Nida malamata complete - Chapter 8
Nida malamata complete Chapter 8: Nida malamata complete Chapter 8. "Ba haka ba ne,momy nafi son irin wanan soyayyar da yake min nafi jin daɗin ta,yanzu…
4,480 words
"Ba haka ba ne,momy nafi son irin wanan soyayyar da yake min nafi jin daɗin ta,yanzu kinga indan muka je gurin bokan avin sai koma kamar bin umarni da dole za'ayi mishi akai na,"
"to ita yarinyar fah zata iya raba ki da shi."
"No momy ba zata iya ba,ni yake so ba ita ba,ni ce ra'ayinshi ba abinda zata iya."
"Haulat kenan ina nan zaune zaki zo ki same ni,bari naje mu fara shiri kafin ya iso".
~~~~~~~~~~~~~
"meyesa zan mata haka? akwai haƙƙin ta mai nauyi akai na,ga alƙawarin dadyn ,yanzun idan tayi fushi ta gayawa hajia fa,ita kuma ta gayawa dady."
Zuciyar shi ta fara bugawa tsoro ya kama shi ,"Sabreen bata da haƙuri zata iya gayawa hajia,nima ban kyauta to yanzu ya zanyi? ya zanyi ko na kirata ne?
Jikin shi na rawa ya ɗago wayar,tsakii ya ji tuno bashi da numberta gashi ya goge list ɗin kiran wayar gaba ɗaya,lokaci ɗaya yaji ranshi ya fara ɓace sai jan zaki yake yi,a hankali ya raba ambaton allah,har ya samu zuciyar shi ta fara sanyi.
Saida ya biya yai mata siyayya kala-kala kayan ci harda kayan sawa ya siya ba ita kaɗai ba harda na ƙannanta,sanan ya nufi unguwar ta su,kamar yadda ya saba shiga da motor shi cikin gidan yanzu ma ciki ya shigar da ita.
Yana isowa harabar gidan ya hango salma sa sauri ya kauda kai daga barin kallonta,gajeran wando ne iya cinya a jikin ta sai ƙaramar riga mai hannun bireziya,ba ɗan kwali a kanta.
Tunda ta hango shi ta fara faɗin,"A dole dole aunty haulat ta ruɗe irin wanan kyau ga izza ga kwarjini,cikin rangwaɗa ta iso gaban shi tana ƙare ma halitta shi kallo,cikin muryarta mai kama da na Haulat ta ce,"Hi sannu da zuwa."
tun kafin ta ƙaraso gurin shi ya saƙa bakin glass,ɗagowa yayi amma bai yarda ya ƙara kallon ta ba ya ce,cikin iyayi da kilibibi da ƙarya harshe da ba kowani harafin haƙƙin,"Hi!
"Waw ka haɗu over Naufal." ta faɗa a ranta haɗe da kafe shi da ido.
"Akwai kaya a bayan motor."
ya ƙara faɗa ita kuwa yana ƙara birgeta,yadda yake hausar kai idan ba haifaffan ɗan ƙasar hausa ba ne,sai ka ce wani yare yake yi.
ɗan aikin gidan ta kwalla ma kira ,da sauri ya zo jiki na rawa,tana ganin kayan ta ƙara ruɗewa.
Duk da kasancewar ita ce a gaba shi yana baya,amma bai ko kalle ta kanshi a ƙasa har suka isa cikin,falon bai taɓa shiga ba yai yau,wani irin ƙamshi me kama da wari ne ke tashi a falon,daman ya lafiyar giwa balle tayi hauka😅sai ƙamahin nan yana dokan hancin shi ta,fara tsotsoke hancin yana taɓe baki yana yamutsa fuska kamar wanda ya shiga cikin masai😀
Momy haulat na shigowa falon ya ɗago kai ya kalle ta,ai da sauri yai ƙasa da kanshi zuciyar shi na bugawa,ita ma gajeran wandon ne a jikin ta da ƙaramar riga gata ba ƙarama ba.
Har ƙasa ya ɗuka yai gaida ita kamar yadda ya saba kaida manyanshi.
Ya birgeta sosai ga tarbiyya,to ashe dai ƴan isaka suna son mutum mai tarbiyya,a ranta ta ce,"Ah dole Haulat ta ruɗe,gaskiya zan matsawa haulat mu tashi tsaye dan irin so mugun riƙo ake mu su.
A fili ta ce,"Salma kai shi ɗakin Auntyn ku."
Wani irin banbara ƙwai yaji ,wai namiji da suna hajira😅,mamaki ya bala'in kama shi"wai akai shi ɗakin haulat." ,tunani ya fara yi wacce irin al-adace wanan.
Da ƙyar ya iya tashi yabi bayan salma dan tsavar kunya,tafiya kaɗan takai su ɗaki.
"Ka shiga nan ne." salmar ta faɗa ta juya,ya daɗe tsaye a bakin kofar,sanan ya tura ,yana turawa ta buɗe ,yana shiga yaji an rungume shi.
"Sannu da zuwa." ta faɗa cikin wata irin siga.
Yarrr gashin jikin shi ya tashi,kallon ta yayi ai tuni zuciyar shi ta fara bugawa wanda hakan ya haufar mishi da mutuwar jiki.
Janyo shi tayi zuwa kan gadon shi ,kamar raƙomi da akala,kuma wa tayi ta rufe kofar sanna ta dawo kan cinyar shi ta zauna,cikin salo ta fara shafa fuskarshi akan lips ɗinshi ta tsaya wasa ta fara yi da su,sanan ta haɗe su hot kiss ta fara mishi,daman an daɗe va'a gamo ba ,ai tuni naufal ya ruɗe ya fara maida raddi,kan ku ce me sun fita haiyacin su,tura shi kan gado n tayi ta kwantar shi koƙarin cire mishi wando ta fara yi.......
Waiii yau ga rubutun wani iri hakan ya faru ne saboda nayi cikin gaggawa,saboda wanda nayi cikin natsuwa har read more biyar ya goge,ban yi niyar kara yi ba amma kuma nayi.
To fah fans me zai faru a ɗakin Haulat,dan naufal yayi nisa?
shin Sabreen zata cin ma burinta kuwa na son raba shi da haulat ɗin shi.?
To idan burin sabreen ya ciki Wani irin mataki haulat zata ɗauka akan ta?
Maganar zuwa gurin bokan da momyn haulat ɗin zata ƙara ma haulat ɗin zata yarda?
Idan ta yarda wa za'a ma asirin tsakanin Naufal da sabreen kuma wni irin Asiri za'a yi ma???
. Sir Anas! [12/22, 5:28 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/23, 1:52 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
*By* *fatima* *Batula*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* Page 13 .....................................................................
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{BA ZAKU WADATAR DA MUTANE TA DUKIYARKU BA, AMMA HALAYENKU SUNA WADATAR DA SU.}*_ °
```[Sahihut Targib;2661]``` ~~ _Wannan hadisin yana nuna mana cewa duk yanda zaka ba ma mutane dukiyarka to ba zaka iya wadatar da su ba, amma in kana da kyawun hali, kana mu'amalantar su da ita to zasu wadata da wannan kyawun halin. Allaahu a'alam._
```Allah ta'ala yasa mudace```
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
__________________
Cikin zafin nama Naufal ya janye jikin shi ya miƙe tsaye,yana wani irin numfashi,koƙarin buɗe baki yayi magana yayi,amma ya kasa bakin ma bai iya buɗe shi ba,cikin kasala da rawar da jikin shi ke yi ya gyara jikin shi ya nufi kofa zai buɗe har yakai hannu Haulat ta riƙo shi,juyowa yayi ya kalle ta da rinannan idanuwan shi,ita kanta kasa mishi magana tayi kuma ga bakinta yana son cewa wani abu amma ta kasa,girgiza mata kan shi yayi alamar bazai tsaya ba,sakancewar jikin ta ba ƙwari yasa ya janye hannuwan shi ya fita.
Yana isa falon ba kuwa yaji daɗin hakan sosai dan ko wani baya son ya ganahi a irin wanan yanayin da yake ciki balle su iyayen ta.
Ta gyar ya iya jan motor ya fita daga cikin gidan,yana fitowa daga gidan ya fara gudu kamar wanda za shi bangon duniya,cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan su,yana zuwa mai gadi ya buɗe mishi ya shiga,a tsakiyar gidan yayi farkin ɗin motor ya fito.
Ba kowa a falon ko da ma akwai ba zai gane ba tunda halin da yake ciki,kai tsaye ɗakin shi ya nufa,bai kula da Sabreen ba wacce ke kwance akan gadon shi,ya faɗa danne tan da yayi ne yasa tayi ƙara.
"Waiyo Yaya baka ganni ba ne zaka danne ni?
Tashi yayi yana kallon ta da rinnanun idanuwan shi,"Mai ya kawo ki?
"Meya kawo ni ɗakin miji na kuma yaya."
Jin amsar da ta bashi ya tabbatar mishi da taji abinda ya faɗa,dan bai yi tunanin zata ji ba.
"Mijin ki! ya faɗa cikin dakushashar muryar shi.
"Eh ko kai ba miji na ba ne."
Lumshe ido kawai yake yi yana kallon ƙaramin bakin ta,da fararan idanuwan ta masu hasken gaske kamar auduga.
Ya shagala da kallon ta,kamar ya janyo ta jikin shi yake ji,"Naufal kana da halal ɗin ka fah,to meye kake kai kan ga haram." shi da zuciyar shi suke wanan maganar.
"Kuma daga yau kullum ɗakin miji na zan dunga kwana."
Cikin kiss da kisisi na da shagwaɓa ta ke maganar,sai zazzaƙar muryarta ta ƙara zaƙi."
"Sabreen!
Ya faɗa cikin wata irin siga wacce ta wuce ya kira hakan da sha'awa saidai shauƙin so.
"Zaki iya kwana da ni?
"Eh zan iy....
Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya janyota rungumeta yayi,dumm dumm zuciyar shi ta fara bugawa da mugun ƙarfi wanda hakan ya haddasar mishi da kasala.
ƙoƙarin janye jikinta ta fara yi,amma ta kasa dan ba ƙaramin runguma yayi mata ba,ƙoƙarin haɗa bakin shi da tana ya fara yi amma ya kasa dan taƙi natsuwa gashi baya da ƙarfi
"Ahnn waiyo allah hajiata ka sake ni."
Tura ta yayi kan gadon ya tashi a fusace ya faɗa bayi ,ranshi ya ƙuna,ya daɗe yana zuwa kanshi ruwan sanyi ko yaji sanyi a ranahi,amma ya kasa ji,yana mamaki irin rayuwar da yake ciki haram na binshi halak na ƙin shi.
"Ohhho dai kuma sai na kwana a ɗakin nan kamin hakan ne dan karna kwana ko ,to sai na kwana." tana maganar tana murguɗa baki kamar yana kallon ta,tashi tayi tai kicin copee da haɗa mishi ta dawo har lokacin bai fito daga bayin ba.
~~~~~~~~~~~~~
Bayan farrah ta dawo gida Momy ta tambayeta mai ya faru,ƙarya tai mata, akan cewa ta tambaye ta ne ta koya mata yadda muke yin kunun gyaɗa ranar da muka kai musu taji daɗin shi kuma shi ma yaya irin shi yake so.
Momyn tajo daɗi sosai ta fara tunanin ya fara son ta.
Zaune suke a ɗakin su Dady yana kan gado ita kuma momy tana gaban mirrow tana cire ɗan kunnayen ta.
"Hajiata uwar gida." Dady ya faɗa yana murmushi.
Bata kalle shi ba ta ce,"Na'am abban Naufal."
"Ya kamata su tafi honeymoon ko?
"Eh gaskiya daman ina son nayi maka maganar gashi sun shaƙu da junan su."
Washe baki dady yayi daman yasan auran Sabreen da Naufal alkairi ne,yasan hakan zata kasance kuma ya saka a ranshi ko ba daɗe sai Naufal ya musu godiyar haɗa sun da aka yi.
"To amma wacce ƙasa kike ganin ya kama ta su je?
"wacce suke so."
"A'a bana son su san da maganar sai ranar."
"To zanyu taya zaka gane wacce ƙasa suke son zuwa."
"Karki damu nasan yadda zanyi."
~~~~~~~~~~~~~
Ganin ya daɗe bai fito ba yasa ta fara gyara ɗakin duk da kasancewar Sabreen bata aikin komai a gurin hajia hakan bai hana ta iya abubuwa ba girki,gyran ɗaki hatta wanki tana yi,bata da ƙyuya ko kaɗan.
Yana fitowa hanci shi yaji wani irin kamshi mai kwantar da hankali lumshe ido yayi ya buɗe,ƙarewa ɗakin kallo yayi kamar ba nashi ba komai tsaf-tsaf
"Wai mijina ashe haka kake daɗewa idan kana wanka."
Zuciyar shi ta fara amsan saƙon muryata sanan kunnuwan shi.
Kallon shi ta fara tsabb da sauri tai ƙasa da kai.
ba komai a jikin shi zai towel shi ma ɗan ƙarami ne.
ganin irin kallon da ta mishi yasa shi yin murmushi,lokaci ɗaya farinciki ya mamaye shi wanda bai san dalilin faruwan hakan ba.
Bai ce mata komai ba ya wuce gurin durowar ya buɗe zai naime kayan da zai saka.
"Ah nima daga yau zan ɗinga daɗewa a bayi gurin wanka,ai sai yanzu na gane ace daɗewan da kake yi ne yasa ka zama fari."
Dariya ta kuɓuce mishi mai ɗauke da jin daɗi juyowa yayi ya kalle ta ,ita ma murmushin dariyan take yi.
"To bari naje waje ka gama saka kayan",tana faɗa ta fita a ɗakin.
Murmushi ya ƙara yi,Sabreen tana burge shi,bai san lokacin da ta fara burge shi akan komai tana ba,ƙanana kaya ya saka mara su nauyi, sanan ya sha mai da turare,kan gadon ya koma ya zauna barici yake ji.
Ɗakin ta shigo fuskan nan ɗauke da annuri,"Ka gama shiryawan gaskiya kayi kyau sosai."
jin shi kawai yayi ya ce,"Tnx ke ma kinyi kyau."
Washe baki tayi,"Thanks my miji!
Murmushi yayi,yana jin daɗin sunan mijin da take kiran shi da shi.
copee ɗin ta miƙo mishi,"gashi ka sha zaka ji daɗin shi,kuma zai saka ka kayi barci ka huta."
Hannu ya miƙa ya amsa yana ɗan murmusawa.
"Yawwa miji na!
Sha yayi yana lumshe ido yana jin zuciyar shi wasai,zama tayi a gurin har ya shanye,ta sama kofin.
"Yaawwa sai ka kwanta ka huta."
Amsar umarnin ta kawai yake yi,yadda ta ce hakan yake yi.
Lamo yayi har barci ya ɗauke shi,tana zaune a gurin tana kallon shi.
Ƙarar wayar shi taji da sauri ta ɗako wayar zumbur ta miƙe ganin hoton haulat saida taji ani abu a ranta,kallon shi tayi sanan ta fita da sauri.
"Hello malama ta! har nayi fushi da ke,akan ƙin zuwan ki ɗaurin aure na alhalin an gaiyaci dukkan mutanan da ke garin abuja da ma kewayan ta."
Haulat wacce ke zaune akan kujera jin muryar Sabreen yasa ta miƙe zumbur.
"Naufal!
"No malama ta,miji na,mijin ɗalibata zaki ce."
"Sabreen!
"Na'am malama ta,zan zo ni da mijina na miki godiya dan da bandan ke ba da ban aure naufal ba,ko kin manta kike ce ina son aure aka gayawa iyaye na."
Saida ta sauƙe gajerar ajiyar zuciya sanan ta ɗaura da faɗin,"Malam ta,jahili daƙiƙi ɗan kauye iri na da aura,ko ɗan gaye mai aji mai ilimi da kyau na aura wanda ko wacce macce take son rayuwa da.?
"Gaya min dan na kasa ganewa,laah ko shi ne wanda malamata ta ke mafarki akan shi?
"Malama ta! ya kike yi shiru ,ki zauna kinji ki natsu,ni Sabreen ba tsararki ba ce,yawwa kuma ki fita harkar miji na,baki da ikon juyamin shi tunda ba ɗalibin ki ba ne,ina fatan kin gane."
"Ƴar aljanna ke dawa kuma?
Ɗagowa tayi ganin hajia ce yasa ta katse wayar a ranta ta ce," *Ni* *DA* *MALAMA* *TA*.
A fii kuwa dariya tayi ta faɗa kan hajiar tana ihuu tana faɗin,"Oyoo ooyoo hajiata.
"Ba wani bayan kin manta da hajiar aure daɗi ko?
Cikin shagwaɓa ta ce,"Kai hajia ba wani daɗi."
"To ya kike? ina ta kewar ki shiyasa na ce bari na zo na ganki."
"Nima hajia ai nayi kewarki sosai."
Fira suka shiga yi sosai da sosai cikin so da ƙaunar juna.
******
Ɓangaran Haulat kuwa tunda sabreen ta katse wayar ta fasa ihuu,mai rikitar wa.
"Lafiya kike haulat mai ya faru? A ruɗe momyn ki tambayarta wanda ihunn na ta ne ya fito da ita daga ɗakin ta.
"Waiyo allah na momy na shiga ukku dan allah mu tafi gurin bokan nan."
"Duk da basan abinda ya faru ba,nasan sai irin hakan ta faru,ke ce banza bara wayau ai."
"Sabreen sai na yi ajalinki walahi sai na kashe ki!!
"Mu tafi yanzun nan."
"Matsalar yau baya sauraran mutane sai gobe."
"Ɓakin ciki sai iya kashe ni kafin goben ba zan iya hakuri zuwa gobe ba."
"Tun ranar da nake miki magana kika ƙi saurarata, amma harda shi zamu haɗa."
"No momy bana son a mishi asiri."
"Giyar so ko!,to shi ne wanda ya kamata ayi wa asirin ma ba ita ba."
"Momy baya da matsala ina son shi,soyayyar da yake min ita nake so,bana son a saka shi dole da bin umrnin."
"Hmm haulat kenan ina fatan zaki gane ki dawo hanya."
~~~~~~~~~~ Bangaran Naufal kuwa tunda ya kwanta ya faɗa duniyar mafarkin da ya saba yi,wanda ya kasa bin jikin shi,dan kullum abin sabo yake zuwar mishi.
Kamar yadda ya saba tashi a irin lokacin da tare barin shi yau ma hakan ne,farkawa yayi zuciyar shi na zafi da ƙuna ga zufa ta mamaye shi kanshi a ƙasa.
Sintar muryar ta yayi tana faɗin, "Miji na ka tashi?
ɗagowa yayi suka haɗa ido,wani iri yaji ,ita kanta kasa tai da kai,"Hajia ta zo tana na jiranka,har ta wuce baka tashi ba,daman yanzu zan tashe ka dan lokacin sallah yayi."
Lumshe rinannun idanuwan shi yake yi,ya kasa daina barin kallon ta.
Ganin kamar ita yake kallo yasa ta fara kame-kame,"Lokaci yana tafiya fah!
"Ko barcin bai ishe ka ba ne?
Dariya yayi dan sanan ya tashi ya shiga bayin,yana shiga ta ƙara gyran ɗakin tayi tsaba sanan ta fashe shi da turare.,ɗaukar wayar shi tayi ta kashe sanan ta fita indomi ta haɗa mishi da kyau sai jus ta kawo har lokacin bai fito ba,zama tayi a bakin gadon.
Yana fitowa yaji ƙamshi me kwantar da zuciyar,idon shi suka sauka akan sabreen wacce ke zaune akan gadon tana wasa zuben da yake hannunta,ya daɗe yana kallon ta,wani iri yake ji a ranshi a duk lokacin da yake kallon ta,yadai kasa gane wani irin abu ne.
Ɗago kai tayi suka haɗa ido kai tai da kai da sauri,"Ka ƙara haske yanzu kawai."
Murmushi yayi,"Waya gaya miki wanke ke saka mutum yayi haske?
"Gani nayi."
"Gurin wa?
"Gurin mijina kuma yaya nah!
Dariya yayi mai ɗauke da murmushi ,yana jin daɗin sunan da take kiran shi da shi"mijina"
ƙarasowa yayi har kusa da ita wani towel ɗin zai ɗauka ya goge jiki da shi,kuma yana bayan ta.
kaff da ita ya matsu ya miƙe hannun shi zai ɗauko towel ɗin jikin su ya haɗu da na juna,yarr dukkan su suka ji ,ruwan girjin shi ya zuba a fuskarta,wani irin sanyi taji har zuciyarta,tsintar kan shi yayi da son rungumeta, faɗawa yayi kan jikinta ya rungume ta,wani irin baƙon yanayi ya fara ziyartar zuciyar shi,mutsu-mutsu ta fara tana kokarin janye jikinta,"Ka gyale ni bana so." ta faɗa.
Zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske,wanan maganar tuno mishi da mafarkin shi tayi,kafin ya ƙarasa tunanin shi,ta ƙwace jikin ta,barin ɗakin tayi da sauri ta barshi da bugun zuciya....
. Sir Anas! [12/23, 1:52 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/23, 2:16 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
*By* *fatima* *Batula*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
Page 14 .............................................
*Addu'a Ga Wanda Yayi sabon Aure*
بارَكَ اللَّهُ لَكَ، وَبَارَكَ عَلَيْكَ، وَجَمَعَ بَيْنَكُمَا فِي خَيْرٍ. Barakal-lahu lak, wabaraka 'alayk, wajama'a baynakuma fee khayr.
Allah Ya sanya albarka a gareka, yayi maka albarka kum aya hada tsakaninku da alheri.
Wanga page na ku ne iyalan bintu Ahmad ,da tana jamcy ina yinki sosai na gode da kulawar ku,ku sha zaman ku ,ku huta batula tana yinku fiye da tunanin ku.
_____________
Ya daɗe kwance a inda ta barshi,"Ka gyale ni bana so",maganar ke mishi yawa cikin kai ,ba yau kaɗai aka taɓa gaya mishi ita ba,abinda ya kasa gane meye halaƙar maganar Sabreen da mafarkin shi,ganin kan shi ya fara ɗaukar zafi yasa watsar da tunanin,ya tashi ya saka kaya mara su nauyi wayar shi ya ɗauko yana sun kiran Haulat,"Mtseww na rasa gane meye matsalar haulat a cikin ɗakin take koƙarin taga mun aikata alfasha",ƙara jan tsakii yayi ya jefar da wayar bai ma kula da wayar a kashe take ba.
Hango kwanan abincin da Sabreen ta kawo mishi yayi,murmushi yayi ya ƙarasa gurin ya buɗe ci ya fara yi yana murmushi.
Cikin salon magana irin nashi ya ce,"Wai zata iya kwana a ɗaki ɗaya da ni,sai bakin tsiya yadda take magana kamar wata mai faɗa a gani."
Saida ya gama cin abincin sanan ɗauko system ɗin shi yana chat,murmushi yayi mai ɗauke da farinciki pics ɗin sabreen ne farrah ta saka a status da kayan makaranta tayi su,nayi kyau sosai fuskar ta ɗauke da murmushi.
"Mijina!
Tsintar maganar yayi a kunnuwan shi,wani murmushin ya ƙara yi,bai ɗago ba ya ce,"Kin ƙara dawowa ne?
Saida ta ƙaraso ta zauna a gefen gadon kusa da shi sanan ta ce,"Eh ya bazan dawo ba,ni da zan kwana a nan."
Sai yanzu ya ɗago ya kalle ta,"Zaki kwana a nan?,ki kwana a ɗakin ki."
"A'a ni tsoron ɗaki na nake ji,to meye idan na kwana a ɗakin miji na."
Kallon ta yayi sosai dan tunda ta fara maganar ya zuba mata ido,har zai yi magana ya fasa,ya maida hankali gurin abinda yake yi.
Bata damu da hakan ba ta ce,"Me zan dafa ma?
"Kin san haƙƙin miji akan matar shi ? a maimakon ya bata amsar tambayarta sai tambayarta yayi.
Kai tsaye ta ce,"Na sa ni."
"To gaya min."
Saida tayi jimm sanan ta ce,"Eh ta kula da shi ta mishi biyayya da kula da kayan shi,ta dafa mishi abinci sai me ma? yawwa sai tarbiyar yaran shi sai...
"Taya ake samun yaran?
"Ciki!
"Taya ake cikin!
"Me?!
"Eh taya ake cikin?
Duk da kasancewar bata san abubuwa sosai ba waɗan da suka shafi ma'arata,amma saida taji kunya rufe ido tayi da hannuwan ta.
Kallon ta yayi yana murmushi Sabreen tana burge shi komai tayi abin kallo ne,"Hm meye na rufe ido ko kin san yadda ake yi ne?
kai ta girgiza mishi alamar a'a
"To ba zaki kwana a ɗaki na ba,tunda baki san haƙƙin aure ba." ya faɗa idanuwan shi suna kan ta yaga yadda zata yi.
"A'a ni anan zan kwana."
Yadda tayi maganar cikin shagwaɓa yasa ta kashe mishi jiki lumshe idanuwa yake yi yana kallon ta.
"A'a ba zaki kwana ba,wacce tasan haƙƙin mijinta ita ke kwana a ɗakin shi,kinga ke baki sani ba."
"To ka gayamin sai in sani."
"Saidai na koya miki."
"Ka koyamin."
"Idan baki so shikenan sai ki kwana a ɗakin ki kawai."
"Ina so toh."
Dariya yayi sosai har saida haƙoran shi suka baiyana sautin muryar shi ya baiyana.
"Sabreen kenan idan gaji yadda ta iya kiran mijina sai ka ɗauka tasan meye mijin,kamar wata wayayya idan ka ganta amma a zahiri bata san komai ba,bata iya komai ba", shi da zuciyar shi suke wanan maganar har lokacin kallon ta yake yi yana dariya.
Ganin dariyar tayi yawa sa ya ita ma ta fara dariyar,yana jin ta fara dariyar ,ya ƙara fashe wa da dariya.
dan dariyarta tana bashi dariya,kamar wasu sababbin kamo haka suka dinga dariya ,dan tsabar dariyar da suke yi bata san lokacin da ta faɗa akan jikin shi ba,kwanciyar da yayi yasa ta kwanta kan ƙirjin shi.
"Sabreen!
"Na'am mijina."
Dariya ta ƙara bashi amma baiyi dariyar ba yadai murmusa.
Kallon ta yake yi ,a ran shi yana faɗin ,"Ina ma kina so na ina sonki,da munji daɗin rayuwa."
"To mai zai hana ka so ni ɗin."
Zaro ido yayi jin amsar da ta bashi ,badai taji abinda ya faɗa ba.
Dariya tayi,"Naji ai."
Lokaci ɗaya girman kai ya shige shi,"Kinji ai ba da ke nake ba,ni bazan so ki ba,dan ba ra'ayina ba ce ke."
Ko kaɗan bata ji zafin maganar shi ma,dan ita ma ba son nashi take yi ba,kuma ba ra'ayin shi ba ce ita,duk abinda take yi dan Malama haulat ne.
A ranta ta ce,"Ban damu da ka so ni ba ni kawai ka manta da waccen banzar wacce bata san darajar muta ne ba,ni ban ma san abinda ka gani a tattare da ita da kike son ta ba."
Shiru suka yi ba abinda kunnuwan su ke ji banda bugun zuciyoyin su,musamman ita da ke saman ƙirjin shi,hannun ta takai saitin gurin zuciyar shi,bata ke komai ba tana dai jin yadda take bugawa ne.
Yana jin ta taɓa ya rufe ido dan ƙaruwa bugun zuciyar ta ƙara yi.
Lumfashin ta kan fuskar shi yake sauka,ɗaga ta yayi yaga tayi barci murmushi yayi,"Savreen kenan mai abin mamaki." zame jikin shi yayi sanan ya ƙara gyara mata kwanciya.
~~~~~~~~~~~~~
"Aunty Haulat dan allah karki biye momy abinda ta ke so kuyi bashi da kyau,kuma ba daidai ba ne,ga tarin zunubai ga ɗaukar haƙƙi gashi kuma baku san abinda zai biyo baya ba,dan allh....
Cikin daka tsawa ta ce,"Keee Sakina zaki gaya mana allah ,ke idan baki fita daga ido na ba,wllh zan ɓata miki rai,ni tsarar ki ce ma,ke a dole malamar addini ko,zaki dinga wani wa'azi an gaya miki ban san allah ba ne,ko ke kaɗai kika taɓa zuwa islamiya da za.....
"Sakina ko." faɗar momy wacce ta shigo ɗakin,kallon Sakinar tayi wacce ke tsugunne a ƙasa.
"Sakina anya kuwa ni na haife ki?da a asibiti na haife ki wllh sai na ce canja min aka yi."
Hawaye ya wanke fuskarta gaba ɗaya ,kuka mai tsuma zuciya take yi,halin uwarta yana ɓata mata rai ga tsanar da take nuna mata da banbanci,cikin muryar kuka ta ce,"Kiyi hakuri."
"Dalla ɓace ki bani guri bazan shasha wawayi wacce ta ɗibo ɗabiyar dangin mahaifinta na."
Jan jiki tayi tabar ɗakin tana kuka mai tsuma zuciya tausayin kanta ya kamata.
Kallon Haulat Momyn tayi ta ce,"Gobe da sassafe zamu tafi ki shirya da wuri dan a katsina ne."
"Momy ban yi tunanin zan yi barci ba,ko tsakiyar dare ne a shirye na ke."
"Yawwa Ƴar albarka."
~~~~~~~ "Sabreen ki tashi an kira sallar maqrib."
Sautin muryar shi ya doki dodon kunnan ta,a hankali ta fara buɗe ido,kan fuskar shi idanuwan ta suka sauka,kallon juna suka fara yi,ganin baya da niyyar barin kallon na ta yasa tai ƙasa da kai haɗe da tashi zaune.
"Kai ya aka yi nayi barci?
"Hm ko dan kin kwanta akan ƙirjin mijin ki ne?
Dariya yayi,yana kallon fuskarta.
"Eh haka ne."
Murmushi yayi a ranshi yana faɗin,"Hmm komai aka faɗa miki yarda zaki yi da shi wawiya kawai."
Tashi tayi ta shiga bayin shi,tai alwala tana fitowa taga baya ɗakin,ita ma ta fita ɗakinta ta nufa saida tayi sallah sanan ta fito kicin ta shiga ta haɗa musu abinci sanan ta koma ɗakinta tayi wanka,doguwar riga ta saka ɓaka ba kwalliya a jikin rigar amma yadin rigar zai tabbatar ma da rigar bata yara ba ce,ta kama jikin ta komai ya fito kamar yarda allah yayi shi,hula ta saka bata ɗaura ɗan kwalin rigar ba.
Turaren miski shi ne turaran Savreen dan haka shi ta shafa a jikin ta sai da haɗa da wani turare wanda hajia ta kawo mata,ba abinda ta sha ko mai bata shafa ba,amma kasancewar yanayin fatar jikin ta mai kyau ce baka ce bata shafa mai ba.
Cikin tafiyar ta irin ta kasaita ta ƙaraso falon,yana zaune yadda ya zauna zaka tabbatar da hanlakin shi ba'a jikin shi yake ba,saida ta ƙaraso daff da shi ta ce,"Miji na tunanin me kake yi ne?
ɗagowa yayi ya kalle ta,fuska ba yabo va fallasa,kamar bazai yi mata na ba,sai kuma ya ce,"Ina tunanin mosoyiya ta ne," ya kuma ɓata rai ya kau da ganin shi daga gare ta.
Haushin gaske taji cikin raunanniyar murya ta ce,"Ai mata gare ka."
"Matar da bata san haƙƙin miji ba."
"Zan koya kaji," da shagwaɓa tayi maganar.
Murmushi yayi har sai da haƙuran shi su ka baiyana,ya rasa dalilin da yasa yake son yi mata magana akan aure.
"Zaka koyamin?"
wanan karan dariya yayi sosai,"Sabreen ƴar hajia."
"Eh ba zaka koya min ba."
"Baki iya ba kike ce kina son aure,saboda fiti na irin ta ki."
"Ba fiti ba ne."
Bai ce mata komai ba dan bashi da lokacin yin magana da ita,baya cikin yanayin jin daɗi ko kaɗan abubuwa sun mishi yawa,gashi yana bugatar macce ga wacce yake so ba aure take so ba,gashi baya jin zai iya kula matar shi.
Ɗakin shi ya tafi,yana zuwa ya faɗa kan gadon.
Ko kaɗan Sabreen bata ji haushi ba dan taɗau alwashin duk abinda zai mata ba gudu ba ja da baya zata shanye har sai lokacin da ta tabbata ya manta da haulat sanan zata rabu da shi.