Kenza eBookz

Nida malamata complete - Chapter 6

Nida malamata complete - Chapter 6

Nida malamata complete Chapter 6: Nida malamata complete Chapter 6. Bata san lokacin da wayar ta faɗi a hannun ta ba,jikin ta ya fara rawa,Ita kuwa Savreen…

4,471 words

Bata san lokacin da wayar ta faɗi a hannun ta ba,jikin ta ya fara rawa,Ita kuwa Savreen ko a kafaɗar ƙafarta.

A haka suka isa Gidan su ya fara sauke ta,sanan ya zo gidan na su.

Hankali kwance tayi wa Farrah Sallama harda faɗin "Sai goben kenan,ki fito da wuri"

A tsora ce farrah ta ce" toh"

Ba wanda ya kalli juna a cikin su.

~~~~~~~~~~ Ta isa falon ta hango hajia zaune akan kujera.

"Hajiyata ya baki tasu kin min oyoyo ba"

Ganin hajia wani iri yasa ta ce"Hajia lafiya?

Saida ta ƙaraso gurinta ta rungumeta"yanzu shikenan xaki barni ni kaɗai"

"Waya gayamiki ba inda zani ina nan"

"Zaki barni mana,zaki koma gidan Naufal"

Gabanta yai mummanan faɗuwa"zan koma gidan Naufal"

"Eh tare zaku dunga yin komai"

Ai sai hawaye ta ƙara rungume hajia,tana kuka ita ma hajiar kuka take yi,basu iya lallashin junan su ba,saidai gajiya suka yi da kukan,a ɗakin Hajia ta kwana.

~~~~~~~~~~~~~

Naufal ƙasa barci yayi abin duniya ya dame shi.

"Meyasa Sabreen zata min haka? "Yanzu ya zanyi da Haulat na mata alkawarin aure? Ba zanyi iya rayuwa da Savreen a matsayin matar aure na ba?

"Haulat nake so, ita ce zaɓina ita ce ra'ayina"

Tsanar Sabreen tana ƙara yawa a ranshi,amma na banza tunda ba abinda zai iya"Ban taɓa ganin irin wanan rayuwar ba"

"Sabreen sai kin gayamin dalilinki na ɓata rayuwa"

Ƙasa barci yayi duk tsawon daran ganin abu yana son mishi yawa yasa ya tashi ya ɗauro alwala ya fara sallar ko ya samu sassauci,ya kowa samu raka'a shidda yayi barci yai awan gaba da shi.

~~~~~~~~~

Tun a masallaci suka fita shi da Dady.

Yau Juma'a Yau ne ya kama bikin Sabreen muh'ad mai taƙama tare da Angonta Naufal mai taƙama.

Gaba ɗaya Abuja da kewayan ta sunyi labarin wanan bikin kuma suɓ hallara,ƴaƴan government tana manyan yan kasuwa da na ma'aikata duk sun hallara,dubbanin mutane ne suka hallara gurin ɗauren Auran.

Chan na hango Naufal cikin Shadda purple harda malum-malum kayan sun mishi kyau matuƙa,amma kallo ɗaya zaka ma fuskarshi ya gane yana cikin wani yanayi wanda ba wanda zai iya tantance wa,amma yanayin yafi kama da damuwa,kusa da shi Dady kalar kayan su iri daya komai da komai,kai ka ce Dady ne Angon dan yadda yake washe baki yana farinciki. Ƙarfe biyu za'a ɗaura Auren wanda yanzu saura minti ashirin da takwas a ɗaura auren.

~~~~~~~~~~~~

Da gudu ta faɗo ɗakin a ruɗe tana haki tana nishi "Haulat Haulat!!

Haulat wacce ke kwance tana mulka barcin ba abinda ke damunta.

Ganin ba zata tashi ba yasa ta ɗaka mata doka a baya "Haulat ke tashi banza kina nan kina barci baki san abinda ke faruwa ba"

"Ke dallah kinsan bana son ina barci a tashe"

"Au haka zaki ce ko"

"To me ya fara?

"ina ce Naufal ɗan Alhaji mai taƙama ne saurayinki?

Yamutsa fuska tayi"Eh shi ne lafiya dai

"Hmm ina lafiya to wllh yau za'a ɗaura mishi aure yanzu haka an hallara gurin ɗauren Auran..

Tsaki Haulat taja"Ke ni bana son irin wanan abun kawai zaki so ki ɗaga min hankali"

"Haulat kenan kina ganin wasa ne to shikenan ba zan matsa miki akan sai kin yarda da ni ba,amma nasan gaskiya zata baiyana,tana faɗa ta fita daga ɗakin.

Ita kuwa Haulat ƙara komawa barcin ta tayi,ko a jikinta.

Ƙarfe biyu daidai aka ɗaura auran Naufal da sabreen fiye da mutane dari sun shaida ɗaurin auren.

Tunda aka ɗaura auran jikin Naufal yayi sanyi zuciyar shi sai faman bugawa take yi,kamar wanda ya tashi daga dogon jinya haka ya ke ji.

~~~~~~~~~~~ Zaune take akan gadonta tasha kyau har ta gaji,ita kanta jikinta yayi sanyi"hmm ko bakomai yanzu na ɗauka fansa akan ki Malama Haulat tunda na aure wanda kika fi so a duniya kina ji kina gani ba abinda kika iya akai,Naufal ni ba tsarar auranka ba ce kamar yadda nasan kai ni ba ra'ayinka ba ce,dan haka bazan zauna da kai ba,nan da ƴan wasu lukuta kaɗan zan rabu da kai"

"Aunty Sabreen tunanin me kike yi"Farrah ta faɗa ta ƙarfi haɗe da jijjiga Sabreen ɗin.

"To meye na tunani bayan an ɗaura auran Naufal ya zama naki ke kaɗai,ko tunanin rabuwa da hajia ne"

Harara ta mata"Ke baki jin magana ko nace karki kira ni da Aunty ki"

Dariya farrah tayi sosai ta ce"Maida wuƙar ƴan mata"

~~~~~~~~~~~~~ Ba su suka samu damar zuwa gida ba sai ƙarfe biyar da wani abu,suka shigo gidan lokacin ba mutane sosai a gidan,kowannen su ya nufi ɗakin shi.

Yana zuwa ya faɗa kan gado,haɗe da sauke nannauyar ajiyar zuciya,ya daɗe a haka yana tunani Tunanin Haulat kawai yake yi ita yake so ita ce ra'ayin shi ita yake da burin ya aura"bazan karaya ba Haulat ina sonki zan kuma aureki dan ke ce muradin raina" ya fili ya faɗa.

Ringin ɗin wayar Dady ne ya shigo wayar,yana ji ya ɗauka

"Naufal karka Zauna fa akwai dinner da za'ayi karfe shidda kayi sauri ka shirya sun gama shiri kai kawai suke jira gidan hajia zaka ku tafi tare da Sabreen ɗin" yana gama faɗa ya kashe wayar shi.

"Why Sabreen? i cant i cant,ba zan iya rayuwa da ke ba Sabreen" idanowan shi sukai jajir.

Da gyar ya iya sarrafa jikin shi yayi wanka ya fito,kallon kayan drower ya tsaya yi ,ya rasa wanda zai saka,wata baƙar suit ya ɗago mai haɗe da ash colour ya saka sun mishi kyau ainun,kallon kanshi a madubi yayi.

"Wai ni aka ɗaura wa aure da Sabreen yanzu ni mijinta ne?

ya nuna kanshi"Ni Naifal nine mijin Sabreen"

Ƙasa yayi da kanshi yana sauraran bugun zuciyarshi wanda take buguwa da ƙarfin gaske.

Turaran da ya shafa sunfi kala goma ta ko wacce gaɓa ya shafa mata turaran da ake shafawa.

Bayan ya gama shiryawa ya fito cikin ƙasaita da izza yana tafiya kanshi aƙasa,baiyi mamaki ba ganin ba kowa a falon,yana fita yaga motoc irin na alfarma gudu shidda kalar su ɗaya ash colour irin kayan shi,sun ganin fitowar shi daga gidan suka fito,suka buɗe mishi kofa ya shiga cikin isa da mulki.

~~~~~~~~~~~~~

"Sabreen ki saka wanan kalar tafi kyau"

"Ke ni bana son shi,wan xan saka,ta nuna wata dugowar riga baƙi da ash kala,rigar ta haɗu iya haɗu

"To bana matsa miki ba Amarya"

Tana saka kayan aka fara mata makeup waw masha allah ashe haka Sabreen ke da kyau ,tayi kyau har ta gai.

Ba'afi minti goma da gama makeup ɗin ba aka aiko Naufal ya iso su fito,taɓe baki Sabreen tayi.

Rigar dugowace sosai tana tafiya tana binta Farrah da hajia su suka riƙo ta har wajen gurin motorcin,motor da yake aka buɗe mata ta shiga,tana shiga wani irin sinadarin ƙamshi ya doki hancinta har saida ta lumshe ido.

Kusa da juna sosai suka zauna hakan ya ƙara haifar musu da matsanaicin bugun zuciya,kowanne yana jin fitar numfashin kowa

"Bata sonka ko kaɗan"

"Na sani kuma kema kin san bana sonki" "But why Sabreen?

Bata kalle shi ba,daman ko ɗazun bata kalle shi ba"Saboda ɗaukar fansa"

wanan karon saida ya kalleta ,zuciyarshi ta buga dan ta bashi tsoro ganin irin kyaun da tayi gashi kalar kayanshi ta saka,cikin wata siga wacce shi kanshi bai san lokacin da ya tsinci kanshi da shiga yanayin tausasawar ba ya ce"Sabreen!

Lumshe idanowa tayi tana jin daɗin yadda yake kiran sunanta a tata cewar da indiyanci yake kiran sunanta.

Shi kanshi saida yai jimm,bai san abinda ya yasa shi yin hakan ba,ganin bashi da niyyar magana ya ce tace mishi"Nima ba zan zauna da kai ba,zamu rabu ne,dan wata manufa na aureka,karka ji wani avu nasan baka so na ka kwantar da hankalinka zamu rabu"

Da mamaki yake kallonta kanshi ya ɗaure hali irin na Sabreen yana bashi mamaki yadda take mishi magana ma abin mmk ne har ya buɗe baki zai mata magana motor ta tsaya tana tsayawa aka buɗe musu kofa.

Yana sauko da kai idanowan shi sukai arba da ƙaton hutun su wanda suka yi matuƙar kyau mamaki ya ƙara kamashi ganin yadda Sabreen tayi murmushi a hoton kamar wacce take son shi,ga hoton yayi kyau kamar ba haɗa shi aka yiba,a tare aka yi shi.

Tana fitowa taga ƴan jarida da masu ɗaukar photo a ranta ta ce" Za'ayi vedio kuma za'a nuna a tibi,wanan dama ce"

Daman yana tsaye yana jiran fitowar ta,murmushi ta fara mai ƙyayatarwa tana kallon masu ɗaukar hoton su kuma sai ɗauka suke yi.

ji yayi ta riƙe mishi hannu da sauri ya juyo ya kalleta cikin mamaki,wani irin murmushi ta mishi mai ɗaukar hankali bai san lokacin daya maida mata da martani ba,a daidai lokacin wani mai hoto ya ɗauke su,suna kallon juna suna murmushi gashi hannuwan su a riƙe da juna.

~~~~~~~~~~~~~ Waw guri ya haɗu ya haɗe abin kamar ba'a 9j ba ,waiyo ni batula abun mamaki daga gefen hannun daman Sabreen sai ga shadow da my Aunty nabeela,waiwai su khadija da fatima shariff suma suna gefe mr parrot da hauwa sule bakin su yaƙi rufuwa ,hauwa'u da ramb kuwa suna gefe sai satar kallon Naufal suke yi,my sis khadija da nafisa kuwa suna kusa da farrah sai fira suke yi,Dr halimatu ma ta faso ita da jermielat , wai su hafsat da safiya abudullahi kuwa hankalinsu yayi gurin kaji, Aysha zango ita da mrs sunusi sai kwaso shoki shoki suke yi,ita kuwa sarauniya jidda ta saki baki tana kallon yadda Naufal ke yamutsa fuska.

Ina zan manta da ku yanzu dai na hango ku,cunkuso ne ya rufe ku iyalan jamliya,dan tsabar ɗauki tun ranar da Sabreen tace Naufal zata aura suka hallaro😅,daga chan gefe gudu kuma jamar batula fans novels ne suka baiyana suma ba'a barsu a baya ba,chan kuma sai ga iyalan bintu Ahmad wato ƴan gidan Shabihaty suma sun ɗan yi kara,iyalan lipton ma na hango wasu ƴan ƙaɗan,tawagar farida kuwa tun kafin a buɗe gurin suka iso,ƴan tangantakar mu,kuma na hango ku,amma ku da alama ƴan team ɗin Haulat ne,tawagar waye sila,kuma sannunku da ƙokari,wai ai idan ba'a ganku ba wa za'a gani😅iyalan tawan,ku da tun kafin a ɗaura aure kuka iso,chan taro ya fara nisa sai ga wasu gungumin al-umma,masu yawan gaske gashi ban gane su ba,gaba ɗayan jama'ar gurin kallon su ake yi ,kasa hakuri Sabreen tayi,ta tambaye su daga ina,

"Mu masoyanki ne masu miki fatan alkairi,muna da nisa amma haka muka ɗugunzumo mu tayaki murna,kuma ki miƙa mana gaisuwa gurin batula"

Suka gayamata haka sanan suka zamu guri suka zauna.

Taro yayi taro al'umma sun hallara taya Sabreen da Naufal murna,chan na hango wasu manyan mutane,tun isowar su aka fara buɗa musu hanya,Abin mamaki Sai na ga Aunty Nabeela ta tashi da murnar ta,guri na ta iso tana murmushi ta kalle ni ta ce"My batul zo muje ki ga waɗan da suka zo"

Kallonta nayi nai murmushi na ce"Toh muje my Aunty"

waiyo allah na wa zanga ni Sarah ce da alfaga da kuma mutumina Sul harda Ruƙaiya,nayi mamaki sosai ganin su gurin Bikin Sabreen.

Hhhh baku ga da Sarah da zauna kusa da Sabreen ba,kunga Sabreen kuwa sai tai wani irin mugun muni,to kyau na gaskiya ya baiyana a gabanta.

"Toh wai ko yarima mu'utasim ya zo kuwa?

hhhh to ya zan sani tunda ba ganinshi zanyi ba.

Ina cikin wanan tunanin Aunty nabeela ta ce min"My batul yarima mu'utasim yana gaisuwa"

A ruɗe na ce"My Aunty ya zo ne"

"Eh kin shiga ruɗani ne"

Wanan shine *Ruɗani* ,littafin Sarauniya beelat(My Aunty nabeela).

biki yayi biki Tunda manyan mutane suka hallara bikin harda su Yarima mu'utasim,na so ganin baba me gadi dan yaban dariya. . [12/16, 5:41 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/22, 5:26 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹

*By* *fatima* *Batula* *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

Page 11 ............................................................ _*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{WANDA YA RUFE WA MUMINI WANI SIRRI(NA LAIFI) KAMAR YAYI CETO NE GA WANDA AKA BINNE DA RAI!.}*_

```[Sahihut Targib;2337]``` ~~ _Duk wanda ya rufa ma mumini sirrinsa na laifi, bai ba mutane labarin abinda ya sani game da shi na sharri ba, to kamar an binne shi da rai ne sai ya ceceshi. Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

....................................................................................

Ansha shagalin baki abun ba'a cewa komai, sai wanda ya gani kawai.

Kallon ta kawai Naufal yake yi yana mamaki gashi sai washe baki take yi ,maganar da ta gayamishi yake tunowa"Bana sonka ba zan iya rayuwa da kai ba,na aure ka ne dan ɗaukar fansa"

A haka taro ya watse hankalin shi baya tare da shi abubuwa sai yawo suke mishi kwakwalwa ,daga sun haɗa ido ya su harara juna suja tsaki.

Ƙarfe Tara taro ya watse,kowa ya kama gaban shi,su kum suka ɗau hanyar zuwa gidan su hajia.

Kallonta yayi rai a ɓace ya ce"Sabreen meyasa kika min haka kin san bana sonki kika ce zaki aure ni"

Ɗagowa tayi ita ma ranta a ɓace ta kalle "Hmm to kai me kake tunani ,ni Sabreen zan iya auran haka kawai allah ya kyautamin da auran....

yaji zafin maganar matuƙa ya janyo ta jikin shi da karfi ya rungumeta ɓacin ran da yake ciki bai bar shi ya saurara feelings ɗin da yaji ba "Ke ni tsaranki ne zaki gayamin irin wanan maganar,ni wllh ko banga dalilin da zai sa na aureki ba,dan banga abinda zanyi da ke ba,ko a jerin mata ban saka ki ba,balle ki xama class ɗina,ke kanki kinsan ke ba aji na ba ce,banda kaddara da wallahi ko kallan ki bazan yi ba"

Ran Sabreen kai ƙololuwa gurin ɓaci idanuwanta sunyi jajir dan takaici gashi ya matseta,cizo ta ganna mishi a hannu da ƙarfin gaske da sauri ya sake ta.

Har yakai hannu zai janyota farrah ta buɗe kofar

"Am. .. sorry"

Har zata maida kofar ta rufe Sabreen ta fito rai a ɓace,gaba tayi ta barshi a ciki.

Wani ƙululon takaici ya kama shi,idan har haka sabreen zata tunga mishi bai jin zai iya riƙe alƙawarin Dady,ya daɗe a cikin motor kafin ya fito.

Yana isa falon gaban shi yai mummunan faɗuwa ganin kowa da kowa yana falon,har ya samu wani guri gefe zai zauna Dady ya ce mishi"Naufal matso nan kusa da matarka."

Ba Naufal ba ita kan Sabreen zaida taji haushi. Ba musu ya matsu kusa da ita ya ɗuka dan a kasa suke harda ita ɗin.

Dady yayi gyaran murya ya ce"Naufal mun gama magana da kai,ni yanzu ba abinda zan ce maka,illa na ƙara tunatar da kai haƙƙin aure wanda su ma kasan su."

Juyowa da kallon shi yayi gurin Sabreen ya kalleta duk da ƙarancin hasken da ke ɗakin amma yana hango fuskarta "Sabreen yanzu zaki shiga wata sabuwar rayuwa wacce baki saba yin irinta ba,abinda nake so da ke sabreen kinga Naufal ɗan uwanki ne,ki riƙe shi, ki mishi biyayya ki bi umarni shi wannan ce shine haƙƙin mata akan mijinta,nasan kina da hakuri amma sai kin ƙara,Sabreen ku riƙe junanku da amana,sanan duk abinda ya miki ki same ni ki faɗimin kina jina?

Ɗaga mishi kai tayi alamar taji.

Kallon hajia da Momy yayi ya ce"Toh baku da abin faɗi ne?

A hankali momy ta buɗe baki saida ta fara gabatar da addu'ar buɗe taro sanan ta ce"Naufal ba wata magana mai tsawo zanyi ba,kasan Sabreen marainiyace karka cutar da ita ka riƙe ta ƴar uwarka ce ,sanan wanan auren shi ne alkairi a gare mu da kai ma,bansan ko zaka fahimce abinda nake nufi ba,sabreena alkairi ce a gareka dan haka ka Naufal ka kula da Sabreen"

Tunda suka fara magana gaban shi ke faɗuwa,ya rasa wani irin tunani zai yi ma.

Hajiya kuwa kasa magana tayi sai kuka sabreen najin hajia ta fara kuka ita ma,ta fara yi,kusa da ita hajia ta zo ta rungumeta suna ta kuka ba wanda ya dakatar da su.

Naufal ma ji yake yi ina ma zai iya yin kukan da yayi ,dan shi ne abin kuka ba su ba.

Ganin basu da niyyar daina kukan Dady ya ce"Ya isa haka kuyi hakuri dole daman sai wanan ranar ta zo."

Kallon Naufal yayi ya ce"Naufal tashi ku tafi"

Gaban shi ya faɗi"Na tashi mu tafi"ya maimaita abinda Dadyn ya faɗa a hankali,shi kanshi zaida yaji wani iri wai yau zai bar gidan su ya kwana a wani gida daban.

Sabreen tana jin abinda Dady ya faɗa ta ƙara ƙanƙame hajia tana kuka mai tsuma zuciya.

Tashi momy tayi taje da riƙo Sabreen tana san ta rabata da jikin hajia.

"Waiyo hajia Momy dan Allah ,Hajia bazan tafi na barki ba,waiyo hajia ki riƙe ni,momy momy kiyi hakuri na fasa auran bana so Allah na fasa bana son ya naufal,hajiyata bazan tafi ba...

Duk da yanayin da suke ciki saida suka yi ƴar dariya,musamman Naufal da farrah A ran shi ya ce"Banza daman haka kike amma kika ce kina son aure n..

"Naufal zo ka jata" Dady ya katse mishi tunani. Hajiya ya fara ja dan baya son ya taɓa Sabreen. "kai ita zaka ja", Dadyn ya taɗa.

Hannun shi yakai kan kafaɗar ta,ya fara janta ,ita kuma momy taja hajia.

"Yawwa kamata ku fita",cewar dadyn

Kuka Sabreen take yi tana ihu "Waiiyoo! wllh Dady na fasa bana so,dan allah ku barni,na zauna da hajia bana son auren,Yaya Naufal dan allah ka barni bana so waiyooo"

Dariya ta bashi sosai har ya kasa ɗaurewa zaida yayi,ita ma farrah dariya tai tayi.

"Karka sake ta Naufal."

"To Dady."

Har suka fito daga fallon tana kuka,gurin shiga motor ma,saida momy ta turata da ƙarfi tana shiga aka kulle kofar,hajia bata fito ba tana chan tana rusa kuka an rabata da ƴar aljanna.

shiga motor yayi direba yaja suka fita daga gidan,Su momy suna nan tsaye har motor ta fita,sanan suka dawo suyi ma hajia sallama su koma gidan su.

Dariya Naufal ya fara yi sosai da sosai wanda bai taɓa yin irinta ba.

Ƙara fashewa da kuka tayi mai sautin gaske.

"ke dare ne ki mana shiru baki son rabuwa da ita kika ce kina son aure."

ys ƙara fashewa da dariyar shi.

Kuka Sabreen ke yi sosai bata kuma kula shi ba har suka isa unguwarsu,wani katafaran gida ne,wanan kallo ɗaya zaka mishi kasan ankace dala,dan ya fituno da kyau abin zai wanda ya gani.

Suna isa harabar gidan direban ya tsaida motor,shi ya fara fitowa"Idan kin ga dama ki sauko idan baki ga dama ba ya maida ke gidan hajia."

Yana faɗa ya shige abinshi yana tafiyar kasaita da izza.

Kamar ta ce direban ya maida ta gurin hajia sai kuma ta fasa ,ta sauko ta bi bayan shi a falon ta isko shi,tana kuka ta karasa gurin shi ta ce"Idan na koma zance kaika kuro ni,ka ce na dawo."

A fusace ya miƙe har zaiyi wata magana ya fasa tuno halin Sabreen ba abinda ba zata iya ba,wani mugun kallo ya mata sanan ya juya ya haye sama.

Har lokacin bata daina kuka ba,kallon falon tayi ya mata kyau sosai,kan gujera ta hau,tana ta kuka har barci ya ɗauke ta.

Daman yasan gidan ya kuma zaɓa ɗakin shi,yana zuwa ya shige saida yayi wanka yayi sallah sanan ya kwanta,ya daɗe yana tunanin irin zaman da zasu yi da sabreen sanan shi ma barci ya ɗauke shi.

~~~~~~~~~~~~~

"mtseww!

"Wai ke wa kike ma wanan tsakin tun ɗazun."

Wani mugun kallo tayi mata sanan ta ce"Ban sani ba".

taɓe baki tayi ta cigaba da yin abinda take yi.

Kallon wayarta tayi ta ce"Naufal meke faruwa ne?

ƙanwarta wacce suke zaune a ɗakin ta kalleta a ƙaro na biyu ta ƙara cewa"Ai daman na sani"

"Kin san me,banson iskancin banza."

Tana rufe baki saƙo ta whatssap ya shigo wayarta,kamar ba zata duba ba,dan baƙowar number ce.

Sai ta duba, a tsorace ta miƙe tsaye haɗe da zaro idanowa,xuciyarta ta fara bugawa da ƙarfin gaske"Wa.i..y.." Numfashin ta ya fara sarƙewa dushu-dushe ta fara gani.

"Aunty haulat lafiya mai ke faruwa? a ruɗe take tambayarta,ko kafin ta ƙarasa gurinta ta faɗi kasa zummama.

"Innalilahi! momy momy Aunty haulat mun shiga ukku.

~~~~~~~~~~~~~

kiran sallar farko a kunnan Sabreen a ruɗe ta fara tambayar kanta "Nayi Sallah jiya? "Innalilahi ta faɗa da sauri ta miƙe tuno bata yiba,saman ta hau a ruɗe ,kasancewar bata san wani ɗaki ba ne tashi ta faɗa dakin shi,bata ma lura da yana kwance akan gadon ba tayi toilet da Sauri.

Jin ƙarar ruwa ya farkar da shi,kunna guluf mai hasken yayi,"waye a baya" ya faɗa a hankali saukowa yayi,sautin tafiya taji a tsorace ta ce"Waiyo Allah na waye"

"Ke meye ya kawoko ɗaki na?

"Bansan ɗakin ka ba ne"

"Bakin san ɗaki na ba ne".

"eh!

"To fito nima zan shiga ne".

"Waiyo karka shiga ya hakuri dan allah dan allah".

Dariya ta bashi a ranshi ya ce "Kamar wata wacce zan ga wani abu ƙwaila da ita"

Murmushi ya fara yi tuno hali irin na ta,mawuyacin abu ne ta ba mutum hakuri,amma yanzu harda wani haɗa shi da allah.

"To na baki minti biyar kafin na dawo ki fito"

Yana faɗa ya juya yana murmushi.

Tana jin ya fita ta fito da sauri,ta faɗa ɗayan dakin wanda ba tazara a tsakanin su da juna,tana shiga ɗakin ta kulle,kallon ɗakin ta tsaya yi,ganin zai shagaltar da ita yasa ta maida hankalinta akan abinda zata yi.

Yana dawowa yaga bata nan daman yasan ba ganinta zaiyi ba,shiga toilet ɗin yayi ,saida yayi wankar tsarki sanan ya fito ya gabatar da ibada.

Zaune yake kan sallayar yana hailala da tasbihi wa ubangijinki,tunanin Haulat ya shigo ranshi zumbur ya miƙe ya fara naiman layinta...

Ringin wayar tayi har ta katse ba'a ɗauka ba,tsoro ya kama shi,tunda yake da Haulat bata taɓa ƙin ɗaukar wayar shi,cikin hanzari da zaƙuwa ya ƙara kira,nan ma shiru ba'a ɗauka ba,saida yai kira biyar abinda bai taɓa yiba ,amma shiru ba'a ɗau wayar ba,jefar da wayar yayi akan gado ransh a ɓace,haɗe da hura hanci.

"Haulat Allah yasa kina lafiya? "Taya zata kasance cikin lafiya bayan abinda ka mata."

Da kanshi yayi tambayar kuma ya ya ba kanshi amsar da ta ƙara ruɗa shi,yasan bai kyauta ma Haulat ba,ya kamata ya sanar da ita koma meye,yanzu idan taji a bakin wani fah.

Tashi yayi ya fara safa da marwa a tsakiyar ɗakin,lissafin shi duk ya dagule,kanshi yayi zafi tunanin halin da masoyiyar shi take ciki yake yi,wanda ya ɗaura laifin akan Sabreen ko kaɗan baya jin zai iya raga mata kan abinda da mishi,zumbur! kamar wanda aka tsungula ya fito da sauri,bibbiyu yake taka matalakar dan sauri,har ya iso cikin falon bai kula da mutanan dake ciki ba,ya fara ƙokarin fita.

"Ango Naufal ina kuma zaka je ka bar amarya ita kaɗai."

Tsayawa chikk yayi sakamakon jin muryar ko ta wacece,a hankali ya juyo dan ƙara tabbatarwa zaro ido yayi ganin ba ita kaɗai ba..

"Naufal saurin me kake yi,baka kula da mu ba."

Momyn shi ta katse mishi tunanin shi,kallon su yayi,Hajiaya ce ita da Momy da farrah sai Sabreen ɗin wacce ke manne a jikin Hajia, "Meye kuma ya kawo su da safe haka? taya zasu zo mana gida a irin wanan lokacin jiya ne fah muka tare", a ranshi yake wanan tambayar,"To meye wani abun zamu yi waɗan da ba son juna muke yiba",duk a zuciyar shi yake wanan tunanin,bai san lokacin da ya ƙaraso tsakiyar falon ba,sai jin shi yayi zaune a ƙasa,cikin harɗaɗiyar murya haɗe ta aro murmushi ya yafawa fuskar shi ya ce"Ina Kwana momy."

Bai tsaya jiran amsarta ba ya juyo da kallon shi ga hajia ya ce"Ina kwana Hajia ya gajiya."

yana kai aya hajia ta ɗauka"Lafiya lau Naufal ka barni da kewa shi ne ko tambayata baka yiba,au naga kamar ba baka so ganin mu yanzu ba."

Kallonta yayi ,yana tuhumar kanshi akan maganar da ta gayamishi ,a fili ya ce haɗe da ɗan guntun murmushi, "Ba haka bane hajia,ya kewa?

"Ba sauƙi jiya ban iya barci ba ,da zan iya da nayi kishi da kai"

Gaba ɗayan su sukai dariya banda Sabreen wacce ta murtike fuska.

"yi hakuri Naufal munzo kawo abinci ne da farrah zata kawo to sai hajia ta ce tana son zuwa."

Murmushi yayi ya ce"Ba komai Momy."

"Amma ina kake ƙokarin zuwa?

"Am..amm..da. amman daman zanje gurin hajia ne na samo mata abinci bata ci komai ba."

ya faɗa yana kallon Sabreen ɗin yana mata guntun murmushi.

Charab hajiar ta ce"Hm to na hutar da kai,amma naji daɗi da kake nuna kulawarka akan Sabreen na gode Naufal Allah ya biyaka da aljannar shi."

"Ba komai Hajia ko kin manta Sabrewn ƴar uwata ce,zan iya yin komai a matsayinta na ƴar uwata,sanan kuma matata! daidai gurin yji zuciyar shi ta buga ƙara maimaita kalmar yayi "Matata!

Wani irin kallo Sabreen ta mishi na mamaki,shi ma ɗago kai yayi suka haɗe ido mugun kallo suka yiwa junan,amma sai suka yi murmushi.

Wani irin daɗi ya mamaye Momy wanda ta kasa ɓoyewa sai yaƙar baki take yi,kamar Ango.

Ita kanta farrah dake gefe murmushi take yi,dan jin daɗin yadda naufal ya aminta da ita cikin ƙanƙanin lokaci haka.

Wai kuma kunsan farinciki gurin hajia ba sai ance komai ba.

Sun ɗan taɓa fira kaɗan,sanan momy ta kalli hajia ta ce"Hajia to mu tafi ko,yadda zasu sake su iya cin abincin da kyau."

Kallon momy yayi a ranshi ya ce"Hm wai mu sake kamar wasu masu cin amarshi."

Sabreen naji abinda momy ta ce,idanowan ta sukai jajir kwalla ta shika su famm,cikin murmuyar kuka ta ce"Hajia yanzu tafiya zaki yi."

Momy ta ce"Kinga idan kuka zaki dunga yi,xata daina zuwa,muma zamu daina zuwa,kina son gobe ta zo?

ɗaga mata kai tayi alamar eh.

"Toh idan kina so ta zo gobe,kiyi shiru."

"Tohhh! kawai ta faɗa.

Kallonta hajia tayi ita ma hawayen ne a idonta ta ce"Kiyi shiru kinji ga mijinki nan zai tayaki zama,kuma baga waya ba,sai ki kira ni mu gaisa."

"Ba zaki xo gobe ba."

"zan zo."

A tare suka fita fita har harabar gidan,suna kallo suka shiga motor,Sabreen sai hawaye shaaa kamar famfo,ko kallon inda take baiyiba ya juyo ɗakin,yana zuwa ya janyo kulolin abinci ya fara ɓuɗewa,kunon gyaɗa ne sha madara sai waina da miyar ita kanta wainar sai tashin ƙamshi take yi,miyar ma haka ga nama zaƙo-xaƙo,sai dangalin turawa soyayye da dafaffe wanda ya haɗe da hanta, sai kuma farfeson kaza,da soyayyan gwai harda lipton,kallon abincin yake yi yana yamutsa fuska kamar wanda yai arba da ɗanyan kashi.

Kunon gyaɗan da waina ya xuba ya fara ciki,yana cikin ci Sabreen ta shigo,kallon shi ta tsaya yi.

"Waya ce ka cimin abinci ai ba kai aka kawo mawa ba."

Bai ɗago ba balle ya tanka ta,saida ya gama ci ,tana kallon shi yana hura hanci kamar warin abincin yake ji.

Yana gamawa ya tashi saida ya fara goge hannunshi da hankey sanan ya tashi har lokacin bai kalla inda take ba.

"Ina zaka?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull