Mutum da duniyarsa complete - Chapter 28
Mutum da duniyarsa complete Chapter 28: Mutum da duniyarsa complete Chapter 28. Alhmdllh jikin Abba yaɗanyi sauƙi, dan kuwa kumburin fuskarsa ya sauka, sai…
2,686 words
Alhmdllh jikin Abba yaɗanyi sauƙi, dan kuwa kumburin fuskarsa ya sauka, sai daifa yanashan azamar ƙafa da ƙugu, wanima tashin hankali shine ɗorin karayar ƙugunsa bata ɗoruba, likitoci sukace sai an sake, ankumayi yau da safe yaci azaba iya iyawa amma ba'a daceba, shine Uncle yahya ya yanke shawarar kiran wani na gargajiya, dan haka yaroƙi likitan akan su sallami Abba za'a canja masa asibiti, sunyi hakanne dan sunsan idan sukace na gargajiya za'a likitocin bazasu yardaba, shikuma tsoro yake kar goma ta lalace biyar bata gyaruba. Sosai hajia hindu tayi murna da wanan sallama, dan itafa ba damuwarta Abba ba, hankalinta nakan kuɗin data saka ƙaninta yazo yay musu fashi. Kamar yanda Umma da Uncle yahya suka yanke shawara haka akayi, kai tsaye gidansu Umma aka wuce dasu Abba, ɗakin dake soro Uncle yahya yasaka aka hudo ƙofa ta cikin gida tun jiya, ita kuma hajia hindu aka kwashe kayansu Zarah daga ɗakinsu aka gyara mata. Su aunty sauda duk basuso hakaba, dan yanzu dai ba gidan Abba baneba na Jiddah ne, saida Umma taita tausarsu sannan suka bar zancen. Sosai hankalin hajia hindu ya tashi, wai ana nufin wanan gidan data bari tsawon shekara sha shida dawasu watannine za'ace ta dawo da zama?, wanan ai ci bayane, dolene ta nemo ƙaninta a yau yakawo kuɗin nan tanemi ƙaramin gida tasai musu itada ƴaƴanta, shiko Abba yazauna nan yayi jiyya, idan ya warke ya nemesu. Abba kam yana cikin azabar ciwo, bayama tantance a ina yake balle asan sirrin ransa Gidan dai yamusu kaɗan sosai, amma haka sukai maleji, da daddare wasu sukaje gidan Uncle yahya suka kwana. Su kalifa kam abufa ya damesu, sai kuka sukema hajia hindu basa son wanan gidan, sudai akoma gidansu. Hajia hindu saita sake rikicewa, dan ita kaɗai yaran suke addaba, basayi gaban su Uncle yahya. Washe gari da safe mai gyara yazo, sabon ɗori ya sakema Abba a ƙugu, suma kam Abba yayita babu adadi, su Zarah kuka kawai sukeyi, hakama Umma takasa daurewa, sosai takejin tausayin Uban ƴaƴan nata dukda tsiyatakun daya shuka mata. An gama gyaran Abba ya samu barci na wahala, a lokacinne hindu tasamu zarafin tambayar Uncle yahya wayarta wai zata sanarma danginta. "Wayoyinku suna cikin wata jakarki na zuba, tana nan inaga an taho da ita, amma ina Zulaiha itace kamar nabama jakar dazamu taho?". aunty Zulai dake sharo ɗakin Umma tace, "Eh Uncle tana nan ɗakinta a jar jaka". "yauwa to kinji tana nan, sauran kayanku suna gidan malam Alfah na roƙi alfarma aka kai can, saboda mu gidajen namu babu inda za'a iya lode waɗan nan kayan, kayan gado dai dasu kujeru duk an saidasu harma katufun, guda ukunan dakika gani kaɗai muka bari, acikin kuɗinne ma akabama mai gyaranan kuɗinsa, dan wlhy nidai kuɗin dake wajena sun ƙare, a jiyama saida na taɓa kuɗin sadakin jiddah dubu ashirin aka ɗako sauran kayanku, amma an maida mata yanzu haka, wanan daliline yasa muka matsa aka sallamoku daga asibiti, tunda bamuda kuɗin cigaba da biyan kuɗin gado da sauransu, yarannan kuma su Hannatu iya ƙoƙari sunyi dagasu har mazajensu, koma nace suna cikinyi". A ɗage hajia hindu ta amsa da "Uhhum". Dan taji haushin saida musu kayan gado kuwa, amma babu komai aiga kuɗinan. Babu wanda yasakebi ta kanta, saboda amsar da tabama Uncle yahya ta Uhum kowa tabashi takaici.
Shidai Uncle yahya yay musu sallama yatafi gida danya ɗan huta kafin Abba ya farka.
***********
Da rana akayi faten doya da wake da alayahu, ƙiri-ƙiri su Hussain sukace bazasu ciba, babu wanda ya tanka musu sai Umma daketa musu nasiha da lallashinsu, amma ƙiri da muzu sukaƙi saurarenta, saima rashin kunya da suka nemi yimata, aiko Aunty Hannatu dukda haƙurinta tai azamar taka musu birki. Hakan saiya harzuƙa hajia hindu tafara sakin magana, gashi tana ƙyaɓe waje ɗaya tana fama da kanta. Aunty Zulai zatai magana Umma ta hana, takumace kar wanda ya sake tankawa, daga yanzuma komi su Halifa zasuyi a gidan babu ruwansu, abinci dai idan andafa a basu, suci ko karsuci wanan yarage nasu ai. Hajia hindu dai tanata neman ƙananun magana babu wanda ya kulata, ga takaicin neman kaninta da take a waya amma taƙi shiga, tamasa kira yafi hamsin sai dai ace mata Busy, tun tana ɗaukar abin wasa har nutsuwa ta fara gagararta.
Hummm hajia Hindatu yaya dai⛹♀😹?.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah na zaune a falo bayan tayi sallar la'asar tana duba littafin *Ahdhari* Aliyu ya shigo da sallama, ɗago idonta da sukai alamun tayi kuka tayi ta kallesa tana amsawa, ya tsaya a ƙofa tareda buɗe mata hannayensa alamar tazo gareshi. Murmushi tayi tamiƙe jiki a sanyaye, dan yariga ya shaida mata hakan dokane acikin tsarinsa, kuma koba komai tana buƙatar jin ɗuminsa a halin yanzun da zuciyarta ta wuni a ƙuntacennan. Shigewa tayi ajikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya. shima numfashi ya sauke, yace, "Nayi kewarki Jiddah na". Ahankali ta furta "Nayi kewarka sosai nima". Babu shiri yay azamar ɗago kanta, dan maganarta tabashi matuƙar mamaki, baiyi zaton hakan agareta ba nan kusa. Lumshe idanunta tayi tana murmushi, dan batason su haɗa ido. "Jiddatulkhair da gaske koda wasa?". Fuska taɗan shagwaɓe tana tura masa baki, "Da gaske mana". Ta kare maganar da maida kanta a kirjinsa. "Masha ALLAH, Alhmdllh Adaratul ainy (Turaren zuciyata) ya kuma rungumeta yanajin sonta nakuma tasiri a ransa". Bayan sun zauna taje ta kawo masa ruwa. Yana sha idonsa a kanta, dan ya kula tana tare da damuwa kamar yanda maimuna ta sanar masa, saboda sashenta yafara zuwa, itama ya isketa cikin damuwa, ya tsareta da tambaya shine ta sanar masa abinda su Hassana sukazo sukayi, ransa ya ɓaci sosai. Amma sanin halin Maimuna bazata taɓa sakasu suma Jiddah hakanba sai itama ya lallasheta akan karta damu, shi yasan bazata sakasu suyiba hakanba ga jiddah, sunyine kawai dan raɗin kansu, amma zai taka musu birki insha ALLAH. hakan sai ya saka zuciyar Maimuna ɗan samun nutsuwa, amma damuwarta kuma halin da jiddah take a ciki. Aliyu ya ɗauki aniyar gwada Jiddah yagani kozata masa maganar abinda su Aminar sukazo sukayi. "Ƴammatana mike faruwa? Na ganki wani sukuku, ga idonkifa kamar kinyi kuka"...... Murmushi jiddah tayi tana danne abinda ya tokare ranta, "Babu komai, kumani ba kuka nayiba, kawai kewar Ummana nakeyi". Idanu ya tsura mata zuciyarsa na tunanin ita takeson sanarma kenan? To amma dataso hakan ai da tayi tunda ga waya a hannunta, saurin kauda wanan tunanin yayima daga ransa, ya ajiye kofin da yasha ruwan yakamo hannunta cikin nasa idonsa akan fuskarta, "Haba tawan, anya kuwa kewar su Ummace kawai? Kodai Auntynki ce?". "lah A'a wlhy, ni aunty tsakanina da ita sai sambarka, kawai dai kewar su Ummance". "Shikenan, insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zan kaiki, yanzuma tashi ki shirya danayi wanka zamuje mu gaida su malam, kinga baki taɓa zuwa gidanba tunda kikazo. Daɗine sosai ya kama jiddah, harga ALLAH tana ƙaunar dattakon tsohon, tuni taji nauyin da zuciyarta yayi kaso mafi yawa ya ragu. tace, "To abincifa?" "Naci abinci a office din mustafa, shiyyasa na kira auntynki nace karkuyi dani". Murmushi tayi, dukda batasan anyi hakanba, kuma girkin Maimuna ne har rana, sai yanzu da yammarnan ita zata karbesa, batareda tace komaiba ta mike, harta nufi ƙofar fita Aliyu ya kirata, juyowa tayi ta kallesa, yace, "Ina zakije kuma?". "Zan haɗa maka ruwan wankane". "Karki damu zoki haɗamin a bayinki kawai". Kanta ta jinjina masa ta dawo da baya zuwa bedroom nata. Binta yayi da kallo harta shige, ya ɗan sauke numfashi yana jingina kansa da kujera, a zuciyarsa yana tunanin miyasa taƙi faɗa masa abinda akai matan? Zai sake gwadata dai ya gani, harga ALLAH yana mamakin yanda wasu lokutan halayyar Jiddah da Maimuna suke kamanceceniya da juna, kodan dukansu sunada ilimin addinine da tarbiyya, kuma Alhmdllh suna aiki da sanin da ALLAH yay musu, sarai yasan salon kishin kowacce amma hakan bai hanasu ƙyautata zamantakewar dake tsakaninsuba.......... Jiddah ta katse masa tinani, idanunsa ya buɗe, ya kama hannunta yana faɗin "Zomuje ki tayani wankan to". Sosai ta zaro idanu da faɗin "Wankafa?". Tabashi dariya data zaro idon, ya ranƙwafo kanta yana jan hancinta, "Malama baƙyason koyi da sunnar MANZON ALLAH ne? ANNABI yana wanka da Matansa har hannayensu na gogayya a cikin ruwa, baƙyason samun wanan ƙatotuwar ladar tawajena". Hannu ta saka ta rufe fuskarta tana ƙaramar dariya, shima yay dariyar yana jan hannunta sukai ciki....
✨✨✨✨✨✨✨
Gabda magriba suka fito da nufin barin gidan, dan Aliyu soyake yay sallah a masallacin ƙofar gidansu, Kasancewar Jiddah ce da girki maimuna tace ya shiga gaba, amma sai taƙi tace, "A'a wlhy Aunty ke zaki shiga, ba girki zaki dubaba, kimarki ta matsayin babba a gareni". Daga Maimunatu har Aliyu binta sukai da kallo harta shige baya, sanan suka kalli juna sukai murmushi, kowannensu yanajin ƙaunarta da kimarta a ransa, yayinda itama hakanne daga gareta. Sun isa anata hada-hadar shiga sallar magriba, Jiddah da Maimuna suka shige cikin gidan, shikuma Aliyu yashiga masallaci..........✍🏻
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [12/30/2019, 1:58 PM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[59➖60]_*
............Duk da agidan Maimunatu ta girma, kuma akwai mariƙiyarta Iya Habi, hakan baisakata kaisu canba itada Jiddah, saita nufi ɗakin hajia bah-bah uwargidan Malam. Sosai Hajia bah-bah taimusu tarbar mutunci, hakama Na'ima tafito fuskarta ajiƙe da alamar alwala tayo tana musu oyoyo. Harara Maimuna ta zuba mata tana faɗin "Anƙi a amsa ɗin, aini yarinya mun ɓata". "Haba-haba Uwar ukunmu, yi haƙuri, nasan nayi laifi amma wlhy tafiya nayi tun bayan bikin yaya Ali, kuma tambaya bah-bah kiji. Aunty Amarya sannu dazuwa kinji". Murmushi Jiddah tayi tana amsawa. Hajia bah-bah ta katse musu jancen da faɗin, "Da wannam surutun da kika tsaresu dashi da alwala kika kaisu sukayi ga Aliyu can zai tada salla". "To bah-bah. Kunga kumuje to". Ɗakin Na'ima suka koma, domin yin sallar acan.
Bayan an idar da sallah Aliyu na gaisuwa da mutane wayarsa tayi ring, cirota yay daga aljihu ya duba, ganin Uncle yahya saiya faɗaɗa murmushinsa, bai ɗagaba saida ta tsinke sannan shi ya kirashi da kansa. Daga can shima Uncle yahya murmushin yayi ya ɗaga, cikin girmama juna suka gaisa, Uncle yahya yama Aliyu bayanin halin da Abba ke ciki kusan kwana uku. Sosai hankalin Aliyu ya tashi, yace, "Uncle aida an sanar mana, babu wata damuwa, ko yau aka kaita washe gari hakan ta faru ai dolene tafito, kuma koni aida nazo dubashi. Insha ALLAH gamunan zuwa bayan isha'i". "ALLAH ya kawoku, nagode a gaida min malam". "Zaiji insha ALLAH". Sosai lamarin ya zauna a zuciyar Aliyu, duk zuciyarsa taimasa babu daɗi, tausayin Abba sosai ya ɗarsu a ransa. Matsawa yay kusada malam dake zaune yana duba alƙur'ani ya sanar masa da abinda ke faruwa. "Ya Salam, ALLAH yabashi lafiya, yasa kaffarane a gareshi, insha ALLAH zanje na dubashi nima". "Amin baba, to ALLAH ya bada iko, suma tare muke dasu sunzo gaisheku, daga nan zamu wuce mu dubashi insha ALLAH". "To masha ALLAH, hakanma yayi". Bayan an idar da salla malam yasaka Abba a cikin doguwar addu'a, wadda ta saka Aliyu jin daɗi sosai.
A cikin gida kuwa su Jiddah suna idar da salla sukazo suka gaida hajia bah-bah, cikin fara'a ta amsa musu tareda sanya musu albarka. Sanan tace suje su gaida su Gwaggo. Sun fara zuwa sashen gwaggo amarya, itama ta tarbesu da fara'a, basu baro sashenba saida za'a kabbara sallar isha'i, sashen iya habi suka shiga, itama ta tarbesu da barkwancinta, tareda jin daɗin ganin Maimunatu ta bata cikin damuwa, saitaji Jiddah ta kwanta mata arai, nanma sunɗan jima dan saida sukai sallar isha'i, suka koma sashen Hajia bah-bah saboda kiransu da Na'ima tayi suzo suci tuwo.
Lokacin da Aliyu ya shigo gidan ya iskesu sunacin tuwo a falon hajia bah-bah. Bayan sun gaisa da bah-bah Na'ima ma ta gaisheshi, bisa kuskure Jiddah ta ɗago kai suka haɗa ido, gira yaɗan ɗaga mata yana nuna mata tuwon da ido. Murmushi ta masa haɗe da ƙaramin gwalo, ya murmusa shima yana miƙewa domin zuwa gaida sauran matan gidan. "Aliyu ka zauna a kawo maka tuwo". "A'a Bah-bah, Alhmdllh, kinsan ni ba cin abincin darenma nakeba kwata-kwata". Cikin hangame baki tace, "Wai wanan halin naka har yanzu baka barshiba Ali? Randa baka yini agidaba shikenan bazakaci abincin iyalinka ba?". "Bah-bah ai inacin na safe, rashin cin abinci dare abune mai ƙyau, yana ƙara lafiya inhar mutum zai iya jurewa". "A'a wlhy badaniba kam, yoni idan banci tuwo da darebama jinake tamkar banida lafiya a gidan nan". Dariya su Jiddah saukayi kaɗan, kujifa hajia bah-bah da wani batu, saikace wadda batayi salla ba. Shidai Aliyu fita yay yana mata dariya. Bai daɗe sosai ba ya dawo yana faɗin, "Kumuje ku gaida malam akwai inda zamuje insha ALLAH". Maimuna da Jiddah suka miƙe, dan dama sungama cin abincin, harma sun wanko hannunsu da baki. Sallama sukaima Hajia bah-bah, suka koma ɗakunan su gwaggo suma sukai musu sallama, harda ƴar tsarabarsu ta kuka da ɗanyen kuɓewa da daddawa suka samo. Saida sukai sallama a ƙofar falo aka basu izinin shiga sanan suka shiga, sun iske malam da Aliyu zaune suna magana, idan ka gansu dolene su baka sha'awa, harsun tsuguna daga farkon falon malam yace, "A'a ƴaƴana ku shigo mana ciki". Duk a kunyace suka koma gabansu sosai, kansu a ƙasa suka gaidashi, ya amsa musu cikin fara'a tareda tambayarsu gidan da rayuwar yau da kullum, sanan ya ɗora da nasiha a garesu su duka ukun mai ratsa jiki, yakuma sanya musu albarka tareda fatan alkairi a zamansu. Suko kansu na ƙasa sunata amsawa da amin, yayinda ƙaunar tsohon da girmansa na ƙara yalwatuwa a ransu. Baija zancen yayi tsawoba yace, "Aliy tashi kuje dare nayi, dan ALLAH ka gaidamin shi, ga wanan kabashi kafin nazo". Tashi Maimuna da Jiddah sukayi suka fita, dukda basu fahimci zancenba sunga yadace su basu waje ko akwai abinda zasu tattauna. Bayan fitarsu Aliyu yace, "Zaiji insha ALLAH baba, amma kabar kuɗinka zan bashi injika insha ALLAH". "A'a karɓi wanan ai tsakanina dashine, kuma nima ina buƙatar ladan sarkin wayo" yaƙare maganar da tsokana. Murmushi Aliyu yayi ya karɓi kuɗin, sanan sukai sallama da malam ya fito. Ya iske harsu Maimuna sun shiga mota, sai Na'ima dake tsaye ajikin motar suna magana. Cikin samarin dake gefe ɗaya yazo ya buɗe masa motar da addu'ar sauka lafiya, dama sunzo suka gaida su Jiddah cikin mutuntawa. Koda suka tafi a hanya bai musu bayanin inda zasujeba. Ita kuma Jiddah gaba ɗaya hankalinta ma bakan hanya yakeba, game kawai take a waya tana sauraren hirarsu jefi-jefi suma, saida har suka shigo cikin anguwar sosai ne Jiddah ta ɗago kanta donson ganin inama suka dosane?. Taɗan waro idanu da faɗin "Ai nan anguwarmune". Dariya Maimuna tayi ta juyo tana kallonta, "Wai da gaske dan ALLAH?". "Wlhy kuwa aunty". Aliyu na jinsu amma yaƙi tanka musu, a ƙofar gidansu Jiddah yay fakin sannan ya juyo yana kallon Jiddah. "Ku shiga, zan shigo daga baya nima". Jikin Jiddah kuma sai yayi sanyi, cikin langaɓar da kai tace, "Basai gobe idan ALLAH ya kaimu kaceminba?". Ganin Maimuna ta fita saiya shafa kumatun Jiddah, shima cikin kwantar da murya yace, "Haka naje, insha ALLAHU zan kawoki gobenma kinji". Haɗiye ƙwallan daya cika idonta tayi, ta sauke ajiyar zuciya sanan ta fita. Har suka shiga gidan idonsa na kansu, saida suka ɓacema ganinsa ne ya sauke ajiyar zuciya da ɗaukar waya domin kiran Uncle yahya.
✨✨✨✨✨✨.