Kenza eBookz

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 5

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 5

Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 5: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 5. Tunda sukayi sallar asuba suka koma bacci karfe 10…

4,262 words

Tunda sukayi sallar asuba suka koma bacci karfe 10 fanan ta tashi daga bacci tsareshi da ido tayi tana kallon yanda yake bacci he looks innocent kamar ba ruwanshi sosai ta shagala da kallonshi murmushi ne ya subuce daga fuskanta hannu takai zata shafa fuskanshi ya dan motsa da sauri ta janye hannun baya ahankali ta furta " Mr azaad zanso ka cikamin burina a yan kwanakin nan amma naga you're very arrogant dole senayi sena cusa maka hakan a ranka " ta karishe magana tana kallon body packs dinshi bargon da yake rufe dashi ya yaye time din data tashi sexy body dinshi awaje ,sauka idonta ya yi akan nipples dinshi dasuke ja sosai ga wasu kana_kanan gashi sun zaga nipples din murmushi tayi tace" kana da kyaun fuska kyaun jiki da sura tako ina ka hadu amma de kyaun hali ya maka wuya " sulalewa tayi ahankali daga dakin dan karta tasheshi daga bacci tashiga nata bedroom din wanka tayi hade da kwalliya tasaka wando pencil crazy blue color tasa riga fara da kadan yarufe mata cibiya me guntun hannu gaban rigan akwai hoton teddy , lallausan gashinta kuma ta rabasu gida biyu ko wanne tasa mishi ribbon ta tubke , seta fito kamar slay queen , takalmi me yar tudu tasaka kallon kanta a mirror tayi taga tayi kyau sosai wayarta dake bedside drower tadauka tafara selfie , tayi sunfi kala goma kafin tabari zama tayi tana kallon hotunan, murmushin dake kara mata kyau tayi dan duk hotunan sun mata kyau , tunawa tayi da Mr azaad a ko wani lokaci ze iya tashi daga bacci yasa tayi saurin ajiye wayar tanufi kitchen. Simple breakfast ta hada musu ta jera a dinning table, aranta tace " anya wannan Mr arrogant din ze yarda yaci ma kuwa?" da wannan tunanin tashiga bedroom dinshi har time din yana bacci be farka ba , zama tayi a bed din ta sunkuyar da kanta har kumatun shi ta sake mishi fresh kiss a kumatu , ahankali ya fara bude wayan nan rikitattun idanunshi dake rikita mata da kuma razana abokan gaba, kallonta yayi yana mamakin sudden change din datayi jin kiss din data mishi wanda yaji tundaga tafin kafarshi har tsakiyar kanshi. _____ sunkuyar dakai kasa tayi dan bazata iya kallon cikin idonshi ba dan yanzu zasu rikitata , yasa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Se yanzu ya kalli dressing din jikinta, kyau tayi mishi aranshi yana fadin " yarinya me jikin manya komai tasa yana fitting dinta" kafin afili yace " me yakawo ki bedroom dina?" langwabe kai tayi tana yatsina fuska tace " Mr azaad I made some breakfast shine nazo tashinka muje muyi" tana magana tana jujjuya kai gefe da gefe kamar wata karamar yarinya, yanayin yanda tayi yaso bashi dariya se yabasar, tsareta da mayun idonshi sannan yace " dama tare mukeyi ne! Ko duk cikin shirin kine?" Satan kallonshi tayi jin abinda yafada tunani tafara anya wannan ba aljani bane kuwa daburcewa tayi ta rasa amsar da zata bashi , hakan datayi ne yasake tabbatar mishi da zarginshi ya tabbata, tabbas akwai abinda take shiryawa wanda ita kadai tabarwa kanta sani se Allah. tashi yayi ya zauna riko hannunta duka biyu yayi yana matsawa kadan kadan " ki kalli cikin idona fanannnn " cike da al ajabi da mamaki take kallon nashi jin yafadi sunanta , bata taba jiba ko da yaushe sede yace mata kee amma baya kiran sunanta duk tunaninta besan sunan bane, se taji yanda yafadi sunan da wani irin style ya burgeta jitayi shikadai ne ya iya fadan sunan , kyasta mata yatsunshi yayi afuska ganin ta tafi duniyar tunani, kallonshi tayi hade da sakin murmushi me tafiya da zuciya , "ya salam" yafurta aranshi yarasa meyake damunshi da yarinyar nan kwanan nan ya lura inbeyi a hankali tabbas zata iya galaba akanshi dukda yanada yakini abinda take shiryawa bawai mugun abu bane . Matsa hannunta yayi kadan yar kara tayi hade da turo dan bakinta gaba tana kunkuni , zaro ido yayi yace " ni kike zagi ?" Tashi tayi zata gudu dan taga sharri yakeson mata wai ta zageshi , maida ita yayi tazauna hade fuska yayi yace " ina zakije kuma?" ganin fuskanshi yakoma na ainihin Mr azaad ne yasa murya asanyaye tace " babu " " fanannnn ! meyasa kikeson sa rayuwata a cikin hadari? ko dan saboda abinda na mikine yasa kikeson ramawa ta wannan hanyar ? shin kina ganin hakan zesa ki huce ne? Kinsan tafiya zakiyi shine kikeson azabtar da rayuwata? kinason nasha wahalar inkin tuna kinsani awannan halin zakiji dadi ko? " Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara zubowa daga idonta dama tasan dole se yayi tunanin hakan kancewa ramuwa takeyi bayan babu hakan aranta , tashi tayi da gudu tafita a dakin tana kuka , ajiyar zuciya ya sauke shi kadai yasan yanda yakeji toilet yashiga yayi wanka. fadawa kan gado tayi tana kuka me ratsa zuciya afili take fadin " Mr azaad wallahi bantaba rikeka azuciyata ba balle inyi tunanin rama abinda kamin taya mutum ze cutar da abinda yakeso Mr azaad ina sanka bazan taba barin wani ya cutar dakai ba balle ni dakaina ya Allah ka kawomin sauki cikin raina " . Yana tsaye abakin kofan bedroom dinta duk wani abinda tafada akan kunnen shi idonshi sun rine sosai yayi ja da karfi zuciyarshi yake bugawa be bari tasan da yana wajen ba yakoma bedroom dinshi zama yayi akan kujera jikinshi duk ya mutu dafa kanshi yayi da ke sarawa kamar ze fita babu abinda yake furtawa aranshi in banda " innalillahi wainna ilaijiraji unnn na cutar da baiwar Allah da take sona! bansan menene so ba amma zanyi iya kokarina in kyautata mata kafin tabar duniyarmu " haka yata saqe_saqe aranshi cikin kankanin lokaci ciwon kai yasauka mishi . Haka suka kai har azhar batare da sunci komai ba ita tayi zatan baya nan yafita ne tayi sallah ,ta canza kaya izuwa riga wanda tsayinshi ya wuce guiwanta yanada fa di light green, falo tafito ta gyara ko ina tasa burner yana fitar da kamshi me dadi bedroom dinshi tashiga saboda tagama gyara ko ina saura nashi , akan kujeran tasa meshi yana zaune idonshi alumshe kauda kallonta tayi daga kallonshi tafara gyara bedroom din ya saura kan kujeran tsayawa tayi nesa dashi tace " Mr azaad zangyara kujeran" shuru yamata bece mata ka la ba tayi magana yafi baki biyar amma shuru tunani tafara kode bacci yakeyi , har zata juya tafita saboda karta tasheshi daga bacci taga ya miko mata hannu alamun takama, batare da tayi tunanin wani abu ba tarike hannun tana kokarin janshi yatashi, tadage se janshi takeyi ko motsawa beyiba bare yatashi haki takeyi kamar wacce tayi gudun tsere harda hada zufa. Jawota yayi tafado jikinshi ya rungumeta muryanshi baya fita yace " patient dinki yana bukatar special care bayida lafiya" sa hannu tayi ta taba jikinshi tabbas bayajin dadi kamar zazzabi ne yakeson rufeshi jikinshi yayi zafi, amma dazun kuma lafiyarshi kalau , kokarin tashi takeyi dan ta dubashi yasake rungumeta sosai kamar wani zekwaceta murya anarke yace " karki tashi ina bukatar dumin jikinki atare dani" yanda yake maganar kamar yana mata rada. Tausayi yabata kamar ba Mr azaad ba hakan yasa tasake jikinta dashi shishigewa jikinta yakeyi sanadiyar warm temperature nata se yaji yana jindadin kasantuwar su a haka , ta takura sosai ayanda suke kujeran ya musu kadan gashi runguman daya mata ba karamin runguma bane , dede kunnan shi tace " Mr azaad kirjina ze balle " saketa yayi yana kallonta da sexy eyes dinshi yace " yunwa nakeji " kyaf_kyafta ido takeyi tana kallonshi dan yamata bazata batayi tunanin haka awajanshi dan so take ta tabbatar ko mafarki takeyi ko kuma da gaske ne, yasan mamakine yahanata magana yasa yasake maimaita " yunwa nakeji" tashi tayi da hanzari tashiga kitchen tayi fast food noddles ta dafa ta soya kwai tajuye a plate kaiwa bedroom din tayi ta ajiye saman center table ta koma kitchen tadauko drinks da ruwa , yanda ta tafi ta barshi haka tasameshi bata zauna ba se tadauko mishi magani ta ajiye komai akan table kafin tace " Mr azaad katashi nadafa maka noddles saboda yafi wuri" " okay" yace tare da mikewa ya zauna nuna mata kusa dashi tazo ta zauna, faracin abincin yayi seda yaci kusan rabi kafin yakai bakinta ze bata dan yasan itama bataci abincin ba make kafada tayi tana " uhmm uhmm " tamke fuska yayi yace " Ina wasa dake ne ?" ba shiri ta bude bakinta yafara feeding dinta har yakare yabata ruwa , fanan de yau gaba daya Mr azaad gani takeyi kamar ancanza shi sewani lallabata yakeyi sau daya kawai ya kalleta yadau magani yasha dan yasan abinda ke ranta. Toilet yashiga yadauro alwala ya shinfida sallaya adaki yayi sallah azhar yau kam yayi missing jam'i . tana zaune akan kujeran babu abinda takeyi banda binshi da kallo duk abinda yayi kyau yake masa takasa janye idonta akanshi dago kai yayi suka hada ido yar harara yawurga mata yace " banason yawan kallo gudun kar acinyeni " dariya tayi jin wai gudun kar acinyeshi , shagala yayi yana kallon yanda dariyan yakara mata kyau , ganin irin kallon dayake mata ne yasa ta tsagaita da dariyan " Mr azaad dan Allah in nemi wata alfarma awajanka ?" ta karishe maganar tana komawa kalar abin tausayi, murmushi kawai yayi yace " kishirya yau zamuje gida karfe 7 karki batamin lokaci " da gudu ta tashi tafada jikinshi cike da murna se dariya takeyi yau zataje gida ,rabonta da gida tunda tayi aure rungumeshi tayi gam tace " nagode sosai Mr azaad" yayi farin ciki da ganin irin murnan data shiga yau de yayi sanadiyar farin cikinta "asshhh" yafurta da dan karfi dagashi tayi tana tambayarshi meyafaru amsa yabata da " kinmanta bana jin dadi kinwani zo kin daddan ne ni" tunawa tayi da hakan dan tsaban murna ne yasa ta shaafa kunya ne yarufeta yasa tafara sosa kai tana turo baki . Hannu yasa yarike laben kasan yace " zaki fara rashin kunyar takine" girgiza kai tayi gudun karta ja yace yafasa " am sorry bari inje gun ummina ka kwanta kasamu kayi bacci kafin la'asar" ko jiran amsarshi batayi ba tafice yau de yasata murna se murmushi takeyi ita kadai, sake nanata abinda tafada yayi " ummina" hakan yamishi dadi saboda yana matukar son dakuma daraja meson umminshi.

" My feena nikam yau naga se farin ciki kikeyi meye sirrin ?" rufe fuska tayi tana dariya sannan tace " ummi Mr azaad ne yace yau zamuje gida " ummi kanta taji dadin labarin dama tanada niyar mishi magana saboda yakamata ace taje taga gida murmushi ummi tayi tace " ahhh to lallai wannan Mr azaad din yakyauta! Feena fatan de babu wani abinda yake miki na rashin jin dadi? " Kwantar da kanta tayi akan kafadar ummi tace " ummi babu abinda yake mini" ko kadan ummi bata yarda da abinda fanan tafada mata ba , domin kuwa yanayin yanda suke ganinta a yan sattitikan sunsan dole akwai abinda ke faruwa kuma ko sun tambayeta sede tace musu bakomai saboda fanan yarinya ce me hankali taki fa dane gudun fadan dazaa mishi bayan haka kuma bazata iya kai karanshi ba, amma yau ganin yanda take murna yasa ummi tafara tunanin Allah yafara hada kansu, hakan yayima ummi dadi sosai takara jin fanan aranta tare da alfahari da ita. " Nikam ummi wai ina zeenat da su ya fawwaz ne gidan shuru sun tafi sun barki ke kadai" shafa kanta ummi tayi tace " ai tun sha daya suka fita sunje gidan daughter! Shine zeenat wai sede taje ta kiraki kutafi tare fawwaz yace shide ba ruwanshi dan yasan son na nan jin haka zeenat dinma tafasa zuwa kiranki " dariya sukayi atare aranta tana fadin" wato Mr azaad de kowa be bari ba " haka tayini agun ummi suna hira nan ne ummi ke sanar da ita yaran kannenta nazuwa daga dubai gobe, ba ita tabar part din ummi ba se dataji ana kiran sallah mangrib yasa ta tafi part dinta tayi wanka hade da alwala tazo ta gabatar da sallah. Shadda lace brown and golding color tasaka Riga da skirt dinkin rigar bubu ne yakawo har guiwa skirt din kuma pencil skirt gashi ta kafa dauri haka tagama shiryawa tsaff bakaramin kyau tayi ba bedroom dinshi tashiga tana adduah Allah yasa ya shirya agaban mirror ta sameshi ya shirya cikin wata hadadden yard white color, " tsarki yatabbata ga Allah Ubangijin talikai dayayi wannan halittan" abinda ko wannen su yake fada aranshi kenan ta cikin madubi yake kallonta yakasa dauke idonshi akanta juyowa yayi suna facing juna tafiya yakeyi cikin takunshi na jaruman maza ya isa gabanta jan dogon karan hancinta yayi "aucchh Mr azaad hancina " sake hancin yayi yana cewa " bana hanaki kallona ba " murguda mishi dan karamin bakinta tayi tace " to aini bakai nake kallo ba kaina nake kallo a madubi" kwaikwayan yanda tayi maganar yayi dariya yabata ganin yanda ya kwaikwayeta in tana magana, tambayar sa tayi " to yanzu ya kakajin jikin naka ?" Amsa yabata" da sauki" . harsuka fito daga part dinsu inta tuna kwaikwayonta dayayi setayi dariya, girgiza kai yayi dan yaga inta fara dariya batasan bari ba . Ahankali suke taka staircase din yana rike da hannunta, jin karan takalmi ne yasa dukkansu suka juyo suna kallonsu, hakan ba karamin dadi ya musu ba barinma yanda suka dace sosai tun kafin su karaso fawwaz yafara musu hoto tare da videos batare da sun sani ba, mutsu_mutsu tafarayi da hannunta tana son kwacewa sake rike hannun yayi kam yaki sakewa kunya ne ya cikata kamar ta nitse akasa haka takeji su abba,ummi , fawwaz,areef duk suna falon banda zeenat da zata kwana a gidan anty amina. Dukkansu murmushi ne dauke akan fuskokinsu yanda fanan ke kokarin kwace hannunta gashi Mr azaad yake sakin hannun abin yaso basu dariya sesuka danne, sallama suka musu suka fita tasowa securities sukayi dan rakashi hannu yadaga musu kawai packing space yaje yafito da motar kirar BMW baka, shiga tayi me gadi yabude musu gate harsuka iso babu wanda yayiwa dan uwansa magana. Yana yin packing akofar gidan tafito da gudu tundaga bakin gate take kwala kiran " mama!mama!mama" duk suna zaune afalo suna hira kamar daga sama sukaji muryanta ya karade gidan tagumi baba yayi Yana kallon mama yace " ohhh mamansu nikam yaushe fanan zata girmane" duka dariya sukasa fitowa ya Usman,ya al ameen sukayi , ya Usman ne yafara fitowa aikuwa tana ganinshi taje da gudu ta rungumeshi tana dariya, dariyar shima yakeyi na farin cikin ganin yar kanwar tashi. Mr azaad na tsaye abakin gate yashigo yana harde da hannunshi akirji yazuba musu ido fuskan nan ahade kamar wanda akawa mutuwa hada ido sukayi da ya usman dake rungume da fanan ganin yanayin Mr azaad abin yabashi dariya domin babu abinda yake hangowa a kwayar idon Mr azaad daya wuce wutan kishi , kamar ancewa fanan ta kalli bakin gate aikuwa karaff suka hada ido dashi mugun kallo kawai yake watsa mata ba shiri ta raba jikinta dana ya usman, kwafa yayi yawucesu yashiga falon suka gaisa da mama da baba cikin girmamawa sosai suke alfaharin kasancewar Mr azaad a sirkinsu da suna tunanin wani rayuwa yarsu zatayi tare dashi saboda ko fuskanshi kadai mutum ya kalla yasan mutum ne me tsatsauran raayi da rashin magana amma bayan aurensu da kwana biyu yazo gidan kusan duk bayan kwana biyu se yazo gidan gaishesu amma betaba fadawa fanan yaje gidansu ba. Rungume auta tayi sosai , haka ya al ameen ma sosai yayi murna da ganinta yana tsokananta " yar kanwa wato seyau kikayi niyar zuwa ko ?" " Ah ah fah ya al ameen" dariya kawai yayi, sake auta tayi ta cigaba da kwalawa mama kira harta shiga falon fadawa jikin mama tayi ta rungumeta sosai tana fadin " mama na nayi missing dinki sosai" " kai!kai fanan kede bazaki taba girma ba mutum kullum ace baya girma dagani karki karya ni" shagwabe fuska tayi ta daga maman tana " yanzu mama bakiyi kewata ba " ganin yanzu seta farawa mutane kuka yasa mama tace " ah nikuwa nayi kewarki shagwababbiyata" dariya tayi ta sake rungumeta yau wani irin annashuwa take cikj na ganin iyayenta, haka taje gun baba tagama mishi shagwaba dariya kawai yaitayi yana kallonta yana jin wani irin daci aranshi babu yanda suka iya dolene seta tafi inde bata tafi ba sede wani ikon Allah shafa kanta yayi yace" Allah yamiki albarka ya kare mana ke da karewarsa " duka suka amsa da abin. haka suketa hiransu dukda Mr azaad ba wani gwanin magana bane amma yau yadan sake wani yabada amsa wani kuma yayi shuru tashi tayi tashige dakinta dan tasan suhaima na ciki tana wayar jaraba kilama batasan tazo ba , aikuwa kamar yanda tayi hasashe tana ciki tashige bargo ta kashe murya tana waya da masoyinta , tsalle tayi tadira akanta afirgice suhaima tamike ganin fanan yasa tasa ihu suka rungume juna. cire wayar fawwaz yayi daga kunnenshi dan yaji muryan fanan murmushi yayi kasa_kasa yace " kai matar babban yaya da baby se adduah" lura da yayi suhaima tamanta da suna waya sun baje da hira yasa yakatse kiran. Shuru_shuru fanan bata fito ba se zuba ido yakeyi yana jiran tafito duk cikin abubuwan tabawa da mama ta kawo mishi drinks da fruit kawai yataba, suma yar hira sukeyi sama_sama da ya usman da ya al ameen kirane yashigo wayar ya usman ya mike yayi waje , picking yayi yanata hello hello bayajin me maganar network ya hana bude gate yayi yafita waje .

Magana yakeyi da yaron shagonshi idonshi ne ya sauka akan khairatyyy dake tsaye ta bashi baya iska se kada kayan jikinta yakeyi da dogon gashinta dayake sharan kasa, yanayin de abin tsoro in bil adama yagani amma ya usman de kara burgeshi tayi babu wani fargaba ko tsoro ya nufeta yatsaya abayanta tun fitowarshi a gida take sane dashi awajen amma batayi tsammanin har yanada karfin guiwan tunkaranta ba domin duk wani bil adama dayayi gamo da ita mugun firgita yakeyi amma shi meya taka haka , batare da ta juyo da gangan jikinta ba tajuyo da kanta kadai fuskanta ba alamun dariya ko wasa idon nan manya_manya dasu tace " meya kawo ka nan kazo ka tsareni da ido babu ko tsoro a tattare dakai " dariya ya usman yayi ganin tadage ita adole seta tsoratar dashi bata san son dayake mata ya kore duk wani tsoro da firgici ba , ganin yaki ce mata komai yakafeta da ido yana murmushi ne yasa ta murguda mishi baki tace " kabari banaso kadena kallona kokuma in hukuntaka" shi komai tayi kyau take mishi dakara burgeshi " kin taba kallon wanda yaji tsoron abinda yakeso ?" yamata tambayar yana kallon cikin manyan idonta dasuka zarce na bil adama, kara zaro su waje tayi tajuya ta kalli gaba daya arean dan tabbatar da babu wani jinni kana nan yaran aljanune kawai suke wajan suna wasa , kasa kasa tayi da murya tace " baka da hankali ne? kokayi hauka ne? kode bakasan nidin wacece bace kakemin irin wannan banzan maganar to koda wasa kar kasake insake jin irin wannan maganar abakinka in bahaka kuwa ze iya yuwa inyi ajalinka " tunda tafara magana yake kallonta sake matsowa daff da ita yayi yace" to aini hakan zezamo abin alfahari agareni ace wacce nakeso ce ta kasheni! balle ma nasan ke ba muguwa me cutarwa bace khairatyyy kiji tausayina kisoni kamar yanda nake sanki dan Allah " yafada yana hade hannunshi duka biyu yana rokonta , dafe kai khairaty tayi yau taga takanta duk iya yanda zatayi ta fahimtar da ya usman kancewa babu maganar soyayya tsakaninsu saboda sudin ba jinsi daya bane amma yaki fahimtarta . Sosai yabata tausayi tabbas ta yarda da irin son da yake mata amma dolene tunkafin yayi nisar da bazeji kira ba ta dakatar dashi , godiyarta daya tasan duk abinda suka tattauna sarauniya taji. _____ zuruf fanan dake hira da suhaima tamike domin duk maganganun da ya usman da khairaty suka tattauna akan kunnenta tana jinsu fitowa tayi daga dakin ganin haka yasa suhaima tabi bayanta ,suna zaune afalo sukaga tafito da mugun sauri kamar zata tashi sama hannu daya Mr azaad yasa yariko ta dan sun lura ba lafiya ba irin yanda tafiton nan duk tunanin su wani abunne yake faruwa, Mr azaad ne yafara magana " lafiya fanannnn ina zakije kike wannan saurin haka?" Ajiyar zuciya tasauke seyanzu ta lura a irin yanayin da tafito ko dankwali babu akanta gashi sun fara tunanin wani abu rike hannunshi tayi suka zauna akan kujera batare da tace musu komai ba ta daga kai ta kalli sama tace " khairat kizo keda ya usman yanzun nan " gaba daya lamarin yadaure mata kai taya akayi har ya usman yafada soyayya da jinsin daba tashi ba, ana haka yayi sallama yashigo yazauna kallonshi kawai fanan takeyi tama rasa mezata ce mishi " kallon bakin kofa tayi tace" kishigo kema " bayyana khairaty tayi taxube akan guiwowinta tagaida sarauniya,umarni fanan tabata data zauna itama, zama khairaty tayi tana satan kallon sarauniya sude da basu san meke faruwa ba sun kasa kunne da sunji abinda fanan zata fada. Gyara murya tayi kafin tace " khairat meye hadinki da ya usman danaji zancen soyayya natashi " dafe kirji mama tayi tace " so me? Kamar de kunne na ne beji dede bako?" alama baba yamata da tayi shuru su gama jin me fanan zata fada sukansu abinda yabasu mamaki amma banda ya al ameen daya san dama zaa rina. ______ kanta na kallon kasa tace" yake sarauniya bantaba sanin da wannan labarin ba se dazun yake sanar dani babu irin fahimtar dashi da banyi ba amma yakasa fahimtar babu wani soyayya atsakanin mu saboda mun kasance jinsi daban daban" sun gamsu da maganar khairatyyy . maida kallonta fanan tayi kan ya usman da har time din idonshi na akan habibiyarshi khairaty " ya usman kabar wannan maganar saboda babu aure tsakaninka da khairaty kai bil adama ne itakuma jinnu ce hakan baze taba yiwuwa ba " hararanta yayi yace" fanan wallahi inasonta ni ahakan na amince zan aureta " daka mishi tsawa baba yayi kafin yadaura da " usman ina maka kallon me hankali ashe babu taya zaka fara tunanin fara son abinda kasan bazaka taba samuba ko so kake ka lalata rayuwarka yar uwarka tafada maka illan hakan amma kai har kana wani cewa zaka aureta ahaka " " nooooo bazeyuba ba Ina san khairaty babu abinda ze rabani da ita se mutuwa! wallahi ba ni na daurawa kaina son taba Allah ne yadaura min bazan iya rayuwa ba in babu ita aciki dan Allah kutaimakamin ku auramin ita " ............

Tofa ana wata ga wata.😨😨

Masu comment Allah yabar kauna ina godiya sosai Allah yamuku albarka.

Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

Page 4️⃣5️⃣

Abinda be taba faruwa ba a tarihin agidan yau shine yafaru , ko da wasa basa yiwa iyayensu musu akan duk abinda zasu zartar amma yau ya usman ne da kanshi baba yayi magana yana cewa bazeyuba tabbas yayi nisan da bazeji kira ba soyayya yariga da yarufe mishi ido,yanzu duk abinda zasu fada baze taba sauraran su ba , babban abinda fanan take tsoro kenan dan tasan so mugun abune in mutum ya fada tarkon so tofa komin munin abu baze taba gani ba gaba daya tausayinshi ne yakamasu dan sun san ya daukowa kanshi dala ba gammo ne hakan baze taba faruwa ba bil adama da jinni. Mama kam tsaban takaicin daya cikata ma ka sa magana tayi da wanne zataji, da tafiyar fanan zataji ko kuma da abinda ya usman ya jajibo musu . Cikin kwantar da murya baba yace " usman yanzu zaka fara bijire min kenan saboda so ya rufe maka ido ? Kasan bazan taba hanaka duk wani abu ba sede inde yakauce hanya hakan kuma bazan taba lamunta ba daga yau kama fara tunanin cireta aranka dan ba samunta zakayi ba nagama magana " ya usman dafe setin zuciyarshi yayi da yakeji kamar ana watsa mishi wuta dan bala'in zafin da yake mishi murya na rawa yace " baba bana fatan ranar da zezo inzama mara biyayya ga iyayena! Amma zanso kuji abinda nakeji wallahi baba in ban samu khairat ba mutuwa zanyi, ku taimakeni kumin wannan alfarman" ya matukar bawa Mr azaad tausayi bama shi kadai ba duk wani wanda yake falon seda ya kashe musu jiki mikewa Mr azaad yayi yarike hannun ya usman suka fita waje. Sallamar khairatyyy fanan tayi nan take ta bace azuciyar fanan kuwa tana tunanin abinda yakamata tayi dan ceto dan uwanta. Auta kam duk abinda akeyi se binsu da ido takeyi kasancewar takan fahimmci wata maganar wata kuma bata fahimta saboda kananun shekarunta ,ta riga da tagane duk wannan maganar akan khairaty ce da ya usman inde ta ita zaabi khairaty tayi mata kyau sosai, ( kuji auta fah ahhh lallai yaro yarone) fanan da ya al ameen ne suka kwantar wa su mama hankali akan zasuyi iya kokarinsu domin ganin ya usman yacire khairaty a ranshi, kirane yashigo wayar suhaima ganin sunan "my hubby" yabayyana akan screen din ne yasa tabar falon tashige daki.

Readers Also Read