Kenza eBookz

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 16

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 16

Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 16: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 16. daga ita se habibynta Mr azaad amotar se driver…

4,460 words

daga ita se habibynta Mr azaad amotar se driver dake driving dinsu tana kwance ajikinshi Mr azaad shikuma yana shafa bayanta tana bashi labari taji ringing din wayarta cirota tayi a handbag dinta ganin my dad tayi yasa tayi murmushi dama sukadai ne basuyi waya da safen ba tayi waya da su baba da mama ya usman da auta Amira ma ta kirata duk sun musu Allah yakiyaye hanya, dagawa tayi da sallama abakinta ta gaisheshi amsawa uncle kabir yayi suka gaisa yamusu adduah shima sannan yamikawa umma rahina itama suka gaisa tamusu Allah yatsare haka suhaima da ya al ameen seda suka gaisa duka sannan sukayi sallama tana kokarin ajiye wayar kiran anty firdausi yashigo itama tayi musu adduah sannan tabawa daddyn junior bayan sun kammala ta kashe kiran. dede kunnenta Mr azaad ya ce " wow gaskiya wifey ke yar gatace kowa na sonki " fari tayi da ido ta ce " ehh mana shisa yanzu nafika fans " murmushin gefen baki kawai yayi, yasa hannu ya matse libs dinta yamatso da fuskanshi daff da nata har suna shakar daddadar kamshin turaren jikinsu da ya hade yabada kamshi me dadi da tafiya da zuciya yace " baby ai ke din ta dabance dole kifini" yagama maganar yana manna mata kiss a libs din sannan yasake ta gyara kwanciyarta tayi ajikinshi tana shakar kamshin jikinshi hade da lumshe ido, har aka iso airport basu sani ba seda sukaji tsayuwar motar , seda kowa yafito kafin yafito yabudewa fanan murfin motar tafito yarike hannunta suka fara tafiya seyanzu Mr azaad yalura da yan jaridun dasuke wajan tun fitowarsu akeyi musu videos da hotuna hankalin al'ummar airport din duk yadawo kansu ganin wannan shahararren dan kasuwan nan ne tare da matarshi bakaramin burge jamaa sukayi ba kowa se fatan alkhari suke musu wasu na burin Allah yabasu masoya irin Mr azaad, duk yanda sukaso suyi magana da Mr azaad bayuba ko kallon su beyiba jin anfara kiran sunaye yasa suka rungumi juna shida yaseer akunne yaseer ya ce " dude karka yarda ku dawo baku samo mana baby ba " dukan kirjin yaseer Mr azaad yayi Yana fadin" seka hanamu dawuwa ai dan iska " dariya yaseer yayi yace"waneni " haka sukayi bankwana dasu gaba daya suka fara hawa matattakalar jirgin suna daga musu hannu harsuka shige , direct Vip Mr azaad da fanan suka shiga sukadai ne awajan bakowa a vip zama fanan tayi Mr azaad yadaura mata belt , fara tafiya jirgi yayi yana kokarin tashi runtse ido fanan tayi sosai Mr azaad yariketa dan yaga yanda ta tsorata saboda wannan shine karonta na farko hawan jirgi shisa duk tabi ta rikice . duk ta galabaita harwani jin tashin zuciya takeyi kamar zatayi amai yana rungume da ita ajikinshi ahaka hartayi bacci.

19:00pm dede jirginsu yayi landing a Denver international airport , wato karfe 7 nadare kenan alokacin Nigeria duk dacewa akwai tazaran 7hours tsakanin Nigeria da USA . kallon fanan yayi da take bacci duk tayi laushi sau biyu tana amai ƙunce mata seat belt dinta yayi sannan yadauketa cak yafara taka staircase din jirgin hasken da airport din ke dashi tako ina yatashi fanan daga bacci tabude idonta tana karewa airport din kallo , kamar rana kowa se sabgar gabanshi yakeyi airport din kanshi abin kallo ne komai nawajan medaukan hankali.

Wasu jibga_jingar motoci guda hudu sukazo daukar Mr azaad and Mrs azaad kuma dukkansu turawa ne sanye da bakaken suits , har suka sauko daga jirgin fanan bata sani ba hankalinta na kan airport dan ya burgeta sosai , cikin girmamawa turawan nan suke gaishesu beko kallesu ba daya daga cikinsu yabude musu murfin motar tsakiya Mr azaad yashiga dauke da fanan a hannunshi kwantar da ita yayi akan seat yadaura kanta akan cinyar shi shafa fuskanta yayi ya ce " sannu ko wifey munkusa isa gida " da muryanta da baya fita ta ce " to habiby" tafiya sukeyi akan titi slowly kamar wayanda suka dauko sarki ko shugaban kasa har suka iso wani hadedden waje me matukar girman gaske wani katon sign bot kamar tv yana fitar da rubutu da colors kala_kala yana rubuta ' welcome to las Vegas ' babban birnin las Vegas kenan dake cikin kasar america .

Horn sukayi a tangamemen gida masu gadi suka bude aljannar duniyar gidan daya kasance daya daga cikin manyan gidaje a las Vegas komai na more rayuwa akwaishi awannan gidan akashe masa daula iya daula,gidan da ya yakasance mallakin Mr azaad, bude musu gate akayi suka shiga fanan kamar bakauyiya haka takoma domin gidansu Mr azaad na Nigeria bekai wannan kyau ba dukda cewa shima dankararriyar gida amma wannan ya hadu iya haduwa aikunsan banbancin gidajen turai dana gida Najeriya, tsayawa fada muku kyaun gidan ɓa ta ɓaki ne buɗe musu motar akayi yafito dauke da ita ahannunshi, turawa dake aiki a gidan se ɗiban gaisuwa sukeyi haka yashiga da ita cikin gidan kai tsaye wani ƙayitatciyar bedroom yashiga ya kwantar da ita akan makeken gado, luf tayi tana kallonshi daga mata gira yayi alamar tambaya girgiza kai tayi , dukunkune jikinta tayi waje daya saboda sanyi da takeji ganin haka yasa Mr azaad kashe ac sannan ya rufa mata bargo , kayan jikinshi ya cire yashiga toilet yayi wanka da alwala,yafito yasamu harta fara bacci batare da yasa kaya ba yana ɗaure da towel yahau kan makekiyar gadon , yaye bargon yayi yaɗagota yafara cire mata kayan jikinta , bacci ne a idonta duk abinda yakeyi tanajinshi amma takasa koda bude idonta ne haka yadauketa yashiga toilet da ita yamata wanka da ruwan zafi tayi alwala sannan yanaɗota a towel yakwantar da ita akan gadon sosai taji dadin jikinta.

Kitchen din dake cikin part din yashiga ya haɗa mata cornflakes yakawo mata hartayi nisa abacci babu yanda ya iya dole seya tasheta tasa wani abu acikinta baze barta ta kwanta haka ba zama yayi agefenta ya ce " wifey kitashi kisha cornflakes seki koma baccin " tana jinshi sama_sama hakan yasa ta make kafada tare da turo mishi dan karamin baƙinta , murmushi yayi yasa hannu yadagota zama tayi tana marairaicewa kamar wacce tasha maganin bacci dakyar ta iya cewa " habiiiiibyyyyy kabarrrrni inyiiiiiii bacciiiii " yanda take jan maganar nata seda yaji tsigan jikinshi yatashi musamman yanda takira shi se dayaji har cikin ranshi , fa ra bata yayi abaki harta shanye duka batama san tashanye ba kwanciya take kokarin yi yarikota ya ce " ki bari muyi sallah seki kwanta" dressing room yashiga yadauko mata wandon da riga na bacci masu kauri se katon jacket din rigar sanyi domin ana sanyi sosai bude trolley dinta yayi yafito mata da hijab , shima jallabiya yasaka , sannan yadawo bedroom din, sa mata kayan yayi ya shimfida musu sallaya jansu yayi sukayi sallolin da ake binsu bayan sun idar tayi addu'a ta haye gado ta kwanta se bacci murmushi kawai Mr azaad yayi shima agajiyen yake hakan yasa yakashe wutar dakin yabar bedside lamp yaja musu bargo hade da musu addu'a bacci .

To sekuma gobe inme duka yakaimu da rai da lafiya .

Waiting for your comments and share fisabilillahi 🙏. https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 ( Yar lelen Jarumai)

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚

⚜️📚 J. W. A 📚🖋️

Gargadi.... Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowani siga ko a karanta minshi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira koda Allah nabar mutum ze sakamin kuma yabimin hakkina.

PAGE 6️⃣0️⃣

NIGERIA

Adamawa Yola

Shigowa lukman yayi yadawo daga office yasamu nusaiba zaune tana chatting dinta hankali kwance tanajin shigowar shi amma ko dago kai batayi ta kalleshi ba balle yasa ran zatace mishi sannu da dawuwa girgiza kai yayi kawai yana mata fatan shiriya domin tunda akayi aurensu yake fuskantar bacin rai daga wajan nusaiba betaba ce mata uffan ba balle yabiye mata haka zata tsaya ta mishi rashin kunya iya isarta ko kadan bata ganin girmanshi ta renashi ga tsanar datayi mishi tunda akayi auren wani abu be taba shiga tsakaninsu ba a matsayin miji da mata , bata daga tsinke bata da aikinyi se chatting da kawayenta ko girki bata tabayi mishi ba kullum a restaurant yakecin abinci duk da akwai me aiki agidan amma nusaiba tahanata shiga mata kitchen bakomai ne yayi tasiri awajan nusaiba ba fa ce huɗubar da mahaifiyarta madina tayi mata.

wanka yayi yafito yazauna afalon har lokacin tana nan a inda yabarta bata motsa ba se hira takeyi da kawayenta a whatsApp, zuba mata ido yayi yana kallonta kamar wani me nazarin wani abu wata uwar harara nusaiba ta watsa mishi lokacin da ta ankara yana kallonta sannan ta ce " meye haka ? Kazo kawani sani agaba kana kallo mtsssw " ta gama maganar hade da jan doguwar tsaki kamar wacce take magana da sa'anta, ran lukman yabaci sosai da tsakin dataja mishi ya ce " nusaiba ni kika jawa tsaki?" Kallon tara saura takwas tayi mishi tana ƙaɗa kafa ta ce" ehh kai nayiwa wannan tsakin lukman! nace kai nayiwa kadau mataki , inka isa cikekken namiji ka sakeni mara zuciya kawai " murmushi me ciwo lukman yayi kafin ya ce" nusaiba kenan kice gaba da barin duniya tana ruɗarki da kuma hure miki kunne duk abinda zakiyi sede kiyi amma bazan taba sakin kiba wannan alkawarine nadaukawa kawu , amma kisani nikaina bawai kaunarki nakeyi ba kawai de so ne na yan uwantaka bayanshi babu komai araina , tun yanzu Yakamata kizubar da mukaman yakinki ki karbi wannan auren namu hannu bibbiyu tun kafin lokaci yakure miki " duk maganar dayakeyi mata nan cikin sanyin murya yakeyinsa dukda kuwa ranshi abace yake lukman yana da sanyin hali sosai , haka yatashi yabarta a falon tana cika tana batsewa , gani takeyi babu wanda aka cuta sama da ita za'a aura mata lukman ita ai ba sanshi takeyi ba kuma dole taci gaba da yi mishi abinda Madina take fada mata domin ta wannan Hanyar ce kadai zasu samu ya saketa.

Yau de Allah yayi dare gari ya waye se yau Mr azaad yabawa su spider umarnin ƙyale alh Ibrahim tijjani su da kansu suka fitar dashi wajan gari suka hankaɗoshi waje yafadi aƙasa timm kamar wani kayan wanki, duk yabi ya yamutse yafita a hayyacinshi ya canza kamanin wannan tumbin nan nashi duk seda ya sa ce dan baƙar azaban dayasha tabbas yaji jiki bana wasa ba, dede da yatsun hannunshi dakyar yake iya dagawa fuskan nan ya kumbura sumtum ya tara jini musamman idonshi , yana yashe akan hanya motar ambulance yazo suka dauke shi suka wuce asibiti dashi .

_____ jikinta na matukar rawa take magana tana nunashi da yar yatsa ta ce " bazeyuba ! baze taba yiwuwa ba ka cuceni ! in kyaleka? baka isaba kayi kadan amjad" wanda takira da suna amjad yana zaune yazuba mata ido hankalinshi kwance ya ce " keee aneesa karki yarda kice zaki nunamin akuyanci koɗan kinga nayi shuru na ƙyaleki ne ? Ni bance kin cuceni ba se kece zakice na cuceki" aneesa dake tsaye a kanshi tana huce idonta yayi ja sosai duk alamu sun nuna kuka tasha ta koshi ta nunashi da yatsa tana fadin " kayi kaɗan ka shafamin cuta sannan ka hanani magana HIV positive fah nagani toma dakake cewa bakai ka shafamin ba agidan ubanwa nasamu to? iyeeh nace agidan ubanwa nasamu inbakai kasamun ba?" murmushi yayi irin nasu na gogaggun yan duniya yabata amsa da " ai badani kadai kike yawon tazubar ɗinki ba , waye besan ke karuwa bace zaki zo ki dameni kina cemin nina shafa miki HIV kije can kinemo sauran abokan holewarki " kukan kura aneesa tayi ta cukumi kwalar rigar amjad afusace ta ce " amjad nikake fadawa haka halaccin dazakamin kenan , kaine na mijin daya fara amfani dani a matsayin virgin , kyautar budurcina fah nayi maka amma yau kaine kake cewa wai ai bakai kadai kake amfani dani ba , to naji bakai kadai bane amma ai kasani kai da ya ne kake sex dani batare da condom ba kaga kuwa dole kaine ka shafamin HIV " fincike hannunta daga kan rigarshi yayi ya ce " karamar yar iska kema yanzu da kanki kinfada ai bani daya kike sex ba to wallahi nasakejin kince nine nashafa miki HIV ranki se yayi mugun ɓaci " Azafafe tadau handbag dinta da wayoyinta tafita a hotel room din tana me danasanin sanin amjad a rayuwar ta.

SATANIC

Duk suna tsaye sunyi shuru suna jiran suji abinda shugabansu tanzarzar zece shikuwa yana hakimce akan kujeran mulkinsa cikin murya me amo ya soma magana " hafsat ta kasance daya daga cikin mu, babba me muƙami ce , amma mutuwar nata shine dede agareku domin zata iya tona muku asiri yanzu amanta da babinta, lokaci kara kurewa yakeyi inason yanzu nan da wani lokaci ƙalilan zamuyi sacrifice (sadaukarwa)mata masu ciki da kuma jarirai sekuma mata masu jego duk wani asibiti dayake cikin wannan gari dole ashiga akashesu wannan shine babban sadaukarwar dazamuyi wanda tun bayan shekara ɗari ba'a ƙara yi ba , idan muka yi shi ze taimaka mana wajan samun sarauniyar nasminaya, nan da yan watanni zaayishi . Akalla muna bukatar masu ciki guda dari se jarirai maza da mata guda hamsin se masu jego hamsin doleeeeee ayi wannan sadaukarwar " yagama magana cikin sake tabbatar musu da hakan ze faru bayan sun gama tattaunawa yabawa kowa izinin tafiya nan da nan suka zama jemage suka ɓace.

U S A

LAS VEGAS ✈️

Gjiyar da sukayi ne yasa tunda sukayi sallah asuba suka koma bacci basu tashi ba har se wuraren karfe 11 na safe kafin suka tashi sukayi wanka, sukayi breakfast sannan suka fito ze nuna mata gidan suna sanye da riga iri daya tshirt se wando jeans tasa hula akanta suna rike da hannun juna suke ta zagaye gidan duk inda suka wuce se ma'aikatan gidan sun gaishe su ita ce ma take amsawa amma Mr azaad ba amsa musu yakeyi ba babban garden din gidan suka shiga dayasha furanni kala da iri wajan ya matukar kayatarwa fito da wayarsa yayi yafara daukanta hotuna sannan yamusu selfie sunyi kyau sosai sun dan jima a garden din suna hiransu gwanin sha'awa kafin suka bar garden sukaje swimming pool yana da girma shima ya haɗu sosai yanda ruwan yake blue in color ne ya burge fanan yasa ta ɗan sunkuya tasa hannunta acikin ruwan tana wasa dashi tana dariya , Mr azaad na gefe yana mata video batare da tasani ba kiran sunanta yayi tadago ta kalleshi ya ce " baby ko zaki shigane " girgiza kai tayi ta ce " noo habiby ai ban iyaba " " yau zanfita meeting dana koya miki amma zan koya miki ko wani lokaci" cewar Mr azaad daya iso inda take yasa hannu yadagota suka koma kan kujerun da suke wajan swimming pool din suka zauna call ne yashigo wayarshi sunan Abba ne yabayyana picking yayi sukayi waya yamusu ya gajiya sannan ya ce yabawa fanan karba tayi sukayi waya da Abba dake falo tare da duk wani dan gidan haka seda suka gaisa dakowa cike da farin ciki sannan sukayi sallama , kiran layin baba Mr azaad yayi yagaisheshi sosai baba yamusu sannu da hanya nan ma seda suka gaisa da duk yan gidan , sun jima awajan suna hira kafin suka koma cikin gida. Haka rayuwar su taci gaba cike da soyayyar juna da jindadi , haka yan gida Nijeriya kullum sesunyi waya dasu harda video call, ranar da ummi takira Mr azaad yana office sukayi waya dama tun zuwansu takeson fada mishi magana ɗan gane da fanan ta ce " son please ka kula da feena sosai sannan la kaita asibiti amata pregnancy test domin ni naga kamar akwai ciki atare da ita " murmushi Mr azaad yayi shima yayi experiencing hakan amma da sukaje asibiti se yazama ba haka bane ya ce " ummina nima nayi tunanin hakan amma kafin muzo seda mukaje hospital aka mata test babu ciki ajikinta" jinjina kai ummi tayi sannan ta ce " to Allah yakawo babban rabo " ya amsa mata da ameen sannan sukayi sallama.

AFTER TWO MONTHS

yau watan su fanan biyu dazuwa USA kuma haka zalika watansu biyar dayin aure , Shakuwa me karfin gaske yasake shiga tsakani Mr azaad da fanan wani irin narƙekkiyar da kuma zazzafar soyayya suke nunawa junansu hankalinsu kwance duk sanda yadawo daga office haka ze dauketa sufita yawa wajaje daban_daban , alhamdulillah Mr azaad ya gama meeting dakuma aikin daya kawoshi , sannan ummi tafara mishi maganar dawuwarsu saboda auren amare da angwaye saura sati uku anata shirye-shiryen biki sannan tasake tuna mishi maganar tsayawar da zasuyi a dubai kamar yanda tafada mishi kafin su tafi .

Bacci yake son yi amma fanan ta hana shi tana zaune akan cikinshi ta cusa hannunta acikin gashin kanshi tana mishi tafiyar tsutsa ranƙwafo da kanta tayi dede kunne shi kamar raɗa zata mishi da karfi ta ce " habibyyyyyy ! Katashi muje shan ice cream din" runtse ido Mr azaad dan sautin muryanta data ɗaga seda yakusa kashe mishi dodon kunne yau tunda ta tashi take mishi rigima akan ice cream kuma ya ce zeyi order akawo mata har gida ta ce ah ah sede suje su siyo .

Juyawa yayi da ita tadawo ƙasanshi ya mata rumfa da faffadar kirjinshi daɓe sanya riga ba ga kwantaccen gashin kirjinshi dasuke ƙara mishi kyau kallonta yayi da rinannun idonshi da suke cike da bacci a cikinsu ya ce " haba wifey yanzu baccin ma bazanyi in peace ba " fiki_fiki tayi da ido kamar wacce batada gaskiya ta ce " nide Allah barakayi baccin nan ba semunje mundawo " zuba mata ido yayi yana kallon yanda take motsa dan karamin baƙinta dayasha libstick se sheƙi yakeyi dawo da kalloshi kan dara_daran fararen idonta yayi dasuka kasance oily eyes suna dauke da zara_zaran gashin ido , hannunshi daya yasa yana shafa kyakkyawar fuskantar , turo mishi baki tayi cike da wani iriyar shagwaba ta ce" katashi mutafi ko in maka kuka " yanayin yanda tayi maganar da yanda ta shagwabe mishi ne yasake narƙar da zuciyar Mr azaad besan lokacin da ya hade baƙin su waje daya ba , daura hannunta daya tayi akanshi tana shafa mishi kai sannan dayan tafara shafa mishi kirjinshi musamman wajan nipples dinshi da kwantaccen gashin kirjinshi, kara ingiza Mr azaad tayi da irin wannan salon nata sa hannunshi yayi ya fincike yar ficiciyar rigar da ke jikinta yadaura hannunshi akan dukiyar fulaninta yafara wasa dasu sannan ya gangaro da hannunshi izuwa private part dinta ya soma wasa da wajan dogon numfashi fanan taja tasake cusa hannunta cikin sumarshi seda sukayi romancing juna sosai kafin suka fara sex tsabar yanda Mr azaad yakejinshi awata duniya har hawaye yakeyi ɗan dadin dayakeji daura bakinshi yayi akan dukiyar fulaninta yafara sha kamar yasamu sweet kokuma lolipop , abangaren fanan ma ba'a barta a baya ba duk wani salo datasan ze gigita Mr azaad seda tayi shi maida mishi da martani gaba daya sunfita hayyacinsu , ganin sunyi nisa ne sunfita anamu duniyar yasa na lallabo nafito naja musu kofar dakin. Bayan one hour nakoma dakin bakowa aciki suna bathroom suna wanka , fitowa sukayi atare jikinsu sanye da rigar towel , hand dryer fanan tadauka ta busar da gashinta tashafa mishi mayuka ta taje daukan ribbon tayi taje wajen Mr azaad dake zaune akan kujera yana danna wayarshi ta mika mishi kallon ribbon din yayi kafin yasa hannu yakarba ɗurƙusawa tayi agabanshi tabashi baya haɗe gashin yayi yamata fakin dinshi sannan ya manna mata kiss a tsakiyar bayanta da wuyanta yana kokarin sa hannunshi acikin rigar ne tayi saurin mikewa dan tasanshi yanzu se yayi loosing control dinshi kuma hakan zesa zuwa shan ice cream din yakai anjuma , kallonta yayi ganin yanda ta mike da wuri ya jefa mata tambaya " kin gaji ko ?" dasauri ta girgiza mishi killer smile yayi ya ce " bari mudawo zakiyi bayani ne " komawa gaban mirror tayi ta shafa lotion hade da fesa body spray dan kadan yanda kamshin baze tashi ba , dressing room tashiga tana sake kallon bangaren da kayanta suke yawancin kayan jeans ne da riguna se rober jeans da kayan bacci se kana nan kayan sawa agida se dogayen riguna wa'yanda ko kaɗan basu da nauyi kuma masu hannun vest, ko falazo datake sawa ta saƙe babu aciki tasan wannan aikin Mr azaad ne , gasu nan ɓirjik rasa mezata sa tayi kawai ta fito da wandon jeans da kuma riga body hook Black color jacket me tsayi datasan ze rufe mata jiki tadauka wanda tsayinshi zekai guiwanta. Saka riga da wandon tayi tasa takalmi shau ciki tadauki gyale da jacket din tariko su a hannunta tafito yanda ta barshi haka tasameshi , sauke sexy eyes dinshi yayi akan hips dinta dasuke acike tam sun cika wandon kamar zasu fito ga body hook din dayabi jikinta yakwanta boobs dinta sun kara cika sosai da kugunta , kasa dauke idonshi daga kanta yayi kamar wanda ya samu tv tacikin mirror ta lura da irin mayen kallon da yaƙe binta dashi yasa tafito da harshe tanayi mishi gwalo hade da juya mishi hips dinta dasuke tsone mishi ido, lumshe idonshi yayi kafin da murya irin wanda yake cike da sha'awa ya ce " baby kici gaba da tsokanoni kika bari nazo wajan nan Allah se na sake round two " ai kafin ma ya iddasa abinda ze fada fanan tadauki jacket dinta daya kasance white color tasaka , tahaɗe botil din jacket din sannan tadaura belt din rigar sosai kayan yazauna ajikinta tayi kyau sosai kamar asace daukan baƙin gyalen tayi rolling dinshi , irin kyau datayi ba'a cewa komai tsaff tagama shiryawanta Mr azaad kawai take jira yana zaune har lokacin be cire towel din ba bekuma tashi daga inda yake ba , ɓata fuska tayi ta ce " habiby katashi kashirya ni nagama fa " yanda tayi maganar yaso bashi dariya amma yafuske, mikewa yayi yazauna agaban mirror daukan lotion tayi ta shafa mishi sannan tafesa mishi body spray ta gyara mishi sumar kanshi tashiga dressing room tafito mishi da kaya da takalmi sannan taje jerin da inda facemask yake tadauko tafito , tayashi tayi yasa kayan sannan ta bashi facemask da alamar tambaya ya kalleta ta ce " ehh kasa ni banason mata su kalle minkai ne ai" sawa yayi batare da yace komai ba, yagama shiryawa ya kamo hannunta suka fito dauko wata ɗanƙararriyar motar driver yayi securites suka bude musu motar suka shiga masu gadi suka bude musu gate suka dau hanya. Tunda suka dau hanya inbanda shagwaba babu abinda take mishi shikuma ya biye mata baturen driver se kallonsu yakeyi tacikin madubin motar yana murmushi domin sun burgeshi .

Packing yayi a ƙayitatciyar wajan shan ice cream a saman wurin an rubuta 'lappert's ice cream ' gurin ya haɗu sosai bude musu motar driver yayi suka fito , tun kafin sukaraso wajan ma'aikatan dake aiki awajen sukazo suna gaishesu hade da nuna musu hadeden wajan zama suka basu list ɗin ice cream din karba fanan tayi taga sunaye kala_kala tama rasa wanne zata zaba , can tayanke decision ta zabi kusan guda uku tanuna musu hade da mika musu list ɗin karba sukayi cikin girmamawa, maida hankalinta tayi kan Mr azaad dake pressing phone ta ce " habiby to in mungama anan zamuje neman wainar masa ko?" Hade hannaye biyu Mr azaad yayi alamar roko ya ce" wifey kiyiwa Allah kiyi hakuri karki ma sa waina aranki dan aƙasan nan ba samu zamuyi ba Please and please " kunshe dariyar dayaso kufce mata tayi yanda yake rokon ta ne yabata dariya ita kanta tasan basamu za'ayi ba kawai tsokanarshi takeyi tanaso taga reaction dinshi hararan wasa yamata ya ɗan ja kumatunta saboda yagane tsokana ce ya ce " zanyi maganinki " suna haka waiters suka kawo mata ice cream kala ukun data zaba akan tray me kyau suka ajiye hade da fadin "enjoy your day ma'am" yatafi daukan na farko tayi daya kasance vanilla flavor ta fara sha, tanasha tana lum_lumshe ido ɗiba tayi zata kaiwa Mr azaad baƙi ya ce " no baby just enjoy banason shan sanyi " gyada mishi kai tayi taci gaba da shan ice cream dinta.

Bayan tagama ne ya kira waiter din ya ce mishi yamusu fakejin din wasu komawa waiter yayi can yadawo suna ahannunshi anyi packing dinsu aguri daya karban acct no su yayi yamusu transfer sannan suka tafi , se yamma liris suka dawo gida, tana tsaye agaban mirror ta sauya kaya zuwa riga yar yalo_yalo mara hannu dede cinya tana cire ribbon din kanta , yashigo yasameta, ta cikin mirror taga shigowar shi rungumeta yayi ta baya yakwantar da kanshi akan wuyanta yana shaƙar kamshin jikinta, kallon kansu sukeyi acikin madubin suna sakarwa junansu sanyayyar murmushi, cire mata ribbon din yayi yasa kanshi acikin gashin nata yana shaƙar kamshi mayukan gashin datake amfani dasu , juyo da ita yayi suna facing din juna kafin yasa hannu yaɗagata yaɗaura ta akan mirror din hannunshi kan cikin gashinta yana yamutsawa , dan ɗuƙowa yayi yamatso da fuskanta daf danashi , bude dan karamin pink libs dinshi yayi yafito da harshenshi waje tana ganin haka yasa tahaɗe bakinsu waje daya suna aikawa juna hot kiss sosai sukasha soyayyar su suka koshi.

Bayan kwana biyu sun kammala shirin su na tafiya ya yanka musu tickets din dubai washe gari suka wuce airport , lokacin da jirginsu yatashi wannan karon bata tsorata sosai ba tayi luff ajikin Mr azaad.

Yan masarautar dubai duk sun hallara a airport din suna jiran Flight dinsu yayi landing. befi 20mint da zuwansu ba jirgin yayi landing a Dubai international airport, fitowa sukayi hannunsu na cikin na juna hango yan familyn nasu yayi, dukkanin su fuskokinsu dauke da murmushi, shimfida musu royal carpet akayi daga bakin matattakalar jirgin har izuwa bakin motocin dasuke wajan wa'yanda aƙalla zasu kai guda goma sha biyar, tafiya suka farayi akan carpet din wanda ajikinshi aka rubuta welcome home , ƙuyangu se watsa musu flowers sukeyi , acikin wa'yanda sukazo tarbansu harda kawunsu asaad da matarshi da kuma yayanshi se kuma ƴayyun ummi rungume Mr azaad sukayi suna farin ciki ganin su fanan na gefe tana kallon su tana murmushi, matar uncle asaad ce tazo gabanta tasa hannu tadago fuskantar tana mata murmushi sannan ta rungumeta haka yan matan da sukazo suma suka rungumeta suna yaba kyanta dukda ita chocolate color ce amma hakan be hana tsantsan kyanta fitowa ba shiga cikin motar sukayi suka dau hanya babban Masarautar Dubai.

Readers Also Read