Kenza eBookz

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 3

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 3

Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 3: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 3. via-…

3,787 words

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by MRS 🌹 ISHAM 🌹

Page 3️⃣7️⃣ & 3️⃣8️⃣

Haka tanzarzar yabace yabarta batare dawani taimako ba , fitowa Mansoor yayi daga bedroom dinshi rikeda shisha pot idonshi ne yasauka akan mommy dake kwance tana fitar da numfashin wahala arazane yanufeta yana " mommy meya sameki haka? Waye yamiki wannan abu?" Ahankali ta iya cemai yakaita dakinta ciccibarta yayi yakaita yana mata sannu.

_____ tana zaune agaban mirror tayi light make up tana sanye da dakakkiyar lace me tsada dinkin dogon riga fitted gown wuyanta yasha sarka da dan kunne na gold tayi kyau sosai takafa dauri , Allah Allah takeyi tagama shiryawa taje ta gaida su abba dan rana harya dan fito karfe 10:30 gama shiryawan tayi tadau gyale tasa da takalmi hill tana tafiya kamar wata me tsoron taka kasa shigowa falo tayi tanajan kofan bedroom dinta jin muryan aneesa tayi se zuba surutu takeyi mamakine yakamata wai ita wannan bata da aikinyi se makalewa mutane, karasowa falon tayi taganta tana zaune atare da Mr azaad jikinsu amanne yakwantar da kanshi ajikin kujeran dasuke zaune idonshi alumshe kamar wani me bacci dan gaba daya surutun aneesa ya isheshi, cike da neman magana taje kusa dasu tatsaya akansu tana rike kugu " ke kam aneesa wace irin mayyace mara zuciya ban rabaki da mijina ba? Kinzo da sassafe zaki hanashi hutawa to baki isaba ki tattara kibarmin part ko kuma inyi maganinki " tana magana ta jijjiga jiki kamar dagaske in anbarta da aneesa din iya dukanta zatayi . Slowly yabude idonshi akan kyakyawar fuskanta shide yagaji da lamarin fanan ciwon kai takesashi dan yalura bajin magana takeyi ba inya biye mata ze iya karyata abanza a wofi.

Sake shigewa jikin azaad aneesa tayi tana fadin " to badole inzo ba keda kwata_kwata bakya bashi kulawa baki masan yanda zakiyi da miji ba so he needs me by his side ! Kinga ni zan mishi abinda bazaki iyaba tunda haryanzu baki gama girma ba" dan zare ido fanan tayi tama rasa mezata fada mata wanda ranta zeyi mugun baci, samun kanta tayi dafadin " aneesa shiyafada miki haka ? To bari kiji jiya kwana mukayi bamuyi bacci ba gabaki daya yanzu haka agajiye nake kawai karfin hali nayi zanfita gaba daya yasa jikina se ciwo yakeyi abinki da yarinya nasan dakece goggiyar yar duniya nasan Koda wasa bazakiji kingaji ba to nina tafi se anjumanku ! Honey sugar bye" tana fadin haka kuwa tayi waje batare da jira amsar da aneesa zata miyar mata ba. Mr azaad kam he's totally out of words lamarin fanan goge mishi hadda takeyi yarinya karama da zaro manyan maganganu kwafa yayi yana fadin " zaki dawo kisameni" ya shige bedroom dinshi yabar aneesa afalon ta cika tayi bam kamar zata fashe.

Ahankali take taka staircase din gaba dayansu sun hallara afalon daga gani abu me mahimmanci suke tattaunawa, tsugunawa tayi tagaida abba da ummi,anty Zainab dasu anty Amina gaba dayansu seda tabisu tana gaidasu, suka amsa da murmushi akan fuskansu areef ne yace " Ina kwana anty ? " Hararan wasa tawurga mishi tana " Allah ya areef banaso kabari " zeenat ma tace " anty fanan ina kwana" banza tayi da ita, dariya sukayi duka , anty shayida tace " yauwa kingama maganarki akeyi segaki nan " murmushi tayi tace " to anty gani " fawwaz ne yace " daman maganar bikinku akeyi kinga kwata_kwata baayi komai ba, so nan da 1 week ko 2 weeks zaayi event din bikin dinner ne da kamu se walima " shuru tayi tana tunanin itada zasu rabu da Mr azaad meye kuma na wani shagalin biki, tana jinsu se tsara yanda bikin ze kasance sukeyi. Abba ne yace " Fatima gobe dukanmu zamuyi tafiya zamu tafi dubai yiwa kakansu zeenat yajiki kwana biyu bayida lafiya bazamu dade ba munso tafiya dake amma kinga ke bakida visa inmun dawo zaku tafi tare da mijinki daga yanzu zuwa lokacin komai dinki zezama ready" cike da kunya tace " to Abba Allah yakaimu" Suna haka se gashi yasauko cikin shirinshi nazuwa office yasha kyau suffarshi ta larabawa yakara fitowa, sakai yayi zefita abba yace " azaad zo nan" dawuwa yayi yazauna kusada abban . __" yauwa namanta banfada maka ba next week inmun dawo in sha Allah zaayi event din aurenka " kaff dinsu zuba mishi ido sukayi dan sonjin mezece. Yau tunda yatashi bayajin yin wata dogon magana ciki_ciki yace " auren waye din ake magana?" Ganin yamanna musu haukane yasa ummi cewa " son auran kai da fanan mana kuma bawai shawaranka muke nema ba! Ah ah munriga da munzartar seka fara shiri zaka iya tafiya" mikewa yayi besake ce musu komai ba dan shibawai ya iya musu bane kuma yasan insukayi magana ba canzawa zasuyi ba.

8:00pm tana zaune afalo tana kallon series din India atashan zee word me suna the promise, jikinta nasanye da guntun wando jeans boom short da wata yar ficikar riga iya cibiya batasa bra ba rabin dukiyar fulaninta awaje wandon yadámeta tam tayi donot da gashinta sosai tayi kyau kamar wata bakar balarabiya, duk da kana nan kayane amma haka taji sundame ta haka tadaure taci gaba da kallon. ___ bashi yashigo gida ba har 9:00 part dinshi yanufa hannu yakai kan handle din ze murda yaji kamar karan tv shiga yayi yahangeta tana zaune tana kallo se shan fruit takeyi batama san da shigowanshi ba, zama yayi akan kujeran dake facing dinta se anan ne taganshi " barka da dawuwa Mr azaad" bece mata kalaba yacire socks din kafarshi yafincike necktie din , tunda tagaidashi be amsa ba bata kara kallon inda yake ba . " Ke tashi kikawo min tea " tashi tayi tashiga kitchen tahada mishi tea tadawo falo bata sameshi ba yasa tawuce bedroom dinshi nanma baya ciki ajiyewa tayi akan center table tana kokarin juyawa taga yafito daga toilet yana daure da towel akugunshi, runtse idonta tayi gam dan tunda take bata taba kallon namiji ahaka ba , karasowa wajanta yayi yasa dukka hannunshi yatallafo fuskanta Murya anarke yace " miyasa kike rufe idonki bayan kina gaban mijinkine ! Ohhh namanta ashe yanzu lokacin dazaki bani kyakyawar kulawa ne oyah Start" gabanta ne taji yana duka da karfi tuna abinda tamusu da safe shine yanzu yake dauko mata maganar, dasauri tajuya da niyar tafiya fincikota yayi tafado akan faffadar kirjinshi dayake dauke da kwantaccen gashi jikinshi gashi ajike da ruwan dayayi wanka gashin kanshi se diga yakeyi mannata yayi da jikinshi hannunshi daya narike da waist dinta. Wani kalan kunyarshine yarufeta tarasa yazatayi tabar dakin. Ganin haryanzu taki bude idanunta ne yasashi sake matseta ajikinshi ba shiri tabude ido, Kallon fuskanshi tayi taga kalan kallon dayake mata nan take tasunkuyar dakai kasa dan bazata juri kallon kwayar idonshi ba , sa hannu yayi ya dauketa kamar yar baby besauketa a ko inaba sekan bed dinshi . kokarin tashi takeyi yasa hannu yamaida ita yamata rumfa kwanciya yayi ajikinta yasake mata nauyinshi duka nan take tafara nishin wahala dan jitayi kamar wanda aka dorawa buhun cement ajiki tureshi takeyi amma ko motsawa beyiba zatayi magana yadaura yatsanshi a libs dinta " shhhh don't say a word ! Kikace jiya bamuyi bacci ba saboda kinbani hakkina? Tom bari inbaki yanzu tunda haka kikeso , aibansan kinaso ba da tun ranar da aka kawoki gidan nan nabaki " fanan ido yarena fata inbanda danasani babu abinda takeyi nan take hawaye yafara wanke mata fuska dan talura Mr azaad babu wasa alamarinshi. Slowly yafara zame mata rigan jikinta harya kawoshi zuwa cikinta sa hannunta duka biyu tayi tarufe kirjinta tana kuka " please Mr azaad don't do this to me" dede kunnenta yafurta " I will! abinda kikeso kenan tunda har kika iyayin shela na gajiyar dake bari ayi na gaskiyan karki damu it won't be hurt" daduk karfinta take dukan kirjinshi tana kuka da rokonshi daya kyaleta bazata karaba. Hade bakinsu yayi waje daya yafara bata hot kiss harda na mugunta na cizon libs dinta da karfi sosai take kuka tana tureshi amma ko motsawa bayayi seda yatabbatar da ta mugun galabaita kafin yadakata yadago yakalleta yana wannan killer smile din nashi dayake kara mishi kyau, shafa libs dinta yakeyi da yayi jajir yadan kumbura dan bakar wahalar dayasha yace " tom yanzu saura inbaki hakkinki ko?" Hawaye na gangarowa daga idonta tace " kayiwa Allah daya halicceka Mr azaad kayi hakuri kabarni" watsa mata harara yayi yace " stupid girl bakince ke mara kunya ba naso yau inga karshen inda rashin kunyan zetsaya yarinya tunbaki tafasa ba kina kokarin konewa harkinsan kicewa wata mijinki ya gajiyar dake saboda taji haushi ko? " Girgiza kai tayi alamar ah ah matse libs din yayi seda tayi kara" ni kurmane dazaki girgizamin kai kokuma ke kurma ce? common open your mouth and talk joo" cikin muryan kuka tace " ah ah " kwafa yayi " I warned you several times amma naga kamar kwata_kwata taurin kanki yahanaki saurarata to muzuba nidake agidan nan kedajin dadi kuma se randa narubuta miki sakinki as from today you're my maid duk wani aikace_aikacen part din nan ke zaki dingayi inkuma ba hakaba " ya kyasta yatsunshi afuskanta, yatashi daga jikinta kifa kanta tayi akan pillow tana kuka daga baya ta tashi tashige bedroom dinta ahaka tacigaba da kuka daga baya bacci yasaceta.

Karfe 5:00am tana kwance tana bacci yana tsaye akanta hannunshi rike da karamin bucket cike da ruwa ahannunshi dagawa yayi ya kwarara mata daga sama har kasa afirgice ta tashi tana salati four eyes sukayi " kitashi aibakiga ta bacci ba kiyi sallah kisameni a bedroom dina" to kawai tace mishi ta tashi tacire bedsheet din da suka jike da ruwa takai toilet ta tasasu a drying machine itama tayi wanka tayi alwala tacanza kaya.

Bayan ta idar da sallah tanufi bedroom dinshi samunshi tayi yana zaune yana pressing din system idonshi sanye da farin glass daga gani wani aiki yakeyi me mahimmanci muryanta ahankali tace " Mr azaad gani" batare da yakalli inda takeba yace kishiga kiwanke toilet dina da jikin toilet din sannan akwai kaya acikin washing machine kifito dasu ki wanke su tass inkin gama kuma banason inga dirty ko kwallin zarrah acikin part din nan and try to finish it before 9" batace komai ba tashiga toilet din tabude washing machine ganin tulin kaya aciki kuma dukkansu wankakkune agoge wasuma baa taba sasu ba sunfi set 50 haka tafito dasu tafara wankewa tuntanayi ta dadin rai hartaji gaba daya tagaji bayanta har rikewa yakeyi. Ba ita tagama komai ba se wajajen 11:30am ko ina tayi kall dashi jiri take gani saboda gajiyan datayi ga yunwa bataci komai ba. Lallabawa tayi tashiga kitchen tadafa indomie da tea tagama ci kenan tadan mike akan kujera har baccin wahala yafara daukanta yadawo tsayawa yayi akanta yana binta da eyes fridge yaje yadauko bottle water yabude yazuba mata afuska dasauri ta mike ganin shine tafashe da kuka " shhhhh yimin shuru dukanki nayi ko zaginki nayi kitashi yanzu muje " yafadin haka yayi gaba babu yanda ta iya haka tabi bayanshi wata kofa taga yashiga bata taba sanin akwai wani bedroom aciki ba seyau shiga ciki sukayi. Sake baki tayi ganin wani room and falon ne aciki sede alamu yanuna kamar yadade duk yayi mugun kura sosai wanda ko mutane uku ne sesunsha wahala kafin sugama gyarawa , tana cikin wannan tunanin taji yace " oya ki gyara side din nan dan zuwa gobe nan zandawo " fita yayi yabarta aciki tunani tafarayi shin ta ina zata fara gyara nan ,neman tsintsiya tayi tashare ko Ina sannan tafara mopping haka tabirkice kamar ba itaba babu abinda yake tsayar da ita se sallah. Har karfe 9 nadare bata gama ba. Hango jakadiya abashiyya nayi da khairatyyy suna tsaye duk wani movement dinta suna wajan gabaki daya ransu abace yanzu sarauniyarsu ake aizabtarwa haka . Khairatyyy tace " shugaba meze hana mudauki mataki akanshi " girgiza kai abashiyya tayi tace " ah ah khairatyyy wannan bangaren rayuwar sarauniya ne shidin mijinta ne mukuma babu ruwanmu da shiga tsakaninsu, domin tsakanin mata da miji se Allah amma abu daya ne nasani shine zeyi matukar dana sani arayuwarshi seyaji yatsani kanshi jizeyi komai na duniya bayamai dadi"

Yinin yau curr su ummi basuji dúriyan fanan ba harsun fara tunanin ko wani abune yasameta , fitowan Mr azaad zasuje masallaci ne yasa suka tambayeshi lafiya kuwa fanan shuru sece musu yayi tana nan lafiya kawai yau batajin fitowane zeenat ne tace " to bari inje intayata hira" mugun kallo yawatsa mata yace koda wasa kar wanda yashigamin part yayi gaba abinshi.

Shigowa yayi bedroom dinta yasamu bata nan side din dayace tagyara yashiga anan yasameta akwance akan tiles ta dukun kune waje daya tana baccin wahala duk tagama aikin dayasata sa hannu yayi yadauketa yanufi bedroom dinshi da ita ajiyeta agan bed tashi tayi tana murza ido kallon ta yakeyi sosai can yace " bace min da gani " atsorace tabar dakin nashi dan ita yanzu tafarajin tsoronshi , batare data cire kayan jikinta ba ta fada toilet tasakarwa kanta shower warm water seda tadau 30mint kafin tafito daure da towel ajikinta duk tagaji batare data shirya cikin sleeping dress ba takwanta dakyar ta iyayin adduah tasamu tayi bacci, haka takwanta batare dataci komai ba.

Yau tun 5:00 ta tashi tafara nafila kafin aka kira asuba tanajin motsinshi lokacin daya tafi masallaci, yau ko komawa bacci batayi ba tafara aikace_aikace koda yadawo yasameta tanayi bece mata komai ba yashiga bedroom dinshi yakwanta , haka tasha aiki se 8:30 tagama komai tahada breakfast taci sannan tashiga tayi wanka tasa riga da wando tazura hijab dinta sadaf_sadaf take tafiya tanason taje gunsu ummi suyi sallama dantasan tsaff zece ze hanata fita tunda yanzu yasata agaba, kamar daga sama taji daddadar muryanshi yana fadin " karki yarda kifita a part din nan kijira tukun " ko waigowa batayi ba haka bata koma tazauna ba fitowa yayi yana sanye da farar jallabiya yabude suka fita. Kowa ya hallara suka dai kawai ake jira sufito jinsu shuru ne yasa ummi tacewa zeenat taje ta kirasu kila basu tashi bane har zeenat tafara tafiya se gasu nan sun sauko sunkuyawa tayi tagaidasu, suka amsa suna tambayarta ko lafiya jiya bata fito ba satan kallon Mr azaad tayi ganin yakafeta da ido yanason yaji mezatace yasa tace " ummi jiyan ne nadan tashi bana wani jin dadi sosai shine Mr azaad yasamomin magani" sannu suka dinga mata. Ahaka suka fito motoci guda 10 ne yakejiransu banda na securities, rungumeta zeenat tayi tana " anty zanyi missing dinki" " zanyi missing dinki nima sosai zee" cewar fanan, zuwa fanan tayi tarungume ummi, murmushi ummi tayi tace" my feena ba dadewa zamuyi ba kinji take care of yourself in son yamiki wani abu kifadamin" tom ummina, haka abba yasake jawa Mr azaad kunne akan yakula da fanan kamar gaske yace " to" sosai tamusu adduah Allah yakiyaye hanya yakaisu lafiya yadawo dasu lafiya, sunjidadin addu'arta sosai. Haka suka shiga motar zuwa airport suna musu bye-bye fanan kam jitayi kamar tayi kuka antafi anbarta da Mr azaad dakyar inzasu dawo susameta araye cewarta. Haka yafinciki hannunta suka koma cikin gidan.

Tundaga wannan ranar fanan bata Kara sanin meye farin ciki ba duk wani hanyar dazata huta taji dadi Mr azaad yadatseshi gaba daya tafita ahayyacinta azabtar da ita kawai yakeyi da aiyuka masu matukar wahala duk tabi tarame tadanyi duhu abun tausayi ko kyakyawar bacci batayi yayi nasarar jefa mata tsoronshi aranta ko muryanshi taji jikinta daukan rawa yakeyi , kuma duk wahalar daze bata baya barinta da yunwa.

Yauma kamar kullum tunda garin Allah yawaye take faman wanke mishi wankakkun kaya da lafiyarsu kalau babu abinda yasamesu haka take tawanki kamar baiwa kwala mata kira yayi da " keee " naman jikinta ne yafara bari tsabajin tsoro haka tafito atsorace tace " Mr azaad gani" cike da izza da gadara yace hadamin black tea " dasauri tafice tashiga kitchen 3mint yadauke tagama tafito dashi hannunta narawa taza mika mishi yadan zuba ajikinshi wani gigitaccen mari yazabga mata a kumatu wanda seda tadena ganin komai nakusan minti uku kawai jinshi tayi yana" ke wacce irin mahaukaciya ce dazaki kona ni da hot tea" hawayen daya wanke mata fuska tagoge tana bashi hakuri dan tasan inya fusata yanzu ze kara mata wani marin daukan cup din tayi takai dustbin dan yadan fashe, tagoge wajan tana danne kukan daya ciyota kiranshi yaseer yayi yasanar mai yana falo.

Hira sukeyi da yaseer tashigo hannunta dauke dasu drinks takawo mishi tunda tashigo yaseer yake kallonta da mamaki ganin lokaci daya tayi wani rama kamar wacce tayi jinya fuskanta asake tace " ya yaseer ina wuni " amsawa yayi yana kare mata kallo dole akwai abinda yake faruwa , harzata juya cikin tsawa azaad yace " ke zonan " jikinta har bari yakeyi itaduk a tunaninta wani laifin takarayi nan da nan hawaye yafara zuba a idonta, kallonta yayi kafin yace " meye nafada miki dangane da falon nan ?" Tana share hawaye tace " kace karna kara shigowa " " okay yanzun renine yasa kika shigo " cewar Mr azaad ja da baya tayi tana" kayi hakuri Mr azaad bazan sake ba" Inbanda salati babu abinda yaseer yakeyi aranshi dama abinda azaad yake aikatawa yarinyar nan kenan tabbas yasan azaad ze aikata haka koma abinda yafi haka amma dayaji shuru yayi tunanin yarungumi matarshi ne suna zaman lafiya ashe bahaka bane, kallon fanan yaseer yayi yace " zeki abinki" dagudu tashige cikin bedroom dinta dan gani takeyi kamar zebiyota yadaketa. _____ Maida kallonsa kan Mr azaad yayi dake danna wayarsa ko ajikinshi gyara zama yayi yace " yanzu dude abinda kake aikatawa dedene? dan Allah wallahi baka rike amana ba wannan karamar yarinyar inka azabtar da ita meye ribarka " kallon yaseer yayi yace" dama aina nace nakarbi amanarta? Laifi tamin shisa nake hukuntata tana gama karban punishment dinta kuma zan saketa " girgiza kai yaseer yayi yace" karkayi haka azaad wallahi fanan ba kamar sauran mata bace ! Koma me take maka kamata yayi kayi hakuri ko kamanta lokaci kadan yarage mata dazatama barmana duniyarmu takoma inda ake bukatarta haba dude kaji tausayinta mana zata tafi tabar kowa nata amma dukda haka kana wulakanta ta wallahi insu ummi sukaji bazasuji dadi ba" daga kafada sama yayi alamar I don't care kafin yace" tafiyanta dakuma rashin tafiyanta nifa duk bedameni ba tatafi har yaumu takumu karta dawo dan nima ba kaunar ganinta nakeyi ba cos she's like a burden to me! Abinda nasani shine intamin laifi zan hukuntata " yaseer gani yayi inya biyewa azaad yanzu zasu iyayin fada yasa yatashi yatafi abinshi.

Yau Kwanan su Abba 5 da tafiya kullum insuka cewa Mr azaad yabawa fanan waya sugaisa ceyata basu uzuri, ummi de tanaji ajikinta kamar akwai abinda yake faruwa gashi wayarta yana hannunshi.

" Mr azaad dan Allah kabarni yau inje gidanmu ko kuma kayi hakuri kakiramin mama awaya " idonshi alumshe kamar bayajinta tunani tafarayi kode bacci yakeyi sake nanatawa tayi nanma yayi banza da ita haka taci gaba da mishi magana harta gaji be kulataba yasa takoma bedroom dinta takwanta tana kukan halin data shiga , daga hannunta sama tayi tana adduah " yah Allah ina rokonka kakawo karshen zamana da wannan bawan naka dayake kuntatawa rayuwata ! Allah kabashi ikon rubutamin takardar saki yau zuwa gobe " haka tadinga adduah tana kuka......

Tom se mun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏

Masu comment damin adduah nagode sosai Allah yasaka da alkhari, kukuma da sede ku karanta kuyi shuru ba sannu bare Allah ya isa🤔 kallonku kawai nakeyi kowa yayi dede yasani .

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & Written by MRS 🌹 ISHAM 🌹

Page 3️⃣9️⃣ & 4️⃣0️⃣

Haka sukaci gaba da rayuwa acikin gidan daga ita seshi se yan aiki wahala babu irin wanda baya bata haka kurum zesata wankin manya_manyan bedsheets da blanket ga fada da tsawa gakuma maruka.

Ana gobe su ummi zasu dawo taje tasameshi yagama shiryawa zefita office " Mr azaad inaso muyi magana " okay kawai yace , tadaura da " Mr azaad badanni ba kayiwa Allah daya halicceka kayi hakuri kasakeni bana kaunar zama dakai dede da dakika biyu banajin zanci gaba da zama dakai yanda ka tsaneni na tsaneka yanda baka sona haka nima bantaba sonka ba duk abubuwan dakamin na yafe maka ka sauwakemin intafi wajan iyayena sukadai ne nazama musu dole " ko kadan kalamanta basu bata mishi rai ba, hasalima tunda tafara magana yake kallonta babu ko kyaftawa yakafeta da wayan nan mayun idon nashi , gyara tsayuwarshi yayi ajikin kofa hannayenshi na harde akirjinshi yana kallonta murmushin gefen baki yayi yace " saurin mekikeyi haka base kinsake tunamin ba am aware kawai Jiran lokaci nakeyi " besake sauraranta ba yafice zama tayi akan kujera tana tunanin rayuwa anrabata da gidansu yan uwanta da kowa nata gashi farin ciki yakaurace mata, haka ta yini jiki asanyaye jitakeyi kamar bata da wani lafiya, sosai takejin sanyi nan take jikinta yabara barin sanyi bedroom tasamu tashiga takwanta taja bargo tarufe jikinta.

Zazzabi me zafin gaske ne yariketa ko kwakwaran motsi bata iyayi tana kwance tun safe daya fita yabarta be dawo ba balle yasan halin datake ciki ko aikin dayasata bata samu tayi ba.

Kwance take adaki se sakin murmushi kawai takeyi waya na manne akunnenta lumshe ido tayi giyar soyayya na dibanta murya anarke tace " hubby wallahi nayi missing dinka!katafi kabarni uhmm uhmm Allah inbaka dawo dawuri ba zanyita kuka kuma bazanci abinci ba haka zanbar kaina da yunwa" ajiyar zuciya fawwaz yasauke yana karajin tsananin kaunar suhaima nakara shiga ranshi besan wani irin so yake mata ba tariga da tazama wani bari na rayuwarshi yanzu sunriga dasun kamu da son juna, kara rungume pillow yayi yana fadin " am sorry baby nima nayi missing dinki fiyeda yanda bakya zato gobe zamu dawo" ihu tasa seda yacire wayar akunnenshi " hubby are you serious? " Dariya yayi dan suhaima itama ba laifi akwai dan sauran yarinta yace " in sha Allah baby gobe zamu dawo just pray for us kinji " nutsuwa tayi ta shagwabe fuska kamar yana gabanta tace " hubby kamin alkawarin kana dawuwa zakazo inganka " murmushi yayi yace " I promise Ina dawuwa ko gida bazan shigaba zanzo inga babynah " rufe fuska tayi tana kyalkyalewa da dariya " baby tsarabar me kikeso in kawo Miki?" Shuno baki tayi tace " hubby i want nothing than you kai kadai kawai nakeso " haka suka dinga zubawa junansu kalaman soyayya masu dadin gaske ( nida ba soyayya nakeyi ba gajiya nayi da hirar nayi gaba abuna karsusa in fusata)

Chapter notes and social links

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

Readers Also Read