Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 4
Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 4: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 4. Yana zaune a office dinshi yana duba wasu files dinda…
4,226 words
Yana zaune a office dinshi yana duba wasu files dinda sakatariya jamila takawo mai na sabobbin ma aikatan dazaa dauka ga faisal shima azaune yadukufa yana aiki a system, ringing wayarshi yayi yayi picking yasa akunne yana fadin " my sweet mom kuna lafiya ?" Abangaren ummi ta amsa mai " da lafiya Lau son yakuke ina fanan tunda mukazo kullum senace kahadamu amma abu yagagara! Kasiya mata waya kabata kasan badadi yan uwanta nason magana da ita sujita shuru" harga Allah seda ummi ta ambaci sunanta tukun yama tuna da ita dan kwata_kwata yamanta da lamarinta okay yacewa ummi sukaci gaba da hira kafin tayi hangup, system dinshi yakunna yashiga footage din gidan na CCTv camera, tun daga sa'ilin dayake gida be fitaba yashiga harzuwa lokacin datashiga daki takwanta around 10:00 besake ganin ta motsaba haryanzu duba time yayi yaga 4:00pm mamakine yakamashi ganin harzuwa time din tana kwance tunani yakeyi ko bacci takeyi sekuma yatuna duk baccin dazatayi seta tashi tayi sallah amma yau shuru ko breakfast batayi ba. Basarwa yayi yaci gaba da aikinshi can kuma yamike yayi switching din system din daukan jacket din suit dinshi yayi. faisal ganin oganshi yatashi yasa yamike yadau briefcase dinshi suka fice tada motar driver yayi dayaga sunfito shiga sukayi suka nufi gida , direct bedroom dinta yashiga yasameta kudundune acikin bargo numfashinta nafita sama_sama batama san yaye blanket din yayi yasa hannu taba jikinta dasauri yacire jin zafin daya dauka daukanta yayi yakaita bedroom dinshi , lalubo wayarsa yayi yakira doctor ammar, within 20mnt doctor ammar yashigo shikanshi yasha mamaki ganin fanan awannan yanayin ga ciwo datake fama dashi , kallon Mr azaad yayi yace " amma tadade tana ciwo ne Koh?" Amsa yabashi da " I don't know" jin haka yasa besake mishi magana ba yafara bata taimakon gaggawa yadaura mata drip yayi mata allurai " ga magungu nanta tana farkawa tasamu tasha abu me dumi like tea setaci abinci kafin tasha magani Allah yabata lafiya " yatabi yabarshi zama yayi agefenta yana kallon beauty face dinta dayayi fayau sa hannu yayi yana shafa gashin kanta daga bisani yakoma kan cusion yazauna. ______ karfe 8 ruwan yakare cire mata drip din yayi yana kokarin cire calular , ahankali tafara bude idonta dasuka mata nauyi dishi_dishi take kallon fuskanshi harta fara ganin komai clearly fisge hannunta tayi daga nashi takoma can kuryan gadon ta dukunkune awaje daya tana " Mr azaad kayi hakuri dan Allah karka dakeni kaina ne yakemin ciwo amma yanzu zanyi aikin kayi hakuri kamin rai bazan sakeba" haka tadinga sambatu tana bashi hakuri, jikinshi ne yadanyi sanyi hawa gadon yayi yanufeta ganin tunkarota yakeyi duk tunaninta dukanta zeyi ko yamata tsawa yasa ba shiri tasauka akan gadon zata gudu jirine yafara dibanta tayi tangal_tangal zata fadi yatarota tafado jikinshi muryanta dabaya fita tace " Mr azaad kabarni intafi dakina" tana magana manyan idonta na lumshewa dagata yayi yamaida ita kan bed din sannan yadanna line din gidan wanda in aka kira masu aiki zasu daga , dagawa abu me aiki tayi umarni yabata data shirya abinci da tea yanzu takawo part dinshi aikuwa haka akayi , bata jima ba tazo tayi sallama jin muryanta yasa yaje yakarbo tana zaune atsakiyar gado tana binshi da ido ita haryanzu gani take kamar ze mata wani abun dan batayi abinda yasata ba . Sa tea yayi acikin cup yamika mata karba tayi tafara sha kadan_kadan hartasha fiyeda rabi taji dadin shan tea din sosai ajiye cup din tayi akan bedside table , food flask yabude jallof din arish potato ne dayasha kifi banda da vegetables diba yayi yadawo gabanta , zefara bata kai mata spoon din yayi zebata abaki taki bude bakin se kawai kallon mamaki datake binshi dashi tafara tunani aranta anya Mr azaad ba poison yasa mata acikin abincin ba kuwa abinda betaba mataba yau shiyake mata. Ganin taki bude bakin yasashi kara tamke fuska yana watsa mata uwar harara bashiri tabude bakin haka yadinga feeding dinta hartace ta koshi maganinta yamiqa mata tasha nan take tabara bata fuska zatayi kuka , lura yayi da kwata_kwata bata kaunar magani hakan yasa yajika maganin a cup yamatseta kamar wata yar jaririya yamata dúre dakyar tasha kokarin amayar da maganin take fuska ahade yace kina amar dashi adaren nan zanbaki hakkinki , aikuwa ba shiri tamaidashi. Kara daukanta yayi yashiga toilet da ita yadireta akasa yafice ,cire rigar jikinta tayi tana kokarin hanging dinshi yafada acikin jacuzzi cireshi tayi ta ajiyeshi a gefe wanka tayi tare da alwala rasa yazatayi tafito tayi iya towel ne a toilet din gashi kayanta din ruwa yajiqashi tafi mint goma tana tunanin mafita daura towel din tayi tafito, godewa Allah tayi dataga baya dakin hanyar fita tanema, harta kusa bakin kofa yafito daga dressing room hannunshi narike da jallabiya. Idonshi ne yasauka akan kyakyawar surar da Allah yamata , kasa motsawa yayi sebin shape dinta da kallo yake musamman hips dinta dasuke acike masha Allah mamaki yafarayi dama wannan yarinyar haka ainihinta surarta yake ga brest dinta da rabinsu suka fito waje aranshi yace" how could that be possible yarinya da jikin manya?" Ganin irin mayen kallon dayakebin jikinta dashine yasa tayi saurin murda handle din dakin tafice tafada bedroom dinta tasamu tasa doguwar riga da hijab ta tada sallah , duk sallolin da akebinta seda tayisu kafin tasa kayan bacci jikinta bawani karfi sosai ta kwanta.
Shikuwa gogan naku gaba daya kasala ce tarufeshi lokaci daya barinma inya rufe idonshi yahasko mishi hoton surarta ,haushin kanshi yafaraji taya zetsaya yana tunanin wannan karamar yarinyar da ko cikekken hankali bata gamayi ba.
Karfe 1:00 na rana jirgin su abba yayi landing,Mr azaad damasu tsaransu ne sukazo tarbansu fawwaz de car key kawai yakarba dan beda burin daya wuce yaje yacika alkawarin daya daukawa babynshi .
Duka suna zaune afalo ummi tace " son ina feena ?" Yana danna waya yace " tana bedroom " "okay jeka kirata " tashi yayi tahaura upstairs din afalo yasameta tana yar goge_goge, kallonta yayi up and down kafin yace " ummi nakiranki afalo " cike da Al ajabi take bin bayanshi da kallo wato su ummin sundawo shine baze fada mata ba lallai Mr azaad. Dama doguwar rigar abayace goldin color ajikinta komawa bedroom tayi tasa gyale me girma tasauko. Tun kafin ta iso gaba ki daya mutanen falon hankalinsu yakoma kanta ganin yanda lokaci daya tayi uwar rama sosai suke kallonta, tashi zeenat tayi suka rungume juna cike da murna tukun suka karasa falon duqawa tayi tagaishesu amsawa sukayi suna kallonta, zama tayi abinta akan lallausan carpet din falon , Abba ne yakalli Mr azaad yace " meyake damun fatima? datayi wannan ramar haka azaad?" Kallonta shima yayi yana neman ramar da akace tayi bayan ko ina najikinta acike bulbul. Shuru yamusu dan besan amsan daze bayarba tunda shide bega wata rama ajikinta ba, girgiza Kai abba yayi yakalli fanan " Fatima meyake damunki kika rame haka kode azaad yana miki wani abune bayan tafiyarmu?" Satan kallonshi tayi taga ko ajikinshi wayarsa ma yake latsawa abunshi , murmushin yaqe tayi tace " Abba babu abinda yakemin kawai de kwana biyu ne nayi rashin lafiya " ran ummi yabaci dajin haka domin kullum sesunyi waya da Mr azaad kuma seta tambayeshi ya fanan take yace mata" lafiyanta Klau" ashe baiwar Allah tana nan tana fama da ciwo amma dan bakin hali irin nashi yaki sanar da kowa. Dago kai yayi suka hada ido da ummi dake doka mishi harara sunkuyar dakai yayi dan yasan dalili. ______ Rai abaci abba yafara magana " yanzu kai azaad ka kyauta kenan matarka bata da lafiya kusan kwana biyu amma baka taba fadawa kowa ba! Sannan kabata wayarta ko kasiya mata wani abu yagagara kullum semun ce kahadamu da ita amma ka kasa to ka kiyayeni kaduba yarinya duk tabi ta lalace kamar ba itaba " shide ko uffan bece musu ba saboda shibega abinda suke magana akai ba daga karshema tashi yayi yabar musu gidan , aranar kam fanan tahuta se lallabata sukeyi kamar kwai da dadin baki ummi take samu tama fanan wayo tasha magani har goma suna hira , jitayi kamar ta cewa ummi zata kwana apart dinta amma inta fadi haka zasuyi zargin wani abu tanaji tana gani sukayi sallama tawuce nasu part din.
Bari muleka Romeo and Juliet
Girki suhaima tayi mishi me ji da lafiya taci ado suna zaune suna sunashan hiran love Yanacin abinci se shagwaba takeyi mishi , bakaramin gigitashi takeyiba intana wannan shagwabar haka sukasha love dinsu ya ajiye mata tsarabanta tarakashi har bakin motar shi yatafi. Komawa gida tayi tadauki fashion bag din daya ajiye mata tashiga dakin mama tanuna mata budewa tayi dogayen ruguna ne masu shegen kyau yan dubai da sarka da dankunne na gold se zobe, murmushi mama tayi tace " ohhh su suhaima anyi saurayi " kunya taji yarufeta tarufe ido suna dariya , " tun jiya babanku yace inbada miki ki mishi magana inde da gaske yake auren zeyi yafito" cike da kunya tace " to mama zan fada mishi".
Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau yakama 1 month dayin auren fanan da Mr azaad, yana nan yana mata abinda yagadama wata rana yasata aiki wata rana kuma kota kanta bayabi, tun su ummi basu farga ba har suka fara fahimtan wani abu wani lokacin fanan setafi kwana biyu bata sauko downstairs ba kuma baya taba yarda wani yaje ciki ,sanda ze barta kuma se inzaayi dinner gaba daya tacanza, kuma komin tambayar dazasu mata amsa daya take basu shine " bakomai bayamin komai" ummi ce ta siya waya iphone 14 pro max tabawa fanan da sim taloda mata kati da data aciki,tacewa Mr azaad saura kuma kar inganshi ahannunta, tanan ne fanan tafara samun saukin wasu kayan bakin cikin kullum setayi waya da yan gidansu, suhaima da amira,auta sunzo wajanta harso biyu suma sunyi mamakin yanda takoma wata shuru_shuru da ita .
Alhamdulillah su Abba da yan uwansu sunje sun tambayawa fawwaz auren suhaima kuma anbasu ansa date nan da wata hudu zaayi ( tom Romeo and Juliet ankusa angoncewa kenan Allah yakaimu musha biki)
Ayau ne ranar asabar akatashi da wani irin gagarumin tashin hankali agarin gombe sakamakon ganin gawawwakin yara da manya , maza da mata ancire wasu sassa najikinsu anyi ritual dashi( tsafi) ansamu gawawwaki kusan 30 lamarin yadagawa mutane hankali kowa yanutsu da iyalanshi agida , jami'an tsaro se bincike sukeyi akan case din daga zaran yaro yafita haka zaa daukeshi baze dawoba sede aji labarin antsinci gawanshi.
Wannan aikin bana kowa bane face kungiyar SATANIC and BAPHOMET dasuke ritual domin yakar junansu domin duk wanda yayi nasara akan daya shize kwaci jaaazana haka suka dinga tsafi da mutane da basuji ba basu gani ba ,babu ruwansu dakoma waye yafita kana yin waje zaa daukeka cakk shikenan kuma katafi, wannan dalilin yasa akasa lockdown agombe.
Duk suna gida suna jin abinda yake faruwa Abba yace karwanda yafita, dukkansu suna zaune afalo sunata kallon labaran da akeyi .
Bangaren mommy kuwa tun ana kwana biyu zaa fara ritual din abin duniya yadámeta gashi bahalin zuwa ayi da ita dan haryanzu bata warke ba tanata kan jinya dan tasan dataje anyi da ita tasan dole tanzarzar yakara mata matsayi.
Jikin fanan ne yafara wani irin kadawa kamar wacce akasawa shocking , nufanta sukayi cikin tashin hankali ,riqeta gam azaad yayi duk jijigan datakeyi tana jikinshi yaki saketa can kuma seta dawo normal, kallonsu tayi gabaki dayansu tana zubda kwalla tace " shin akwai abinda ake boyemin ne daban sani ba? Kufadamin jinake kamar zanmutu yanzu inbanji ba wayyo Allah na" takarashe maganar da karfi tana rike kanta da yasara mata tabbas abu takeso ta tuno amma takasa sede yadinga mata flash, duk shuru sukayi sun rasa abin fada shin yau ne fanan zatasan ko ita wacece? Kokuma yau ne zatabar duniyarsu? gaba daya tambayar dasukewa kansu kenan.
Areef ne sukaga yaje gabanta yazube akan guiwowinshi kanshi akasa , nan ne jikinsu yasakeyin sanyi domin sunsan tabbas wannan ba areef bane. Cike da mamaki takalleshi ganin yadúrkusa agabanta goge hawayen fuskanta tayi tace" ya areef Meye haka ?" Girgiza kai yayi cikin muryan daya manyanta " yace sarauniya ba areef bane! Sunana abdud Shakur nine galadiman masarautar nasminaya! Nazo ne domin in amsa miki tambayoyinki sannan insanar dake ko kedin wacece.......
Hakikanin gaskiya inajin dadin adduah dakukemin dakuma comments dinku it means alot to me, wallahi ina matukar kaunar ku sosai Allah yabarmu tare daga nan har gidan aljanna 🙏😘😍, ku Kuma masu karantawa kuyi shuru ba sannu balle Allah ya isa kallonku nakeyi kawai kowa yayi dede yasani amma zaazo time dinda mutum in yaganshi awaje karyaga laifina domin nima mutum ce ba engine ba.
Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏.
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
🧑⚕️🧑⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺
Story & Written by MRS 🌹 ISHAM 🌹 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION ✍️✍️
Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum iname mika sakon taaziyata ga alhalin anty hadiza salisu sharif dakuma marubuta da kowa gabaki daya, Allah Ubangiji yajikanta da rahama, Allah yasa tahuta , Allah yakai haske kabarinta ya yafe mata 🙏🥺 Allah yasa innamu yazo mucika da imani da kalman shahada , Allah yagafarta mata 🙏🙏 Ameen ya hayyu ya qayyum.
꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁
Page 4️⃣1️⃣ & 4️⃣2️⃣
Fa ra bata labarin tun daga lokacin da take ciki har zuwa haihuwarta da kuma abinda take dauke dashi a jikinta da yakar kungiyoyin kaff seda ya fada mata sannan yakara da " labari mara dadinji shine! gaskiya sarauniya a ko wani irin lokaci za ki iya tafiya domin yawan rashin adalcin da akeyi yana kusantoki! Jaaazana nakara bayyana a jikinki , duk inda aka samu irin wannan bar nan ya afku sau uku nan take zaki koma masarautar ki , ko da kuwa kin shirya ko baki shirya ba yanzu de anyi biyu ina tunanin saura daya". Takasa cewa komai se hawaye da kuma murmushin datakeyi atare lokaci daya , Tabbas masarautar take gani yana mata flash dakuma sarki abdud daar ashe itadin shugaba ce dazata kawo gyara .
Se yanzu take jinta cikakkiya amma dà se ta dinga jinta kamar akwai abinda ta rasa ,kamar ta rasa wani bàri a tare da ita amma yanzu da tasan ita wacece se taji duk wani gurbi yacike,
Duk suna jira suka reaction dinta ya zataji intaji wannan labarin, abinda basu taba zata ba tayi sujjada tayi ta daga hannunta sama tana yiwa Allah godiya " Allah nagode maka dakasa nazama zabàbbiya ! tabbas zanyi aiki da duk wani wani karfi danake dauke dashi domin kare rayukan al'umma daga jinsin bil adama harzuwa jinni koda kuwa zezama sanadiyar rai ne , Allah kasa ta dalilin haka in zama me rabo a aljanna " amma data tuna za tabar iyayenta da duk wayanda ta sani se taji gaba daya duniya bata mata dadi. Kallon Abdud Shakur tayi dake jikin areef tace " inson magana da kai sirri" dago kai kawai yayi ya wuro iska a bakinshi yace " sarauniya za ki iya maganarki ayanzu babu wanda zeji me muka tattauna " kallon yan falon takeyi dan ta tabbatar yasa tace " zeenat kinaji ?" Shuru zeenat bata mata reply ba sede ta bita da ido . Su kuwa su abba kallonsu kawai suke suna magana amma basajin abinda suke fada azaad de ya kafe bakinta da ido dansan gane abinda zata fada, gam yarike yanda bakinta yake motsi amma yagagara seta kalmomin. Suna gama maganar abdud Shakur ya fita daga jikin areef, tashi areef yayi dan besan meyafaru yace " antynmu yanaga kamar hawaye kikeyi wani abu yafaru ne?" Girgiza mishi kai tayi tace " babu abinda yafaru ya areef" "okay" yace tare da wucewa part dinsu . murmushi kawai takeyi da gaba dayansu sun rasa gane na miye , tabbas samun irinsu fanan acikin al'umma abune dazeyi matukar wahala awannan duniyar koda kuwa akwaisu zasuyi wahalan samu sannan basuda yawa , ta yarda zata sadaukar da rayuwarta akan yakar azzalumai bata damu ta mutu ko ta rayu ba farin ciki ma takeyi da hakan akan shahadar da zatayi . Jikinsu ya mutu sosai nan take tun kafin lokacin tafiyar ta yayi harsun fara kewarta , shikanshi Mr azaad seda yaji ba dadi part dinshi yatafi yabarsu afalon, lura fanan tayi baya falon yasa itama tabi bayanshi, zama sukayi duk basa cikin dadin yanayi kiran baba abba yayi ya sanar mai da fatima tariga da tasan ita wacece , murmushin takaici kawai baba yayi ranshi na kuna yace " alh nariga da nasan wannar ranar na nan zuwa na sawa zuciyata dangana kullum kokarina in kwantar wa mahaifiyarta hankali ! Nasan yau inde taji labarin abinda yafaru hana kanta sukuni zatayi" haka sukata jinjina lamarin cikin rashin jin dadi amma babu yanda zasuyi sede sumata adduah Allah yabata saa a abinda zatayi yakareta daga sharrin wayan nan mugayen azzaluman. bedroom dinta tashiga takwanta tana tunanin tafiyarta nan take ta tuna wani abu tasa zuruf ta mike. Toilet tashiga tayi wanka ta wanke gashinta da shampoo's masu dadin kamshi, koda tafito she didn't bother to dry it gogeshi kawai da towel tayi , tunawa da shawarwarin da anty amina tabata tayi , killer smile ta sake daya fito mata da kyaunta ta bude tankamemen wardrobe dinta , one by one take bin kayan dake lode aciki da kallo ,sauka idonta yayi akan bangaren wasu tsinannun kana nan kaya, tun kafin ta dagosu kunya yakamata taya zatasa wayan nan kayan taje gabanshi , dubawa takeyi hartazo kan wani yar iskar riga da ita da babu duk daya daukoshi tayi ta dagashi sama tana kare mai kallo daga sama har kasa , gallawa kayan harara tayi sekace shi yace ta dauko shi . tafi minti 5 tana tsaye tana juyashi rigar kalanshi sak da wayanda karuwai suke sawa, wurgashi kan bed tayi tadau wayarta tayi dialing number anty amina dagawa tayi tana " assalamualaikum my feena kina lafiya?" Zama tayi a gefen mirror ta amsa sallaman tana tambayarta yasuke da junior kafin tadaura da " am! am anty amina dama maganar da mukayi kwanaki ne to yanzu kuma.....uhmmm " kasa karasawa tayi jin kunya yakamata, anty amina ta rigada tasan inda maganar ta dosa ,kunya ya hanata fada , yar dariya tayi jin yanda fanan take in da in da takasa fadar taka memen abinda yasa takirata " calm down my feena kidena jin kunyata kifadamin duk abinda kikeson fada se munsan yazaayi ko?" Sosa wuyanta tayi tarufe idonta kamar anty aminar na gabanta tace " dama zanje wajan Mr azaad ne tom kamar yanda kikace inde inaso muja hankalinshi da wuri dole se inasa kana nan kaya dakuma sauran abinda kikace" sosai anty amina taka sa kunne tana sauraranta cike da jindadin yanda fanan ta shirya karban shawaranta sannan tace " ci gaba ina jin ki " sake runtse ido tayi ta daura da " tom nayi wanka na dauko wata riga wallahi anty amina baki gantaba kamar irin wayanda karuwai sukewa rigar fah yar iska ce sosai" ta karishe maganar tana dan fito da dara_daran idonta . Dariya anty amina ta keyi sosai jin abinda fanan ta fada wai rigar fa yar iska ce sosai hhhhhh, tsaqaitawa tayi da dariyar tukun tace " wallahi my feena za ki kashe mutum da dariya ! duk yanda rigar take karki damu kisata ahaka sannan kuma................." tasake fada mata wasu abubuwan da nikaina banji ba . bayan sungama wayan ne taje gaban mirror tazauna ta shafa lotion masu tsada da dadi , tayi usual make up dinta, daukar rigar tayi tsaban yanda yake da yanka_yankan tsagu ajikinshi ta rasa ma ta ina zata sashi haka tafara gwadawa dakyar tasamo kan rigar . Kallon kanta tayi a mirror zaro ido waje tayi ganin yanda rigar tamata , guntuwar rigace roba yana yalki red color du ka tsayin rigar da kadan yawuce Santala_santalan cinyoyinta da suke glowing gefen hagu na rigar tundaga hannu har inda rigar ta tsaya tsagu_tsagu ne manya ana kallon fatarta awaje yana da dogon hannu se wuyan rigar daya kasance me fadi sosai open shoulder kenan dukiyar fulaninta duk suna waje rabi ne aciki ya matseta sosai duk wani structure dinta seda yafito fili , ga lallausan chocolate fatarta awaje , inde tayi kwakwaran motsi jikinta seya motsa , seyanzu nikaina na sake mata kallo sune ainihin matan da ake kira masu shape din coca-cola, juyawa tayi tasake kallon kanta a mirror slice smile tayi tace " Allah yashiryeni" hills black color tasa tafeshe jikinta da wasu irin daddadar tururuka masu sanyin kamshi , gashin kanta be gama bushewa ba sunyi wara_wara nan ne takara fitowa very sexy, tsayawa fadar kyaun datayi bata bakine , wani taku takeyi step by step cike da nutsuwa take tafiyarta , yanda body ta ke juyawa dakanshi wani zeyi tunanin da gangan ne amma ita kanta batasan sunayi ba . ___ kitchen ta nufa ta hada mishi coffee ta daura cup din akan plate dinshi. Tsayawa tayi abakin bedroom dinshi tare dayin knocking "come in " kawai yace shigowa tayi hannunta na rike da plate din coffee din , tun bayan shigowarshi part din yazauna kenan faisal yakirashi bayan sungama wayar ne yashiga toilet yayi wanka yafito daure da towel akugunshi yana digar ruwa yasamu waje yazauna zeduba sakon da faisal yace yatura mishi a email kenan tashigo , batare da ya dago ya kalleta ba yace " how can I help you?" Shuru tayi bata bashi amsa ba tana bin surar jikinshi da kallo babban abinda yake daukan hankalinta kenan atattare dashi murdadden jikinshi da kuma faffadar kirjinshi dake dauke da kwantaccen suma. Jin shuru ba amsa ne yasa yadago yakalleta lokaci daya yayi suman zaune sanadiyar cin karo dayayi da yarinya me jikin manya lolx, tun daga yatsun kafarta yake binta da wani slow motion look har zuwa fuskar ta , koda kwakwaran motsi yakasayi inbanda kafeta da sexy eyes dinshi dayayi nan take idanuwanshi suka canza kala har lumshewa sukeyi , murmushin cin nasara takeyi domin babban burinta shine tayi galaba akanshi dan tacinma burinta da takeson cimma in harde Mr azaad yafada wannan tarkon komai zezo da sauki, karasawa tayi gabanshi ta duqa ta ajiye mishi coffee din ,hango dukiyar fulaninta yayi suna mishi kwalele dake batasa bra ba , sosai ya rude yana binta da mayen kallo juyawa tayi zata tafi yasa hannu yafisgota tafado jikinshi, bin cute face dinta yakeyi da kallo babu ko kyaftawa . Shafa fuskanta yayi kafin yace " so bakiji warning din da na miki bako ? Shine kika dawo da wannan salon right? tunda naga abinda kikeso kenan yasa kika kawo kanki well bari in taimakeki " cike da kissa tayi farí da ido tace " to ai abinda nakeso din kenan shisa nakawo kaina " yanayin yanda ta kashe murya take magana bakaramin tafiya tayi da imanin shi ba, maida gashinta yayi gefe daya yasa kanshi a wuyanta yana shakar kamshin dake tashi a jikinta , se shinshinta yakeyi turaren da tasa yadada tada mishi da hankali tallafo habarta yayi ya hade bakinsu waje daya yafara bata hot kiss, kashe wutar dakin yayi yabar iya bedside lamp shima me multi color dakin yagaurayi da different colors of light se yakara kayatarwa , mayar mishi da martani takeyi sosai hakan yakara susu tashi ,zame rigar jikintan yayi yafara shafa dukiyar fulaninta dasuke birkita mishi lissafi ita kuma ta cusa hannunta atsakiyar gashin kanshi tana shafawa hade da mishi tafiyar tsutsa so take kawai yaje inda take jira dukda tana dar_dar amma she has no choice dolene hakan yafaru. Sosai Mr azaad yayi wasa da ita seda yaji hankalinshi yadawo jikinshi sannan ya kyaleta koda wasa beyi gigin yin sex da itaba saboda yasan abune mawuyaci ta daukeshi, tana kwance ajikinshi suna cikin bargo tana baccin wahala jikinta gaba daya ciwo yake mata dan ya jagulata ne son ranshi musamman ma dukiyar fulaninta yafi ko ina shan wahala , amma hakan be dameta ba saboda kudirinta aranta yanzu shine tasamu ta cimma abinda tasa agaba burinta seya kawar daduk wani tsoro atare da ita.
Mannata yayi ajikinshi yana kallon sleeping beauty face dinta intana bacci kara kyau takeyi ganin ta turo bakine yasa yayi murmushi ahankali yafurta " stubborn girl" tunani yafara yanda fanan take tsoronshi yau shine takawo kanta batare data nuna wani fargaba ko tsoro ba tabarshi yayi yanda yaso da ita tabbas akwai abinda take shiryawa amma koma menene seya gano , tashi yayi yashiga toilet yayi wanka yafito yasa kayan baccinshi daukanta yayi yadireta acikin jacuzzi ware idonta tayi da bacci ke cike aciki ganin sa tsaye akantane yana kare mata kallo yasa tayi saurin kallon jikinta ganin bakomai ajikinta ne yasa takare kirjinta da du ka hannunta murya a shagwabe tace" wayyo nikam kafita inyi wanka " fita yayi yabarta tayi wanka tafito daure da towel, yana tsaye yaga fitowar ta duk tunaninshi bedroom dinta zata tafi with his surprise yaga ta dàle gado ta kwanta ko kaya batabi takanshi ba taci gaba da baccinta girgiza kai yayi shima yahau gadon ya kashe light din dakin yabar bedside lamp jan bargo yayi yarufesu.........
Semun hadu ran Monday inme duka yakaimu da Rai da lfy masuyin comment Allah ya suburbuda muku albarka🙏🙏🌹 I love you so much.
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
🧑⚕️🧑⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺
Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹
🔔 📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚
Page 4️⃣3️⃣ & 4️⃣4️⃣