Kenza eBookz

Nida malamata complete - Chapter 7

Nida malamata complete - Chapter 7

Nida malamata complete Chapter 7: Nida malamata complete Chapter 7. A fusace ya juyo gabanta ya ƙaraso dabb da ita har suna jin fitar numfashin juna,kallon…

4,472 words

A fusace ya juyo gabanta ya ƙaraso dabb da ita har suna jin fitar numfashin juna,kallon ta yayi ido cikin ido ya"Momy ko Dady,kuyi hakuri dan allah zani gurin wacce nake so ne."

"Toh ban aminci ba."

Dariya ya fashe da ita sosai yana mamaki hali irin na Sabreen,a lokaci ɗaya kuma ya murtike fuska kamar ba taɓa dariya ba,rikiɗewa yayi ya dawo ainihin Naufal mara dariya ɗan gilibibi da iyayi da yatsine isa izza mulki.

kallon ta yayi ya ce"me zan miki idan na tsaya?

"Ai.. dan...

"Hm Sabreen dan kin aure ni,da ƙarfi ba ki da ikon juyani,kin gane yana maganar yana ƙarya harshe cikin iyayi.

Kallon ƙaramin bakin shi Sabreen ke yi,yadda yake fito da maganar take kallo.

Ƙara matsuwa yayi dabb ta ita ƙokarin haɗe bakin su ya fara yi,tureshi Sabreen ta fara ƙokarin yi,amma ina ta kasa.

"Yadai ba abinda kike so ba kenan."

"Allah ya kyauta ni ba ƴar iska ba ce."

"Ni kuma ɗan iskane,u know what Sabreen?i cant share anything with you,"

"Ni bana jin yaren india."

Haba me Naufal zaiyi dariya ya fashe da ita harda komawa baya ya zauna kan gujera.

Ta ƙule gurin takaici hararshi take yi ,shi baima san tana yiba,saida yayi me isarshi sanan ya tsaya ,ɗaure fuska yayi ya ce"u are very funny Sabreen."

Ko kaɗan Sabreen bata gane abinda yake faɗa,ko hausar ma ba ko wani lokaci take ganewa ba.

Fita yayi yabarta a tsaye tana jin hauci.

"Kai Anya banyi kuskure ba,gashi gurin Haulat zaije kuma sai ya gayamata abinda ya faru ni nace zan aure shi baya so na,waiyo allah na yanzu ya zanyi? ya zanyi???

Naime naime ta fara yi,chan ta hango abinda take naiman wayarta ce. "To yanzu wa zan kira? "Dady nace mishi me? "Na kira Naufal yawwa shi ,to me zanje mishi ya dawo.

Cikin rashin abinda zata faɗa mishi ta kira shi,yana tafiya a cikin motor shi da tunanin yadda zai fusanci Haulat a ranshi,jaji ringin ɗin waya,baƙowar number ya gani dan bashi da number ta,kamar kar ya ɗauka sai kuma ya ɗauka,tana jin ya ɗauka tai shiru.

"Hello! waye?

"Ya Naufal ka dawo gida yanzu Dady ya zo yana son ganinka."

"Ohhh no! Am coming" yana faɗa ya katse wayar ya juyo da sauri a zuciyar shi yana tausayawa kanshi halin da zai shiga,ya kamata a kyaleshi ya sarara amma yaga alamar ba'a da niyyar barin nashi.

"To ni yanzu idan ya zo me zan ce mishi,ko na ƙara mishi wata ƙaryar ."

"Ah'ah ba zan kara mishi wata ƙaryar ba,gaskiya zan faɗa mishi." "To idan yaji hauci fah? "to sai me ba abinda ya isa ya miki"

Murmushi tayi haɗe da juyo kanta"Hm ni ce fah ƴar aljanna ƴar gata kuma shalelen Hajia da Dady,sai abinda na ce,baka da yarda zaka iya Ya Naufal zan juyoka"

🤕waiyo aka ce raahin sani yafi dare duhu Sabreen kina da ƙuruciya kuma kinyi kuskure.

Tana gaba faɗa ta haye sama tana jin daɗi,wanka tayi ta saka riga da sikit na atamfa shiff-shiff suka mata kamar dan jikinta aka yi kayan,ko mai bata shafa ba,ta fito falo ta zauna akan 1seater ta kunna tivi tana kallo hankali kwance.

********************

Kwance take akan gadan ta hannuta ɗauke da drip,barci take yi,tun jiya har yanxu bata farka ba.

Momynta ta kalli ƙanwarta salma ta ce"Kai salma lamarin Haulat yana ban tsoro ,ban taɓa tunanin akwai namijin da zata shiga wani hali akan shi ba,tun yaushe nake gaya muku,daga kun ga abinda yake son ya gagareku ,kuje gurin malam gajere zai warware muku komai amma kun ƙi jira kuke yi saina kama ku na kaiku".

"Ba haka ba ne momy,shi ma yana sonta dan ya sha matsa mata akan ta bashi izini ya turo."

"Yana sonta shi ne zai aura wata ke baki ga hoton ba,yadda suke wa juna kallon soyayya."

"Wllh momy yana sonta bansan yadda aka yiba,kuma ita ma tana da laifi tunda tun lokacin yake mata mita ya fito taƙi amcewa."

"Ni na kasa gane abinda kike son faɗi,kina nufin wanan zoƙeƙen saurayin ne zai tsaya a mishi auran dole,bari kiji yanzu ko wacce mace ba'a zaune take ba ,musamman ma shi wanda kowacce mace ke buri ,to da ƙyalla ido ta ganshi bazata bari ya ƙuɓuce mata ba,amma ita dayake bata da wayau shashace ta zauna haka ai gashi nan tana ji tana gani an ƙwace mata shi,ba yadda zata yi."

"Hm momy kenan ai ko ni kinsan ba hakura zanyi ba,balle Aunty Haulat kuma akan abinda tafi so a duniya ai wallahi zata iya yin komai akan shi,ba zata haƙura ba."

"To da dai yafi mata,ta ɗau mataki,akwai wani sabon malami wanda ƙawata tamin hanyarshi ya iya aiki,aikin shi kamar yankan wuƙa yake,idan ta tashi sai muje a san yadda za'ayi"

"Yawwa momyn mu shiyasa muke sonki kuma muke alfahari da ke allah yabar mana ke."

Murmushi tayi ya ce"Hm dole na so ku,ban yarda da rashin nasara ba,shiyasa zanyi komai akan nasararku.....

. [12/22, 5:26 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/22, 5:28 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹

*By* *fatima* *Batula*

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* Page 12

.............................................................................................

🌈 *FALALAR* *KWANCIYA* *DA* *AL* *-* *WALA* .

_Hadisi ya inganta daka *Annabi Sallallahu Alaihi wasallam* yace:_ *→(من بات طاهرا بات في شعاره ملك فلم يستيقظ إلا قال الملك :اللهم اغفر لعبدك فلان فإنه بات طهرا)* ...• _( Wanda ya kwanta da alwala, mala'ika zai kwana acikin mayafinsa bazai gushe ba yana masa Addu'a yana cewa "Ya Allah ka gafartawa bawanka wane domin ya kwanta yana da tsarki (alwala)"_ ...• _*Abdullahi bin Mubarak yaruwaitoshi acikin littafinsa "azzuhudu" (64) ta hanyar hasan bin Zakwaan, Ibnu hibbaan ya fitar dashi acikin saheeh dinsa (1052).*_ ...• _Saidai isnadine mai rauni, domin Alhasan bin Zakwann imamu Ahmad ya raunatashi da ibnu ma'een da sauransu.._ ...• _*Duba Mizanul I'itidali (1/489),*_ ...• _Amma yanada wani hadisin dake mara masa baya wanda imamul dabarany yaruwaito acikin *Mu'ujamul kabeer (13620) da waninsa.*_ ...• _Hadisin dake goyawa wannan baya wanda imamu dabarani ya ruwaito daga Abdullahi bn Umar Allah ya kara masa yarda shine wanda manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:_ *→"( طَهِّرُوا هَذِهِ الْأَجْسَادَ طَهَّرَكُمُ اللهُ، فَإِنَّهُ لَيْسَ عَبْدٌ يَبِيتُ طَاهِرًا إِلَّا بَاتَ مَعَهُ مَلَكٌ فِي شِعَارِهِ لَا يَنْقَلِبُ سَاعَةً مِنَ اللَّيْلِ إِلَّا قَالَ: اللهُمَّ اغْفِرْ لِعَبْدِكَ فَإِنَّهُ بَاتَ طَاهِرًا )* ...• _Ma'ana"ku tsarkake jikinku Allah zai tsarkake ku, domin babu wani bawa da zai kwanta da alwala face mala'ika ya kwana tare dashi acikin mayafinsa babu wani lokaci a cikin dare da zai shude face wannan mala'ika yanai masa addu'a yana cewa: " ya Allah ka gafarta wa bawanka domin ya kwanta da alwala"._ ...• _Wasu malamai Suntafi akan hadisine kyakkyawa saboda wasu hadisan da suke mara masa baya._ ...• _Duba *"Attargeebu wattarheeb, na munziry (1/231) da muj'ma'ul zawa'id na haisami (1/226) da Sil-sila saheeha na Albany (2539), dabarani yaruwaitoshi acikin Ausaad (5087) daka ibn Abbas*_ ...• _isnadan hadisin dukkansu babu wacce ta kubuta daka wata tawaya saidai idan ka hadasu wani yana karfafa wani saboda haka Albani ya hukunta hadisin da cewa kyakkyawane idan ka hadashi da waninsa. *Saheehul Targeebu wattarheeb (599).*_ ...• _*Falalar karanta Suratul Mulk*_ _Falalar karanta Suratul Mulk (Tabarakallathi biyadihil Mulk) tazo adunqule sannan kuma Falalarta tazo kafin kwanciya bacci a kebance, *Imam *Tirmidhiy yaruwaito hadisi (2891) da Imam Ahmad a cikin musnad nasa hadisi na (7915) daga Abu huraira Allah ya kara yarda dashi* daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Akwai wata Sura mai aya talatin a cikin Alqur'ani, ta ceci wani mutum har aka gafarta masa, itace Suratu Tabarakallathi biyadihil Mulk), Sheikh Albani ya ingantashi a cikin sahihul Tirmidhiy "_ ...• _*Tirmidhiy ya ruwaito hadisi (2892) da Imam Ahmad (14249) daga Jabir Allah ya kara masa yarda"* Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya kasance baya barci har sai ya karanta Alif laam miim Tanzeel da kuma Tabarakallathi biyadihil "Sheikh Albani ya ingantashi a cikin sahih sunanul Tirmidhiy._ ...• _Abinda yafi shine mutum ya karanta Suratul Mulk kafin ya kwanta barci a kowane dare, saboda irin yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya yi, da zai karanta ta a sallarsa ta isha'i to da hakan ya isar masa, saboda gamewar zancen Hadisin farko da ya zo game da ceton Suratul Mulk ga wanda ya karanta ta, domin lokacin karanta ta ba a iyakance shi ba._ ...• _Saidai ba'a shar'anta dawwama akan karanta ta cikin sallar isha'i ba, domin dawwama akan karanta ta nau'i ne na iyakancewa, ita kuma iyakancewa a cikin Ibada bata kasancewa face da dalili, amma don anyi haka lokaci bayan lokaci to babu laifi._

..................................................................... " Ni Naufal yanzu shikenan rayuwata a haka zata tabbata cikin rashin ƴanci,sai abinda Sabreen ta ke so zanyi,ba'amin adalci ba,an aura min ita bata son ta amma ba za'a gyale ni ba,yanzu ya kenan idan naje ma Dady da maganar auran Haulat..

Da ƙarfin gaske zuciyar shi ta fara bugawa,zufa na ƙeto mishi ta ko'ina a sassan jikin shi,kamar motor ba AC a cikin ta.

Da gudun gaske yake jan motor kamar wanda zai bar ƙasa,cikin ƙanƙanin lokaci ya iso unguwarta su,yana zuwa gurin get ɗin gidan mai gadi ya buɗe mishi gidan da sauri ya kunna kai,bai kai ga gurin da ake yin parkin ba ya tsaida motor ya fito.

Har yana harɗewa dan saurin gurin isa cikin falon,yana isa ya fara kalle-kalle yaga Dady bai ganshi ba,a kwance ya hango ta akan 3 seater ko ɗan kwali babu akan ta,hankali kwance take kallonta tana murmushi tana jin daɗin kallon ga juice a gaban ta.

ƙarasawa yayi kusa da ita bata san ya shigo ba sai ji tayi ya ce,"Sabreen ina Dady har ya koma ne?

Hankali kwance ta juyo ta kalle shi tana murmushi ta ce,Wani Dady?

"Wani Dady? tambayata kike yi wani Dady."

Ɗan yaƙuna fuska tayi ta ce,"Eh!

"Haba Sabreen me kika maida ni,ki kira ni ki ce min Dady ya so yana jira na,kuma shi ne kike tambayata wani Dady."

Ta sigar da yayi maganar ya ɗan bata tausayi abinda tayi niyyar ce mishi ta fasa.

"Ba Dady ba ne,Dady bai zo ba,bana jin daɗi ne kuma ina jin tsoro shiyasa na kira ka dan ka dawo nasan idan ba hakan na ce maka ba,ba zuwan zaka yi ba."

Zama yayi kan kujera ya dafa kanshi, "Sabreen wai dan allah meye matsalarki da ni ?

kai tsaye ta ce mishi "Haulat karka je gurinta ka daina sonta"

"Na so wa? naje gurin kuwa? tashi tsaye yayi kusa da ita ya matsu ,yasa hannuwan shi ya ɗago ta daga kan kujerar da take zaune ,suka fuskanci juna sosai har numfashin su yana cuɗanya da na juna,mayun idanuwan shi ya zuba mata,yakan rasa dalilin da yasa idan ya fara kallonta baya so ya tsaya,kawata-kawata.

duk fitsara irin ta Sabreen saida ta sauke kanta kasa yau kawai yai mata ƙwarjini idanuwan shi suka tsorata ta,mutsu-mutsu ta fara yi alamar ta gaji da tsayuwar.

cikin wata irin murya ya ce"Na so ki! na zo gurinki ɗan iska fa kike ce min"

"am.. ni...nifa.."

"ke fah me?

"Ni bance ka so ni ba,amma karka so Haulat"

"Meyasa?

"Malama ta ce!

Tura ta yayi ta faɗa kan kujerar" Whay? Sabreen meyasa kike son taƙura rayuwar mutane ne,kin san irin son da haulat ke min kuwa? ko kina ganin zaki iya hanani son Haulat,kinyi kaɗan Sabreen,ina son Haulat ita ce muradin Raina da ita zan rayu zan aure ta,idan kuma kina ganin zaki iya hanani to mu zuba mu gani."

Yana faɗa ya juya zai hau zama har ya taka matakalar ta ce ,"Ya Naufal!

Chikk ya tsaya,ƙarasawa tayi idan yake jin ta a bayan shi yasa shi juyowa.

"Hm ni Sabreen muhammad sai na sa ka mata da waye Haulat ,ko sunanta sai ka manta da shi ." cikin izza da ƙwarin gwuwa tayi maganar.

Dariya ta bashi sosai,ya kalleta yana dariya maimata abinda ta faɗa yayi,"Ke Sabreen muhammad mai taƙama sai kin saka na manta da Haulat."

Anan ya dakata kafin ya murmusa ya ce"So fuuny! how? When Where?

"Sabreen muhammad kike,plss ki tabbatar min ke ɗin ce ta hanyar cika avinda kike faɗa,ko ma nace tatsuniya,yana faɗa ya juya.

"Yaya Naufal har yanzu baka san ko ni wacece ba,ban taɓa faɗin abinda bazan iyaba,duk abinda nace zanyi sai nayi shi,amma zaka ni,wanan alƙawari ne sai ka manta da ka taba sanin wata me irin suna Haulat."

Bai juyo ba jin ta gama maaganar yasa ya wuce abinshi yana mamaki da hali irin na Sabreen.

Yana zuwa ɗakin shi ya faɗa kan gado kanshi yana kallon sama "Meyasa yarinyar nan take magana da ƙwarin gwauwa ne? zata iya aiwatar da abinda ta faɗa ne? to taya?

Bai bawa kanshi wahalar naimo amsoshin ba,dan yasan ba sanin su zai yiba,deep breath yayi "any where! ba zata iya ba ,dariya yayi tuno yadda tayi maganar"Sabreen kenan!

A hankali ya ƙara kiran Sunan "Sabreen" wani irin murmushi yayi wanda bai san dalilin shi nayi ba.

hhhh banza tun yanzu har ya manta da batun Haulat,tun kan aje ko ina😅

~~~~~~~~~~~~~

sama-sama ta fara buɗe idanuwanta waɗan da sukai mugun nauyi,"Naufal!Naufal!

Da sunan shi a bakinta ta ƙarasa buɗe ido,saida ta kalle ɗakin tsabb sanan ta kara rufe ido ,hoton su Naufal Da Sabreen ne kwakwalwarta ta hasko mata ,wani zazzafan hawaye suka fara fito mata,zuciyarta na zafi da raɗaɗi,"Sabreen! Ta faɗa sunan ta cike da muguwar tsana.

Ƙanwat bai binta wacce suke kira da baby ta shigo ɗakin jin Auntyn tata tana kiran Savreen ya bata mamaki a iya saninta,Naufal ne sillar shigar ta wanan halin,kusa da ita ta kasara,"Aunty Haulat kin tashi? ya jikin? waye kuma Sabreen?

Hawayen ta basu yanke ba,kuma bata da niyyar daina su yanzu.

"Ya isa haka kiyi hakuri Aunty"

Kamr bata san da wata halitta va,a gurin,kiran sunan shi kawai take yi "Naufal Naufal.

"fiye da sau biyar ya kira ba'a ɗauka ba."

Zumbur da miƙe,da sauri baby ta komar da ita"Ki natsu Aunty,karki ɗaga hankalinki akan mutumin da ya yaudare ki...

ta katse babyn da sauri "Ina sonshi Baby ba zan iya rayuwa idan babu shi ba,pls baby kira min shi "

"Ya isa ki kwantar da hankalinki bamu rasa abinda muke so Aunty."

"Yana so na Baby basan yadda aka yiba,bai taɓa kira na sau biyu ba,amma tunda kika ga ya kirani sau biyar yana so na,amma taya zai yi aure..

Sittt tayi kamar wacce ka tsaida tuno waye amaryar ta shi ,"Sabreen!

"Waye Sabree?

"Ɗalibata!

"ɗalibarki meye haɗinki da ita kuma?

"Ban wayata ,ki ban wayata na ce, a fusace tai maganar

"Tana ɗakin momy na saka ta a charji."

"Je ki ɗauko min"

"Toh! tana faɗa ta bar ɗakin da sauri.

~~~~~~~~~~~~~

Safa da marwa take yi a tsakiyar falon,"Taya zan saka shi ya manta da ita? ta ya?

"Yaya yana da taurin kai naci,waiyo allah na taya? nannauyar ajiyar zuci tayi,"""koma taya sai na aiwatar da abinda nai alƙawari, Malama Haulat ba zaki iya yin nasara akai na ba,yanzu taƙamar ki yana son ki ,to zanga abinda zaki yi idan ya manta da ke"

"Waiyo allah yanzu ta ina zan fara yaya murɗaɗan mutum ne,ya zanyi? ya zanyi? dafe kanta tayi rashin madafa yadda zata ɓullowa al-amarin.

"Farrah! ta faɗa a gaggauce,"na kira farrah ,to me zance mata? "na gayamata gaskiya,a'a yawwa nasan abinda zan faɗa mata"

Da sauri ta haye sama,kai tsaye ɗakinta ta nufa naiman wayarta ta shiga yi da kira farrah.

Hango wayar tayi a gaban mirrow ƙarasawa gurin tayi,ta dau wayar number farrah ta shiga naima,ringin ɗaya tayi farrah ta ɗauka "Hello farrah pls ki zo yanzun nan akwai maganar da zamu yi me muhammanci."

Cikin zaƙuwa farrh ta ce"ki natsu abin sai ahankali da sannu zaki saba.",dariya tayi sosai.

"Mtseww ke fah banza ce,na saba uwar me?ni idan zaki zo ki zo."

"To fah ai da gudu kuwa ko dan nasha lavari zan zo,yanzu kuw." tana faɗa ta kashe wayar.

~~~~~~~~~~~~~

kyakyyawan ɗaki ne mai ɗauke da kalar fari zalla ,komai na ɗakin fari ne fess irin farin nan me haske,kallon gurin nayi da kyau sai naga kamar na taɓa ganin gurin,to bari dai mu gani.

Kwance suke akan makeken gadon su,kanta na kan lafkeken ƙirjin shi ,mai ɗauke da kwantaccen baƙin gashi,gashin kanta yake shafawa cikin zalo so.

"Ina sonki! ki rayu da ni,zan kula da ke fiye da yadda zan kula da kai na,ki aminci da ni."

Hasken dake ɗakin bai bari ya gane yadda fuskarta take ba,a hankali ya fara sarrafa hannayen shi a sassa jikinta ba inda bai taɓa ba a jikinta,kasancewar ba kaya ajikin ta,wani irin nishin daɗi suke yi,charrab ya tallabo fuskarta bai sha wahala ba gurin haɗa bakin su,cikin zaƙuwa suke kissing ɗin junan,lokaci daya suka rasa natsuwar su,bakin shi yakai🤦‍♀ya dinga kissing,gaba ɗaya ya fita haiyacin shi.

jan jikinta ta fara yi,"A'a ni ka gyale ni"

Cikin wata irin murya wacce baiyi tunanin abinda zai faɗa zai fito ba ya ce"Sorry don't do ds to me,i need u ,plss try to understand."

bata saurari magiyar da yake mata ba,ta cigaba da janye jikinta daga nashi.

Wani irin nishi mai ɗauke da kuka ya fara faɗi,"I need dan allah ki tausaya min karki barni srry i beg u."

Ita ma kukan ta fara yi "No i can't stay with u let go of me ."

Da ƙarfi ta tureshi ta tashii,hasken da ke ɗakin bai bari yaga inda tabi ba.

Kuka mai tsuma zuciya ya fara yi yana faɗin,"Pls i need u!i need u! don't like ds."

Zummbuurrr! ya miƙe daga barcin da yake yi,da kalmar" i need u" a bakin shi.

Wani nakasaccen numfashi yake futarwa ,gaba ɗaya jikin shi rawa yake yi,ga uban zufa da ta wanke dukkan jikin shi,ga yadda zuciyarshi ke zafi,inda sabo yaci Naufal ya saba da irin mafarkin da yake yawan yi,amma kullum abun zabo yake zuwar mishi,na baƙinciki da takaicin barinshi da take yi a lokacin da yake matsanaicin muƙatar ta.

Cikin wata irin murya ya ce"Meyasa?idan kinsan haka zaki dunga min meyasa kike zuwar min,abin yana ɗauremin kai,kullum ke kike zuwa inda nake kuma ki ban kanki but sai kinga na shiga wani hali sai ki tafi ki barni, whay?

Nidai na ce shirme wa kake tambaya.

ganin ba wanda zai bashi amsar daye buƙata yasa shi ya tashi jiki ba gwari ya faɗa ban ɗaki.

Cikin Sauri Farrah ta tashi ta fara shiri,bayan ta gama shiryawa ta fito falo.

Momy ta kalle ta "Farrah ina zuwa haka kina ta sauri."

"Momy gurin Sabrewn."

"Zaki je ki takura musu ko."

"A'a wllh momy ita ta kira ni."

"Ta kira ki kuma lafiya dai?

"eh lafiya halan wani abun ne,shine nake son zuwa naji."

"To ki gaidar min ita da sosai."

"To zata ji insha allah."

tana faɗa tai gaba abinta,direba yakai ta,kasancewar ba wata lafiya a tsanin su ,yasa ta isa gidan cikin ƙanƙanin lokaci,tana iya fallon ta kirata a waya.

"Hello kina ina na hauwo ne.?

"kin iso ne? ki shigo ina ɗaki." ta katse wayar.

Saman ta hau,tana shiga ta ganta akan gado washe baki tayi"Amaryar mu kinga yadda kika yi kyau kuwa gaskiya amarci ya amshe ki."

Harara ta banga mata"Ke dai halinki sai ke."

"Yoou daman ai halin mutum sai shi."

ƙarasawa kan gadon tayi ta zauna ,tana kallon Sabreen ɗin tana murmushi.

"To gani a bani labarin."

saida ta doke ta a cinya sanan ta ce"Ke banza ce wllh,labarin me zan baki,ni idan zaki natsu ki gayamin abinda zan tambaye ki to,idan kuma ba natsuwa zaki yi sai ki gayamin."

"Zan natsu."

Natsuwa farrah tayi ta tattara dukkan natsuwarta akan Sabreen.

Ganin hakan yasa Savreen ta ce"Am.am..kinsan me?

"A'a hmm Yau Sabreen ki magana cikin inda-inda,kin chanja daga savreen ƴar aljannar da na sani."

"Na chanja taya zan chanja ina ban chanja ba niɗin ce dai ƴar aljanna shalelen Hajia",a zuciyarta tayi wanan maganar.

"Kiyi magana Sabreen ko da gaske kin chanja ne."

"Hmm ba zan chanja va,farrah ni ɗin ce dai..

"Na sani ba ƙaramin abu ne zai iya chanja ki ba,amma naga kina dabur-dabur ne,ko maganar ce kika rasa ta inda zaki faɗa min?

"Eh Farrah na rasa ta inda zan fara ne."

"Sabreen ki natso ni ƴar uwarki ce karki ji komai ki gayamin kai tsaye abinda ke ranki."

Kallon Farrah Sabreen tayi ta ce,"Kin san yayah ba ni yake so ba akwai wacce yake so,to shine nake son ya manta da ita,kuma bansan ta inda zan fara ba."

Dariya farrah ta fara yi sosai harda kwanciya kan gadon.

Rai a ɓace sabreen ta ce,"meye haka farrah kin abinda bana so kenan ina magana ana dariya."

Cikin dariyar farrah ta ce,"Ni mamaki ba kika bani."

"Mamaki me kefah banza ce."

"Ba dole ba wai ƴar aljanna ke tambayat yadda zata sa mutun ya manta da wani,bayan kin fini sani."

Tsaki Sabreen tayi "da na sani da zan kira ki ne."

"Kin sani savreen baki na tuna miki."

Zaune ta tashi da tsaida dariyarta ta ce"Sabreen kin iya kiss kisisi shagwaɓa duk wani salon jan hankali kin iya,to da su zaki yi amfani ki sa yaya ya manta da budurwar shi cikin ƙanƙanin lokaci,Sabreen ba zaki sha wata wahala ba gurin mantar da shi akan ko wacce mace domin kin samu dama duk yadda kika yi da shi dole yayi ko da bai so ba,kinga wanan babbar dama ce,idan kina so ki mantar da shi akan ko wacce mace dole sai kin kusance shi kin jashi a jiki kin nuna mishi kulawa."

"Ba abinda bazan iya yiba idan har sai sa ya manta da malama Haulat." A zuciyarta tayi maganar.

Hannuwanta Farrah ta riƙo cikin kulawa ta ce,"Sabreen kina son yaya ya manta da budurwarshi."

"Sosai ma kuma cikim ƙanƙanin lokaci."

"Yawwa to bari na gaya miki abubuwan da na sani,ya zama dole ki tausassa kalamanki nasan ba'a ɗaki daya kuke kwana ba ,to kiyi yadda zaki yi ku dunga kwana ɗaki daya shi,kuma ki hana shi zuwa gurinta,ki kusance shi sosai duk inda yaje ki bishi,kissa kisisi na yaudara shagwaɓa ki dinga mishi ba zai baki wahala,kin gane inda na nusa."

"Kina ganin hakan zai yasa ya manta da ita kuwa?

"ki yarda da ni tabbas idan kika yi hakan zai manta da ita."

"To bari na jaraba."

"Sabreen karki ce haka lallai ki ɗauka hakan zai mantar da shi ita."

Murmushi Sabreen ɗin tayi dan jin daɗi "Hmm ni fa ƴar aljanna cikin ƙanƙanin lokaci zan saka ya manta da ita."

Dariya Farrah ta ce,"Yaya fa an shigo hannun manya,"

haka suka cigaba da firar su cikin jin daɗi da nishaɗi da kula da junan su.

~~~~~~~~~~~~~

Bayan ya fito daga bayin ya shirya tsabba ya ɗauko wayar shi pic ɗin Haulat yake kallo ya kasa gane dalilin da yasa yafi jin daɗin kallon pic ɗin Savreen akan Haulat,yana cikin kallon pic ɗin kiranta ya shigo ya daɗe yana kallon sunan da yasa mata,kafin ya ɗau waƴar ita ta fara magana.

"Hello dear!

Saida ya lumshe ido dan dalin muryarta.

"Ya kike?

"Ba lafiya ba,meyasa Naufal,"cikin raunanniyar murya tayi maganar.

Hankalin shi ya tashi jin yadda take maganar a ruɗe ya ce,"Kiyi hakuri Haulat kin san ina sonki ba zan iya miki haka ba,Dady na ne ,amma kin san ina sonki ke ce ra'ayina."

Gaba ɗaya farinciki ya mamaye ta duk wani baƙinciki ya kau,ji take kamar bat taɓa shiga cikin ƙunci ba.

Cikin wata irin sigar da ke ɗaga mishi hankali ta ce,"Na sani Naufal ka kwantar da hankalinka bana son ka shiga damuwa."

Yadda tayi maganar ya kashe mishi har tsigar jikin shi saida ta tashi.

Lumshe ido yayi ya ce,"Tnx dear nasan zaki fahimta,karki damu zanje gurin hajiya babba(Wacce ta haife momy) akan maganar auran mu nasan zata samu dadyna da maganar kuma nasan zai aminci."

Ko kaɗan Haulat bata son ayi mata maganar aure dan baya ganta,shiyasa bata ji daɗin mgnr shi ba,tadai ji daɗi da ya nuna mata yana son ta.

"Yaushe zaka zo,?bani da lafiya fa!

"Subhananllah meye sa meki?

"Hm ciwon son ka da kishinka tun ranar ina nan kwance sai yanzu ta tashi."

Saida yayi jimm shi ya yarda da son da haulat ke mishi na gaske ne,cikin sigar tausayi da ban baki ya ce mata,"Sorry zan zo yanzun nan,ba amfanin wahalar da kanki domin ni naki ne ke kaɗai ba wata maccen da nake so ,ke ce muradi na ra'ayina."

Gaba ɗaya ya kashe mata ji da kalamanci waɗan da suke ƙara narkar da ita,cikin murjar jan hankali ta ce"Okkk sai ka zo dear."

Ta katse wayar,daman ya gama shirin shi tsaba key motor kawai ya ɗauko sanan ya sauko ƙasa,a falo ya haɗe da su Sabreen da farrah.

Farrah tana ganin shi ta miƙe ta ce," ina wuni yaya?

"Lafiya lau ya hajia?

"Lafiya lau tana gaida ku."

Kallon Sabrewn farrah tayi ta ce,"To zan tafi sai anjima."

"To ki gaida momy da Dady."

"Zasu ji." tana faɗa ta wushe abinta.

Shi ma kai yasa zai fita da sauri ta ce,"Yaya ina zaka je,zan biki tsoro nake ji."

Kallon ta tayi kamar zaiyi mgn sai ya fasa ta ya juya abin shi.

"Yaya Naufal!

Banza yayi da ita ya fice abinshi.

Wani ƙululun takaici ya kama cikin faɗa da ɗacin rai ta ce,"Ni nake ma magana kayi banza da ni,wllh yaya kayi sa'a dan ina son cika kudiri na ,amma da ba zan yafe maka ba,yanzun ma ba yafewa zanyi ƙafa zan ɗaga ma,kuma ba zanyi fushi ba duk abinda zaka min har sai na mantar da kai waye Haulat a rayuwar."

Kamar yana gaban tayi maganar tana gamawa ta hau sama cikin fushi.

~~~~~~~~~~~~~

Momyn su Haulat muguwar macce bara ilimi da imani bin bokaye ɗabi'ar gadon gidan su ne,Dadyn su haulat mutum ne kamili mai rikon addini da sanin ya kamata ɗabi'a ƴan boko bata dame shi ba,tun kafin suyi kuɗi,kullum burin shi yaga yaran shi suna riƙo da addini,yana kwaɓa musu idan suka kauce hanya,wanan dalilin yasa momyn mai suna balaraba ta asirce shi,sai yadda tayi da shi baya iya yin komai daga ita har yaran basu jin tsoran shi ko kaɗan.

Haulat ita ce babba wanda yanzu tana da shekara ashirin da shidda a duniya,tun tana candy ta fara lalewa da bin maxa lokaci har jami'a,halayen ta iri ɗaya sak da na mahaifiyara,har tafi mahaifiyar ta taƙama fariya gadara uwa uba wulaƙanci da alfahari ,Salma ita ka bi mata ita ma halin su ɗaya,sai auta sakina baiwar allah mummuni ga tausayi saboda halinta yasa basu sonta ko kaɗan dan tana faɗa musu gaskiya.

"A lallai kinji sauƙi irin wanan waahe baki haka." cewar momyn haulat wacce ta shiga ɗakin haulata ɗin dan duba jikin ta.

Ƙara faɗaɗa fara'arta tayi ta ce,"Eh momy naji sauƙi,Naufal zai zo gani na yanzu."

"Kunyi waya ne? ki son shi sosai,sai yaushe zamu je gurin bokan.?

"A'a tukun na dai,yana so na sosai momy."

"Hmm haryanzu da sauran ku."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull