Kenza eBookz

Mikiya complete Novel - Chapter 5

Mikiya complete Novel - Chapter 5

Mikiya complete Novel Chapter 5: Mikiya complete Novel Chapter 5. _"Waya baka umarnin kai harbi? Ka gaya min waya baka umarnin kai Harbin?" Ya fada a…

4,494 words

_"Waya baka umarnin kai harbi? Ka gaya min waya baka umarnin kai Harbin?" Ya fada a matukar tsawace _"Ba kowa Sir"_ Wani dan iskan kallo sir din ya cillo mass cikin yanayin fusatar zuciya ya doka table din dake gabansa. _"Me yasa kayi?.... Folding hannuwansa yayi akan kirjinsa tare da furta. _"Bacin Raine sabo da manyan shugabaninmu suna Neman ruguza kasar da muke_" ya furta cikin rashin shakkun a gaban Wanda yake. _"Sanin kan Kane wannan mutumin da muka kama shine babbar hujjarmu......_ _"wacce hujja kuma sir kullum maganar kenan, munje mun shayo bakar wuya tukuru wajen kame masu laifi amma daga karshe manyan kasar sai su fitar dash_" ****** _" Shi yasa kai kuma ka harbe shi?, Hukumar soja tana da dokoki bada k'awa zuci take aikiba. Sojoji sama da dubu dariya ne a wannan sansanin maciya kyakytattukan yabo macimma nasarori masu lambobin yabo. Saidai a cikin su akwai wani bakin digo daya Kaine. A duk lokacin da Muke kan aiki irin haka Kaine mutum na farko da take fara bamu marsala, A matsayinka na soja ko kadan baka iya sarrafa kanka. Ko kadan baka iyawa koda yaushe cikin fada kaiba kowa bane face Dan matsala ba bama sojoji da kasar sa matsala ABDULMALEEK KUUWAIT_" Wani irin doka coffee table din dake gabansa yayi, cikin tsananin bacin rai ABDULMALEEK KUWAIT da gajiyawa da rainin yawon da sir din nake yake kawo masa ya damki wuyar rigar sir din. _"Sabo dani jirgin kasa ne duk Wanda ya shiga hanyata markadeshi nake, sannan zaku iya dakatar da ruwa idan kuka tare shi saidai idan ya tashi ballewa tamkar teku yake hadawa yake ya tafi da duk wani gurbatacce wadan da suka kasance marassa amfani_" Wani wurgi yayi da Mr.president tare da sutale rigar kakin sa ya cilla masa a saman fuska hadi da hular pcarp nasu na soldiers. "DUDEeeee.... Jaheed ya fada da karfin bala'i amma ina duk yadda jaheed yake kiransa da son dakatar da shi haka ya fice abinsa. Wannan shine mafari silar komai da komai......

************

"Are you okey Boss?" Muryar Vincent ta katse shi daga zurfafa dayay a duniyar tunani. Shisha pot dinshi ya janyo zuwa gabansa ya kunna tare da janyi pipe din ya fara zuka yana fesar da hayakin ta baki ta hanci. Comfortably yake shan shishan yana streaming shudadden lokacin. Runannun idonsa ya dago tare da duban Vincent dake tsaye akansa har lokacin tamkar wani me gadin hana dan Aiken mutuwa daukar ransa. "Ina bukatar a safiyar gobe media tayi kalace da wancen luxuries story in!" Dan risinar da kansa yayi tare da furta "An gama Boss"

★★★★

Duk yadda naso sha re dinner lunch da ake ajje min as dinner night kasawa nayi, domin kamm kowa yasan bana da juriyar yunwa don ko ina cikin ciwo ne tofa bana iya fushi da abinci bana wasa da cikina samm. Warner's din na janwo gaba na takeaway ne kusan 3color's akwai pizza, sai potato's abalon, sai jollop rice wacce taji namomi masu dan banzan yawa.

*🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀}

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 15&16 #ROMANCE## #BLACKMONEY #KIDNAPPING *DRUG TRAFFICKING #AGGRAVATED ROBBERY## #AMAZING W*w☞ ☞

______________ #DON

_Wannan itace duniyar da muke rayuwa a cikin ta wacce take kunshe dajin dadi da kuma tsatsanin azaba. Kalilan daga cikin ta sine suke jin dadinta mafi yawan cikin ta kuma sune suke shan hawalarta. KIYAYYA, HASSADA da MUGUNTA sune ababen da suke kara ta'azzara komai a cikin wannan duniyar. Karni bayan karni shekaru naci gaba da shudewa amma babu wani Abu da yake sanjawa, saima kara ta'azzara yake abun tambayar anan shine. Shin wannan duniyar zata taba sanjawa kuwa?.... Sabo da masu karfin ikon cikin sune koda yaushe suke azabtar da talakawan cikinta, burinmu NIGERIAN'MU ta gyara dama duniyar baki daya. To amma ta yaya hakan zata faru???...... Let's go a comments section DON√_

Wannan kayataccen rubutun shine baki daya yayi trending a safiyar yau ta raba.

Inda baki daya ya message din ya dauki hankalun mutane fiye da tunanin mai karatu, domin magana ake ta gyara da gyara kai.duk wata kafa sune dai labaran da suka zama latest irinsu.....

Facebook Tiktok Instagram Telegrams Twitter

Jikin sanyin safiyar yake dan running kadan kadan a cikin kewayen anguwar ta victoria Islan gefensa lioness, said gefen damar sa Vincent ne gefen haggunsa kuma axton ne, daga baya kuma miles ne sai lioness dake a gaba. Kare ne na musamman ba irin sauran karnuka bane ROSER ce ta Haifa mishi. Tana haihuwasa tabar duniya shi kuma Ak ya dauke shi ya kaishi wajen ZAKI aka chakudashi da yayanta ita ta shayar da shi duk ayyukansa irin na zaki yake yi komai tare da lioness yake yi. Suna kaiwa gida ya bude dakinsa ya maida shi bayan ya dan shafa saman kansa tare da zuba masa ruwa a tsakiyar kansa. Tamkar wani mutum ya wani irin girgiza tare da fesar da ruwan dake jikinsa, Ahankali yabar wurin yana nufar compound din gidan. Duk inda ya wulga sai kaga wadan nan samudawan dai suna risina masa tare da gai da shi.

★★★

"Will you shut that your dirty mouth up!, are you stupid Ina magana kana yimin zancen banza da wofi, kodai ka samu tabin hankaline ban sani ko ban sami labari Impossible wannan bamai yiyuwa bane".. Yadda ya hayayyako yana masifar kadai zai sheada maka koma miye aka fada masa a cikin wayar bame dadi bane. " Me gida ka yarda dani na rantse da uban daya haifi ubana Salman baya cikin airport din nan, kasan bazan maka yawa ba fa me gida" Sosae jikin Isa Manu ya dauki wani irin Mazarin bala'i Wanda safiyar yau ne aka sallameshi daga hospital, ta karfin tsiya bawai don ya gama samun sauki ba. "Kai lele karka sa jinina ya tafasa fa, in banda zancen banza taya za'ace an rasa dan mutum sukutum tum a airport. Hauka ma kenan yanfa kaga last call nawa da salman din du du du bai wuce 40 minutes ba"

"Na rantse da assamadu me gida bincike iya bincike nayi amma fa maganar gaskiya salman sammm baya cikin airport din nan.....

"Stop your dirty mouth Lel... Chak ya tsaya ba tare daya kai ƙarshen Eee ɗin ba sakamon rumgumeshin da yaji anyi ta baya, kafin ya tsinci murya ɗa mafi ƙololuwar soyuwa a gareshi yana furta. " Nayi Surprise Daddy" Wani irin guntun numfashi Isa Manu ya fesar tare da juyo da Salman zuwa gabansa, sai kuma yaɗan shiga bubbuga gadon bayansa tare da furta. "Daddy's boy kafa tsoratar dani sosai irin sosae ɗin nan fa nake nufi" "So sorry daddy" Salman ya furta tare irin kama gefin kunnen sa guda. Wani ƙayataccen murmushi Isa Manu ya saki tare da nufar stairs da yaron nashi Yana faɗin "kai dai muje sama akwai abubuwan yi da yawa a gabanmu" nan suka nufi saman abinda. Har ɓangaren sa ya kaishi saida ya tabbatar Salman ɗin ya shige bethroom kana yabar ɗakin yana furta. "Karka ɗauki dogon laƙaci daddy's boy ka sameni cikin office ɗin cikin gida just 40 minutes kawai na baka" Ficewa yayi a sashen ta wata ɓarauniyar hanya. 45 minutes ago Sai gashi ya fito sanye cikin ƙananun kaya na shan iska, office ɗin daddy'nsa dake cikin gidan ya nufa direct. Yana tafe yana latsa faskekiyar wayar dake rike a hannunsa. Kai tsaye ya tura office ɗin mahaifin nashi ba tare dako neman izini ba, da sauri Isa Manu daya lula wata duniyar ta daban ya ɗago kansa tare da duban her yaron nashi abin alfaharinsa, ganin yadda daddy'n ke kallon sane ya sanya shi ƙarasowa cikin office ɗin yana zama kan kujerar dake facing da mahaifin nashi. Wasu files ya janyo tare da turasu zuwa gaban Salman. Files ɗin ya shiga dubuwa sosae kafin ya ɗago kansa yana dubar mahaifin nasa tare da ɗan fada fuska yana wani irin yamutsata. "Daddy?" Ya faɗa cikin wata kasalalliyar muryan dake nuni da taɓarar nan irin ta ƴaƴan hutu. "Yes daddy's boy duka abin da kagani a jikin files ɗin haka nake son komi ya tafi a yadda na tsara" "Amma daddy meye amfanin haɗa alaƙana da ita yarinyar da ka sako batun neman neman aurenta?" Wani dogon numfashi Isa Manu yaja tare da tattaro hankalin sa baki ɗaya zuwa ga Salman ɗin. "Ita kuwa take da amfani daddy's boy, idan har hasashena ya bani daidai yarinyar tana da wani ɓoyayyan abu kodai tana akwai abinda ta riga ta sani kame da wani abu!" Ya sauƙe numfashi kafin yaci gaba da faɗin. "Tunda har akayi kidnapping nata Ni meyasa basu haɗa dani ba, neman aurenta da zaka shiga shine zai janyo hankalin koma waye zuwa gare mu. Kuma yarinyar zata kasance a ƙarƙashin ikon mune hakan shine first kafin mu tafi plan B"

"Amma daddy....

"Amma me? Daddy's boy" Isa manu'n yay saurin tarar numfashin Salman ɗin. Hakan ya sanya shi yin shiru ba tare daya sake yunkurin furta ko wacce kalma ba. "Hakan shine best solutions namu boy kana a tada hankulan jama'a. Ka sanya su Bom fire su tada zanga-zanga game da kwamushen su governor da kuma minister da Akayi ta haka ne kaɗai zamu cimma burin mu. Ya zaman mun jefi tsuntsu ɗaya da dutse biyu kenan Ni dasu Boshosho zamuji da sauran". "Wow Wow hoooooo wuuuu woohoo hooo good idea daddy ina alfahari dakai.... Salman ya fadi yana ihu tamkar wani ɗan daba.

Mu haɗe a next fage my gold fan's......

~ BY AMMEY LAYLERH ✍️~

*🦅 MIKIYA 🦅*

_Mai hangen nesa 👀_

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________

*NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 17&18

🤍🔥✅

★★★

#ANNEH POV

Kwananta biyu aka sallamota bawai don ta gama warware wa ba saidan sallamar data naima da kanta. Tunda ta dawo cikin matan gidan babu wanda ya ko leƙo inda take, duk da kuwa cewar suna sane Amma baƙin hali da sama Rai wahala ya sanya babu wanda ya kalli inda take. Ita kuwa samm ba su bane a gabanta ɓatan ƴar tane kawai damuwanta, duk irin uban fari da jikin da take da a cikin kwanaki uku babu shi ga duhun da farar fatarta da sirka. Kasancewar jikinta da suffarsu irin na cikakkun larabawan nan ne wani irin kyau da haiba Anne ke dashi. Wannan shine kyau nata da yanayin kyawun jikinta shi yafi komai ƙona zuciyarsu abokan zaman nata. Tana zaune saman darduma tayi irin kifa kan nan na rashin samun nutsuwar zuciya. Yanzu a wanne hali *DIDI* take dama haka rashin ɗa a kusa dakai yake?, Dama haka ko wacce uwa take ji idan tana a irin halin da take?. Toma wai miya haɗa *DIDI'ƊINTA* ta wannan AK ɗin? Ak is a known criminal in Lagos, ta gagari kowa he is a kidnapper as well as an arm robber. "Ya ALLAH ya ARRAHAMANU ka kare min *DIDI* aduk inda take ka bayyana min ita cikin amincinka ya zul'Arshim majeed" Wani irin suya zuciyarta take mata yau inama ace tana da Asali? Inama ace tana wata ko wani ɗan uwan, yau inama ace tana da mahaifiyar da babu abinda zai hana ta rungume ta tayi kuka, tayi kuka iyaka kuka tayi kuka me sunan kuka ko zuciyarta ta samu salama da nutsuwa. Cikin zubda hawaye ta furta _"SHIN WACECENI?"_

Kamar daga sama taji Muryar maman haidar tana furta. *"KEBA KOWA BACE face tsintacciya mara asali mara galihu ƴar tsintuwa wacce uwarta tayi cikin shegenta ta hullar a bola"*

Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfin bala'i tana jin yadda ƙirjinta ke sama da ƙasa. "YA RABB!" Ta faɗa tana wani irin fesar da iska ta cikin bakinta me zafi. Kamar daga sama taji ƙarar shigowar sako a wayar *DIDI'ƊINTA* Sake kulle idanuwan tayi kafin jikinta na rawa da janyo wayar data zame mata tamkar itane meerah'ɗinta. Hannunta har karkarwa yake wajen buɗe saƙon domin gani take a kowanne loƙaci kan iya turo saƙon bayyanar meerah'ɗinta ne ta cikin wayar. Sai dai kash!.....

Saƙon ma bai hada hanya da kidnapper's ɗin ba, saƙo ne da akan turo mata duk shekarar duniya na zagayowar ranar haihuwarta ta wata ɓoyayyar Number. Ga abinda sakon ya ƙunsa.

*_ OHhhhh On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a woman like you is indeed a gift, People tell me that the best years are still to come. I have to agree with that because my upcoming years will be spent with the world's most amazing woman. Happy birthday to someone who improves every life she enters. You always know how to make an impact, but none so strong as the one you made on my heart. I will turn your black and white world into full-blown technicolor. Happy birthday to the leading actress of my JAAN my SUNSHINE, If anyone is deserving of all the happiness in the world, it's you, you are a wonderful mom, a loving woman, and a fantastic human being. Happy birthday 4ever❤️ Barka da zagayowar ranar haihuwa my JAAN May your birthday be filled with joyful moment❤️_* Tun bata kai ƙarshe ba taji wasu zafafan hawaye suna bin gefen kumatunta *"ALHAMDULILLAH"* Ta faɗa cikin wani irin amon murya Incheerfully. "ABTINI MEERAH, I Missed her with All my heart ANNE ki kaini wurin beloved Nima" Raiha ta cikin muryan da yaci kuka sosai. "DIDI adda'armu take da bukata yanzu Raiha kici gaba dama addanki adda'a Allah ya bayyana mana ita cikin amincinsa.....

Da sauri Hajiya Hajiya umma dake tsaye tun ɗazun ta sanya bayan hannunta tana sharce ruwan hawayen tausayin Anne'n, Wacce ta kasance itane tamkar uwaa ga Anne'n. Domin wani irin girma take bata irin na ƳA da UWA. Labulen ta tura tare da shiga ɗakin da sallama kasa amsata duk suka yi domin rumgume junansu sukayi suna wani irin kuka me tsuma zuciya. Zaune takai kan ɗaya daga cikin kujerun parloun. "Shin dama ashe idan Allah ya jarrabi bawansa da wata ƙaddarar kuka ake AYSHATUL HUMAIRA?, Allah ake miƙama dukkan al'amurran ata kai kuka a gareshi domin shine buwayi gagara misali mai kowa mai komai! Ce ALHAMDULILLAH" "ALHAMDULILLAH" Ta sake maimaita wa cikin ɗacin murya, kafin ta kife kanta saman ƙafafun Hajiya umma cikin wani irin raunin murya ta shiga faɗin. "Ni ma ina da buri ina da mafarkai irin na kowacce ƴa mace ina da burin na rayu tare da ƴaƴana ba kamar yadda nawa IYAYEN suka zabi wulaƙantar dani ba. sai dai kash ƙaddara ta shata min liyi da hakan ta sanja min nata salon yadda alƙalamin ya zana dole haka zanbi babu yacce na iya. Ni musulma mace me ƙarɓar ko wacce iriyar aduk yadda tazo min. Daga loƙacin da Akayi kidnapping DIDI sai tsoro da fargabar me zai faru ya tasoni gaba! Amma dana tuna Allahu buwayi gagara misali sai tsoron hakan ya fita a raina. Zuwa yanxun yaci ace na daina ma ko wacce iriyar ƙaddara kuka UMMA idan nai duba da yadda zanen tawa ƙaddarar ta kasance min. Kenan ƙaddarar ɓatan DIDI Share fagen wata tafiya ce mai sarkakiya da ɗaure kai. Wata kalar ƙaddara ce mai rikitarwa shimfiɗa ce wacce take tafe da nata salon. Yaushe wannan rufaffen sirrin dake shimfiɗe a cikin zuciyata! Zai fito fili?, A cikin ko wacce rayuwa akwai mutuwa haka ma a cikin mutuwa akwai rayuwa toni a wanne mizanin nake? Mabuɗin kowacce ƙofa makulli ne sai dai Ni tawa ƙofar wani irin wawakeken rami ne wanda aduk loƙacin da wani yayi yunƙurin bi ta cikinsa yake ruftawa dashi. Shin Me nama nawa IYAYEN da suka zabi wulaƙantar dani? Ki bani Amsata UMMA!!!.......... Ta faɗa da wani irin gursheshen kuka irin wadan yake fitowa daga cikin tsakiyar ƙirjin nan "ALHAMDULILLAH Allah abin godiya Allah mun gode maka" Sune kalaman da Hajiya umma tayi ta maimaita wa kafin ta shiga nanata kalmar _INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN²_ Hakan ya sanya Anne kamawa itama suka hau maimaitawa a tare harda ma Raiha.....

By AMMEY LAYLERH ✍️~

*🦅 MIKIYA 🦅*

_Mai hangen nesa 👀_

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________

*NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

Page 19&20

🤍🔥✅

★★★★

*_KUWAIT_*

_Kuwait officially the state of Kuwait. Is a country in west ASLA.. it is situated in the northern edge of Eastern Arabic at the tip of the Persian gulf. Bordering Iraq to the north and Saudi Arabic to the south. With a coastline of approximately _

*_KUWAIT_*

*_7:16pm_*

_ARABELLA BEACH HOTEL_ *_Bad decisions mayco lates is let's party alcohol our later. The palms beach_*

★★★★★ Wani irin deep romantic sound ne ke tashi ƙasa sosae cikin wata iriyar romance voice ne ke tashi cikin muryan larabawa. Sanye yake cikin wasu fitinannun fararen qanannun kaya da farar singlet yayi stocking farar singlet in ta cikin wandon ya ɗaure da belt. Sai farar rigar daya ɓalle duka maɓallanta ya barta a bude. wuyanshi rataye da guitar yana kaɗawa ahankali.... Abinda zaifi ɗaukar hankalinka a wajen shine tarin jama'ar dake cike da wurin, yadda kasan tururuwa sai ihu suke da whistling yayinda shikuma ke rero waqarshi cikin cool voice nashi cikeda nutsuwa da kuma burgewa. kamillaliyar fuskarnan tashi ma'abociyar fara'a dakuma yadda dimple dinshi ke loɓawa shine abu mafi ɗaukar hankali a gareshi. Idanunshi a lumshe suke wanda hakan yaba zarazaran lashes ɗin shi damar haɗewa, ga uwa uba pointed nose ɗin shi daya dace da fuskarshi. Dama duk wani ɗan zafin Kai duk inda 8pm to a Arabella hotel take mashi kowa hankalinshi da imaninshi ya tattare ne akan wannan tsayayyen matashin dake tsaye gabansu.

kanshi sanye da headphones samm babu ko pcarp a kansa, sai kwantaccen gashin dake nan kwance saman qeyarsa irin na cikakkun larabawan nan in banda walwali da ɗaukar idanu babu abinda sumar take aikin yi, ga wani irin qamshin haɗa haɗen mayuka masu azabar ƙamshi da tsada keta faman tashi. Har wani irin luuuuuu ya keyi da idonsa alamar waqar na hawan kansa sosea Tsaiwarsa ya ɗan gyara hannuwansa zube cikin aljihun wandon sa idonsa lumshe, Cikin wani irin Sound wizard In dake tashi a cikin iyaka zagayen room ɗin da yake. Ga color's blue red popple dake haske irin ta cikin dum Night ɗin room ɗin. Mutane sai ihu da whistling suke suna ƙiran *_ZAID EMAAR's_* *_ZAID KUWAIT_* Shi kuwa ya riga yayi nisa Afif tajuddeen ne ya hauro kan step ɗin da ZAID ɗin ke tsaye ɗan raɗa ya masa a kunnen sa kafin ya lalubo tafin hannun ZAID ɗin ya saka mishi BURGER yana barin wurin. _9:30pm_ ya tashi duk da kuwa maganar da Afif tajuddeen ya raɗa mashi amma saida ya gama harkan gabansa.Duk da haka Bai samu kansa daga barin hotel ɗin ba sai 10:10pm. Yana fitowa coumpaun ɗin hotel mahaukatan security'n dake girke da wurin suka yi saurin buɗe may ƙaruwar 2024 Toyota grand Highlander. Yana faɗawa ciki suka ma manyan motocin key tare da cilla hancinan motocin nasu kan shimfiɗeɗen kwaltan babban birnin kasar Kuwait ɗin.

A gaban wani irin Mahaukacin katon gine nema zance ne ko mention OHO min, amma dai zanen ginin kai da gani ma ba sai an tsaya baka amsa ba zaka gane cewar a masarauta ce. *_EMAAR's EMARANCE MENTION_* Shine sunan dake walƙiya ta saman ginin DPY WELPAPER ɗin dake haskaka ginin da difference color's. A ƙa'idar wannan masarautar ba'a hong ko kaɗan. Wani ɗan ficik ɗin yellow'n card ɗaya daga cikin security'n dake cikin motar ya zira. Abin mamaki sai kawai Ross gold get suka raba tsaƙiya nan motocin suka sake danna hancinan motocin su da mugun gudun tsiya. Ya Ilahi wani irin Mahaukacin katon mention ne ya bayyana masu passage daban da daban. A bakin Ross gold get ɗin farkon wasu irin mahaukatan TIGHT SECURITY ne jibga jibga. Hannuwansu rike da manyan bindugu na tashin hankali. harabar gidan kanta tamkar gari guda ne domin girmanta abin azo a kallane. gashi qasan shimfide yake da kwalta ga flowers of different types shufke a gefe gefen titin.

Haka suke wuce get na farko cikin uban sharara gudun nan tafiya mai nisa koko ince gudu mai nisa suka kafin su isa maid entrance ɗin gidan. Nan ma saidai Saida suka sanya wani card ɗin different da wance domin samm ma basu haɗa koda kama bane kana get na biyu ya buɗe. Ya Ilahi kai jama'a shi kanshi wannan gida ko ince masarauta yafi qarfin a ƙirata da SOLDIER'S HOUSE sai dai a ƙirata da HOUSE DIE. Eeeeeeehhhhhh mana tabbas kuwa house die tunda abinda idanuwana suka gano min kenan. A haka har Saida suka kai get na ƙarshe wanda a nan babban tashin hankalin yake. #tight security #Movel : mobile #Police interpol Kai jami'an tsaron da babu wandan da babu a cikin wannan shahararriyar masarauta, banda tarin kuyangain da suma sukama masarautar ƙawanya suka mata GARKUWA. A hankali wannan 2024 Toyota Highlander grand tai parking a dab da wani irin azababben flat Wanda yake zagaye da tarin barori na tashin hankali, fararen sawayensa ya fara zirowa wacce take sanye cikin lallausan takalmin fata irin na sarakai,kafin gangar jikinsa ta biyo baya. Ga hasken street lights ɗin da haske harabar wurin tamkar rana, hakan shine ya sake bayyanar da tsantsar kyawun da subhanahu wata'ala yamay kana ganin mutumin kasan ƙarshe ne wajan tsari da kuma iya ado. Tuni wannan tarin kuyangain suka shiga masa kirari cikin harshen larabci. Wani irin mugun kallo Zaid ya watsa musu Azafafe cikin tafiyarsa ta sanyi² zafi² ya juya kai tsaye ya nufi plat na mai martaba *ONOYIN* (sarki).....

_"OUMMIEYHHH?.....

Ya faɗa da ƙarfi cikin ɗaga murya yana shiga makeken falon daya qawatu da kayan alatu ga tattausan carpet da duk takawa ɗaya zakaji kamar zaka nutse aciki don taushi da laushi ne. "OUMMIEY! ONOYIN أين هو بابا ن ياكي؟ " Ya faɗa da sautu me amsa amo. Sama ya nufa ya fara hawa stairs ɗin da shima kanshi abin kallo ne Kasancewar stairs ɗin irin mai lanqwasar maciji nan ne. Saida ya ɗauki loƙaci kafin ya isa. Wani qaton falon ya sake kutsa kansa ciki shima mai mugun kyau ya sake wuceshi sannan ya shiga passage din dazai sada shi da ɗakin oummiey. Koda ya qarasa ƙofar ɗakin oummie banda haki babu abinda yake yi don yasha ha gudu sosai gani yake tamkar elevator bazai kai shiba. Wata kyakkyawar dattijuwa na hanga zaune bisa tattausan carpet gefe kuma irin pillow dinnan ne masu kyau zagayayyu irin wanda akafi gani mostly dama na gidajen sarauta ne ta kishingiɗa akai, plate ne a gabanta cike da yankakkun fruits wanda take ɗauka da ɗaɗɗaya tana ci. Ɗayan gefen kuma shako mako ne, sai tea party, tare da mia piatte ga kuma milagro

Saurin dagowa matar tayi ta kalli saitin data jiyo muryan hubby Inta hasken dake haskaka duniyar ta wato ZAID.

(_Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai talikai daya halicci wannan halitta mafi kyawu mai cike da haiba_) Na faɗa daga cikin zuciyata

"Where is my papa? Oummiety!"

Ya sake tambayar mahaifiyar nashi cikin cukurkuɗaɗɗen English nashi. Idanunta ta ɗan lumshe kafin ta miƙa mashi kyakkyawan farin hannunta, noƙe nashi hannun yayi a bayansa tare da furta. "Ohh ohh Papa na" ya faɗa cikin sakalci tare da noƙe kafaɗa. Da hannun tamai nuni da wani tsararren room wanda yafi kama da ɗakin tan garan Domin an kawata room ɗin ne da wasu shiles row glasses tamkar irin gidan lantarkin nan. A zafafe ZAID ke taka ƙafafunsa yana tafe yana fesar da numfashi ta cikin bakinsa kansa ƙasa yana tafe cikin sassarfa. koda wasa bai yadda ya ɗaga kansa ba bare ya kalli irin yadda uban kuyangain ke zubewa ƙasa bisu gwuiwowinsu. Shifa sammm koda wasa bai ƙyaunar duk wani abu daya dangaci sarauta ya tsani gaba ɗaya calture nasu komai a takure yake yinsa. So shi yasa sammm Allah bai haɗa jininsa da wannan sarautar ba shi mutum ne da yake son yayi rayuwarsa yadda yake so. Da wani irin sauri yakai gwuiwowinsa ƙasa tare da kafe mahaifinsa da lulu eye's nashi da suka sosae ganin yadda jikin PAPA'N ya koma loƙaci guda. "PAPA?" Ya ambaci sunan mahaifin nashi cikin wata iriyar raunatacciyar murya. Tare da ƙoƙarin kai hannunsa jikin PAPA'N shi. Da wani irin Mahaukacin mari yaji ya ɗauke kyakkyawar Innocent face nash, amma tsabar jinin sarautar dake yawo a gaba ɗaya ko wacce magudanar jini ta jikinsa ya sanya ko gezau be yi ba. "Kada ka kuskura ƙazamin hannunka ya taɓamin tsarkakken jikin ɗan UWA na" muryar 2wins ɗin mahaifinsa ya katse shi a kausashe a karo na biyu da yake kokarin sake kai hannunsa jikin PAPA'N shi bayan uban marin da MOH Ta bashi. Da wani irin mugun gudu *JESRA* ta kulle idanunta cikin kunar zuciya. A nutse Zaid ya ɗago da kansa zuwa ga baki ɗaya jama'ar parloun. EL-HUSSAIN wanda ya kasance biyunini PAPA'N shi, sai MOH JIDDO wadda ta kasance mahaifiyar su PAPA'N shi. MAHBOOB,DAWOOD, MUZAFFAR, MUSADDIQ, AL-MUSTAPHA, MANDOOD, EYESHA, MANSOOR ,REYNA. Sune a room ɗin baki ɗaya wanda mafi yawancin cikin su ke binsa da wani irin mugun kallo, kallo ne irin na tsantsar tsana suke binsa dashi.

A...MALEEK..... Idan baiyi ƙarya ba kamar haka Papa ya ambata saman laɓɓansa ko takan jama'ar da suka ma room ɗin ƙawanya bai biba ya haɗe fuskarsa dana mahaifinsa sa. Ta ƙarfin bala'i ZAID ya furta "ABDOUL-MALEEK?" Wani irin razanannen kallo mafi yawancin ɗakin suka shiga bin ZAID dashi. _ABDOUL-MALEEK_ kowa ya shiga maimaita wa cikin zuciyarsa har jikkunan wasun na ɗaukar mazari, sunan da Ambatarsa kawai tashin hankali yake haifar wa, sunan da jinsa yake tada hankula bama hankali, sunan da suke ɗaukar sa wani shuɗaɗɗan al'amari a cikin tarihin rayuwar su. _Tasssss_ Wannan karon EL-HUSSAIN ne ya ɗauke fuskar ZAID da wani irin bahagon marin da dole ya sanya shi dafe kuncinsa. Kiiiiiiiiiiiiiii MANDOOD da yafi kowa na wurin zuciya haka yaja hannun Zaid ya kaishi har bakin door yana cilla shi woje. Cikin tafasar zuciya MANDOOD ya dubi Zaid rinannun eye's nashi ya furta. "Wannan wani shuɗaɗɗan al'amari ne, wata kirkirarriyar tatsuniya ce, sunan ABDOUL-MALEEK shafaffene a cikin tarihin wannan masarauta ka kula" Fuuuuuuuu ya kaɗa da niyar juyawa chark ya dakata jin wata mahaukaciyar dariyar da Zaid ya sheƙe da ita. Hakan ya sanya A tsananin fusace mandood ya ɗaga hannu zai wanke fuskar Zaid ɗin da wani wawan mari. Cak Zaid ɗin ya rike hannun nasa tare da cewa "Kada kayi wannan ganganci" Zaid ya faɗa tare da wurgar da hannun mandood ɗin gefe tare da sakin wani ɗan iskan kill smile Yana furta. "Waya faɗa ma cewar haihuwar Sarki a Dawa kamar ABDOUL-MALEEK yana zama shuɗaɗɗen al'amari, An haifesa ne a Dawa tsaƙiyar karnuka domin farauta. Ubangiji ya bashi ƙarfin zuciyar da zai iya fuskantar ko wanne irin ƙalubale, Iyaka ambatar sunan sa yakan sanya wasu girgizar ƙasa......

"ZAID!!!!..... MANDOOD ya katse shi a matuƙar tsawace.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull