Kenza eBookz

Mutum da duniyarsa complete - Chapter 27

Mutum da duniyarsa complete - Chapter 27

Mutum da duniyarsa complete Chapter 27: Mutum da duniyarsa complete Chapter 27. Umma da yara gida suka nufa gwiwa a sake, Uncle yahya kuwa yabi jami'an…

3,327 words

Umma da yara gida suka nufa gwiwa a sake, Uncle yahya kuwa yabi jami'an tsaro dake tare da abba. Kasuwa aka fara zuwa babban shagonsa dake danƙare da kayan kicin, nan take mahukunta suka fara ƙiyasta abinda ke cikin shagon da shagon kansa, dan tuni yazama mallakinsa dama. Har magriba suna cikin kasuwa ana cakusawa, daga ƙarshe akaima shago da kayan ciki kuɗi naira milyan ashirin da biyu, sai cinikin ciki dubu ɗari tara da wasu canji a sama, amma basu cika miliyan ɗayaba, hakanne yasa akabarsu a miliyan 23 kawai. Sallah kawai sukayi aka nufo gidansa, dama tuni su ashir sun kawo dillalalai ana zuwa maganar kuɗi kawai akayi, ansaya naira miliyan bakwai shima gidan, kuɗi sun kama miliyan talatin kenan, saura miliyan goma ake nema kenan harda na Jiddah. Hindu dai kuka take rurus yaranta na tayata, wanan wace iriyar masiface, shikansa Abban kukan zuci yake, shikenan yau tashi tagama ƙarewa, ƴar kwanciyar hankalinsama ɗayace sune kuɗin da akace yabama jiddah, yasan insha ALLAHU hannunsa zasu dawo, dan karɓewa zaiyi koda karfin tuwone. Komawa akai da abba station, Uncle yahya yawuce gida jikinsa a sanyaye. Sunbar Hajia Hindu na neman yin ƙaramin hauka, dan taci alwashin sam bazata amince da wanan tsarinba. A daren ta kira ƙaninta tantirin ɗan isaka yana zaune a legas tace yataho kano gobe-gobe. Baƙaƙen magana yafara sakar mata dan basa shiri sosai dama, ta dakatar dashi tanai masa bayani dalla-dalla, jin zancen kuɗine saiya kwantar da hankalinsa, atake yay mata alƙawarin baro legas shida yaransa da adaren ranar. Wannan shine yaɗan saka mata kwanciyar hankali, dan tasan bazasu tashi a tutar babuba dai kenan suma.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Jiddah duk batasan hidimar da akeba, dan Umma ta hana kowa ya sanar mata, amma su Aunty Nafisa dasu Aunty Sauda duk an sanar musu da halin da ake ciki, dukda abinda yay musu kasancewarsa mahaifinsu hakan bai hanasu shiga tashin hankaliba da tsananin damuwa.

Washe gari aka ida tattare kuɗin dake bank accaunt ɗin Abba da wani gidansa dake karkasara ana haya, kuɗi sukakai miliyan talatin da shifa da ƙyar, baida wata sauran kaddara sai gidan dasu Umma suke ciki, shima sai akayi cinikinsa miliyan uku da rabi, yamayi darajane saboda a cikin tsohuwar anguwa yake wadda gidaje keda daraja komai lalacewarsu, dukda ma dai gidan fes yake, ballema anmasa fenti lokacin bikin Jiddah da alhaji garba. Dabarar da Uncle yahya yayi itace roƙar alƙali a saka gidan dasu Umma suke ciki a lissafin kuɗin jiddah, hakanne yasa aka ɗeba kuɗin Alhaji garba miliyan ashirin da biyar aka danƙa hannun su ashir, sauran miliyan sha shida da takardun gidan dasu Umma ke a ciki aka damƙama Uncle hayha, saura dubu ɗari biyar Abba zai cikama jiddah, anbashi sati ɗaya yakawo cikon kuɗin Jiddah rabin miliyan. A ranar aka sako Abba da yamma liƙis suka taho da Uncle yahya daya ɗakkoshi da nufin ajiyeshi gida, shikuma yakoma yakai ƙuɗin Jiddah banki, dan canne kawai zasu tsira sai ƙura ta lafa kuma asan abinyi da su. Zuciyar Uncle yahya a tsarkake take, dan haka yayma abba rakiya har cikin gidansa da aka sayar wanda hajia hindu take ciki. Abin mamaki saiga hajia hindu taimusu tarba mai nuna alamun damuwa da halin da Abba yake ciki, harda rungumeshi a gaban yara babu ko kunya. Da wanan damar Abba yasamu damar gwargwaɗa mata wata magana. Kanta ta jinjina masa sanan ta sakesa tana kallon Uncle yahya. "Dama dawowarku muke jira yahya, dan harma munfara haɗa kayanmu, kwanaki biyu kawai suka bamu mubar gidanan, dan ALLAH kozaka taimaka mana da kimtsa kayan ɗakin Abban kalifan". Kallonta uncle yahya yayi, kamar zaice wani abu saikuma ya fasa yaɗan kalli agogonsa, yamma tayi lis, ga kuɗinnan da yakeson kaiwa banki "Hindu inaga mubar aikinan zuwa da safe, yanzukam dare yayi gaskiya". "To shikenan hakanma babu damuwa, amma taimakamin ka dakkomin wani akwati dake sama a cire takardun gidan Jiddah karsu shiga ruguntsumi". Uncle yahya bai kawo komai aransaba, ya maida kallinsa ga Abba dake zaune su Hussain sun zagayeshi, "Babu damuwa, wannene ɗakin?". Da hannu ta nuna masa, babu musu ya nufi ɗakin kansa tsaye, saɗaf-saɗaf hajia jindu tabi bayansa, yana shiga taja ƙofar ta rufe. Da sauri Uncle yahya yajuyo yana ƙwala mata kira da roƙon ta buɗesa, amma ƙiri da muzu taƙi. Dawowa tayi wajen Abba tana faɗin "Nagama aikin da kasani Abban kalifa". Da sauri Abba yaja hannunta sukabar gaban yaran, "Yauwa hindu, abinda yasa nace mu kullesa saboda mu samu mubar gidanan, dan ko sama da ƙasa zata haɗe bazan bama jiddah waɗannan maƙudan kuɗinba, maza duk abinda yadace ki haɗa mu kama hanyar kamaru, dagacan zamuyi sudan, munbar Nageria kenan har abada". "ɗari bisa ɗari na gamsu da jawabinka, amma muyi haƙurin asubanci, dan yanzu dare yafara, tafiya da waɗannan makudan kuɗin haɗarine Abban kalifa". Shiru Abba yay yana nazarin maganarta, zuwa can yace, "To babu damuwa, yanzu dai ki haɗa mana dukkan abinda yadace, a yanzu mu lodasu a mota, ko yara karki sanar musu komai". "Hakan yayi amma kuma matsala ɗaya, idan Yahya yakira mana ƴan sandafa?". "Kwantar da hankalinki, saida na tabbatar yabar wayarsa a mota sanan". Daɗi ya kama hajia hindu ta rungume abba cikeda ɗoki.

Duk bugun ƙofar da Uncle yahya keyi basu buɗeshiba, harma yagaji ya bari, hankalinsa yayi matuƙar tashi dajin bayanin da Abba yazo yamasa a bakin ƙofa. Idanunsa na zirar da hawaye yace, "Yaya karka aikata haka, Jiddah fa ɗiyarkace data fito daga jinin jikinka, miyasa zaka aminta da cigaba da zalintarsu suda mahaifiyarsu, kana ganin adalcine gudun da zakayi ka barmu saboda dukiya? Baka tsoron ita wadda zaka gudun da ita taci amanarka?, wlhy nasan jiddah zata iya barmaka kuɗinnan, amma sh........" Cikin daka tsawa Abba yace, "Ya isheka haka munafiki, babu abinda ya isa dakatar dani wlhy". "shikenan naji yaya, Amma makomar auren maman Nafisa fa?". "Aurenmu na nan munafiki babu mai rabashi, bazan taɓa yadda bakin inna ya biniba, tunda tace idan na saketa ALLAH ya isa ko bayan ranta to bazan saketanba balle kaje ka aureta, dan nasan burinka kenan a kulum, saidai ta mutu da aurena wlhy". "Yaya karkayi haka dan ALLAH, wanan zaluncine wlhy, ka tausayama baiwar ALLAH nan koda a wanan gaɓarne". Tsaki Abba yay yabar masa bakin ƙofar.

Sosai hankalin Uncle Yahya yakuma tashi, haka yahaƙura ya zauna yana ƙulla abinda zai fisheshi, gashi wayarsa na a mota ya bari.

Cikin dare saiga ɓarayi sunyi dirar mikiya a gidan Abba, tun Uncle yahya najin hayaniya sama-sama harya fara jiyo magiyar da Abba kema ɓarayi da roƙonsu. Zuwa can kuma yajiyo suna dukan Abba yana kukan ihu, sai ihun hajia himdu da yara dayake jiyowa suma, gabannin asubahi saiyaji tsitt alamun ƴan fashin sun tafi, sai koke-koken yaran da hajia hindu.

Hindun yashiga ƙwalama kira yana buga ƙofar, kalifa yaje ya buɗe Uncle yahya. Uncle yahya na fitowa yaci karo da Abba a yashe tamkar gawa, kallo ɗaya zakai masa kasan amatuƙar jigace yake da duka. Kansa kawai Uncle yahya yayi yana kuka, itama Hajia Hindu da alama an daketa a ƙafa, dan zaune kawai take gaban Abba tana hawaye. Ganin Abba ko motsi bayayi yasaka Uncle yahya barinsa yatashi ya fita neman motar kaisu asibiti....

★★★★★★★

Taimakon gaggawa aka shiga bama Abba, da ita kanta hajia hindu da aka jima ciwo a ƙafar haggu. Hankalin Uncle yahya bai kwantaba saida akace masa Abba ya farfaɗo, amma anmasa Allurar barci. Itama hajia Hindu barci takeyi. A lokacinne yasamu nutsuwar ɗaukar su Hassan yakai gidan Umma. Duk da Uncle yahya bai sanar musu tushen matsalarba, Hankalinta yatashi daga ita harsu Zarah dajin abinda ya faru, kuka sukeyi sosai abin tausayi. Umma da Uncle yahya ne kawai suka koma asibitin, akabar su kalifa anan gida taredasu Walida. Batun tashin hankalidai ba'a maganarsa ga wanan family yau, dolene kagansu su baka matuƙar tausayi, ƴan adamawa ma duk an sanar dasu, hakama Aunty Zulai dake huntuwa. Aunty Nafisace ma hartazo asibitin, Jiddah ce kawai Uncle yahya yaƙi sanar mata. A ranar a asibitin Uncle yahya da Umma suka kwana wajensu Abba. Su Kalifa kuwa acan wajensu zarah, sukaita zubama su Zarah rashin kunya akan bazasuci garau-garau da Walida ta dafa ba, wai sai dai aimusu miya, su Mom bata basu abinci da mai da yaji. Daga Walida har Zarah watsar dasu sukayi suka cigaba da hidimarsu, idan yunwar ta rarakesu ai saci. Ilai kuwa zuwa dare da sukaga babu mafita sai suka ɗauka sukacin.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Washe gari su aunty Hannatu dawasu a cikin dangi suka iso, Abba dai ya farko, sai dai ko magana baya iyayi saboda kumbura da fuskarsa tayi dam, tsakaninsa da mutane sai dai ido, ga karaya har biyu a ƙafarsa da ƙugunsa saboda duka sukai masa na fitar hankali. Itama hajia hindu ta farko, kuma ita da sauƙi sosai, dan nata gocewar ƙashine. Duk wanda yaga Umma da Uncle yahya a wanan lokacin saisun baka tausayi, dan dukkan lokacinsu yanakan Jinyar Abba da hajia hindu ne, hakama hidimar asibitinsu sai da kuɗinsa akeyi. Zuwa dare su Aunty Sauda suka ƙarasa gida dansu huta. Dukda ba abin daɗi bane ya kawosu, kuma basu daɗe da tafiyaba daga bikin Jiddah hakan bai hanasu Zarah murnar zuwansuba. Su kalifa kam sai suka hau kumbure-kumburen baki wai basason wanan gidan hayaniya tayi yawa da ƙauyawa. Hakanne ya fusata Aunty Nafisa ta zubama kalifa mari har biyu ƙwarara, aiko ya zauna yana zaginta, Aunty Zulai tasa wayar caja ta zaneshi sosai, dama haushin yaran sukeji to🤣 Wanan duka da akaima kalifa yasaka su Hassan nutsuwa waje ɗaya suka haɗiye tasu rashin kunyar, shi dama Munner bashida matsala, kasancewarsa ƙarami baikai sauran wayoba. Zarah ce ta sanar musu Jiddah fa bata san halin da ake cikiba, Uncle yahya ya hana a sanar mata. Numfashi Aunty Sauda ta sauke tana faɗin, "Nidai a ganina yakamata ta sani, dan gaskiya Abba yanajin jiki, mubama Uncle shawarar ya sanarma koda mijintane koya kukace?". "Wanan shawarar taki tayi aunty Saudah wlhy". Cewar aunty Nafisa dake bama yaron aunty hannatu akamu. Sun yanke shawarar masa magana da safe idan sunje asibiti.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Yau Jiddah cikin ɗoki take Aliyu zai koma wajen Maimunatu. Dan kwanakinta goma sun cika harda kwana shidan da maimuna ta ƙara musu. Dukda ba takurata yakeba itadai sotake ya koma can. Su kaɗaima sukai hirar dare yau, danshi tunda safe yay tafiya shida malam dawasu malaman yin wa'azi jihar katsina. Har sukai sallama Jiddah tatafi sashenta bai shigoba. Saida tagama shirin barci tana ƙoƙarin kwanciya taji bugun ƙofa da sassanyar muryarsa yana kiran sunanta. Hijjab ta saka tazo ta buɗe masa ƙofar falon. Taɗanyi mamakin ganinsa da jallabiya, kenanma harya dawo yay wanka, haka kawai saitaji wani iri a zuciyarta, ya dawo amma ba'a sanar mataba balle tafito masa sannu da zuw....... Numfashi ta sauke saboda jinta a jikinsa, cikin kunnenta ya raɗa mata "Yadai Jiddatulkhair? Ko bakiyi kewata baneba?". "Humm nayi mana". "Shine kikaƙi zuwa tarbata?". Shiru tai bata bashi amsaba, hakan yasakashi ɗago kanta yana kallon fuskarta data canja alamar damuwa. "Mike faruwa? Naga kamar ranki a ɓace". "Babu komai" tai maganar tanason janye jikinta daga nasa. Rikota yayi daƙyau, yajata zuwa saman kujera, saida ya zauna sanan ya ɗorata a cinyarsa. "Mike faruwa? Faɗamin kinji Habibty". "Nifa nace babu komai". "Uhm-uhm ban yardaba wlhy Jiddah, karkiga ban daɗe da saninkiba kiyi tunanin ban fara fahimtar halayyarkiba, wani abun akai miki". "Ba aimin komaibafa ni, Amma shine ka dawo bamsaniba har saida ka daɗe, bayan tun ɗazun muna dakon zaman jiran dawowarka tare da auntyn". Murmushine ya ƙwace masa babu shiri, wato duk yanda mace take baka rabata da kishi, wanan jinin jikinsune, rungumeta yay sosai yana faɗin "To amin Afuwa amarsu, nayi tunanin kar in takurakine, dan kina baro sashen auntynki babu daɗewa ina shigowa". Yinƙurawa tai zata tashi yay saurin maidota a cinyarsan, zatayi magana ya ɗora bakinsa kan nata.....🙊

Ajiyar zuciya taita saki bayan ya saketa, uffan bata iya cemasaba har ya kawota ɗaki ya kwantar, saida yay mata addu'a ya tofeta sanan yashiga mata tausa a hankali. Luf tayi tamkar tayi barci, hakanne yasaka Aliyu barinta, ya kashe mata fitila sanan ya fita tareda ja mata ƙofar. Yana fita hawayen da batasan dalilinsuba suka ziraro mata, itadai tasan tayi murna dazaije can ya kwana, dan itadai takura takeyi da kwanciyarsu a gado ɗaya, amma batasan dalilin dayasa wani sashen zuciyarta yakejin ɗaciba, komi hakan yake nufi oho?. Ta daɗe batayi barciba tanata juye-juye, sai can tsakkiyar dare barci ɓarawo yay awon gaba da ita.

★★★★★★★

Da asuba lokacin daya leƙo tashinta salla harta tashi, tana zaune a bakin gado tana addu'ar tashi daga barci ya shigo. Kallo ɗaya taimasa tai ƙasa da idonta tana gyara wuyan rigarta take a buɗe sosai. baice da ita komaiba ya juya ya fita, ta ɗanbi bayansa da kallo harya ɓacema ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke tamiƙe zuwa bayi ɗauro alwala............✍🏻

_Masoyan Abba zakari Amin afuwa fa, babu ruwana Alƙaline🙊⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀🤣_.

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [12/29/2019, 1:44 PM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*

*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*

*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_[57➖58]_*

.............Ciwon dake ƙafarta ba shine matsalarta ba, hankalinta naga kuɗin hannun ƙaninta, gashi bataga alamun wayarta na tare da itabama........ Umma ta katse mata tunani da faɗin, "Maman Hussain ki daure kici abincin nan, ciwo bayason zama da yuwafa". Hajia hindu ta ɗan sauke numfashi, ta ƙasan ido ta harari Umma kafin ta yatsine fuska, "Zanci Maman Nafisa, abincinne gaba ɗaya bayamin daɗima ni wlhy". Umma taɗan murmusa, saboda tasan baƙa hajia hindu ta faɗa mata. Abba ma na jinsu, sai dai babu bakin magana, a zuciyarsa kam babu abinda yake jinjinawa sai ƙyaƙyƙyawar zuciyar Umma, wai ita wace irin mutumce mai maida sharri da alkairi?. Bashida mai bashi wannan amsar, sai hawayen da suka gangaro masa ta gefen ido wanda su Umma basu gsniba. Shi kansa baisan dalilin zubarsuba, zafin ciwone? tausayin kansane? Kokuwa nadamace?, shidai yasan har yanzu baiji a ransa ya aikata badaidaiba gasu Umma, yanzu da ace ƴaƴansane maza sukazo a manya da ƙasar waje za'a kaisama jiyyarnan.........

Shigowar Uncle yahya ce ta katse tunanin Abba, tare yake da mijin Aunty Nafisa, saisu Aunty Zulai dake a bayansa suduka harsu kalifa. Da gudu su Hassan suka nufi uwarsu, Maneer ne kawai yaje wajen Abba yana faɗin "Abbanmu bakada lafiya? Miya sameka?". Ummace ta janye Muneer ganin zai fara kuka, Abba ya janye idonsa daga Muneer da Umma ya maida kansu Kalifa da ko sau ɗaya basu kalli inda yakeba, sun zagaye uwarsu suna faɗa mata ƙarya da gaskiya da akai musu a gidan Umma. Tuni ita kuwa launin fuskarta yagama canjawa... Tsawa Uncle yahya ya dakamusu, kafin ya zubamusu daƙƙuwa da faɗin, "Kunci gidanku, toku su wanene da idan kukai laifi baza'a hukuntakuba?, waɗannan ba yayyenku baneba?, ko Walida ce ta tsawatar muku ba dole kujiba balle Zulaiha da Nafisa, duk wanda na ƙarajin bakinsa saina zanesa a asibitinnan, gida kam ai dole kuzauna tunda bakuda kamarsa yanzu. Kekuma maman kalifa kin zauna saurarensu bazaki ko tsawatar musuba". Cikin Kumbura fusaka tace, "Yo yahya minene abin tsawatarwa anan?, daba a cuta musuba zasu faɗane". Tsit gurin yay duk suna kallonta, Abba ne kawai yaji daɗin abinda tayi a ransa, danshima yaji haushin an dokar masa ƴan lelensa, saidai babu bakin magana. Daganan babu wanda yakuma tofa baki acikin lamarin su kalifa, anan suka yini a asibitin har yamma liƙis sanan Uncle yahya yace su koma gida. Hajia hindu naji na gani Uncle yahya ya kora su kalifa daketa ƙunƙunai su bazasu komaba, wai tuwo da koko da shinkafa kawai akeci a gidan, sukuma basu iya ciba (hhhhh ƴaƴan turawa😹). Ko kallonsu Uncle yahya baiyiba, danshi dariyama suke bashi wlhy. Su Aunty Saudah suka tuntuɓi Uncle yahya akan batun faɗama Jiddah, murmushi yayi, "Karku damu zata sani, amma sonike sai zuwa kamar jibi haka, duka yaushe taje gidan mijin da za'a sakata fitowa?, sonake sai zuwa jibi ta cika sati biyu insha ALLAH, suma zuwa sanan sun fara samun sauƙi, kunsan Jiddah da ruɗiya, kuma zuwanta bashine zai basu lafiyaba ai". Sun amsa da to, tareda gamsuwa da maganarsa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*_Bayan kwana biyu_*

Har zuwa yau Jiddah batasan mike faruwaba, kuma tana waya da Umma da Uncle yahya, hakama aunty Nafisa, babu kuma wanda ya faɗa mata. Yauma dai haka ta yini ita kaɗai a sashenta, saboda zuwan da Amina da Hassana sukayi gidan, sanda sukazo tana sashen Maimuna suna kallon wani tafseer ɗin Sheikh Aliy, amma tundaga shigowarsu jikinta yay sanyi, dan wani kallon banza sukaita binta dashi, koda ta gaidasu babu wanda ya amsa saida Maimuna tace Auntys jiddah nafa gaisheku. Duk a yatsine sukace "oh ALLAH sarki, bamuji bane". Jiddah bata gazaba takuma maimaita musu gaisuwa, lokacin ita Maimunatu taje kicin kawo musu ruwa, tsaki sukayi mata basu amsaba, hakanne ya sakata miƙewa tabaro sashen ta dawo nata jikinta sanyi ƙalau da tunanin sukuma su wanene? Tagadai ɗaya na bala'in kama da Maimunatu (Hassana). Koda ta dawo sashenta sai abin yakuma ƙuntata zuciyarta, tana cikin tunani a falo saigasu sun shigo Maimuna ta rakosu wai zasuga ɗaki, dan ita maimuna batasan abinda suka kuma yima Jiddah ba. Jiddah ta saki fuska takuma tarbarsu da mutuntawa a nan ma, babu inda basu shigaba, amma sai wani yatsine fuska suke, komai suka gani sai Amina tace, "Aunty Hassana nikam ba wanan abun bane ranar muka taya a wajen ƴan gwangwan ɗincan dubu uku?". "Shinefa ƴar uwa, kinma manta dubu biyu suka barmana daga baya". "Hakanefa wlhy, nama manta". Gadajen Jiddah ma da kujerunta haka sukaita musu iskanci, wai Hassana taje kasuwa akace za'ai mata a dubu arba'in, amma tace basuyi mataba tawuce nan. Ran Maimunatu ya ɓaci sosai, dan haka taja hannun aunty hassana suka fice, amma saita fisge tana mata masifa. Acan kuma Amina nata gaggasama Jiddah magana ta rashin mutunci, itadai jiddah batace mata komaiba, saima kanta data duƙar a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, har Amina tayi tagama ta fice sanan ta ɗago tana kallon ƙofa hawaye na ziraro mata, ta daɗe a falon tana kuka kafin ta koma bedroom ta kwanta, ganin zata ƙuntata kanta da yawa ta kunna karatun Al-Qur'ani tana saurara, a haka barci ya kwasheta. Sai da Maimuna tazo kawo mata ɗanwake da tamusu na ranane ta tadata dan har anyi salla ma. Sannu tamata da godiya, Maimuna tafita saboda su Amina basu tafiba, da zama ta kawo mata abincinan da hanawa sukayi sunata mata masifa, sai da tace wlhy zata kira Malam ta sanar masa kafin shima Aliyu ya dawo ta faɗa masa, sannan ne suka bata hanya suna zaginta wai baiwar kishiya. Itadai batabi takansuba ta fito kawoma Jiddah abincin.

Har yamma lis su Hassana suna gidan, sai bayan la'asar ne suka tafi, jiddah najin tafiyarsu saboda dariyar da sukeyi suna sakin magana a kanta, amma sai taƙi fita, dan duk zuciya nason mai ƙyautata mata. Maimuna sashenta ta koma, duk zuciyarta babu daɗi itama, dolene tasaka a takama su Aunty Amina birki akan zuwa gidan, dan itadai baza'azo a haɗa mata fitina a gidan aurenta ba, suna zaune lafiya a ɓata musu zama, badan Jiddar tanada hankaliba da biyema su Aunty Hassana zatayi sosai, dan ba kowa zai yarda da wannan cin kashinba, jitai Jiddah takuma birgeta, sai dai yanzu tsoronta karta faɗama Aliyu abinda ya faru ne.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull