Mikiya complete Novel - Chapter 3
Mikiya complete Novel Chapter 3: Mikiya complete Novel Chapter 3. Kamar kullum gidan na nan kamar kasuwa, duk uban sallamar data rinka yi amma babu wanda…
4,078 words
Kamar kullum gidan na nan kamar kasuwa, duk uban sallamar data rinka yi amma babu wanda yayi ƙoƙarin amsata, itafa har mamakin gidan su take yadda abubuwa suke tafiyar musu tamkar irin gidan jahilan nan, kanta kawai ta sanye xuwa barandar da mahaifiyarta take zaune tana aikin zuzzuba humra cikin kwalabe. Zaune takai dab da mahaifiyar nata tana faɗin "AMMANMU sannu da aiki!, ina raiha tayi ne naga ban ganta ba?" Dago kanta wacce ya kira da amman tayi tana cewa "yawwa meerah raiha na ɗan aike ta ne bayan layi, gidan jajiya kareemah zata kai mata humra" Nooding kanta kawai tare da cewa "Ina Affan naga ban ganshi ba..... Kafin ma ta rufe bakin saiga wani ɗan bakin yaro nan a guje irin ɗan shekara shida ɗin nan zuwa bakwai, a guje ya faɗa jikinta tare da faɗin "oyoyo aunty meerah na!" Rungume shi tayi tana sakin dariyar farin cikin nan ta buɗe bakinta kenan da niyar yin magana, gaji an wani janye shi a jikin ta. Cikin haki da masifar dake cin gabjejiyar matar dake tsaye ta rike hannun yaronta ƙammm, "meerah ki fita a harkan Affan fa, ko sai kin iskan tamin da?, duk yaran gidan nan da suke nan ga sunan kamar jamfa a Jos, amma duk babu wanda kika liƙema sai ɗana dalilin ki iskanta min ɗa ko?, to wllh bari malam ɗin ya dawo bazai yiwu ba dole ne yau na datse alaƙar dake tsakanin ki da Affan" Kanta dake mata ciwo ta riƙe domin dama komai take yi dauriya ne kawai sharrrrr wasu hawayen takaicin familynta ya saukar mata,
_Wai sai yaushe kan family's nasu zai haɗu wuri guda?, sai yaushe zasu gane Allah da girma yake?, yaushe ne zasu san daɗin zumunci da ƴan uwan taka, gidan mu ya kasance wani irin gida ne me cike da son kai da son zuciya, kowannensu yana tafiya ne ya kife kansa kaɗai ya sani da rayuwar yaran sa. Gidan mu yafi karfin a ƙira shi da ko wanne irin suna, domin kafff iyaka bincike na na gaza samun sunan da yayi daidai da rayuwar gidan mu, kawai zan baku abin a dunƙule ne kowa yaje ya nemi fassara!. Mahaifin mu malam Abdullahi gwani yana da mata huɗu, duk wani haƙki na uba ɗa yana bamu saidai sammmm iyayenmu basa taɓa fashimtar hakan, kullum babban burinsu shine meda gidanmu filin yaƙin sunƙuru dana fili. Ga yawan tarin iyalan da Allah ya bashi, gamu da masifar dangin kamar tsaƙi amma sai ka kasance jajirtacce ɗan zamani zaka zauna da kowa lafiya a sannu a sannu muna tafiya, zaku fashimci halin kowa da kuma manufa na_ Wannan keñan
Amma dake zaune tana ci gaba da zuzzuba humrarta cikin kwalabe idan ƙasa tana magana to kuwa tayi ita ma, haka Maman Saude ta karaci bala'inta tayi gaba ita da Affan dake ta kuka, yana miƙo min hannu, sai tallar ƙeyarsa take. Na yunƙura zan tashi keñan ƴar ƙaramar wayata irin tecno common ɗin nan tahau ruri cikin waƙar hamisu breaker me taken _Kada ki bari zuciya ta zuga ki_ saurin kallona Amma tayi tare da tsare Ni da manyan Idonta wanda duka muka gada daga gare ta, Cikin in ina nashi ga faɗin. "M.... MD ne, Ammah wai yana son za'a fira dani, kuma kinji wai dole sai dani za'a yi firarn, bayan duk ga su mardiyya nan su hayatu amman dole sai dani za'a yi wai" Kanta ta mayar taci ga
*🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀}
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
____________________
*NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 7&8
🤍🔥✅
Aikin ta ba tare da tace komai ba, haka yaci gaba da ƙiran Ni ban ɗaga ba kuma ban tafi ba. "Ki amsa shi, Idan kuma baki so ki bashi amsa ki dena ja masa rai har haka!" Ganin abinda nake son ta fashimta ɗin bata fashimta bane, ya sani faɗin. "Fuskata za'a haska a yayin firan Ammah!" Saurin ɗagowa tayi tare da dubana sai kuma tamin nuni dana shige ɗakin kawai, alamun bata son maganar. Handbag ɗina na ajje a kan doguwar kujerar dake parlourn mu, dake ciki da parlourn ne dakin namu, kayan jikina na rage ina faɗawa kan kujerar tare da kwanciya bayan nasha maganin ciwon kan. A take nannuyan barci yayi awon gaba dani, ban farka ba sai bayan sallar magrib, daƙyar nake Iya buɗe ido na sabo da nauyin da suka min, Adda'ar tashi daga barci nayi tare da tashi ina fita alwula na ɗauro na data salla ina zaune na haɗe kaina da gwuiwa na abin duniya duk sun gama sanyoni gaba raiha ta shiga ɗakin, zama tayi kusa dani tare da daura kanta saman ƙafafuna tace, "Yaaya kije Inji baffa yana ɗakin zaure" Dammmm gabana ya bada sautin bugu baffa kuma yake ƙirana a irin wannan loƙacin kuma. Jiki babu ƙarfi na miƙe ina fita tare da nufar ɗakin zauren. Da sallama na shiga ya amsani tare da nuna min wurin zama, zaman nayi tare da gaisa shi ya amsani a nutse, "ko miye dalilin daya sanya Maryam ƙin amincewa Md firar da ake son yi da ita?" Kaina sunkuyar ina wasa da yatsun hannuwana cike da ladabi na furta, "Videon kai tsaye ne za'a haskaka ma duniya!, shi yasa sammm naƙi aminta da hakan, domin acikin sharruɗanka babu ɗaukar video!" Wani gwauron Numfashi ya kawo ya sauƙe tare da dubana, "A gaskiya banyi tunanin haka abin yake ba amma kije babu komai kije ayi firar kariyar Ubangijii yaci gaba da tabbata a gareki, Allah Miki albarka tashi kije" Da saurin umman mariya ta ɓoye bayan bishiyar dake kofar fita a dakin, domin dama badai iya laɓe ba, Ni kuwa banma san tanayi ba tunda cikin yanayin dana kasa gane masa na baro dakin.
*AK*
Ahankali cikin nutsuwar sa yake saƙkowa daga upstairs nashi zuwa wangamemen parlourn gidan, loƙacin sha ɗaya da minti sha biyu, kunga kenan minti uku ya rage masa.
Zamani tv
Duk da kasancewar yau kwata kwata bata niyar zuwa wurin aiki, amma haka ta danni zuciyarta ta fito tun sha daya saura, gudun kada tayi lettt, sai gashi kuma har yanxun wajen sha ɗaya da minti goma shiru shiru babu labarin zuwan nashi. Ɗan madaidaicin Agogon Rolex ɗin dake hannunta ta shiga dubawa ganin har sha ɗaya da mintinan ashirin da biyar tayi bai iso ba, hakan yasa ta jan ɗan ƙaramin tsoƙi, domin jira na ɗaya daga cikin abinda tafi tsana a cikin rayuwarta. Na miƙe kenan ina fita daga cikin department namu wasu irin fitattun narkakkun motoci guda uku suka sanyo kansu cikin coumpaund na gidan jaridar namu, hakan ya sanya ni ja baya ina komawa cikin dakinmu inda mardiyya ta shiga tsokana wai kwana biyun nan kamar wacce akama turen rashin son magana, nidai ci kanki ban ce mata har zuwa loƙacin da Md ya ƙara so cikin department namu, cikin wani irin rawar jiki sai faman zazzare idanuwa yake ya tsohon maye. A kaina ya fara sauƙe Idanu, cikin rawar murya ya furta, "MEERAH da dukkan alamu wannan baƙon namu wani ƙusar ne ke kinga wasu irin rantsantstsun motocin da yazo dasu?, tare da wasu samudawan escort, baki ɗayan sa tun daga ƙafarsa kamo fuskarsa a rufe suke cikin wasu haɗaɗɗun suit baƙaƙe ke hatta takalmin ƙafarsa abin kallo ne, maza yi sauri ki fito, kana ki tabbatar kin cire wannan liƙabin da kika kwama a fuska" Ko amsata bai ji ya fice harda haɗawa da ɗan gudu gudunsa, yake zai shiga kenan ya kusa cin karo da hancin bindigar dake hannun miles, wani irin zaro Idanu Md yayi, domin shifa sai yanxun ma ya kula da uban manyan bindugun dake hannuwansu, kuuuuuuu cikin sa ya bada sauti, gumi na keto masa, miles dake zuƙar cigarettes Samm bai kula da yanda ya tare hanyar da bakin bindigar saba, hakan ya sanya shi saurin janye wa yana tsare Md da firgitattun idanunsa da suka kada sukayi zajurr. A gujeeeeeeee MD ya zura har yana neman hantsilawa "innalillahi wa'inna ilair raji'un, me yake shirin faruwa damu kodai kidnapped namu aka zo yi " Ya faɗa a bayyane amma sai ya daure yana ƙaraso cikin Office ɗin nasa.
A ƙalla Saida na ƙara wajen 10 mint da fitar Md ɗin, kafin na fito, Nima dai ganin wannan samudawan hannuwansu riƙe da manyan bindugun Saida ya razanani, amma na dake don nasan matsoraci baya taɓa zama gwani. Haka na ratsa tsaƙiyarsu na fice cikin takun daya fi kama da a ƙira shi dana yanga, saidai sammm ba haka bane haka Allah ya halicceni, zuwa wannan loqacin tuni wanda yake zaune harya fara fusata da zaman jiran yarinyar da murya ta kaɗai yaji, don ko photon ta bata yarda ta taɓa ɗaurawa a media. Wani irin mahaukacin ƙamshim turare ne ya fara welcome nawa, tun daga bakin ƙofar, a nutse na sanya zara zaran yatsuna ina tura ƙofar Office ɗin, ya ɗago kansa da Nijar yama Md magana yaci karo da zanen jan lallein yatsun hannunta, kafin na bayyana kaina cikin qaton hijjabina da kuma niƙab ɗina. Cikin ƴar siririyar muryata nayi sallama wanda Md ne kaɗai ya amsa ni banda mutumin dake haƙimce saman kyakkyawar kujerarn da nayi tunanin daga ina Md ya samo ta, don dai nasan Bama da irinta cikin kaffff gidan jaridar namu. Banko damu da yadda duk mutanen dake cikin Office zubo min Ido ba, domin duk da ko ina na jikinsa a ɓoye yake amma sai suka gaza samun sukuni. kujerar dake pacing dashi naja na zauna,kasancer nasan shine nawa mazaunin. sai table ɗin dake gabanmu wanda ya raba tsakanin mu, an ɗaura glass cup guda biyu masu ɗauke da ruwa, sai dai an rufe su da ɗan ƙananun fai-fai. Ta ƙasan ido na ɗan saci kallon sa dan koda na zauna ban tanka musu ba, ban kuma zare niƙa ɗin fuska na ba. Haka naci gaba da ƙare masa kallo duk kuwa da cewar bana iya ganin komi nashi, har yatsun hannuwansa kuwa abinda zan iya faɗi kawai shine da ganinsa ba karamin mutum bane, ko daga yanayin zaman da yayi irin na shahararrun sarakunan nan ba muna sarki ba, sai hujin dake kunnensa ta ɓangaren hagu ya sanya wani diamon ring barima color'n gold. Ɗan taɓe baki na nayi tare da janye idanuna dake kansa, Cike da ladabi Md ya ƙaraso tare da maƙala masa abin magana a jikin jacket suit ɗinsa. Nima ya miƙomin na maƙala a jikin hijjab ɗina, Sai da aka tabbatar mun gama kimtsawa sannan aka ɗora camara a kanmu. A nutse na sanya fararen hannuwana ina janye niƙab nawa zuwa saman fuskana, cikin aro jarumta da bada attention Kamar bani ba, sai da na kalla cemara naima masu kallo sallama tare da gaisuwar barka da wannan loƙaci tare da fatarn sake kasancewa damu a shirin mu na kai tsaye, dangane da wannan bawan Allah dake son bamu ƙarin haske game da AK. (Wama ya sani ko AK ɗin ne) Na faɗa aceñnn ƙasar zuciyar, sai kuma nayi saurin faɗin (kai hakan ba bazai taɓa iyuwa ba, bayan ance shi kamar aljani yake kuma tunda yake babu wata cemara data taɓa haska shi aduk tsawon rayuwarsa, saidai kawai sunan daya karaɗe ko ina sabo da mumman aikinsa) Saurin dawowa cikin hayyacina nayi dan gyaran muryan da aka min a take na dawo da ainihin nutsuwa na zuga ga dubban jama'ar da ke son kallon mu. Cikin tsare sa da Idanuwana duk da cewar bana iya ganin ƙwayar idon sane, na furta.
"Assalamu alaika ranka ya daɗe". A hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa min da "Wa'alaikissalam" cikin muryar dake tamkar wanda akama dole. Kai tsaye zaka taɓa fahimtar kallona yake ko akasin haka ba saboda akwai eyeglasses mai duhu a idonsa. Bayan irin hular nan ta sojojin da suke sanya wa. Yinai kamar ban damu da abinda yay ɗin ba nima, na cigaba da faɗin, "Wannan shiri na maka barka da zuwa, tare da nuna farin ciki matuƙa wajen zaɓarsu da kayi duk da bamu san dalilin ka nayin hakan ba, duk da bamu san waye shi ba"
"Barkanmu tare fatan Alkhairi ma duka jama'ar dake sauraraen wannan shirin!" "To masu kallo zan iya cewa duk sai ku sake matsowa gaban akwatinan talabijin naku, masu rediyo su ƙara sauti domin ji daga bakin babban baƙon namu da musan waye shi ba!" Sai kuma na sake juyowa garesa tare da faɗin, "Ko zamu iya sanin cikakken sunan ɓoyayyen baƙon namu?" Wani irin kafirin murmushi ya saki irin na gefen bakin nan, Cike da wani salo ya sake harɗe ƙafafunsa da yay crossing cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta. "ABDOUL-MALEEK KUWAIT"
"to Saidai kanmu ya daure da sunan baƙon namu, gashi kuma bama iya kallonka kai tsaye, duba da cewar kazo mana da batu ne akan wannan babban CRIMINAL ɗin Wato EAGLE, wanda ya kasance cikin aikata tarin ɓarnuka marasa ƙyau, wannan shi yaja hankulan masu bibiyar wannan tasha ta zamani tv jin batu ne akan CRIMINAL ɗin da ake nema ruwa a jallo!"
Wata zazzafar iska ya fesar daga cikin bakinsa na wasu sakanni sannan yay wani ɗan murmushin gefen baki, a taƙaice ya furta, "Kai tsaye ki ɗauka kina tare ne dashi wannan babban CRIMINAL ɗin da kowa ke nema ruwa a jallo" Manyan Idanunta da suke kama da na mashayiya, uwa uba tsarin halitarsu da girman da suke ta ware baki ɗaya, tare da wani irin zaro su Wanda har saman fattar idon Saida ta ɗan kara faɗi kadan. Tana tsare shi dasu tamkar irin me tuhumar nan nasa, A nutse ya zare baƙin sun glasses in daya manne fuskar sa dashi, tare da kafe ta da nashi manyan Idon wanda kana kallon su zaka so fara kawar da dubanka, dan ba irin idannuwan da ake tsatsarewa da kallo bane, ga wani ruwa ruwa mai nuni da cewar Saida aka shawu kafin a fito,wanda ba dan ta kasance mai tsaurin ido ko mai taurin kai bane da taurin zuciya babu abinda zai hana ta kutsawa a gujeeeeeeee. hasalima ana ƙiran da farar kurane amma Halittarta mai bayar da tsoron ce ita ma Farar fuskarta dake ɗauke da kwantaccen gashi a gaban goshinta, wanda lafcecen hijabinta bai hanna su bayyanuwa, A hankali ta sanya hannunta mai ɗauke da awarwaraye na roba irin masu kyallin nan kwaya biyu pitch color ta shiga mirza saman goshinta irin tana cike dashi ɗinnan.
A hankali ya sake zuba mata ido tun daga yanayin yadda ta zazzaro ido har zuwa sanda ta shiga mirza saman goshinta yadda Idannuwanta suka rinqa sama da ƙasa. Haƙorinsa ya ɗan datse yana ci gaba da mata kallon ƙasar Ido. "Duk da ance shi ɗin ba kamar sauran mutane bane, amma a yadda nake ji ɗinnan idan har nayi gaba da gaba dashi zan iya kashe shi a matsayina na me kishin ƙasa" Haka ya riski muryan ta me kama da waƙa take rerawa ba masifa take sirfawa ba, harda irin mutsitstsike hannuwan su bada sautin ɓasss.
Dade beyi niyar jimawa a zaman tattaunawar ba domin akwai manufar shi na yin hakan, akwai saƙon da yake son masu shi su ɗauka. Don haka cikin wani irin jannn hankali da salo me kyau ya ɗaga hannunsa sama tare da mirza shi irin gintsewar nan yace.
"Mutuwa dai kika ce idan kuma ya kasance shi ɗin baya tsoron mutuwar ba fa?"
Zuciyarta ce ta ji ta buga da mugun ƙarfi amma cikin ƙarfafama kanta gwiwa ta mayar masa da amsar daya bata daidai dashi. "Idan harya kasance baya tsoron mutuwar, ya bayyana kansa mana ga jami'an tsaron da suke fafutukar nemansa ruwa a jallo, nasani dai baifi ƙarfin hukuma ba saidai idan ya kasance shi ɗin matsoraci ne, domin jarumi ba'a san shi da yakin suƙuru ba ya fito ayi na sarari gaba da gaba shida matakan tsaro a gabza yaƙi" Wani irin ɗan waro mata Idanu yayi, tare da mata alamar jinjina da hannuwansa, kafin cikin hosky voice nashi ya furta.
"Idan kuma ya kasance su jami'an ne da kansu suke tsoron tun karar safa? Mutumin daya Kasan ce baka gane gabansa balle bayansa balle ka gane inda ya dosa, yanzu duk rikicin da tarzomar da ya haɗa a garin nan amma ace yasha, kinga kenan ƙarfinsu yafi ya musu zarrar da basu taɓa iya ja dashi ba, idan kuma sun shirya to Bismillah, hakan bai hana shi ya shiryawa kansa zuwa mataki na gaba ba kamar yanda ya tsara ma kansa , yana da karfin hali sosai, komai zai aikata yana aikatawa ne cike da kwarin gwiwa ɗari bisa ɗari, tare da yaƙini da kuma sanyawa a ransa tabbas zai yi nasara, Ki sani sawa a rai ne yasa falke baya jin wahalar tafiya,wanda idonsa basa gani sunanshi makaho, Ammah cikakken makaho shine wanda zuciyarsa bata gani kamar dai jami'an tsaron ku. Haka za Kafin ya sanya kansa cikin harkar sai da ya shiryawa kansa komai da komai, tare da tsara ko wanne mataki!, don haka idan ma da wata manufar suka tsoma zancen zuwa gidan jarida, wannan shine yaƙin sunƙurun da suƙe ikirarin AK EAGLE yana yi, wannan yaƙin iya na filin daga ne bawai na media ba, don haka sojoji, ƴan sanda, wannan yaƙin ba na nan bane, yaƙi ne na iyaka jami'an tsaron da suke ikirarin suna son kare ƙasar su, kana Idan suna jin sunkai sun kuma isa su nuna jajirwarsu, wajen dawo mana da governor da kuma minister ta hanyar nuna jajircewar su a aiki".
Zuciyar tace taji ta matse da tunanin irin fassarar da yayi ma Maganganun sa Atake taji tana jin wani abu na narkewa a cikin jikinta kamar ƙarfen da ake ƙonawa a cikin wuta, tabbas yayi maganar gaskiya, wannan yaƙi ne na jami'ai, bawai su kawo media ba, kafin ta ɗago wayammmm taga babu shi babu alamunsa, a wurin da yake zaune, jikinta ne ya shiga wani irin mazari da tsoron masifa, tuni ta gaza sarrafa kanta wajen dawo da nutsuwar ta, tana shirin tashi ne kuma tayi gamo da Katar ɗin ganin ƴar ƙaramar fara tasssss ɗin takarda, wanda take ƙaya ce cikin kyakkyawarn ado, tare da tsarin rubutun daya fi kama da a inji aka zana, cikin manyan harrufa aka yi rubutun kamar haka. *" FLOWER BERRY PIE, THANKS DA KASANCEWA DA AK EAGLE 🦅 "*
A razane ta tayi cilli da takar dar tana juwo gasu MD, bata tashi aune ba sai ganin Md tayi ƙarƙashin dujuwar office ɗin.
To ai shikenan kooooo saimu gimtse🫰
*By AMMEY LAYLERH ✍️*
🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀}
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH #HOT LOVE #ROMANCE #AK FOV #DEEP ASSUMING FOV ____________________
#*NA MARYAM NASEER* #~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 9&10
🤍🔥✅ __________________ ★★★★ Ba md kaɗai ba duk wani ma dake ƙarƙashin zamani hankalin sa idan yayi billions dollars to a tashe yake. Cikin tsananin tashin hankali itama ta shiga zara idonta, bawai don tsoron abinda ka iya zuwa yaje ba. Sai don kawai hangen irin tashin hankalin da Annenta da zata shiga harma da baffan ta. Hankalin ta bai sake tashi ba saida jiniyar ƴan sanda ta karaɗe gidan jaridar baki ɗaya cikin fitar hankamotar ƴan sanda,wasu zafafan hawayen ta kuma sharewa wanda take jin zafinsa tun daga tsaƙiyar ƙirjinta, me cike da tsantsar tsabar AK me zafin gaske wanda a duniya taji bata taɓa tsabar wani abu ba kai tsaye kamar AK ɗin. Gangan zunzurutun matasan da suka yi zanga-zanga bakin gidan jaridar ne suka yunƙuro da niyar kai hari ga MEERAH tare da Md, wanda zuwa loƙacin yake neman fita a hayyacinsa. Banda zazzara ba ido babu abinda yake ga uwar zufar data riga ta gama kwaranye masa jiki, na tsabar tashin hankalin da yake ciki, kamar bashi bane mintoci kaɗan yake cikin mafi ƙololuwa a farin ciki, amma gashi komai ya zama shuɗaɗɗe cikin abinda bai wuce 30 mint ba. Zufar dake tsatstsafo masa ya share a karo na ba adadi tare da sauƙe numfashi kaɗan, sai kuma ya ɗan kiwo da dubansa zuwa ga meerah amma ga mamakin sa sam babu wani alamun tashin hankali tattare da ita. Hakan ya jefa zuciyarsa cikin kokwanton ko dai ta samu attack ne koma shock zai ce shidai baima sani ba, bai dawo daga duniyar tunanin daya afka ba yaji tsaiwar motar su a police station GTA ɗin dake babban birnin Lagos ɗin. Babu ɓata loƙaci akayi ciki dasu wanda suka kuma tadda cincirindon al'ummar dake cike da bakin police ɗin, suna fadin a sudai adalci suke so,mebi ba ai harda haɗin Md ɗin dá yayi fira dashi. Shidai Md ido ne kawai nashi sai kunnuwan sauraren domin tuni gaɓoɓin jikinsa suke tsaya cak da aikin su, wajen iya sarrafuwa, A gaban babban d.p.o aka sune su kai tsaye Su kuma sauran jami'an sukaji da matasan da suka yi zanga-zangan, kai tsaye dake akan babban criminal ne ake magana yasa sam babu wani jan batu akan jinkirta maganar. *Army Headquarters* Suna ganin komi dake wakana amma sukayi biris babu abinda suka furta akan maganar dake ƙara yaɗuwa game da kamen da aka yi. Amma ta ƙasa sune sane da komi ɗin dake wakana a police ɗin, amma a zahiri kam shiru kake ji. A police station kuwa dake Md shine namiji shi suka fi tsananta bincikensu a kansa, amma amsar ɗaya ce sam baya da masaniya akan Ak ɗin. Hakan yasa jami'an ganin kamar raina musu hankali yake son yi, shi kuwa Md tsoro ne me tsanani tattare da zuciyarsa na irin uban gargaɗin da yasha wurin wanda suka bashi batun kai tsaye, don haka baya da yacce ya iya dole ne yayi gum da bakinsa, tunda yasan idan allurar sojoji ta tashi sunfi Mahaukacin kare iya hauka, bare ma wanda ya bashi bayanan kai da ganinsa kasan ba ɗan ƙaramin mugu akayi ba. *********Gidan su meerah kuwa idan hankalin Annenta yayi dubu to a tashe yake, Raiha kam zuwa wannan lokacin duk da ƙananun shekarun tayi kukan rashin kwanan meerah ba'a gida ba, amma haka anne ta danni zuciyarta ta hana nata tashin hankalin bayyanuwa, ko washe gari kuwa mutan gidan tamkar sabuwar kasuwa haka suka tashi da hada hadarsu, tamkar basu san abinda yake faruwa da meerah ba. Baffa kuwa tun bayan da akayi sallar isha'i babu wanda ya sake jin motsin sa daga mutanen gidan, domin kuwa kai tsaye meerah itace raunin sa, haka za itace sanyin idaniyarsa. A loƙacin da wannan mummunan labarin ya riskeshi, saida yaji numfashinsa ya tsaya cak da aiki, duk wata hanya saida yabi a sirrance don ganin al'amarin bai girma har haka ba, amma akace idan wani sammako yayi to wani kwanan tsaye yayi inji masu iya magana. Shi ɗin babban malami ne na addinin musulunci amma sai gashi ya rasa duk wata ta ganin meerah ɗin ma kawai, wannan shine dalilin hana bayyana kansa da yayi, domin sam bazai iya kallar tsakiyar idon Anne ya faɗa mata an hana shi ganin meerah ɗin ba. Sosai bakar Ralls Rayce ɗin ke shahara uban gudun fitar hayyaci a shimfiɗeɗen kwaltan, babban burin Isha Manu bai wuce ace ya ganshi cikin police station ɗin ba, domin tun jiya daya sami zancen hankalin sa yaƙi kwanciya, bacci ma ɓarawo gwanin iya sata kasa sace sa yayi, haka ya kwana cingirgir a zaune domin gani yake ai kamar ma Ak ɗin ne aka kama, don gani yake shine mutum na farko da ak ɗin ya fara illatawa mafi muni a cikin rayuwa. *AK* Tunda ya riga da yabar baya da ƙura bai sake bi ta kan kowa ba, duk kuwa irin fifigen da jama'a harma da jami'an tsaron suke famar yi a kans, amma yayi shiru yayi biris da dasu yaƙi magantuwa akan komi. Badan baya da yacce zai yi ba a'a sai don kawai yana son ganin gudun ruwansu ne, ya dai manna musu bajon haukane kawai ya fisge abin sa, burin sa dama saƙon nashi ya Isa duk wuraren da yake son isar kuma sun isa, don haka yaci gaba da shimfiɗa life ɗin sa yadda yake so. Zaune yake akan ƴar ƙaramar couch ɗin dake dining room, cikin hadaddiyar shigarsa da mafi yawanci yafi amfani dasu, fararen Dior sweet shirt ne sanye a jikinsa, sai kuma dogon wandon trouser kansa sanye cikin luxury fcap ɗin daya sanya cikin natsuwa yake breakfast nashi da ƙayatattun dinner ɗin da Vincent ya musu odar daga wani tsadadde kuma Hadadden eatary luxury Chips pepper soup na zallar tsoka sam babu ƙashi ko kaɗan a jiki, sai kuma ketchup