Kenza eBookz

Mar'adams book 4 - Chapter 44

Mar'adams book 4 - Chapter 44

Mar'adams book 4 Chapter 44: Mar'adams book 4 Chapter 44. bayan maryama ta gama had'a kayanta ne fa ta fara jin ciwo na ratsa mararta sosai dan haka ta…

3,261 words

bayan maryama ta gama had'a kayanta ne fa ta fara jin ciwo na ratsa mararta sosai dan haka ta shiga bayi nan fa hankalinta yayi mugun mugun tashi ganin yadda jini ke fita daga jikinta har da guda guda wani rikitaccen kuka ta fashe dashi tana d'aura hannuwanta duka a saman kanta "shi kenan na rasa cikina gashi kuma tasan tunda ya furta sai ya mata rashin mutunci tabbas bazai barta ba sai ya ci kani yarta,wani irin murd'awa mararta tayi da sauri ta kai hannuwanta duka ta dafe cikinta tana murkususun ciwon mara,rarrafe ta fara acikin bayin tana tunanin yadda zatayi ta gudu ta bar gidan kafin ya dawo ya sameta ."da kyar ta mike ta dafe bangon bayin ta dinga jan jiki ga jinin na tsiyaya ajikinta hankalinta ya sake tashi gabad'aya ta kasa amfani da komai domin tare jinin sai dai hannuta na dafe da mararta dake mata wani irin azababen ciwo .da kyar ta samu ta fito daga bayin,ta zube kasan d'akin tana sakin numfashin wahala,har lokacin jinin dake zuba a jikinta bai tsaya ba tana kuka tana kiran wayyohhl Allah cikina zan mutu muryarta da gangar jikinta duk rawa suke cikin haka ya shigo d'akin ya isketa kwance cikin jini dafe da cikinta da kyar ya iya furta sunanta da karfi. "maryama "! "meyasa kika min haka?" nace me yasa kika min haka? me yasa kika sa bakinki ?ita kuwa kuka take sosai tana jujjuya kai, yayinda hannuta duka ke kan cikinta tana murkususu ciwo kmr ranta zai fita jini kuwa sai malala yake ta kasanta bai san sanda ya buga mata tsawa yana sake furta"me yasa zaki min haka maryama ?tamkar zaki ya' karaso gareta ya d'agata tsaye zai kai mata gigitaccen mari".

tace "dan Allah karka mareni ka barni da azabar da nake ji"wani iri yaji a gabad'a ya ilahirin jikinsa wanda yasa yaji ya kasa marinta .yayinda rashin kwarin da babu ajikinta yasa tayi kasa ta zube cikin matsanancin ciwon mara da sauri ya durkusa a gabanta ya kai hannunwansa duka ya tarairayota ya manneta ajikinsa ya zuba mata idanunshi kamar zai yi kuka dishi dishi take kallonsa da idanunta da suka gama canzawa tsabar azaba."a haka doctor ta shigo ta samesu. Ahankali ta karasa gabansu tana kallonsu a fusace yace"kin ja kin tsaya,I think abd ya kawoki kenan ki duba min ita ?tace "sorry sir dama nake jira abani, a zafafe yace" ki duba min ita nasan halin da take ciki"ta d'an tsugunna tare da daga hannuta tana jin yanayin numfashnta sannan ta fito da kayan aiki cikin kwarewa da iyawa gurin aikinta.ahankali tasoma hada allurar da zata mata da kyar doctor ta somu jinin dake siyaya ajikin ya tsaya ."idanun maryama a rufe suke sai dai tana jin duk taimakon da doctor take mata da maganar da adamcy yake furtawa " meyasa zaki bari damuwarki ta zubar min da ciki na ? yayinda ita kuma take furta "wayyo Allah cikina mutuwa zanyi ka tamakamin " ji yayi kamar ya zuba mata lafiyayyun marukan ko zai samu sau sauci"luuuf idanunta suka rufe tana sakin numfashin sama sama ga azabar ciwon dake nukurkusanta ga azabar tashin hankalin da kalaman adamcy ke sakè jefata ciki tunda take bata ta'ba ganinsa cikin yanayi makamancin na yau ba.idanunshi sun kada sunyi jawur gabadaya jikinsa babu inda baya kirma tsabar tashin hankali da yake ciki muryarsa na rawa yace" doctor cikin ya fita ko "?ya fad'a yana kai tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa."

"bazan tabbatar da haka a yanzu ba sai mun dangana daita hospital zamu tabbatar da komai ta hanayr duba mahaifarta duk da ita a tunaninta a yanayin yadda ta zubar da jinin cikin ya fita sai dai wani ikon Allah,da kyar ya iya cire tafin hannushi yana kallon fuskarta hawaye ne kwance acikin kwayar idanunshi ya d'agata ya rungumeta ajikinsa muryasa na rawa yace" maryama me yasa zaki min haka ? yana tafiya yana kallon face dinta ya nufi kofar fita daita ." Suna isa hospital likita ta soma aikinta sai dai cikin kankanin lokaci ta gano cikin jikinta ya fita ta dawo d'akin da take kwance bata ga adamcy ba ta tsaya akanta tana kallonta kwance tana sauke numfashi ahankali "wasu matan dai suna da sa'a a rayuwarsu. karamar yarinyar daita amman kuga yadda tayi saa shahararren d'an kasuwar nan ke ji daita kallo d'aya zaka masa ka fahimci zallar son da yake mata tsagwaron so ne wanda babu cutarwa acikinsa ." tana k'okarin fita daga d'akin shi kuma yana k'ok'arin shigowa tayi saurin dawowa cikin d'akin inda ya zubawa maryama idanunshi batare da yace komai ba ,ahankali doctor ta soma masa bayani cikin sanyi murya"cikin ya fita ko?"ya fad'a yana ciza lip's dinsa da karfi tace "kayi hakuri yalla'bai ya fita sai dai fatan Allah ya bada wani rayayye mai albar.."tun kafin ta k'arasa maganarta ya runtse idanunshi da karfi yana sakè ciza lip's dinsa ."ahankali ta juya ta fice daga d'akin da kyar ya soma neman number umma bayan ta d'aga da kyar ya iya bud'e bakinsa yayi mata bayani halin da maryama take ciki aiko ta rikice yace ta shirya zai turo azo a d'auketa yana gama fad'ar haka ya jawo kujera gabanta ya zauna tare da riko hannunta cikin nashi ba'a d'auki lokaci ba umma tazo dan haka ta maye gurbin sa shi kuma ya wuce police station dan tun awanni uku da suka gabata yake samun kira ta bangaren dabam dabam acikin yan'uwansa koda ya isa station ya cika makil da yan uwa duk wanda ya bud'e bakinsa acikin yan uwa cewa yake ban da halin adamcy wannan case din ai na gida ne a gida ya dace ayisa ."

Har sanda adamcy yazo alhji kabir bai sakè d'aga kiran aunty khadija ba dan tana fad'a masa abinda ya faru yace babu ruwansa" nan fa hanka linta ya soma tashi sai dai ta dake taki nuna damu warta. gabad'aya zaune suke a Office din commissione yayinda adamcy ya bala'i had'e rai aka bukaci ya fara magana a natse yayi bayani komai da yayita faruwa yace "gasu nan babu wacce ban kira mijinta acikinsu ba amman suka d'auki maganata banza gashi a yau sun zama sanadin dana rasa gudan jinina "me nayi maku da yasa kuka zabi ku min haka ?kun zubar min da cikina "aunty khadija ta sauke sanyayyen ajiyar zuciya tace "ka dai zubar da abunka "ni yanzu banason Jin komai commissione take us to court" aunty khadija tace "sai me muje mana wake jin tsoron shari'a "amar yace " aa aunty khadi kiyi shiru karki sake cewa komai saboda sulhu ake nema. cikin haka alhaji bashir ya shigo customer controller ne na jahar lagos kuma miji ga aunty shahida."

cikin haka alhji kabir ya Kira commissioner yace yasa wayar a handsfree ya soma bawa adamcy hakuri yana kuma tabbatar masa shi dai zai d'auki mataki akan matarsa "takama take da matsayinka ni kuma zan nuna mata kafafuna suna da tsawon daya fi na mijinta "ba sai anyi haka ba amar ma ya saka baki yana bashi hakuri sai dai fur adamcy yaki"kun sa fa matsalarsa taurin kai awa mutanen farko inji cewar salim ya waigo inda yake ya watsa masa kallon banza. juyin d'uniya akayi dashi yace wallahi sai anje kotu idan kuwa har sai anje kotu ai babu makawa anan zasu kwana.nan fa hankalin maryam yafi na kowa tashi dan ma salim ya kawo mata khaira ta sha nono ."aka kira baba babba shima yace ai hjy zulai ta kirashi bazai zo bane kuma bazai kira adam ba ai sai daya fad'a masu sukai kunnen uwar shegu da maganarsa suna taimaka da mazajensu to sai suyi amfani da karfin ikon su su fito dasu ".

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun hisham ya furta adaidai lokacin da adamcy ya mike ya fice abunsa yana waya "Aunty khadija ta kalli aunty shahida tai mata rada a kunne"kin wani daga hankalinki ki kwantar da hankalinki bafa zamu kwana anan ba, ni wallahi ko kwana nayi bazan yi takaici ba tunda cikin shegiyar yarinyar nan ya zube ."Kus kus haka sukai ta magana hisham yace "bari na kira momy ko idan tasa baki zai ji aiko itama tace babu ruwanta har karfe goma na dare mami sai faman Kira waya take taji halin da'ake ciki amman babu wani bayani sai ce mata sukai magana ake zuwa anjima za'a sallamesu zabiba kam ta sha kuka har ta gaji idanunta sun kunbura "bakincikin ta wai yau danuwansu wanda yafi kowa so da kaunar su shine ya zama silar kawo yan'uwanta hukuma wannan wacce irin rayuwa ce."?

Abu fa kamar wasa dare ya fara hankalin kowa na sakè tashi alhji kabir ya sake kiran commissioner sun jima suna waya yace shifa gaskiya kar ya bari matarsa ta kwana a gurin.ya d'aga kafa ne saboda adam danuwan matarsa ne if not shima yasan zai iya amfani da matsayinsa na commissioner wannan haka yake amman dake case din na gida ne dole ayi hakuri ai saboda kai nima na tsaya da yanzu na Kama gabana suna gama waya alhji kabir ya kira adamcy bai wani tsaya bashi hakuri ba yace "kaga kaje ka janye case din"adamcy yace akan wani dalili ne kenan zan janye case ?" "saboda bazan d'auki wulakancin ga matata ba wannan ma ai tozarci ne "aikin banza kawai ni kuma abubuwan da sukai matata ance maka zan d'auka ne ?bari kaji idan zaka zama cikakken namiji a gidanka ka zama idan kuma zaka cigaba da zama lusari ne fine amman ni ba a haifi matar da zan fad'awa magana taki bi ba ko na kafa mata doka taki ba, babu wannan matar matsayi kake takama dashi to bissimillah kayi amfanin dashi ni kuma zan biyo maka ta sama adamcy yana fad'a shima alhj kabir yana fad'a."

cikin haka direban mami ya kawota itama tayi kuka kamar me hisham ya sake kiran mumy "dan girman Allah kisa baki mumy a halin yanzu nayi imani ke kad'ai ce zaki masa magana yaji dan girman Allah mumy kinsan halinsa sai ya bari su kwana anan kinga kuma hakan ba daidai bane da kyar aka shawo kanta ta kirasa tana bashi hakuri yayi shiru yana sauroronta har ta dasa aya yace "shikenan mumy sunci darajanki wallahi if not da sai dai mu had'u a kotu tace "aa baza'a yi haka ba yaron kirki allah yayi maka albarka kayi hakuri da yanuwanka Allah kuma ya sake bamu wasu baby's rayayyu masu albarka ka gaishe min da maryama zan kirata zuwa gobe in sha allahu Allah yayiwa rayuwarka albarka yace "ameen! "na gode daka mutuntani suna gama wayar ya kira commissioner alokcin hankalin kowa ya kara tashi yan uwa kowa yayi curko curko adare aka sallamosu akace su rubuta undertaking akan bazasu sake shiga lamarinta ba aunty khadija tace bazata rubuta ba sai aunty shahida ce ta rubuta ."

maryama dai batasan iya awanni nawa ta kwashe a hospital ba ita dai ta farka karfe d'aya na rana ta ganta kwance a gadon hospital ganinta kwance a dakin hospital yasa ta fashe da wani matsanancin kuka tana kiran sunan Allah cikin haka ta soma jiyo kamshin turarensa da motsin shigowarsa take tayi shiru ta hadiye kukanta.tana ganinsa ta hau rawar jiki ta sunkuyar da kanta kasa tana son ta rokesa sannan ta bashi hakuri amman bakinta ya kasa furta hakan " jikin bango d'akin ya k'arasa ya jingina jikinsa tare da zuba mata tsumammun idanunshi batare da yace komai ba sai dai zuciyarsa ban da tafasa babu abinda take "wato bazata ce masa komai ba ita kuwa duk hankalinta a tashe yake shirunsa ya sake d'aga mata hankali.kusan mintuna talatin yana tsaye yana kallonta sannna ya soma magana"na gode sosai maryama ,shiga cikin abinda bai shafeki ba ya janyo min asara na rasa d'ana ko 'yata amman kisani zaki girbi abinda kika min "sai daya mai mata mata haka har sau uku sannan ya fice daga d'akin yana huci ".

"Inna lillahi wa inna lillahi rajiun kawai take furta wa tana maimaitawa a fili yayinda take Jin wani irin mugun zafi da ciwo "da gaske ta rasa cikinta? "mike wa tayi zaune ta had'e tafin hannu wanta duka waje d'aya tana kuka "dame zataji da cikinta data rasa ko kuma da fushin daya d'auka daita ?tana cikin wannan halin umma ta shigo d'akin da sauri ta karaso tana cewa "ke kuma daga tashinki sai kuka? "umma .." sai kuka yaci karfinta ta kasa cigaba da magana umma tace "kiyi hakuri Allah zai baki wasu masu albarka."ba rayayye bane shiyasa kuka rasa ta rungu mota tana shafa bayanta tana rarrashinta ." Kullum adamcy zai zo ganinta akalla sau biyu amman babu wata magana dake shiga tsakaninsu kota gaishesa baya amsawa ita kam tarasa mene ne laifinta, ba wani abu tayiwa cikin ba daya d'auki fushi daita ,idan ma sanadi ne ai shine ya janyo ta rasa cikinta , dan haka itama ta fita batunsa ta d'auki fushi dashi ko yazo bata ma kallonsa har sai taga idanun umma ne take sakin fuska idan ta fita kuwa had'e fuska take har ya gaji ya wuce ."

adaidai wannan lokacin idan akwai abinda take so be wuce ta samawa kanta mafitar da zata kubuta daga fushinsa ba sai dai babu fuskar da zata samu sausauci ,lumshe idanu tayi da karfi lokaci guda ruwan hawaye dake kwance a tsakiyar idanunta suka fara zubowa cikin tsananin tausayin kaina.tambaya daya ce ke damunta da har yanzu ta kasa samun cikakkiyar amsar da zata gamsar da kanta ,"shin ta ya zai d'aura mata laifi har ya dinga mata barazana da fushinsa ,wallahi sani ne bai yi ba amman fushinsa na raunana zuciyarta .wani kuka ta fashe dashi umma tace "dadina dake raki da son kuka yanzu sabida Allah bazaki hakura da kukan nan haka ba Ifyrki fa itace komai cikin kwana nawa zaki sakè samun wani indai ciki ne sai kin gaji dashi ". Maryama ta share hawayenta tana shesheka ita fa umma duk tunaninta saboda tayi barin cikin ne batasan damuwarta ta mijinta bace shiru tayi batare da tace komai ba taci gaba da tsiyayar hawaye ahankali ta gyara kwanciyata tana tunanin had'uwarsu dashi gobe a gida tunanin take sosai most especially maganarsa ta karshe a ranar da abun ya faru "wallahi wallahi kikayi gigi wani abu ya samu cikin nan zan bala'i canza miki maryama zan miki abinda har ki mutu bazaki manta dani ba canzawa kam ta gani sauran abinda zai mata da har ta matu bazata manta ba Anya kuwa zata koma gidan ko dai tabi umma zuwa gida?to a gidan ma nashi ne!ta zabga tagumi tana sauke numfashi ."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 4

AYSHA A BAGUDO WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Page 30

Sadam dake kwance akan doguwar kujera yaji an watsa masa hotunan a fuska,sama yayi da kwayar idanunshi yana duban nadia dake tsaye akan shi tana faman cika tana batsewa,ahankali ya mike zaune tare da dawo da idanunshi kasa yana kallon hotunan data yayyaga sosai gaban shi ya tsananta fad'uwa k'irjinshi na dokawa da wani irin k'arfi. hannunshi na rawa ya kai kan yagaggun hotunan yana dubawa a nutse hotunan daya sha wahala ya bari akayi masa print dinsu ne duk tama wulakancin haka ?"dan gabad'aya tayi masu kaca kaca idan ba wanda yayi wa maryama mugun sanin gaske ba ba zai ta'ba gane itace ba .cke da tarin damuwa ya sake d'agowa ya zuba mata kwayar idanunshi cikin 'bacin rai batare da yace mata komai ba "sadam !"ta kira sunansa tana jin fad'uwar gaba mai tsananin "still kallonta ya cigaba da yi "bafa zan juri wannan iskancin a gidana ba ,ko da yake idan ma ba hauka da toshewar basera irin naka ba banga ta inda matacce zai zauna yana 'batawa kanshi lokaci ba." kayi maza ka dawo tunaninka domin kuwa abinda kake hangowa kanka yayi maka nisa kuma har abada bazai dawo gareka ba gara ma tun wuri ka zauna ka shiga hankalinka sannan ka daina tunanin zaka dawo da abinda ka rasa sannan duk abinda ya faru recording video's din yadda kayi mutuwar karya yana nan a gurina kuma zan bayyanasu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso ,sannan ga babban albishiri a halin yanzu maryama matar aure ce "

sakè tsareta yayi da idanunshi kafin ahankali ya soma furta kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..! yana goge gumi d'aya rufesa alokci guda hankali ya b'alle mab'allan gaban rigarshi saboda zafin da yaji yana ratsa har cikin b'argon shi lokaci d'aya kuma jikinsa ya kama rawa"ya rage naka ka cigaba da rayuwar a sabuwar duniyarka ka manta da abinda ya faru abaya ko kuma ka zauna kana tuna nin abinda ka rasa rashi kuma na har abada "shiru yayi yana sauraronta har ta dasa aya gabad'aya yama rasa abinyi ya rasa me zayyi."maryamarsa ce tayi aure ?"ya tambayi kansa cikin tsananin firgici da tashin hankali. "yes tayi aure tana gidan mijinta idan ma da rabo watakilla zuwa yanzu ta samu, dan haka life goes on ka saki ranka kazo mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka tsara .bai san a fili yayiwa kan shi tambayr ba sai da yaji amsar data bashi "anya kuwa abinda nadia ta fad'a gaskiya ne?"aiko idan ya kasance gaskiya ne ba'a ta'ba fad'a masa abinda ya girgiza zuciyarsa ba sai yau .har ta juya tayi taku biyu ta tsaya tare da juyo da fuskarta kad'an tana masa murmushi wanda kana kallo kasan na mugunta ne ."

"Ka tuna yadda aka shirya komai akan mutuwa rka?"kika shirya komai dai!"ya bata amsa a zafafe yana huci yana jin kamar ya tashi ya rufeta da duka .tai murmushi"okay naji amman ka tuna ka amsa makudan kudad'e akan zaka saki mryama?" yayi shiru yana kallonta jikinsa na rawa "nasan duk ka manta da hakan ?"ta cigaba da magana tana kallonsa abun na mata dadi "ka amshi maku dan kudi kuma kace saki mai sauki ne amman bayan mun dawo gida babu yadda banyi da kai ba kace na baka lokaci zaka saketa amman kaki sbd munafurci irin naka "saurin runtse idanunshi yayi da karfi yana jin bugun zuciyarsa na karuwa "ko kasan su waye wad'an da suka bada kud'aden nan ?"ya bud'e idanunshi da sauri ya zuba mata kawai yana kallonta yana jiran ta fad'a masa ko su waye sai dai yaga tayi dif tana cigaba da yi masa murmushi wanda yayi masa lakabi da harsashi dan jinsa yake tamkar harbinsa dashi take ."

"tunda yake ba'a ta'ba yaudararsa anyi wasa da hankalinshi da tunaninsa irin wannan ba a iya tsayin rayuwarshi, lallai nadia tayi wasa da rayuwarsa kuma muguwa ce ,mahainciya ce kuma makiyiyarsa ce sa'banin yadda take nuna masa duk duniya tafi kowa son shi ahankali ya mik'e tsaye ya nufi fridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi ya kafa a bakinsa. sakamakon makoshinsa daya ji ya bushe ,sai daya sha sosai sannan ya cire robar daga bakinshi tare sauke ajiyar zuciya da k'arfi yayi wurgi da roban yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa sannan ya nunata da d'an yatsansa "daga kaina kin gama rainawa kowa hankali nadia,in sha Allahu koda zan rasa raina ,koda zan rasa komai sai na dawo da maryama tunda dai har yanzu ban furta mata kalmar na saketa ba, sai na dawo daita rayuwarta idan zaki zauna daita fine idan bazaki zauna ba a shirye nake dana rabu dake nayi rayuwa daita ban san me ya faru dani ba da nayita biye miki amman nayi danasanin mara misaltuwa hatta had'uwa dake Ina danasaninsa a yanzu ".yana gama fad'ar haka ya ra'ba ta gefenta ya haye sama."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull