Mutum da duniyarsa complete - Chapter 31
Mutum da duniyarsa complete Chapter 31: Mutum da duniyarsa complete Chapter 31. Washe gari Uncle yahya yasa aka kama hindu, dai bata cancanci cigaba da…
2,721 words
Washe gari Uncle yahya yasa aka kama hindu, dai bata cancanci cigaba da zama batareda ta fuskanci hukunciba. Abinda yabata matuƙar tsoro da mamaki shine ko damuwa su kalifa basuyiba, sai Munner ne kawai ke kuka da riƙeta. Abba kam saida aka kaishi asibiti, dan jininsa yayi ƙololuwar hawa sama.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Alhamdulillah ALLAH ya sauki Maimuna lafiya gabannin asubahi, sai dai tasha matuƙar wahala abin tausayi, ta haifi babynta Namiji mai kama da Sheikh Aliy masha ALLAH, bayan sun shiga sun dubata tana barci suka fito suka barta. Rige-rigen ɗaukar jariri akai tsakanin Aliyu da Jiddah, ALLAH yabama Jiddah damar karɓa, shiko ya haɗa da Jiddah n da jaririn duk ya rungume, Jiddah ta ɗago tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi ta furta, بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي الْمَوْهُوبِ لَكَ، وَشَكَرْتَ الْوَاهِبَ، وَبَلَغَ أَشُدَّهُ، وَرُزِقْتَ بِرَّهُ. *_Barakal lahu laka fil mawhubi laka, wa shakartal wahiba, wa balagha ashuddahu, wa ruzikta birrahu_*. _ALLAH Ya yi albarka ga abin da aka azurta ka da shi, kuma Ya sa ka godewa wanda ya baka (shi), kuma Ya sa shi ya rayu har zuwa ga matukar karfinsa, kuma a azurta ka da biyayyarsa._
Aliyu yakuma rungumeta yana amsawa da "Ameen ya rabbi Noorunnisa, nagode sosai, ALLAH ya kawomin kema ta tsatsonki". Murmushi kawai tayi tana sumbar goshin yaron, yanda takejin ƙaunar mahaifinsa haka shima takejin tasa ƙaunar.
★★★★★
Tunda gari yay haske bayan Aliyu yadawo sallar Asubahi yafara sanarma Malam, daganan sai Aunty Ruƙayya da Aunty Siyama da gidansu Maimuna. Kafin kacemi labari ya gama zagaye dangi, zuwa tashin hantsi duk masu kusanci dasu sun iso asibitin, lokacin kuma Maimuna ta farka daga barcin datai na hutawa. Zuwa ƙarfe sha biyu aka sallamesu suka koma gida tareda babynsu abin sha'awa, fuskar Aliyu kawai zaka kalla ka tabbatar yana tareda tsantsar farin ciki. Addu'oi dai yaro ya shashi tuni har yamasa huɗuba da suna Muhammad. Maimuna kam yanda yaketa nuna mata tattali har kunya abun yake bata, duk mintuna kaɗan ya kirata yace ya jikinta da babynsa.
Dukda Jiyyar Abba haka Umma ta fisge tazo tayi barka ita da maman sadiq, hakama su Aunty Nafisa tazo tayi, haka su aunty Hannatu duk sai da suka kira a waya sukaima Maimuna barka da shi kansa Aliyun.
*_Bayan sati ɗaya_*
Ranar da yaro ya cika sati da haihuwa aka raɗa suna a masallaci, da yamma akayi walima. Su Jiddah ansha hidima, dan kuwa tayi lis da gajiya, tunda akayi haihuwarnan bata samun kanta, koda yaushe cikin hidima take, danma su Aunty Siyama na taimakonta da wasu ayyukan, da dare kuma Sheikh Aliy yay mata tausa har tayi barci yana jera mata sannu da saka albarka. Washe garin sunan Maimuna ta koma gidan malam wankan jego badan Aliyu yasoba, ko Jiddah saida ta shiga damuwa, harda ƴar kwallanta kuwa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan sati ɗaya da sunan yaron Maimuna aka shiga kotu da hajia hindu wanda tagama jigata da fita hayyacinta wajen kwalawa . Zan iya cewa wanan zaman kotu yazama silar tone-tone ne masu tada hankula, dankuwa hajia hindu bata ɓoye komaiba gameda yanda suka ƙulla karɓe ƙuɗin itada ƙaninta, sai dai tace ita batace su dokeshiba....... Kafin ta rufe baki wata murya a cikin kotun tace, "Ƙaryane, tunda kika iya shirya kasheni shima zaki iya sawa a kasheshi". Gaba ɗaya jama'ar kotun juyowa sukayi domin son ganin mai maganar. Zaune yake cikin ƙananun kaya, fuskarsa lulluɓe da hular rigar sanyi ƙatuwa dake a jikinsa. Babu mai ganin fuskarsa.... Alƙali ya yanke shirun da faɗin kowaye mai maganar ya fito. Tunda ya taso kowa ya zuba masa ido, kansa a ƙasa babu mai ganin fuskarsa har yanzu, idanun hajia hindu kai kace faɗowa zasuyi ƙasa wajen son ganin wanene shiɗin?, sai zufa ke keto mata a kowanne sashe na jikinta. Bayan an nuna masa ya tsaya a akwatin kotun Alƙali yace ya buɗe fuskarsa. Wani murmushi yasaki kafin ya janye hular kansa fuskarsa ta dattijantaka alamun yanada shekaru ta bayyana. Ƙara hajia hindu ta ƙwalla tareda zubewa a sume, da sauri jami'ar tsaro taje ta yayyafa mata ruwa ta farfaɗo. Hajia hindu sai sambatu take tana faɗin "Wlhy karku aminta dashi fatalwane, na rantse da ALLAH ba mutum bane fatalwane. Banda murmushi babu abinda mutumin keyi, yayinda dukkan jama'ar kotun suka zuba musu ido sunason jin mike faruwa?. Tsawatarma hajia hindu Alƙali yayi, dan haka ta nutsu tana maƙyarƙyatar tsoro. Alƙali ya gyara zamansa yana faɗin, "bawan ALLAH kai ɗin wanene?". "Da farko dai ya mai shari'a sunan SHAZALI, ni ɗan asalin garinan ne, anan natashi nai wayo har zuwa samartakata, bayanan ne nabar garin kano dalilin rabani da akai da ita Hindu aka aurar da ita ga wanina, takaicin hakanne ya sakani barin kano, amma sai sonta ya hanani sukuni a inda nake, hakanne yasani yin waiwaye adon tafiya, na dadawo kano rama abinda mahaifinta yaymin, dan iyayenta sunce bazan aureta bane saboda tantirine ni, gashi babu wanda yasan sana'ata, babanta ya haɗata aure da ɗan abokinsa badan tana sonshiba. Da wanan damar nayi amfani wajen jawo ra'ayin hindu muka cigaba da soyayarmu a ɓoye da auren nata, harma takaimu ga fara aikata zina. wataran mijinta yazo ya iskemu awanan halin, shine ya saketa, tareda ƙwace abinda suka haifa, amma sam yaƙi sanarma iyayenta abinda yasa ya saketa, saidai yace kawai zamanne ya ƙare. Wanan shine cikar burina daman, Hindu tacigaba da zaman zawarci a gidansu, yayinda nikuma na maidata tamkar wata matata, ana cikin haka wata hanyar samu tazo mini, banyi baƙin cikin jawo hindu jikinaba na biya mata makka. Tayi mamakin a ina na samu kuɗin, dan nidai tasan ko sana'a banida ita sai kame-kame. Amma koda ta tambayeni saina ɓata rai akan ta rainani, haƙuri ta bani taje ta sanarma iyayeta, Koda wanan magana taje kunnensu sai suka ƙaryata, musamman babanta, amma mamanta sai ta nuna murnarta har tana jifan baban hindu da kalmar yanama ɗiyarta baƙin cikin cigabanta. Wannan magana ta ɓata ransa yace ya zare hannunsa daga kan hindu da harisu ƙaninta dayazama ɗan iskan gaske. Bata wani damuba muka tafi saudia aikin hajji, saida mukaje can nake sanarmata ma'anar zuwanmu saudia, dan satar kuɗin jama'a ƴan aikin hajji zamu rinƙayi, da farko taƙi, amma dana kalamayeta da daɗin baki saita amince muka fara, kafin kacemi mun tara kuɗi masu yawa, duk abinda muka samu wani abokina mazaunin saudia yake amsa yana tura mana ta banki. Dalilin haɗuwarmu da Alhaji Zakari kuwa ɗakinmu ɗaya ni da shi, wataran sai naji Alhaji zakari yana waya da labarin miliyan hamsin dayaci a banki zai faɗaɗa kasuwancinsa, tunda naji wanan batu sai hankalina ya tashi, dan haka nasami hindu da batun na yarda su ƙulla soyayya da Alhaji Zakari dan muci kuɗin, da farko taƙi amincewa saboda tana sona sosai, saida nagama lallaɓata da daɗin baki akan ai muna tare bamu rabuba, kuma zamu cigaba da Mu'amularmu sanan ta amince. tashiga jikin Alhaji Zakari har suka ƙulla soyaya tun'a can, muna kuma dawowa aka ɗaura musu aure dashi, shirinmu shine bayan kamar wata ɗaya mu mallake kuɗin tasa ya saketa. Sai dai tun bayan aureta da Alhaji Zakari muna tare muna cigaba da mu'amularmu, cikin farko data samu nasan nawane tabbas, dankuwa inada hujjata, abin daɗi kuma saita haifi namiji kamar yanda Alhaji Zakari yake buri, wanan ne yakuma sakata ƙin yarda tarabu da Alhaji Zakari, nayi-nayi amma taƙi, sai dai tace mudai cigaba da tarayya, bazanyi takaici kojin kunyar faɗama duniya abinda basu saniba, abinda yasa zan faɗa kuwa danya zama izina ga ƴan baya masu aƙida irinta Alhaji Zakari yaro, dukda ƙyautar da ALLAH yay masa saiya bijire masa, ya manta ALLAH shike bada haihuwa ga wanda yaso, yakuma hana wanda yaso, sanan shike bayarwa daga jinsin dayaso, mutane da yawa zasuyi mamaki idan nace su Kalifa ba ƴaƴan Alhaji Zakari yaro baneba, indan kacire autansu dabansan sunansaba........" Tuni kotu ta rikice da ƙananun magana, Abba kam yama daskare acikin WheelChair ɗin dayake ciki, hakama Uncle yahya dasu Umma da Jiddah. Alƙali ya buga gudumarsa alamar ayi shiru. Tsit kotun tayi aka maida hankali ga Shazali daya cigaba da faɗin, "Tabbas ƴaƴansa duk nawane, zama a iya gwada jinsu daduk dalilan da zasu tabbatar da hakan, bayan ta haifi ƴan biyu ne na matsa mata akan a kashe alhaji zakari mu kwashe kuɗin, amma sam sai tace bata yardaba, wai ba yanzuba, tabi ta tsarani da zance na yarda da ita. Sai dai danayi bincike saina gane wayo tamin, ni tama saka a kasheni saboda taci kuɗin ita kaɗai. Ban nuna mata na saniba har tayi ƙulla-ƙullarta a motata da nayi shirin yin tafiya a lokacin, daga baya muka canja komai na biya waɗanda tasaka su kasheni suka kaima babanta motar shi ya shiga ya mutu a lokacin. Daga baya bayan sunsha alhinin mutuwar babanta labari yazo mata nima na mutu, sai dai tana shirin samun dukiyar Alhaji Zakari itama ciki ya bayyana a jikinta, shine ta hakura saita haihu. To bayan haihuwar tatane kuma abubuwa sukaita faruwa ta gagara kashe auren ta gagara mallakar dukiyar tasa har wanan abun ya faru na ƙwatar kuɗaɗen Alhaji Zakari aka bama Alhaji Garba da ƴarsa, ta tura ƙaninta yaymusu fashi ya amshi kuɗin dan itama ta samu rabonta karta tashi a tutar babu, shine suka jibgi Alhaji Zakari saboda gardamar dayay musu, dama tace ko kasheshine ya kama ayi itadai kuɗin take buƙata, shikuma ƙaninta dama yajene da nufin amsar kuɗin ya hanata, nikuma na saka aka bishi aka amshe kuɗin shima aka kasheshi, dan nayi alƙawarin bazataci kuɗinba itama. Wanan bayanin danake muku duk ina samunsa ne ga direban gidansu, wanda ni yakema aiki tsawon shekaru ba tareda hindu ta saniba, na zaɓi zuwa na faɗi wanan sirrine domin Alhaji Zakari yasan ƴaƴan daya ƙwallafa rai a matsayin nasa to ɗayane nasa, ita kuma na nuna mata ramin mugunta ƙurarrene, ta gina kuma ta afka, sanan tasan ina nan a raye ban mutuba kamar yanda tayi fata". Kotufa takuma ruɗewa da ihu, daga masu ALLAH ya ƙara sai masu faɗin maganin Abba kenan, sai masu tsinema hindu da shazali, Su Jiddah kam kuka suke sosai, dan ita kasama daurewa tayi tafito daga cikin kotun itada Umma. Da ƙyar Alƙali ya samu kotu ta nutsu, aka tambayi hindu abinda shazali ya faɗa gaskiya?. Batayi jayayyaba ta amsa da eh hakane tana sharar ƙwala. Alƙali ya yankema hajia Hindu hukuncin shekaru Ashirin a gidan yari, shikuma Shazali saboda kisa da yayi ɗaurin rai da rai. Ihu Hajia hindu take tana kururuwa, amma ba'a sauraretaba aka fiddata, shazali ya roki alfarmar abashi ƴaƴansa, dan sukaɗai ke gareshi a duniya sai mahaifiyarsa. Atake kotu tace ta bashi, mahaifiyarsa tazo ta amsa. Har aka wuce da hajia hindu da takoma tamkar mahaukaciya tanata sambatu su Uncle yahya basu iya motsawaba, saida kowa ya watse suka fahimci Abba a sume yake ma. Da gaggawa aka ɗaukeshi zuwa asibiti mafi kusa........✍🏻
*_Abba kagani ba aima ALLAH wayo, kuma ba ai masa tilas_*.☹☹☹⛹♀
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [1/2, 1:04 PM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[67➖68]_*
............Kuka sosai su Jiddah keyi, tunda suke basu taɓa gamo da makamancin wannan rikitacciyar rayuwarba, bakuma su taɓa kawo faruwarta a zahiriba sai yau, ashe abinda ke faruwa a films da hikayoyin marubuta yana faruwa a zahiri?. Dafe kai Jiddah tayi saboda wani jiri dake neman kwasarta ƙasa, da sauri ta durƙushe a ƙasa tana toshe baki da hanci saboda wani warin magani daya doki hancinta. Da hanzari Zarah da Walida sukai kanta suna tambayar lafiya? Hakama Uncle yahya, Umma nadaga tsaye tana kallonsu amma ta kasa koda motsa ƙafarta balle tazo garesu. Da hannu tai musu nuni da Amai. Zarah data fahimta tai saurin faɗin, "Yaya Jiddah Amai?". Kai ta ɗaga mata tana kuma danne bakinta dan gab yake da zubowa. Kamata sukai da hanzari sukayo waje, bama su ƙarasa inda ya daceba tafarashi babi ƙaƙƙautawa, sauƙinma sunbar idanun mutane, sosai Jiddah ta galabaita, idonta sai lumshewa sukeyi, ga wani azababben ciwon ƙirji daya taso mata lokaci ɗaya, kafin kace mi tuni tagama fita hayyacinta, daganan bata sake sanin abinda ke faruwaba kuma.
★★★★★★
A hankali ta buɗe idanunta da sukai mata jingim saboda nauyi, ƙamshin turarensa ne yabata amsar shaidar yana kusa da ita, takuma ɗaga idonta da ƙyar takai dubanta gareshi, dishi-dishi take ganinsa. Sheikh Aliyu da shima idonsa ke a kanta ya sauke ajiyar zuciya tareda kai bakinsa saman goshinta ya sumbata, hannunta dake cikin nashi ya matsa a hankali, kafin cikin sanyinsa ya ce, "Sannu Jiddatulkhair kinji, ALLAH yabaki lafiya". Bata iya cemasa komaiba, sai idanunta data maida ta lumshe hawaye na zirarowa ta gefen idonta. "Ya isa kukan haka Hauwa'u, ki kwantar da hankalinki Abbanma ya farfaɗo, likitoci na Complain jininki ya hau, gashi kuma bake kaɗai baceba". Babu shiri takuma buɗe idonta tana kallonsa, kamarya ba ita kaɗai baceba? Kardai maganar dayaketa ambata mata kwanannan ace tazama gaskiya?. bayan tafiyar Maimuna wanka da kwana biyu saitaita fama da ciwon kai da jiki, ko tausar yay mata batajin ya daina, saiya fara cemata anya kuwa wanan ciwon nata bana ƙanin Muhammad ko ƙanwarsa bane? Ko kaɗan bata ɗauki batun da muhimmanci ba, dan itadai bayan ciwon kai babu abinda takeji sai ciwon jiki wanda take dangantawa da wanan hidimar haihuwar dasuka sha. Kwana biyu dayi mata wanan zance ya kasance da ita, tun a daren yaketa maimaita mata lallai tanada ciki, dan takuma canja masa gaba ɗaya. Ita maganarma kunya taita bata, taƙima yarda su haɗa ido balle ta yarda da maganarsa, yau kuma sai gashi yakuma maimaitawa, hakan kuma na nuni da cewar doctor ne ya faɗa musu......... Hawayen dayake share matane yasata dawowa hayyacinta, ta kama hannunsa ta riƙe tana kallonsa, "Abbu Muhammad ina Umma yanzun?". "Sun wuce gida, sabod Abba ya matsa akaishi gida". "Dan ALLAH mu bisu to, inason ganin halinda Abbana yake ciki ko zuciyata zata samu nutsuwa". "Kinga kiyi haƙuri, dare yayi yanzun kalli agogo ɗaya saura na dare, insha ALLAHU da safe zan kaiki idan kinji ƙwarin jikinki". "Ni wlhy na warke". "To naji ya isa haka bar kukan Umm Muhammad". Murmushi tayi badan ta shiryaba, a duk sanda ya danganta sunanta matsayin Uwa ga ɗansa tanajin wani sanyi a ransa, hakama Maimuna yanzu gaba ɗaya takoma kiranta Umm Muhammad, tana yaba karamcin waɗannan bayin ALLAH a ranta a kullu yaumin, tamusu kutse a zamansu amma sai suka jawo hannayenta suka riƙeta da zuciya ɗaya, itako mizatayi ta biyasu dashi?. Ajiyar zuciya ta sauke saboda abinda taji Aliyu na mata, ta riƙe hannunsa tana tura baki kaɗan. Murmushi yayi ya janye hannunsa yana tashi zaune, itama ya taimaka mata ta tashi, da mamaki tabi ɗakin da kallo sanan ta kallesa. "Yaushe ma na dawo gida to?". "Ai tun bayan farkowarki a asibiti sai likita ya fahimci warin magani da Asibitin yakeyine baƙyaso, dan yunƙurin amai kika fara farkawa dashi, shine yakuma miki allura, a lokacin kuma Zarah ta kirani da wayarki a ɓoye, dan Uncle yahya ya hana a kirani a tadamin hankali". Jiddah tayi murmushi tanajin ƙaunar kawun nasu wanda takeji ƙaunarsa tamkar mahaifi. Da taimakon Aliyu tayi wanka sanan ta rama sallolin dake kanta, da ƙyar yasamu tasha tea ɗin daya haɗa mata, tana gama sha ma ta amayar dashi. Kallo ɗaya zakai masa ka hango tsantsar tausayinta a gareshi, ya gyara mata jikinta sannan ya kamota suka dawo ɗaki suka kwanta yana saka mata albarka da jera mata sannu.
*WASHE GARI*.
Da ƙyar Aliyu ya yarda ya kaita gwammaja kusan ƙarfe ɗaya na rana, dan kallo ɗaya zakai mata ka fahimci batajin daɗin jikinta, gashi takasa cin abinci, tace, "sai taje gida zataci awara".