Kenza eBookz

Mar'adams book 4 - Chapter 45

Mar'adams book 4 - Chapter 45

Mar'adams book 4 Chapter 45: Mar'adams book 4 Chapter 45. wani murmushin mugunta ta saki sannan ta biyo bayansa tana magana tana taka step "ai muddin…

3,277 words

wani murmushin mugunta ta saki sannan ta biyo bayansa tana magana tana taka step "ai muddin maryama ta bar matsayin da take a yanzu ta dawo maka lallai ya tabbata talauci ajininta yake kuma ita da arziki har abada .sai abu na gaba sadam kana da yawon mantuwa anan fa mukayi aure da kai ba'a africa ba kayi singn nayi sign idan ka shirya rabuwa dani fine ni kuma na shirya makaka a kotu duk ta hanayr da kake son kabi dani zan bi da kai ko zaman lafiya ko akasa sinsa "bai tsaya ya cigaba da sauraronta ba ya cigaba taku yana jin yadda zuciyarsa ke sake d'aukar zafi ."ya shiga d'aki ya kasa zama sai zariya yake gumi na sake tsatsafo masa ta koina ajikjnsa .ta turo kofar ta shigo d'akin ta kallesa tana jin dadi acikin ranta ko babu komai a yanzu tana da makaman da zata yakesa ta hana rayuwarsa sukuni da samun kwanciyar hankali . maryama tayi aure idan ta tuna da haka wani farinciki ke mamaye zuciyarta sannan da hannunsa ya kar'ba kudin sakin maryama .wani sanyi taji ya sake ratsa ilahirin jikinta kuma duk tana da sheida a hannunta dan haka zata ga ta yadda zai mallaketa arayuwarsa tunda tasan bashi da wad'an makudan kud'ad'en dashi suka yi komai kuma dashi suka cigaba da gudanar da rayuwarsu kafin samuwar aikinsa kuma tayi imani maryama bazata rabu da mr ata ta dawo masa ba most especially ma idan taji abinda yayi ya waigo ahankali ya kalleta yana jin kamar yaje ya shake mata wuya ya kasheta ko ya huta da bakinci da tayi sanadin jefasa ciki amman kuma d'an cikinta fa?" ko bama haka ba bazai ta'ba iya kisa ba ."

"Kana kallona!ya d'auke kanshi yana jan tsaki ". "A kallon da kake min kana tunanin kasheni domin ka biyawa kanka bukatar ka ko ?"da zan iya aikata hakan zanyi amman bazan iya ba amman nadia me yasa kika yi wasa da hankalina da tunanin ?"me yasa kika yaudareni me yasa kika bari na kar'ba kud'ad'an nan ?"ya jera mata wad'an nan tambayoyin yana cizan lip's dinsa da karfi dan wani irin rad'ad'i azaba yake ji acikin zuciya dama gangar jiki "duk saboda Ina sonka ne sadam kasan zan iya rayuwa da kai ko baka da kowa baka da komai tunda kasan a baka da komai na fara sonka to kai mai yasa zaka canza raayinka bayan nasan ni kad'ai zuciyarka take so ."tsura mata idanunshi yayi yana kallonta yana nazarinta "tabbas yasan tana matsanancin son shi kuma zata iya aikata komai akanshi shima kuma yana sonta daga baya ne ya fara jin son maryama da tunanin komawa ga mahaifiyarsa wanda yasan hakin ummansa ne yayi saurin Kama shi.to shi yanzu menene mafuta agaresa ?" Yayi shiru yana tunanin yana son nemawa kanshi mafuta tun lokaci bai sake Kure masa ba ".

"Ka zaunar daita ka tsarata kawai ka nuna mata ka hakura da maryama wajen ummanka zaka tasan kana raye .kana ganin zata amince da haka ?"zaka iya gwada sa'arka mata kuma da karamin kwakwaluwa tsab zata amince idan ta kama ka sakin maryama sai kayi alabashi bayan ka furta sakin sai ka dawo daita tunda yasan shi Allah da zuciya yake amfani .wannan itace mafutar da zuciyarsa ta tsayu akai dan haka ya sake kallonta adaidai lokacin data mike tsaye ta haura kan gado ta kwanta tare da juya masa baya ."ya sauke numfashi ya karaso ya kwanta abayanta yana kokarin kai hannunsa jikinta tayi saurin mikewa zaune tana cewa "bana son muna furci menene haka kuma ?"I'm really sorry nadia kin san Ina sonki son maryama hakinta dana mahaifiyata ne Allah ya jarabeni amamn nayi tunanin hakura daita tunda har tayi aure ." numfashi kawai ta sauke ba tace masa uhm ba bare uhm ta sauko ta d'auko takarda da biro ta mika masa rubuta mata sakin anan tare da sa hannunka kana min haka magana ta kare zaka iya tafiya ."

"Yayi shiru yana kallonta daman yasa karshe abinda zata bukata Kenan daga garesa nan da nan kwakwaluwarsa ta shiga kai kawo "in dai har acikin zuciyarsa yasan da gaske ba sakinta zai yi ba koya furta bata saku ba sai dai idan yasan da gaske ya saketa to wannan fa ta saku dan shi saki koda wasa akayisa ya saku kuma ko batasani ba ta saku kuma duk randa labari yaje mata a sakè take daga ranar zata kama gabanta amman shi yasan a zuciyarsa ba sakinta zai yi ba neman mafuta yake kuma zai iya mata saki d'aya kuma ya dawo daita a take. ya sauke numfashi yace anything for you ya kar'bi takada da biro tace "saki uku zaka mata ya tsaya yana dubanta yace "ai kinsan a muslimci ba'a saki uku a take ko anyi amatsayin d'aya ne dan haka zan mata d'aya ." tai shiru tana tunanin can tace bari na tambaya ta mike tare da wayarta ta fita ta barshi cikin tsana nin tashin hankali bayan kamar minti goma ta dawo d'akin tace "ka rubuta d'ayan yayi kmaar yadda ta bukata ya mika mata ta nad'e takardar ta tura karkashin pillow ta rungunesa ajikinsa "ban ta'ba jin natsuwa da kwanciyar hankali irin na yau ba." ka faranta min sosai ka yafe min duk abinda nayita maka nayi saboda sonka da kishin ka ne" nasani nadia nima ki yafe min ai kai mutumin kirki ne, matsalarka wannan maryama din kuma tunda an rabu shikenan kowa ya zauna lafiya "yayi murmushi yana sakè had'eta da jikinsa ."a ransa kuwa yace idan kinsan wata baki san wata ba ko waye ya aurar min mata wallahi sai ya dawo min daita tunda addini ya bada zabi idan an nemi miji an rasa duk ranar daya dawo za'a bawa matar zabi ."

***** Maryama tana kwance akan gadon hospital kawai sai ganin maryam tayi ta shigo sanye cikin doguwar riga baka wacce aka yiwa stone work da pink stone a gaban rigar da hannun rigar tayi rolling kanta da mayafin abayar tayi kyau sosai ga wani kamshi da tunda ta shigo d'akin ya sauya yayinda khaira ke rungume a kafad'anta sosai tayi mamaki ganinta adaidai lokacin ."wani tsoro da matsanancin firgici maryam taga ya bayyana a kan fuskar maryama yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da karfi numfashinta ya soma barazanar d'aukewa cikin sanyin jiki ta yunkura ta zauna tana cigaba da kallonta still fuskarta d'auke da mamakin ganinta ."ta kara taku biyu ta tsaya nesa kad'ai da inda take tana shafa bayan khaira sannan ta motsa bakinta ahankali "maryama sannu ya jikin ?"wani sanyayyen ajiyar zuciya maryama ta sauke a fili sannan tace "Alhamdu lillah da sauki tana k'ara mamaki acikin zuciyarta.

"D'akin ya d'auki shiru tamkar babu wasu halitta aciki kowanesu da abinda zuciyarsa take kissa masa bayan kamar minti goma maryam tace "kiyi hakuri da duk abinda ya faru duk da nasan akwai matukar wahala ki iya hakura amman dai kiyi hakuri komai ya wuce na ari bakin gabad'aya 'yan uwana " maryama tace "babu komai dan ni a wajena komai ya wuce ."maryam ta had'iye wani tuttukin bakinciki da zazzafan kishin maryama dake makale cikin ranta ta cigaba da kallonta da kananun idanunta "ance kin rasa cikinki ko ?"maryama tai shiru tana kallonta tana tunanin abinda zata fad'a mata wanda ya jawo suka sakè d'aukar wasu minti goma sannan ta bud'e baki zatai magana sai ga likitoci sun shigo su uku suna cewa "good afternoon mrs adam ?!maryam ta d'an matsa kad'an domin basu dama suyi aikinsu dan taga suna kallon maryama wacce ta amsa da "afternoon! excuse us suka fad'a tare da duban inda maryam take tsaye."

fita tayi daga d'akin ta tsaya a bakin kofar d'akin tana zance zuci .""we have checked all your scan and checkups is all fine I hope your husband can be here in few minutes ?"ahankali ta gyd'a masu kai alamun "eh!"suka dubata sannan suka fita maryam ta sake shigowa d'akin "ki zauna mana !maryama ta nuna mata kujerar dake ajiye wanda an ajiyesa ne saboda mai kula da mara lafiya " ta girgiza mata kai alamun bata bukata sai dai tayi shiru tana kallonta tana tunani acikin ranta bata ga abinda ta fita wanda yasa yaya adam yake mutuwar sonta ,har ma ya iya rufe idanunshi ya kai yan'uwansa ga hukuma ba.wallahi ita dai a ganinta bata ga shararren kyawau da take dashi ba gashi ita din bakowa ba ,sannna ba diyar kowa ba ,wannan son da yake nuna mata itace tafi cancanta ya nuna wa ba ita ba amman tasan ita kam har abada sai dai ta hangesa daga nesa shiyasa ma tayi tunanin gara ta zubar da maka manta ta rungumi maryama din koda bata so ko hakan zai sa ya tausaya mata ."anya maryam kina ganin wannan mufutace agareki sai kinbi matarsa kafin ki samu shiga a wajensa ?"kyak kwar zuciyarta ta jefeta da wannan tambayar "hakika wannan ba mafuta bace ki tsaya a ra'ayinki dana yan'uwanki kawai gur'batacciyar zuciyarta ta fad'a mata haka ."

Maryam bata Jima da dawowa d'akin ba sai ga adamcy ya shigo turus yayi alokcin da kwayar idanunshi ya sauka akanta cikin tsananin tashin hankali yace "what are you doing here ?jiya ma naga sunanki cikin list din wad'an da suka zo me kika zo yi ?menene had'in ki da matata ?ya jera mata wad'an nan tambayoyin ajere ita kuwa tunda ta ganshi ta birkice tasan ta shiga uku a hannunsa "tamabayarki nake "what are you doing here!"tayi shiru tana kallonsa jikinta na rawa wata razananniyar tsawa ya buga mata yana sake tambayarta bakinta na rawa tace "na kawo khaira ne bata jin dadi shine nace na shigo na.." "enough!"ya katseta ta hanyar fad'ar haka nan take ta ji wani irin mummunar fad'uwar gaba ta dirar mata "ki tsaya iya limit dinki bana son shishigi kuma bana son ganinki a kusa da matata domin idan wani abu ya samu matata bazan d'aga miki kafa ba dan banga dalilin da zai sa ki fara bibiyar matata ba tunda ke kanki kinsan cewa muguwa ce kuma macuciya ce"yana gama fad'ar haka yace "leave !"ya nuna mata kofa da yatsan hannunsa yana huci ."

Mmn Sudais

MAR'ADAMS PAGE 31 "wani murmushi maryam ta sake saki tare da share hawayenta ta d'ago ahankali ta kalli mami dake goge nata hawayen"Ina son d'anki mami ina matukar son shi Ina ma zai soni kamar yadda nake son shi da yaji dadi arayuwarsa domin kuwa zan sadaukar masa da rayuwarta ta hanayr masa biyayya tamkar baiwa sai dai ya nuna ya fi karfi na?"tayi maganar a kasan ranta idanunta na sakè cika da kwalla"na rokeki maryam karki sake shi ga harkar adamcy da wacan yarinyar ko babu komai adamcy makiyinki ne kinga matarsa ma makiyiyarki ce"ita dai ce makiyiyata mami sabda mutun d'aya muke hari daita amman shi fa mami"?tai mata tambayr tana kallonta idanunta cike da kwalla "yaya ba makiyi bane a wajena bayan danganta akwai khaira a tsakaninmu duk abinda na aikata nayi saboda shi ne"karki sakè bana so dan yanzu baki ji yadda naji araina ba cike da sanyin murya tace "to mami kiyi hakuri in sha allahu bazan sakè ba ".tana gama fad'ar haka ta yunkura ta mike ahankali ta d'auki wayarta ta bar d'akin inda mami tabi bayanta da kallo cike da tausayawa"Allah mai yadda yaso sai ya jarabe ka da son abu ya kuma hanaka shi,Allah ka kawo wa maryam mafuta ka bata ikon cinye jarabawa.

"bedroom 'dinsu ta shiga tana zubar da hwaye ta haura gado ta tura wayarta a karkashin pillow ta kwanta kusa da khaira ta kamo yatsun hannunta tana kallo tana k'ok'arin danne damuwarta sai dai hawayen dake cikin kwarnin idanunta yaki tsayawa dan haka ta bar gogewa ta bar shi yana tsiyaya akan pillow ."ahankali taji wayarta tana ringin da kamar bazata d'aga ba saboda halin da take ciki sai kuma ta tura hannunta ta lalu'bo wayar tana dubawa sunan aunty shahida ta gani numfashi ta sauke tana goge hawayenta sannan ta mike zaune ta d'aga kiran cikin raunanniyar murya tace "hello aunty Ina yini ?"hello maryam lfy ya kike?"lafiya lau !ta fad'a tana kallon saman d'akin "mami tace ta sakè baki damar komawa gidan adamcy amman kin yanke hukuncin bazaki koma ba salim zaki auren?tace "eh aunty !." Aunty shahida ta numafasa kana tace "maryam garaje ba naki bane ki tsaya kiga yadda a sannu zamu tarwatsa rayuwar yarinyar nan , da duk wani munafukin dake zugata"gidan adamcy dake yafi da cewa ba da wannan yar matsiyatan ba .

maryam tayi shiru tana sauraronta batare da tace komai ba har ta dasa aya sannan tace "Aunty kuyi hakuri nasan kunyi iyakar kokarinku akaina kuma na gode maku sosai Allah ya bar zumunci amman Ina ganin ya dace zuwa yanzu kowa ya hakura ,ba kuma dan na daina sonshi ba wannan abu ne da bazan ta'ba dainawa ba har karshen numfashina da son shi zan mutu "shikenan zaki je gidan wani da son wani ?"ya zanyi aunty yaya adam yaki ni to the extended ya nuna wa duniya baya sona ba kuma zai soni ba kinga ko darajan khaira bana ci agurinsa kunga kona koma gidansa wahala kawai zan cigaba da sha zan auri salim kawai aunty. Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi arayuwata "ke dai karki yi gaugawa da saurin yanke hukunci tukun nan ki bamu lokaci dan wannan yarinyar sai ta bar gidansa dama aurensa gabad'aya.tana gama fad'ar haka ta katse kiran maryam tayi shiru rike da waya tana juya maganar aunty shahida ."

Bayan adamcy ya gama bawa maryama magani ya tashi zai bar d'akin "tai saurin riko hannunsa cikin nata tana murzawa tana kallon cikin kwayar idanunshi da nata idanun dake bukatar a tausaya masu dan tayi missing din jikinsa da komai nashi "menene kuma ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi yana karantar yanayinta dan kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin bukatarsa.ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana motsa bakinta ahankali "zumana na kasa gane kanka ." me yasa kake son rayuwar aurenka ya fita raina? ya kamata ka hakura ka manta komai mu cigaba da zamanmu kamar yadda muka faro ."zare hannunsa yayi cikin nata yace"baki san halina bane that's why maryama". "nasani mana!.ta fad'a batare da ta d'ago ta kallesa ba sannan ta sauko daga kan gadon ta tsaya abayansa jikinta yana gugan nashi "kana da kirki sosai amman baka da saurin yafiya amman kasani banyi laifin komai ba ".alright tunda baki yi laifi ba ki cigaba da tsayawa akan haka "tunda ka aureni na ta'ba maka abinda ya 'bata maka rai ne ?"no amman kin bari gangancinki yasa cikina ya zube" ya fad'a tare da juyowa ahankali ya zuba mata idanunshi "kin d'auka aure suna ne kawai ?ko kin d'auka aure sex ne kawai ?wai a gidan nan ake takaki ake wulakantaki har wacan yarinyar tasa hannunta ajikinki tana k'okarin miki illa amman kika min shiru saboda ko kasheki suka yi baki da asara ."

Ta sauke numfashi da ajiyar zuciya atare tana d'ago kanta ta zuba masa shayayyun idanunta "Haka fa aka dinga shirya makirci akan kiyi auren wucin gadi dani ,wannan tsoron naki yasa kika amince kuma kika kasa fad'a min har sai da asiri ya tono ,ki sani acikin horon da zan miki ban miki komai ba domin sex ma da kika ga Ina yi dake all the time sa kaina nayi yanzu kuwa no sex no romance no fellings kinga I only love you understand "ya fad'a yana kara matsota tare da zura hannuwansa duka cikin aljihunsa yana kallonta da tsumammun idanunshi muryarta na rawa tace "na fahimta amman kayi hakuri dan Allah .."ai hakurin bashi da wani amfani a wajena yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi kofar fita ."tabi bayansa da kallo tana furta kalmar"inna lillahi har ya fice daga d'akin tana tsaye gabad'aya ta rasa me zata masa dan laifi kam yanzu tasan tayi laifi amman ita saboda gudun abinda zai faru ne yasa bata iya fad'a masa komai .amman shi gashi ya kasa fahimtarta ."

yana shiga d'akinsa ya sauke numfashi ya kai hannu jikin rigar jikinsa ya cire nan take murd'adden jikinsa ya bayyana ya ajiye rigar ya k'arasa ya bud'e bedside ya ciro kwalin sigari ya bud'e tare da ciro kara d'aya ya kai bakinsa ya kunna ya fara zuka ahankali yana fesar da hayaki cikin mintuna da basu wuce shabiyar ba ya tashi da kara uku ya kai na hud'u bakinsa ta shigo d'akin cikin sanyin jiki ta tsaya ajikin kofar d'akin ta tsura masa idanunta tana kallonsa zuciyarta na wani irin tafasa kamar ta k'arasa garesa ta cire karan sigarin ta far fad'a masa mgn sai dai ta kasa k'arasa inda yake bare ma ta aiwatar da abinda yake ranta kallo d'aya yayi mata ya d'auke idanunshi akanta ya zuge zip din wondonsa ya soma cirewa yana tafiya yana zukar sigar har ya shige bayi ."wani wahalallen numfa shi ta sauke da karfi tana dafe goshinta da hannu d'aya "ya rab ka kawo min mafuta wannan bawa naka so yake ya kasheni ."yana shiga ya kunna shawa ahankali ruwa ke sauka ajikjnsa ya kai hannu wansa duka saman fuskarsa yana wankewa kwata kwata bai ji motsin shigowarta ba sai jinta yayi ajikinsa ta rungumesa ta baya tare da kwantar da kanta a lafiyayyen bayansa jikinta d'aure da farin towel iya cinyarta .

juyowa yayi da sauri yana janye jikinsa daga nata yace "what are you doing here ?tai shiru zuciyarta cike da matsanancin tsoro da tashin hankali take kallonsa kamar ranar ta fara ganinsa ya matsota sosai ta mannu da bangon bayin hannuwanta duka ta kai daidai nipples dinsa at the same time tana kallon faffad'an k'irjinsa da ruwa ke sauka "i want you to give me a child again ta fad'a tana murza kan nipples dinsa zuwa gefen fuskarsa ."ahankali yabi yatsun hannunta da kallo jijiyarsa na mikewa ,zai kawar da fuskarsa gefe tai saurin tsaidaita suna kallon juna "I want to have your baby zumana wallahi a shirye nake dana sake samun wani ciki." ta fad'a tana kai bakinta ta had'e da nashi ta soma tsotsa bakinsa shiru yayi yana jin yadda take sarrfa bakinsa nan take komai na jikinsa ya fara sauyawa kamar zai bata had'in Kai sai kuma ya fixgeta daga jikinsa ya rike damtsen hannunta duka biyu wanda yasa hantar cikinta kadawa."bakiji abinda na fad'a miki bane bazan sakè kusantarki ba ,ko ance miki maye ne ni ?"ko dan kinga Ina yawon having sex dake kike tunanin saboda shi na aureki da kike son kija hankalina dahi ".

"amman ai ni matarka ce "so what ?"ya kamata ka dinga saka tausayi cikin zuciyarka "ai kin dade da sanin zuciyar dutse gareni "ya fad'a yana tamke fuska wato maganar data ta'ba fad'a masa abaya"amman ni Ina bukatar .."no sex I only love you. ya fad'a a tsawace "yasan yayi mata mugun horo mai tsananin wahala ,yayi mata horon da bazata iya hakura dashi ba haka zalika bazata iya yarda da kowa ba bayansa"wannan wace irin rayuwar zamuyi ?irin wacce kika zabar mana ita zamuyi.ya fad'a yana sakin hannunta ya tokare bangon bayin dashi fuskarsa na kallon nata Allah ya sani kawai daurewa yake amman gabad'aya ilahirin jikinsa suna bukatarta da mararinta ta tsura masa ido kamar yadda ya tsura mata sai daya gama kallonta ya d'auki towel ya fita ya barta tsaye rungume da hannuwanta a k'irji duk ruwa ya jikata da towel din jikinta "kayi hakuri nasan ka damu dani ne amman banason kana samun matsala da yan'uwanka ne yasa bana fad'a maka abubuwa ta fito cikin sanyin jiki taga har ya gama shirin bacci ya kwanta ya dafe goshinsa da mararsa ."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull