Mutum da duniyarsa complete - Chapter 29
Mutum da duniyarsa complete Chapter 29: Mutum da duniyarsa complete Chapter 29. Su Umma duk suna tsakar gida zagaye da Abba da Uncle yahya ke bama Abinci.…
3,352 words
Su Umma duk suna tsakar gida zagaye da Abba da Uncle yahya ke bama Abinci. Hakanne yasaka Jiddah yin turus tana binsu da kallo, dama ƴan uwanta basu tafiba? Idonta ta sauke akan Abba dake kwance ɗaɗɗaure da karan ɗori, sai Hajia Hindu dake gefe zaune ƴaƴanta zagaye da ita itama. "Lah yaya Jiddah kece?" 'Cewar walida data fito daga ɗakin Abba ɗauke da kwanon magani'. Sauranma duk sai suka maido kallonsu ga ƙofar, Zarah tazo ta rungume Jiddah suka saki kuka tare, dan Jiddah ta fahimci gidansu babu lafiya. Aunty Hanantu data hangi Maimuna ce ta miƙe tana faɗin "Ashe tare kuke? Shigo mana Maimunatu". Gwiwar Maimuna a sanyaye itama ta shiga ciki, dan alamu dai sun nuna babu lafiya kam. Uncle yahya yayma Jiddah da Zarah magana sanan suka saki juna, Jiddah tazo gaban Abba ta durƙusa tana hawaye, "Abbanmu miya sameka?". Dukda haushinta da yakeji dan shi duk akanta yadora laifin, data zauna gidan Alhaji garba wanan bala'in da duk bai afka masaba, amma ya daure yace, "Wannan kukan ya isa haka ko?". Kasa tsayar da kukan Jiddah tayi, Maimunatu tazo gabansa itama ta durkusa ta gaidashi, da masa ya jiki?. Amsawa yay cikin alamun yanajin jiki matuƙa, itama Jiddah ta gaidashi, ana cikin haka Uncle yahya daya fita suka shigo da Aliyu, dama su Umma duk sun kimtsa, gashi a kwai wutar nepa. Tabarmar dake shinfiɗe a farkon shigowa wadda Jiddah taje ta zauna kusa da Abba Uncle yahya ya nunama Aliyu, kansa a ƙasa bai kalli kowaba ya zauna, Jiddah da gaba ɗaya hankalinta baya wajen saijinsa tayi kusa da ita, miƙewa tai tabar wajen, takoma inda Umma take tana sharar hawayenta. Aliyu ya gaida Abba yana faɗin, "لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ . La ba'asa tahoorun in sha'al-lah. (Ba komai, tsarkaka ce in ALLAH ya yarda). أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات) Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (7). (ina rokon ALLAH mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa). *_(MANZON ALLAH, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya")_*. _Falalar Da Ke cikin Ziyarar Mara Lafiya._ *_(ANNABI, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, yace; "Idan mutum ya ziyarci dan uwansa Musulmi (da ba shi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambunan aljanna yana tsinkar 'ya'yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta lullube shi. Idan da safe ne Mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya wayi gari)_*. Aliyu yaja doguwar addu'a ga Abba yana share kwallar da shima suka cika mada ido na tusayin Abban Su Aunty Sauda na amsawa da amin. Duk sun gaidashi da masa godiya, itama Umma ya gaidata tareda jajanta lamarin, Jiddah na jikinta tana hawaye, yayinda Umma keta shafa kan Jiddah alamar lallashi. Aliyu ya janye idonsa daga jiddah ya maida akalar gaisuwar ga Hajia Hindu data cika tai fam da haushi, itama yay mata addu'ar samun afuwa. Ta amsane kawai dan yayi mata mugun kwarjini, yanda takema mazajen su Aunty Nafisa yatsine-yatsine shi saita gaza masa, harshenta har sarƙewa yake wajen saurin amsa gaisuwarsa. Basu baro gidanba sai goma da rabi, shima saida Uncle yahya yace yakamata su tafi dare yayi, ƴan dubiya daketa shigowa ma sinɗan rage saboda dare ya farayi. Ƙiri-ƙiri Jiddah ta sanya kuka ita anan zata kwana, tun kowa na ɗaukar abin wasa har suka lura da gaske take, shikuma Aliyu baice uffanba yay musu sallama ya fice abinsa bayan ya ajiye kuɗin da malam yace aba Abba da wanda shima ya bashin, sai kayan marmari dasuka tsaya a hanya suka saya. Uncle yahya ne yayma Jiddah jan ido sanan ta miƙe su Zarah suka rakota inda Maimuna da Aliyu ke jiranta. Babu wanda ta kalla ta buɗe bayan motar tashiga tana cigaba da kukanta, Uncle yahya yabama Aliyu hannu sukayi musabaha da godiya shikuma Aliyu nama Abba addu'ar samun lafiya. Saida suka bar ƙofar gidan su Zarah da Uncle yahya suka koma cikin gida. A hanyama Jiddah kukanta takeyi, sai dai bamai sautiba, amma su Aliyu na jinta, Maimunatu ce kawai keta lallashinta da bata baki, amma sam Aliyu yaƙi tankawa, ita kuma shirunsa saiya kuma tunzurata takasa yin shiru kodan lallashin da Maimuna ke mata. Suna isa gida itace farkon fita tabarsu a mota, da kallo kawai Aliyu ya bita, Maimuna zatabi bayanta Aliyu ya dakatar da ita, "Kinga Maimoon barta kinji". Cikin langaɓe kai tace, "Haba yaya yazakace a barta, kukafa takeyi?". Fitowa yay daga motar shima, "Tunda nace kibarta kawai ki barta, kukan nata harda na hanata kwanane, indai banda rashin son gaskiya taya za'a ƙara musu nauyi bayan wanda suke ciki, idan tayi haƙuri da safe zata koma insha ALLAH". Shiru kawai Maimuna tayi, amma ita harga ALLAH bataga laifin Jiddah ba, ko itace sai taso kwana ɗin, to amma ita kanta shaidace akan wannan halin nasa, zata iya rantsewa tunda akai aurensu bai taɓa barinta taje gida ta kwana ba, yini ma yata ɓata rai kenan. Dan haka sai bataja maganarba ta wuce sashenta. Shima nasa ya nufa batare da yabi ko wannensu ba.
Tunda Jiddah ta shigo ko hijjab bata cireba ta kwanta a gado tana cigaba da kukanta, tausayin Abbansu da baƙincikin an hanata kwana cikin ƴan uwanta yake kuma tunzura kukan nata, ga haushin Aliyu, dan da ace yaso ta kwana ai zaice ta zauna, kuma babu wanda zai hana, rashin amincewar tasane ya saka Uncle yahya korota. Tana nan kwance harya shigo, dukda taji ƙamshinsa ko motsi batayiba. Kansa kawai ya ɗan girgiza, ya ajiye kofin shayinsa da Maimuna ta haɗo masa sannan ya zauna kusa da ita. "Hauwa'u!". 'Ya kirayi cikakken sunanta abinda bai cika yiba, saboda sunan mahaifiyarsa kenan'. Tsoro ya kama Jiddah, saboda jin yanda ya kirata a dake, tamkar ba shiba, hawayenta ta goge sanan ta amsa cikin rawar murya. "Tashi zaune ki cire wanan hijjabin". Bata musa masaba ta tashin, takuma cire hijjabinta amma taƙi kallonsa. Shima bai kalletan ba yace, "Tashi kiyi shirin barci". Tamkar munafuka haka ta tashi sum-sum zuwa bayi. Shikuma ya ɗau shayinsa yafara sha yanamai jin tausayinta da ahalinta, sosai lalurar Abba ta tsaya masa a zuciya, ita kuma tana neman ƙara masa zafi da ƙuruciyarta. Yana shan shayin ta fito, kayan barcinta ta ɗiba ta dawo ta bayansa ta saka, nanma baice mata ƙala ba, amma da lafiya-lafiya ne cazai shi zai saka mata. Tana gama shiryawa ta ɗaura zani tazo ta kabbara shafa'i da wutiri. Shidai Aliyu na zaune yana kallonta harta idar. Sai kumbura fuska takeyi tana cigaba da share hawayen dake zubo mata, hannu ya miƙa mata alamar tazo, da tayi nufin noƙewa, amma sai taga rashin dacewar hakan, tadai turo baki sanan ta matsa kusa da gadon. Hannunta ya kamo ya jawota zuwa jikinsa a hankali. Tana jinta kwance a ƙirjinsa saita kuma fashewa da sabon kuka. "Oh ALLAH, ya isa haka mana Jiddah, ko sokike nima namiki kukan ne?". Kanta ta girgiza masa alamar A'a. "To kiyi haƙuri kinji, insha ALLAH zai samu lafiya, Addu'a ya kamata muyi masa ai ko". "Amma shine kaƙi yin magana danace zan kwana?". Murmushi yayi yana shafa kanta, cikin kuma sanyaya murya yace, "To nayi laifi amin afuwa, amma kema kinsan hakan bai ƙyautuba, kwananki ai ƙarin wani nauyine, idan ALLAH ya kaimu saikije ki yini kinji". Da sauri ta kallesa, "Da gaske dan ALLAH?". Yanda tai maganar saita so bashi dariya, amma sai ya gimtse ya sumbaci goshinta yana faɗin "Insha ALLAH Qurratul ain, ALLAH dai ya basu lafiya, yakuma tsare gaba". "Amin ya rabbi, ammafa ni babu wanda ya faɗamin abinda ya faru". "Ni dai Uncle yace min ƴan fashine suka shiga, amma nasan za'a faɗa miki insha ALLAH, sai kinje gobe idan ALLAH ya kaimu". Shiru kawai Jiddah tayi, tausayin Abba nakuma ratsata.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe gari da wuri ta tashi ta haɗa breakfast, kunun gyaɗa sai soyayyan dankalin hausa data yankashi dogaye, saita soya miyar attarugu zalla da albasa, harta gama Aliyu bai shigoba daga massalaci dayaje. Tana gyaran bedroom ya leƙo. Durkusawa tayi ta gaidashi, bai shigoba ya amsa daga inda yake tsaye a ƙofa, "Mizan tayaki dashine?". Kanta ta girgiza masa tana faɗin "A'a ka barshi, shara kawai zanyi". Kansa ya jinjina mata ya juya ya fita, ta bishi da kallo saida ya fice sannan ta miƙe taci gaba da aikinta. Ko morping yau ƙinyi tayi, tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atanfa, kayan karin kumallon ta ɗiba zuwa sashensa. Shima har yayi wankan yana shiryawa ta shigo. Idanu ta zaro tana ɗan dafe ƙirji, sanan ta marairaice fuska tana faɗin, "Dan ALLAH kayi haƙuri, banzo na haɗa maka ruwan wankaba". "Tab ai bazan haƙuraba yarinya".. Durƙusawa tayi agabansa, "Dan ALLAH fa nace". "To saikin faɗi sunana". Babu shiri ta ɗago ta kallesa, yako yi kicin-kicin da fuska tamkar gaske, "Idan har baki faɗaba gwammajan ma bazaki jeba ko". Tuni ta fara hawaye, "ALLAH ni bazan iya faɗar sunanka ba". "To saikin faɗi abinda zaki ringa kirana dashi, danni nagaji da maidani surukinki da kikeyi". Wai shi dama haka wanan mutumin yake? Jiddah ta ambata a zuciyarta dan takaici, harga ALLAH da burin zuwa gidansu ta kwana, hardasu mafarki, dan haka gara tafaɗa tasamu taje, kuma kasa tayi da kanta sanan tace, *_"Zauji ghaliy"_*. Kafaɗunta ya kamo ya ɗagota zuwa jikinsa yana faɗin "Masha ALLAH Aglannissa, daga yau karna sakejin an ɓoyemin suna ana kwana-kwana". Kanta ta ɗaga amasa alamar amsawa. Sakinta yayi ta taimaka masa ya ƙarasa shiryawa, sanan taje kiran Maimuna dansuyi kari..........✍🏻
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [12/31/2019, 3:25 PM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[61➖62]_*
............Koda su Ashir suka amso kuɗi a kotu ƙiri da muzu suka hana Alhaji Garba, hasalima shi baisan wainar da suke toyawa ba, dan yakoma sashen amaryarsa ya tare, kwata-kwata baya barin rana ta gansa, musamman ma da yanzu yasan yanada laifi a wajen ƴaƴansa akan abinda yayma mahaifiyarsu, toshi babban ma abinda yakeji a ransa gameda ita shine tsananin tsanarta, ko kaɗan baya sha'awar koda tunata ma. A yau yay nufin kiran Abba ya tuna masa zancen kuɗinsa, amma sai wayar taƙi shiga, hakanne yasakashi maida akalar kiran ga yaransa na kasuwa akan su bincika masa Alhaji Zakari a shagonsa. Mamaki ya kama Labaran, yace, "Alhaji wane kuma Alhaji Zakari za'a gani a kasuwa bayan shagon nasama yadawo naka?". Zaune sosai Alhaji garba ya tashi, dama kwance yake amarya namasa tausa, "Labaran ban fahimci zancen nakaba ai nima, bani a warware". Labaran dai baiyi jayayya ba ya ɗakko labari tundaga tushe ya zayyanema Alhaji Garba, babu shiri kuwa ya rikito a gado, amarya na tambayarsa mike faruwa bai kulataba. Sashen Hajia Deluwa ya nufa, wadda zuwa yanzu ka ganta dole tabaka matuƙar tausayi, dukta kuma ficewa hayyacinta, ƴan kuɗin da su Ashir suka amso miliyan goma suka bata, sukuma suka rabe sauran harda ƙanwarsu dake karatu. Shagon kuma yazama na yayansu saboda shine ya saya. Amma sai sam kuɗin basu gusar mata da damuwarta ba, itadai tafi buƙatar mijinta a gareta, babban tashin hankalinta na gaba kuma warin da takeyi, wanda hatta ƴaƴanta saisun toshe hanci suke iya zuwa inda take, jiya wata ƴar uwarta tazo gidan, amma sam kasa zama tayi tanata faman toshe hanci, ita kuma ko kaɗan batajin warin saima ƙamshinta na gayu datake zubawa a kullum........ Banko ƙofar da Alhaji garba yayine da ƙarfi yay matuƙar firgitata ta miƙe zumbur tana kallonsa, "Alhaji lafiya kuwa?". Hannunsa toshe da hanci yace, "Ban kuɗina". Cikin sanyaya murya tace, "wane kuɗi Alhaji?". "O bama ki saniba ko? To wanda ƴaƴanki sukaje suka amsa a kotu". Baki ta taɓe cikin ƙarfin hali, "Yanzu dan ƴaƴanka sunci waɗannan ƴan kuɗin daga cikin abinda yake haƙinsu shine zakazo kanamin hayaƙi, idan ka mutu sukeda gadon su ai". Galala yay yana kallonta tamkar wani soko, yace, "Aiyyyy dama maganar danakeji a gari gaskiyane? Bakida buri saina mutu kuci gado keda ƴaƴanki, to aiko yau ɗinnan basai gobeba zaki kama gabanki, saidai kisa a biyo dare yau a kasheni, kosu su Ashirun suzo su karni gobe a raba muku gado, bankuma yadda keɗin jahila baceba sai yau wlhy, dama da ALLAH yayma namiji arziƙi to kullum burin mace ya mutu suci gado itada ƴaƴanta, shiyyasa kikaita korar min mata kina musu asiri ko?, to ai dama tuni bokan naki yazo ya sanarminin kafin ya mutu, dan har kasuwa yazo ya sameni ya faɗan duk tsiyatakun da kuka aikata, harda haukata yarinyar Alhaji zakari, wanan ne yasani burin barmasa kuɗin, dama ina masa barazana ya banine domin hakan yazama izinina a garesa ya kiyayi halayyar cin bashi, shine ku ƙwararru kukaje kuka amshi kuɗin, kisani wanan karon bazakuci a banzaba kamar yanda kuka sabaci, insha ALLAHU kuma saikin rigani mutuwa, kije na sakeki saki Uku, kuma a yau nakeson ki barmin gidana". Wani gigitaccen ihu hajia deluwa ta kwala ta yanke jiki ta faɗi a wajen babu rai. Alhaji garba baibi takantaba yay fitowarsa.
A wanan mummunan yanayin autarta data dawo daga makaranta yau cikin ɗokin ganinta ta isketa, bata sanarma kowa zatazoba saboda ta basu mamaki, sai ita ta tarar da abin mamakin. Itace takira baban yayansu a waya. Ankai hajia deluwa asibiti a sanƙame, bakuma a samu farfaɗowarta ba sai washe gari, wanda har zuwa lokacin babu alhaji garba babu dalilinsa, ama ranar suka cane dubai yawon amarci shida amaryarsa. Hajia deluwa dai sai yamma lis ta farfaɗo, saidai kuma tasamu mummunan ciwon ɓarin jiki, ɓarinta na dama baya aiki gaba ɗaya har ido ɗaya, saida ɗaya take gani shima bishi-bishi, baki kuwa ya karkace yana zirar da yawu. Ƴaƴanta sun shiga tashin hankali matuƙa, sunyi kuka sosai dan suna ƙaunar uwar tasu, sai dai basuda yanda zasuyi. Haka suka cigaba da jiyyarta, tun sunayin abun da marmari har suka koma biyan likitoci su kula da ita, suko suka koma kan harkokinsu, sai dai suzo su dubata. A kwana a tashi kuma sai dubiyarma ta fara gagararsu zuwa, dan saisu haɗa kwanaki biyu basu leƙata a asibitiba. Likitoci suma suka fara ƙosawa da ƙazantarta, aiko suka kira su Ashir suzo su kwashi abarsu. Wannan ne silar dawowarta gidan jiyya, har kuma sanan Alhaji garba bai dawoba, dan sunacan suna hutawarsu da amarya dake fama da ƙaton ciki, haihuwa yau ko gobe. Tunda aka maido hajia deluwa gida fa babu mai mata kallon arziƙi, dan bilki mai aikima tuni ta gudu abinta, haka hajia deluwa zatayi kashinta da fitdari babu mai gyarawa, ga tsoro da ake bata kullum, taita ganin halittu masu ban tsoro, haka zataita kuka babu damar ihu, wanima lokacin dariya za'aita ɓaɓɓakawa, amma tarasa a inane, kokuma aita kuka, ko kukan dabbobi kala-kala, gaba ɗaya ta susuce, itaba mahaukaciyaba ita ba gawaba. Mai kula da itanma saita gadama take bata abinci tana toshe hanci, data zirara mata take baro sashen. autarta kuwa ƙiri-ƙiri tabar zaman sashen, takoma sashen babanta, saitayi satima bata kalli sashen hajia deluwaba. Ruwa a jallo hajia deluwa ke fatan ganin koda ɗaya daga cikinsu Jiddah ne ta nemi gafara, tasan dai bama kowane zai yafe mataba, dan ita kanta batasan iya adadin matan data salwantar ba akan kar'a zauna mata da miji, wasu jini ta sakar musu, wasu warin jaɓa, wasu hauka, wasu kuwa taita ɓarar da cikin da suka samu dan karsu haihu a gidan, watama muguntar data saka bokanta yayi ta manta kalarta, gashi a yau tana girban abinda ta shuka.
ALLAH ka shiryemu, ka tsaremu daga son zuciyoyinmu😔🙏🏻
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau dai kam a gida Jiddah ta yini abunta, sosai takema Abba hidima tamkar sauran ƴan uwanta, komai yace yanaso kafinma ya rufe baki an masa, yau kuma ƴan adamawa ma sukazo suka dubashi, amma basu kwanaba suka juya gida, kowa ya gansa saiya tausaya masa, dan sosai yanajin jiki. Hajia Hindu ce dai da sauƙi sosai, dan harta fara ɗan takawa, ita babban tashin hankalinta yanzu kuɗin dake hannun ƙaninta, kwata-kwata takasa samun Number sa, takuma rasa wazata kira ya haɗata dashi, itama dai ƴan uwanta na zuwa jefi-jefi dubata, dan ba kowaba, acewarsu batada mutunci, mutum ko zuwa gidanta yayi tata masa yatsine-yatsine kenan, ko ta saka ƴaƴanta suyita maka rashin kunya.
★★★ Tun daga ranar duk bayan kwana biyu Jiddah sai tazo gida ta yini, kullum dare kuwa Aliyu sai yazo duba Abba, haka mijin aunty Nafisa ma, mazan su Aunty Hannatu ma duk sunzo, kasancewar ba'a kusa sukeba basa gajiyawa da kiran waya kullum safe da yamma. Malam ma da tawagarsa yazo har gida ya duba Abba, yadai sha addu'oi kam. Hakama dangin Umma duk sunzo dubashi. Haka aka cigaba da jiyyar Abba dake matuƙar shan baƙar wahala karayar ƙugunsa, dan na ƙafar Alhamdllh harma an kwance, dukya rame yayi baƙi. Dolene ya baka tausayi saboda jigatuwa da yakeyi, zuwa yanzun kam yafara laushi. Dan matar son nasa Hajia hindu ko ruwa wanan bata taɓa damuwa da zaman bashiba balle sannu da jiki, kullum cikin sakar masa habaici take da takalar su Umma fitina, idan anyi abinci sai tace bazasu ciba, yaranma harda kuka wai basu iya ciba, abinda yakuma birkitata kuma shine koro su kalifa da akayi daga makaranta, dan an kasa biya musu kuɗi, ta kafa tijara sai a siyar da motocin Abba biyu data kai yaran makaranta a biya musu su koma, Uncle yahya kuma yace bata isaba, tunda ba haƙinsu bane su kaɗai, kuma motocima ko an sayar jiyyar Abba za'a cigaba dayi da kuɗin, idan zata bari a maidasu ta gwamnati ta bari, dan kalifa ssce zaiyi, su Hussain kuma kwalfayin. Amma sam saitace ƴaƴanta sunfi ƙarfin makarantar gwamnati, shiko Uncle yahya yace suyita zama babu karatu, dama ba islamiyya suke zuwa ba, danshi yagaji da iskancinta hakanan, tabarsu suji da jiyyar Abba amma taƙi, kullum cikin tadama mutane hankali takeyi a gidan, ga rashin kunyar su kalifa da basa ragama kowa harshi Abban. Dan jiya da daddare zafi yasa akama Abba shinfiɗa a waje aka fiddoshi yasha iska, to babu wuta, Umma kuma tashiga da fitilar ɗaki zata ɗakko maganin sauro ta kunna, dan yanzu duk su Aunty Sauda sun koma gidajensu, sai dai suna ƙoƙarin kiran waya, sanan duk bayan sati biyu suna zuwa suyi kwana biyu su koma, Zarah kuwa an kirata hira tana gidan Uncle yahya, tare kuma suka fita da Walida tai mata rakkiya. Ihun Abba kawai Umma taji, aiko tafito a guje, kuka sosai da ihu yakeyi yana faɗin Hussain ya kasheshi. Umma ta riƙe ƙafar daya riƙe yana ihu da tambayarsa miya faru?. "Yagana Hussain ne ya takani, amma ko juyowa ya kalleni yaronan baiyiba ya fice abinsa". "Hussain kuma? To baya ganine kokuwa?...." "To inda yana gani zai takashine baƙar annamimiya". 'Hajia hindu ta faɗa tana fitowa daga ɗakinta'. Uffan Umma bataceba, saima hawayen tausayin Abba daya cika mata idanu, waya ta ɗauka takira Uncle yahya, babu jimawa yazo. Shikam kasa haƙuri yayi saida ya zane Hussain daya dawo. Wanan duka kuwa shine yasaka hajia hindu zama taita tata ruwan bala'i a gidan har dare ya raba. Babu kuma wanda ya kulata sai Zarah data yaɓa mata baƙar maganar data kuma tunzurata, Umma kuwa tahau kan Zarah da faɗa tamkar zata daketa.