Nida malamata complete - Chapter 5
Nida malamata complete Chapter 5: Nida malamata complete Chapter 5. "Tabbb gaskiya momy da kamar wuya a ƙi samun matsala dan Yaya ma yana da budurwa"
4,491 words
"Tabbb gaskiya momy da kamar wuya a ƙi samun matsala dan Yaya ma yana da budurwa"
Jikin momy ya mutu "Waya gaya miki yana da budurwa farra?
"Yasan da maganar auren?
"A'a me sani ba"
"Hmm to saidai kawai muyi addu'a dan yaya dai baya son Sabreen ita ma ɗin,amma zasu dace ita ce daidai ce,idan ya fara sonta zai chanja,na kam naji daɗi bari ma taje gurinta"
Tana faɗa ta tashi jiki na rawa,ita kuwa Momy jikinta ya mutu tausayin Naufal ya mamayeta,amma ya zata yi.
Cikin zumuɗi da rawa jiki Farrah ta isa Gadan a falo ta isake hajia ta washe baki ta ce "Hajiya ashe muna da babban biki"
Ita ma hajiyar washe baki tayi "Bari dai farrah zamu sha biki ,ya hajiar ta ku"
"Tana lafiya ita ta gayamin ma,hajia ina Sabreen"
"Tana ɗakinta barci take yi,amma halan ta farka"
ai tun kafin hajiyar ta gama magana ta haye sama.
Tana isa ɗakin ta faɗa kan gadon"yeeeh Amaryar Yaya,shi ne ba za'a gayamin ba na shirya faty"
Sabreen tana jin Farrah ce ta tashi yana mutsike fuska cike da ƙarfin hali ta kalle farrah tana murmushi.
Dungurinta tayi akai tana dariya ta ce "Gayamin yaushe kika fara son mutumin naki?
Bata son ta gaymata dan kar da gayawa hajia,murmushi tayi ta ce"Tun shekaran jiya na nayi mafarkin shi"
Dariya farrah tayi sosai "Ah lallai wato mafarki wani irin mafarki?
"Ke nidai karki ishe ni,da tambayoyi kamar wata ƴar jarida,yanzu dai faty nake so a haɗa.
Ƙara farrah tayi"Yeehhh ai lallai ana son yaya Wai nifa abin mamaki yake ban Wai Sabreen ɗin d na sai ƴar aljanna ƴar gatan hajia wai ita ke son Yaya Naufal ɗan iyayi da kinibibi"
"To meye"
"A'a ba komai duk love ne,amma abin da mamaki fa"
"Ni kidaina mamaki ,ki tsaya muyi magana"
"To na tsaya Aunty Sabreen"
Doka sabreen ɗin ta kai mata"Waye Aunty?
"Sabreen amaryar yaya"
"Ke fa ai"
"Ni me? yaushe ne bikin naji ance cikin satin nan ?
"Jibi!
ƙara farrah ta buka ta haye kan Sabreen ɗin tana ihuu.
"Wai hajia farrah zata kashe ni"
ɗaga ta farrah tayi tana dariya "Lallai Sabreen tun yanzu to gaba wa zaki kira ya taimake ki?
Cikin rashin fahimta ta ce"Hajiata mana"
Dariya farrah tayi sosai ta ce "Akwai wata ƙawar momy tana gyaran jiki na amarya ya kamata momy ta kai mu gobe,abubuwan ne sun matse kamar wata wacce ta ƙagara za'a sa biki kwana ukku,haba ace mai taƙama family zasu aurar da yara biyu yaran ma ƴan gata ace ba abinda za'ayi haba,gaskiya ba zai yuwu ba yadda nake da buri akan bikin wani daga cikin ku"
Ta kai hannu ta doki cinyarta,ƙara Sabreen tayi"Ann Haba farrah ke mugu ce daman"
Dariya farrah tayi ta ce"Tab akwai aiki kuwa yaya zai wahala,to nidai gasky tashi yanzun nan mu je kasuwa,muyi siyayya ya kamata ma kuyi photo fa wanda za'a sa a memo da jaka da wanda za'ayi amfani da shi gurin faty"
Kallon farrah Sabreen tayi "to yanzu ya za'ayi"
"yawwa ina da pic ɗin yaya zai muje ki ɗauka sai a haɗa kamar kunyi tare,daga nan sai muje a haɗa mana memon da jaka"
"to bari ta saka kaya" ta faɗa tashi tayi daga kan gadon ta je gurin drower towel ɗin ya zamo.
"Waiyo ni gaskiya Sabreen yaya zai ja kaya irin wanan hips haka"
Cikin rashin fahimtar abinda Farrah ke nufi ta watsa mata harara ta ce"To yanzu ina zamu samu kuɗi?
"Dady zaki tambaya"
harararta ta ƙara "baki da hankali kawai sai na tambaye shi kuɗi.
"Ke nidai yi ki saka kaya kuɗi ba matsala ba ne hajia zata ba mu,momy ma nasan zata ba mu"
Tana sa kaya suka sauko ƙasa farrah ta gayawa hajia zasu fita su fara shiri,hajia taji daɗi sosai ta basu kuɗi sosai,har zasu tafi ta ce su jera tare zata gurin Momy suyi magana.
Ko da suka isa gurin momy ,momyn tana ganin su cikin farinciki ita ma farincikin ya kamata,musamman da taga Sabreen ta tuno da maganar da dady yayi"Idan har jini na ke yawo a jikin Naufal to jinin Sabreen ma yana yawo ajikin shi zai so ta idan har yana so na"
Hankalinta ya kwanta sosai,ta saka a ranta zai so ta ne.
Ita ma ta ƙara musu kuɗi masu yawan gaske ta kuma kira idan zasu je ai mata makeup sanan a haɗa hotonsu tare,kuma a haɗa komai da komai wanda za'a saka photon,kuma ta ce zata kama tsadaddan holl wanda za'ayi fatyn,sanan suka fito,ita kanta hajia daɗi ya mamayeta ainun.
. [12/16, 5:35 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/16, 5:36 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*By* *fatima* *Batula* Page 9
.............................................
*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_
_*ZIKIRAN DA AKEYI BAYAN IDAR DA SALLAH*_ : . _*(1)* -“Astagfirullahi” sau uku,(3)_ . _*(2)*“Allahumma Antas Salam, Wa minkas Salam, Tabarakta Yaa Zal Jalal Wal Ikram”_ _*[Muslim ne ya rawaito shi].*_ : _*(3)* -“Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir._ . _*(4)* Allahumma La mani’a lima aadaita, Wala mu’udiya lima Aaxait, Wala Yanfa’u Zal Jaddi Minkal Jadd”_ _*[Bukhari ne ya rawaito shi].*_ . _*(5)* -“Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir._ _La haula wala quwwata illa billahi, Laa ilaha illal Lahu, Wala Na’abudu Illa Iyyahu, Lahun ni’imatu Walahul Fadlu, Walahus sana’ul Hasan, Laa ilaha Ilal Lahu, Mukhlisina lahudden, Walau karihal Kafiruun”_ _*[Muslim ne ya rawaito shi].*_ : _*(6)* -“Subhanallah, Wal Hamdu Lillahi, Wallahu Akbar” Sau talatin da uku.33_ : _*(7)* “Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir”_ _*[Muslim ne ya rawaito shi].*_ : _*(8)* La Ilaha Illallahu Wahdahu La Sharika Lahu Lahul- Mulku Wa Lahul-Hamdu, Yuhyi Wa Yumitu Wa Huwa ala Kulli Shai'in Qadir.._ _*sau goma(10)bayan sallar Asuba da magariba*_ : _*(9)* -“Allahumma A’inni Ala Zikrika, Wa shukrika, Wa Husni Ibadatika”_ _*[Abu Dawud ne ya rawaito shi].*_ : _*(10)* - Karanta ayatul Kursiyyi, da suratul Al-ikhlas, da Falaqi da Nasi *dai- dai.......1 -1*_ _*Sanna (Sau uku-uku)3-3* bayan sallar magariba da asuba_ _*[Nasa’i ne ya rawaito shi].*_ : _*(11)* - Fadin “Allahumma Inni As’aluka Ilman Nafi’an, Wa zirqan Xayyiban, Wa amalan Mutaqabbalan”_ _*[Ibnu Majah ne ya rawaito shi]*_ _Bayan an yi sallah daga sallar asuba._ : _An kar6o daga *Aisha – Allah ya yarda da ita* ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana bude sallah da kabbara, karatu kuma da “Alhamdu Lillahi Rabbil Aalamin”. Hakanan ya kasance idan ya yi ruku’u baya daga kansa sama, kuma baya sunkuyar da shi qasa, sai dai yana sanya shi tsakanin haka. Idan ya dago kansa daga ruku’u baya sujjada har sai ya daidaita a tsaye, hakanan idan ya dago daga sujjada baya komawa sujjada har sai ya daidaita a zaune. Ya kasance yana faxin tahiya a dukkan tsakanin raka’o’i biyu. Hakanan ya kasance yana shimfida kafarsa ta hagu, ya kafe ta dama (a zaman tahiya). Ya kasance ya hana zaman shaidan (zama akan dugadugai), yana hana mutum ya shimfida tsintsiyar hannunsa kamar yadda dabbobi suke yi. Yana qare sallah : _*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ. ............................................. kallon Momy Hajiya tayi ,tana murmushi ta ce"Hajiya kinji yadda muka yanke shawara ba mu tambayi ra'ayinki ba"
"Ah haba Hajiya ba komai kun isa ne,kuma shawarar tayi daidai naji daɗi sosai, ubangiji Allah ya haɗa kan su,ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗaiyaba"
"Amin ya Allah"
"Bari nima na tashi ba'ayi biki haka ba,naje nayi siyayya na gaiyaci ƴan uwa da abokan arziƙi"
"To gaskiya kuwa abin ne yazo da sauri"
Bayan sun gama maganar su Momy ta kawo Hajia gidan ta,ita kuma ta wuce kasuwa daga nan ta tafi gidan su gurin iyayan ta.
~~~~~~~~~~~~~
Tun Safiyar ranar da Haulat ta tashi take jin ɓacin rai duk saboda Wayar Naufal a kashe tun jiya da ya kashe bai kunna ba, da safen ma ta kira bai shiga ba,ranta ya ɓaci haka nan ta tafi makaranta ranar student sun sha zagi da bala'i ,ganin bata ga Sabreen ba yasa ta ɗan ji daɗi,amma bata ji labarin wani abu ba,akan sharrin da ta haɗa mata ba.
Tun a makarantar ta kira shi yafi sau biyar amma yaƙi ɗauka a lokacin suna tare da dady.
Haka ta dawo gida jikinta ya mutu.
"Haulat wai ke ba zaki ragewa kanki wanan irin mugun son da kika ma wanan mutumin ba"
Saida ta ɗago tai mata wani irin kallo sanan ta ce"Ni ban san meyasa yaƙi ɗaukar wayata ba tun ɗazun nake kiran shi,ko yana fushi da ni ne"
"Fushen me?
saida taja guntun tsaki sanan ta ce"Shi wani iri ne kamar bai waye ba,ni na ɗauka ma baya sha'awa ne"
"Kamar ya kika ce a india yayi karatu"
"A nan ne ,amma karki ga yadda gudu na,idan kika ga yamin kiss to ba ƙaramar sha'awa yake ji ba,ni haushi nake ji "
"Kai Haulat,yanzu ke da zaki yi alfahari da hakan,kana gani dai kowa burinshi ya taɓaka,amma har ki samu wanda ba jikin ki yake so ba,amma kina wata magana,kin san komai haulat a.....
tun kafin ta ƙarasa maganar ta katse ta"ke allah dan baki ganshi ba ne,amma ina tabbatar miki duk macen da ta ganshi sai taso wani abu ya haɗa su..
"Haulat sha'awarshi kike yi ko sonshi?
"Duka biyu"
"Hm Haulat kenan ni yanzu ƙawarki ce dole na baki sha'awa"
"Yawwa ƙawar Arziƙi mu je ɗaki na"
Ashe duk wanan maganar da suke yi a falo ne.to allah ya kyauta.
Zama suka yi akan gado salma ƙawar Haulat ɗin ta kalle ta tace"Irin waɗan nan mazan a hankali da dubara ake binsu,tunda ya nuna yana jin tsoran wani abu ya faru,to karki matsa mishi ,idan ba haka ba kuwa zai fara ja da baya,hankali xaki haɗa mishi tarko daya faɗa shikenan"
Dariya Haulat ɗin tayi suka taɓa" shegiya ƙawa shiyasa nake sonki,yanzu ba wanan baki na kira faisal(tsohon saurayinta) dan a matse nake,yaushe rabo na,nayi ma ƙokari"
"Ke Haulat baki da dama,ni kuwa kinga tun lokacin da na rabu musa(saurayinta)ban ƙara saduwa da wani ba,saidai ƴan abun da ba'a rasa ba,yawwa ban tambayeki amma zai aureki dai ko"
Kallonta Haulat ɗin tayi tai dariya"Aure ni da aure yanzu ina,allah ya kyauta haka kawai na haihu na tsofa,ke ma kin san bani da ra'ayin aure yanzu,shi dai tunda bai waye ba,daya min maganar auren nake katse shi"
Shiru Salma tayi tana mamaki ina da ita ta samu irin wanan damar"Haulat ni kin ban tsoro na ɗauka kin cire wa kanki wanan ra'ayin banzan,Ina jiye miki abun da zai iya biyo baya"
"mtseww na me? ba abinda zai faru"
"hm murmushi tayi kawai suka cigaba da firar su mara amfani.
~~~~~~~~~~~~~
Saida nayi da ƙyar na iya gane Sabreen ban taɓa tunanin tana kyau irin haka ba sai yau,nayi fitinan kyau,makeup ɗin ya amshi fuskarta ainun,cikin wata dugowar riga wacce ta ɗan kama ta,pink da golden colour kalan ya ƙara fito da ita ga ɗaurin ɗan kwalin ,ita kanta rigar abun kallo ce,bayan an gama yin makeup ɗin aka ɗauke ta hoto na,kala-kala,idan ba ita ta gayama ba son auran take yiba,ba zaka taɓa yadda ba,dan yadda ta saki jiki tana zabga fara'a.
Kallon ta farrah tayi tana washe baki"Da yaya ya ganki na tabbata bazai gane ki ba,ko yanzu sai yayi da ƙyar zai iya gane ki balle an haɗa pic ɗin ku"
Murmushi Sabreen tayi bata ce komai ba,ita yanzu yarda zata haɗu da malama Haulat take yi gashi bata da number ta.
Sunyi yawo sosai da n farrah saida ta je gurin ƙawayanta,ta gaya musu,Da aka haɗa hoton abun ba magana kamar a tare suka yi hoton sun dace sosai ita kanta Sabreen da taga pic ɗin saida taji gabanta ya faɗa da ƙarfi wanda bata san dalilin faɗuwar shi ba.
Gidan su momy suka sauka bayan sun dawo ita ma lokacin bata daɗe da dawowa ba,taji daɗi sosai musamman da taga an haɗa hoton sai ta ƙara tabbatar da sun dace da juna,ita ma nayi siyayya sosai da kayan da zasu saka da komai da komai.
Ana idar da Sallar maqrib Su dady suka dawo,a lokacin suna zaune a falo suna fira akan bikin,Da sallama suka shigo,Sabreen tana jin muryarshi gabanta yai mummunan faɗuwa.
Ko kaɗan bai kula da Sabreen tana nan ba,dan shi ba mutum ba ne mai kalle-kalle ba,har suka iso falon suka zauna bai kula da ita ba.
Dady ya kula da ita tun isowar shi ɗakin yana zama ya kirata"Ƴar aljanna zo nan"
Jin dady ya kira sunanta yasa ya ɗago kai da sauri haɗa ido sukai wani abu ji ya soki ƙirjin shi,da sauri da kau da idonta,a harɗe ta ƙaraso gurin dadyn kanta a ƙasa ,hannu ta Dady ya riƙo yana murmushi ya ce"Ƴar aljanna ya kike"
Kamar me tsoron magana ta ce" lafiya qalau"
"Momyn ku ta gayamin kun fita ke da farrah ,kunyi siyayya,kuɗin sun isa ko kuna buƙatar wasu?
"Am..dam..sun is..
Charab farrah ta ce"Eh dady ba mu gama ba,kuma sai maganar holl ɗin da za'ayi...
"Eh baku da matsala da wanan zanyi komai ni da yayan duk mun shirya komai"
Ko kaɗan Naufal bai gane ba,mamaki yake yi,wani abu xa'ayi..
Bai ƙarasa yin tunanin shi ba Wayar Momy ta fara ringin duk hankalin su ya koma gurin ta.
Ganin mai kiran yasa momy tayi murmushi ta kalli Dady shi ma murmushin yayi,ɗaukar wayar tayi.
"Assalamu alaikum,Haba hajia tun kafin Ayi Auran zaku rike min ita ,yanzu idan aka yi auran shikenan"
"A'a hajia ba haka bane,kin san basu dawo da wuri ba ne,kuma...
"To naji yanzu dai ku turomin ita"
Tana gama faɗa ta kashe wayar.
Dady ya kalle ta yana murmushi ya ce"hajia ku"
ya juyo ya kalli Naufal ya ce"Naufal kai Sabreen gida"
"Toh" Kawai ya faɗa Amma ranshi a ɓace baya son raini Sabreen kuwa ƴar raini ce,bai tsaya jiran wani abu ba ya fito daga falon yana hura hanci.
Momy ta ce "zo nan Sabreen"
A kunya ce ta isa gurinta,zaunar da ita momyn tayi kusa da ita "Sabreen ki kwantar da hankalin ki kinji,gobe da sassafe zan zo ni da Farrah mu fita,ki tashi da wuri dan da safe zamu zo"
"To momy"
"A'a ya zaki ce ta tashi da wuri"
Murmushi momy tayi ta kalle shi ta ce" hmm tafi abinki Sabreen yana jira ki gaida hajia"
"To saida safen ku"
"Yawwa ki tashi lafiya suka faɗa a tare.
A hankali take tafiyar har ta isa gurin motar shi,gaban motar ta buɗe ta shiga,bata ce mishi komai ba.
"Mtseww! ya ja tsaki Sabreen ta tsani tsaki a rayuwarta,bata san lokacin da ita mata ta ja tsakin ba.
A fusace ya ɗago kai,hannun shi yakai kan lips ɗinta masu taushin gaske ya tsungule su da kunbar shi,ƙara tayi da ƙarfi ta ce "Waiyo hajia"
"Wa kike wa tsaki ni tsaranki ne,hajia ko kirata ta zo"
Jin xafi yasa ta cije shi a hannu ,yaji zafi ya cire hannun shi da sauri.
Kallonta yayi ya kalli hannun shi inda ta cije shi ɗin,bai ce mata komai ba yaja motar suka fita daga cikin gidan su,sai da ya raba tafiyar tsakanin gidan su da gidan su hajiar sanan ya tsaida motar,ganin ya tsaida motor yasa ta ce"Me muka tsaya yi a nan ,ni ka kaini gida"
"Ke ba kin raina ni ba,ni kike so ki maida direba ko,janyo ta yayi jikin shi,ya rungumeta wani irin abu yaji yarr tsigar jikin shi ta tashe wani irin shuƙi ya kama shi ,bai taɓa tunanin zaiji wani iri ba,da ko kaɗan baiyi karanbanin haɗa jikin shi da nata ba,ya raina Sabreen ne,kallon kwaila yake mata.
lokaci ɗaya ya tsinci kanshi cikin wani yanayi gashi ta ƙasa natsuwa sai goga mishi dukiyar fulaninta take yi a ƙirjin "Waiyo Allah na hajia ,ka sake ni ,ka sake ni,bana so ni ba ƴar iska ba ce"
Da sauri ya sake ta,yana maida numfashi sama-sama shi kaɗai yasan abinda yake ji,"Meye yasa nake jan abinda xai sa yarinyar nan ta ƙara rainani? wanan tambayar yake wa zuciyarshi yana me jin haushin zuciyar shi
Jan motor yayi da gudu nan da nan ya isa gidn,yana tsaida motor ta fito da ƙarfe ta tura motar"Allah ya isa"
Tana faɗa ta wuce tana tafiyarta hankali kwance.
Dokan kujerar yayi inda ta tashi haɗe da jan wani dogun tsaki yana jin tsanarta a ranshi.
**********
" Alhaji gobe ya kamata ka gayamishi tunda zai ga mutane sun fara zuwa"
Cikin tausasawa ya kalleta ya ce"Xan gayami shi,ki kwantar da hankalinki nasan Naufal ba zai ja da ni ba,ban taɓa saka shi abu yaƙi yi ba komai girman abun,nasan zaiji wani iri amma na ɗan ƙankanin lokaci ne"
A haka ya kwantar ma hajia hankalin.
~~~~~~~~~
"ohhh ni Allah ƴar aljanna tun yanzu zaki fara min haka"
Idanuwanta tabb ta kwalla ta ce"Hajia ba zan iya nisa da ke ba,ko yaushe zan kasance tare da ke,wa gare ni banda ke,hawayen da suka maƙale suka gangaro.
Ita ma hajiar kuka ta fara yi haka suka kwana suna kuka.
~~~~~~~~~~ Haka ya koma gida jikin shi a mace yana ƙara jin tsanar Sabreen, amma wata zuciyar tajin shauƙin yadda take abubuwanta kai tsaye ba tare da jin shakkar komai wai ta kalli shi ta ce mishi allah ya isa, shi mamaki ma abin ya bashi, kashe wayar shi yayi gaba ɗaya.
Yau ma irin mafarkin nan yayi,tashi yayi yana keta zufa,haɗe da sauke nannauyan numfashi "Idan har haka zaki dunga min ki daina zuwar min mafarki" ya faɗa kamar wanda yake jin tsoron maganar,wankan tsarki yayi ,sanan ya fita zuwa masallaci salar asuba,yana dawo wa ya shige ɗakin shi,wayar ya kunna,sakonin Haulat ne suka fara sintirin shigowa,number ta ya kira,tayi ringin tayi har ta katse bai iya kira sau ukku ba iyaka biyu shi ma idan ya matsu yake yin shi.
~~~~~~~~~~~~~
"Yanzu taya xan haɗu da Malama Haulat gashi bani da numberta kuma ban san gidan su,dole na haɗu da ita,numberta ya kamata na samu"
Hajia ta shigo ta ganta ita kaɗai a zaune kan gado tana magana ita kaɗai "Sabreen ke dawa?
Juyowa tayi ta kalli hajiar a ranta ta ce" *NI* *DA* *MALAMA* *TA*
"eyyah ki dawa kike magana ki kaɗai?
Murmushi tayi ta ce"Hajia ba kowa ina tuno wani abu ne"
"Meye shi?
"Hmm Hajia ta ba komai "
" to na yarda tashi ki je kiyi wanka ,yanzu xaki ga su Momyn ku"
"Toh tana faɗa ta tashi ta faɗa toilet"
~~~~~~~~~~~~
Tana farkawa ta duba wayarta ganin kiran Naufal yasa ta ruɗe ta shiga kiran shi da sauri,a lokacin yana ɗakin shi yana duba laptop din shi kiran ta ya shigo yana jin ringin ɗin ya ɗau wayar ita ta fara magana"Hello dear lokacin ban tashi ba,kuma wayar bata kusa da ni sai yanzu na tashi"
"ok ba komai,kin tashi lafiya?
"Lafiya lau,meyasa kake min haka dear,dan ina sonka shine na cancanta irin wanan wulaƙancin"
cikin sigar lallashi ya fara bata hakuri"ba haka ba ne,duk lokacin ina tare da Dadyne mun fita.
"to shikenan bana iya fushi da kai ko kaɗan"
A haka suka cigaba da fira cikin so da ƙaunar juna.
Suna gama wayar Dady ya kira shi yace mishi ya fito falo,yayi mamaki bai ga su hajia ba ya kalli dadyn ya ce"Dady ina zu hajia naga ban gansu ba?
"Eh sun fita zasu je gurin su Sabreen wai zasu je gurin gyaran jiki"
Murmushi yayi ya ce"Mata ƴan kwalliya"
Gyaran murya Dadyn yayi ,ya ƙara gyara zama ya tattara dukkan hankalin shi gurin Naufa ya ce"Naufal ka natsu kaji abinda zan faɗa maka da kunnan basira"
Yadda yaji Dadyn yayi maganar yasa ya tattaro dukkan natsuwar shi yai ƙasa da kai "Ina jinka Dady"
"Naufal Naufal Naufal,Sau nawa na kira ka?
"Sau ukku!
"To ina son ka ji avubuwa ukku da zan gayamaka,ka ɗauke su ka saka su a cikin kwakwalwarka da tunaninka"
Zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske kamar zata fasa ƙirjin shi ta fito.
"Abu na farko Naufal ni na haifeka kuma ina sonka ina alfahari da kai,baka taɓa faɗa min rai ba ,ko na saƙon ɗaya kullum cikin bin umarni na kake,wanan dalilin yasa na son na tausasaka akan hukuncin da na yanke akan rayuwarka ba tare da naji naka ra'ayin ba,Naufal gobe zan ɗaura ma aure da Sabreen
Dumm Dumm zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske wanda tai nasarar sandarar da tunanin shi komai ya tsaya mishi chikkk ,sai zufa da take keto mishi ta ko ina a jikin shi,gashi ya kasa ɗaga kai ya kalle Dady.
"Ban san ra'ayinka akan ta ba,Naufal da wanan nake cewa kayi hakuri.
"Abu na biyu Naufal Inhar ka ɗauke ni uba to ina so ka ɗauke Sabreen a matsayin matarka kuma ƴar uwarka,ko kaɗan karka nuna mata ƙiyayya idan ka nuna mata ƙiyayya ban yafe maka ba..
A zabure ya ɗago kai da jajayen idanuwan shi ya kalli Dadyn na shi.
"Sabreen ina sonta fiye da yadda nake son ka,idan ka cutar da ita ko bayan ba raina ban yafe maka ba,Naufal,kuma idan har ka ɓata mata rai ta zubda hawaye Naufal ban yafe ma ba.
"Sai Abu na ukku wanda shi zan roƙe ka akai ,idanuwan shi sukai jajir muryarshi ta fara rawa abinda bai taba faruwa ba kenan tunda Naufal yazo duniya bai taɓa jin mahaifin shi a irin wanan raunanniyar muryar ba.
"Naufal dan allah dan annabin Rahma Naufal ka riƙe amanar marainiyar allah nan,ba dan hali na ba...
"Dady...dad..dady ka..
"A'a naufal wanan ba umarni ba ne,roƙan ka neke yi,Sabreen amana ce a guri na,zan danƙa mata ita,Naufal ka riƙe ta amana..... . [12/16, 5:36 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/16, 5:41 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
*By* *fatima* *Batula*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* Page 10 ...................................................
*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
*_*بسم الله الرحمن الرحيم*_ _*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{IDAN ALLAAH YAYI NUFIN MUTANEN WANI GIDA DA ALKHAIRI, SAI YA MUSU JAGORAR (SAKA) 'KOFAR SAU'KIN HALI(A GIDAN).}*_ ° ```[Silsilatus Saheeha;523]```
_Duk gidan da suke da saukin hali to lallai Allaah Ya na nufin su da alkhairi. Arziki ne babba mutum ya siffantu da saukin hali. Allaah Ya azurta mu da shi. Allaahu a'alam._
```Allah ta'ala yasa mudace```
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
................................................ Kasa ƙarasa maganar Dady yayi,jikin shi ya mutu ga kwalla ta cika mishi ido.
Cikin wani irin yanayi Naufal ya ce "Dady baka yarda dani ba ne, Dady komai girman abu zanyi shi idan har ka saka ni yinshi k....
"Ba haka nako son ka ce ba Naufal ina son naji ka ɗau alkawarin da zan baka ne"
Cikin raunanniyar murya Naufal ya ce"Na ɗau alƙawari zan riƙe Sabreen,zan kula da ita kamar yadda zan kula da kai na,ba zan bari wani abu ya faru da ita ba,nayi alkawari"
wata irin raguwar ajiyar zuciya Dady ya sauke"Kasan daraja da muhimmanci alƙawari ,ba sai na tunatar da kai ba.
"Naufal tun farkon rayuwarka kake min biyayya,amma ban taɓa jin daɗi abunda ka min irin na yau ,na gode Naufal"
"Dady dan allah ka daina gode min"
"Dole ne,amma Naufal karka yarda ka ƙara min alƙawarin da ka ɗauka,karka wulaƙanta Sabreen ,wllh Allah idan makamancin hakan ta faru zan iya fushi da kai ,zan iya rabu da kai,daga ranar ma karka ƙara kira na da sunan Dadyn ka"
Wasu zafaffan hawaye suka fito mishi zuciyar tana radaɗi da zafi,yau shi mahaifinshi ke gayama irin wanan maganganun masu zafi gaske "Dady ba zan ƙara alƙawari"
"Na sani Naufal kai jini na ne,ina ƙara ma ƙarfi ne yadda zaka riƙe da muhammanci,Sabreen tana sonka ita ta fara magana,na san kai ma kana son ta"
A razane ya ɗago yana kallon dadyn maganar da yayi tana mishi yawo a cikin kaI"Sabreen tana sonka ita ta ce tana sonka" kai anya ina wa...
"Naufal bamu ga ta zama ba,tashi mu fita gobe ne fah
Gaban shi ya faɗi" gobe gobe!!
"Ba'ayi biki haka ba,bakin ƴaƴan gata ka tashi mu fita,baka da wani abu da kake son ayi"
ƙasa yayi da kai,dan kanshi yayi nauyi.
"Naufal ko auran dole ne"
"uhm ina tunanin abinda za'ayi ne"
"to mu fita"
dadyn ya fara fita yabar nan,da ƙyar ya iya jan jikin shi,ba abinda yake tsorata shi irin da yaji Dady ya ce wai sabreen ta ce tana sonshi,tabbas yakan sabreen bata son shi,ko kaɗan" to meyasa zata min haka? dan tsana"
ya tambayi kanshi ya kuma bawa kanshi amsa"meyasa Why?Sabreen ke wacce iri ce kin dagula min rayuwata,da kika haɗa rayuwar mu tare,bana sonki bana ra'ayinki amma saida kika cusa kanki a rayuwata meyasa baki gane bana sonki ba, am helpines,ba zan iya komai ba Sabreen kin cuci ni kin....
"Naufal kayi sauri ina jiranka, dady ya katse mishi tunanin daya ke yi"
~~~~~~~~~~~~~
Su Sabreen manya ana chan ana gyaran jiki ita da farrah harda Momy ma, tasha lalle wanda ya fito da yar madaidaiciyar hasken jikinta,yaƙe kawai take yi amma bata jin daɗi a zuciyarta.
"Toh yanzu taya zan haɗu da malama,ko na bari bayan an ɗaura aure"
"Keeee tunanin me kike yi Aunty Amarya"
Ɓata rai Sabreen tayi"Farrah ki daina ce min aunty bana so"
"To matar yaya"
harara da gallama ta "waye matar yaya?
Dariya Farrah tayi "Kai Sabreen lamarin ki sai ke,ranar da kuka ,kina son yaya ya ɗaura muku aure amma yau wa waye matar yaya kike tambaya"
"ina son Yaya allah ya kyauta me xanyi da ɗan kilibibin nan"A zuciyarta tayi wanan maganar ,A fili kuwa harar ta tayi.
Momy bata gurin su kaɗai ne,ita ta koma gida dan tayi wasu aikin.
Sun daɗe har bayan maqrib suna nan ana abu ɗaya.
~~~~~~~~~~~~
Bayan su dadyn sun dawo ya tambayi momy ina su Sabreen ta gayamishi suna gurin gyaran jiki,Ɗadyn ya ce Naufal ya je ya ɗauko su.
***********
Wayar Farrah ya ya kira"Hello Ki fito ina waje" Ya katse wayar
Kallon Sabreen farrah tayi"Angon ya ƙaraso"
"Mitsewww!
"Ni tashi mu je yana jira idan mun je kin mishi tsakin"
Suna fitowa daga shagon motor shi,gaban Sabreen ya faɗi amma ta ɓata rai.
Daman ya lafiyar giwa balle tayi hauka,wanda ko farinciki yake ya ga damar ya ɓata rai balle kuma.
Bai ɗago kai ya kalle su ba,har suka shiga cikin motar,harar shi sabreen ke yi ta gefan ido a ranta tana faɗin"Ban kaddara da me zai haɗa ni da kai,kuma burina yana cika na son ɓatawa Haulat rai zan rabu da kai ne,dan ba zan iya rayuwa da kai ba"
kiran wayar farrah ne ya katse musu shirun da suke yi,ƙawarta ce,ita kuwa farrah ko a jikinta ta saki jiko suna fira akan bikin ma,hayaniyar ta fara damun shi
ya daka mata tsawa"Keee baki da hankali ne"