Nida malamata complete - Chapter 4
Nida malamata complete Chapter 4: Nida malamata complete Chapter 4. katse wayar yayi dan ya tabbata idan ta cigaba da mishi magana a haka ba zai kai labari…
4,487 words
katse wayar yayi dan ya tabbata idan ta cigaba da mishi magana a haka ba zai kai labari ba,kashe wayar yayi ma, dan yasan zai ta kara kira tunda maiyace anace🤣.
~~~~~~~~~~~~~
Gaba daya ya rasa natsuwar shi tunda sukai magana da hajia, ƙarfe da ƙyar ya tsaya yayi salar maqrib a office ɗin,cikin gaggawa da hanzari ya iso gidan su hajiyar.
Suna zaune a falo ƴar aljanna tana kan cinyar hajia kamar yadda ta saba indai suna tare da ita to a kan cinyarta take kwanciya.
"Assalamu alaikum"
Sabreen tana jin sallamar shi ta miƙe Hajia ta amsa mishi sallamar,yana ƙarasowa yayi gurin Sabreen ɗin fuska ɗauke da Annuri ko wani irin yanayi yake ciki idan yaga Savreen zai yaji farinciki.
"Sabreen ya jikin ki" kanta a ƙasa ta ce"yayi sauƙi Dady"
"Alhmdllh! allah ya ƙara miki lafiya Sabreen"
Hajia ta katse shi da faɗin"ƴar aljanna je ki ɗaki" "to kawai ta faɗa ,ta tashi ta hau sama ,duk da tasan dady ba zai ƙi amincewa ba amma saida ta tsinci kanta da faɗuwar gaba wanda ta rasa dalilin yin shi.
Bayan sun ƙara gaisawa ta kalle ta ce"Alhaji kana jina koh?
"Eh ina jinki hajiya"
"Yawwa to,tun lokacin da likita ya ce ayi wa Sabreen aure na shiga tunani da wa za'a haɗa ta,tun a lokacin Naufal ya faɗomin a rai ,domin bana son mu ba wani wanda bamu sanshi ba,kar ya cutar da marainiyar allah,amma zai ban nufe ka da maganar ba,kuma kai ma nasan kayi irin nawa tunanin ,duk ba mu san muyi mata dole shiyasa ba muyi wa juna maganar ba"
"Wanan haka ne hajia kuma ɗazun malamin makarantar su ya kira ni ya shawurce ni akan muyi mata aure"
"To alhmdllh! Allah yaga zuciyar mu ya ga kuma tsoran mu,yau tana dawo wa daga makaranta da tabbatar min da tana son Naufal"
Wani irin farinciki ya mamaye alhaji"masha allah alhmdllh,hajia allah ya dube mu,daman muna tunanin ko ba zata so shi ba,amma abin allah gashi tana son shi,ba ƙaramin daɗi naji ba,cikin gaggawa kuwa za'a ɗaura auran nan"
"Yawwa ni kaina naji daɗi mara misaltuwa,yanzu zai a tsaida ranar auren.
"To kwana nawa kike ganin ya kamata a saka"
"To bari mu sai gobe idan munyi magana da ita"
Hmm tofah ana wata ga wata,ko ya naufal xaiji idan yaji maganar auren shi da Sabreen,ga kuma mutumiya haulat.
Bayan ya tafi hajia ta shiga gurin Sabreen ɗin ,a kwance ta ganta tayi lamo kamar me barci,tana jin an buɗe kofa ta tashi zaune,kusa da ita ta zo ta zauna.
"Ƴar aljanna bana son ganin ki kina damuwa Naufal ya zama naki,yaushe kika so a ɗaura muku auren?
Dumm dumm zuciyarta ta fara buguwa wani irin abu zuciyarta ke bijiro mata da shi me kama da tsoro,amma dan tsabar ƙarfin hali irin na Sabreen ta ce"Sati ɗaya,A'a kwana huɗu ranar juma'a kenan,sati ɗayan ya mata yawa.
"To baki da matsala yanzu ai a fara shiru"
"Hajita ina son a tsara bikin nan sosai irin na ƴaƴan gata"
"ke ƴa gata ce Sabreen karki ji komai ko da ɗukiyar alhaji zata ƙare akan yasa ki farinciki zai kashe,za'a haɗa biki irin wanda sai ƴaƴen manya ƴan gata"
Wani irin farinciki ya mamaye Sabreen ,amma a ƙasan zuciyarta tana jin wani iri.
~~~~~~~~~~~~~
Ko da dady ya koma gida suna zaune a falo suna fira.
duk da sun san dady da fara'a amma yau kuwa sunyi mamakin ganin irin fara'ar da ke fuskarshi kamar wanda akai wa bushara da aljanna,zama yayi suka yi fara sosai sai ƙarfe goman tare kowa ya tafi ɗakin shi.
"alhaji wai yau naga kana cikin wani irin farincike ne"
murmushi yai mata sanan ya ce" hmm wani irin abu ne kike ganin zai sani irin wanan farincikin"
"eh to abu ɗaya ne zuwa biyu na farko dai magana akan Savreen na san ko...
da sauri ya katse takYawa uwar gida,ma tso kusa na baki labari"
Ba mutsu ta matso"to ina jikin ka
Saida yai gyaran murya ya kara natsuwa sanan ya ce"Kin san lokacin da likita ya ce ayi wa Savreen aure hankali na ya tashi akan da wa zana haɗa ta wanda sai riƙe ta da amana yaji tausayin maraicinta"
"Haka ne ni kai na abin yana damu na domin Sabreen abin tausayi ce"
"To allah ya ga zuciyar mu,ita da kanta ta ce tana son Naufal kinga faɗuwa ta zu daidai da zama,yanzun mun kama magana da hajia daman ba wanda ta cancanta da ya aure sabreen sai shi,kuma cikin satin nan za'a ɗaura auren nan"
Ba ƙaramin daɗi momy taji ba,dan tana son Sabreen tana jin tausayinta,amma abin da ya ɗaure mata kai daya ce wai Sabreen ta ce tana sonshi,a iya ganinta basu shiri dan ra'ayin su bai zo ɗaya ba. "To Naufal yana sonta kuwa?
"Tunanin me kike yi?
Murmushi tayi ta ce"Naji daɗi sosai da sosai amma shi Naufal ɗin ka ji ta baki....
Da sauri ya katse ta da faɗin"Ba buƙatar jin tashi Sabreen ƴae uwarshi ce dole ya sota yana ma sonta,idan jar jinin jiki na ke yawo a jikin shi,to na Sabreen ma yana yawo a jikin shi,kuma idan har yana so na to yana son Sabreen,kuma kar yaji wanan maganar sai ranar da za'a ɗaura aurank
Ganin rance ya fara ɓace yasa tai saurin tarar shi cikin sigar lallashi ta ce"Ba wai ina nufin wani abu ba ne,ina nufin ya kamata ace ya san da maganar ne...
"To idan bai sani ba ,wani abun zai yi?
Shiru tayi dan taga alamar ya hau sama,tashi tayi ta fita a ɗakin....
lallai Sabreen saboda ɗaukar fansa zaki aure wanda baya sonki baki son shi. . Sir Dboy [12/9, 1:13 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚 [12/16, 5:46 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
*By* *fatima* *Batula*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
.............................................
_*YAWAITA SALATI GA ANNABI S.A.W ARANAR JUMA'A*_ ➖➖➖➖➖➖➖➖ _*Annabi s.a.w* yana cewa: (Yana cikin mafificiyar Ranakunku Ranar Juma'a, dan haka ku yawaita yin Salati agareni acikinta, domin ana bujuromin da salatinku gareni)._ _*@Saheehu Abu Dauda.*_
_*Annabi s.a.w* yace: (Duk wanda yayi salati a gareni, *Allah* zaiyi masa salati Guda Goma)._ _*@Saheehul Jami'i*_
Page 7 ___________
Kallon Sabreen ɗin yake yi cikin mamaki,ya ƙasa yarda da abinda aka gaya mishi dan yanayin ta ba irin na matan nan ba ne,ga kuma hawayen da yaga tana yi.
"Dan Allah kayi hakuri karka kore ni,bamu taɓa yi ba sai yau.
Kamar wata wawiya ta juyo ta kalli shi,tana hawaye.
Shi kanshi principal ɗin kan shi ya ɗaure ganin yadda sani nani yake magana,gashi ita ta kasa cewa komai.
"Daman ba tun yau ba nasha ganin ta tana zuwa toilet ɗin maza" cewar wani mai aikin makarantar.
Kallon shi cikin mamaki da tsoro Sabreen tayi, duk bakin Sabreen yau naiman shi tayi ta rasa.
"A hukunta su daidai laifin da ta aikata" cewar uncle ɗin maths ɗin su wanda shi ma yana cikin office ɗin.
Kallon su kawai Sabreen ke yi tana zubarda zafafan hawaye zuciyarta na ƙuna.
Saida yaja numfashi sannan ya ce" ku bani guri zanyi magana da ita"
Basu su hakan ba musamman sani nani shi da yaso jin hukunci da wulaƙancin da za'a mata,amma haka nan suka fita.
Kallonta yayi cikin jin tausayi ya ce"Sabreen mai ya faru?
Sai yanzu kuka mai sauti ya kamata,kuka mai tsuma zuciya ta fara wanda tunda ta zo duniya bata taɓa yin irin shi ba.
"Kiyi magana ganin ba zata yi ba yasa ya ce mata" to ya isa hakan.
A zuciyarshi y ce" kukan ki ya tabbatar min da baki aikata komai ba,amma dole zan yi hukunci dan dukace amma tabbas zan rufa miki asiri ba zan tuzarta ki ba"
Wata ƙararrawa ya danna alamar su shigo,cikin zuguɗin abinda zai faɗa suka shigo.
Kallon su yayi ya ce "Kamar yadda duka ta tanadar za'a gayama iyayenta sannan a koreta daga makaranta,amma ba zan koreta ba,zan dai gayama iyayenta sanan bana son jin wata ƙaramar magana na,kai sani ya kalle shi
"Kai ne abin ji wallahi idan har iyayenta suka ji wanan labarin ka bani,baka san matsayin su ba ne,balle ta tabbatar mu da ƙarya kake mata,ba kai ba har makarantar gaba ɗayanta ka ja mata kalle ta ya nuna Sabreen ɗin wacce dan tsabar kuka jikinta ya mutu yayi tiɓiss. Sanan ya ɗaura da faɗin"Hm kai kasan komai,ni bani da abinda zan ce a cikin ku waye ma gaskiya ,amma abu ɗaya tabbas idan har iyayenta suka ji kai ne mara gaskiya dan sai sun hukunta ka.
Jikin sani yayi sanyi tabbas yasan bashi da gaskiya ko kaɗan.
Kallon shi principal ɗin yayi yaga yadda jikin shi ya mutu sanan ya ce"Hmm zaka iya taimakon kanka ta hanyar ƙin gayama kuwa dan wllh idan ka yarda iyayenta suka ji wanan mgnr ka kaɗe"
Kallon sauran malaman yayi ya ce musu"Ku kuma nasan kun waye mahaifinta kuma kun san abinda zai iya to wllh ku rufama makarantar nan asiri domin idan ba haka ba,kun san abinda zai biyo baya,kuma wllh duk idan naji wani yayi kokarin gayan wata magana a bakina aikin shi"
Gaba ɗayan su jikin su yayi sanyi dan sun san mai taƙama,musamman sani.
"Kuma abinda yasa ba zan koreta ba ,dan gudun kar ayi zargin wani abu,ina fatam kunji abinda na gaya muku da kyau"
"Eh munji suka faɗa a tare sanan kowa ya gama gaban shi.
Har suka gama magana suka fita Sabreen na kuka.
"Sabreen na san ƙarya ya miki,yana da wata manufarshi na yin haka,shiyasa ba zan matsa sai ya gaya ba domin idan nayi hakan wasu zasu ji daɗi,shiyasa na rufe musu baki,sanan ke kuma kiyi hakuri tunda kin san baki aikata komai ba,plsss Sabreen kiyi hakuri kuma karki gaya ma kuwa abinda ya faru harda gidan..
Sai yanzu Sabreen ta samu bakin magana cikin shekar kuka ta ce"Ban...s..san..abin..da..suk...ke..magana...b...n rantse da girman allah bansan...
"Ya isa haka ya ƙatse ta,na sani shiyasa na ce ki kwantar da hankalin ki,idan kika nuna danuwa waɗan da suke son ganin kin tuzarta daɗi zasu ji"
Allah sarki Sabreen baiwar allah ko kaɗan bata kawo Haulat a ranta ba,bata ma yarda wani zai iya mata hakan ba dan yasa ta wulaƙanta tabar shi a matsayin an samu kuskure.
Ya daɗe yana lallashin ta,har lokacin an kusa tashi ma,sanan yasa ta shi toilet ɗin office ɗin ta wanke fuskarta,ta wuce classa ɗin su.
Number Alhaji ya fara naimo wa cikin sa'a kuwa ya ganta ya danna kira,ringin ɗaya tayi ya ɗauka.
"Assalamu alaikum Alhajn ya faɗa.
"wa'alaikum sallam Alhaji ya gida ya kokari ya iyalai.
"Alhamdulilah komai lafiya
"Mash allah! Alhaji daman ina son yin wata magana ne akan Sabreen"
yana jin ya kira sunanta ya natsu ya tattara dukkan hankalin shi"ina jinka lafiya take dai ko"
"Lafiya qalau take daman shawarace zan baka da wasu malaman suka lura suna ganin ya kamata ayi wa Sabreen Aure"
Zaida Alhaji yayi jim kaɗan shi ma bai kawo komai a ranshi ba dan likita daman ya gaya musu suyi mata aure.
"Ba komai insha allah daman nasan da zancen auren ina wani shiri ne dan Sabreen bata kula maza ni kuma bana son yi mata dole"
Ba wani fahimtar maganar yayi ba ya ce"to haka ne kam za'a mata dole ba"
A haka suyi sallama.
Ita kuwa Haulat ta kasa kunne taji labari ya fara yawo amma shiru bata ji komai ba gashi bata ga sani ba,gashi har an tashi gida.
Duk wanda yasan Sabreen idan ya ganta yau sai ya gane chanji ƙarara dan fuskarta a ko yaushe ɗauke da annuri amma yau kuwa ba annuri ba alamar shi sai ma yanayin ƙunci da ya baiya na a fuskar.
Tana tsaye tana jiran direba,kanta a kasa idanuwanta cike da hawaye dan ba abinda ya taba ɓata mata rai a duniya irin wanan abun taji zafi kamar me.
🤧lallai akwai aiki kuna ganin idan Sabreen ta gane aikin haulat ne zata iya hakura?
Cikin salon yanga da iyayi da kinibibi Haulat ta fito daga office ɗinta,hango Sabreen da tayi yasa tayi murmushin mugunta musamman da ta hango yanayin da take ciki.
Sabreen bata san Haulat ta matso kusa da ita ba sai ji tayi ta ce"My illiterated student! yadai
Ƙasa ce mata komai tayi dan bata cikin yanayin.
Ganin hakan yasa Haulat murmushi tana ganin kamar tayi nasara ta ce"Tun kafin a baiyana abinda kuka aikata har kin shiga wani irin hali.
Cikin rashin fahimta Sabreen ta kalleta.
Murmushin mugunta Haulat tayi ya ce"Yess! baki kina tunanin zaki iya ja Haulat ba har kika sa aka bani suspension,to bari ki ji ni na haɗa komai na biya sani,ke ba kin sa an bani suspension ba,ni kuma zan sa a wulaƙanta ki ,ki tozarta ki kunyata kuma a koreki a makarantar sanan a gaya ma iyayenki abinda kika aikata, daman baki son karutu ke jahila ce sai a haɗa ki da jahili ɗan ƙauye irinki,dan ko mai washe bola ba zai iya auren ki ba"
Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara bin fuskar Sabreen zuciyarta na ƙona tana mata radaɗi.
Ganin halin da take ciki yasa Haulat farinciki cikin dariyar mugunta ta ce"Hmm ja da Haulat ba irin ki ba jahila ƴar kauye kuma yarinya,hmm karki wahalar da kwakwalwarki gurin yin tunanin zaki iya ɗaukar fansa akai na yarinya domin ni ba tsararki ba ce,tana gama faɗa wushe tabar Sabreen tsaye da zafin zuciya.
Hmm ikon allah yau Sabreen baki ya mutu🤣.
Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi,daidai lokacin direban ya iso ,tana ganin shi ta ruga da gudu ta buɗe motar ta shiga tana kuka.
A ruɗe yake tambayarta lafiya dan ko a mafarki bai taɓa tunanin akwai abinda zai sa Sabreen irin wanan kukan ba.
Suna isa gidan ta buɗe motar ta fito da gudu a falo ta hango hajia zaune gurinta tayi ta faɗa kan jikinta tana kuka,a ruɗe Hajiar ke tambayarta"Lafiya Sabreen ke da waye???????
A ranta ta ce" *NI* *DA* *MALAMA* *TA*.
Tsananin kuka ya hanata magana. Hajiya ta ruɗe tana faɗin"Na shiga ukku ke dawa me ya faru wa ya taɓa ki,ko baki da lafiya ne????
charab ta ce"Bani da lafiya
Ai hajia sai ta ƙara ruɗewa ta ma rasa abinda zata yi,ganin hakan yasa Sabreen,faɗin "zan kwanta ki kaini ɗaki na"
A ruɗe hajiar ta tallabo ta suka hau sama,suna shiga ɗakin Sabreen ta kwanta hajiar har ta rufe ta.
Amma Sabreen bata daina kuka ba tuno kalaman malama Haulat take yi,tana jin zafi a zuciyarta.
Ganin hankalin hajia tana ƙara tashi yasa ta daina kukan ta fara yin na zuciya,tayi lamo kamar tayi barci,tana jin hajia tana ta maganganu,A haka har barcin ya ɗauke ta.
~~~~~~~~~~~~~
A hankali ta fara jin muryar hajia da na Momy da na farrah,bata ji muryar shi ba amma ƙamshin shi ya tabbatar mata yana nan,a hankali ta fara kokarin fuɗe ido domin taga a inda ta ke.
Akan hajia idonta ya saura dakin da mutanan da ke ciki ta fara ƙarewa kallo,ɗakinta ne,chan daga bayan su akan kujerarta ta hango shi fuskar nan kamar kullum a yatsine.
Sannu suka mata ɗaga musu kawai kawai take yi.
Momy ta kalle shi ta ce"Naufal baka ga ta farka ba"
Bai ce mata komai ba ya ƙaraso gurin tana ganin shi da juya kanta.
Taɓe baki yayi ya ce"Ya jikin?
Ɗaga mishi kai kawai tayi,bai damu ba,ya koma ya zauna ta gefan ido yake satar kallon ɗakin ,ɗakin ya mishi kyau ga wani irin ƙamshi irin wanda yake ji a jikinta,ya shagala gurin satar kallon ɗakin.
Momy kalleta ta ce"Ƴar aljanna bari mu barki ki samu ki watsa ruwa"
Bata ce bata komai ba suka tashi suka fita yana jin hakan ya riga su tashi,kash saidai ya manta da wayarshi a hannun kujerar da ya tashi a kai.
Hajia ta kalleta ta ce"Zaki iya wankan"
Murmushi tayi ta ce a hankali "zan iya"
"To ki kula kinji"
Kai kawai ta ɗaga mata,hajiar ta fita.
Tana ganin sun fita ta sauko daga kan gadon ,ta cire kayan makarantar ta ɗaura towel,har zata shiga bayi ringin ɗin waya taji kalle-kalle ta farayi charab idanta ya sauka akan wayar Naufal ɗin wacce ya manta da ita a ɗakin.
Ƙarasa gurin tayi tana faɗin"Garin ya ya manta da wayarshi a ɗaki na?
Tana kai hannu ta ɗau wayar ,tsaro idanu tayi tana ƙara tabbatar a abinda idanuwanta suka ga ni.
"Malama Haulat! ta faɗa ita ɗince pic ɗinta ne ya baiyana a gaban wayar har kiran ya katse Sabreen bata sani ba ,dan mamaki ƙara shigowar ringin ɗin ne ya dawo da ita daga duniyar mamakin abinda ba abin mamaki ba ne.
Katse wayarta"Malam haulat ita ce kenan"
Wani kiran ya ƙara shigowa a fusace ta ƙara katse kiran.
"Ya Naufal ne wanda keke mugun so daman"
Jin tafiyar mutum yasa tai sauri ta ajiya wayar ta faɗa toilet ɗin da sauri.
Farrah ce ta shigo ɗakin ta ɗauki wayar daya aikota ta ɗauko mishi.
"Sabreen zamu tafi amma anjima zamu dawo momy tayi baki"farrah ta gaya tana kallon toilet ɗin,bata tsaya jiran amsar Sabreen ɗin ba ta fita daga ɗakin dauke da wayar a hannunta.
"Malma Haulat"
Ta faɗa tana tuno kalaman da ta gaya mata.
kamar wace abu ya tsikara tayi zumbur ta mike ta ɗaura towel ɗin ta fito,tana fitowa hajia na shigowa,tana ganin hajiar ta fashe da kuka mai tsanani ta faɗa kan gadon.
A kiɗime hajia ke tambayarta"Lafiya Sabreen ki gayamin abinda ke damunki ko meye shi zan miki magananin shi"
Cikin kukan ta ɗago kai ta kalle hajia ta ce"Ya Naufal na ke so,kuma ya Aure ni"
Ba hajia ba ni kaina saida taji wani yarr
"Naufal kike son aura
"Eh kuma a wanan satin" Tana faɗa ta ƙara fashewa da kuka.
Cikin sigar lallashi hajiar ta ce"Kiyi hakuri indai Naufal ne ya zama naki ke kaɗai kuma ko gobe kike so za'a ɗaura muku aure!
tirƙashi!!!
😱😱 waiyo me kike shirin aikatawa Sabreen duk ɗaukar fansar ne!! . Dboy [12/16, 5:46 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚[12/16, 5:35 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
*By* *fatima* *Batula*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
بسم الله الرحمن الرحيم
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{KAYI ALKHAIRI, KUMA KA BAR LAIFUKA. ALLAAH ZAI MAYAR DA LAIFUKAN KA(NA BAYA) BAKI 'DAYA SU ZAMA ALKHAIRI.}*_
```[Sahihut Targib;3164]``` ~~ _Duk mutumin da Allaah Ya azurta da halin kirki ya rin'ka aika alkhairi, kuma ya guji aikata sabon Allaah, toh sai Allaah Ya mayar da laifukansa na baya ma su zama masa alkhairi. Allaahu a'alam._
```Allah ta'ala yasa mudace```
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
Page 8 .......................................
Kamar yadda ya saba yin mafarkin yau ma hakan ne, Ya kai tsawon minti ashirin yana nazari akan mafarkin wanda yanzu abun ya fara tsorata shi, dan saidai idan har bai kwanta ba, amma sai yayi mafarkin ta.
Tashi yayi ya shiga toilet ya daɗe yana watsa ma kan shi ruwa kafin ya samu yayi wankan ya fito.
Cikin jallabiya baƙa ya shirya ,ta mishi kyau ainun,ga ƙamshi da ke tashi a jikin shi saboda yawan saka turare yasa ko mai shafa ba,jikin shi yake ƙamshi.
Kallon agogon bangon dake ɗakin yayi ƙarfe tara na ranar laraba,ya mutsa fuska yayi haɗe da hura ɗan ƙaramin hancin shi,wayar shi ya ɗauko ya kunna,yana kunnawa saƙonnin Haulat suka fara shigowa,shefar da wayar yayi haɗe da jan tsaki.
Gaban shi yai mummunan faɗuwa jin ringin ɗin kiran Dady da sauri ya ɗauka murya a harɗe ya ce"Assalamu alaikum"
Cikin jin daɗi da annashuwa Dadyn ya ce"Wa'alaikum salaman"
"ina kwana dady
"Lafiya lau Naufal baka tashi ba ne?
"Na tashi dady
"To ka fito ina jiranka a falo"
"to ganin nan zuwa ,tun kafin ya rufe baki ya tashi ya fito,a ranshi yana tunanin me yasa dadyn nashi cikin farin ciki tsakanin jiya da yau,sanin ba zai iya bawa kan shi amsar ba yasa shi ya bar maganar.
A Falo ya same su,da dukkan alama suna cikin jin daɗi,shi ma aro annuri yayi yasa wa fuskar shi,xai da ya zauna sanan ya kalli momy cikin kulawa ya ce "Good morning
"Morning Naufal
Farrah ma ta ce"Ka tashi lafiya Yaya Naufal"
"Lafiya lau"
Allah sarki momy tana son Sabreen amma bata son ya aure wacce baya so,dan ƙiyayyar namiji bala'ai ne.
A tare suka yi breakfast cikin son da ƙaunar juna,bayan sun gama Dady ya kalle shi cikin kulawa ya ce mishi"Naufal tashi muje yau akwai abubuwa masu muhimmanci da xamu yi"
Cikin rashin fahimtar abinda dadyn ke nufi ya ce"To Dady A office ne?
"A'a wanan yafi aikin offfice tashi dai mu tafi"
A ranshi ya fara tunanin wani irin avu ne wanda yafi aikin su mahimmanci.
"Gidan hajia zamu fara zuwa"
"to Dady ya faɗa ba komai a ranshi.
~~~~~~~~~~~~~
Zaune take akan tanƙameman gadonta ,gaba ɗaya jiknta ya mutu sakamaƙon mafarkin da tayi Naufal ya tsare da ido yana mata wani irin kallo wanda ƙaramar kwakwalwarta ta ƙasa gane ina kallon ya dosa.
"Ina haba Sabreen tun yanzun zaki karaya,dan ɗaukar fansa zaki yi fa,bai kamata ki karaya ba" Zuciyarta ke mata wanan maganar a fili ta ce haɗe da yin murmushi "Sabreen ƴar aljanna ƴar gatan hajia,duk abinda nasa gaba sai nayi shi"
Zuciyarta ta ƙara yin ƙarfi duk wani tsoro da fargaba ya fito,Cike da izza ta tashi tai toilet fuskar nan ɗauke da annuri.
A Falo suka iske hajia ,hajia tana ganin Naufal ta sake wani irin murmushi,ta ce "Mutan India manya Har ka fara ƙamshin dogon buri"
Cikin rashin fahimtar zancen ta ya ce"Ina kwana hajia"
"Lafiya lau,yanzu fah ka ɗau hanya"
Banza yayi da ita tunda shi bawai ya iya hausa sosai ba ne,baya gane magana cikin magana,dan ma su momy suna mishi hausa da ba zai iyata sosai ba,a ranshi ya ce"To yau kuma ita ma naga tana cikin farinciki Sabreen fa?
"Sabreen meye nawa da ita,duk a zuciyar shi yake wanan maganar,ya kas....
"Naufal hau sama ka kira Sabreen"
Hajia ta katse mishi tunanin da yake yi,kallon ta yayi ta sakar mishi wani irin murmushi,kallon dadyn yayi shi ma murmushin yake yi.
Tsaye ya miƙe ya hau saman a ranshi ya faɗin"Meyasa hajia zata aike ni ɗakin ta?
Tura ƙafar yayi,lokacin ta fito daga toilet daga ita sai towel dan ƙarami iya karshi gwiwa.
Jin an buɗe kofa yasa ta juyo"Waiyo!! ta faɗa a tsora ce.
Ƙamewa yayi a tsaye zuciyar shi tana bugawa da karfin gaske kuma ya kasa sauke idanuwan shi da suka kafe akan brest ɗinta,lokaci ɗaya jikin shi ya mutu wani irin bakon yanayi ya fara ziyarta zuciyar shi,wanda ya ke tunanin yafi ƙarfin ya kira shi da sha'awa.
"Laaa.....fiii....y...yaa...me...y..yaaa....k.k..ka.wo..ka.."Ta faɗa a ruɗe.
Bai ma san tana magana ba,dan gaba ɗayan hankalin shi baya tare da ita.
Idanuwan shi ta kalla ai sai ta ƙara ruɗewa ganin yadda suka chanja kala,gashi ta ga nonowan ta ya zubawa ido,A ruɗe ta faɗa kan gadon ta ƙudundune da bargo tana ihu.
Ringin ɗin wayar shi ne yai nasarar dawo da shi haiyacin shi,lumshe idon shi yayi waɗan da suka rine.
Da ƙyar ya iya sarrafa hannun shi gurin lalubo wayar da ke ringin ɗin,ringin ɗin kiran Haulat daban ne amma saboda tsananin shiga wani irin yanayi bai iya tantance ringin ɗin ba.
ya san ko ya ɗauka ba zai iya magana ba ,yasa ya kasa ɗaukan,ga shi kafafuwan sun mishi nauyin da zai iya saukar da kan shi ƙasa.
Hawaye ne taji sun fara bin fuskarta a hankali ta ce "daman ɗan iska ne! kuma zan aure shi"
Tuno irin yadda taga ya kafe nonowanta da ido tayi haba sai hawaye shaaa kamar an kunna famfo.
Ko kaɗan su hajia basu kawo komai a ransu ba ,daman tayi hakan ne dan suyi magana ita da dadyn.
Jin sheƙar kukanta yasa shi ya ƙasa shigowa ɗakin "Keee ya daka mata tsawa,uwar me kike yiwa kuka,wani abu ne ya faru banza kawai kiran ki aka ce na zo nayi"
Yana gama faɗa ya fita a fusace ranshi a ɓace,kan me zata yi kuka wani abu yayi mata,ji ƙarfin hali irin na Naufal ko tabarmar kunya dai zai naɗe.
Ai wani sabon kukan Sabreen ta ƙara fashe wa da shi,abinda ya ɓata mata rai tsawar daya ɗaka mata,wacce saida tasa hanjin cikin ta yin kuka,dan tsoro,kuma meye nashi idan tayi kukan,ba shi ne yaja ba"
"Ko me zaka min ba zan fasa aurenka ba,kuma na baka bashin tsawar da ka dakamin amma bazan yafe ba"
Ita kaɗai tai tai maganganun ta,tana kuka.
baƙin glass yasa kafin ya sauko kasan,yana isa hajia ta ce mishi
"Tana ina?
"Gata nan zuwa"ya faɗa cikin wata irin murya,fita yayi daga falon yaji daɗi da dadyn bai hanashi ba ,yaɗai ce mishi ya jira shi a motor
A motor ya zauna ya jingina kai da sitiyarin motor zuciyar shi tana bugawa,kamar wanda bai taɓa ganin makamancin haka ba,yasha ganin mace tsirara amm bai taɓa jin irin na yau ba,ko Haulat tasha ɗaukar hoto da towel a jiknta ta turomishi,amma yau sai yaji wani irin abu wanda ya kasa ganewa.
"Mtseewww me yakai ido na jikin wanan wawiyar yarinyar yanzu zata raina ni,dan taga irin kallon da na mata mtseww"
Ya faɗa cike da jin haushin zuciyarshi da idanuwan shi.
Hajia da dadyn sun gama magana akan ranar juma'a za'a ɗaura aure,hamshaƙin aure irin na ƴaƴan gata,Sanan sunyi magana akan gidan da zasu zauna da komai da komai,sanan dady ya bata maƙudan ƙuɗi dan yin wasu abubuwan,sanan ya tashi a falo ya tarar da shi.
"Ya Aka yi ne Naufal"
"Ba komai dady ya aro murmushi ya ɗaurawa fuskar shi"
Hoto nan gidaje Dady ya nuna mishi "Wanne yafi kyau Naufal"
Gaba ɗayan gidjen sun haɗu kamar ba'a 9j ba,saida ya tsaba wani madaidaici mai ɗankaran kyau sanan ya nunawa Dady ya ce"Waw dady wanan yafi kyau"
Murmushi yayi sanan ya ce"Sabreen zata so shi ko"
"Sabreen me ya kawo maganar Sabreen a nan kuma?ya tambayi kan shi a zuciya murmushi yayi tuno komai za'ayi sai idan yayi mata sanan ake yi.
"Eh dady zai mata kyau ai yana da kyau"
hhhhh Shiyasa baka da masoya Naufal dan baka gane komai🤣.
Murmushi dadyn yayi "Yawwa.
******** Ganin ta daɗe bata fito ba yasa Hajia ta shiga ɗakin ganin ta a kwance yasa hajiar ta ruɗe"Ƴar aljnna lafiya? ta ƙarasa gurinta da sauri.
Tana jin hajia ta ƙara duƙunƙunewa kamar me barci.
"Ƴar aljanna buɗe mana lafiya"
Cikin irin muryar barci ta ce"Barci nake ji hajia ki barni nayi"
Cikin nuna kulawa ta ce"Kin tabbata barci kike ji"
"uhm.. ta fara kukan shagwaba ta ce"Barci hajia ki barni"
"To ya isa haka,ta faɗa ta tashi ta fita.
*******
Kallon farrah momy tayi ta ce"farrah Naufal zai aure Sabreen cikin satin nan"
"What? ta faɗa haɗe da zaro idon.
"Taya momy Ya Naufal ɗin?
"Hmm nima saida naji wani iri anya kina ganin ba za'a zamu matsala ba kuwa"