Kenza eBookz

Mar'adams book 4 - Chapter 6

Mar'adams book 4 - Chapter 6

Mar'adams book 4 Chapter 6: Mar'adams book 4 Chapter 6. cak taja ta tsaya batare data juyo ba shima bai ce ta juyo ba yana tsaye yana kallon bayanta ita da…

3,353 words

cak taja ta tsaya batare data juyo ba shima bai ce ta juyo ba yana tsaye yana kallon bayanta ita da kanta ta juyo ta kallesa zuciyarta na wani irin bugawa da sauri sauri har lokacin fuskarsa na d'auke da murmushin data misalta shi dana mugunta "dan Allah ne kad'ai yasan me zai aikata akanta bayan wannan murmushin ,dan wannan murmushin nashi gara ace had'e fuskarsa yayi zata fi fahimtar irin mummunar hukuncin da zai mata ."daga sunanta daya Kira bai sake cewa komai ba ya juya Cike da natsuwa yayi taku uku ya k'arasa inda kujeru suke ya zauna tare da d'aga kwayar idanunshi sama yana kallon celling parlour'n nasu." wani iri taji a gabad'aya ilahirin jikinta,sosai taji babu dadi tare da rashin kyauta wa, kallonsa ta cigaba dayi yayinda son shi ya sake k'aruwa a zuciyarta haka ne ma yasa ta soma takowa zuwa inda yake zaune bata san sanda ta durkusa agabansa tace "gani yallabai "ta fad'a tare da tsura masa idanuwanta da gabad'aya suka canza "yallabai ka kirani "!

Shiru yayi yaki cewa komai illa ma gefen lip's dinsa na k'asa daya kamo yana cizawa ahankali ahankali ,itama shiru tayi durkushe a gabansa jikinta na d'an karkarwa hakan ne ma yasa ta kamo yatsun hannunta ta fara murzasu kafin taji saukar hukuncinsa tafi second hamasin a gurin banda rawa babu abinda jikinta yake yi da kyar take iya lumshe idanunta zuciyarta na cigaba da bugawa babu abinda kwakwaluwarta ke hango mata atattare dashi sai tashin hankali tasan yadda yake ji aransa ,ta kuma san tunanin yadda zai yi daita yake ita dai Allah ya taimaketa kar ya ta'ba lafiyar jikinta dan har lokacin tana jin zugi a idanunta." bayan kamar minti goma ya soma magana a natse "me nayi miki maryama da yayi zafin haka wanda na cancanci ki dinga kirana da wad'an nan kalma ?"shiru tayi gabanta na wani irin fad'awa ". "Maryama kina son na kafa miki mummunar tarihi kafin aurenmu ko "!?da sauri ta girgiza masa kai"alamun a'a."

"no !no !!" "da alamun kina bukatar na akafa miki mummunar tarihi da bazaki ta'ba manta wa dashi ba har abada sannan idan kina son kanki da arkizi wannan kalmar ta zamo kalma ta k'arahe da zaki sake furtawa adam domin shi din mai mutunci ne kuma cikakken mai hankali ne idan kuma kikayi gardama to wallahi ki shirya wa kanki irin rayuwar da zakiyi dani dan wallahi bazan ta'ba d'aga miki kafa ba ,zanyi komai dan naga kin canza daga yadda kike ."duk abinda nake miki Ina yi ne saboda kiji dadi." tai saurin girgiza masa kai alamun bata so "me kike son nayi yi miki mryama wanda zai sa kiji dadi arayuwarki bayan wannan "ni dai ka daina ta'bani yallabai sannan ka daina sona kamar yadda na daina sonka shine kawai abinda zaka min naji dadi ba wai kayi ta ta'ba min jiki ba ". tayi magana jikinta na sake d'aukar rawa a durkushen da take a gabansa gabad'aya fargaba da tsoronsa sun taru sun mamayeta har sun mantar daita inda take ."

Yayi murmushin nan nasa mai rikita mata kwakwaluwa da lissafi sannan ya matso da fuskarsa daf da nata "kina son na daina sonki ?" yayi mata tamabayr yana janye fuskarsa daya sunkuyo daita kusa da nata zuciyarta cike da matsanancin tsoro ta gyad'a masa kai alamun "eh!"to ai baki barni na k'arasa abinda zai tabbatar min da kin daina sona har a cikin zuciyarki ba bare nima na daina sonki ". shiru tayi yayinda idanunta suka sake cika da kwalla "kina son kiyi kuka saboda ita zuciyar taki tasan karya kika mata dan tana tsananin son adam matukar so "ko ina sonka yanzu bana sonka ."ta fad'a tana danne hawayenta domin zubarsu tamkar bashi wata dama ce ". gara ta hakura dashi tunda ma ta fahimci ya gane shirin yanuwansa akansu ta saukakawa kanta ta cigaba da rayuwarta cikin 'yanci da kwanciyar hankali amamn yaya zatayi da hotunsu dake hannunsu da kuma hukuncin da suka ce zasu d'auka akanta da yan'uwanta ?" "Karki damu da wannan tunda ya rigada ya sani komai zai zo miki da sauki ."

"kika ce bakya sona ko kin daina sona ne ?yayi mata tamabayr yana mata wani irin shu'umin kallo wanda yasa hantar cikinta kadawa muryarta a sanyaye tace "eh sai dai Ina maka so na addini namuslim "A'a so na aure nake so ba na addinin muslimci ba, duk da dai nasan karya kikewa zuciyarki "dan Allah yallabai ka bar wannan maganar dan gsky yanzu na daina sonka ". shiru yayi yana kallon k'aramin bakinta da take motsawa kamar mai koyon magana wai ta daina son mutun kamar shi ?"shi da mata dayawa suke kawowa rayuwarsa hari ko matsayin friendship ne yayi dasu amman yaki bada wannan damar saboda tsananin sonta da Allah ya jarabesa dashi." bai san ya'akayi ya sake kai hannuwansa ya kamo fuskarta ya haɗe da nashi ba ."tayi kokarin kwacewa ta kasa dole ta hakura ta tsaya a yadda yake so yana zukar numfashinta tana zukar nashi sannan ya fara magana a natse kamar mai koyon magana "maryama kika ce me ?shiru tayi tana lumshe masa shayayyun idanunta dake kwance da hawaye " kin daina sona ko ?sake lumshe masa ido tayi tana jin wani iri a gabad'aya ilahirin jikinta kamar ana jona mata shocking."

Muryarsa a kasalance yace " maryama bani ni ne banda hankali ba kice baki da hankali ." ta ware idanunta sosai idanunsu ya tsarke cikin juna ,cikin idanunta yake kallo yana hango tarin kaunar da take masa "duk yadda take son ta danne hawayenta sai da suka samu nasarar zubowa ,wani miskilin murmushi adamcy yayi wanda yake nuni da karfin ikon da yake dashi akanta ya janye jikinsa yace "maryama kenan da kin daina asarar hawayenki a banza amamn kafin nan ki natsu sosai ki tmby kwakwaluwarki da zuciyarki zasu fad'a miki matsayin adam arayuwarki ,wallahi maryama babu wanda zai kalleki a yadda kike durkushe a gabana yace bai fahimci irin zallar son da kike min ba ."cikin kuka ta hararesa yace "you see wallahi yanzu na kara tabbatar da kina son adam tariq Abdullah dan wannan kallon sai wanda ake tsananin so akewa shi "inna lillahi !"ta furta a fili tana kai hannunwanta ta dafe goshinta."

Ahankali ya cigaba da magana "zuwa anjima zanje wajen sweetheart in sha allahu idan komai ya daidai a goben nan ma zaki iya tashi daga matsayin bazawara zuwa cikakkiyar matar aure "yallabai da dai an bar maganar auren nan please tunda mahaifiyarka bata so,ka guji yin duk abinda iyaye basa so, su iyaye suna da darajar da zasu ce ka bar abu ka barshi duk kuwa da tsananin son da kake wa abu haka zalika idan sunce kayi abu to ka hanzarta yinsa domin kuwa anan duniya kad'ai muke da damar kyautata masu domin mu samu aljanna barin ma Kai da kake matsayin namiji wanda Allah yace aljanarku tana tafin kafafun iyayenku tai shiru tana dubansa ganin kamar maganarta ta shigesa yasa ta cigaba "dan Allah kabi umarninta dan..." " babu ruwanki matsalata ce damuwata ce kuma ni nasan yadda zanyi da rayuwata .".yayi saurin dakatar daita ."

Shiru tayi na minti goma tana tunanin tauri kai irin nasa ahankali ta motsa bakinta "sir me yasa kake da taurin kai ?"walllahi kanka kamar dutse yake "ya d'age mata girarsa d'aya "ga wani abu wai shi zafin zuciya ga rashin tausayi , idanunshi ya zuba mata yana kallonta a ranshi yace " yarinya har yanzu baki ga komai akan taurin kaina ba ko rashin tausayi ba sai ranar da kika shigo hannuna a matsayin mata bana jin zan daga miki kafa "amm.." dan Allah sir Ina son nayi wata magana "sai daya lasa lip's dinsa na kasa sannan ya bata dama "kayi hakuri akan cin amanar da nayi maka duk da dai kayita kokarin na fad'a maka amman na kasa sai dai zuwa yanzu zuciyata ta fahimci kasan halin da'ake ciki". " wace magana kenan "?ya tambayeta yana sake tsareta da idanunshi tayi shiru tana kallonsa cikin wani irin yanayi "tamabayrki nake wacce magana kenan"?still dai shiru tayi tare da sunkuyar da kanta k'asa "ki d'ago ki kalleni maryama " kasa d'agowa tayi saboda idanunshi dake yawo a sansar jikinta "dake nake magana fa ?" "amm d'azu kamar naji kayi wata magana ni kuma sai baka am..."sai kuma ta tsinci kanta da yin shiru tare d'ago kanta har lokacin idanun shi na kanta ita yake kallo yana murmushi with unreadable expression akan fuskashi ."

"Ina jinki sai kika bani amsa dame ?"cike da fad'uwar gaba tace d'azu kamar naji kace"alkawarin da kika d'aukar masu fa ?"ni na fad'a haka ?"kuma a yaushe kenan ?"gyada masa kanta tayi tana kallonsa jikinta na d'an rawa tace "d'azu muna magana da kai "ya langwabar kai gefe kamar abun tausayi yace "baki ji daidai ba amamn dai idan ma kina cin amanata ne kiyi duk abinda kike so bazan hanaki ba amman kisani duk abinda zakiyi Allah yana kallonki sai dai daga yanzu zan nuna miki Ina da karfin Iko da kuma mutanen da zasu dinga kula da duk wani takun da zakiyi Kama daga tsayuwa da wani bare har ya tsaya kusa dake duk zan sani ya fad'a yana kamo hannuwanta cikin nashi yana kallonta bayan matsayinki acikin zuciyata kina bani tausayi ya fad'a yana murza hannuwanta dake cikin nashi tayi saurin zare hannuwanta daga nasa tana yarfawa kamar wanda shocking ya Kama saboda wani blood rush da taji ya fito daga cikin hannunsa ya shiga nata cikin seconds ya zagaye duk ilahirin jikinta cikin tsarke war mury tace "bazaka ta'ba canzawa ba "kin ta'ba ganin mai hali ya canza halinsa kad'an ma kika gani ki jira shigowarki hannuna ni zan wuce na bar mutane suna jira amman may be gobe zan dawo ka dai ji tsoron Allah ka daina wahalar da mutane suna jiranka dan kaga kana da kudi ."

"Aikuwa ni a ganina Ina kulawa dasu daidai gwargwado bakiga sometimes ni kad'ai nake zuwa abuna ba amamn dai duk da haka zan kara kiyayyewa tunda uwar gidana tayi magana ta d'an yi murmushi tana cewa uwargidanka tana gida tana jiranka dan wani lokaci kana manta kanka "duk abinda nake yi akan daidai nake yi "shikenan sai anjima bari naje nasan umma tana can tana jiran shigowata Allah yasa ma tayi bacci dan shine samun natsuwata na cewar bata ga komai ba "wani shuumin kallo yayi mata "bazaki bawa umma shawara ku tare a gidanku ba ?"ta yatsuna fuska alamun a'a "ai daman nasan duk kece matsalar rashin tarewarsu "?ko d'aya ni babu ruwana "ganin bashi da niyyar tafiya yasa tayi masa sallma dole ya wuce ta shige d'akin umma aiko ta iske ta idanunta biyu ."

ta zauna jiki a sanyaye zaman jiran tsamanin zata jeho mata tambaya,umma ta kalleta tace "Ina kikaje ne?bata son tayi mata karya dan bata sani ba ko ta fito ta gansu ko kuma ta jiyo maganarsu da mr ata ,dan haka tace mata "mr ata ne yazo umma tace tun yaushe dan kin dade da barin d'akin nan ?eh ya d'an jima da zuwa amman yanzu ya wuce yama ce zai zai je suyi magana da mahaifiyarsa zuwa gobe zai dawo "to Allah yasa muji alkhairi ,maryama ki rike mutuncinki karki sake ki bari so ya yaudareki duk da gabad'ayanku Ina maku kyakkwan zato amamn dai ki sake rike mutuncinki "tana gama fad'ar haka ta mike ta nufi bayinta itama haka ta mike jikinta a sanyaye tana tunnain maganar umma ruwa baya tsami banza ko dai umma taga wani abu ne "?inna lillahi ta fad'a cikin tsananin damuwa tare da shigewa nata d'akin."

********

karfe tara daidai a gidan mami tayi ma mr ata da amar adaidai lokacin mami na zaune a babban parlour'nta tana vedio call dasu khaira kawai taga shigowarsu bakinsu d'auke da sallama "assalamu alaikum."a hankali mami ta buɗe idanuna sosai akansu tana jin wani sanyin dadi na ratsata alokacin da idanunwanta sukai tozali da adamcy nta sanye cikin wasu hadaddun kanana Kaya Wando da riga ash colour kanshi rufe da facing cap nan take parlour'n ya sauya da kamshin turarensu ta amsa da" walaikumssalam tare da d'auke kanta dan kar ya gane tayi farinciki da ganinsa, amar ya gaishesa cike da girmamawa ta amsa masa fuskarta babu yabo babu fallasa sannan ya samu waje ya zauna shi kuwa mr ata kujerar da take zaune ya nufa ya zauna a kusa daita yana kamota hannuwanta cikin nashi tana kokarin zare hannunta ya ake riko hannun yana cewa "I'm very sorry sweetheart I don't mean to hurt you my world best nayi nadama abinda nayi kiyi hakuri ki yafe ma adamcynki"shiru mami tayi tana cigaba da kallon fuskar khaira ta cikin wayar inda adamcy ya kar'bi wayar hannunta bata hanashi ba fuskar khaira yayi tozali daita tana murmushi "yaushe rabon ya ganta bama zai iya tunawa ba haka nan yaji wani sanyi ya ratsashi ya kalli mami "sweetheart khaira ce haka ?"ta gyda masa kai kawai "gsky ta girma "ya fad'a yana kashe wayar ya ajiye a gafenta ".

Ya zaka kashe min waya bayan wayar nan tafi min ganinka mahimmanci murmushi mr ata yayi yace "haba dai sweetheart saboda ni fa kike son khaira "waye kai a wajenta da zan sota saboda kai?"kasani ba dan kai nake sonta ba maryam jinina ce kuma kasan ko wani ta haifawa diya dole zan sota Ina son khaira ne saboda diyar maryam ce yace "shikenan naji Sweetheart mu bar wannan maganar muyi maganar data kawo ni "ai dole kace abari tunda ba imani dake kai ba sai da yayi daya sanin kar'ba wayar da yayi "ina jinka Allah yasa maganar data kawoka ba shirme bace ?"ta fad'a tana karkada kafa ya numfasa yace "nazo ne na baki hakuri akan abinda ya faru kiyi hakuri ki yafe min kiyi min lamani na auri maryama"ya fad'a tare da yin shiru yana jiran yaji me zata ce masa "sai dai har tsawon minti goma bata ce komai ba ya kalli amar yayi masa alamar ya sake bata hakuri "sweetheart dan Allah kiyi hakuri ki duba lamarina "na duba lamarinka akan yarinyar daka nuna tafini daraja ".

"haba sweetheart me yasa zaki fad'a haka kema kinsan babu wata mace da zata kai darajarki ?" matsayinki dabam nata dabam" banga alamun haka ba tunda har zaka iya kaurace min amman ita kana zuwa wjenta kuyi iskancin da kuka ga dama ai d'auka zaka aureta ne a boye batare da izinina ba wallahi da kayi dana sanin cewar ni uwar aka ce "ta fad'a tana zare hannunta dake cikin nashi ."shiru yayi yana kallonta inda amar yayi gyaran murya ya soma magana "mami kiyi hakuri dan Allah adamcy bazai ta'ba auren yarinyar nan ba muddin bada izininki ba kuma kinsan da zai aikata hakan da yayi amman tsananin son da yake miki ya kasa samun sukuni kuma ya kasa biye wa zuciyarsa bare ya aureta a boye ,shiyasa ma yace na rakosa ya baki hakuri ki lamince masa,a yadda yayi nadama ko cewa kikayi ya hakura daita ina mai tabbatar miki zai hakura daita domin farinciki "haka yace maka zai iya hakura daita ?"mami ta tambayesa tana kallonsa zaune shiru yayi ya kasa bata amsa "nifa na haifa adamcy kuma duk duniya nafi kowa sanin halinsa zan amince yayi auren ne tare da sharadi idan har ya amince yaje yayi Allah ya bada sa'a ".

"Sharadi kuma sweetheart ?"ya fad'a tare da sake kamo hannunta "eh sharadi kafin kayi auren nan idan ka amince na fad'a kaje kayi aurenka idan kuma baka amince ba shima kaje kayi aurenka sai dai babu hannuna kuma babu ni babu kai har abada ,kallonta ya cigaba da yi zuciyarsa na wani irin tsalle hakan nan yaji sharadin mmai masu wuyar aiwatar wa ne agaresa amamn dai zai bita ahankali yaji sharadin nata Allah dai yasa masu sausauci ne "muryarsa a kasalance yace "Ina jinki sweetheart ki fad'a min ni mai biyayya ne agareki "wacce ni agareka da matsayina "?ke mahifiyata ce kuma duniyata ba kuma zan iya fadar matsayinki a zuciyata ba dan duk yadda zan fad'a kin wuce haka acikin zuciyata "da kyau da kasan haka ,sharadina guda uku ne da zan fad'a maka kuma acikisu sai kayi duka idan kaga zaka iya to". ta fad'a tana sake had'e fuska shiru yayi yana kallonta yana Jin zallar damuwa Allah yasa babu sharadin maida wannan duwaf din yarinyar cikin rayuwarsa "a matsayina na mahaifiyar Ina son ka kar'bi khaira har acikin zuciyaka ka janye kalmar ba yarka bace "sweetheart wannan ai tun tuni na kar'bi khairat Allah shine sheida ta tunda na d'aura kwayar idanuna akanta na tabbatar da jini ce ban kuma isa nayi wa Allah wayo ba ."

Wani sanyayyayen ajiyar zuciya mami ta sauke tana godewa Allah sannan ta cigaba da magana sharadi na biyu "idan ka auri ita wannan yar gwal din da kake so a gidan nan zaku zauna "gidan nan kuma !?"ya furta hakan a fili ko bazakayi ba ne ?"ya kalli amar inda ya gyad'a masa kai alamun ya amince "numfashi ya sauke yace "shikenan sweetheart wannan ai ba wata matsalar bace."tayi shiru tana tunanin sharadinta na uku wanda itama sai da taji bugun zuciyarta a fili "sharadi na uku Ina son ka maida maryam kafin ka auri wancan yarinya". da wani irin sauri yace"sweetheart wace maryam kuma ?"wace maryam ka sani ?"maryam dai tawa wacce ta haifa maka diya ita nake nufi nan take kansa yayi wani irin mugun sara ya ajiye wayar hannunsa akan a gefensa tare da cire hullar kanshi ya ajiye yasa hannuwansa gabadaya ya dafe kanshi dashi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa bashi ba hatta amar ya shiga damuwa sai dai maganarsu ce bai isa ya saka bakinsa ba muddin ba izini aka bashi ba ."

bayan kmr second biyu ya d'ago yana duban mami kmr zai yi kuka yace "why sweetheart "?ban maka dole ba idan kana bukatar aurenka ga abinda nake so sharadina guda uku kuma dole ayi min su a qalla ya kusan minti talatin zaune cikin tashin hankali yana girgiza kafafunshi batare da yayi magana ba yana tunanin sabon tashin hankalin da mahaifiyarsa take son kunno masa jikinsa sai tsatsafo da zufa yake ahankali nasihar maryama ta dinga masa yawo acikin brain dinsa"su iyaye suna da darajar da zasu ce ka bar abu ka barshi duk kuwa da tsananin son da kake wa abu ,haka zalika idan sunce kayi abu to ka hanzarta yinsa duk kinka da abu domin kuwa da zarar sun mutu shikenan anan duniya kad'ai muke da damar kyautata masu domin mu samu aljanna barin ma Kai da kake matsayin namiji wanda Allah yace aljanarku tana tafin kafafun iyayenku "mami tai shiru tana dubansa ganin kamar maganarta ta shigesa sai dai zuciyarta rawa take kar yace mata bazai yi ba ."

ya d'ago Idanunshi ya dubi agogon dake manne a bangon parlour'n yaga goma da wasu 'yan mintina sun wuce da kamar yace mata bai amince ba da sharadinta na uku ba amman hakan nan maganar maryama taki barin zuciya da kwakwaluwarsa ta huta kuma tabbas yasan gaskiya ta fad'a masa duk da alokcin ya dakatar daita da Zara mami ta bar duniya duk son da yake mata shikenan kuma duk yadda yake son ya kyautata mata babu halin yin haka gara ya kyautata mata tun tana raye sai dai abinda take so din ne yana da daci a zuciyarsa ahankali ya motsa lips dinsa yace "shikenan sweetheart na amince ."a natse ta kallesa tana jin wani irin sanyi zuciyarta "ba wai ka kar'beta da wata manufa acikin zuciyarka ba ?"ko d'aya sweetheart zanyi komai matukar zai faranta ranki ." ai nan da nan mami ta saki fuska ta soma saka masa albarka ta kalli inda amar yake yana murmushi "amar kaji abinda adamcy ya fad'a ka zama sheida babu wulakacin babu tozarci dan bazan d'auki cin kashin da yayi mata a baya ba dan ko yanzu hukuncina ne ita kanta maryam batasan da zaman maganar ba amman tunda ya amince da umarnina zan fad'a mata kuma nasan maryam bazata bani kunya ba "."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull