Kenza eBookz

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 2

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 2

Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 2: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 2. Tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana azkar…

4,498 words

Tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana azkar se karfe 6:30 ta tashi takoma kan gado takwanta dan bacci be isheta ba, se karfe 10 ta farka ta shiga toilet tayi brush tawanke fuskanta fitowa tayi tana shafa cikinta dake kukan yunwa falo tafito jikinta nasanye da kayan baccin dube_dube takeyi tana neman kitchen wata kofa tagani akusa da inda dinning area yake wajan taje tabude kofar katon kitchen ne irin nayan gayu komai akwai aciki kamar wanda tundama mace na ciki tunani tafarayi to dama Mr azaad na girkine karewa kitchen din kallo takeyi yaburgeta sosai wani kofa tagani tabudeshi store ne kayan abinci ne aciki iri_iri kwalin idomie tabude tadauki guda daya se kwai biyu da gesher tafito standing gas takunna tadaura tukunya akai tahada indomie ta jollof da gesher kwai din ta dafashi daban kamshine kawai yaketashi a kitchen din tana gamawa tazuye a plate tasa cokali tafito falo tazauna kure A.C tayi dan tasamu yahuce dawuri seda tafaraci ne talura da basket din dake kan dinning ashe ankawo musu abinci cigaba tayi da cin indomie ta se shishitan yaji takeyi sekace wani ne yasata sawa dayawa ahaka tacinye abincinta , fitowa yayi daga bedroom dinshi babu riga ajikinshi dagashi se short din three quarter kokadan beyi tunanin zesameta ba bema kawo apart dinshi zaa ajiyetaba zama yayi akan kujera yana amsa kiran Faisal dake sanar dashi komai ready su kadai kawai BBC news suke jira okay kawai yace jin muryanshine yasa tadago tace " Ina kwana Mr azaad" kamar bejitaba yacigaba da danna wayarsa tabe baki tayi aranta tana fadin " kaika sani karka amsa din " haka suka zauna a falon kamar wasu kurame can yamike haryakai bakin kofar bedroom dinshi yace " kishirya yanzu zamu tafi and banason jira" yashige bin bayanshi da harara tayi tana kwaikwayan yanda yayi magana sannan tamike tayi wanka tafito da atamfa super wax me touches din pitch da sky blue riga da skirt dinki yayi kyau sosai duk pattern yasha stones ajiyesu tayi tadauko gyale da takalmi half cover se jaka masu matukar tsada zama tayi agaban mirror tadanyi light make up tayi kyau sosai ta gyara gashinta tayi packing dinshi se kyalli yake kayan tasaka sun zauna mata ajiki kamar dama sundauki measurements dinta das das da ita dawuwa gaban mirror tayi da dankwali ahannunta dauri tayi mekyau me shigen ture kaga tsiya wanda akesa mishi kwali aciki amma ita batasa komai ba tayi abunta daurin yazauna sosai akanta akasan daurin kuma gashinta ne wanda tayi packing dinshi feshe jikinta tayi da daddadan turare masu masifar kamshi, gyale tayafa yanada dan girma yarufe mata jiki tadau jakanta tasa takalmi tayi masifar kyau dan karamin bakin nan seyayi kamar tasa janbaki kasancewar libs dinta ja ne gashi tasa mishi libs gloss se shinny yake. fitowa falon tayi tazauna zaman jiranshi seda takusa 10mint tana jiranshi se gashi yafito, yana sanye da tsadadden yard milk color half jumfa gashin nan yasha gyara yayi matukar kyau , wuceta yayi abinshi bece mata ci kanki ba ganin haka yasa tamike tabi bayanshi suka gangaro main falo su Abba da ummi da kowa suna zaune afalon jin takun takalminsu ne yasasu juyawa suna kallonsu bakaramin burgesu sukayi ba sunyi making perfect match zama Mr azaad yayi, tsungunawa fanan tayi har kasa tana gaishesu suka amsa fuska asake zama tayi akusa da zeenat " kai anty fanan wallahi kinyi kyau sosai dama wai kin iya kwalliya shine bakyayi wallahi baki ganki bane " hararanta tayi jin takirata da anty tace " bansan wani iyayi dazaki wani cemin anty tam " batagama magana ba taji areef nafadin " antynmu Ina kwana " waro ido tayi cikeda mamaki qin amsawa tayi kara nanatawa yayi " anty ina kwana" kwabe fuska tayi da shagwaba tace " Abba kanajin su ko kace musu subari banaso " takarashe maganar kamar zatayi kuka dariya sukasa banda azaad daya wurga mata harara , Abba yace " to ai fatima dole suce miki anty tunda yanzu ke matar yayarsu ce " Kara daure fuska azaad yayi jin abinda abba yace karsusa ta renashi mikewa yayi yace " ke tashi mutafi " yayi gaba tashi tayi tace " to muntafi semun dawo " Allah kiyaye hanya suka musu tabi bayanshi ganin motoci har guda goma sunyi shirin fitane ga securities da Sojoji suna fitowa suka dinga kwasar gaisuwa ganin ogansu da wata macen dake jikin hotunansu da aka yada yasa suka fara tunani bude musu motar tsakiya akayi yashiga tsayawa tayi bata shiga ba dagowa yayi yace " dallah malama kishigo mutafi karki batamin lokaci mana" bashiri tashige tazauna nesa dashi fita motocin sukayi agidan suka hau kan titi.

Tunda suka fara tafiya babu wanda yakula dan uwanshi harsuka iso bude musu motar akayi suka fito kusan atare shiga ciki sukayi manager jikinshi na rawa yamusu sannu da zuwa yakaisu har inda zaayi hira dasu.

Photographer's masu shooting videos duk sun hallara suna jiran afara saboda direct live zaayi kowa zega shirin alokacin da akeyinsa , wanda ze gabatar da shirin ne yace start nan da nan suka fara shooting.

Gyara zama yayi yafara da " assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum jamaa kamar yanda kuka sani nine naku me suna jamilu abubakar wanda yau nazo muku da manyan baki wato bakowa bane bace wannan shahararren dan kasuwan damuka dade muna jiran opportunity samun hira dashi Allah beyi ba seyau wanda ayanzu ake zargin kancewa shidin womanizer ne ahausance manemin mata zakuji komai de daga bakinshi wannan kuma itace Fatima muhammad Umar mahaddaciyar Al qur'ani wacce ta taciyo kyaututuka da dama saboda kwazonta itama zamuji komai daga bakinta "

Seda azaad yayi kusan 5min fuska adaure kamar wanda akawa wani abu cike da izza yace " kamar yanda kuka sani am azaad muhammad mainasara sauran labarina kuma beshafe ku ba dan bawan nan ne yakawo niba nazo ne akan qazafin dakukamin nida wife dina kuka bata mana suna saboda kawai biyan bukatarku saboda kawai kusamu kudi kuke watsa abinda ze taba rayuwar mutane batare da bincike ko wani abu ba acikin abinda befi 20 mint ba kuka bata mana suna" mamaki dauke akan fuskar jamilu yace " shin kana nufin kace mana hafeza fatima matarka ce? Amma tayaya? yaushe ? Kayi aure ba tare da sanin duniya ba Mr azaad? Zamuso Karin bayani " azaad kamar bazeyi magana ba yace " itadin matatace anyi aurenmu nida ita a lokacin da saukanta saura 1week aka bari se anyi sauka tukun nan ayi biki nasan jamaa da dama sunganni awajan walimar to bari kuji infada muku nayi shuru ne saboda wasu yan dalilai narabu daku amma ayau din nan banfito ba seda natsayar da matakin dazan dauka akanku kukuma al umman duniya wayanda basawa yan uwansu musulmai kyakyawan zato hakkinmu nakanku irin mugayen alkaba'in dakuka dinga binmu dashi ku kuka sani da Allah " bakaramin sanyi jikin duk wani wanda yake kallon gidan tv yayi ba dasu kansu BBC news seyanzu sukasan sun tabka babban kuskure .

Sallama tayi da muryanta me dadin sauraro sannan tace " Kun batamin suna dukda ni matar aure ce amma haka yayi matukar taba darajata abisa kalaman dakuka rubuta ko tsoron Allah bakuji ba kuka kirani da dadiro harda cewa wai nasha zubar da ciki innalillahi wainna ilaijiraji unnn karku manta kuma kunada yaya mata in baku dashi kuma kunada kanne mata ko kun mantane khamatu dhinu tudanu kunjefa ni ama wuyacin hali saboda bakowa bane sukasan munyi aure ba bakomai nayafe muku amma kusani inkunwa wasu sun yafe wasu fah sede ku hadu agaban Allah tunda ku kwata_kwata bakwabin yan uwanku da kyakyawan alkhari se sharri " sosai jikin jamilu yayi sanyi saboda shi yayi editing da printing din labarin. Murya asanyaye yace " to jamaa ansamu babban kuskure domin labarin nan ba gaskiya bane duk masu bukatar karin bayani ko tambaya zasu iya kiranmu awannan layin wayanmu ayanzu " aikuwa yana gama fadin haka telephone din dasuke amsa kira dashi tayi ringing dannawa yayi yadaga wanda duk maganar dazaayi acikin duniya zataji . " Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum sunana sheikh Sulaiman Ahmad gombe nakirane domin bada shedan ido! Aranar da malama fatima tayi sauka nida kaina naje nasamu malama fatima domin nayaba da dabi'un ta nabukaci tabani daman insamu iyayenta da maganar aure amma taban hakuri ta shaida min ita matar aure ce agaskiya musulman duniya muji tsoron Allah muguji yada karya da jita_jita kokuma sharri " jamilu ne yace" to masu gani da sauraranmu fatan kunji abinda sheikh Sulaiman Ahmad gombe yace muna gdy da shaida sheikh Allah yakara girma " yakatse kiran yaci gaba" agaskiya mun tabka kuskure...

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by MRS 🌹 ISHAM 🌹

Page 3️⃣5️⃣ & 3️⃣6️⃣

" Batare da hujja ba munyi abinda be kamataba a madadina da tashar BBC news muna me matukar bawa Mr and Mrs azaad mainasara hakuri akan laifin da muka musu " shigowa manager da chairman sukayi suname basu hakuri akan kuskuren da akayi domin sunsan muddin Mr azaad yabar wajan nan batare daya hakuraba to kashinsu yabushe. Kafin nan da abinda be wuce 1hr ba labari yabaza duniya kota ina se sakon bada hakuri ne yake shigo TikTok, YouTube, Facebook, Twitter, Instagram, mikewa Mr azaad yayi yace " Nina gama abinda yakoni nan dan haka banda lokacin batawa " yafada yana rike hannun fanan suka fara tafiya se hotuna da video ake musu har suka fita bin bayansu masu tsaronshi sukayi suna bude musu marfin motar shiga yayi yana rike da hannunta zama tayi tana kallon fuskanshi sake hannunta yayi haka sukaci gaba zamansu kamar kurame harsuka iso gida ana bude motar tayi gaba dan sotakeyj taje tabawa su ummi labari , aharzuke ta hango aneesa ta nufota, tana isowa gurinta ta wanketa da mari ta shaketa " wallahi yau sena kasheki ko ni ko ke " kakari fanan tafara saboda shakan da aneesa tayi mata bana wasa bane cikin sauri azaad yakaraso yafisge aneesa daga jikin fanan rike wuyanta fanan tayi tana kuka mari azaad yawanka mata yana fadin " bakida hankali ne kasheta kikeson kiyine " kuka tafashe mishi dashi " baby you betrayed me nizaka yaudara kaje kayi aure a munafurce bayan anmana baiko dama kai munafiki ne bansaniba " ji yayi tabashi tausayi yasan baa kyauta mataba riko hannunta yayi yace" calm down muje ciki " wuce fanan sukayi dake tsaye tana kuka kallonta aneesa tayi tana mata gwalo, goge fuskanta tayi tashiga falo babu kowa aciki haurawa tayi part dinsu afalo tasamesu aneesa nakwance akan kafadarshi shikuma yana aiki a laptop ko kallonsu bata sakeyi ba tashiga bedroom dinta tarage kayan jikinta zuwa wata dogon riga me hannun vest mara nauyi yakamata sosai duk shape dinta yafito tasa hula fitowa falon tayi still suna zaune suna kallon labaran da akeyi akan sharrin da akamusu an wanke sunansu tare dabasu hakuri tanajin sanda Mr azaad yayi kiran waya yana cewa adakatar da su dukda batasan dawaye yake magana ba Amma tafahimci BBC news yabada umarnin adakatar . Jin haka yasa fanan tashiga matsanancin farin ciki jitayi duk bacin rai dinda take ciki ya yaye kitchen tashiga tayi jallof din macaroni da beef yasha vegetables se tashin kamshi yakeyi tadawo falon dan nesa dasu tanacin abincinta gaba daya kamshin yacika musu ciki sedataji ta koshi ta ajiye plate din gefe kasa hakuri aneesa tayi tamike tashiga kitchen din bude tukunyan da fanan tayi girki tayi kozata samu sauran macaroni babu komai aciki dan iya cikinta tadafa dawuwa falon tayi " baby yunwa nakeji kuma abinci kadan tayi basaura kace mata tamin wani kaji" shuru yamata be kulata ba sake nanata maganar tayi ganin zata dameshi ne yasa ya kalli fanan dake zaune tana kallon tv tanashan drinks hankalinta kwance yace " Meye dalilin dazesa kiyi abincin dan kadan tunda yakare seki dafa mata wani " dariyar renin hankali tayi ta kalli aneesar cike da tsiwa tace " ohhh really indafa abinci wata katuwa taci ? To ni baa kawoni gidan nan dan indafawa wata katuwar banza abinci taci ba" cike da mamaki azaad ke binta da kallo with his sexy voice yace " me aka kawo ki kiyi?" Ko ajikinta tace bautar aure da kula da miji dan haka kar wata takara cemin inmata abinci yauwa" mamakin yanda take zaro zance yakeyi yar yarinya da ita wato hartasan wani bautan aure . Akule aneesa tace " to dakike maganar wani kinzo bautar aure nasan komai baby yafadamin dalilin auren naku kuma yanzu da sunanshi yawanku zesake ki ya aureni kinzo kina wani iyayi " magana fanan tayi azuciyarta yazama dole in koya mata hankali , fari tayi da manya_manyan idonta tadaura kafa daya kan daya, Mr azaad de da ido kawai yakebinta . Sa idonta tayi cikin na aneesa tana fadin" kalleni dakyau namiki kama da wacce zaa aura asaka? To shi saurayin naki daya fada miki hakan yafadane dan kawai yakwantar miki da hankali amma inbanda haka meye zeyi dake nifa yarinya ce me kananan shekaru shisa yakyasa yatakura, hankalinshi be kwanta ba seda yaga nazama matarshi kuma yana bani kulawa sosai ko bahaka bane honey sugar ?" Tafada tana kashewa Mr azaad ido daya, yama rasa mezece mata kullum iyayin yarinyar nan da yarintar ta karuwa yakeyi cize libs dinshi nakasa yayi. Kuka aneesa tasa tafita da gudu zuwa part din mommy tana kudurta aniyar ganin bayan fanan domin yau ta wulakanta ta setadau mataki . Seyanzu tafara danasanin abubuwan data fada meya kaita nema, mikewa tayi simi_simi tashige dakinta takwanta tana dariya inta tuna abinda tawa aneesa , kamar amafarki taganshi atsaye akanta tashi tayi tazauna tana narai_narai da ido dukufowa yayi, ja baya tayi, rumfa yamata da faffadar kirjinshi da hannayenshi guda biyu , kallon cikin idon juna sukeyi without a blink sa hannu yayi yazame hulan dake kanta gashinta yazubo akan bed din hannunsa yasa yadamki kan da karfinshi ihu tasa jin azaba rike hannunshi tayi da duk hannayenta biyu tana kuka dagota yayi tsaye still yana rike da gashin. dayan hannunshi yasa yamatse dan karamin bakinta yace " banason inga ina hurting din mutum amma kinja dole sena hukuntaki abinda nakeso dake stay in your limits don't try to cross it inba haka ba sekinyi dana sanin sanina! Bantaba sonki ba kuma har abada bazansoki ba dan ke yarinyace dakanta ke cike da yarinta impact ke bakima kai girman dazan yi rayuwar aure dakeba kinmin yarinya kikarewa kanki kallo dakyau reason din dayasa akayi auren nan shine saboda awanke sunanmu and komai yanzu is steady zansake ki kije kiyi rayuwarki freely kwaila kawai " duk maganar dayakeyi besaketaba yana damke da gashin kanta da kuma bakinta daya matse seda yagama magana tukun yayi wurgi da ita kan gadon yafice. Kukanta tasha mecin rai ahaka bacci yadauketa.

" Mommy wallahi sena kasheta inbahaka ba hankalina baze taba kwanciya ba " cewar aneesa dake magana tana kuka tsaki mommy tayi tace " yanzu ke ko kunya bakiji ba kanwar bayanki zaki tsaya kina mata kuka baki kamata ba kin manta jakin duka ! Wallahi shame on you" sake fashewa tayi da kuka tazo tafada mata instead of sunemi solution tahau ta da fada lura da hakan ne yasa mommy takwantar da murya " is okay my angel karki damu yau yau din nan zandau mataki setayi danasanin abinda ta aikata miki karki kara shiga part din se gobe kinji ko angel din dadi" sake fuska tayi tana murmushi seyanzu hankalinta yakwanta jin mommy tace zatadau mataki akanta.

Har seda time din sallah yayi ta farka taje tayi sallah har time din tana tuna bakaken maganganun da Mr azaad yamata haka tazura dogon hijab dinta tayi falon ummi samun zeenat tayi afalo tana shan rufaida yogurt zama tayi tana karban roban yogurt din tafara sha sake baki zeenat tayi dan batasan da shigowarta ba tace " ikon Allah anty fanan yaushe kika shigo " tana Shan yogurt din tace mata " sanda kike kwadayi mana" dariya zeenat tayi tace" to naji ya kike ya program munganku a tv alhamdulillah komai yatafi successful yanda akeso" " hmmm kede bari kawai nikadai nasan irin farin cikin danake ciki " hira sukeyi har anty Amina tafito tasamesu kallon fuskan fanan tayi taga alamar tayi kuka kiranta tayi wajanta fanan taje tazauna waigawa tayi ga zeenat tace " to anty kwadayis kidan bamu waje zamuyi magana " tashi tayi tayi dakinta maida kallonta tayi kan fanan sannan tace " my fanan meke damunki wani abu azaad yamiki " dasauri ta girgiza mata kai alamar ah ah ta fahimmci tanason boye mata ne yasa tace " karkimin kallon sirka kidaukeni amatsayin antynki firdausi duk wata damuwarki karki boyemin dakuma tsakaninki da azaad semu samo solutions kinji" sosai hankalinta yakwanta dan dama tarasa wazata fadawa damuwarta , bata labarin tun daga dawuwarsu da shaketa da aneesa tayi har izuwa abinda Mr azaad yamata dakuma maganganu daya fada mata. Jinjina kai tayi dan tasan zaa rina kuma bakomai yasa yakula aneesa ba sedon taji haushi amma yanzu dole tadaura fanan akan hanya dazata gyarawa azaad zama dakuma ita kanta aneesa datakeson takurawa rayuwarsu. ____" kinaji abinda kikayi yau kinmin dede domin inkika sake kika kyale aneesa tsaf zata renaki sannan inason kinunawa azaad ke ba yarinya bace kamar yanda yafada shida kanshi zedawo yana baki hakuri da lallabaki ! Tunda harya ce miki kwaila yayi mukuma zamuyi iya kokarinmu dan muyi proving dinshi wrong " zare ido tayi tana kallon anty Amina kamar amafarki " yanzu Mr azaad dinne zewani lallaba mutum har yabada hakuri tabb " sosai anty Amina ta dinga bata shawarwari tayanda zatajawo hankalin Mr azaad duk da fanan tanajin kunyan wasu Abubuwa amma haka tanutsu tana sauraran anty Amina dan tadau aniyar nunawa Mr azaad ita ba yarinya bace. Farin ciki anty Amina tayi ganin fanan tadauki shawararta dakuma wayon data mata yayi tasiri dan ita tayi hakan ne da tasamu su dede ta kansu dan tasan yanda Mr azaad baya son fanan, haka itama fanan bata sanshi auren kawai Allah yayi de zaayi shine .

Duk sunyi sallah isha suna zaune akan dinning zasuyi dinner kowa ya hallara harta Mr azaad yafito serving dinsu akayi suka faracin abinci kwarewa fanan tayi tana yar tari kadan_kadan suna mata sannu abu kamar wasa tari yayi karfi hartana biga kanta da table din gaba daya rudewa sukayi suna mata sannu anty Amina da ummi suna bubbuga bayanta. Nan take kuma tarin yatsaya suka bata ruwa tasha idonta yayi ja dan wahala , rike wuyanshi yayi dayaji kamar anshake shi jin shakewan yayi yawane yasa yamike rike da wuyanshi yana kakari kamar wanda zemutu tashi sukayi arude suna nufo wajanshi sosai aka shakeshi amma su basa kallon kowa se rike wuyanshi dayayi babu yanda basuyi ba dan su cire hannunshi akan wuyanshi amma sun kasa. lokaci daya jikinta yayi wani irin kaduwa akayi walkiya da karfi farin haske yarufe ko ina tashin hankali baasa mata rana gaba daya yau sunga abinda basu taba gani ba hasken seda yakai 5mint kafin yawashe duk sundukufa akan Mr azaad dake kakarin mutuwa se adduah sukeyi mishi ga farin hasken daya tsorata su mikewa azaad yayi yazauna yana sake wuyanshi jin ansakeshi , Karan sarkan kafa sukaji duk taku daya idan tayi se yayi kara juyawa sukayi domin ganin ta idan karan kefitowa tozali idonsu yayi da SARAUNIYAR nasminaya cikin shiga ta jarumar sarauniya dakuma sadaukiya wacce ta amsa sunan ta jaruma farin wando ne me fadi kamar wandu nan Pakistan kafan wando kamar ansa mishi roba se riganshi me hannun vest tsayinshi har kusada guiwanta farin kayane sol anmishi kwalliya da zinari domin kayan da sarki da sarauniya suke sawa ma daban ne asaman kayan kuma ga irin rigunan nan kamar nakarfe da akesawa idan zaa fita yaki bayanta nadauke da kwari da baka dasuke cikin gidansu akillace suna jiran kota kwana. se kugunta dake dauke da wukane dogo na sarauta awajan , kunnent,wuyanta duk suna sanye da sarka da dankunne harta dantsen hannunta nadauke da wasu irin saraquna , kafanta tana sanye da sarkokin kafa na zinari dawo da kallona na iya izuwa fuskanta da kanta gashinta nagani yakara tsayi amma bawani sosai ba yayi curly anzubasu agefen wuyanta nadama dana hagu sauran kuma suna gadon bayanta anmusu kwalliya da sarkan kai ( head band chain) ga crown 👑 akanta me matukar kyau fuskanta kamar wacce akayiwa kwalliya ( umm to aidole ma aga fuskar sarauniyar aljanu da kwalliya ) dan karamin bakin nan yasha dark maroon janbaki idonta na sheki sosai . Fuskanta ahade kamar hadari gaba daya ta tashi daga fanan din dasuka sani se takoma ainihin sarauniya babu abinda takeyi daya wuce yalki saboda gwala gwalan dake jikinta gaba daya gakuma daddadar kamshin dake fitowa ajikinta wani irin masifar kyau takara . Suman tsaye sukayi suna kallonta tunani suka farayi kode yaune ranar komawarta masarauta gaba daya sukaji tayi musu gwarjini jikinsu yayi sanyi, tafiya tafara kamar wacce take lankwasa jiki da gangan takaraso wajansu ko kallon direction din dasuke batayiba tasa hannu tashake iska tunani suka farayi meye to tashake dansu basu ga komai ba. Cikin wata murya me zaki da amo tayi magana tana karkata kanta gefe kamar wata robot " ki bayyana kanki " seda falon ya amsa da muryanta aikuwa tana gama fadin haka wata halitta tabayyana cikin bakaken kaya mara kyaun gani seda sukaja baya banda azaad.

Dagata tayi suka fara tafiya a sararin iska acikin falo seda suka kusa roof din falon suka bace batt.

Sunshiga cikin damuwa yanzu shikenan bazasu sake ganin fanan bah kenan zeenat se kuka takeyi, iyayenta zasuji zafin tafiyanta batare da sunyi bankwana ba, Mr azaad ne yace " Amma ai waadin tafiyanta beyi ba bekamata ace tunyanzu harta tafi ba " abbane yace " Kuma hakane waadin tafiyanta beyi ba taya zaayi ta tafi yanzu kila abinda yafaru harin da aka kawone yasa jaaazana bayyana ajikinta da sauri " jimami suke tayi har sha Daya nadare basu kwantaba wani security ne yashigo falon da gudu haryana kokarin faduwa zuba mishi ido sukayi suna kokarin tambaynshi lafiya yayi saurin fadin " ranka yadade naje zanrufe kofan garden ne naga mutum akwance awajan jin haka yasa Mr azaad fita da sauri yafice yanufi gadin din suma suka rufa mishi baya tundaga nesa daya hango hijabin jikinta tana kwance plat bata motsi yaganeta sa hannunshi yayi yadagota kamar yar babyn roba yayi ciki da ita ahanya yahadu dasu ummi duk sunfito sunbi bayanshi ganinshi dauke da itane yasa suma suka koma ciki haurawa yayi da ita part dinsu dakatawa sukayi afalon suna alhamdulillah sannan abba yacewa kowa yaje yakwanta se gobe haka kowa jiki amace suka tafi.

Direct bedroom dinshi yayi da ita yakwantar da ita akan bed hannu yasa yacire mata dogon hijab din jikinta da kayanta yarufeta da blanket yashiga bedroom dinta yabude wardrobe yadauko sleeping dress white color me guntun wando yadawo yasa mata kallon kirjinta dake cike da dukiyar fulani yayi nan take yaruntse ido yanajin haushin kanshi naganin dayayi mata yagyara mata kwanciya, yayi toilet bayan kamar 15mint yafito yayi wanka yasa sleeping dress dinshi yahau bed din dan nesa da ita kadan yaje yakwanta yana rufe jikinshi da blanket yayi musu adduah yakashe wutan dakin yabar bedside lamp. ____ cikin dare tafarka da zazzabi jikinta rau zafi cikin bacci yaji kamar sheshekar kuka tashi yayi zedubata yagansu manne da juna yana rungume da ita ajikinshi kokarin raba jikinsu yakeyi tasake rikeshi tana " uhmm uhmm sanyi nakeji karka tashi" tafada ashagwabe kallon fuskanta yayi da hasken dake gefen bed din idonta arufe ga hawayen datakeyi gashin idonta sunyi zara_zara seturo baki takeyi duk abinda take fada acikin baccine da zafin zazzabi kallon cute face dinta yayi yasamu cikin dabara yatashi toilet yaje yadibo ruwa a bowl medan fadi yafito da karamar towel ahannunshi zama yayi akan bed din yatallafo ta jikinshi so yakeyi yadan goge mata jikinta da ruwan sanyi saboda zafin da jikinta gashi dole seya cire yacire mata riga amma yana tunanin karta tashi tayi tunanin wani abu tazo ta renashi he has no choice hakan yayi yacire rigan yafara goge mata jikinta da towel din jin hannunshi na gogan kirjinta ne yasa yahakura yamaida mata rigan yakwantar da ita locker dayake ajiye magunguna shi yabude yadauko mata magani tashinta yayi , kallon fuskanshi tayi tace " miye! miye ? katasheni nikam bacci zanyi " sa mata magani yayi ahannunta yace tasha bata fuska tayi ganin kwayan magani fashewa dakuka tayi nikam " bazan shaba " tafada tana make kafada ganin inya biye mata dagasken bazata shadin ba, yasa yawatsa kwayoyin maganin cikin glass cup suka jiga dan kwantar da ita yyi ajikinshi yasa hannu yamatse bakinta yadùra mata kakarin amai takeyi yahade bakinsu waje daya seda yatabbatar aman ya koma kafin yakwantar da ita shima yakwanta manne da ita ajikinshi

Karfe 5 dede tafarka jinta ajikinshi yasa tayi saurin tashi sosai abin yadaure mata kai metakeyi ajikin Mr azaad akuma dakinshi duk abinda yafaru adaren jiya ta manta kallon jikinta tayi taga kayan datake sanye dasu waro ido waje tayi data tuna ai ita dogon riga ne da hijab ajikinta taya akayi suka dawo kayan bacci kuma gata a dakin Mr azaad zuciyarta ce tace " waye kike tunani zeyi haka Mr azaad ne mana" cikin sauri takalleshi bacci yakeyi abinshi hankali kwance sadaf _ sadaf ta tashi tabar dakin tashiga nata dakin wanka takesonyi dan kwata_kwata batajin jikinta da karfi.

To bari muleka bangaren mommy.

Awurge a tsakiyar falonta nahangota acikin mawuyacin hali se numfashi takeyi dakyar kamar zata mutu kayan jikinta duk ya yayyage ga jikinta nafitar da jini kamar wata al majira. Abinda yafaru shine bayan tayiwa aneesa alkawarin gamawa da babin fanan atime din dasuke dinner taje da niyar kasheta tayi iyayinta ana haka taji anbuga ta da kasa kallon wacce tamata hakan tayi taga ashe khairatyyy ce ganin mission dinta na kashe fanan beyi bane yasa takoma kan azaad kokadan khairat batayi yunkurin hanata ba domin ita umarnin kula da sarauniya kawai jakadiya tabata. Ganin zaayi kisane yasa wani bangaren jaaazana yamotsa shisa fanan ta bayyana a ainihinta ta sarauniya domin takareshi cike da jindadi ganin sarauniya tabayyana khairaty ta duka kasa cikin girmamawa, lokacin da sarauniya ta rike mommy suka bace sararin samaniya takaita tamata mugun duka kokarin ramawa mommy tayi amma ina ko kadan karfinta beze iya da sarauniya ba haka tanaji tana gani taji mata mugun raunika ajiki sannan tasaketa tafado kasa dakyar mommy ta iya lallabawa takoma gida. ___ wasu irin sambatu tayi nan take tanzarzar yabayyana yana wannan dan iskan dariya nashi mara dadinji kafin yafara magana " hafsat nadade da fada miki da ki nisanta kanki da ita gashi yanzu kinjawa kanki ina matsayin shugabanki amma kikasa bin umarni na wannan shine hukuncnki babu abinda zanmiki kije kiyi jinyar jikinki taurin kai yanzu yamiki rana ai" ya karashe maganar yana dariya me karfin gaske kafin yabace bat.

Masha Allah masoyana inata ganin ruwan comments da adduah ina godiya sosai Allah yabar kauna love you Lodi lodi 🌹🫂🥰🥰🥰🥰

Readers Also Read