Nayi nadama book 1 complete - Chapter 13
Nayi nadama book 1 complete Chapter 13: Nayi nadama book 1 complete Chapter 13. Washe gari da safe wannan lbrin ya iski Anuty Sadiya Duk da mijinta ta ya…
3,329 words
Washe gari da safe wannan lbrin ya iski Anuty Sadiya Duk da mijinta ta ya ji dashi akayi komai Amman ya rasa ta INA zai fara kawo mata wannan zance Sai da safen yace ta shirya suje gida Su gaidasu A mota ta kalli mijinta Cikin sanyi tace Abban Yumin. Na,am ya amsa mata Cikin sanyi Sai kuma tayi shiru gamida dafe qirjinta Hannushi yasa ya kamo nata yace Kin kirani kin Kuma yi shiru Kai ta daqo ta kalleshi Cikin rawar murya da alamar kuka zatayi Tace Abban Yumin Zuciyata Na tsinkewa tsoro nakeji ban San meyasa ba tun jiya nakejin faduwar gaba A hankali ya jawota ya manna ta a jikin shi cikin fargaba yace ki rinqa addu,a ki Kuma kasance mai yarda da gaddara Dai dai nan yayi parking a farfajiyar gidan nasu A hankali ta zame jikinta ta fito Cikin tsoro da firgita ta bude idanta da kyau ganin gaba daya harabar gidan a cike yake da mutane a take qafarta ta fara rawa Cikin tsoro ta juyo gareshi tana Abban Yumin me ya faru me kake boye min Hannushi ta riqe tana jijji gawa da qarfi tana ka fada min INA Abba ban ganshi anan ba Allah sarki ita Sam bata kai tunanin ta kan qaninta ta rasa ba Rabi,u dake gefe ne yayi saurin isowa gareta durqushe wa yayi a gaban ta Cikin kuka yace Anuty Sadiya ya Ahmad ya tafi ya Ahmad ya tafi ya barmu Ido ta zaro Cikin tsoro Sai kuma tayi Cikin gida kai tsaye dakin Nenne ta nufa Can ta hango Ummi da sauri taje gaban ta ta fada Cikin kuka tace Ummi Me nakeji Ummi meya samu Dan uwana wayyo Allah wayyo Dan uwana wayyo Nenne Na wayyo cikina Ummi shike nan Na rasa Dan uwa Adam ne ya kamo hannuta Cikin kuka yace Anuty Sadiya mun rasa Ahmad Anuty Sadiya Ahmad ya tafi ya barmu Gaba daya suka ruda parlon kakace ta tashi itama Cikin kuka ta kamo hannu Sadiya Da Adam tayi Cikin daki dasu
Suna shiga Sadiya ta hango Yusuf Wanda tun jiyan bai tashi a wurin ba sai sallan asuba da ya tashi yayi da taimakon hydar Tana hoggo shi ga Nenne a gefenshi Tana riqe da hannushi tana fadin Haba Yusuf kayi mgn mana Yusuf katashi kaje qun baqin da sukazo yi maka gaisuwa Haba Yusuf fushi kakeyi da yin ubangiji ne Shin ase bazaka rungumi qaddara ba Yusufa mufa musul Maine Shi kam Yusuf ido ya zubawa Anuty Sadiya Ita Kuma gabanshi tazo ta durqusa ta kamo hannushi ta kifa kanta kan cinyarsa ta saki wani kuka mai ban tausayi Tana kuka tana fadin Yusuf ya zamuyi Allah shi yabamu Ahmad Kuma shi ya dauke shi Dama kullum haka Ahmad ke gayamin ai Wanda ya Baku ni yaga fiku sona Anuty Sadiya ki dena damuwa da halin da nake ciki ase Ahmad duk maganganu da yakejin wasiyace
A hankali ya daura nashi kan kan kafadarta Yasa hannushi ya riqe nata Sai ya kuma kura mata ido Yana jujjuya kai A hankali tace Yusuf kayi min mgn ma ko zanji sanyi a raina dama kullum Ahmad cemin yake ko ya mutum kar Na damu gaka ga Adam da Abubakar duk abin da nake so zaku min Kai ta juya cikin kuka tace Ummi INA Abba Ummi a wane hali Abba yake ?
Cikin duseshewar murya tace Sadiya Abba tun a Daren jiya ya tafi Abuja shida Hydar Kuma yau dinnan zasu wuce India A Dan tsorace tace Ummi Abba ne ba lfy ko ehh Sadiya abbanku baya Cikin hayya cin sa Hawan jinisa ne ya tashi Sai hawayen ke bin fuskar ta
Adam ne ya kalleta Cikin sanyi yace anty sadiya ko zakizo kije dakin Ummi ki zauna da su Maryam da Aysha da Amira suna can Sai kuka sukayi ba mai lallashin wani Cikin sanyin jiki ta nufi dakin Ummin
Ayyah Maryam da aysha suna zaune tun jiya da Aysha ta farfado suke ta kuka abin tausayi Aysha abin ya hadu mata jiya tasan ba ummi bace mahaifiyar ta kuma a jiya ta rasa ya Ahmad dinta Kuma a jiya tasan mahaifiyata ta rasu a lkcin aihuwarta Ganin Sadiya yasa ta fada jikinta tai ta wani sabon kuka Ta ruggumi meta nan sukayi ta kukansu Da dyar dai suka samu suka tsagaita Da kukan
Rayuwar gidan ya canja musu gidan ya koma tamkar ba kowa Sai masu zuwa gaisu da zaran bakin suntafi kuma to shike nan gidan yayi shiru Rayuwar Yusuf ta sauya ta koma abin tausayi baya mgn da kowa komai za acemai da kai ko ido yake bada amasa duk masifar Na ta Yusuf da bala,I da mishkilanci yanxu babu su Ya koma abin tausayi Baya iya mgn 5 lafiyeyyu Komai ya rigada ya gama sauyawa Aysha kam ko yaushe Sai ta shiga toilet tayi ta kukanta Sai fuska ta kumbura Maryam Kuma yanxu bata iya kukan ya rigada zuciyata ta bushe
Yau ne akayi sadakan 7 gaba daya baqi sun waste su Bappa Yaya ne kadai suka rege basu tafi ba
Yau kwana 10 da rasuwar Kuma yaune su Bappa Yaya ya zasu koma Shiyasa da safe ya Tara zuriyar tasa Bayan ya gama musu nasiha Ya kalli Yusuf da Adam yace Dudabe Na,am ya amsa cikin sanyi Ido ya zuba mai cikin tausayawa yace Yanxu me kakeyi a qasarnan ? Kai ya sunkuyar gami da cije lips enshi yace me zanyi Kuma a qasarnan bani da abin da zanyi Toh ka shirya kaida matarka Ku koma kaje kaci gaba da kara tunka Aysha dake takure a jikin Nenne Cikin kuka tace Dan Allah Bappa Yaya Ku barni ni bana son komawa can To me zaki zauna kiyi a nandin ?
Ni dai banson komawa canne Ta bashi amsa Cikin kuka Shi dai Yusuf shiru yayi Dan yanxu qoqolwarsa bata fiye gane me ake yiba
Haka kuwa akayi randa akayi kwana 15 da rasuwar a ranar baba bello ya kamma lawa su Yusuf shirin tafiyar su A Kuma ranar ✈ jirginsu zai tashi
A hankali suke fitowa daga parlon suna zuwa harabar gidan Bayan su Rabi,u sun gama Sa musu kayansu a but
Cikin sanyi Yusuf yaje ya durqusa gaban baba bello murya Na rawa yace baba zan tafi Kanshi ya dafe Cikin qarfafa mai guiwa yace Allah ya kaiku lfy Yusuf amin yace Gami da miqewa yaje gaban Nenne itama ta mai addu,a A hankali ya qarisa gaban umminshi Ya durqusa guiwa bibbiyu yace Ummi zan tafi Amman bazan sake zuwa qasarnan da wuriba
Cikin ajiyar hrt Ta kamo shi ta tsaida shi A hankali taja hannu Aysha ta samai Cikin nasa tace to ga amanar da Dan uwanka ya baka Yana Cikin qabarinshi mu kuwa mune masu ganin irin yadda zaka riqe amanar da ya baka a dai dai lkcin da ransa yake fita a jikin shi
Hannu yasa ya kamo Na Ayshan ya juya Cikin Rashin sanin me zaiyi Ya jata Suka qarisa gaban Adam ya ruggume juna sukayi musabaha Ya kalleshi Cikin sanyi yace biyaye Allah ta sadamu kan alkhairi Amin yace dai 2 lkcin da suka shiga mota
Usmanne da Rabi,u suka kaisu airport
3:37 pm jirginsu ya tashi
By garkuwan Fulani [4/9, 2:25 PM] +234 909 785 3276: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
NAYI NADAMA 👇🏻👇🏻👇🏻 MI,WASMITI page 7⃣4⃣to7⃣5⃣ Na Aysha s Garkuwa 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Allah sarki rayuwa mai juyawa A cikin jirgi Yusuf ya zauna kan kuje rarsa ta number 24 yayinda Aysha Kuma nata number 23 ne Nata kujerar itace kusa da window jirgin A hankali Yusuf yake takawa har ya isa wurin zaman nasu Jiki a sanyaye ya zauna Gamida yin taqumi da hannushi daya ya Sada kanshi qasa Bai tuno komai Sai ran da suka dawo India a lokcin da suka kamma la kara tunsu A wannan jirgin suka dawo a wadannan kujerun suka zauna inda ya ke zaune anan ya zauna a wancan lkcin Na gefenshi Kuma biyayenshi ne A hankali ya zubawa sit din ido Zuciyarsa Na suya Sai cije lebenshi yakeyi sabida kuka yake son yi Amman kuma ya kasa samun kukan
Yana Cikin wannan halin Yaji abi Na diga kan wuyanshi Hannushi yasa ya shafo wurin kamar ruwa yaji Kai ya dago ya zubawa Aysha dake tsaye a gefenshi dafe da kan kuje ranshi Hawaye wannan Na koran wancan Kallonta yayi Cikin shawa,a A ranshi yake cewa Kinji dadi da kika samu kina kuka kina zubda qollah😭 nasan koba komai zakiji sauqi a ranki
Sanarwan da akeyi Na koma ya koma gun zamansa jirgi zai tashi shine ya dawo dashi daga tunanin da yakeyi Ido ya sake zuba mata A hankali ya daqo Hannushi ya kamo nata Ya jawota Gami da Dan Jan qafafunshi Dan ta samu gun wucewa Kan sit din gefenshi ya yaja hannuta ya zaunar da ita
Ita kam Aysha ido cike da qollah😭 ta bi fuskar shi da kallo Lkci guda Kuma ta tuno Lkcin da zasu tafi wancan karon Da ta tsaya a kanshi haka tana kuka Cikin masifa ya rinqa surface mata bala,I harda yarfa mata mari yana mayya kawai kin wani tasa mutane a gaba kina kuka toh kanki zakici ai tunda kikayi kuskuren yadda kika biyoni toh wlh baqin jaki Sai ya fiki jin dadi Cikin tsawa ya jawota ya tura a wancan lkcin
Tana Cikin tunanin taji jishi Cikin wani irin voice yace Kija bel dinnan ki saka Kai ta sunkuyar Cikin zubar qollah😭 A hankali Jirgin ya rinqa Qugi da Dan diri Cikin tafiya a hankali ya rinqa Dan tashi sama A hankali Yusuf ya maida kanshi jikin sit din ya lumshe idansa jikin jin wani irin azaba a karo Na forko da yaji yana qaunar barin qasarsa ta aihuwa A karo Na forko da yaji ya qagu ya daina shaqar iskar qasar A ranshi yakeji to me y rege masa a qasar nan Babu ya fada a bayyane Gami da bude idanshi da jin zafi a ransa Ita kam Aysha ta window take yiwa qasar ta wani irin kallo da jirgin ya gama tashi sama Ta kifa kanta jikin window ta saki kuka mai ban tausayi
Ido ya zuba mata gami da jinjina kai A ranshi Kuma cewa yayi kuka ma Rahama ne bazan hanaki ba
A haka Cikin kukan bacci ya debeta Yayinda shi Kuma Sai ajiyar hrt da yake tayi 9:00 Am agogon Nigeria Dai2 da 11:00Am saudiya
Jirginsu ✈yayi landing Cikin birnin Madina A hankali fasinjoji suka rinqa fita Ido Yusuf ya rufe a sannu Kuma ya budesu Kan fuskar amanar Ahmad dinshi Cikin sanyin murya yace Ke Ke tashi mun iso Kamar a mafarki taji muryar shi
Sai kuma taji tsoro Dan tuna wancan Zuwan nasu inda ya rinqa zuba mata mari Cikin fushi yace ko ki taso ko Na tafi Na barki Bira alaqaqai kawai Banza mayya..a wancan lkcin
A hankali ya katse mata tunani da takeyi Muryar shi ta kumaji Cikin Dan kauri yace Ke INA mgn kinyi shiru A hankali ta miqe Tabi bayan shi Har inda aka ta naji motici Dan ma tafiya wani ma aikaci Na biye dasu riqe da jakarsu Har zuwa gun motar Suka shiga suka tafi
A dai dai harabar wani qaton gida mai kama da ma aikata part part sun kusa 7
Abakin qofar su direban ya tsaya dai2 bakin qofar shiga Suna fita Yaja motarsa ya tafi Jakar ta ya zubawa ido Cikin ranshi yasan bazata iya dagawa ba Amman kuma shima ga nashi Sai kuma ya kalli inda take ta tsaya Sai rawan sanyi take Dan daga dukkan alamu anyi ruwan samane ya dauke Sai walqiya akeyi da iska mai sanyi da take kadawa Hannu yasa ya dauki jakar tata yasa qafa ya tura mata nasa
Ya juya yayi gaba a hankali tabi bayan shi
A parlo ya ajiye mata nata ya karbi tasa ya juya yabi Cikin Dan koridon da zai Sa dashi da parlon shi Yana shiga ya fada kan 3 str Cikin Yanayin shi da yafi kama da maraya Ido ya lumshe ba tare da yayi bacci ba zafi yakeji sasoi a rayuwarsa A hankali ya daqo phone dinshi Nenne ya kira Tana dagawa tace Yusuf kun isako ? ehh yace mata Gamida cewa ki gaida baba Sai da safe Toh Allah ya bamu alkhairi tace dashi gamida katse woyar Shi kuwa a nashi gefen kashe phone din nashi yayi gaba daya
Ita kuwa Aysha da qyer taja jikinta ta tafi bedroom dinta Kan gado ta fada Cikin kuka a haka a ranan ta kwana kuka Shi kuwa Yusuf kukan ya nema ya rasa shiya sa ya tashi Cikin rawan jiki yaje yayi alwala yazo ya rinqa nafilfili Idan yayi sujjada ba abin da yakeyi Sai nemawa Dan uwan shi gafara
Washe gari da safe Abokan Yusuf laraba suka rinqa zuwa mai taziya da dama daga cikinsa sun San Ahmad Wasu sunsu Kuma insun zo kuka sukayi kamar zasu suma
Akwai wasu abo kansu su 2 Sulaiman da Bashir Wanda tare sukayi karatu a inda Kuma suma yanxu suna Jami,atul madinan ne suna kara ilimi Bashir Dan Katsina ne Kuma tare da matarsa sukazo Mai suna Zakiya Tunda sukazo Sulaiman yake kuka kamar mace dan shi ya shaqu da Ahmad sosai kusan halin su iri daya Bashirne ya rinqa Dan bashi baki yayinda dashi ma yake ta sharar qollah😭 Shi kam Yusuf Sai cije lebe da yakeyi Cikin daburcewar murya yace Zakiya ki isa gun qaunar Ahmad tana ciki Ku gaisa Toh tace mai gami da miqewa Tayi candin A hankali tayi SLM Cikin parlon ba kowa Ido ta Dan bude Cikin zubar hawaye tana kallon parlon a shirya yake tsafta ba datti ko kadan komai Na parlon farine da jaa gashi labulayen suna sasake shiyasa Sai parlon yayi dubu kamar dare SLM ta kumayi gamida zuwa jikin gini ta kunna wutan tsakiyar parlon Ba kowa har ta juya zata fita Sai kuma taji sautin kukan a cin bedroom din Juyawa tayi ta shiga dakin Kan gado ta hangota tayi rufa da ciki Sai kuka takeyi tana Ayyah ya Ahmad yanxu mun rabu kenan bazan Kuma ganin ka ba Zuwa tayi ta zauna gefen ta Cikin sanyin murya Da qoqarin danne nata kukan tace Kiyi haquri Aysha ki daina bin Dan uwanka da kuka kiyi ta masa addu ,a shi yafi buqata a gareku ba hawayen ki ba Dagowa tayi tana kallonta Cikin rashin Sani Fahimtar hakan da Zakiya tayi shiyasa ta kamo hannuta Tace Ni suna Zakiya ni matar abokin Yusuf ne sunan mijinta Bashir Muma muna qasar nan Kuma tare muke da mijina yana can gun Yusuf dinne .
Allah sarki Aysha rashin Dan uwa shiyasa a take taji zaki tamkar Maryam da Amira Cikin hawayen tace kinsan ya Ahmad dinako ? Eh Na sanshi Aysha ! Ayyah to shinefa ya rasu. ehh Na Sani Aysha Kibar kukan Dan Allah Wlh nima zaki Sani kuka Kai ta jinji na gami da share hawayen ta tace Ni ma banson yi mishi kukan kasawa nake in banyi kukan ba ji nake kamar zan mutu Cikin tausa yawa tace ki rinqa addu,a kinji ko Aysha Toh tace Cikin goge qollah😭 Haka dai Zakiya tayi ta lallashinta Har ta samu ta jawota suka shiga kitchen Suka danti girki mai Dan sauki Dan dama ba abin da babu a cikin kitchen din Ita ta dauka ta kaiwa su Yusuf T juya zata tafi Bashir yace in kin gama kizo mu tafi Toh tace Cikin sanyi Dan tanajin tausayin yadda Yusuf da Aysha zasu kasance su kadai
A Parlon ta zuba abinci ta matso ayshi cin lallashi tace Ayyah Aysha ki matso kici abinci kinji ko Kai ta girgiza tace bazan iyaba bakina daci nakeji Ta Dan sunkuyar d kai tace Aysha bakya son nazo gobe ko ? Da sauri tace a a wlh inaso To kici abinci Ayyah Zakiya nima ina son ci bazan iya bane shi yasa Miqewa tayi gamida yin Cikin kitchen din furts ta dauko ta kawo mata tace gashi ki daure kici koda inabinnan da Dan dabino ga Apple Karba tayi ta danci Sannan sukayi sallan insha
A parlon Yusuf Kuma shi da sulamai sun kasa cinnkomai shima Bashir sai dan tea ya Dan Sha
Bashir dinne ya miqe gami da kallon Yusuf Cikin sanyi yace Yusuf zamu tafi Sai gobe in Allah ya kaimu insha Allah zamuzo Amman dan Allah Yusuf ka rinqa Sa dauriya a ranka Yusuf ka rege tunani Dan Allah kar ya maka illa Kasan kana da matsalan zuciya Kai ya sunkuyar Cikin ceje lips dinshi da gaba daya yanxu sun kubbura sunyi jazur sabida rashin kukan da bai samu yayinba Sai yayi ta cizon lips din nashi Haka dai Bashir ya rinqa bashi baki Sannan suka wuce parlon Aysha
Sulaiman kam yana ganin ta Sai hawaye Dan shi yasan irin son da Ahmad yake mata Kuma itama tasan Sulaimanu Durqusawa tayi a gabanshi tana zubda qollah😭 Cikin rawan murya yace Sannu Aysha sannu da rashi Allah ya jiqanshi da Rahama
Amin ya rabbi ta fada Cikin kuka shima Bashir ya gaida ta sannan suka fita suka tafi
Shi kam Yusuf parlon shi ya koma Cikin kuncin zuciya Yadda ya kwana jiya hakama ya kwana yau Washe gari da safe Bashir da Sulaiman sukazo Zakiya kuwa sai da ta tsaya tayi musu girki sannan ta taho Daga ranan haka sukayi tayi Sai randa suka cika kwana 7 da dawowa sannan suka daina zuwa Su wuni Sai dai duk da haka kullum zakiya ke musu girki ta bawa Bashir ya kawo musu duk da baci sukayi ba yadda Bashir ke kawo shi haka yake zuwa ya dau keshi
Sannu a hankali yau watansu daya da dawowa Rayuwa ta juya ta canxa Yusuf Dan qolisan nan gaba daya ya zama abin tausayi banda wonka ba abinda yakeyi ko mai bai shafawa A hankali Dan sirinrin sajenshi Na ya rinqa qaruwa yana yawa yana bajewa ga wani irin rama da yayi duk ya canxa sai dai kyau kam kamar qara mai akeyi kullum da safe yana dawowa masallaci Sai ya leqa gun Aysha a cewarsa amanarsa CE ita Duk da ita kam bata ganin shi
Wata ranar jummah da daddare misalin qarfe 2 Na dare Aysha dake parlo Wanda a yanxu parlon ya zama dakin kwananta Dan Da zaran tayi bacci a bedroom sai mafarkin ya Ahmad dinta ke bibiyarta Shiyasa ta dawo parlon Inda zata kwana kuka yayinda zata kwana jin sautin karatun Yusuf Kuma a parlon shi Sai dai abin tsoro da firgici jin a yau ba sautin karatun Yusuf din take jiba Cikin firgita ta tashi da sauri ta nufi parlon bashi..... Tsoron ta ya qaru ganin abinda Yusuf din keyi ta kidime ta rude ta kidime da sauri tayi kanshi..........
I love you all my frns😘😍😘 Allah ya barmu tare
By garkuwan Fulani [4/9, 2:25 PM] +234 909 785 3276: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 NAYI NADAMA 👇🏻👇🏻👇🏻 MI,WASMITI page 7⃣6⃣to7⃣7⃣ Na Aysha Ali Garkuwa 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Kina raina Asma,u Adam admin din zauren guzurin gobe alqiyama😘😍 I love you all my frns😘😍
Kuka yakeyi cikin fitar hankali kuka mai ban tausayi gaba daya ya fita hayyacinsa Jikinsa kab zuface ke tsatsafo mai tako ina Ya zaune kan sallayah runqqume da qur,ani mai girma a jikinsa ga qaton photo su su 4 Shi da Ahmad din da Adam da Abubakar Hannushi yasa ya dafe kanshi da hannu bibbiyu Cikin kuka Da ya samu rabbi ya sauqo mai dashi a yau Cikin dashewar murya yaketa nanata wayyo Allah Na Wayyo Allah Ya rabbi ka bani ikon cin jarra bawar da ka jarab ceni da ita ya ubangiji kayiwa bawan ka Ahmad Rahama rabbi ka haskaka mai qabarinshi Kanshi ya dafe da hannushi daya gaba daya jijiyoyin kan nashi sunyi rudu rudu Hannushi daya Kuma qirjinshi ya dafe da qarfi Gaba daya jikin shi rawa yakeyi Sai zamewa yakeyi a kan carpet din Cikin wahala ya rinqa kiran Ahmad shi kenan mun rabu Ayyah biyayena Bani da wani masoyi kamar ka bani da mai gayamin gsky kamar ka bani da Wanda nakeji a jikina kamar ka Kaine maisani farin ciki