Kenza eBookz

Nida malamata complete - Chapter 2

Nida malamata complete - Chapter 2

Nida malamata complete Chapter 2: Nida malamata complete Chapter 2. Tsayawa chikk tayi bata kuma juyo ba,ganin bata da alamar juyowa yasa ya ƙara faɗin…

4,492 words

Tsayawa chikk tayi bata kuma juyo ba,ganin bata da alamar juyowa yasa ya ƙara faɗin "Wai ke wacce irin yarinya ce kina ganin mutane ba zaki iya gaida su ba,kuma dan rashin tarbiyya ko sallama baki yi ba"

Yadda taji maganar yasa ta tabbatar da Naufal ne dan iyayin da taji yana yi,ɓacin ran da take ciki ya hana da yin dariya.

Juyowa tayi Zaune ya ke akan one siter ta ganshi yasha baƙin glass fuskar nan a dagule kamar wande ke zaune a cikin bola.

Kamar zata ce mishi wani abu ta fasa,tai wucewar ta zama da sauri.

"Ɗuk ɗady ne zai ja min raini kamar ni za'a ce na zo har gurinta"

Cikin ɓarin rai yayi maganar wanda ɓacin rai har ya samu gurin zama a fuskarshi shiyasa ɓacin rai ke mishi kyau,tashi yayi yabar gidan gaba ɗaya.

Tana isa ɗakinta ta shige toilet ta daɗe tana watsa ma jikinta ruwan sanyi.

"Ba abinda na ya taɓa min rai ban rama ba,karki yi tunanin zan gyale ki dan kin kai ne ƙarshe zan miki abinda sai kin zubur da ƙwalla da idanuwan ki,kuma sai kin ce na haifu ni sabreen muh'd mai taƙama,bana ɗaukar bashi" wasu zafafan hawaye suka biyo kyakykyawar fuskarta.

Tana cikin yin Sallah hajia ta shigo ɗakin ,zama tayi har ta idar.

"Ƴar aljanna lafiya ki kuwa ,ki faɗamin abinda ke damunki zan miki maganin shi komeye shi"

Sabreen bata iya ɓoye ɓacin ranta ba shiyasa hajia ke ganewa.

Kan jikin hajiar ta dawo ta kwantar da kanta,ta ƙaƙalo murmushi ta ce "ba komai hajia ta kin san ina gaya miki abunda ke damu na,karki damu ba komai"

"Taya ba zan damu ba,dumwarki damuwa take sa ni "

"hajia zan sha ice-cream muje ki sai min"

"Ice cream to yar aljanna muje direba ya kai mu ko"

Tai saurin katsi ta" a'a Yaya Naufal nake son ya kai mu"

Hmm baka san waye Sabreen ba da zaka min tsawa ni nace ka zo gidan mu ko da zaka sauke fushin ka a kai na ,a zuciyarta ta ke wanan tunanin haɗe da yin murmushin mugunta.

Cikin sigar rarrashi hajiar ta ce "Naufal to shi zai kai mu,karki damu je ki shirya,wai ba alhaji ya ce yazo yau ya miki karatu ba"

taɓe baki tayi "hm ai dan raini ne ba zuwa zai yiba"

"Bari zan haɗa shi da dady "

Murmushi tayi na jin daɗi ta ce " to ki kira shi bari na chanja kaya" tana faɗa ta tashi ta nufa gurin kayanta ,ita kuma hajia ta fita falo.

Cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga ta shirya ,rigar ta matuƙar yi mata kyau kuma ta kama jikinta wanda yasa dukkan shape ɗin ta ya baiya na,pich colour ne rigar da ratsin baki,bata ɗaura ɗangwalin ba ɗan karamin gyalen kayan ta yashi a kanta,kana iya hango baƙin gashinta mai santsi,duk da tana da ɗan tsawonta amma tana son dugon takalmi,shi kuwa ta sa ɓaki mai ɗan karen kyau,bata yi wata kwalliya mai yawa ba,huta sai kwalli da pink ɗin jan baki wanda yai ma ƙaramin bakin ta kyau.

Cikin yanga da ƙasaita take saukowa daga matattakalar.

Hango shi tayi a zaune cikin ɓarin rai duk da ɓarin ya saba zama a fuskarshi ,amma yanzu kam kana ganin shi kasan ɓacin ran mai tsanani ne,yai hura hanci yake yi yana wani yamutsa fuska.

Cikin fara'a ta isa fallon ,kallon shi tayi tana murmushin mugunta ta ce "Ya Naufal ina wuni ya gida ya aiki?

Ko kallon inda take bai yiba,ya miƙe tsaye "Zamu iya tafi?ya faɗa cikin salo da ƙaƙale.

Kasa ɗaurewa tayi saida dariya a zuciyar ta tana faɗin"Bala'i Wai hausa ma sai an mata ƙaƙele wannan da kai ka kawo yare da ni kuwa bani ba koyan magana"

Hajia ta kalle shi rai a ɓace ta ce"Kai kana jin tana gaida kai wai meyasa kake wa yarinyar nan haka ne"

Taƙaici kamar yayi kuka,gashi yanzu da yayi wani abu zata gayawa dady shi kuma baya son ɓacin ran dadyn shi ko kaɗan.

Wani mummunar kallo ya mata ya ce "Me kika ce Sabreen maimaita ban ji ba"

Saida da lumshe idon daya kira sunanta ji tayi kamar ba wanda ya taɓa kiran sunan da daɗi,sabo sunan ya dawo mata,ydda ya kira har zuciyarta saida ta ji shi,amma saboda hali irin da Sabreen cewa tayi haɗe da taɓe fuska"Salo sunan ma da turanci za'a faɗa kai dai abunka yayi yawa"

A zuciyarta tayi wanan mgnr amma a fili cewa tayi" Cewa nayi ina son ganin gari,zaka kai ni duk inda ka sani"

Bai san lokacin da wani tsadaddan murmushi ya fito ba saida jin haƙurin shi a waje iskar falon ta duke su.

Ba komai ne ya haifar mishi da wanan tunann ba sai jin mamakin sabreen da ƙarfin hali,ita gani take ita me wayau ce.

"Laaah ashe ya iya murmushi to ko me yasa yayi ? ohhhon mishi .

Ta tambayi kanta sanan ta ba kanta amsa.

Har ya bar falon ,binshi a baya suka yi ,yayi tunanin a gaba zata zauna sai ya ga kuma ta zauna a baya.

Sai zubawa hajia shagwaɓa take yi da biyu ganin yana ɗan gutun tsaki yasa ta ƙara yinta da salo ma.

"Kun lalata yarinya,kun koya mata fitsara" a zuciyarshi yake wanan maganar.

ostrich bakery wanda ke unguwar sarki ya fara kai su,kaya mai yawan gaske ta zaba duk da biyu tayi hakan dan hajia ta saka Naufal ya ɗauka.

"Washh hajiata ba zan iya kai kayan na n gurin motor ba"

"To daman ai ba ke zaki ɗauka ba Naufal zai ɗauka"

Juyowa yayi ya kalle hajiar.

"Ko ba zaka ɗauka ba ne"

kasa magana yayi dan ɓacin rai bai iya cewa komai ba ya ɗau kayan,har yayi dan nisa Sabreen ta kira shi "Ƴaya tsaya na duba wani abu"

Tsayawa yayi yana mata wani irin mugun kallo ,wani murmushi yayi na mugunta dan ya ga yadda zai mata ,ruwan da ke hannun shi ya kalla,a hankali da dubara ya buɗe ruwan yayi kamar zai sha ya zubar a ƙasan gurin.

Allah sarki Sabreen bata sani ba,kuma dai ita ma bata san ba ko wacce fansa ake ɗauka ba.

Cikin yanga ta tawo habba sai jinta tayi dimmm ta zame ta faɗi har saida ƙafarta tayi ƙara.

"Waiyooo Allah na hajia ta ,ta sake ihuu da karfi.

Da gudu a ruɗe hajiar ta ƙaraso gurinta "Na shigo ukku ƴar aljanna me ya same ki ,gaba ɗaya hajia ta ruɗe .

Ko mutsi daga inda yake bai yiba,kallon su kawai yake yi yana murmushin mugunta.

Sabreen ga raki kasa tashi tayi ita kuwa hajia ta ƙara ruɗewa.

chin chiɓar ta aka yi har cikin motar,shi kuwa ko gyalenta bai taɓa ba,gashin kanta ya mishi kyau bai taɓa tunanin a 9j xa'a samu me kyaun gashi ba.

Motar shi ma ya shiga ya fara tafiya a hankali yake jan motar yana jinta tana raki,murmushi kawai yake yi.

"Yanzu ina zamu? ya faɗa hankali kwance.

Cikin faɗa hajia ta ce "wacee irin magana ce haka,gana ganin halin da muke ciki"

"hajia daman naji ta ce wai tana son na kaita duk inda na sani ne"

"Toh a hakan"

ta juyo da kallon ta gurin sabreen ɗin "Sannu kinji ko muje asibiti ne?

Da sauri ta ce "A'a muje gida ki shafa min magana "

"to yadda kika ce ƴar aljanna"

Wanan karan har saida haƙuranci suka baiyana "Wai ƴar aljanna"

Gida ya maida su ,amma bai shigaba a harabar gidan ya tsaya suka sauka yai wucewar shi.

Ranar a ɗakin ta hajia ta kwana.

~~~~~~~~~~~~~

Ƙiran sallar farko hajia ta farka,ɗakinta ta koma.

Sai shidda saura Sabreen ta farka tana farka ta ma manta da tana da ciwo a kafa saida taji zafi,amma haka nan ta ɗaure tayi sallah,ko kaɗan sabreen bata wasa da ibada.

Bayan ta idar ta sallar wata dubara ta faɗo mata,da sauri ta tashi ta hau shirin makaranta,Cikin kankanin lokaci ta gama shiryawa,ƙafar tana mata mugun ciwo amma haka nan ta ɗaure ta sauko ƙasa.

Ɗakin hajia ta nufa tana kiranta"Hajiata! hajiata?

Da sauri hajiar ta durgo daga saman gadon ta "Ƴar aljanna lafiya ƙafar ce.. ganinta da kayan makaranta yasa ta ƙasa maganar.

Murmushi Sabreen tayi dan tasan kallon da hajiar ke mata,mugun ƙarfin hali tayi ta ƙara gurin hajiar cikin tafiya mai kyau ta ce "Kin gani ko hajia naji sauƙi sosai yau ina da test ne shi yasa zanje da ba inda zani"

Cikin wata irin siga hajiar ta ce"Sabreen kiyi hakuri karki je"

Murmushi Sabreen ɗin tayi ta ce "Hajiata wai baki yarda da ni ba ne,baki ga yadda nayi tafiya ba ne,naji sauki sosai zamu yi test ne shiyasa" Tana ƙarasa maganar ta isa gurin hajiar kwanciya tayi akan ta.

"To Sabreen duk abinda kike so shi zanyi ,dan bana son ɓacin ranki ko ƙaɗan"

Wani lafiyayayyan murmushi Sabreen ɗin tayi ta ce"Hajiata ina sonki !

"ni ma ina sonki Savreen ki kula sosai kinji bana son wani abu ya same ki"

"to hajita zan kula sosai,bari na tafi kar tana yi latti,byee sai na dawo,tana gama faɗa ta tashi.

Hajiyar ta ce "ba zaki bari na raka ki ba "

"Eh ki huta abinki lokacin har ta bar ɗakin.

Gaisawa da direban suka yi sanan ta shiga motar,a tsorace yake dan jiya yasan planing ɗin su bai yiba,kuma yasan Sabreen bata yafiya ba hakura zata yiba taurin kai gareta.

Jin bata ce mishi komai ba har suka isa makarantar ya bashi mamaki tunani ya farayi wani irin hukunci zata ɗauka kuma.

Ba mutane a makarantar sosai.

office ɗin malama haulat ta nufa kai tsaye ta shiga.

Zaune take akan kujerarta tana duba wasu litattafai cikin wani tsadaddan material wanda yai matukar yi mata kyau,fuskar nan a yamutse kamar kullum.

Saida ta tsorata jin an buɗe kofa ba'a ƙwanƙwasa ba.

Cikin ɓacin rai ta kalli Sabreen"Ke wacce irin dabbace jahila mara hankali"

Har Sabreen ɗin zatai magana ta fasa ko meye ta tuno? ohoo.

Takai tsawon minti talatin a tsaye a gurin ,ita kuma malama haulat ganin bata da niyyar magana yasa ta fita lamarinta ta cigaba da abinda take yi.

Ganin mutane sun fara yin yawa yasa Sabreen ta kalli Malama Haulat ɗin cikin ɓacin rai ta ce"Ke wawiya karki ƙara kira na da waɗan nan sunayen"

"Ɗago kai Haulat tayi cikin mamaki tsaye ta tashi tana kallon Sabreen ɗin.

Ganin ta tunzura yasa Sabreen ɗin kara faɗin "ni ba wawiya bace ke ce wawiya kuma dabba jahila"

Ran Haulat ɗin yai mugun baci,bulalar take kan tebur ɗin ta ɗauko,ta zubawa Sabreen a jiki.

Haba ai abin naima ya samu ai da Sabreen ta sake wani irin gigitaccen ƙara ta zube ƙasa tana ihuun gaske tana birgema a kasa haɗe ta faɗin " waiyo Allah na zata kashe ni ƙafata ciki na waiyo kaina kai na nashi ukkku hajiata ku taimake ni zata kashe ni!!!

Dan tsabar mamaki Malama haulat tsayawa ma tayi tana kallon ta jikin ta duk ya mutu.

gafin ka ce me office ɗin ya cika da mutane Sabreen tana ganin haka ta fara nishi tana ɗauke numfashi ai sai suka ƙara ruɗewa ga malama Haulat tsaye da bulala a hannunta.

A ruɗe aka ɗauke Sabreen wani ɗaki aka kaita ita kuwa sai ɗauke numfashi take yi tana kiran hajia.

Ganin za'a mata allura ai sai ta fashe da kuka tana faɗin" waiyo ƙafata ku kaini gurin hajiata ƙafa ta ta ƙaryamin ƙafa"

da sauri ya duka ƙarfa ya ganta taji ji kuma ta kumbura duk da ba wani haske gareta ba amma ƙafar tayi ja.

Gaba ɗayan malaman makarantar sun ruɗe suna tsoron kai wani abu ya faru da Sabreen ɗin.

Allura ya mata tana ihuu tana kuka dan bata son allura amma haka nan suka mata cikin ƙamƙanin lokaci barci ya ɗauke ta.

~~~~~~~~~~~~~

Ranshi a ɓace ya kalli haulat wacce ita ma ranta a ɓacen yake ya ce mata"yanzu me kika aikata kina son ki ja mana wani abu ne a makaranta dan baki san waye wanda ke ɗaukan nauyinta ba ne,duk abinda ta miki ba zaki iya kawo kararta ba,zaki yi mata irin wanan dukan yanzu ga shi ta samu matsala a ƙafa,ni wllh yanzu ban san yadda zanyi ba,ansa ya miƙa mata wata takarda.

gabanta yai mummunan faɗuwa kallon takardar ta tsaya yi.

"Ki ansa nace" ya faɗa cikin faɗa.

jiki na rawa tasa hannu ta ƙarɓa.

"mun takatar dake na sati biyu"

Dumm Dumm gaban haulat ya fara faɗuwa da ƙarfin haske haɗe da zaro ido tana kallonshi.

"Tashi ki fita ya faɗa rai ɓace"

jiki ba ƙwari ta tashi...

..........................................

tirkashi!!!!

gaskiya ni comment na ke so,bana son wani tnx ko wata heart haba ga tawa ga taku ai sai tamin yawa.

ku ƙara gyara zama dn zanyu zan fara. . [12/9, 1:07 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/9, 1:10 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹

*By* *fatima* *Batula*

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

Page 4 ...................................................

Fita tayi daga cikin ajin ranta a ɓace,ita kuwa ko a jikin ta daman hakan take so ,tana jin zafin maganganun da Aunty ke gaya mata,shiyasa ta ke son ganin ɓacin ranta.

" *Sabreen* *Muhammad* *mai* *taƙama*" Da ƙarfi ya kira sunan cikin faɗa.

"Kina ina?yana maganar yana kallon ƴan class ɗin.

Gaba daya ajin yayi shiru kamar ba halitta a ciki dan ko numfashi a hankali suke yi dan tsabar tsoron wanda ya shigo ajin.

Cikin nuna ko a jiki na ta tashi daga gurin da take zaune ,hankali kwance ta nufi inda suke,kallon Aunty ta fara yi wacce tare suka shigo class ɗin da shi.

Saida ta matsu kusa da shi sosai sannan ta tsaya ,ta kuma zuba mishi manyan idanuwanta wanda ba alamar tsoro a tare da su.

"Me kika cewa Malama *Haulat* *Hashim* *Kabir* ?eyeeh ba dake nake ba,kin kafe ni da ido"

Saida ta kalle malama Haulat ɗin sanan ta dawo da kallonta gare shi "Ce mata na yi ni bana jin turancin ƴan chaina,tamin na ƴan nigeria"

Shi kanshi bai san lokacin da dariya ta suɓuce mishi ba,dan duk makarantar kowa yasan iyayenta gurin turanci amma ba wanda ya taɓa mata magana sai Sabreen.

Ganin shi ma ya fara dariya abin ya ɓata mata matuƙa ga yan ajin suna dariya,a fusace tabar class ɗin,tsanar sabreen kuma da niyyar ɗaukar fansa.

Ganin ta fita yasa shi ma yai sauri yabar ajin.

wani annuri ya baiya na a fuskar sabreen dan jin daɗin yadda ta ga ranta a ɓace,komawa tayi ta zauna amma duk ji take yi bata rama hulaƙancin da malama haulat ɗin ke mata.

Zaune take ita kaɗai a staff room tana tunanin wani irin abu zata ma Sabreen ta huce,murmushi naga tayi wanda ya ƙara baiyana kyawun ramammiyar fuskarta,wato abinda zata ma Sabreen tayi shi yasa ta yin murmushi.

Ƙarfe ukku daidai aka buga ƙararrawar tashi,koya hankalin shi ya koma gidan, gaba ɗaya malamai da ɗalibai sun fito kuwa ya nufi hanyar gurin ajiyar motoci.

Har aka gama zuwa ɗaukan dalibai Sabreen tana zaune ita kadai ,ranta ya ɓace sai huci take yi,tana turo baki,tashi tayi zata fita bakin get.

Da mugun gudu motar malama Haulat ta zo wuce wa,ta gabanta kamar zata ɗauke ta,da sauri a ruɗe sabreen ta matsa har saida ta faɗi kasa,wani irin ƙululon takaici ya kamata,da zafin nama ta tashi ta nufu motar.

Tana ganin ta nufota ,ta fito daga motar tana wani yamutsa fuska kamar wacce tai arba da kashi

" U are very no what u are,okkk i forget u are illiterate ,baki da gwagwalwa ne ko a garin mahaukata aka daukoki da kina ganin mota ba zaki iya kaushewa ba"

Tunda ta fara magana Sabreen ki binta da idanuwa wadanda sukai jajiir dan tsabar takaici.

Ita kuwa malama Haulat ganin ta cinma burinta yasa ta wuce ta barta anan tsaye, ta kuma ja motar da karfi har saida ta watsa mata kura.

Wani lafiyayyan hawaye ya fara bin fuskar Sabreen wanda ita kanta bata san da zuwan su ba, sai jin su tayi a fili ta ce tana huce kamar wacce tai faɗa da zaki "Hmm baki san waye Sabreen Muhammad mai taƙama ƴar Aljanna ba ne,bana yafiya kuma bana biyar bashi zan rama ramuwar gaiyya"

Tana faɗa ta sa hannuwanta ta fara goge hawaye tana faɗin "Hm kika sa ƴar aljanna hawaye zai kin biyasu"

"To yah zanyi idan na gayawa hajiya ,A'a ba zan gayawa hajiya ba,ni da kai na zan ji da ita "

Ita fitowa bakin get ɗin direban ta ya zo ,bata ce mishi komai ba ta buɗe motar ta shiga.

"ƴar aljanna kiyi hakuri wallahi faci tayar motar tayi,jikin shi har rawa yake yi dan tsoron karta gayawa Hajiya"

Banza tayi da kamar bata san da wani a cikin motar ba.

Sai magiya yake mata akan karta gayawa hajiya.

"To naji amma zai kamin abu ɗaya ta faɗa tana kallon shi

"to zanyi ƴar aljanna koma meye zanyi"

Murmushin mugunta tayi da jin daɗi ,harda sauke ajiyar zuci.

Daidai wani katafaren gidan direban yayi horn aka buɗe mishi,giɗan ya haɗu iya haɗuwa abin sai wanda ya gani,dan tsayawa kwatanta muku sai ya ɗauke ni lokaci mai tsawo.

Tana jin ƙarar motar su,ta fito da sauri har bakin motar ta fito tana wace baki ,ita da buɗe mata kofar hade da faɗin "Ƴar aljanna kin dawo tun ɗazun naji shiru ina ta jira hankali na ya tashi ina fatan dai kina lafiya"

Murmushi tayi sannan ta rungumeta "Kina lafiya hajiyata yau bamu fito da wuri ba ne,wanan ƴar iskar malamar ce ta tsayar da mu"

"Cikin nuna damuwa ta janye jikin ta tace"Wai ko sai na tura anje gurinta ne aja mata kunne,ko na fitar da ke daga makarantar gaba ɗaya ma"

"A'a Hajiya ki barta kinji "

"to ni bansan duk wani mahalukin da zai ɓata miki rai,zan iya yin komai akan farincikin ki"

Daidai da isar su cikin katon falon wanda shi ma ya ƙyyatu har tsoro yaban dan tsabar kyaun shi,ga wani asirtaccen kamshi wanda ya haɗe da AC ɗakin.

Murmushi tayi cikin shagwaba ta ce "Nima na sani hajiyata,amma tunda na ce ki barta kawai ki barta zanyi maganin ta ,zan gwada mata ni ɗin ƴar gata ce"

"Hajiya bari na hau zama nayi wanka sai nayi sallah na huta"

"Yawwa ƴar aljjanna na manta ban gaya miki ba,ɗan india ya dawo an jima sai ki je ku gaisa"

Yamutsa fuska tayi yin sunan wanda ya dawo din"Wanan dan iyayin wanda aka je ɗauko mu tare"

"Eh shi fa"

"Tabbb gaskiya ni ba zani ba saida shi ya zo "ta faɗa tana hada rai

"to shikenan ba zai kin ɓata rai ba,zan sa ya zo da kanshi,kinji hankalinki ya kwanta"

ta washe baki "eh hajiyata,ta haye sama ,a ranta tana faɗin yadda zata ganshi dan tun sanin farkon da ta mishi kafin yaje india dan iyayi da kinibibi ne,to bari yanzu da yaje india.... .....Cikin yanga da ƙasaita take saukowa daga matakalar benan gidan, idan ta ɗaga kafa daya kafin ta ƙara ɗaga ɗayar ta sai ta ɗau saƙonni,duk wanan abun cikin kayan makaranta take yi,sikit ne ɗan ƙarami iya gwuwarta nevy blue sai rigarta fara mai ratsi-ratsin blue ba hijjab a jikin ta sai hular da ke kanta.

Wata kyakykyawar dattijowar matar da ke zaune a cikin tanƙameman falon ta hango yadda take saukowa daga benan murmushi tayi sanan ta ce "ƴar aljanna!! ke kullum sai kinyi latti,kinsan ƙarfe nawa ne yanzu kuwa? cikin tausasawa take mata maganar.

It kuwa wacce aka kira da ƴar aljanna ko a jikinta banda ma ƙara rage saurin da tayi.

Wanan dattijowar bata ƙara ce mata komai ba, binta da kallo da tayi ko kaɗan bata nuna alamun ɓacin rai ko wani abu makamancin haka a fuskarta ba banda ma wani lafiffayan murmushi da take yi .

Ƙamar ta ƙarye dan tsabar yanga,ta iso falon,kan jikin dattijowar ta faɗa ,kanta matar ta taɓa,cikin so na nuna damuwa ta ce "Ƴar aljanna ko ba zaki makarantar ba ne? idan ba zaki ba muje ki cire kayan sai ki gayamin inda kike son zuwa mu je"

Kamar mai tsoron magana ta buɗe bakinta cikin shagaɓa ta ce "Zani *Hajiya* bana son wahala ne gashi wanan ƴar iskar malamar ce maiyar turanci zata fara shiga ajin ,ta kai ƙarshen maganar haɗe da ramutse fuska tana kallon Hajiyar.

"Kam to kina jina,duk abinda aka miki ki kira ni,zasu ga wanda ya tsaya miki,ni da su ne shege ka fasa ɗan halar sai yanka"

Washe ƙaramin bakinta tayi ,tana jin daɗi da alfahari,rungume hajjiyar tayi "Ina sonki hajiyata"

Tana faɗa ta tashi tabar falon cikin jin daɗi.

"Nima ina sonki ƴar aljanna sai kin dawo"

Tun kafin hajiya ta gama maganar ta bar falon.

Ɗaidai waata ƙatowar makaranta wacce kallo daya zaka mata ka fahimce makarantar bata ƴaƴen yara ba ce,ta tsaro da navy blue da farin fanti,yanayin makarantar idan ka gani ka ce ba'a j9 ba ne dan yadda suka tsarata,ƙatowar motar ta tsaya.

horn ɗaya direban yayi aka buɗe ya kunna kai,saida ya isa inda ake faking ɗin motoci sannan ya tsaya,bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta fito.

J S S 3 Aka rubuta a saman ajin,kai tsaye ta kutsa kai ba tsoro ba tantamar komai,kanta a ƙasa.

"Hy how dare u enter me class without any excuse"

Saida nayi da ƙyar sanan naji abinda take faɗi,dan yadda take turanci kamar ba ƴar 9j ba,ko wacce tai karatu a kasar turai.

Ko ƙadan bata ji tsoro ba ta ɗago kai ido biyu suka yi,da wacce tai maganar

Tsaye take a gaban Allon,kyakykyawa ce ajin farko kallo daya zaka mata ka fahimce yadda tsarin halitar jikinta yake,ƴar gajerace ba cancan ba,sirirya ce ga dogon hanci kyakykyawa,bata da wani girman jiki amma kana kallon fuskarta zata san cewa wanan ba yarinya ba ce,dan ta kwana biyu.

Tun a kallo na farko na gane ƴar iyaye ce,dan yadda take yamutsa fuska kamar tana kallon ɗanyen kashi.

Ido cikin ido suke kallon juna,bata ɗauke idanta ba ta fara tafiya.

"Keee wacce irin dabbace mara hankali da wayau kuma jahila" Cikin ɓacin rai da kausassaiyar murya ta faɗa.

Wani irin mugun kallo ta bita da shi mai cike da tsana ,amma sai naga ta sake wani ɗan karamin murmushin keta ta ce "Au sari kinsan bana jin turanci balle irin naki me kama da yaren chaina"

Tana rufe baƙi yan class ɗin suka fashe da dariya wanda daman tunda ta shigo hankalin su ya dawo gareta dan sun san sai anyi drama...

yawan comment yawan typing

. [12/9, 1:10 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/9, 1:11 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹

*By* *fatima* *Batula*

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

Page 5 __________________________.

Sabreen bata daina dariyar ba har saida ta gaji ,ta tsaya dan kanta, ta juyo ta kalleshi ya ɗaure fuska kamar me shirin yin kuka,sai ya ƙara bata dariya ta ƙara fashewa da dariya.

Ya ƙasa tashi ya fita kuma ya ƙasa mata magana kallon ta kawai yake yi,yana murmushi wanda bai san dalilin yin shi ba.

Bayan ta gaji da dariyar ta matso da litattafan gaban shi har ya ɗauka ya buɗe aka kira wayar shi yana ganin kiran na waye yai wani irin murmushi.

Kallon shi Sabreen tayi a zuciyarta ta ce "Ikon allah waye kuma da ake mishi irin wanan murmushin"

Duk yadda Sabreen ta so jin abinda yake faɗi ta ƙasa dan yadda yake maganar ko maciji ba zai ji ba.

Sun daɗe suna wayar har sabreen ta fara gajiya sai wurga mishi harara ta gefen ido take yi.

guntun tsaki taja ta tashi ta haye sama.

Bayan ya gama wayar ya ga ba Sabreen a gurin yamutsa fuskar yayi ya tashi ya wuce abinshi.

~~~~~~~~~~~~~

Yau ma ƙarfe ukku da rabi da dawo daga makaranta,kamar yadda suka saba zama a falo kafin a kira sallah yau ma hakan ne,kiran sallah shi ya tashi su kuwa ya wuce ɗakin shi dan gabatar da ibada.

Bata yi sunanin Ya Naufal zai xo ba,cikin ƙananan kaya da sauko kasa kanta ba ɗan kwalli ,lokacin hajiya ma bata fito ba.

Cikin salo da ƙarya murya yayi sallama ,kasancewar tibin a kashe yake yasa taji sallamar,amsawa tayi ba tare da ta juyo ba.

A yatsine ya shigo ya zamu kujera ya zauna,yana zama kiran Haulat ya shigo.

"Hello ita ta fara faɗa.

"Hi my dear ya kike?

"Lafiya qalau ya su momy,gaskiya yau ina son ganin da wuri jiya kawai amma ji nake kamar na shekara ban ganka ba,kasan irin damuwar da nake shiga kuwa idan ban ganka ba,plsss ka zo kar zuciyata ta fashe"

Murmushi kawai yake,ita ke kira kuma ta fishi yin magana.

"Ok to zan zo karki damu"

Duk wanan maganar da suke yi Sabreen bata jin komai,tana jin ya gama wayar ta juyo ta kalle,bai san lokacin da murmushi ya kuɓuce mishi ba.

Yaƙuna fuska tayi ta ce "Ina wuni tana faɗa bata tsaya jiran amsar shi ba ta tashi ta hau sama"

daman bashi da niyyar amsa mata gaisuwarta.

Da jakar ta fito ,tun daga sama ya hango ta ,da sauri ya sauke kan shi ƙasa,duk sai yaji ya ruɗe kamar wanda bai taɓa ganin macce da irin wanan shigar ba.

Ita kuwa hararar shi ta dinga yi har ta matso kusa da shi ta aje jakar ta zauna,ganin bashi da niyyar cewa wani abu yasa ta ce "Gashi

Ɗagowa yayi fuskar nan a ɗaure tamau ya amsa littafin yana ɓuɗewa kira ya ƙara shigowa wayarshi,ɗaukar wayar yayi yana murmushi ya ce " my dear"

Wanan kalmar kuwa Sabreen tayi sa'ar ji a ranta ta ce "Dear tabb yanzu wanan yana da budurwa ita kuwa wacce iri ce? eh fah saidai irin shi dan idan ba irin shi ba wacce zata iya da shi" har ya kama wayar idonta yana kanshi.

Ƙafin ayi karatun nan kuwa haulat ta kira yafi sau biyar,har Sabreen ta lura da tafi damuwa da shi,dan shi duk da bajin abinda yake cewa take yi ba,tasan ta fishi yin magana dan tana lura da bakin shi.

~~~~~~~~~~~~~

Har sati ya zagayo sun ƙara turuwa a gidan su ɗin.

Sabreen har ta ƙama lura da Haulat tafi son shi,dan kullum a gabanta sai ya ƙira shi a gabanta sama da sau biyar.

Yanzu ya rage bata dariya akan maganar shi,tayi mamaki da ta gane yana jin indian ,gashi tana mugun son yaran indiyanshi.

~~~~~~~~~~~~~

Yau sati ranar monday Haulat zata koma bakin aikinta.

Zaune take akan kujerar dake falon su tana latsa wayarta.

A fili naji ta ce "Hmm Sabreen kin sa an bani suspension ke kuma a makarantar zan saka a kore ki gaba daya baki san hali na ba, da zaki ce zaki ja da ni"

" ke dawa kuma aunty Haulat"

Kallon wacce tayi mata maganar tayi ƙaramar kanwar ta ce sadiya.

Murmushi Haulat ɗin tayi ta ce"Yarinyar da ta ja aka bani suspension"

"allah karki raga mata,ki ci mutuncinta"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull