Mutum da duniyarsa complete - Chapter 26
Mutum da duniyarsa complete Chapter 26: Mutum da duniyarsa complete Chapter 26. A gidan Sheikh Aliyu dai sai muce Alhmdllh, dan suna cikin aminci…
3,365 words
A gidan Sheikh Aliyu dai sai muce Alhmdllh, dan suna cikin aminci gwargwadon iko, bandama dai Maimuna dake fama da lalurar laulayi, wadda kuma Alhamdllh tana samun kulawa ga mijinta da Jiddah ma, dan ƙiri-ƙiri Jiddah ke ƙoƙarin hanata wasu ayyukan, dukda itama Maimuna na hana jiddah, acewarta amaryace saita gama amarci sannan. Amma sam Sai Jiddah taƙi bari. Hakanne yasaka Aliyu kuma samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, a gefe kuma yana addu'ar ALLAH yasa su ɗore hakan. Shida Jiddah dai kam tun ranar bai kuma takurata ba, dan soyake takuma sakin jikinta tamkar yanda yaga ta fara, ƴan wasanni dai kam yakanyi da ita, dan har yanzu a sashenta yake kwana saboda kwanakin da Maimuna ta ƙara musu, da safe Jiddah taita ɓoye fuska batason su haɗa ido, shikam yata tsokanarta kenan yana dariya.
Yaukam tunda suka gama fira a sashen maimunatu ta dawo nata sashen, tana gama shirin barci saiga Aliyu ya shigo shima cikin nasa shirin. Kallonsa taɗanyi tana amsa sallamar a saman laɓɓanta, mamaki yabata, takula tunda yasha kunun kwakwar ɗanzun yakoma wani shiru, firarma daina saka musu baki yayi, yabarta itada Maimuna kawai. Cikin sauke numfashi tace, "Kobaka jin daɗine?". Murmushi yay mata danya kula batasan dawan garinba, amma harga ALLAH tausayintama yakeji shi, dan yasan yau kam bazai iya juriyar binta a hankaliba tunda yasha kunun kwakwarnan............😶✍🏻
*_Ya Sheikh masoyan jiddah fa sunce kabi a sannu dan ALLAH🙊😆⛹♀_*
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [12/27/2019, 11:35 AM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[53➖54]_*
............A matuƙar kasalance ya zauna a bakin gadon idonsa akan ƙirjinta, hakan data fahimtane yasata yinƙasa da kai da ƙoƙarin gyara ƙaramin gyalen data ɗaura akanta ya rufe mata ƙirji sosai. Sassanyan murmushi yayi yana lumshe ifanunsa da sauke ajiyar zuciya kafin yakuma buɗewa a kanta yana miƙewa tsaye, hanyar fita ya nufa, saida yaje ƙofar sanan yajuyo yana kallonta "Idan kingama abinda kike, Kisameni a ɗakina". Kamar zata fasa ihu tace, "to". Bai kuma cewa komaiba ya fice abinsa. Shiru jiddah tayi a tsaye, zuciyarta sai saƙawa da kwancewa take, tana mamakin miyasa yace taje can? Tunda tazo gidan bata taɓa shiga ɗakinsaba, kullum shike zuwa ya sameta, taja wasu mintuna kafin ta matsa gaban madubi ta ɗauki turare ta fesa da wasu sirrikan ƙamshi na humra, sannan ta saka hijjab har ƙasa ta fita. Gidan tsitt babu wata hayaniya gashi babu nepa, rabonsu da wutarma tunda safe, saida aka tada gen ɗin masallaci, kuma suna kammala karatu aka kashe, koda Aliyu ma yashigo gidan har an kashe. Taja wasu adadin mintuna a bakin ƙofar falon kafin ta tura ta shiga da sallama. Babu kowa a falon, hasalima dunɗum yake da duhu, fitilar wayarta ta haska falon dashi, komai yamata ƙyau gwargwadon iko, kujeru da labuloli duk kalar ruwan siminti, sai baƙi kaɗan, ƙofa ɗaya dake rak a falon ta nufa, ta ɗora hannunta saman handle ɗin, harzata murɗa saikuma ta fasa tayi tsaye tamkar mai fargabar shiga ɗakin jarabawa. Saida taja kusan mintuna biyu kafin ta murɗa ƙofar ta buɗe, da sallama ta shigo a bakinta kanta a ƙasa. Aliyu dake zaune a bakin gado laptop a gabansa yana dannawa ya ɗago ido yana kallonta da amsa mata, kafin ya ɗauki kofin shayinsa yakai baki. "Kosai na taso nayi tarbane Amarya?". Kai Jiddah ta girgiza tana cigaba da takowa ciki da faɗin, "A'a nagode". Murmushi yayi yacigaba da abinda yakeyi, "Bismillah ki zauna to". Takowa tayi zuwa bakin gadon ɗan nesa dashi ta zauna. Kofin shayin ya miƙa mata. ta girgiza masa kai alamar a'a. Baice mata komaiba ya cigaba da akinsa, itama saita jawo littafin *KITABUT TAUHID* daya ajiye tana dubawa. Kusan mintuna huɗu suna a haka kafin ya ɗago yana kallonta, "Afuwa gimbiya inaɗan rage saƙwannine, kozaki tayani?". Murmushi tayi tana riƙe baki, "Wai inani ina wannan saƙwannin? Aina manyane". Ɗan murmusawa yay kawai yana cigaba da aikinsa, "Hakadai kikace, amma ai kuma bana wasa baneba Jiddatulkhair. Shin Kin haddace littafin nan ne?". Ɗagowa tai taɗan kallesa ta janye idonta "A'a ba dukaba, mun fara babu daɗewa na daina zuwa makarantar". Sosai ya kalleta yace, "miyasa?". da ƙyar ta iya fisgo maganar tana inda-inda, tunda yataɓa cemata bayason ya tuna ta taɓa aure, "lo lokacin wancan au..ren ne". "Humyim" kawai yace yamaida kansa. Kasa daurewa tai saida taɗan kallesa saboda yanda ya bata amsar, ganin yacigaba da aikinsa itama saita cigaba da duba littafin. Minti kusan ashirin yanata aikinsa, kafin ya janye laptop ɗin gefe yana faɗin "Alhamdulilahi, hajiyata basai kicemin na huta hakananba". Cikin rufe fuska Jiddah tace, "Haba saikace wani aiki?". "Aikine mana tunda nabar Matata ita kaɗai" yay maganar yana Matsowa jikinta. Jitai duk kasala ta saukar mata, taɗan matse jikinta waje ɗaya tana sinne kanta. Sumbatar hannunta yay dake riƙe a nasa, "kinyi alwalar barci?". "A'a" ta faɗa tana girgiza masa kai. Batareda yace komaiba ya fara ƙoƙarin cire mata hijjabin, batayi jayayyaba ta barsa ya cire, kayan barcinta wando da riga kalar pink suka bayyana, sihirtaccen ƙamshin da take zubawa ya shaƙa yana lumshe idonsa, kansa ya ɗaura bisa kafaɗarta, gashin gemunsa dake taɓata ya saka tsigar jikinta tashi, hancinsa yakai jikin wuyanta yana shinshina, tuni jikinta yakuma yin sanyi ƙalau. Ganin yana neman zurmawa tace, "Zanje nayi alwalan to". A kasalance ya sauke numfashi kafin ya matsa daga jikinta yana nuna mata hanya alamar taje tayi. Sum-sum tamkar munafuka ta wuce bayi ɗauro alwalar barci. Bayinma yamata ƙyau, gashi a tsaftace babu wani ƙazanta, kodayake dama batai tunanin samunta daga gareshiba, dan ko farcen malam ka kalla kaɗai ya isa shaida maka shimai matuƙar tsaftane. Taɗan jima sannan ta fito, yanda ta barshi haka tazo ta iskeshi yana duba littafin data ajiye. Ta gefen ido yake kallonta harta zo ta ɗayan gefen ta kwanta can ƙarshen gadon. Ruwa takeson zuwa tasha, amma kallon ƙurullar da yake mata duk saita daburce. Shima lura da hakanne ya sakashi ɗauke idonsa daga kanta yana faɗin, "Ko kina buƙatar wani abune?". "Uhm zan sha ruwa ne" jug ɗin Ruwan dake ajiye a dirowar gefen gadon ya tsiyayo ya miƙo mata. Zaune ta tashi ta karɓa tanasha, shikuma ya miƙe yanufi bayi. Lokacin daya fito Jiddah hartayi addu'ar barci tai luf. Baice mata komaiba ya shinfiɗa abin sallah domin yin shafa'i da wutiri kamar yanda ya saba. Duk abinda yake Jiddah na kallonsa, amma taƙiyin koda ƙwaƙwƙwaran motsi dazai tabbatar da hakan. Yaɗan jima yana addu'a kafin ya miƙe yay shirin barci, tunda Jiddah taga zai cire jallabiyar jikinsa saita rumtse idonta, shi baimasan tanayiba, duk zatonsa kotayi barcine mashi. Harya hawo gadon ya kwanta da kashe fitilar tana jinsa, hannu yasa ya lalubota yana jawota jikinsa, "Haba Kairunnisaa, waya ce miki haka mata da miji ke kwanciya?". Shiru tai takasa koda tari, saida taji yana hura mata iska a kunne ne tashiga sauke numfashi da ƙyar, hakanne yasakashi fahimtar idonta biyu dama, sai kawai ya canja zuwa wani salon daban..........🙊⛹♀
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Baƙi dai duk sunyi ƙaura, hatta dasu balu duk sun tafi, sai umma taji gidan duk babu daɗi, yayinda kewar jiddah ta dawo musu sabuwa fil a zuciya. Koda Uncle yahya yazo ɗazunma da safe haka yaytajin babu daɗi da baiga jiddah ba. Yazone sun tattauna akan batun sauran kuɗin sadakin Jiddah daya rage a wajensa, shinema har yake sanar mata Abba yaje nemansa ranar, amma sai ya cema yaron yace yaje Adamawa, kuma yana gida babu inda yaje. Murmushi Umma tayi tana faɗa masa suma dayazo nan bai zaunaba ya fice abinsa. "To ALLAH ya ƙyauta, insha ALLAH idan ya huce zanje nabashi haƙuri, dan nasan da gaske ba a ƙyauta masaba ɗin, amma bamuda wata mafitane sai wannan ɗin". Murmushi kawai Umma tayi, dan tasan ko maƙiyi bazaice yahya baiyiba, mutumin kirkine dayasan haƙƙin ɗan adam da darajar zuminci. a wannan zamanin irinsu ƙalilanne a cikin al'umma.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Su Ashir harsun kama hanyar gidan Abba sai yayansu ya dakatar dasu bayan zuciyarsa tamasa wani tunani. Canja hanya yayi zuwa police station. Bala yace, "Wai ina kuma zaka kaimune yaya?". "Station zamuje Bala, ɗaukar hukunci a hannunmu bai daceba, ai dama da jiƙaƙƙiyar kuɗi a tsakani, kunga daganan saimu wuce kotu". A fusace Ashir yace, "Amma yaya kabarmu muɗan sassafashi mana, kaga daga yanzu baya sake munafincin zuga waniba ai". "cooldown ƙanina, abinda zamuyi masa yanzu saiyafi duka zafi ai". Shiru duk sukayi badan sun soba, a station duk abinda ya dace sun yishi, atake akaje kamo Abba.
Abba yana kasuwa hankalinsa kwance, dan sosai yakejin daɗi ganin a kwana ukunan babu sammacin da Alhaji garba yace za'a kawo masa na kotu, shi kansa Alhaji garban ma baya zuwa kasuwa gaba ɗaya....... Yana tsaka da wannan tunaninne ƴan sanda suka iso shagon bisa kwatancen dasu Ashir sukai musu. Sosai gaban Abba ya faɗi, amma saiya fuske yana mazurai, ƴan sanda dai bayani sukai masa na buƙatar ganinsa a ofishinsu. Kamar Abba zai musa saikuma ya fasa ganin idanun mutane yadawo kansa gaba ɗaya.
Tunda aka baro kasuwa da Abba ƙananun magana ke tashi, kowane baki da abinda yake faɗa akan wannan tafiya da ƴan sanda sukayi dashi.
★★★★★★★★★.
Hajia hindu da yara tun suna tsumayen shigowar Abba har suka bari, gashi yau yamusu alƙawarin sayo musu kayan daɗi idan zai dawo kasuwa, hakanne ya saka yaran zumuɗin dawowarsa, amma har goma na dare tsit kakeji babu amo babu labari. Ƙosawar dasu kalifa sukaice tasakasu fara tsaki, itako hajia hindu takaicinta da tunaninta yanakan cewa Abba yana gidan Ummane jarabarsa ta kaisa, hakanne yasakata ɗaukar masifaffen fushi, tacika tayi fam dan kumbura, sai kaɗa ƙafafu take na tsumuwar bala'i. Wasa-wasa dai har shabiyun dare, tuni ta kora yaran ɗaki sunje sun kwanta, itakam tana zaune tana shiryama Abba shika-shikan bala'in da zata ɓarar masa idan yadawo gidan. Dataga lokaci ya jane taje ta kwanta itama.
Hummm😑😶
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Iya tantance tsakanin aya da tsakuwa jiddah tayi a daren jiya kam, shikansa ya Sheikh yasan yabuɗe ƙwanji da yawa, kuka dai hajjaju jiddah an shasa har an godema ALLAH, sai taji ranar ashe wasan yara akayima, yau ɗinne ta tabbatar da menene daren farkon. Tana zaune bisa abin salla ya dawo masallaci, kanta a ƙasa ta amsa masa sallamar. Muskarsa shinfiɗe da murmushi ya zauna a bakin gadon yana kallonta, cikin rawar murya tace, "Ina kwana". "Ba irin wannan gaisuwar akema mijiba ai kairunnisaa". Batareda ta shiryaba taɗan ɗago ta kallesa tai saurin janye idonta gefe. "Ya kika fasa kallon nawa Hauwa-Jiddah?". Shiru tayi takasa bashi amsa, tasowa yayi da kansa ya kamata ya miƙar tsaye, dukda tagaza kallonsa bai damuba, ya cire mata hijjabin tareda sumbatar goshinta da laɓɓanta, cikin kuma sanyaya muryarsa yace, "ALLAH yay miki albarka kinji, yabama su Ummi ladan tarbiyar da suka baku". Hawayen da take maƙalewa suka silalo, a zuciyarta ta amsa da amin. "Kukandai bazai ƙareba Jiddatulkhair?". Yay maganar yana share mata hawayen. Haɗiye sauran kukan tayi da ƙyar, cikin sinne kanta tace, "A'a na daina, bara naje kar aunty tace zatayi aiki da kanta, kaga jiya ta yini batajin daɗi ma". Murmushi yay idonsa akan laɓɓanta dake motsawa a hankali, ya ɗora goshinta saman nasa yana kallonta, "Ai kema bakida lafiyar, kiyi kwanciyarki zanje na tayata ni, dan yau a gida zan yini". Ba ya da ta iya dole tabi Umarninsa ta kwanta ɗin, shikuma ya fice sashen Maimuna. A kicin ya sameta tana ƙoƙarin kwaɓa filawar da zatai fankasu, ya sumbaci gefen kuncinta yana faɗin, "Jazakillahu bil jannah Ummudduniyah". Murmushi tayi dukda kishinsa da takeji na taso mata, taɗan juyo itama ta sumbaci kuncinsa tana amsawa da, "Tare da kai Kalby". "Ya babyna?". Yay maganar yana zagayo da hannunsa a cikinta daya fito sosai. "Yana cikin ƙoshin lafiya Nurry, sai dai kewar Abbunsa da yakeyi sosai". Numfashi ya sauke a cikin kunnenta, cikin raɗa yace, "Shima Abbu yana kewarsa matuƙa, ko zamuje yanzu mu gaisa". Dariya Maimunatu ta sanya, "Yaya nikam rufamin asiri, ina ƙanwata?". Murmusawa yay yana sakinta kafin ya shafa kansa, cikeda jin kunyarta yace, "nabarota tana azkar, mizan tayaki dashine?". Maimuna tai murmushi kawai, dan tasan badai azkarba, da azkarne ai dabaizo tayata aikiba, a filikam sai tace, "A'a na hutashsheka". "Nikuma ban hutar da kainaba madam". Babu yanda ta iya dole ta barsa sukayi aikin tare, bayan sun kammala yakoma ɗakinsa. Wayam ya tarar babu kowa jiddah ta gudu, amma an gyara ɗakin tsaf yanata ƙamshi. Wanka yayi yashirya cikin ƙananun kaya, sosai yay ƙyau tamkar ba shiba.
Jiddah data gudo tuni koda tadawo sashen natama ba kwanciyar tayiba, gyara ɗakinta zuwa falo taɗan kumayi, ta ɗaura ruwa ta dafa takuma gasa jikinta sosai sannan tai wanka, tagama shirinta tsaf tana ƙoƙarin kunna wayarta Aliyu ya shigo. Kallo ɗaya tamasa ta ɗauke kanta tana amsa masa sallamar, sai dai yamata ƙyau sosai, yaune ranar farko data taɓa ganinsa da ƙananun kaya, ashe dama yana sakawa....? Har ya iso gabanta bata saniba, saida ya riƙo hannuntane tadawo hayyacinta. "Malama jiddah tunanin mi akeyine haka? Ko nawa?". Murmushi tamasa kawai. Shima saiya murmusa yana faɗin "Kinyi ƙyau sosai tawan, irin wannan gayu haka mai hana ango fita?". Sosai ta dara yanzukam tana rufe baki, shima dariyar yakeyi zuciyarsa namasa daɗi da sakin jikinta da takeyi dashi sosai yanzun.
Saida ta saka gyale sanan suka nufi sashen Maimunatu, yauma dai kosau ɗaya Jiddah bata yarda sun haɗa ido da maimuna ba, sanan bata saka baki yau a hirarsu sosai kamar sauran ranakun, shi Aliyu yasan kunya da sauyin da jikinta ya matane ya kawo hakan, itakuma Maimuna sai takejin tsoro a ranta kar jiddah ta fara sauyawa saboda daɗin miji data fara ji.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da safe koda su Kalifa suka wuce makaranta sai hajia hindu tai shirin zuwa gidan Umma da nufin mata barka da tashin baƙi wai, amma kuma abinda ke a ranta shine son ganin idon Abba.
Ta iso Umma ce kaɗai a gidan, Walida da Zarah duk sun wuce makaranta, zarah wata islamiyya ta shiga anan anguwarsu ta matan aure, ana zuwa tara a taso sha ɗaya, gani tagama ssce exam ɗinta da zaman banza sai Umma tace tashiga islamiyyar kafin ALLAH ya kawo mafita, idan auren ne kokuma saɓanin hakan. Umma na jan ruwa a rijiya Hajia hindu tayi sallama ta shigo. Ɗagowa Umma tayi tana amsa mata sallamar da mata sannu da zuwa, sai dai ƙasan ranta tayi mamakin ganinta, dan ranar tariyar jiddah ma sai yamma liƙis tazo gidan, kuma bata daɗeba ta tafi. Amma sai Umma ta tareta da ƙyaƙyƙyawar fuska, bayan tace mata tashiga falo itakuma ta ɗiba ruwa ta bita. Kafin Umma ta shigo hajia Hindu tai saurin leƙa bedroom ɗinta wai ko Abba yana ciki, wayam ta gani, hakanne ya sakata saurin komawa ta zauna saboda jin motsin tahowar Umma. Ruwan Umma ta ajiye mata sanan ta zauna suka gaisa suna tambayar juna yara. Kafin cikin kissa hajia hindu tace, "Ai zuwa nai dama Zarah ta rakani nagano gidan ƴata Jiddah". Umma tace, "ALLAH sarki, gashi kuma kunyi saɓani tanama islamiyya". "Kai amma banso hakanba wlhy, shiyyasa naita roƙon Abbansu ya jirani mufito tare tunda yace nan zaizo". Murmushi Umma tayi batace komaiba, hakanne yasakasu yin ɗan shiru na wasu mintuna...... Sallamar Uncle yahya ne yasaka Umma miƙewa tafito tana amsawa, yanda ta gansa kamar a rikicene ya sata tambayar "lafiya kuwa Uncle ɗinsu?". "Wlhu Maman Nafisa babu lafiyarnan, dan yaya aka kama tun jiya, sai da safenan naje kasuwa nakeji, naje station ɗin da aka kaisan kuma sunƙi bani belinsa, yanzu dai haka zancen danake mikima sunce kotu za'a shiga gobe idan ALLAH ya kaimu". Cikin dafe ƙirji Umma tace, "Akanmi ni Yagana?". Cikin tsantsar damuwa Uncle yahya yace, "maganar kuɗin Alhaji Garbane". Hajia hindu tafito itama a rikice tana sallallami, mamaki sosai Uncle yahya yayi da ganinta, amma dayake a ruɗe yake sai baibi takantaba suka shiga maganar mafita kawai.............✍🏻
*_Masoya ina miƙo ɗunbin gaisuwa a gareku tareda fatan alkairi, alkairin ALLAH ya kai a gareku aduk inda kuke, Comments naku na sakani nishaɗi ƙwarai da gaske, shikuma ke ƙaramin ƙwarin gwiwar muku typing koban niyyaba, ina godiya da addu'oinku gareni ga mahaifina😄🥰🥰🥰😘🤝🏻👍🏻❤_*
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
[12/28/2019, 12:33 PM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[55➖56]_*
..............Belin Abba dai ya gagara gasu Uncle yahya gaba ɗaya, dagashi har Umma kallo ɗaya zakai musu ka fahimci suna tare da damuwa, hakama su Zarah harda kukansu, sai Ummace taita lallashinsu. Ɓangaren Hajia Hindu ma tashiga damuwa, hakama yaran data sanar musu duk sai suka shiga rashin walwala, itama saita kwantar da kai suka haɗu dasu Uncle yahya akai cuku-cukun lauya aranar.
*WASHE GARI*
Washe gari ƙarfe shabiyu aka shiga shari'ar su Abba, tun a bayanin ƙarar jikinsu Uncle yahya yay sanyi, anama Abba tambaya, amma sai yaƙi amsa laifinsa, saida aka kai ruwa rana shida Lauyan Alhaji Garba, saida shedun dake tsakani lokacin da aka amshi kuɗin suka bayyana kafin Abba ya nutsu. ya amsa karɓa kuɗin Alhaji garba da yayi, amma yay bayanin yanda sukayi dashi daya bashi auren Jiddah, daga baya kuma saiyace ya janye. Sosai ran Alƙali ya ɓaci jin sunyi amfani da yarinya cikim harƙallarsu, take anan ya yanke hukunci dan ƙ Shari'ar bata buƙatar zama na gaba kuma "Bisa ga sauraren wannan shari'a da mukayi, dakuma amsa laifin da wanda ake ƙara yayi, tareda shaidu ƙwarara, wananan kotu ta yanke hukuncin dolene Alhaji Zakari yaro ya biya Alhaji garba kuɗinsa naira miliyan ashirin da biyar kamar yanda suka tsara lokacin auren ƴarsa, sanan miliyan Ashirin da biyar dayace ya barmasa dolene yacika alƙawari ya bar masa ɗin, tunda anyi auren, kuma yarinyar harma ta tare a gidansa, wani abune daban ya rabasu bayan auren, shikuma Alhaji zakari yaro bazaici miliyan ashirin da biyar ɗinnan shi kaɗai ba, zai ɗauke miliyan goma ne a ciki, sauran miliyan sha biyar kacokan zai ɗaukesu yabama ƴarsa da yay auren jari da ita. anmasa sassauci yafara biyan Alhaji garba ƙuɗinsa kafin ƴarsa, yanzunan za'aje da dillalai gidansa da inda yake sana'a a ƙiyasta da kuɗin da ake binsa, idan sunkai abashi canjinsa, idan basukaiba yanema ya cika nanda sati ɗaya kacal. Kotu". Alƙali ya buga guduma an tashi kenan. Sosai hankalin Abba yagama tashi, banda zufa babu abinda yakeyi, kotu kam tuni ta ɗauki ƙananun maganganu, kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan wannan lamari Ita Umma ma tarasa abin cewa, jinwai Jiddah taci miliyan goma sha biyar. Shi kansa Uncle yahya abin yay masa wani gingiringin, su zarah kam sunrasa mizasuyi, baƙin cikin halin da abbansu yake ciki, ko farin cikin kuɗin da ƴar uwarsu ta samu. Hajia hindu kam ai tana cikin ruɗani, a ganinta wannan shari'ar batayiba, ita kuma ƴaƴanta shikenan su tashi a tutar babu, kai ina da sake alƙur'an.