Mar'adams book 4 - Chapter 25
Mar'adams book 4 Chapter 25: Mar'adams book 4 Chapter 25. murmushi yayi ganin yadda ta natsu tana amsar sakonsa jikinta na narkewa bud'e idanunta tayi da…
3,361 words
murmushi yayi ganin yadda ta natsu tana amsar sakonsa jikinta na narkewa bud'e idanunta tayi da kyar ta kallesa da idanunta da suka sauya kalar bacci da shaawar daya saukar mata ,shi kuwa babu abinda yake aika mata dashi sai murmushinsa mai matukar burgeta da birketa mata lisafi "na cigaba ne? ya fad'a yana shafa kitson kanta hade da kissing din wuyanta nan take tsigar jikinta suka mike yabi jikinta da ido yana kallon yadda tsigar jikinta suka mike ya kai hannu yana shafawa a hankali yana sake kashe mata sansar jiki ."me yasa tsigar jikinki ya tashi ?tai shiru ta kasa bashi amsa tambayar da yayi mata,kallonsa da wasaninsa na matukar birkita mata lissafi har ma ta manta da kanta kuma ta lura ya fahimci haka shiyasa yake mata wasu abubuwa da zasu sake dilmiyar daita cikin tafkin soyayyarsa "maryama! ya kira sunanta da wata rikitacciyar murya da duk sanda yayita yana cikin kololuwar bukatuwa "ki barni nayi romance dinki please babu abinda zan miki iyakata romancing kawai"a'a wallahi dashi ka yaudareni "ta fad'a da sauri ya fad'ad'a mur mushinsa har fararen jerarrun hakoransa suka bayyana yana sake yamutsa tafin hannunta cikin wani irin salo saboda hannunta dake kife cikin nashi hannu ".
"dole kayi murmushi tunda kasan gaskiya na fad'a yaudarata zaka.."saurin hade bakinsu yayi tare da matsota sosai yana kokarin zuge zip din gaban rigarta ta rike masa hannu gam amman yaki sakar mata baki sannan yaki cire hannunsa itama ta kasa dauke hannunta a saman nashi wani irin kissing yake mata mai fitar da mutun daga haiyacinsa duk da tana jin sakonnin da yake aiko mata amman zuciyarta gbdy ta cika da tsoro kar yayi mata irin na shekaranjiya zuciyarta wani irin bugawa yake da karfi shi kuwa sai faman tsotsar bakinta yake yana lumshe tsumammun idanunsa sonta da son kasancewa tare daita yayiwa rayuwarsa yawa ."ya dauki lokaci yana sarrafa bakinta ganin yadda take girgiza masa kai tana kwalla ya zare bakinsa a natse zuciyarsa na cike da matsanancin soyayyarta ,sauke numfashi yayi da karfi itama haka sai dai ita sai data had'a masa da harara sannna ta janye jikinta byn ta dauke kwallar idanunta ".
da alamun baki son na barki lafiya bakisan wannan hawayen da hararar nan da wannan 'bata ran da kike yi zai iya tunzurani na kwance dinki jikinki ba ? to me nayi kuma "bakiyi komai ba amman dan allah karki sakar min fuskarki da jikinki zan baki mamaki" ya karasa maganar yana sakar mata murmushin mugunta kallon kyakkyawan fuskarsa tayi tasan zai iya aikata fiyye da abubuwan da yayi mata a yanzu." ta cigaba da kallonsa har ya tashi ya nufi bathroom yana kallonta itama kallonsa take ya kashe mata idonsa d'aya yana sakar mata murmushi "komai yayi kyau yake masa haka kawai ta shagaltu da kallonsa anya kuwa zata iya rabuwa dashi "wayyo ni allah son bawan nan naka ya fara min yawan da bazan iya rabuwa dashi ba ,Allah mai yasa kai jarabeni da son shi "?da sauri tace "Allah na tuba Allah ka kawo min mafuta arayuwata."domin ta gano maganarta kuskure ne ta zauna shiru tana tunanin yan'uwansa dan matsalar mahaifiyarsa mai sauki ce akan matsalar yan'uwansa."
*******
Washegari kamar jiya adamcy shi yayi mata komai cike da so da kulawa bayan ya gama ya tsaya yana daddana wayarsa ,alert ta gani ya shigo waayrta na 300 million a natse ta d'ago kanta ta kallesa tana neman Karin bayani ahankali ya kashe mata idonsa d'aya yana cizan lip's dinsa ya karaso kusa daita ya riko hannunta yana sakar mata murmushi yace mata"wannan shine tukuicin farincikin da kika sani shiru tayi tana kallonsa zuciyarta na wani irin rawa "zai fita zuwa gidanmu dake cbm estate akwai kayanki dasu umma zasu kai miki can bazan dade ba yayi kising dinta "ki kular min da kanki "!kasa magana tayi har sanda ya mike tana zaune rike da waayrta tana kallonsa "me zatayi da wad'an makudan kudaden ?shiru tayi tana lissafa abubuwa rayuwa kenan wato idan Allah ya soka da jin dadi babu wanda ya isa ya hana."bayan fitar adamcy da d'an jimawa su aunty khadija suka shigo gidan suka shiga bangaren mami bayan sun gaisa suka fito suka hauro saman adamcy cike da isa ,basu iske maryama a parlour'n ba alokacin tana kwance a d'akinta tana waya da subai'a, sam bata ji motsin shigo warsu ba sakamakon tv dake aiki a d'akin kamar daga sama taga an banko cikin d'akin babu ko sallama."
wata irin zabura tayi ta mike tsaye jikinta na rawa da sauri ta katse wayar da take tace "sannuku da .."da hannu aunty khadija ta dakatar daita tana wurga mata mugun kallo "dole ki baje wa mutane tunda babu jin dadi a house anzo an samu abinda ba'a saba samu a gidan uwani da ubale ba "maryama ta sunkuyar da kanta kasa tana k'okarin gaishesu "kul kika sake kika gaishe mu !"tai tsit jikinta na bari da fargaban abinda zai biyo baya yau ,sai dai bazaka gane hakan a zahiri ba saboda aro dakiyar da tayi ta sanyawa jikinta sai dai zuciyarta ban da dukan tara tara babu abinda take ,ta d'ago kanta ahankali tana kallon bayansu ko Allah zai jeho mata adamcy." "Makira wato ke har kin isa ki yi watsi da abinda muka kawoki kiyi ?"maryama tai shiru zuciyarta cike da matsanancin tsoro "sai da muka ja kunne ki da gargadi mai karfi akan adamcy amman dan jaraba irin naki sai da kika sakar masa jikinki yayi yadda yake so ."
Shiru tayi tana kallonsu fuskarta da bayyana ne mamaki ,ya'akayi suka san abinda ya faru a tsakninsu "ke ga jaka ,ballagaza, jarabbabiya banza ko cikakken kwana biyu bakiyi a gidan ba har kin sadaukar masa da kanki "aunty kuyi hakuri wallahi ba laifina bane abun ne yafi kar...tass tass !!"kake jin aunty khadija ta d'auketa da wani gigitaccen mari har biyu ajere tana nunata da d'an yatsan hannunta" idan kika sake ce min ba laifinki bane sai shake miki wuya na kashe ki kuma idan na kasheki na kashe banza dan babu abinda za'ayi "tsit maryama tayi duk da azabar radadi da kumatunta yake "kisani kwanaki kad'an suka rage miki acikin gidan nan karki kuskura na tako gidan nan akanki duk yadda zakiyi kiyi amman ki tabbatar da baki kara second d'aya akan waadin da muka baki ba idan kuma kika kuskuren kika sabawa umarninmu kisani rayuwarki data iyayenki zaki jefa a cikin halaka domin kuwa zan sa a tarwatsa rayuwarku " sai loakcin taji sauakr hawaye suna gangaro mata "zaman lafiyarki ki gaugauta yin abinda ya kawoki ki tattara ki kama gabanki dan zamu iya aikata komai domin babu abinda muke bukata daga gareki face ki fita arayuwar adamcy kuma acikin d'an lokacin nan kinji ko baki ji ba ?"ahankali ta gyad'a mata kai tace "naji ".
"Kin samawa kanki lafiya !"inji cewar aunty shahida ai bazata bar gidan nan ba sai na wankewa shegiya mara dan kar bayan ta tafi abiyo mu da bakar yad'iya" good! inji cewar aunty khadija tun yanzu ki fara had'a kayanki ki ajiye abakin kofa dan nan yafi dacewa dake zagi kam babu wanda basu mata ba da gargadi da dunguri kafin kace me tunin yanayinta ya sauya idanunwanta sunyi tulu tulu sannan suka kama hanaya suka wuce ."ahankali ta zauna dafe da kuncinta hawaye na zubo mata tunanin take ta Ina zata fara"? bayan taci kukanta ta koshi ta zuba tagumi tana tunanin mafuta dan dole ta nemawa kanta mafuta kafin su illata mata rayuwa "jajurcewa zama dashi zatayi ko kuma rabuwa dashi?tambayar data jefawa kyakkwan kwakwaluwarta kenan" tafiyar ki itace mafi alkhairi arayuwarki kwakwaluwarta ta bata amsar tambayar data aika mata ."
Tana nan zaune har adamcy ya dawo kallo d'aya yayi mata ya fahimci akwai abinda ke damunta ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sunbatarta yana tamabayarta, tace babu komai "yasan abinda zata fad'a kenan dan haka ya zareta ajikinsa ya tsura wa fuskarta ido yana karewa fuskarta kallo gabad'aya ta canza har cikin kwayar idanunta"kukan me kikayi ?" tayi shiru"wani abu aka miki?"ya sake tambayarta still dai shiru tayi idanunta na cika da kwalla "shiru yayi kafin ahankali yace "su wa suka shigo da bana nan ?shiru tayi tana tunanin abinda zata fad'a masa "su khadija sun zo ne? "kai tsaye ta fashe masa da kuka tare da had'e hannuwanta duka rokonsa take son yi ya sauwake mata sai dai ta kasa sarrafa harshenta dan tana mutuwar son shi haka zalika tana son rayuwar iyayenta da ace matsalar a iya kanta zata tsaya da babu abinda zai hana bata sadaukar masa da rayuwarta ba tana kallonsa ya ciro wayarsa yana duba cameroring gidan daya saita a wayarsa."
Wani irin tsareta yayi da idanunshi yana kallon fuskarta ji yayi kamar alokcin khadija tai mata marin ,nan take kwayar idanunshi suka canza zuciyarsa ta dinga tuttukin bakinciki .yadda ya tsareta da idanunshi yayi matukar bata tsoro shi kuwa kallonta ya cigaba da yi yana jin zallar bakin ciki na ratsa shi ,bazai iya cigaba da danne wannan matsalar ba gara ayita ta kare dan bazai d'auki cima iyalinsa zarafi ko barazana ba wata irin zabura taga yayi ya mike tsaye tai saurin riko hannunsa jikinta na rawa "Ina kuma zaka ?wani kallo yayi mata mai firgitarwa wanda yasa ta sakar masa hannu da sauri ."fuuuuuu ya fice daga d'akin ta yunkura da kyar ta biyo bayansa sai dai a parlour'n ta tsaya tana Kai kawo ."kai tsaye d'akin da hajiya zulfa'u take ya shiga yana wani irin huci ya isketa tana zuge zip din akwatinta yanayin yadda ta gansa yasa tace lafiya ?"Ina son ki bar tafiyar nan a yau ?meke faruwa ka fa san tun jiya ya kamata na wuce ?ta kallesa tana neman karin bayani "nasani akwai gagarumar matsalar dake faruwa acikin gidan nan "subhanallah !"Allah ya rabamu da matsala "matsalar akansu shahida da khadija kuma Ina son ayi maganar kina nan idan ba haka ba zanyi abinda ran kowa zai 'baci koma ya raba zumunci gabad'aya ba damuwata bace ,daman ni tuni na cire kaina acikinsu ".
"wannan wace iri magana ce haka adamcy "?ka dinga hakuri da yan'uwanka batare da bata lokaci ba ya karanto mata duk abinda ke faru wa tun daga farko har zuwa yau din nan " karka zargi yanu wanka adamcy "aunty ba zargi bane gaskiyar da nake ta k'ok'arin boye ce akansu , Ina ruwansu da rayuwata ?"maryama zabina ce kuma duk duniya babu wanda ya isa yasa na rabu daita Allah ne kawai zai rabamu na hakura amman ba mutun ba" kalli kiga irin mummunar wulakanci da khadija sukai mata"ya fad'a jikinsa na kyarma ya fito da wayarsa ya nuna mata marin da khadija ta zabgawa maryama hajiya zulfa'u tace "Kai gaskiya basu kyauta ba". baiwarsu ce ko dan sun ga bata da hayaniya ?na rantse da Allah bazan yarda ba ".kayi hakuri lallai basu kyauta ba amman ka bari abi komai ahankali ai kamar ma basu wuce ba jirani bari naje na dubosu ayiwa tufka hanci "ta fita har da saurinta kasa cigaba da jiranta yayi ya biyota aiko suna nan zaune tare da mami suna zantawa suka ga sun shigo kamar an jehosu ."
wani irin mummunar kallo yake binsu dashi wanda yasa suka ji mummunar fad'uwar gaba mami ta kalli hajiya zulfa'u a tsanake sannan ta kalli adamcy dake tsaye yana huci kamar wani zaki ,hajiya zulfa'u tace "aunty ko zaki d'an bamu guri zanyi magana dasu shahida, mami ta mike tsaye ta shige bedroom dinta sai dai ta kasa kunnenta taji tautaunawar akan me ye inda hajiya zulfa'u ta zauna tana dubansu d'aya bayan d'aya kafin ahankali ta soma magana "khadija shahida me yasa zakuyiwa d'anuwanku haka ?" "me yasa zaku dinga cutar dashi a boye har kullum Ina fad'a maku matsayinsa da martabansa ya zarta na maryam a wajenku uwa d'aya uba d'aya fa ya wuce wasa "yanzu wani irin cutarwa yace anyi masa "?hajiya zulfa'u ta soma bayani kamar yadda adamcy ya koro mata "tana dasa aya aunty khadija tace "tabbas babu karya akan haka aka kulla aure kuma shi bai isa yasa mu janye kudirinmu ba ,mari kuma ta dinga shansa kenan muddin tana cikin gidan nan "Acikinku duk wanda ya sake marinta zan d'auki mataki kuma banga uban daya isa ya hana ba ta yunkura ta mike tsaye tana dubansa "yanzu ma ka d'auki mataki akan wanda nayi ma"...ai bata gama rufe bakinta ba ya sauke mata mari biyu ajere ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗
BOOK 4
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim
Page 18
"Wani razanannen kara aunty khadija ta saki tare da kurma ihu ta dafe kuncinta da hannu biyu saka makon kara data saki ne yasa jikin mami ya kama rawa, hakan yasa ta sake matsowa jikin kofar da sauri ta tsaya gabanta na wani irin fad'uwa,tana son fitowa amman tana jin tsoron abinda zai biyo baya dan tasan tabbas akwai abinda yake faruwa a parlour'n, cigaba da tsayu wa tayi agurin cikin tsananin tashin hankali sosai ta kasa kunnuwanta dan so take taji abinda ke faruwa. hajiya zulfa'u kam d'aya bayan d'aya take kallon fuskar kowannensu cike da tsananin tashin hankali. yadda aunty khadija ta dafe kuncinta tana kallon adamcy haka aunty shahida ta dafe nata kuncin tana dubansa amatukar firgice,hajiya zulfa'u ta kai hannunta goshinta ta dafe tana mai runtse idanunta cike da matsanancin bakin ciki abinda adamcy ya aikata."shi kuwa gogan ko d'ar bai ji komai ajikjnsa ba sai faman huci yake yana k'arawa yana kallon fuskokinsu ."
mami dake tsaye acikin d'akinta duk ta damu tace "meke faruwa ne?"me yasa khadija tai kara haka ?" tai wa kanta tambayr da bata da mai bata amsa sai su gashi so take ta fito taji ba'asi sai dai zuciyarta ta gargad'eta akan haka dan haka ta cigaba da tsayuwa sai dai ta k'ara kasa kunnu wanta sosai domin ta jiyo abinda zasu cigaba da tautaunawa dan tana jiyo wasu hirarsu wasu kuma bata jiyo wa ."aunty shahida ta kalli idanun aunty khadija jini ta gani akwance acikisu ."cikin tsananin tashin hankali ta matso kusa da aunty khadija ta sauke hannuwanta tana duba cikin kwayar idanunta "yanzu adamcy akan waccan banzar yarinya ka mari khadija haka ?" "karki sake ce mata banza dan ba banza bace." a d'an rikice mami tace "Khadijar ya mara kuma akan waccan yarinyar"? ta furta cikin tsananin tashin hankali ".
"akan wannan tsinanniyar yarinyar fa ka mari khadija ,khadija fa ka mara ? "wacece ita da ba zan mareta ba !"? "wallahi adamcy ka haukace ka zama rago ka zama wawa , ace akan wannan matsiyaciyar yarinyar tsinanniya zaka mari yar'uwarka lallai adamcy an gama da kai wayyo Allah ka cire adamcy a inda yake"babu ruwanki da inda nike kuma idan an gama dani meye damuwarki "?ya fad'a yana zabga mata harara"kasan Allah sai nayi mata dukan mutu wa kuma a yau din nan zata bar gidan nan dan kar shen aurenku yazo."tana gama maganar aunty khadija wacce gigita tasa ta dawo tamkar mutun mutumi a tsaye ta zube jagwab akan kujerar data tashi tare da sunkuyar da kanta kasa ta dafe cikin tsananin jimami.yayinda aunty shahida ta juya da sauri zata nufi hanyar fita da zumar zuwa ta samu maryama taci uwarta ,adamcy yayi saurin riko tsintsiyar hannunta cikin zafin rai yana cewa"kul shahida"!tsayawa tayi shiru tana kallonsa tana tunanin abinda kalmar" kul!din daya fad'a mata yake nufi "cikin zare idanu tace "adamcy kana hauka ne ni ka rike wa hannu tare da min gargadi ?". shima cikin zare idanu yace "ba iya rike hannun kad'ai zanyi ba in dai zai ta'ba lafiyar matata to zan iya ciresa gabad'aya in yi wurgi dashi ".ya k'arasa maganar da karfi tare da sakin hannunta yana huci kamar zaki ."wani irin asirtaccen murmushi aunty shahida tayi tare da kallonsa "ai ko zaka ga abinda zai biyo bayan wannan rashin mutunci da kayi mana"karki sake ki aikata abinda zakiyi dana sani sannan kina maganar maryama zata bar gidan nan akan wani dalili kenan zata bar gidan nan"?.ya fad'a yana kafeta da tsumammun idanunshi da suka gama canza kala tsabar 'bacin ran da yake ciki "."
"Kasan Allah bazaka cigaba da zama da yarinyar nan ba ko zaka mutu sai ka saketa"ke kanki kinsa ko sweetheart bata isa ta hanani son abinda zuciyata take so ba bare ku, ban aurin maryama dan na rabu daita ba, kuma bana tunanin akwai abinda zai sa na saketa sai dai mutuwa ta rabani daita amman muddin Ina numfashi a doron duniya Ina tare daita ."ware idanunta tayi sosai akanshi tana cigaba da kallonsa alokcin da mami ta gaji da tsayuwa ta samu guri ta zauna dafe da kuncinta dan Allah ya sani tana son fita tasan halin da ya'yanta suke ciki sai dai hakan nan zuciyarta ke gargadinta dan gabad'aya maganganunsu akwai rud'ani da tashin hankali aciki""Wallahi wallahi!!kinji na rantse shahida bazan canza maganata ba duk wanda ya sake ta'ba min lafiyar matata acikinku sai na masa rashin mutuncin da har ya mutu bazai manta dani ba zaman lafiyar mutun ya tsaya iyakarsa ".
"idan kuma ba'a tsaya iyakar ba fa me zai faru ?"tayi maganar cikin d'aga murya da zare masa ido" "ni duk zare idanunki da ihunki ba d'aga min hankali zai yi ba illa ku sakarwa matata kuruwa"okay kuruwarta ma muka Kama "?"sosai kuwa dan kun hanata natsuwa da samun kwanciyar hankali, kuma wallahi bazan d'auka ba duk abinda zaku yi ku tsaya iya kaina "ya k'arasa maganar yana nunata da d'an yatsansa "to ko nima zaka mareni kamar yadda ka mari khadija? cikin zare idanu da matsifa yace "ba zaki gane hakan ba sai kin ta'ba lafiyar maryama zaki ga yadda zanyi daku "."enough adamcy !"ya jiyo sautin sanyayyiyar muryar hajiya zulfa'u"ya isa haka!"ta sake fad'a tana dubansu d'aya bayan d'aya ".ke shahida samu waje ki zauna ,kai ma adamcy zauna tai maganar tana nuna masa wajen zama jiki a matukar sanyaye aunty shahida ta zauna kusa da yar'uwarta tana huci,haka shima adamcy cike da jin kai da kasaita ya matso ya zauna akan kujerar da hjy zulfa'u ta nuna masa ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya, haka ma hajiya zulfa'u zama tayi tana fuskantansu kafin ahankali tai gyaran murya ."
Ahankali damcy ya kau da kanshi gefe yana cika yana batsewa cikin tsananin fushi dan baya ma son ko kallon fuskokinsu ."ahankali hajiya zulfa ta fara masu nasiha tana basu hakuri tare da bawa su aunty khadija rashin gaskiyar akan abinda suka aikata, shima kuma adamcy tace yayi gaugauwar d'aukar mataki ai khadija yayarka ce duk abinda zata wa matarka bai dace ka zabga mata mari ba,amman duk ku taru kuyi hakuri ku yafewa juna komai ya wuce ." sai dai rufe bakinta ke da wuya cikin zafin rai aunty khadija ta d'ago idanunta da sukai jajur ta soma magana cikin zafin rai "aunty banki duk abinda kika fad'a ba amman kinsan Allah zaman lafiya a gidan nan ya kare bare wani sulhu a tsakaninmu kuma sakamakon marin da yayi min shine sakin yar iskar yarinyar nan ."da sauri adamcy ya juyo cikin tsananin tashin hankali "wannan kuma karya kike yi dan babu wanda ya isa ya rabani da matata ."
"a she kuwa zaka had'u da tashin hankali kala dabam dabam dan zan nuna maka karfin ikona yadda kake kare matarka kasan nawa mijin zai iya min fiyye da haka,idan kasan wata bakasan wata ba ka jira sabuwar jaridar da zata fito cikin satin nan na rantse sai na tozartaka "ahankali ya tashi ya mike tsaye yana kallonta a wulakance"bazan hanaku yin duk abinda zaku yi ba bissimillah ga fili ga mai doki "har yayi taku biyu yaji ance "adamcy dawo nan ! "muryar wacce yaji ne yasa wani irin azababben zufa ya fara tsatsafo masa a ilahirin jikinsa, ahankali jikinsa ya Kama rawa mami dake tsaye gabad'aya idanunta ta zuba masa cikin tsananin 'bacin rai ." ahankali ya juyo gabad'aya ya sauke idanunshi akanta yana kallonta da fuskarsa dake had'e dan ya rantse da Allah komai zai faru sai dai ya faru amman bazai d'auki cin zarafi ga maryamarsa ba "meke faruwa ne duk da naji wasu maganganu wasu kuma banji ba ?".