Mar'adams book 4 - Chapter 43
Mar'adams book 4 Chapter 43: Mar'adams book 4 Chapter 43. "ni masoyinki ne na gaskiya, ina da yak'inin nafi kowa sanki maryama bazan so nayi abinda zai…
3,229 words
"ni masoyinki ne na gaskiya, ina da yak'inin nafi kowa sanki maryama bazan so nayi abinda zai cutar dake ba I m sorry "to ni me kaji nace da kake ta faman bani hakuri ko nace kayi min laifi ne ?" tai mgn kamar zata sakar masa kuka suna makale da juna sai can yamma ya riko tafin hannunta cikin nashi ya tsarke yace suje kasa ta d'an mike jikinta bata masa mutsu ba suka sauko zuwa kasa ya zaunar daita akan kujera yasa masu aiki suka kawo mata Kayan fruit iya wanda mai ciki zata iya ci da kanshi ya dinga bata cikin haka Maryam ta fito daga bangaren mami cak ta tsaya tare da zuba masu ido tana kallonsa duk ya wani dawo tamkar bawa agaban maryama ."nan take idanunta suka cika da ruwan hawaye wani dogon ajiyar zuciya ta dinga saki har ana iya ganin yadda jijiyon makogoronta suke mikewa saboda tsananin zafi da zuciyarta take hankalinta bai tashi ba sai data ga ya kwantar daita a saman cinyarsa yana shafa cikinta cikin tsananin kad'uwa jikinta ya Kama rawa shi kuwa adamcy da bai ma san da zamanta da rayuwarta acikin gidan ba."sakè kwantar da kai da murya yayi sosai luf luf dashi yana fad'a wa maryama kalamai masu sanyi da kwantar da hankalin" Ina sanki fiye da son da nake wa kaina ,kece burin zuciya ta ki kalli cikin idanuna babu abinda zaki gani face tarin soyayyarki dake neman illatani, yadda kika bani jan ragamar rayuwarki a tafin hannuna ni kuma nayi miki alk'awarin bazaki tab'a yin nadamar yin rayuwa dani ba, ya k'arasa maganar yana had'e tazarar datai saura atsakaninsu cikin salon d'aukar hankali ya lumshe idanunshi da goga kumatunshi a saman fuskarta muryarshi can k'asan makoshi wanda sai kayi da gaske sannna zaka iya fahimtar abinda yake fad'a"an halicci ruhina da soyayyar ki maryama a kullum burina mu mutu tare bana son na barki wani ya aureki kuma banason rabuwa dake ."hawayen dake gangarowa a saman kuncinta yasa harshenshi yana d'auke mata su,ahankali ta lumshe idanuwanta hawayen na sake gangaro wa, ta sallama mishi kanta tasan bata da zab'i bata da wani abunyi daya wuce ta mika masa rayuwarta gabad'a ya kuma ta rigada tayi haka amamn tana jin tausayinsa soyayyar da yake mata tayi yawa kuma ko tace ya rage haushinta yake ji tana jin yadda yake sake shigewa jikinta yana manne mata, cikin salo ya had'e bakinsu ya soma sucking din lips d'inta while yana tura mata harshenshi cikin bakinta ai da sauri maryam ta juya ta koma tana haki zuciyarta na wani irin mugun bugawa da karfin gaske "
wani irin deep kiss adamcy yake yi mata mai rikita kwakwalwa da hargitsa lissafi ya manta da inda suke dayake a hannu yake cikin k'ank'anin lokaci ya rikice ya birkice ya d'imauce,ya soma fitar da nisha akai-akai kamar wanda yayi gasar tseren gudu, tana jin yadda yake wasa da sassan jikinta amma babu yadda zatayi,jin zai zame rigar jikinta domin ya kai hannu saman boobs d'inta a fili ta fitar da wahalallan numfashi tace "ka bari mana ko ka manta inda muke ne ?"bai tsaya ya sake jin mai zata sake cewa ba ,cak ya d'auke ta yayi sama daita tun daga parlour'n ya soma rabata da kayan jikinta daga ita sai pant ya hau saman bed da ita, sosai yake romancing d'inta a gaggauce, saboda yadda ya k'agu bai tsaya yin long romance ba, ya jefa kwallosa a raga, sakaka ta sakar mishi jikinta aiko yayi yadda yake so daita sosai ta bashi had'in kai kusan a tare suka yi releasing, ya kwanta saman ruwan cikinta yana mayar da numfashi yana kissing sansar jikinta ita kam ta soma zuba masa raki bayanta ciwo mararta ciwo ya tsaya yana kallonta yana murmushi "okay bayan kin gama Jin dadin zaki fara complain?allah da gaske nake Jin abinda ta fad'a ya sauka akanta ya soma massaging din jikinta ."
*******
Bayan wata uku da sati d'aya wanda cikin maryama yake da daidai wannan kwanaki dan zuwa watan gaba za'a fara mata awo duk wani gata da Kuluwa adamcy yana bata kuma babu ruwansa ko a gaban waye haka zai makaleta yana bata kulawa wanda kusan ita take janye jikinta idan taga idanun mami amman idan a gaban maryam ne ko yan'uwansa sakar masa jiki take yayi yadda yake so daita babu abinda zata ce wa Allah sai godiya daya mata arziki da samun miji kamarsa mutumin daya kasance miskili amman yanzu akanta bakinsa ya d'an bud'e kullum kalmarsa dadina Ina sonki maryama Ina sonki me kike son nayi miki shiyasa kyautatawarta bazata gushe ba agaresa daga shi har mahaifiyarsa haka ma yan' uwansa a yanzu tana barinsu dan sbd darajarsa sai dai kullum tunaninta yaushe ne zasu bar gidan saboda kalu balin da take fuskanta daga yan'uwansa dan a yanzu ma zaune take tana shafa kuncinta inda tasha mari daga aunty khadija kan abinda bai kai ya kawo ba kawai dan ta d'auki khaira ."tana zaune shiru dafe da kuncinta ya karaso ya tsaya kusa daita sai dai bata san da dawowarsa ba bare shigowarsa d'akin ahankali ya zauna kusa daita ya janyota jikinsa wanda yayi sanadiyyar data dawo haiyacinta ta sauke wani wahalallen numfashi tana dubansa "sannu da zuwa yaushe ka dawo ?"kayi hakuri ban san ka shigo ba bari naje na kawo mata lemu ko ruwa ka sha ta fad'a zata mike ya dawo daita jikinsa ya tsura mata idanunshi yana kallonta kafin ahankali ya motsa bakinsa "menene yake damunki ne na dade tsaye acikin d'akin nan kina tunani tai shiru tana sakè zurfafa tunaninta tana Shafa kuncinta "fad'a min me ya faru ne "uhm babu komai ta fad'a tana karyar da kai kallon natsuwa yayi mata ."Amman ya naga kamar kuncinki yayi ja ?" nace maka babu komai d'azu ne na zame a bayi na buge kaina bayan shi babu wani abu da yake damuna bugewar dai da nayi ce ta k'arasa maganr tana yatsuna fuska "akwai alamu bakya fad'ar gasky ya d'auki wayarsa yana daddanawa ita kuma ta had'e hannuwanta waje d'aya ta dafe ha'barta dashi jin shirunsa yayi yawa ta cire hannunta ta d'an leko cikin wayarsa "sarkin bincike bincike me kake binciko wa?.
yace "nothing !ya fad'a yana d'auke fuskar wayar tace da gaske yace "uhm yana cigaba da ganin duk abinda ya faru a gidan bacin ransa ya niku sai dai bai nuna a fuskarsa ba yayi kokarin ya danne damuwarsa yace mata suje kasa da kyar ta yunkura suka fita inda suka iske gabad'aya yaran mami zaune ban da mutun d'aya zabiba wacce kusan ta rage zuwa gidan yanzu tare suka zauna akan kujera d'aya maryama na kokarin gaishe da mami amman kiri kiri ta d'auke kanta"can kasan makoshinsa yace tashi ki d'auko min khaira ".a d'an rikice ta kallesa gabanta na fad'a uwa da matsanancin karfin gaske "ko baki ji abinda na sakaki bane?"tace uhm amm sai kuma tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta ya d'ago fuskar nan tashi a had'e tamkar an aiko masa da sakon mutuwa da sauri ta mike ta fara taku ahankali tamkar kazar da Kwai ya fashewa aciki cike da sanyi jiki ta k'arasa inda khaira take rarrafenta ta duka ahankali zata d'auketa taji sautin murya biyu ajere "karki sake ki d'aukar min ya !"aiko cak maryama ta tsaya tare da zuba masa idanu tana kallonsa jikinta na rawa shima suna gama rufe baki ya zabura ya mike tsaye yana nuna su da yatsansa."yarki ko tawa!"ya fuskanci maryam yana zaro mata ido dan bashi da lokacin aunty khadija nan take abu biyu ya had'e wa maryam waje d'aya tashin hankalin ganin yanayinsa da kuma farinciki ya furta kalmar 'ya ga khaira daga mami har aunty khadija da maryam da nana hauwa'u zuba masa idanu sukai suna kallonsa irin mugun kallon da yake ma maryam ta fahimci amsarta yake bukata dan har lokacin idanunsa na kanta."
muryarta a tsarke tace"yarka ce "!okay tunda har an yarda cewar 'yata ce good"ya kalli maryama dake tsaye jikinta na cigaba da bari yace "kina son khaira zaki riketa !"bata da zabin daya wuce ta amincewa hakan , dan haka ta gyda masa kai alamun zata rike "good daga yau ta bar hannun wannan har abada ta dawo hannunki dan haka ki d'auketa na baki ita kyauta kiyi duk yadda kike so daita "ai Maryam na gama Jin haka ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali "ma..mami ki taimakeni ya kyautar min da yarinya bayan duk wahalar dana sha tun kafin haihuwarta har zuwa ranar dana haifeta mami karki bari ya kyautar min da khaira "wannna maganr tasa jikin maryama yayi sanyi dan tayi imani rainon ciki kawai akwai wahala bare haihuwa tana kallonta tana kuka tana rokon mami tasa baki cikin maganar aunty khadija tace "dan Allah kiyi shiru hauka yake a ina ya ta'ba ganin an kyautar da mutun khaira yarki ce idan kuma har ya tabbatar haka walalhi sai munyi sharia dashi mara mutunci kawai da bai san ciwon Kansa ba "kece mara mutunci da bata san ciwon kanta ba ya fad'a yana kallon inda mami take zaune cike da mamakinsa yace "sweetheart kiyi hakuri dan matakin da zan d'auka yau bazai miki dadi ba ke mahaifiyatace duk abinda kika min da maryama kin ci lafiya kuma kinci banza saboda kece kika kawoni duniya ."amman kinga wad'an nan ya'yan naki wallahi bazan sakè d'aga masu kafa ba ko duba wata halaka dake tsananimu ,tsakanina dasu back to back ne ya d'auke idanunshi daga kallon mami ya zuba masu "ku kuma muatanen banza zaku gane kurenku a yau ne zaku gane bani da mutunci ya ciro waya ya soma kiran commissione of police yace "police din sun karaso okay shikenan bari nasa a shigo dasu yana gama rufe bakinsa ya juya ya fita cikin tsananin tashin hankali duk suke kallon bayansa maryama kam hannunwanta ta d'ora duka saman kanta ta koma ta jingina bayanta da bango tana karanta" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun mami ta kalleta "idan nace aurenki ya zame min alkhairi nayi wa Allah karya kin shigo rayuwarmu kin ruguza komai tsakanina dake Allah ya isa ban yafe miki ba,ai dai ciki gareki ba zaki haifa kuma za ki san me nake ji akan d'ana Ina addua Allah yasa ayi miki irin abinda kika min "maryama ta dukurshe kasa tana jan gwiwowinta tare da had'e hannunta duka tana rokonta "dan girman Allah mami kiyi hakuri ki yafe min wallahi ban rabaki da d'anki ba Allah shine sheidata ."
Tana kuka tana rokon mami har ma da aunty khadija tana bata hakuri adamcy ya shigo da polisawa yana nuna masu aunty khadija da nana hauwa'u da maryam,ya kalli auta afusace yana cewa "ina shahida!?bakinta na rawa tace tana d'akin mami tana sallah maza ki shiga ki kirata zan nuna maku tsantsar rashin tausayi ta nufi hanyar da sauri inda take jikin mami ya Kama rawa tana kallon adamcy wanda yaki kallonta dan kallonta zai sa ya kasa aiwatar da komai ."maryama ta ja gwiwowinta zuwa gabansa "ke kuma menene haka please get up? " ya fad'a a tsawace yana jifanta da mugun kallo da sauri ta girgiza masa kai "dan Allah ka duba halin da mami zata shiga akan matakin daka d'auka "kuma menene amfanin wannna matakin ?dan Allah ka janye kudirinka idan dai akaina ne wallahi na yafe masu duk abinda suka min "idan ke baki da hankali ni inda hankalina kuma nasan ciwonki "wai har ita wannna take yunkurin kasheki baki fad'a min ba "ya fad'a yana nuna maryam da d'an yatsansa "well da man kisan kai ba sabon abu bane a gurinta amamn idan ta gwada yi akanki ne zata sheka lahira dan da hannuna zan kasheki."Ya dawo da idanunshi ga maryama data had'a gumi tana rokonsa "ya d'an yi kasa da muryarsa "kima daina wahalar da kanki dan kema baki tsira ba bari na gama dasu zan dawo kanki ne .""Naji ka had'a duka hukuncin kayi min wallahi na yarda kuma na amince mutuncin mami da darajanta zaka duba pls d'auke kanshi yayi yana tura hannuwansa cikin aljihu yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa cikin tsananin tashin hankali auta suka fito tare da aunty shahida ta kallesa tsaye tare da polisawa sannan ta kalli mami dasu aunty khadija tace "meke faruwa !"ta tambaya ."officer's ga cikonsu nan ku tafi dasu" "what !"wallahi adamcy kayi hauka mu zakayi arresting?"bazaki san nayi hauka ba sai mun had'u a kotu cikin muryar kuka maryama ta mike tsaye ta riko hannunsa tana cigaba da rokonsa "kasan Allah muddin ka bari aka tafi dasu sai dai ka sakeni ".:
a matukar zuciye taga ya d'aga hannusa sama zai sauke mata mari tai saurin runtse idanunta ko ya tuna tana d'auke da cikinsa ne ya sauke hannunsa shiru bata ji saukar mari ba ta bud'e idanunta fess akan shi gabad'aya yanayinsa ya sauya ya dawo asalin mr ata din data sani yace "bar nan kafin nayi kwallo dake!"officers nace ku wuce dasu aiko suka tasa su gaba suna k'ok'arin fita dasu aunty khadija tace "zan Kira mijina kafin a wuce damu d'aya daga cikin jami'an tsaro yace "babu dama kin kirasa idan munje move"kasan kuwa ko ni din matar waye?" "karku saurareta sai kunje headquarter ."adamcy ya fad'a yana jifanta da wani mugun kallo ."yana rufe bakinsa maryama ta kwasa da gudu ta hau sama biyu biyu take taka step jini yaga yana bin kafafunta da sauri ya dawo da kallonsa gefensa inda ta tsaya nan ma jini ya gani ahankali ya dinga bin jinin yana kallo cikin tsananin tashin hankali da kad'uwa ya biyo bayanta yana kiran sunanta."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗
BOOK 4
AYSHA A BAGUDO WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Page 29
"Ahankali ya kutsa kai ya shiga parlour'n bai ganta ba ,sai dai idanuwanshi suna cigaba da kallon kasa ,sosai hankalinsa ya k'ara tashi sakamakon ganin yadda jinin d'anshi ko 'yarshi dake malale a kasa ,ji yayi kwalkwaluwarsa ta soma juyawa tmkr zata tarwatse tsabar tashin hankali,take launin idanunshi suka sake kad'awa ga wani irin zafi da kirjinsa ke masa tamkar zuciyarsa zata buga ."kai tsaye d'akinta ya shiga inda ya isketa tsaye a gaban wardrobe tana fito da kayanta, cikin tsananin tashin hankali ya soma mata magana cikin d'aga murya "maryama jini ne fa ke zuba ajikinki ". ya fad'a yana huci tamkar wani zaki ,sai dai ko kallonsa bata yi ba duk da tasani ,dan tana jin dumin fitarsa ,sai dai ta cigaba da abinda take ,ta juyo ahankali ta ra'ba ta gefensa ta shigesa ta barshi nan tsaye cikin tsananin tashin hankali."ta isa inda ta ajiye karamar akwati akan gado ta zuba kayan data d'ibo tana jin wani sabon tashin hankali na shigarta ".
"maryama !" ya sake kiran sunanta still bata amsa ba haka zalika bata d'ago ta kallesa ba "karki kuskura wani abu ya samu cikin jikinki ."me ye amfanin cikin da'aka tsine masa ai gara ma ya zube nima na huta,ya riko hannunta cikin nashi tayi hanzarin fixge hannunta tana cewa"bana so kaje ka cigaba da rashin mutun cinka tunda kai babu wanda ya isa yace ka bar abu ka barshi sai abinda zuciyarka ta kitsa maka amman kasani ni mryma a yau zan bar gidan nan kuma har abada na bar shi kenan bazan dawo cikinsa ba idan yaso hankalin kowa ya kwanta tunda daman nice matsalarku to zan barku ku cigaba da rayuwar ku . ya had'e fuska sosai yana cewa "wai Ina ruwanki da hukuncin dana yanke ?ina ruwana fa kace ?ta tambayesa tana tsaida abinda take ta zuba masa idanu cikin tsananin damuwa ".
"Kullum kuka ake yi dani gashi yau akaina ka zartar wa yan'uwanka hukunci mai tsauri ga.." "babu ruwanki da hukuncin dana yankewa 'yanuwana"yayi saurin katseta ta hanyar fad'ar haka "yanuwana ne ba naki ba dan haka babu ruwanki "okay kaga gara na bar gidan gabad'aya kuma gara cikin ya zube ba sai na koma gidanmu dashi ba dan bazan cigaba da zama da mutumin da baya d'aukar shawara"yana jin haka ya zaro mata tsumammun idanunshi cikin kar karwa"wallahi wallahi kikayi gigi wani abu ya samu cikin nan zan bala'i canza miki maryama zan miki abinda har ki mutu bazaki manta dani ba ."ya k'arasa maganr yana mata gargadi da yatsan hannunsa daga haka bai sakè cewa komai ba ya juya fuuuuu ya bar d'akin kunnensa manne da waya."jikinta ne ya d'auki rawa sai dai bata fasa had'a kayanta ba .parlour'n ya koma yana cigaba da kiran number likita mutun d'aya daga cikin polisawan yace"yalla'ba zamu wuce. "ku wuce dasu ."ya fad'a atakaice yana cigaba da neman doctor aiko suka tasasu gaba suna basu umarni ".
aunty shahida tace"ita mryam shayarwa take a barta a gida mu zamu biku .adamcy najin haka ya d'ago da sauri yace"karku saurarawa kowa acikinsu ku wuce har daita"wai adamcy ko dai kaje kayi shaye shayen ka da kasa ba?ba shaye shaye nayi ba wuta na sha na rantse da Allah tunda kuka gwada min rashin imani nima zanyi daku zaku sha mamakina aiko polisawa suka soma kokarin fita dasu khaira na ganin mamar ta zata fita tasa kuka tare da rarrafawa ta biyosu aiko kukan maryam ya k'aru tana tafiya tana waigenta adamcy yasa hannu ya d'auki khaira ya rungumeta a kafadansa."mami dake zaune tana kallon sarautar Allah an tattara mata ya'ya gabad'aya an wuce dasu "ta mike tsaye tana zaro idanu waje tare da fasa ihu muryarta a tsarke tace "meye haka zan gani yau ni zulai ?"yanzu adamcy abinda zaka min kenan?"ta fad'a tana kallon inda yake tsaye yana huci gashi gabadaya jikinsa rawa yake itama mami jikinta ya d'auki rawa da sauri takarasa kusa dashi tana kallon sa da idanuwanta cike da ruwan hawaye. "yanzu sakayar dazaka min kenan adamcy ?ka rasa hukuncin da zaka d'auka sai wannan?"Sweetheart kiyi hakuri hukuncin da yakamacesu kenan kuma na d'auka kina zaune acikin gidan fa suke wulakanta min mata, baiwarsu ce ko kashe min ita zasuyi ?ya k'arasa maganr adaidai lokacin da likita ta d'aga kiransa cikin gaugauwa ya bata umarnin tazo yanzu yanzu yana katse kiran mami tace"wai ma me aka mata daka damu mutane ?"kuma ko me aka mata a ganinka ya kamata kayi masu irin wannan tozarcin da auren su fa ?"ko rikonsu nake a tunanina bazaka masu haka ba bare ya'yan cikina."
Adamcy dake tsaye sai faman huci yake yana fidda numfashi sai dai ya kasa cewa maminsa komai ya barta tana fad'ar duk abinda taga dama dan wallahi yasan yana bud'e bakinsa bakar mgn zai furta mata a yadda zuciya take cinsa kuma bazai so faruwar haka ba ,dan zata sakè d'aukar wutar tsanar maryama ne ta k'arawa zuciyarta ta kuma ce ya zageta saboda matarsa .dan haka ya kiyin magana, hakan yasa mami ta sake Jin haushi ta d'aukesa da mari tana kwace khaira a hannunsa tace "maza maza kasa a dawo min dasu kuma a yanzu idan ba haka ba sai dai nima ka sameni a police station din ".ya zuba mata tsumammun idanunshi da suka rigada suka rine sai dai bai ce mata uffan ba kuma baya ji zai ce din kma bazai sa a dawo dasu ba sai ya nuna masu iyakarsu cikin tsananin fushi mami ta shige bangarenta rike da khaira tana shiga d'akinta ta soma neman layin baba babba ta fad'a masa abinda ya faru kai tsaye yace babu ruwansa ."