Mutum da duniyarsa complete - Chapter 30
Mutum da duniyarsa complete Chapter 30: Mutum da duniyarsa complete Chapter 30. Anyi haka da kwana biyu Hajia Hindu tai shirin tafiya legas. Babu wanda…
3,333 words
Anyi haka da kwana biyu Hajia Hindu tai shirin tafiya legas. Babu wanda maganar bata bashi mamakiba, Abba yace, "Maman kalifa legas kuma? Keko mizakiyi a legas dan ALLAH?". "kajimun musakin mutuminnan fa da wani zance, ina ruwanka da abunda zanjeyi acan? Kana kwance rigif tamkar wani tsohon ƙarfen Mota talauci yabi ya cinyeka kace zakamin iyayi, to wajen Harisu ƙanina zanje, shiyyace naje na amso kuɗi na maida ƴaƴana makaranta nasayi gida mu koma mubar wanan gayyar ƴaƴa da jikokin". "Humm Hindu kenan, yaushe shi Harisun yay hankalin nutsuwa waje ɗayan da har kikasan inda zaki sameshi balle yabaki waɗanan kuɗin da kika lissafo?". "Tofa, tanan kuma ka ɓillo, to ta ALLAH ba takaba, kana aibanta min ƙani ne, to saidai kagani akan ƴaƴanka da insha ALLAH saisun haifa maka ƴaƴan tsakar gida". 'Ta ƙare maganar tana nuna Walida dake bakin rijiya'. Murmushi kawai Umma tayi tacigaba da fifita wutar gawayinta dazata ɗora abincin rana, walida ma da zatayi magana saita harareta damata nuni datai shiru. Abba kam kasa cemata uffan yayi, saima ya maida kallonsa gasu kalifa dake leƙensu ta window suna kwasar dariya, kai kace wani Comedy film suka samu suke kalla. Cikin haɗiye wani Abu daya tsaya masa a makoshi ya ɗauke kansa kawai. Hajia hindu taja dogon tsaki tabar wajen tana faɗin, "da kayi magana mana" Daga jikin Window kalifa yace, "Mom aike boss ce, babu ubanda ya isa tanka miki idan kinyi magana. Shida Dady yama zama gurgu inashi ina faɗa damai ƙafa irinki, kema ba cazakiyi suyi cikiba, kin manta baya sonsu, cazakiyi ALLAH yasa a guntule ƙafafunsa". Ya ƙare maganar da kwashewa da dariya su Hassan na tayashi. Ba Abba kaɗaiba hatta da Umma saida maganar kalifa ta girgizata, walida kam kaɗan yarage ta afka rijiya saboda tsorata, Jiddah dake ƙoƙarin shigowa kam jakkar hannunta ta saki ƙasa sata hawaye da kallon su kalifa dake dariyarsu har yanzu. "Lafiya kika tsaya nan?". Maganar Aliyu ta dawo da Jiddah hayyacinta, saurin duƙawa tayi ta ɗauki handbag ɗinta tana goge hawaye, taji daɗi da Aliyu baiji rashin tarbiyyar da ƙannen nasu ke zubama mahaifinsu ba. Cikin murmushi ta ɗago ta kallesa, "Babu komaifa "Kalby, tuntuɓe nayi". Cikin raɗa dan kar ajisu saboda suna soro kuma gabda shiga cikin gidan, amma su Umma basa hangosu, itama taga su kalifa ne saboda window ɗin ɗakin da Hindu ke ciki yana saitin ƙofar sorone, "Kifa kula hajjaju ban gama amarciba". Gaba tai abinta tana murmushi, amma bata tankaba. Shima saiya biyota yana murmushin. Ita tafara sallama ta shiga, kafin tace, "Tare suke". Tashi Umma tai ta saka hijjab, Walida tazo ta rungumeta tana murnar ganinta, dukda kuwa jiyama Jiddah tazo gidan. Har Aliyu yayi gaisuwarsa yagama hajia hindu bata fitoba, kuma sarai tana jiyosa, hakama su kalifa Aliyu na shigowa sukabar jikin window ɗin suka koma ciki. Jiddah bata zaunaba, tare suka koma da Aliyu, dama zasuje gaishe da Aunty Ruƙayyane datai mura, to hanyar gidn ta anguwarsu jiddah ne, shine Aliyu yace su biyo suga Abban, dan zuwa dare da wuya ya samu zuwa sunada majalisin dare na ƙarshen wata da akeyi a masalaccin ƙofar gidan malam. Umma ta ɗakko magani a leda tanabama Jiddah. "Jiddah gashi idan kunje a jiƙa, maganin zakine Yaruwaiya nasa ta amsoma Maimunatu, jiya da Bunami zaizo yazo dashi, dan yanada ƙyau sosai, saura kuje kuƙi jiƙawa saboda ƴar banzar shiriritarku, kuna komawa gida dan ALLAH ki jiƙa matashi, ALLAH ya raba lafiya, ki gaidamin ita, ki kuma cemata tacigaba dashan farin zoɓonnan shima, gobe idan ALLAH ya kaimu Zarah zata kawo mata wani". "To Umma ALLAH ya saka da alkairi, yabama Abba lafiya". "Amin ku gaida gida".
Aliyu dake jiyosu yay murmushi, shiyyasa yake ƙaunar Umma, baiwar ALLAHr tayi, akwai dattako, tunda cikin Maimuna ya tsufa bata gazaba wajen bata maganin zaƙi da duk wanda zai taimaketa ta haihu lafiya, yanda yasan zata iya taimakon ƴarta Jiddah ta cikinta haka takema Maimuna, har zuwa tai ta dubota sau biyu dayake Maimunan ta kwanta a asibiti har sau biyu, tundama cikin ya tsufa tace tabar zuwa duba Abba hakanan sai ALLAH ya sauketa lafiya, sanan duk wasu dabaru na mai ciki Umma faɗama Maimuna takeyi tamkar mahaifiyarta. Hakanne ya saka iyayen Maimuna suma jin daɗi, suka ƙara ɗaukar Jiddah da muhimmanci da janta a jikinsu, koda yaushe suna ƙoƙarin zuwa duba Abba, dan zuminci mai ƙarfi ya ƙullu. Jiddah na fitowa Aliyu yay yunkurin rungumeta sai Walida ta fito dan musu rakkiya, hakanne ya sakashi matsawa baya yana susar gefen wuyansa da key ɗin mota. Walida ta gimtse dariyarta dan ta fahimci abinda da za'ayi ganinta yasa aka fasa. Sai da ta rakasu har mota. Aliyu ya kalleta bayan yama motar key, "Auta wai yaushe zaki dawo mana kwana ne? Daga zuwa sau ɗaya baki sakeba, ko gidanmu babu daɗi? Inama Zarah ban gantaba". "Yaya Zarah taje gidan aunty Nafisa ne". Wlhy malam akwai daɗi sosai, hidimar gidace kawai kemana yawa, ga makaranta kuma, amma insha ALLAH weekend ɗinnan zanzo na sake muku kamar wancan, ALLAH yasama Aunty Maimuna ta haihu ina nan". Sheikh Aliyu yace, "Amin auta, ki gaida Zarah idan ta dawo, mu munyi hanyar ƙauyenmu". Jiddah ma ta amsa da amin. Dariya Walida tayi tana ɗaga musu hannu har suka ɓacema gsninta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Cike yauma massalacin yake da jama'a, tsit kakeji babu wata hayaniya, sai sautin muryar Sheikh Aliyu data karaɗe micrephone ɗin massalacin, bayani yake dalla-dalla bisaga abinda ke rage kuzarin namiji da wanda ke ƙara masa ƙarfi. "Waɗan nan abubuwan dazan lissafo suna taka rawar gani wajen ragema namiji ƙarfinsa ƙwarai da gaske, ga wasu kaɗan daga ciki, sun haɗa da. Hawan jini, Maleria, Ciwon ƙoda, Ciwon sanyi, Ciwon hanta, Wasa da azzakari da hannu, Shan lemon tsami, Sammu (sihiri), Aljanar dare, Ciwon Sukari, Basir, Rashin samun ishashan Hutu, Yawan Bacin Rai, Yunwa (Qaranci Cin Abinci ). Indai kana tare da waɗan nan matsalolin dolene kazama ka kasa gamsar da iyalinka, na lissafo kaɗanne a ciki dan akwai abubuwa da yawa baya waɗan nan ɗin. Saikuma waɗannan magungunan dana ɗan tsakuro muku, Shi maganin ƙarin kuzarin Namiji, ya bambanta ne daga wani mutumin zuwa wani. Misali maganin da wani yasha yaji daɗinsa, ba lallai ne kai idan kasha yayi maka aiki ba. Amma dai ga wasu abubuwan da zanyi bayaninsu anan, kuma mutane da dama sunce sunyi amfani dasu kuma sunji daɗi". *_"1 MAN HABBATUS SAUDA_* : Ka samu shayin Na'a-Na'a wanda aka sanya Na'a-Na'a ɗin sosai. Ka zuba masa Man Habbatus Sauda cokali 1, sannan kasha. Safe da dare kafin kwanciya. Ko kuma ka samu ƙwan Tantabara ko ƙwan Kazar gida guda biyu ko uku, Ka zuba garin habbatus Sauda cokali 1 a ciki. Agauraya a soyashi da Man Habbatus Sauda ko Zaitun, sannan kaci". *_"SAIWAR GINSENG_*: Wani itace ne ingantacce wanda ake kawoshi daga ƙasar China. Idan Namiji ya yawaita amfani dashi zai samu ƙarin Kuzari da girma". *_"KANKANA_* : Kankana tana kunshe da irin sinadarin dake cikin ƙwayoyin Viagra. Don haka tana ƙara ƙarfin Namiji sosai, kuma ƴaƴanta suna ƙara ma Namiji girma ba tare da wata illa ga jikinsa ba. Ka samu ƙatuwar Kankana ka yanka bayan Magriba ko Isha'i ka shanyeta gaba daya. Kuma ka riƙa taunewa ƙwallon. In sha ALLAH U zaka ji bambanci mai yawa". *_"RUWAN CITTA_*: Ka samu Madarar Peak ko Luna, ka tsiyaya ruwan chitta ko kuma garinta daidai misali. Sannan ka samu garin Kustul Hindi cokali guda ka zuba aciki, sannan ka sanya zuma daidai Misali ka shanye, Minti 30 kafin kwanciya". *_"MAN JIRJEER_* : Yawancin Maza masu fama da raunin Mazakuta, Basur ne ke damunsu ko kuma Majinar Kwankwaso (Waist). Shi Man Jirjeer yana ƙone irin wannan Majinar ne, har majinar ƙirji. Don haka yana ƙara ma Namiji ƙarfi. Waɗanda suke zaune a ƙasashen Larabawa kamar Saudia ko Misra zasu iya samun ganyensa cikin sauki. Domin shi suke sanyawa a saman abincinsu kamar yadda muke amfani da Lettuce anan". *_6 ZOGALE_* : Ɓawon jikin itacen Zogale idan aka shanyashi aka dakashi, ana hadawa da Madara ko Zuma ana sha. Shima yana Qara kuzarin Namiji sosai". "Abin lura anan, yawancin waɗannan Magungunan ba wai daga yin amfani dasu sau daya ko sau biyu zaka ga canji gaba daya ba. Dole sai ka juri amfani dasu yau da kullum kana hadawa da Motsa jiki, kuma ka rage amfani da abincin zamani waɗanda suke kunshe da sinadarai masu ƙarfi. Irin su Lemon kwalba, Biscuits, Chocolate, Alawa, Succarine, Farin Magi, etc. Ka koma amfani da kayan sha irin na gargajiya kamar irin su Kunun aya, Mazarkwaila, ƴaƴan itace irin su gwanda, ayaba, Lemo, Karas etc". "Sai kuma za'a iya asamun tafarnuwa cokali biyar 5, Kurtafalu cokali uku 3, Citta cokali biyu 2, Fijil cokali biyar 5, Zuma kwalba daya 1. Sai a haɗasu wuri ɗaya a cakuɗa su da zumar kullum asha cokali biyu a yini kawai insha Allahu za'a samu da cewa da izini ALLAH . ALLAH yasa mu dace"...........✍🏻
Zamu cigaba a page na gaba😄🤝🏻
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽 [12/31/2019, 4:18 PM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[63➖64]_*
.............."kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya". *_"HATSI:_* 1 Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2 Shinkafa. 3 Wake. *GANYE*: 1 Albasa, Galik, Karas, Dankali, Kwakwa. *ƳAƳAN ITATUWA*: Ayaba, Mangoro, Tuffa, Abarba, Kankana, Lemo, Goba, Yazawa. *DABBOBI*: Tsuntsayen da suka halatta aci, Ƴan shila, Naman kifi, Agwagwa, Naman shanu, Hanta. *ABINDA DABBOBI SUKE SAMARWA*: Madara, Yogot, Ruwan zuma, Kwai, Bota". "HaƘiƘa su waɗannan dangogin abincin na kara ruwan maniyyi a jikin ɗan Adam, kuma suna motsar da sha'awar jima'i tare da samar da kuzari ga uwargida ko amarya ko shi kanshi angon. An samo daga sayyidina ALI KARAMALLAHU WAJAHAHU WA RIDIYALLAHU ANHU yace: wani mutum ya gayawa MANZON ALLAH S.A.W cewa bashi da ƴaƴa saboda rashin abinci mai sanya kuzari, sai MANZON ALLAH S.A.W ya umarce shi daya rika cin ƙwai". "Shawara ta farko kada ka taba yaudarar kanka da cewa dole sai kaga ( gaban ka ko azzakarin ka ). yayi girma cikin Gaggawa. kamar yadda Baka Iya komawa young boy haka azzakarin ka, Duk yadda ALLAH yayi halittar Sa, ka hakura da yadda ka samu kanka. Girman azzakari ba shine matsalarba, ka fahimci ya zaka Iya gamsar da Matar ka. Akwai hanyoyi da yawa ta yadda zaka gamsar da Matar ka. Akwai Matar da kalaman soyayyar ka kawai ya gamsar da ita. Akwai Wanda kiss kawai ya gamsar da ita. Akwai Wanda sai kayi da gaske sanna zaka gamsar da ita. Bari mu dauki matsala ta Biyu da kuma ta uku mu tattauna". "(Wato kiss & jima'i ) Kiss yana da matukar muhimmanci a rayuwar ma'aurata, Idan Baka taba kiss ba yana da kyau ka dauki 40minutes kana kiss da Matar ka. Amsar tana nan zaka bani. Jima'i yana bukatar wasa sosai ta yadda zaka Saki jikin ka kayi Mata wasa sosai, kada ka saka girman Kai zaka samu matsala. ka tambaya Matar ka, dan ALLAH Inaso Ki gayamin gaskiya menene Idan Na taba miki kikejin Daɗi. Idan kuma bata Baka amsa ba ka rubuta Mata a takarda 📝 ta Baka amsa". "Akwai Wanda abinda takeso farko ka fara taba Mata (N+Ɗ) (kuyi haƙuri abinda zai amfanemu ake taɓowa, amma wlhy duk kunyarku ta lulluɓeni🙈), Akwai kuma Wanda kalaman soyayya zaka dinga Mata kawai su gamsar da ita fiye da zatonka. Duk waɗannan matsalalolin Ku da kanku ya kamata Ku zauna domin gyarawa. gaskiyar magana kusan 80% Na mutuwar aure a yanzu jima'i shine matsala. Duk mace Mai lafiya sosai, ta rasa jidaɗin jima'i gaskiya duk soyayyar ta ga namiji zata Iya rabuwa dashi. ka daina shan kowanne magungunan Saboda girman azzakari". *"MAN ZAITUN- ORIGINAL*: Idan zaka kwanta ka Shafa ko ba sex zakayi ba sannan kasha cokali🥄 2. Yana taimakawa wurin karfin gaba. *MAN KWAKWA* yana taimakawa sosai ka dinga sha cokali daya ko cikin abinci ne. Waɗannan abubuwan Suna taimakawa sosai ka gwada". "Abinda muka faɗa dai-dai ALLAH ka bamu ladansa, wanda mukayi kuskure ALLAH ka yafe mana, ALLAH ya sakama malaman mu da alkairi damu gaba ɗaya. سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ. *Subhanakal-lahumma wabihamdik, ashhadu an la ilaha illa ant, astaghfiruka wa-atoobu ilayk.* _Tsarki ya tabbata a gare Ka, ya Allah, da yabo gare Ka. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafararka, kuma ina tuba izuwa gare Ka._
*(Wanan Addu'ar Tashi daga Majalisi ce, (Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin. A'isha, ALLAH ya yarda da ita, ta ce: MANZON ALLAH, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, bai taba zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alkur'ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da wadannan kalmomi. (Sai A'isha ta ce: Ya MANZON ALLAH! Na lura cewa ba ka taba zama a wani majalisi ba, ko ka yi karatun Alkur'ani, ko kayi sallah face ka fadi wannan kalmomi. Sai ya ce; "Kwarai. Duk wanda ya fadi wani alheri sai waɗannan kalmomi su zama kamar hatimi ne ga alherin da ya aikata, wanda kuma ya faɗi sharri, sai su zama kaffara ne gare shi)*.
Tuni Sheikh Aliyu ya sulale yabar massalacin, yabar mutane da tattauna wanan lecture ta yau, koda yaje yima malam sallama ma sai wani sunkuy da kai yake tamkar yana gaban surukinsa, shi malam ma dariya ya bashi, amma saiya danne baiyiba, yasan dai wannan lecture ɗince ta yau takawo wanan sinne kan, haka Aliyu yake da tsananin kunya, ALLAH ya bashi sani kuma bai gazaba wajen bayyanama mutane, sai dai ko faɗar yake zaka sameshi mai tsananin jin kunya a garesu. Shiyyasa inhar malam yasan Aliyu zaiyi wa'azi a wajen da zasu kasance inuwa ɗaya to bayama kallon inda yake, dan kuma sakashi a wata kunyar zaiyi, yauma fitowa yay daga massalacin tunda Aliyu yafara bayanin magungunan can, daga soro ya zauna yana saurarenshi yana murmushi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kasan cewar cikin Maimunatu ya tsufa sosai sai dukkan kulawar Aliyu da jiddah suka koma kanta, yanzu haka kowanne dare a sashenta yake kwana bisa amincewar Jiddahn, dan koda ranar girkintane idan yazo wajenta zai kusan raba dare, idanma yana da bukatarsa daya samu nutsuwa zai tsaftace jikinsa yakoma wajen Maimuna ya karasa kwanan. Bawai dan Jiddah batajin damuwar hakan bane ta hakura, a'a a ganinta wannan adalcine, dukda har yanzu bata san raɗaɗaɗin koda laulayin cikiba Maimuna na bata matuƙar tausayi, tanada tabbacin da ace itace a wanan yanayin babu abinda zai hana Maimuna sadaukar mata da Aliyu harta haihu, dan ayanzu hakanma ranar girkin Maimunan idan yakasance ranar batajin daɗi sosai, kuma bazata iya karɓarsa ba, Aliyu kuma yanada buƙata takan amince masa yaje ga jiddah ya samu nutsuwa, haka itama idan Jiddah na al'adah Aliyu yanada bukata kuma lafiyar Maimuna ƙalau takan yarje masa yaje ga Maimuna ya damu nutsuwa, wannan adalcin nasune ke ƙara dasa masa ƙaunarsu mai yawa a cikin ransa, shiyyasa kullum burinsa ya faranta musu da soyayyarsa da kuma abinda ALLAH ya hore masa, sanan ya tsare musu mutuncinsu bisaga haƙƙoƙin da ALLAH ya ɗaura masa. Randa kuma ALLAH ya kawo saɓani a tsakaninsu sukan zauna su fahimci juna wajen warware abin, dan kowa dai yasan zama na yau da kulkum sai ALLAH, tsakanin harshe da haƙorima ana saɓawa balle zaman kishi kona mata da miji. Amma idan aka sanyama zuciya salama sai kiga komai yazo da sauƙi, to hakane ga zaman su Jiddah, Saɓani yakansha gittawa harma Aliyu ya fahimta ya zaunar dasu yamusu nasiha da sauraren tushen lamarin, atake kuma zaibama mai gaskiya haƙƙinsa ya nunama mai laifi kuskurensa, shima kuma yakan samu daɓanin tsakaninsa dasu, wanan kam daduk wadda yasamu sukan yitane a ɗaki su kaɗai batareda ƴar uwar zamanki tajiba kota sani, kuma ko afusaka bazata saninba, saboda kowanne ya iya takunsa daga Aliyun har matan nasa.
Lokacin daya iso gidan saiya iske Jiddah na kuka rungume da Maimuna daketa murƙususu. Hankalinsane sosai ya tashi, bai wani zauna jan jikiba ya ɗakko hijjab ya sakama Jiddah da Maimunan suka fiddata mota, asibitin dake kusa dasu wanda Maimuna keshan kwanci sukaje. Haihuwace gadan-gadsn dan haka suna zuwa aka shiga da ita ɗakin haihuwa, kasancewar asibitin na kuɗine baya rabo da ma'aikata. Jiddah sai kuka take, tama kasa tsayuwa waje ɗaya, ganin a rikice take Aliyu ya kamota ya sakata jikinsa ya rungume yana lallashinta. "Addu'a take buƙata Jiddah, kiyi hakuri kibar kukan, muyi mata fatan ALLAH ya sauketa lafiya kinji". Kanta kawai ta iya ɗaga masa, tareda ƙara lafewa a jikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/1, 5:11 PM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[65➖66]_*
............Hajia hindu dai shirinta tai tsaf domin tafiya, Sai dai kuma ita kaɗai zata tafi bada yaraba, ƴan kuɗin da ake tarama Abba na dubiya tasaka Kalifa yabi duhun dare ya lalubesu tas, shima saida ya ɗiba rabonsa sanan ya kawo mata sauran. Kafin ta kwanta kamar wasa ta gwada Number ƙaninta harisu kamar yanda ta saba, yaukam saiga waya ta shiga kamar almara, jikinta har rawa yake ta fara faɗin hello-hello tunkan a ɗaga. Sai da takusa tsinkewa ne aka ɗaga wayar. Cikin mamaki tace, "Wanene? Ina kuma mai wayar?". Dariya yaron harisu yayi irinta basawa wadda harta tsorata Hindu, saida yayi mai isarsa sanan yace, "Wanan yakwana biyu a barzahu. Halan kece yayarsa da tai mana hanyar samun ƴan canji". Zumbur hindu ta miƙe dan bata fahimci maganar tasa ta farkoba, tace, "Eh wlhy nice, tun washe gari nake nemanku a raba kuɗin amma wayar taƙi shiga, dan ALLAH ina harisun yake?". Wani wawan tsaki yayi yace, "ke wai halan kanki baya kawo wuta ne, kajimin mumun mata, nace miki yana barzahu, bara na miki gwari-gwari danna kula ƙwaƙwalwar kifi gareki, dama Oga haris baizo amsar kuɗi danya raba dakeba, yazo amsane ya ware abinsa, shiyyasa ya saka miki Number busy yanda kokin kirashi bazaki samuba. Duk wahalar da mukasha wajen amso kuɗin nan muka wanke ƙafafunmu tundaga legas mukai masa rakkiya amma yay nufin cin amarmu, muko bazamu iya ɗaukaba, sati huɗu kenan muka caccake cikinsa da wuƙa muka aikashi gidan kowane shege da shegiya (lahira kenan), yanzu kema na ɗauki wayarkine danki daina wahalar nemansa ma, kisamu gobe kisa ai masa addu'ar uku data bakwai data arba'in, wainar da za'a bamu kirabama almajirai, muna miki gaisuwar ta'aziyyarsa fa, kuma karki damu sai da mukai masa salla kafin mu jefashi ruwa......" Ƙitt ya yanke wayar. Ihu kawai hajia hindu ta dage ta fasa, ta kware baki tana rusar kuka da kiran "Wayyo kuɗina, shikenan na mutu, Harisu ka talautani..." Wanan ihune yay sanadin tashin su Umma a barci, sukazo suka rufu akan hajia hindu ana tambayar miya faru?. Batareda tasan mi takeba tashiga sakin surutai akan yanda ta ƙulla makirci da haris aka amshe kuɗin Jiddah, harma da dukan da Abba yaci wanda gashinan ya zame masa sanadin doguwar jiyya. Wannan lamari yayi masifar girgiza su Umma da Abba dake cikin ɗaki kwance yana saurarensu, jiyay hawaye kawai suna gangaro masa, matar daya fifita fiye da kowace ta aiko masa ɓarayi? Wadda yay burin guduwa da ita suci kuɗin tare, dama abinda ta ƙulla masa kenan shiyyasa ta lallaɓashi subari sai da safe su wuce, tini wutar kan Abba ta ɗauke gaba ɗaya, yaji komai yamasa ɗif, bayajin sautin komai, baya ganin komai sai duhu, daga haka bai sake sanin inda kansa yakeba kuma.
************