Mikiya complete Novel - Chapter 4
Mikiya complete Novel Chapter 4: Mikiya complete Novel Chapter 4. Hankali kwance yaci gaba da yin ɗinner gefe guda kuma yana sarrafa laptop ɗin dake…
4,294 words
Hankali kwance yaci gaba da yin ɗinner gefe guda kuma yana sarrafa laptop ɗin dake gabansa. Kamar koda yaushe yauma zagaye samudawamsa suke dashi tamkar wasu masu gadin gidan wuta, a kasaitance yaci gaba da dakilar laptop ɗin bayan ya kammala breakfast in da kamar 20 minute ya kunna cigarettes yana busa hayaƙin. Almost 30 minutes ya miƙe cikin yana nufar upstairs cikin takun mazan taka. A police station kuwa duk yadda kuke tunanin wannan abu da sauki toya zarta haka, domin kuwa ta ko ta ina ƙara rura wannan wannan maganar ake. Abin kamar wata alamara saiga labarin kama su meerah ya zama lates a yanzu musamman media da gidajen rediyo a cikin kwana guda kawai. Kusan dai ko ina ba'a rasa ƴan adawa tuni labaran ya gama karaɗe media dama kusan duka duniyar zance baki ɗaya. Md kuwa cikin kwana ɗaya takk ya fita a hayyacinsa sa, gogar tamu kuwa da ido ne kawai take bin kowa take kuma kallon duk wani abu dake wakana a tsakan kanin su, zuciyarta ta bushe ta ƙekashe taƙi kuma ta magantu duk kuwa uban jaddagadeden da d.p.o yake a kanta zuwa sauran jami'ai tun a yammacin har zuwa wayewar garin ranar.tana zaune ta kafe wuri guda da idonta daya yayi jaaaaa, a hankali wata police ta Turi ɗakin tsananin hasken daya haske mata idone ya sanyata ɗago da kanta, plate ɗin robar dake hannun ta dake shirin ajje mata a gaba, amma kuma ga mamakin ta sai taga meerah ɗin ta ɗaga mata hannu alamar bata da buƙata. "ma'am Ina buƙatar text book da pen idan ba dmw pls" Tayi maganar ba tare data motsa daga yadda take ba, ɗan jim police ɗin tayi alamar tunani kome ta tuna kuma sai tayi saurin juyawa tana barin ɗan suƙurƙurin ɗakin ajje masu laifin baya ta rufe. 10 minute sai gata ta dawo ɗauke da text book ɗin da kuma pen tsaye tayi akanta, ba tare data damu da tsaiwar data mata a kai ba ya ta fara aiwatar da abin da zuciyarta ta gama tsara mata, kyawawan idaniyarsa masu kama dana mage ta shiga zanawa a pepper ɗin, exactly tayi zanen full face nashi sai dai iyaka eye nashi ne a bayyana ne. Ita kuwa wannan police ɗin har wani sake karkatar da kai take wajen hango zanen. Tana kammala zanen ta miƙa ma police ɗin text book in, jiki na mazara ta fice ta text book in a hannun ta kai tsaye babban office ɗin d.p.o RT Atya ta nufa. A lokacin d.p.o na tare da Isa Manu Atya ta ajje text book in gabansa. "What are you doing to say?" "Sir. Meryam yebdullahi goni meerah!" "What?" D.p.o ya faɗa a zabure tare da miƙewa yana nufar hanyar woje, har da ƴar sassarfa yake haɗawa ganin ya cimma ɗakin da take. Hasken daya sake haske idonta a karo na biyu ne ya sanya ta sakin wani lalataccen kill smile dama tasan za'a rina, samm ta rasa mine ma ya hanata aiwatar da hakan tun a juya. Zanen fuskar da tayi aka d.p.o ya tura gabanta, "muna buƙatar ƙarin haske akan zanen da kika bamu!" (Anzo wajen) ta faɗa a cennn ƙasar zuciyarta. A zahiri kam ɗan duban wanda ake da d.p.o tayi a kai kaice ba tare da shakkar komi ba ta furta. "AK kenan! Inda har da gaske kuna kan aikin ku, ga Ak nan ku baza yaranku su fara farauta iyaka idonsa ne kawai nima na sama gani" jikin d.p.o har tsuma yake ya furta "da gaske kina da tabbacin wannan face ɗin na Ak ne?" Noding kanta tayi alamar tabbatar wa. A 380 suka bar ɗakin tsabar sauri hular d.p.o har faduwa take. Cikin ƙanƙanin loƙaci aka baza fuskar Ak da ake nema ruwa a jallo. Kanka ce me matasa sunyi caaaa a media game da fuskar Ak da aka ɗora. ★★★ Wani irin kafirin murmushi Ajmaal ya saki a lokacin daya kalla zanen fuskar Ak ɗin shishar daya ke zuka ya feso da hayaƙin matashiyar budurwr ko nace ƙaruwar da yake tare da ita ya sake mannata da jikinsa, a bayyane ya furta. "AK muje zuwa da dukkan alamu wannan wasan me zafi ne!, Lallai na yarda da tauraron ki yana haske ƴar jarida meerah, kece tsanin Ni! Kuma nine mahayin" sai kuma ya sheƙe da wata iriyar dariya ta marasa hankali. Tare da hade bakinsa dana wannan budurwar, ita kuma cikin kwarewa a fannin ta wani shiga sarrafa gangar jikinsa tana karasa fitar dashi daga ɗan hankalin daya saura a gareshi.
★★★ Safa da marwa kawai yake famanyi a karo na ba adadi ke nan sai yana dab da cimma burin sa. Sai wannan ɗan gaba da fatihar yazo ya rugaza masa aiki. Baki ɗaya ya gama jigata kansa gumi sai kwaranye masa jiki yake. Idan bai manta ba governor da kuma minister suna hannunsa,kenan target ɗin Ak na gama dole shine. "Inaaaaaaa hakan ma bazai taba yiyuwa sammmm" ya faɗa da ƙarfin masifa haɗi da kaima bango iska nashi, sai huci yake saukewa. (Kai wannan yaro uwarka ta haifo mana masifa da bala'i wllh) ya faɗa a cikin zuciyarsa. "Dole na dakile duk wata hanyar da nasan wannan ɗan shegiyar yaron da nasan zai ganni, kafin na gama samun mafita" ★★★ A bazata murmushin ya subce daga fuskar Ajmaal (dole na fara nuna maka ba kai kaɗai ne teterors ba Ak) ya ayyana hakan a cikin zuciyarsa tare da ciro wayar sa yana dialing wata number. "AK! AK!! AK!!!, Da kyau tsohon abokina sheɗanin sheɗanu, kuma tsuntsu me wayo" "Kwarai kuwa haka ne sabo da mun saba sheƙe sheɗanu tare da kai ba Ajmaal" "Uyummmm naji daɗi dake fashimce haka Ak baban shadanu a yanzu haka dai nasan ka girgiza ba?" Jin Sautin lalataccen murmushin Ak ɗin da yafi natsa a kaff cikin duniyar ne ak ya sakar masa. Ɗan zame wayar yayi tare da kallon screen ɗin sai kuma ya sake manna wayar da kunnunsa, still Sautin fitar murmushin ya kuma ji daga Ak ɗin. dip dip dip yaji sautin katse ƙiran da akayi ba tare da an sake furta masa komi ba. Shima murmushin ya saki domin wannan loƙacin yaci alwashi akan Ak ɗin sosai, shi kaɗai yasan shirin daya danajama hakan ciki kuwa harda ziro meerah acikin tafiyar.
To ai shikenan kooooo saimu gimtse🫰
*By AMMEY LAYLERH ✍️*
*🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀}
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 11&12 #KIDNAPPING *DRUG TRAFFICKING #AGGRAVATED ROBBERY 🤍🔥✅ __________________ ★★★ *Police station* Zaune farin dattijon yake gaban d.c.o bayan gama koro masa jawaban sa akan meerah ɗin,duba da uban kuɗaɗen daya zube masa wanda dama already yau za'a sallames, ganin tsuntsu daga sama gashashshe ne yasa jikin d.p.o har mazari yake wajen bada umarnin a kawo meerah ɗin. Cikin ƙankanin loƙaci sai gasu da meerah ɗin, shi kuma ya miƙata ga wannan dattijon. A kamilance ya musu sallama yana ma Meerah nuni da suke, saida ta ɗan yi dammm na alamar mi hakan ke nufi.kana dai tayi gaban, bata sani ba ko duk cikin aikin ne hakan. Gaban wata arniyar bakar mota suka tsaya shi da kansa ya buɗema meerah ɗin ta shiga domin kuma zuwa yanzu ta fuskanci kamar gida ne za'a maida ta. Uban gudu yake tsalawa a cikin motar wanda gudun har ma ya kusa tsorata meerah amma dake zuciyarta a dake dake sai taƙi barin tsoron nata baiyanuwa. Sunzo daidai round about wata kafurar Mota ƙirar Mercedez Benz tazo tasha gabansa, sai kuma yaji tsaiwar wata ma da bayansa hakan ya sanya zuciyarsa tsinkewa, amma sauya dake yana kawar da hasashen da zuciyarsa keson bijiro masa. be gama tunanin me ke faruwa ba ya ji ana ƙwankwasa window'n Motarshi da Bindiga daidai saitin kanshi kululu cikinsa ya kaɗa hanjinsa ya ɗuri ruwa nuni suka mishi da ya fito. hannu na rawa ya fito ganin wasu uban samudawan da yasan kuskure kaɗan zai musu su aika shi inda in aka tafi ba'a dawowa, yayi ɓeshi dukkaninsu suka yi suna sanye da facial Mask. Umurnin da suka sake bashi ne a karo na biyu ne ya sa shi tunanin wannan wasu irin ƴan fashi ne? Inda ɗaya daga cikin wannan samudawan ke ce mai "Take off your clothes" da sauri yace "What?" sauƙar wani abu me ƙarfi yaji a gefen fuskarshi, da sauri yayi ƙara tare da dafe gefen kanshi yaji danshi danshi Alamun jini, cikin ɗaga murya yace "take off your clothes,i wont ask again" da sauri dan farin dattijon yayi yanda sukace, ya rage daga shi sai gajeren wando da guntun singileti, hatta takalmanshi zobe da Agogo, sai da ya cire, bai dawo daga duniyar daya tafi ba na wuccin gadi yaji sauƙar Bindiga a kanshi. Ɗaya daga cikin samudawan ne yama na kusa dashi alamu da ido. Gaban motar ya nufa kai tsaye Sleeping powder'n dake hannun sa ya shaƙama Meerah, Kafin ta samu damar cewa komai ne taji abu a fuskanta. Yuuuu taji kanta ya fara mata, Cikin zabura tai yunƙurin dira daga cikin motar ɗin, sai dai ta kasa hakan dan cikin ƙanƙanin loƙaci jikinta yay wani irin masifar nauyi nan ta silale jikin kujera idanunta na lumshewa. Daga haka bata sake sanin mike faruwa ba kuma.
Baifi 10 minute da fitar motar ba baffan meerah ya shigo station ɗin, sosae hankalin sa yayi wani kalan masifar tashi, jin wai mahaifin meerah ɗin yazo yayi belin meerah ɗin. To waye mahaifin meerah kuma wanda ya wuce shi?, Kodai hankali ne kawai suke neman rena masa. Amma saiya danni zuciyarsa cikin tsanako da dattako irin nasa yabar station ɗin ya barma zuwa an jima kaɗan, wai a ganin sa kawai yau ɗin ma basa da ra'ayin barin sa ya ganta ne kawai shi yasa suka ɓullo masa da wannan zancen. ★★★ Wani kalar furzar da iska yayi yana maida kansa jikin saman sopa ya kwanta tare da lumshe idanunsa a hankali. Shi kaɗai yasan abinda yake ji game da taurin kan yarinyar data zaba buga game dashi. Ya fahimci lallai bata fahimci a ramin da take neman jefa ƙafarta bane. Amma zai bata loƙaci ta gama nata kalar ɗan ƙaramin wasan kafin ya fara buga babban game da sai tayi dana sanin sanin AK a rayuwarta da tayi. Idan ita ƙaramar ƴar iskar layi ce, zai tabbatar mata shi na duniya ne baki ɗaya, dan ba zubar da jini kawai ya iya ba harda cin uban duk wanda ya shiga sabgarsa. Lallai ta ɗaukarma kanta Dala ba gammo tunda tayi kuskuren zana fuskar sa, ya fahimci ita ɗin ƴar zafin kaice tun daga yanayin yadda ta mu'amulance shi a gidan jaridar su, amma ba komi tayi nata zafin kan ta gama duk zai sauƙe mata su kuwa nan bada jimawa ba. Ya jima a wajen zaune har su Axton suka dawo ɗauke da abincin da Vincent ya sasu suka yo order. Amma shi boss ɗin sai yace bazai ci ba. Ya haɗa coffee kawai da biscuits mai daɗi. yana shan coffee ɗinsa da biscuit tare da nazartar yarinyar. Koda ya kammala shan coffee ɗin bedroom ya wuce kai tsaye Maimakon kwanciya bathroom ya faɗa, ya haɗa ruwa mai ɗumi cikin bathtub tare da haɗa kayan ƙamshi kala-kala a ruwan sannan ya shiga ciki. Sai da ya kashi mituna a cikin ruwan na ratsashi da miƙar masa da kowace gaɓa sannan ya fito ya shiga wajen wanka ya ɗauraye jikinsa. Bayan ya fito salla ya fara gabatarwa tare da shafa'i da wutiri sannan ya shiga shiri. Yayi ƙyau sosai cikin shigar tasa tamkar ka sacesa ka gudu. Ga wani uban ƙamshi na tashi tamkar duka Company'n haɗa turaren ne a jikin sa. Sumar nan tasha gyara daka gansa kasan ya haɗa jini da masu jajayen kunnuwa. Hakama kwantaccen gashin sajensa sai walƙiya yake gashi kwance luf-luf ya sake fidda taswurar doguwar fuskarsa. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata sannan ya fito cikin nutsuwarsa da takunsa na tsayayyen namiji.
National Hospital atarubus 3:45pm
Accidents and Emergency aka shiga da wannan farin dattijon dake sananne ne shi babu wanda bai san waye Isa Manu ba, A kaff cikin Lagos harma da zagaye ta cikin ƙanƙanin loƙaci aka shiga bashi taimakon gaggawa.
Ba ƙaramin tashin hankali su anne suka shiga ba ganin har bayan sallar isha'i babu baffa babu dalilin sa Raiha sai kuka take, baffa kuwa da kansa ya gama kullewa ne yasa jininsa naiman hawa nan take, bai sake tsorata da lamarin ba sai loƙacin ƴan sanda suka zo da batun mutumin da ya yi belin meerah ƴan fashi sun sun tare sa a hanyar sa ta mika Meerah ga iyayen ta a round about ɗin sa na shan kwanar anguwar su malam Abdullahi gwani. Cikin abinda bai wuce kiftar ido ba labaran suke zake hargitsa media, ƙura takai ƙura kam a wannan loƙacin, a kuma daidai loƙacin ne aka shiga musu da malam Abdullahi gida a yanayi mafi munin gani. Nan da nan matan baffa biyu suka shiga yaɓama Anne maganganu baƙaƙe. Wai akan yarinyar data gama gantalewarta a titi suke neman rasa malam, wllh baza su yarda ba. Anne kammm zuwa lokacin ma ita kam babu abinda take iya fuskanta daga cikin maganganun nasu, a fisge taji kalmar ƙarshe daga cikin ɗaya daga cikin matan. "Dama ai barewa ba zata yi gudu kuma ɗan ta ya rarrafa ba, wllh malam ka auro mana masifa da bala'i, gashi kuma masifar daka ɗaya ƴanta sune suke ƙoƙarin ajalinka, kaje garin kwashe kwashenka ka auro mace mara asali wanda ba'a san inda asalin ta take ba, wanda ya wuce ƴar gaba da fatiha me bakin duniya" Dipppp ji da ganinta suka ɗauke daga nan bata sake sanin ainihin abinda ke faruwa ba. ★★★ Sannu a hankali na shiga motsa idanuna da suka min matuƙar nauyi da ɗaurewa. Sai kuma na shiga buɗesu sannu-sannu harna gama buɗesu. hasken daya cika idanunane ya sanya na ɗan tashi a zabure da sauri. komi daya faru ya ringa dawo min daki daki har zuwa sleeping pawdern da suka shaƙa min. Ƙirjina ne yay wata irin masifar bugawa da sauri na ambaci sunan Allah. Cikin sauri na mike na nufi ƙofar bathroom ɗin da nayi amfani dashi wajen uzurina. Alwala na ɗauro sauri² gudu² na fito praymad ɗin da nayi sallah akai jiya yauma na nufa, a nutse na fara sallar cike da nutsuwa.bayan na idar na sulale a wajen ina saki wani irin kuka mai tsuma rai da da zuciya. Na jima kwance a wajen ina kuka kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Nama rasa ina zan kai tunanin na. Handle ɗin dakin naji an taɓa tare da shigowa mutumin jiya da dare ne duk da cewar fuskarsa a rufe take amma tsab na gama gane shi, kasancewata mutum bai kaifin basira, plate ɗin dake ɗauke da soyayyar wainar kwai ya ajje min tare da ledar bread recipe ya juya abinsa da niyar tafiya. "Lallai hakan da kuka yi shi ne ya sake tabbatar min da cewar ku dukkanin ku lusaraine, kolaye ne tunda har kuka rasa abinda za kuyi sai kidnapping mace" nayi maganar tare da jan wani mugun tsaki. Duk da ya tsaya cak tun fara maganata bai juyo ba. Harna kammala maganar kuma bai tanka min ba ya buɗe ƙofar ya fice tare da sauri tare da kulleni ta baya. Ido kawai na zubama ƙofar wasu kalar hawayen bakin ciki na sake gangaro min da gudun tsiya. A yanzu ba wai kaina kawai nake tausayi ba su Annena baffana Raiha ɗina nake tausayi da halin da zasu shiga sune suke matuƙar tada min da hankali fiye da komai. Bai cika 20 minute da fita ba sai gashi ya sake dawowa farin handkerchief ɗin dake hannun sa ya jefa saman fuskana hakan yasa na fara ganin bibbiyu kafin kuma na tafi luuuuuu. Ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai bayan sallar zuhr, a wani bedroom ɗin na daban na sake tsintar kaina ba wanda aka fara kaini ba. Da kyar cikin mutuwar jiki na miƙa na nufi hanyar da tsammanina ya gama bani bathroom ne, ilai kuwa bathroom ɗin ne toothpaste da brush na farke su a ledartarsu, saida na fara wanke bakina kafin alwala sallar zuhr tayi tare da fara duk wasu addaoin da suka zo bakina. Ledar takawey ɗin dake gaban gadon naja bisa dole zuwa gabana. Domin kuwa in banda kukan yunwa babu abinda cikina yake. Kaɗan na ɗan chakala na ture gefe domin ma samm sai naji bana jin cin abincin ma. Mahaukacin ƙamshim da hancina ya shaƙar min ne ya sanya ni saurin ɗago kaina zuwa Said ɗin da naji ƙamshim na fitowa. Da wannan idanuwan dana zana na fara cin karo, wanda har ƙarshen numfashina baran taɓa mancewa dasu ba. Sanye yake cikin wasu tsadaddun luzary Ride vizzon sky blue colour daga ƙasar rigar kuma fari kaɗan irin hadarin Dubai ɗin nan ce dai.sai lallausan farin wando trouser kansa sanye cikin hular luxary supereme irin ta sanyin nan sai facemask irin Turkish ɗin nan shima, yau kam babu glasess ɗin da yake toshe idonsa dashi. Fuskarnan a matukar haɗe. Chair lind ɗin dake gefe da gadon ya janyo zuwa gabansa, zaune yakai zama irin na wanda suka isa zama ne irin na zaratan sarakunan da suka kai sarakai ba muna sarki ba. Wanda hakan da yayi ne ya shagaltar da Meerah a kallonsa. "What wrong with you flower pie?" Ya faɗa cikin daƙilallalliyar muryansa, a rikice ta dawo nutsuwarta tana dedeta kanta, tare da hararar inda yake zaune. A fusace ta furta "miye Amfanin kidnapping na da kuka yi?" Wani malalacin kill smile ne ya subce mishi a bazata. Domin samm baiyi zaton bakinta zai iya murta wata magana ba, amma kuma idan yayi duba da tsaurin idonta da tsaya samm hakan ba abin mamaki bane. "Wannan bakin naki zai kaiki ya baro ki silly girl! Idan kika ce zaki buga game da Ak to kuwa tabbas zubar hawaye bata shirya barin idaniyarki ba ke nan" Cike da tsiwa da son hana ganin lagona na sake maida fuskana gare shi tare da furta "Never for ever ka rubuta ka ajje Ni Meerah Abdullahi gwani saina sanya ka gudun ceton rai a tsakiyar karnuka" A bazata yaji sauƙar kalaman nata don haka ya zuba mata cat eye's nashi tare da folding hannun wansa saman ƙirjinsa. Don shi maganar nata dariya ne yaso bashi amma dake tantirin kansa ne hakan ko ajikin shi. Saima gira ɗaya daya ɗage mata tare da furta "weldone pie" tare da juyowa da kallonsa a kanta ya sakar mata wani lalataccen murmushi. "Tabbas kuwa karen zai mutu da haushin kurar" ya faɗa idonsa cikin tsakiyar nata idanun still murmushin gefen bakin nan bai bar fuskarsa ba. "Bad boy da dukkan alamu kana wasa da wannan Meerah ɗin amma dai muje zuwa musu iya magana sukance ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare" Cikin majestical takunsa ya nufo inda nake tare da matsowa daf dani. "Did I look like a comedian to you?" Yana faɗar maganar ya nufi hanyar barin bedroom ɗin baki ɗaya cikin nutsatstsen takunsa mai cike da ƙasaita. Bayan ya mata wata halamar data gaza fashimtar kota miye. ______ Shigar Isa Manu a zancen ya saka ƴan sanda sake ɗaukar zafi, Dan a yanzu D.c.o ɗin ne ma da kansa yake gudanar da binciken kidnapping ɗin Meerah ɗin tare da Inspector atya murail. Al'amari kamar wasa akan ɓatan Meerah ƙaramar magana na neman zama babba. Dan ƴan sanda sun matuƙar zafafan bincike akan maganar duk inda ka wulla magana ɗaya ce, duk da kuwa shi kansa Isa Manun kidnapping yarinyar yaso yi.
*🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀}
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 13&14 #ROMANCE## #BLACKMONEY #KIDNAPPING *DRUG TRAFFICKING #AGGRAVATED ROBBERY## #AMAZING W*w(☞ ಠ_ಠ)☞
https://www.aihausanovels.com.ng********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. ******* FOLLOW US ****** WhatsApp Number: 08104493215 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************* _______________________________ ***Sosae police report ɗin da suke kan aikin nemo wanda sukai kidnapping yarinyar tare da case na Isa Manu suka sake ɗaukar zafi na gasken gaske.duk da shi kansa bai san inda kansa yake ba tunda yana very critical condition ne, wanda hakan keda matuƙar haɗari sosae. Duk wasu wuraren da suka san zasu sami news ko yaya ne samm basa wasa da damar su, gashi babban yaron Isa Manu'n wanda baya a Nigeria'n ma yana daga ƙasar Poland ne yayi stating ƙarar . sannan yasa a tsananta binciken case ɗin duk faɗin Lagos dama kewayenta ya kuma yi musu albishir ɗin kyauta mai tsoka, muddin suka samo masu hannu acikin case ɗin. Abinka da manya nan da nan suka bazama don sosai ya mugun sakar musu kudi masu gwaɓi, tako ta ina jami'an tsaro sun ɗau zafi sosae kawunansu ya ɗauki ɗumi. Kan kace me maganar tayi spreading kamar gobara a bushashshen ciyayi. Gidan su Meerah sosae hankalu suka sake tashi ganin malam Abdullahi yana a mugun yanayi,ga Amma dake hospital har yau bata san inda kanta yake ba. Sai wasu siraran hayawe da suke ɗan zubo mata time to time sosae likitoci suke iyaka bakin ƙoƙarin su akanta. Sai dab da Asr Amma ta farfaɗo abu na farko data fara nema itane Meerah. "WHO WHY su waye ? Su waye masu son rabani da hasken rayuwata! Su waye ku?¿" Dr nimra dake tsaye tun farkon farkawar Ammance ta shiga bama Ammn baki akan ta kwantar da hankalinta. Sadda kanta kawai ƙasa not saying anything saidai ita kaɗai tasan irin halin da zuciyarta take a ciki da irin ɗacin dake danƙare acen cikin tsakiyar ƙirjinta. A hankali ta maida idanunta ta lumshe tana haɗiye yawun daya tokare makoshinta, zafi mea mugun raɗaɗi take ji a zuciyarta ji take kamar ana gasa mata zuciyar a oven ne kuma a tarfa mata narkakkan Salman. Meerah ita kaɗai ce jininta daga ita Raiha sune suka maye mata gurbin ƴar uwa, ɗan uwa, UWA,UBA dangi baki ɗaya. Su kaɗai ne hasken rayuwarta kuma sannan rana tsaka ace irin waɗannan muggan musifun sun faru da rayuwarta?. Ita da Meerah ɗin ta kuma har ake tunanin ma zata kwantar da hankalinta abin ma da bazai taɓa yi yuwa ba kenan. Ahankali ta maida idanunta ta lumshe tana jin yadda ƙirjinta yake mata wani mugun bugu tarkar ƙirjinta zai fashe zuciyarta ta fito fittt haka take ji. Faɗowar mutum ajikin da kuka kukan da aka fashe mata dashi ne yasa ta san Raiha Raihan tace a jikin ta. Wani irin ƙanƙameta jikinta tayi domin gani take itama amana iya kidnapping nata kamar meerah'ɗinta. Ahankali ta shiga ɗan bugun gadon bayanta comfortably tana streaming abubuwan dasu faru da ita koma tace suke kan faruwar. Malam Abdullahi da ya zuba mata idanunsa tun farkon shigowar su da Raiha ne ya ɗan shiga takawa zuwa gareta jiki a matuƙar sanyaya. "Ita ƙaddara wajibatunce akan ko wane bawa kuma mumini mai iman domin Allah baya taba dorama bawansa kaddarar da bazai iya dauka ba. Kana ita kaddara da kike gani rubutacciya ce tun daga rabbis samawati! Me yasa kike ma taki ƙaddarar kuka?. Idan muka sanya ma zuciyarsa mu nasibi da miƙa al'amurra ga Sarkin da shi kaɗai ne buwayi gagara misali sai kiga ya sauƙaƙa mana tarin ƙalubalen dake cikin makauniyar ƙaddarar mu. Ya kuma kawo mana mafita akan hakan cikin sauƙi!, Duk da zuwa yanxun nasan shuɗaɗɗan al'muran da suka faru ne shuke zeroying main naki. Ki daure ki daure ki daure kiyi haƙur AYSHATUL MUBINA" Ƙara ƙanƙame Raiha tayi a cikin jikinta tana jin inama inama inama ace, saidai tasan wannan inama ɗin ta barta har gaban gaban abada abadan. Ahankali ta shiga noding kanta tanayi tana ƙara ƙanƙame Raiha dake matse a cikin jikinta. "Bawai ƙaddarata nake ma kuka ba Abbu maira tarin ƙalubalen dake tattare da ita nake ma kuka. Bawai kukan faruwar wani abu ba kukan ƙinnn..... Sai kuma wani irin kuka yaci ƙarfinta irin mai sarke numfashin nan. Hawaye taci gaba dayi tana sobbing ahankali tana jin raunin zuciyarta daya fara kamewa komai daya faru na dawo mata kamar yanxune komai ke faruwa. " Hasbunallahi wani'imal waqeel! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ya Allah help me, don't take her away from me now.Not now please I can't take it.... Malam Abdullahi ya shiga fada cikin tsananin tashin hankali ganin numfashinta chakkk ya tsaya da bugu. A guje Norse suka yo dakin don suka komi dake faruwa ta cikin camera'r dakin, Nan suka shiga kokarin ceto numfashinta.
*AK*
Tsaye yake jingine da jikin Railer fuskarnan a matse wandan jeans ne a jikinsa army green da farar singlet yayi stocking nata ta cikin wandon ya daure da beld. Sai light green din top wadda ya balle duk maballanta ya barta a bude iskar da ake kadawa a gurin na diban rigar nashi kamar zata cire. Gaba daya rigar tabar jikinsa sai singlet din kawai, zaune akan chair lind din dake cikin balcony'n tare da crossing kafarsa daya kan daya. Sosae iskar dake kadawa a wurin tare da kamshin flowering dake wurin suke bashi cikakkiyar nutsuwa, Shi yasa most especially yake zaman wurin. Lumshe idanunsa yayi tare da fadawa duniyar tunani tamkar komai daya faru ne a wancen lokacin haka komai ya Shiva zeroying maind nashi.