake kara mata wasu maruka dan da alamun na jiya bai shigeta ba sai dai a yadda yake kallon gefen idanunta yana kara mata idanunta zai ta'bu idan ma bai tashi aiki ba .yalalbai ni banason haka dan Allah ka daina dan kana shiga rayuwata dan wlh ban saba da irin wannan rayuwar ba ." "shine dalilin da yasa zaki kirani da kalmar mahaukaci kuma mara mutunci ?".yayi mata tamabayr yana tsareta da tsumammun idanunshi "I'm very sorry sir amman dan Allah ka daina ta'ba min jiki banaso "tayi maganar kmr zatai kuka ."ahankali ya gyad'a kanshi still idanunshi na kanta kafin d'aga baya wani kyakkwan murmushi ya bayyana akan kyakkwar fuskarsa nan take wani irin tsoro mai tsananin ya shigeta wanda yasa babu shiri ta juya zata shige ciki taji ya kira sunanta cikin wata irin murya."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull