Mijin malamah by nimcy luv - Chapter 43
Mijin malamah by nimcy luv Chapter 43: Mijin malamah by nimcy luv Chapter 43. Shigowar Abraham kenan daga yawon neman Majeederh, a ɓoye yake komai gudun…
1,612 words
Shigowar Abraham kenan daga yawon neman Majeederh, a ɓoye yake komai gudun kada mutane su fahimta a karo na farko ya ji ya ɓoye wani abu a rayuwarsa bai faɗawa Latifa asalin abinda ya samu Majeederh, sai ya ji ya ƙara neman nutsuwarsa ya rasa bakiɗaya, damuwa ta masa yawa ya fara yin abu sama-sama kamar wani ke shirin komawa da ciwon hauka, shi kaɗai sai ya fara kiran "Am sorry Mami" Ko "Don't leave me Jee" wayarsa ta fara ringing ya yi banza da ita idanunsa kuma a lumshe ƙirjinsa na ɗagawa da ƙarfi. Kiran wayar ake babu ƙaƙƙautawa hakan ya sa ya miƙa hannu ya ɗaga ba tare daya buɗe idanu ba. "My darling Grandson" Grandpa ya faɗa lokacin da Abraham ya ɗaga kiran wayar, ya yi shiru domin he has no words a bakinsa na yin magana. Grandpa ya ce "Surprise surprise, am in the airport, ka zo ka ɗauke ni" Abraham ya kwaɓe fuska yana ɗan riƙe kansa bai ce komai ba "Darling Grandson" A hankali ya ce "Grandpa sorry" Ya ce "For?" quietly ya ce "I can't come" "You most, bayan na san idanunka rufe kake neman Maminka? Kazo kaga abun mmki" Da sauri ya miƙe tsaye yana layi ya ce "Are you sure Grandpa?" Ya ce "Absolutely sure darling" Ya miƙe yana ɗaukan key daga shi sai gajeren wando da armless, da ƙyar yake tafiya sbd bashi da cikakkiyar lafiya ga yunwa damuwa da wani irin sabon son Maminsa dake ƙara yawa a zuciyarsa. Driving yake da wani irin gudu yana yi yana duba time deep down kuma gabansa na faɗuwa for no reason. A haka ya ƙarasa Airport ya yi parking motarsa ya kira Grandpa yana ɗagawa ya ce "Are you there?" A hankali ya ce "I'm already there" Grandpa ya ce "Ok ka fito daga motar ka shigo cikin airport ɗin wajan shiga jirgi" Yana faɗin hakan ya kashe kiran, mmki Abraham ya yi shi me zai kaisa wajan jirgi? Ya fito daga mota ya nufi ciki fuska haɗe yana tafiya majestic ɗai-ɗai yana ɗaga shoulder's a haka ya shiga ciki, har ya ƙarasa yana ƙoƙarin kiran Grandpa kamar ance ya ɗaga kansa idanunsa ya sauka akan Escorts uniform ɗin su kawai ya gani gabansa ya faɗi ya fahimci ko su waye, nan da nan ya haɗe fuska yana ƙoƙarin juya aka ce "Don't move" gabaɗaya suka zagaye shi da wasu manyan guns kamar wani ɗan daba ko ɗan kidnaping. Grandpa ya ce "Sorry dear mani da zaɓi sai haka, dole kabar wannan ƙasar dole kabar musu yarinya tayi rayuwa ita kaɗai dole ka bar musu yarinya tayi aure, kayi mata ƙarami addininku ba ɗaya bane, yau da ace tun farkon ɓatanka data tsince ka, kake a hannunta har kawo yanzu da babu shakka a musulunci zaka tashi, yanzu kuma babu abinda ka sani dangane da Muslunci daga wannan ƙasar ta turawa kana nan" Wani irin kallo Abraham ke watsawa Grandpa kafin ya yi magana wayarsa ya fara ƙara ganin sunan Latifa yasa ya ɗaga da sauri ta ce "Majeederh ta dawo, tana cikin ƙoshin lafiya sai dai bata cikin walwala gabaɗaya ta rufe kanta a ɗaki mun rasa meke damunta, plx ka zo" Abraham ya yi me ya sa zata ce ya zo? Yana da kyau ɗin kuma yaje ya bata haƙuri ya mata al'ƙawari ba zai ƙara ba zai kiyaye duk abinda addinin su ya hana "I'll come" Ya ce a hankali yana kashe wayar. Ba tare daya damu ba ya juya zai bar wajan ya ji an riƙe shi "Grandpa let go of me, i want to see my Jee i want ask her forgiveness" Grandpa ya ce "It's too late to cry Abraham, ur dad needs you" Wani ihu Abraham ya kurma wanda ya bawa Grandpa tsoro amma bai sake shi ba ya ce "Dole ka koma Germany a yau ɗin nan" raguwar ƙarfinsa ya saka ya hankaɗe Grandpa tare da kwantar bindiga hannun wani ya ce "Duk wanda ya biyo ni zan harbe shi, remember?" Ya faɗa yana ja baya Grandpa ya ce "Abraham ka tsaya ka saurare ni, Abraham wait" Bai tsaya ba ya buɗe motarshi ya shiga tare da rufewa, wata farar peper ya ɗauka da pen ya shiga rubutu cikin sauri dan a jikinsa ya ji ba lallai su barshi ba, gabaɗaya hankalinsa tunaninsa nutsuwarsa da komai yana wajan Majeederh ƴar madararsa, ya jima yana rubutun kafin ya gama ya ɗakko envelope fara tas sai wani ƙamshi take fitarwa ya ɗauki hanky tare da paper ɗin ya saka cikin envelope ɗin, a hankali ya kifa kansa a string motar jikinsa duk rawa yake sau ɗaya ya taɓa tsintar kansa a yanayin da yake jin kansa a yanzu, wannan ya zame masa 2rd round ya rasa tunaninsa da abinda yake masa dadin zafin ransa dana zuciyarsa ya ƙaru damuwarsa ta ninku, ya daɗe a haka can ƙasan maƙoshi ya ce "I love you Jee, am sorry i don't mean to hurt you anymore am sorry ƴar madara" knocking Glasses ɗin motar aka fara ya ɗago kai a hankali ganin Taj tsaya ya yi saurin buɗewa ya fito kafin ya yi magana ya ji gabaɗaya Escorts ɗin sun riƙe shi zai magana ɗaya daga cikinsu ya buɗe masa screen ɗin system nan take fuskar Dad ɗinsa ya bayyana ya runtse idanu ya ce "I hate u Daddy" Daddy ya tsorawa ɗan nasa idanu kafin ta cikin system ɗin alamar vedio call ya ce "Ku kawo mini shi" Yana faɗin hakan ya kashe kiran, dambe suka fara yana wani irin ihu da kiran sunan Majeederh amma ina ya kasa kwancewa sun masa rufdugu wani irin takaici ya sanya idanunsa zubar da hawaye yana faɗin "Am sorry Jee" Ya cillawa Taj envelope Taj ya riƙe Envelope ɗin ya ce "Make sure ka bawa Mami yau ɗin nan plx Taj, ka bawa Mami promise me" Taj ya ce "I promise you that, zan bata today" Abraham ya runtse idanunsa ya ce "Tell ta jirani, ta jirani, ta jirani I'll be back sooner or" Taj ya ce "I'll" Daga nan Escorts ɗin suka ɗauke shi gabaɗaya har zuwa cikin private jet ɗin Abraham na wani irin kururuwa kamar mahaukaci a haka jirgin ya fara lulawa da shi zuwa sama.....
Bear with the errors🤓ban edited ba kawai rubutu nake and kun san keyboard [8/4, 5:30 PM] _KHADSALT_🌹💞: MIJIN MALAMA 50 End of book1 The begen of the beginning... Continuation
*AUTHOR'S NOTE* _*This information is for those who do not understand this book.. Ni ban wani niyyar cewa komai ba, to na ce me? Kowa ya yi ta kansa da haka nasu na barku, to ganin ana ta yagalgala nama na yasa nace bari na tofa tawa. I have a question for you guys! Kunga na gama labarin nan na sauke? No??? Me ya sa aka bawa littafin suna MIJIN MALAMA?babu mamaki mijin nata ke shan wahala, babu mamaki masu neman aurenta suke da yawa shi ya sanya aka ce Mijin Malama Ko kuma ƙaddara aurarraki ta faɗa kanta duk wanda ta aura ya zama MIJIN MALAMA babu mamaki wannan Christa ɗin shi ne mijinta kasancewarta Christa sai a fara kiransa da MIJIN MALAMA.... Idan ƙaddara zata faɗawa mutum daman Ubangiji na neman shawarar shi? Ko kuma idan Allah ya jarabce ka da abu sai kace kada ya sake jarabtarka tunda ya taɓa? Ashe ɗan adam a karan kansa zai iya tunanin Ubangiji bai kyauta masa ba tunda yana ta jarabtar shi da abubuwa kala-kala? Abinda baku sani ba shi ne wannan labarin full of density ne cike yake da zanen ƙaddara, shaidar zur na mutane, ƙalubaleln da masu jinkirin aure suke samu, son zuciya da mugun baki na Iyaye, rashin kulawar su ga yaran su.... Saboda Majeederh ta kasance malama shike nan bai dace ayi ta ayi ta jarabtar ta ba? Ai cikakken mumini wanda ya yarda da Allah da Manzonsa shi, ya yarda da ƙaddara ya yi imani da ita shi kaɗai Ubangiji ke jarabta sbd nuna masa soyayyar shi, mutane wagairawun Ubangiji ba fiya shiga al'amarin su ba. Cewa akai ko wata guda kayi bakai ciwon kai ba, to ka tuntuɓi imaninka😞 Ga misalin Annabawa nan wanne irin ƙalubale ne basu fuskanta ba, suka jure ya zame musu tarihi. Taya zaki haɗa su da Ƙaruna wanda Ubangiji ya zuba musu idanu suna tunanin sun fi kowa Sa'a a duniya? Kuna ganin Fir'auna wacce tsiya ce bai shuka ba? Ga su hamana to haka al'amarin Ubangiji yake, ku bar ƙaddara tayi aikinta plx..... Sannan azana cewa wai ina barin ana taɓa jikinta wanne yaƙunannen kuga ya taɓa ta? Abraham bad boy? To a rayuwa duk abinda kake so Ubangiji ya fi jarabtarka da shi, babu mamaki zunubin hakan ya sameta nan gaba kuma har zuciyarta kallon ɗa wanda ta raina take masa bata taɓa bari ya riƙeta hannunta da nufin wani abu ba. Sai mema matar ta ce ne? Ni Afujajen na karanta write up ɗin nata, wai ina nuna masu liƙab basu da gaskiya? To ban ce komai ba idan kin karantar posting na yau zaki fahimta ni duk takaicina bana biya tayi ba, a wata ƙasar taci karo da shi... A ƙaddarorin Malama Majeederh babu sa hannunta a faruwar komai ni dai bari kawai na yi shiru a nan kada bakina ya yi tsayi ana zama lafiya.... Zamu fara BOOK2 ban yi kuma al'ƙawarin farin ciki har ƙarshe ba, tunda rayuwa bata taɓa tabbata da farin ciki amma nayi muku tanadin wata kalar tsaftacciyyar soyayya mai narkar da zuciyar mai karatu, In sha Allah wacce tayi write up ɗin nan ina zaune zata sake yin wani na yabon bama ita kaɗai ba. THANK YOU I LOVES YOU SO MUCH GUY'S😞🤓🥰*_